Share this page
makara, sai ki shirya amsan punishment." Ba tare da wani damuwa ba ta ce "Ai na shirya." Fatima ta ce "OK I see." Da haka suka kama hanyar school hannunsu rike dana juna suna fira suna kwasar dariya cike da nishadi hankali kwance, duk da ita Joy tsoron al'ameen bawai ya gama sakin ta bane, da ka gansu zaka hango yadda suke tsananin kaunar juna. Kamar yadda suka tsammata kuwa sun tarar ana kama late comer a bakin get ana musu bulala, sosai Fatima taji babu dadi a ranta dama abin sa take gujewa Joy kenan, amma ta lura ita Joy din babu alamar damuwa ko nadama a fuskarta. Koda suka Isa class har teachern da zai dauke su first period ya shiga class kasancewar sa ba mai tsauri ba yasa excuse kawai suka dauka ya basu izini suka shiga ciki. Suna shiga idanun Joy ya sauka akan na David daya zubo musu ido yana kallo yana gyada kai, harara ta maka mai tare da dauke kai daga kallon shi, sit din su suka nufa Wanda yake a layin gaba suka zauna su biyu, dama bibbiyu ake zama a kowane sit. Haka sukai ta daukan karatu cike da himma da kwazo don dukan su ba baya ba wajen kokari, wannan malamin ya shiga wannan ya fita har har zuwa break time, Joy ta fito musu da su chocolate da biscuit din da ta zuba a jaka suka zauna a class suna ci suna hiran karatu, sai jin tsayuwar mutum sukayi a kansu, kusan tare suka dago suka kalle shi, harara ya fara watsama Fatima wanda itama bata yi kasa a gwuiwa ba wajen ramawa kafin cikin wani yare wanda Fatima bata ji ya fara ce wa "dama nasan gidan su wannan matsiyaciyar zakije kuma ki rubuta ki ajiye daga wannan karan kinyi na farko kinyi na karshe don sai na gayawa papa halin da kike ciki a makarantar nan kin san kuma abin da zai biyo baya, wannan ai zubar mana da Kimar family kike yi." A harzuke ta ce da harshen turanci don shi tayi ji fiye da yaren su da David ke mata magana da shi "David ka fita harkata babu ruwanka dani kayi harkan ka nayi nawa a cikin makarantar nan." Ya ce "bazan fita a harkar taki ba, kiyi abin da zakiyi." Kwafa tayi ta ce "to ka ci gaba da shiga zan yi maganin ka." "Ni dai ne zan yi maganin ki, wawiya kawai Mara kishin kanta da addininta." Yana gama fadin haka ya juya ya fice daga class din, joy taji zafin zagin ta da yayi hakan yasa a zafafe ta mike zata bishi don ta rama, da sauri Fatima ta rikota tana bata hakuri, batasan takamaimai abin da suka faɗa ba tunda da yare ne amma ta fahimci a kanta ne suke wannan cacar bakin, kamar yadda ta bangarenta Joy ke fuskantar barazana da kiyayya a wajen yayanta, haka take fuskantar kiyayya da kyamata daga wajen duk wani ahlin Joy uwa uba iyayenta. David dan uwan Joy ne cousin dinta ne, mahaifiyar shi kanwar papa ne uwa daya uba daya. Rarrashinta Fatima ta shiga yi tana bata hakuri, da kyar ta hakura ta koma ta zauna don Joy akwai zafin zuciya idan ta fusata, basu fita ko ina ba har aka dawo break aka ci gaba da lesson, har kuma akayi closing bata daina hararan David tana kwafa ba, Fatima dai sai aikin rarrashi take kasancewar tasan halin kayarta. Tare suka fito daga cikin school din kamar yadda suka saba hannun sakale da juna, sarai Joy taga driventa peter yazo daukarta amma ta yi fuska ko kallon inda yake bata yi ba saboda tana so ta jera da Fatima ,sau da yawa takance Fatima tazo su Shiga mota su sauke ta amsa ƙememe take ƙi saboda gargadin ummi. Peter bai damu ba don Inda sabo ya saba da hakan, rana daddaya ne idan yazo daukan ta take yarda ta bishi. A hanyar su sai da Fatima ta san yadda ta yi, ta mantar da Joy ɓacin ran da take ciki na David, sai gata tana dariya har da kyakyatawa. Wani me sai da yalo ne ya zo wucewa yana talla a bairo, har sun gifta shi Fatima ta ce "laaa Joy bari na sai ma yayana yalo." Kafin Joy ta amsata har ta juya ta isa gare shi, hamsin din da ummi ta bata ta mika mishi ya bata na