Allah ya saukawake." Da kai ya amsa mata don baya jin zai iya bude baki ya yi magana, a rude Fatima ta shiga jeromai sannu, da kai ya ke amsa mata, tuni idanunta ya ciki da kwalla, da hannu yayi musu alamar su tafi kawai, jiki duk a sanyaye suka mike, har sun kai kofa, cikin wata irin wahalalliyar murya ya kira sunan Fatima, duk dakatawa suka yi, ya ce "Kar ki gayawa Ummi halin da nake ciki bana son hankali ta ya tashin, kin ji ko. " ta gyada kai tana sharar kwalla, cikin shesheka ta ce "Yayana to kasha magani." Ya ce "zan sha yanzu nan." Ta amsa da "Toh ."suka fice.
Da kyar Amira ta tafi gida ranar, barci kuwa kaurace mata ya yi juyi ta dinga yi, tana ji kamar ta koma ta kara duba shi duk da dare ya tsala, karshe dai ta lallaba tayi alwala ta yi nafila ta shiga nema mishi sauki a wajen Allah, tare da mika nata kokon baran.
Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda yake ciwon shi bai taba tashi da karfi irin na yau ba,ya sha maganin shi amma a banza, jarumta ce kawai ta hana shi sumewa a cikin daren nan.....
*Jama'a masoya masu bibiyar littafin JOY, pls Ku kara hakuri da ni, wallahi kwana biyu nan nayi busy da yawa, amma insha Allah zuwa ranar Monday komai zai daidaita daga ranar zaku dinga samun update kullum, harda weekend bi iznillah na muku alkawari ni dai kawai comment dinku da addu'ar Ku nake bukata, sai kuma shearing fisabilillah* 🙏
[12/29, 2:39 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
DAGA ALƘALAMIN
*AyshaNalado*👉
ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiya Writers Association*
*PAGE 21*
Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda yake ciwon shi bai ta6a tashi da k'arfi irin na yau ba,ya sha maganin shi amma a banza, jarumta ce kawai ta hana shi sumewa a cikin daren nan, wani irin hank'oro had'i da jijjiga jikinsa ke yi masa, babu abin da yake muradi irin ya samu biyan bukata, rashin samun hakan ya haifar masa da mummunar zazzabi, tare da matsanancin ciwon mara, duk dauriya da jarumtar Al'ameen sai gashi yana zubar da hawaye yana mulmula a tsakar d'aki, tare da rok'on Allah ya d'auka ranshi ya huta.
A 6angare d'aya kuma shaidaniyar zuciyar na masa zuga tare da bashi gurbatacciyar shawara akan ya ta shi kar ya yarda ya hallaka kanshi, ya samarwa kanshi sauki ta kowacce hanya, ta shiga zano mashi hanyoyin mafi sauki da zai bi ya samu cikar muradin gangar jikinsa.
Dakyar da taimakon Allah wani wahalallen barci ya sure shi ba tare sa zato ko tsammani ba.
Kimanin awa biyu ya kwashe yana barcin wahala, wani irin azababben murdawar da mararsa tayi ya tilasta masa farkawa a zabure, cikin fitar hayyaci da rufewar idanu ya rarumi sacet din maganin shi da ke yashe a gaban katifarsa, guda uku ya 6alla ya watsa a baki, daga kwancen da yake ya d'auki ledar ruwa ya kora. Komawa yayi ya kwanta lamo ya lumshe rinannun idanunsa yana sauke wani irin wahalallen numfashi mai fita tare da hucin zazzafar zazzabi, hannyen shi duka biyu dafe da mararsa. Jinsa yake kamar a duniya, kamar matacce kamar yarayye shi sai gashi na, sai dai duk da haka bakinsa bai yanke da ambaton Ubangiji ba.