hamsin. Dawowa Inda Joy take tsaye tana jiranta tayi cike da farin ciki ta ce "nasan yayana zaiji dadi sosai don yana son yalo kamar me." Taɓe baki Joy tayi tare da cewa "Wanna yayan naki dabe dariya bashi da fara'a ko dan murmushi ni ban taba gani yayi ba kullum yayita yiwa mutane muzurai, shine zaiyi wani farin ciki don kin sai mai yalo, ni fa shi yasa yaya ko kani basa burgeni." Wani kallo Fatima ta mata kafin ta ce "waya gaya miki yayana baya dariya, waya gaya yayana baya fara'a ina jin duk unguwar nan babu wanda ya kai yayana iya murmushi." Joy ta ce "Au haka ne fa."ta fadi maganar cikin sigar tsokana, fon ita bata yarda ba gani tke yi fatina wasa take yi, Fatima ta ce "koma me zaki ce kice, kuma da kike cewa yaya ko ƙani bass burgeki wlh don bakin hadu da irin yayana bane, ganin kamar fa da gaske take yi, yasa Joy cewa "wai da gaake kike yi ko wasa." murmushi Fatima ta yi tana girgiza kai, nan kuma ta shiga ba Joy labarin yayanta yadda yake kula da ita yadda yake sonta da yadda baya kaunar bacin ranta, tun Joy na jinta sama sama har kuma labarin ya fara shigar ta, nutsuwa tayi ya maida dukkan hankalinta tana sauraren Fatima a ranta tana mamakin abubuwan da fatima tace al'ameen nayi, ji tayi a ranta koda so ɗaya ne zata so taga murmushinsa,a haka suka iso kwanan gidan su Fatima Wanda sai an wuce shi kafin a isa na su joy, ji tayi bata son su ru don bata gaji da jin labarin ba, har kofar gida ta raka fatima sannan suka yi sallama ta kama hanyar nasu gidan. Tana tafe tana murmushi ita kaɗai tana tuna labarin yayan Fatima, da haka ta ƙarasa nasu katafaren gidan, knocking tayi, jiki na bari me gari ya bude mata yana mata sannu da dawowa, bata da wulakanci da girman kai ko kadan ita dai barta da tabara da shagwaba, hakan yasa ta sakar mai murmushi tana amsawa ta sa kai ta nufi entrance din gidan. Fuskarta cike da murmushi ta turo ƙofar falon ta shiga, a bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin iron kallon da mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani...... Me bukatar Shiva group ya tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 3* Fuskarta cike murmushi ta tura ƙofar falon ta shiga, ta na kwalama Mom kira, a bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan Mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin irin kallon da Mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani. Sai da ta hadiyi miyau mukut! Kafin ta kirkiro murmushin dole ta sakar musu , cike da fargaba ta nufi Mom don ta rungumeta kamar yadda Mom d'in ta sabar mata, hankad'e ta Mom tayi saura kad'an ta fad'i Allah ya taimaketa ta dafa kujera, cikin tsananin bacin rai ta ce "kar ki kuskura ki ta'ba ni Joy!!!" Ta karashe maganar a kausashe. A razane ta sauke manyan idanunta da lokaci d'aya suka tara kwalla a fuskar Mom, cikin karaji Mom taci gaba da ce wa "kije na yafe musu ke,tunda sun fini a ajenki kije kqai tunda ke kince baza kiji magana ba."daga haka ta mike a fusace ta bar falon ba tare da kara kallon gefen da Joy take ba. Lumshe manyan idanunta zuciyarta na wani irin tsinkewa, hakan da tayi ne yaba hawayen dake kwance a idanunta daman zubawo, minti biyu ta dauka a haka kafin ta waresu akan David dake kallonta yana sakin murmushin mugunta. Gaban shi ne ya fad'i ganin yadda lokacin d'aya manyan fararen idanunta suka rine zuwa launin jaa, take yaji wani shakkarta da tsoronta ya kama shi duk da kuwa ya girme mata don ya bata kusan shekara daya a haihuwa. Bai gama fita daga wannan yanayin ba ya tsinkayi muryarta a kunnayenshi, a kausashe ta ce "David!!! Burin ka ya cika yau ka hadani da iyayena ko, nasan kaji dadi ranka yayi maka fari ko? To ka rubuta ka ajiye na rantse da wanda ya busa min rai da numfashi sai kayi nadamar wannan abin da ka aikata." Mikewa tayi ta kama hanyar hawa upstairs. Ji yayi duk ya muzanta ida ta wuce bai mayar mata da martani ba zata ga kamar ya tsorata da furucinta ne haka yasa ya danne zuciyar shi tare da ce wa "Joy James." Da karfi, dakatawa tayi tare da juyowa suka hada idanu, takowa yayi ya iso gabanta ya tsaya, kamar zai fadi wani magana, sai kawai ya barke da wani mahaukacin dariya mai ban haushi, wani irin yawun takaici Joy ke hadiya a jejjere, ganin kuka na shirin kwace mata yasa ta juya a guje ta karkare hayewa saman bata zame ko ina ba sai dakinta kan gado ta fada tare da fashewa da kuka da iya karfinta. Mom koda ta shiga dakin ta kasa zama tayi safa da marwa kawai ta shiga yi ta kai gwouro ta kai mari, hankalinta a matukar tashe, girgiza kai tayi a bayyane cikin irin yaren da David yama Joy magana d'azu a school ta shiga ce wa " meke shirin faruwa da ni ne ni Alice, kardai asirin da na rufe tsayin shekaru goma sha biyar ke shirin tonuwa, tabbas ya kusa tonuwa." Bango ta kai ma duka kafin kamar zararriya ta ce "Ina!!! Ba zan taba bari hakan ya faru ba indai na haifu cikin pastor Samuel da Mrs Deborah." Da sauri ta rarumi wayarta ta danna ma wani lamba kira, ringing wayar keyi amma ba'a daga sake kira tayi still ba,a daga ba jife tayi da wayar a kan gado tare da zama da'bas tana tafa hannaye, can wayar ta dake kan gado daga bayanta ya fara ringing da sauri ta raruma don duk a tunanin wanda take ne ya biyo bayan kiran, ganin sunan me kiran ne yasa gabanta yankewa ya fadi, *Dr Hassan* ta ambaci sunan a bayyane tana zare ido lallai bata ga ta zama ba wai an saci san barawo. Tafi awa d'aya tana kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta hargitsa suman kanta ko takalmin school bata jire ba jakar ma jifa da shi tayi da shi can gurin kofar toilet, jinta take yi wani iri ji takeyi kamar ta aikata baban zunubi tunda take da Mom bata taba koda dungurinta bane, bata taba fushi mai tsanani da ita haka ba duk kuwa iya girman laifin da zata mata, amma yau ita ce Mom ke hankadewa lallai ta san ba karamin fushi Mom ta yi da ita ba, bata ga laifin Mom ba domin tun ba yau ba ta riga ta san yadda Mom ta kasance mace mai kishin addininta, tana tsananin kyamar addinin musulci, bata shan inuwa daya da musulmi, tana kyamarsu kamar me, ji tayi baza ta iya jurar fushin Mom, hakan yasa ta mike dakyar ta nufi dakinta. ******* KANO STATE *Dr Hassan special hospital Amenity word room number 5* Wani farin dattijo ne me kimanin shekaru 65 a duniya ke kishingide akan gadon marasa lafiyar dake madaidaicin haddadden dakin wanda kwata kwata baiyi kama da dakin asibiti ba, hannun shi sakale da karin ruwa, saman roofing dakin fuskar shi ke fuskanta idanunshi a lumshe, idan ba ka kula da yadda yake motsa bakin shi a hankali da kuma yadda yake danna caunter dake sakale a daya hannun shi da babu Karin ruwa ba zaka dauka barci ya ke yi. Daga gaban gadon wata dattijuwar mata ce zaune a kan daya daga cikin kujeru biyu dake dakin, a kalla zata kai shekaru hamshin da haihuwa amma tsabar hutu jin dadi jin iya kula da kai da yadda naira suka zauna zaka dauka batafi 38 to 40 ba, kallon dattijon mutumin nan take yi fuskarta cike da matsanancin damuwa, hannunta plate ne mai dauke da tuwon almaka da miyar alayyahu da nama, kasa ta yi da muryar a karo na barkatai cikin sanyi ta ce "Alhaji ka tashi kaci abincin mana gashi na zuba maka tun dazu yana hucewa." Bude lumsassun idanunahi yayi kafin a hankali ya ce "bana jin yunwa bazan ci ba." Shiru ta yi tana ci gaba da kallon shi tana tuna rabon shi da abinci tunda asuba da Dr yasa shi yasha tea lokacin da za'a daura mishi drip, kallon agogon dake manne a bangon dakin tayi karfe biyar harda mintuna biyu, ajiyar zuciya ta sauke, cikin son jaraba sa'arta ta sake ce wa "alhaji kayi hakuri ka tashi ka ci abincin nan, lafiya bazai samu ba idan