Wani haske ne ya mamaye idanunsa, da sauri ya rintse idanu saboda sun gaza daukar hasken, bayan wasu sakonni ya bud'e su a hankali har ya gama waresu, bai san tahowarta ba bai san ta ina ta shigo d'akin ba sai dai kawai ya ganta a agaban shi, sanye da fari kar d'in dogon riga mai sulbi da taushi. Fuskarta ya kurawa idano yana son gane ko wacece, amma ya kasa saboda rufe shin da tayi da farin mayafin rigarta kamar nikab, banda kwayoyin manyan sexy eyes din ta babu abin da yake iya gani, a gaban shi ta tsuguna, tare da sanya kwayar idanunta cikin na shi, a hankali da wani irin tattausar murya ta furta cikin rada "I Luv u Ameen, zan kareka da dukkan karfi da iyawata, ruhina da naka suna tare tun fil azal, zamu rayu a tare bakin rai bakin fama nice cikon farin cikin rayuwar ka kuma nima kaine farinciki na." Wani dakowa zuciyar shi ta shiga yi har ya kai ga kirjin shi na sama da kasa kamar mai shirin barin duniya, kallonta ta mayar kan kirjin, na wasu sakonni, a hankali ta dago hannunta masu dauke da Zara zaran faratuna ta daura akan kirjin shi ta shiga balle boturan rigar.
Wurgi tayi da rigar bayan ta zame shi a jikinsa, faffadan kirjinsa ya bayyana mai dauke da tattausar kwantaccen bakin gashi.
Kamar an kwato zancen daga bakin shi cikin rarrabewar harshe ya ce "Wa ce ce ke?" Murmushi ta saki a hankali ta ce "FARHAT."
Bai yi aune ba ya ji ta fada jikin shi gaba daya tare da bashi wata irin runguma, wani irin karkarwa jikinsa ya shiga yi.
Sark'ewa nunfashinsa ya fara yi lokacin da ya ji tattausar tafukan hannayenta a gadon bayan shi tana shawafa, wani irin karfi ya ji ya ziyarce shi, yunkura yayi ya yi wani juyi, ya mirginata kasan shi ya dawo samanta kamar mayunwacin zakin daya dade bai ci abincin ba, ya samu daga sama haka ya shiga yamutsarta, laushi hadi da taushin fatar ta tare sa wani irin mayataccen kamshin da jikinta ke fitarwa suka hadu suka kara zautar da shi, cikin zafi da fitar hayyaci ya ke bin duk wani sakon jikinta da wani irin romance wanda bai san yaushe ya koya har ya iya ba. Lokacin daya isa inda yake muradi, ihu ya takarkare ya yanka saboda jin shi a wata duniyar da gangar jikin shi ya dade yana muradi, da taimakonta ya samu satisfaction koro na farko a rayuwar shi.
Cikin karkarwar jiki da gushewar hankali ya juye mata duk lalurarsa. Kwanciya yayi lamo a jikinta tare da kamkameta kamar zai maidata cikinsa, ya shiga maida wahaltaccen numfashi, jin shi yake sakayau kamar jariri sabuwar haihuwa.
A lokacin ya farka daga nannauyan barcin daya kwashe shi bayan ya yi overdose!
A hankali ya ware idanun shi, yana bin dakin da kallo, akan labbansa ya furta dream! Tabbas mafarki yayi, mafarki mai cike da rudani.
Abin mamaki Normal ya farka babu wani ciwo a jikinta sai rashin kwarin jiki, don a lokacin ko dan yatsarsa akace ya daga bazai iyaba.
Lamo ya kwanta brain din shi na sake tariyo masa mafarkinsa, me yasa baiga fuskarta ba, mai yasa duk irin abinda ya faru nadin fuskarta ko gezau bai yi ba, wacece ita. "FARHAT."
Zuciyar shi ta bashi amsa, "FARHAT." Ya sake maimaitawa sunan a bayyane, wani irin damuwa yaji ya mamaye zuciyar shi, kar sai ace aljana ce ta Aureshi. Tabbas! Abin tayi kama da apmara ko tasuniyar gizo. kafin yayi aune ya ji ladan ya rangad'a kiran sallar farko.
Ga al'adarsa ta yau da kullum, da anyi Kiran sallar farko yake tashi, yau ma bai bari shaidan yayi tasiri akansa ba, bakin shi ya samu da furta adduar tashi daga barci tare da Karin wasu addu'oin, wani karfi yaji ya shige shi, yunkura yayi ya mike zaune, rass! gaban shi ya fadi, ta yaya zai gusar da najasar jikinsa ba tare da Ummi ta sani ba yana matukar kunyarta baya so ta yi wani tunani akan shi, take duk karsashin daya ta shi da shi ya ji ya ragu.
Jiki babu kwari ya mike tsaye, cike da kyankyamin jikin shi ya dauki buta da jallabiyarsa wankakke da short ya dauki kuma extra leda da zai saka short din jikinta idan ya cire, daga haka ya fice daga dakin zuwa cikin gida, ya saba buga ma su Ummi kofa kullum daya fito amma yau direct toilet ya wuce, cike da kyankyami da taka tsantsan ya kwabe short din jikin shi ya saka a Leda ya kulle, sannan ya cire riga.
Duk sanyin da akeyi bai ji ba haka ya rintse idanu ya tsarkake jikin shi, a hankali cikin taka tsantsan don kar kwarafniyar shi ya farkar da Ummi ko Fatima.
Jallabiyarsa ya sako baya ya kammala wankan, sai da ya gabatar da alwala a tsakar gida, ya mayar da butar shi da kayan shi daki, sannan ya tukarin dakin su Ummi, kamar ya kyale su ranar don gani yake kamar zasu iya gane wani Abu, dakewa yayi ya karasa bakin kofar ya bubbuga musu, sai da Ummi ta amsa sanna ya tafi masallaci.
Koda suka idar da sallar subh, samun waje yayi a masallaci ya zauna yayi addu'oinsa tare da karatun alkurani, don ya tabbata idan yake gidan ya kebe tunani bazai bar shi yi ba, sai da gari ya fara haske sannan ya fito ya nufo gida.
Sallamar shi ya fito da Fatima sake kitchen tana wura charcoal da sauri, cikin raunatacciyar murya ta ce "Yaya Ina kwana ya jikinka, tun dazu nake duba dakin ka baka dawo ba." Murmushi ya sakar mata tare da matsawa gabanta ya kama kumatunta ya dan ja da sigar wasa ya ce "Fatiman Yayanta." Dagowa ta yi ta kalleshi da idanunta da sukayi yi raurau da hawaye ta ce "Jiya dakyar na yi barci saboda tunanin halin da na barka ciki Yayana." Cike da so da kulawa ya ce "Na ji sauki sosai kanwata baki gani ba." Ta gyada kai hawayen daya taru a idanunta na sakkowa, ya ce "Kukan fa Bintan Ummi, oya share wahayenki," da Saudi ta share ya ce "then smile." Murmushi ne ya subuce mata, shima murmushi tayi ya ce "Da fatan baki gayawa Ummi ba." Ta girgiza kai alamar A'a ya ce " Yawwwwa! Gud gal! Ci gaba da aikin ki bari in gaisa da Ummi inzo in tayaki." Daga haka ya nufi dakin Ummi, a falo ya sameta karamin kur'ani ne a hannunta tana karanta suratul kahfi. Wuri ya sama ya zauna yana saurrenta wani natsuwa na huda zuciyar shi, sai da ta kai karshen surar tayi addu'arta ta shafa sannan ta juyo ta kalle shi da kulawa, murmushi dauke a fuskarta.
A ladabce ya duka gabanta ya sunkuyar da kai, ya ce "Ummina ina kwana."
Cike da alfahari da kasancewarsa d'a a gareta ta ce "Lafiya kalau alhmdllh Amintacce, da fatan kai ma haka." Bayan gaisuwa zama yayi su ka dan taba hirar duniya.
kallon agogon yayi ganin bakwai da rabi ta yi, ya mike ya ce "Ummi bari na je na kimtsa yau ina da lecture safe." Ta ce "Allah ya taimaka, Allah ya yi albarka ." ya amsa da "Amin Ummi." Sannan ya fito, sharar tsakar gida ya tarar Fatima na yi, ya ce ta kawo ya karkare ta kama wani aikin kememe ta ki yarda wai ya je ya huta bashi da lafiya.
Yana saka kai a kofar shiga zaure su ka zabga karo. Taga-taga ta yi zata fadi, da sauri ya rikota, Zazzare idanu Amira ta shiga yi cike da kunya, bata taba tunanin zata same shi tsaye haka akan kafafafun shi ba, saboda yadda ta barshi, tun asuba take son shigowa ta ganshi tana tunanin idan shigo, ta ce musu meya kawota, yanzu tana zaune ta ji mamanta zata yi aike wajen Ummi tayi caraf ta amsa ta ce bari ta kai.
Sake ta yayi ta tsaya akan kafafunta ya ce "Ki dinga kula mana, ina kike kallo haka?."Cikin inda- inda ta ce "ina kwana Yaya Ameen, ya karfin jiki." Babu yabo babu fallasa ya amsa mata da "lafiya jiki Alhmdllh." Ya rabata ya shige dakinsa, yana shiga daga bakin kofa yaji ya taka Abu kamar takarda, kallon shi ya kai wajen, paper ne a nannade, da mamaki ya tsuguna ya dauka tare da budewa da sunan ta idanun shi ya fara tozali. Cike da dumbin mamaki ya furta "What!!! Amira!".........
Ga mai bukatar shiga group ya tuntunbeni kai tsaye.
09116099486.
[12/29, 2:39 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
DAGA ALƘALAMIN👉
*AyshaNalado*
ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉
*Mikiyi Writer's Association*
*PAGE 22*
Dunk'ule paper n ya yi bayan ya gama karanta abin da ya k'unsa, ya dafe goshi cike da takaici, ko kad'an bai ji wani karsashi ko shauk'i game da kalamanta ba, sai ma ganin tsananin wautarta da shirmenta da ya yi, dama he is wonder yadda ta ke yawan kallon shi ashe da dalili, guntun tsaki ya ja, ran shi duk ya 6aci, cike da takaici ya ce "Yara tun baku tafasa zaku k'one!" Wurgi ya yi da paper'n ya shiga kimtsa d'akinsa, tattara komai ya yi, ya shere d'akin tass! kamar yadda ya saba, wurin tattara shara ya sake cin karo da paper n kamar ya share da shi ya zubar sai kuma ya dauka ya warware ya linke, zai ajiye saboda evidence, gurin da tarin littfansa suke ya nufa, ya dauki wani babban textbook da yake saka paper's ya bud'e da nufin ajiye wa a ciki, karaf! ya bud'e dai-dai page d'in da ya ta6a ajiye letter n Joy, gaban shi ne ya yanke ya fad'i, kurawa latter n idanu ya yi, brain din shi na tuno masa abin da ya faru tsakanin su rannan' lokacin da take sand'a da za ta shiga gidansu, yadda ta firgice daga jin muryarsa kadai, yadda ta riko kafafunsa tana rokonsa, yadda ya fisge kafarsa da k'arfi ta fad'i ta fasa goshi, yadda ta mik'e tana hawaye ta kakka6e jikinta, ta tashi tana tafiya a slow, bin bayanta da ya yi, guduwan da ta yi ta barshi a tsaye rik'e da handkerchief, k'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya sauk'e. Hakan na nufin bata yafe masa ba fa kenan, take jikin shi ya yi mugun sanyi, hakika ya cutar da ita, kuma he regret, zai yi kok'ari ya gyara kuskurensa.
Latter n ya d'auka ya koma bakin mattress d'insa, ya warware yana bi da kallo tare da sake karantawa, yana maimaitawa, zuciyarsa na k'ara shiga matsanancin tausayin yarinyar kamar yadda ya fassara lamarin.
Bai san adadin lokacin daya 6ata a haka ba, ya tsinkayi sallamar Fatima a k'ofar d'akin shi, da sauri ya linke wasikar, ya tura karkashin pillow, sannan ya bata izinin shigowa, kayan breakfast d'in shi ne ta kawo, guri ta samu ta ajiye, godiya ya mata, sannan ya tsareta su ka yi breakfast d'in tare. Yana ta so yayi mata zancen Joy zuciyar shi na hana shi, a haka su ka kammala, ta kwashe kayan ta mayar cikin gida shi kuma ya d'ibi ruwan wanka ya shiga.
Har ya yi wanka ya shirya tunanin Joy ya ke, da kyar ya yakice ta a rai ya samu ya fita, school ya tafi daga can kuma bai dawo gida ba, ya ta fi harkar kekensa.
Karfe takwas ya shigo gida, as usual su Ummi na tsakar gida, nan ya zauna su na shan iska, a nan ya ci abincin suna sauraren shirin kwarmato! A redion Ummi abin mamaki ranar Amira bata shigo karatu ba, Ummi ta ce "Wai ni kam yau banga Amira ba tun safe ko lafiya? " Fatima ta ce "Nima Ummi wallahi tun d'azu abin ke raina."Ummi ta ce "Allah dai yasa lafiya, da safe idan Allah ya kaimu sai Ki dubo mana ita." Al'ameen na jin su bai saka musu baki.
Hira suka shiga yi, sai sha d'aya saura suka ta shi lokacin tuni Fatima ta yi barci. Shi ya kwashe tabarman bayan sun ta shi, sai da ya d'aura alwalar barci sannan ya nufi d'akinsa, shafa'i da wutiri ya gabatar, ya rage kayan jikinsa ya haye katifarsa, sai dai me! Tunanin yarinyar ne ya yi wa kwakwalwarsa kawanya, ya rasa me yasa ya damu da ita cikin y'an kwanakin nan, tun ranar da abin nan ya faru bai ta6a wayar gari ba ta fad'o masa a rai ba koda sau d'aya ne, tausayinta ya ke ji kamar me, sai dai ya alakanta hakan akan abin da ya gifta tsakanin su ran nan, hakan yasa ya daura damaran gyara kurensa, ya dauki tsawon lokaci kafin barci ya d'aukesa.
Cikin barci yaji yanayin shi ya fara sauyawa, tun yana d'aurewa har sai da da ya kai ga bud'e idanu, "Allahumma ajirni fi musabati! Hasbunallahu wa ni'eemal wakeel!" Ya shiga maimaitawa, iya hasashe babu wani abu daya faru cikin abubuwan da ke tasar masa da ciwonsa, babu ruwan sama babu sanyi a garin hasalima zafi ake yi saboda kwallara ranar da akayi a yinin ranar, bai shaki wani abu makancin kamshi ba, bai ga wani sura ko wani abu da zai iya daga mashi hankali ba, to menene dalili?
Jin abin na k'ara yawa yasa ya yi ta maza ya d'auko maganin sa ya 6alla sai dai ko gezau, sai ma ci gaba da hauhauwa da abin ya k'ara, hankalin sa ya ta shi mak'ura, abin da ya lura yanzu tab! 'Din ya daina mishi aiki ma, kardai maganar Dr Abdul ne ya tabbata.
Tuni ya fara ficewa a hayyacinsa, sharkab ya had'a gumi, jikin shi na karkarwa tare da soma daukar zafi, gefe guda ga mararsa da yayi wani irin kumburi ya yi tauri had'i da k'ullewa, numfashi ma dakyar ya ke iya ja da saukewa.
Cikin lalube da malelekuwar da yake yi, hannun shi ya sauka akan sachet din maganinsa, kamar jiya, wawura yayi ciki rufewar ido ya 6alli uku ya watsa a baki.
Da farko kamar ya k'arawa ciwon karfi, don sai da ta kai shi ga fara mirgina a tsakar d'aki.
Kimanin 15 minute ya kwashe a haka, kafin kuma ciwon ya fara lafawa, dakatawa ya yi da mirginan ya yi lamo yana sauke numfashi, a hankali komai ya tsaya cak! Kamar an yi ruwa an d'auke, kumburin maran ya sace, sai dai duk da haka jikinsa na nan da zafi rau, a haka wani wahalallen barci ya kwashe shi.
Kiran farko ya farka as usual, Alhmdllh! Zuwa lokacin zazza6in ya sauka, babu wani alamar ciwo sai idanunsa ne kad'ai su ka nuna, zaune yayi a bakin katifarsa zuciyarsa cike da damuwa, sachet d'in maganin shi dake yashe a k'asa ya dauka ya tsurawa idanu yana kallo, tsakanin jiya da yau ya sa guda takwas, abin da ake shan d'aya d'aya, kuma ba kullum ba don da sai yayi sati biyu uku bai sha ba, hakan na nufin d'aya ya daina mishi aiki ke nan, tabbas akwai gagarumin matsala, dole ya koma wajen Dr Abdul, amma kafin nan yana bukatar shawara, yana bukatar shearing din matsalarsa da wani, wayar sa ya d'auka ba tare da la'akari da lokaci ba ya dan nawa Aliyu kira.
Ringing biyu Aliyu ya daga, tare da sallama, Al'ameen bai taba kiransa a irin wannan lokacin ba, cikin dan tashin hankali ya ce "Ustaz lafiya, hankali ya ta shi da naga kiranka a irin wannan lokaci." Numfashi ya sauke kafin ya ce "Aliyu ina cikin damuwa."
"Subhanallah! Me yake faruwa Ameen? Bai amsa mishi tambayar shi ba, ya daura mishi da wata "Yaushe zaka dawo? Maganar bata waya ba ce." Jim! Aliyu yayi kafin ya amsa da "Zan kai karshen wata, ka fa'di ka d'an daga damuwar ka abokina zaka ji sauki." Girgiza kai Al'ameen yayi kamar suna kallon juna ya ce "Sai dai ka dawon zan kira ka." Daga haka su ka yi sallama jikin Aliyu duk a mace, ya san halin Al'ameen ba tun yau ba, tun da ya bukaci su tattauna akan matsalarsa to ya tabbata babbar matsala ce, zai yi duk yadda zai yi ya samu ya koma gida a karshen watan don su zanta kuma zai taya shi da addu'a Allah ya kawo ma shi d'auki.
Tun daga wannan rana kusan kullum sai ciwon shi ya ta shi, walau da sanyi ko babu, taimakon shi daya bai tab'a tasar masa da rana ba, sai dai wani lokacin tun da yamma zai fara jin alamun shi, da yaji haka ranar da wuri yake komawa gida da ya yi isha kuma yake shiga d'akin shi ya kulle.
A bangare daya ga damuwar FARHAT zuwa yanzu kusan sau hudu yana yin mafarki da ita, tana maimaita masa kalamanta na ran nan, sai dai har zuwa yanzu bai yi nasarar ganin fuskarta ba duk irin kwakwanshi da son ganin hakan, lamarin yana matukar damun shi. Duk wannan matsanancin yanayin da ya shiga bai manta da Joy ba, sai dai idan bai samu sarari ba sai ta fado masa a rai, ya kan alakanta hakan da cutar da ita da ya yi ran nan kuma yana fatan ya samu damar da zai nemi yafiyarta.
*****************
Kamar yadda Al'ameen ke cikin damuwa haka a bangaren Amira, zuwa yanzu ta daina zuwa daukar karatu kasancewar tuni sun fara exam, sai dai kusan kullum tana gidan, bata da aiki sai ajiye masa wasika, a mabanbantan wurare amma koda wasa, Al'ameen bai taba daga ido ya kalle ta ba balle ya nuna ya san da zamata, tuni ta fara rama a tsatsaye kasancewar so ne take masa mai girman gaske, abin na matukar damunta, ya haifar mata da damuwa da duk wani wanda yake makusancinta zai lura, baga iyayenta ba hatta da Ummi da Fatima sun fahimci tana cikin damuwa, sai dai banda Allah! da Zainabu babu wanda ya san halin da take ciki sai ko Al'ameen, wanda shi kuma damuwar gaban shi ta sha kan shi, kwata kwata bata gaban shi , don tun yana bude wasikun shirmenta acewarshi yana karantawa har ta kai ga ya dai na budewa idan ya gani sai da ya dauka ya ajiye ba tare da ya bude ba.
***************
*JOY*
Cikin abin da baifi wata daya ba soyayya ta gama ragargaza jini da bargon jikinta, i zuwa yanzu bata ji bata ganin komai sai Yayan Fatima, tun tana karyata zuciyar ta akan lamarin har ta yi surrender.
Sai dai takan shiga matsanancin damuwa, hankalinta kan tashi a duk sanda ta hango k'urar dake tafe da lamarin, ta ko ina idan ta hanga ta hango babu sauki, baga Al'ameen ba baga Mom da sauran ahalinta ba, har Papa bata tunanin a wannan karon zai kalle ta da idon rahama, a duk sanda tayi irin wannan tunanin takanyi kokari ta yakice shi daga zuciyar ta amma ina! Abin ya ci tura, kullum sai Dada hauhawa ya ke kamar farashi.
Gaba daya ta koma so silent, bata da aiki sai rubuce rubucen kalaman soyayya, sai ko kuka da ya zama mata kamar ibada, tuni ta yi rama ta dishe.
kwarafniyar Anty Esther tuni sun daina gigitata, gani take hargagin Mom da anty Esther ya fiye mata sauki akan tashin hankalin dake tunkarota, zuciyar ta na daf da yi mata bore, sai dai ta lashi takobin ko zata mutu bazata ta6a bata dama ba, don tana ganin yin hakan tamkar tarwatsa rayuka ne, gara ita nata rauyuwar ya tarwatse.
Tuni anty Esther ta bata wayarta, sai dai abin mamaki tunda ta karbu wayar Papa bai taba kiranta ba itama idan ta kira shi baya dagawa, idan ya daga ma da sun gaisa sama sama zai kashe gaba daya ya dena nuna mata kulawa kamar da. Bata wani dauki abin serious ba ta mishi uzuri don a ganinta aiyuka ne suke sha kan shi.
A cikin wannan dan tsukin girgin su Mom ya yi dirar mikiya a 9ja, ko gezau bata yi, babu yabo babu fallasa a tare da ita, suka dunguma ita Anty Esther, David, zuwa airport don tarbota, babu wani karsashi ko kewa a ranta su ka iso, lokacin tuni jirgin ya sauka, da sauri Mom ta iso gareta tare da rungumeta, lamarin ya dan so ya daure mata kai, amma tuna yadda Mom dinta ke matukar kaunarta, ada kafin ta soma canzawa yasa ta saki jiki itama ta rungumeta, cikin kunnenta Mom ta rada mata "I missed u a lot daughter." "I missed u 2 my Mom." Ta amsa mata.
"Ki yafe min abubuwan da suka yi ta faruwa a dan kwanakin nan, kuskurene." Hawaye ta ci ya ciki mata idananu, "take daskararriyar soyayya ta fara narkewa." Tsaki Anty Eshart ta za a bayyane, tare da kauda kai zuciyar ta na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 22