har haka cin abinci." Wannan karan bai bude idanunnashi daya mayar ya lumshe ba kuma bai amsa ta ba, sai ci gaba da yayi da motsa bakin shi alamar yana ci gaba da lazumin shi, ganin haka yasa ta cigaba da yi mai magiya, jin ta dame shi yasa ya bude idanu tare da daka mata tsawa "keee! Nace bazan ci ba dole ne wai." Ta ke alhini da tausayin dake kan fuskarta ya bace bat lokaci daya bacin rai da bakin ciki suka maye gurbin su, ranta ya kai kololuwar baci , a hassale ta ce "wai har sai yaushe ne zaka cire wannan damuwar daga ranka? sai yaushe ne zaka dangana ka fawwalawa Allah lamuranka?, yau fa kimanin shekara goma sha biyar kenan, sai yaushe ne, iyeee alhaji na ce wai yaushe ne?" Ta karshe maganar cikin karaji tare da fashewa da kuka. Bude lumsassun idanun shi yayi ya kalleta kika take yi bil hakki, guntun murmushin karfin hali ya saki, cikin muryar shi ta marasa lafiya ya ce " ya isa haka Lubabatu kina son kisan sai yaushe ne ko?" Da sauri ta gyada kai tana sharar kwallah, idanun shi ya saka cikin nata kafin yace a kausashe "sai ranar da asirin wad'anda suka kashe ta ita da abinda ta haifa Tonu...." Yau ba yawa kuma ba editing🙏 Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 4* Mom na kallo har kiran Dr Hassan ya katse bata iya d'agawa, gaba d'aya a tsorace ta ke, banda zufa babu abin da ke tsatsafo mata, ajiye wayar ta yi a gefen bed ta rafka tagumi da hannu bibbiyu, wayarta ce ta sake d'aukar ringing kallon wayar ta yi bata d'auka ba don duk daukarta Dr Hassan ne again sai dai ganin me kira yasa ta zabura ta mi'ke, hannu na rawa ta yi received, tun kafin ta kai ga cewa komai ta ji ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya wanda sai da ta tsorata, kusan minti uku ya kwashe sai da yayi mai isar sa kafin lokaci d'aya gimtse fuska. Jin yayi shiru yasa Mom cikin rawar baki ta shiga kokarin yi ma shi bayani, wani tsawa ya daka mata Wanda saura kadan ta saki wayar, cikin amon sautinsa mara dad'in ji ya fara magana cikin irin yaren su ba ibo "kin yi sake! Kin yi sake! Na ce kin yi sa ke Alice, tabbas abin da kike 'boyewa tsayin shekaru sha biyar zai bayyana matukar baki raba alakar *jini da jini* ba." Kan Mom ya kulle take ta 'kara tsorata jin ya ce asirin data binne tsayin shekaru zai bayyana, bata gane me yake nufi da Kalmar *jini da jini* ba, sanin hakan da yayi ne yasa ya ce "kiyi gaggawan raba Joy da ra'bar wadan nan ahlin musulman idan kuma ba haka ba." Sai kawai ya kara kecewa da dariya kit ya kashe wayar ba tare daya mata cikakken baya ni ba ya barta tana zare ido. Hakan yasa da sauri ta sake dialing number shi, daga wa yayi bai bata damar yin magana ya ce, "babu taimakon da zan miki idan har baki rabata da wadannan ahlil ba, dama na gaya miki tun farko ai karkiyi sake, idan kuma kika yi sake tabbas jini da jini ba karya bane." Daga haka ya sake kashe wayar bayan ya kwashe da dariya kamar mahaukaci. lallai bata ga ta zama ba, dole ta yi duk yadda zata yi domin taraba Joy da wadan nan tsinannun talakawan musulman, tana son jin cikakken bayani tana son sanin me Kalmar jini da jini yake nufi dan baza ta yi sake wani dan kankanin abu ya bata mata aikinta na kimani shekaru goma sha biyar ba. Saga da marwa ta tashi yana yi tare da tunanin me ya kamata ta yi, wasl zai taimaka mata, cak ta tsaya lokacin da kwkwalwa ya hasaso mata mafita. Kamar zararra haka ta rarumi wayarta ta fara dialing lambar Papa. Daidai nan kuma Joy ta karaso dakin, tana tangad'i kamar yar maye tsabar bata cikin hayyacinta, motsinta yasa Mom saurin dagowa ta kalli kofar, gabanta ne ya fadi ganin yadda Joy ta fita hayyacinta idanunta sukayi luhu luhu cikin kasa da awa daya, kwarai rauninta yaso ya bayyana a lokacin, saboda ba karamin so take ma Joy ba, a duniya Joy ce kadararta Joy ce arzikinta Joy ce rufin asirinta, dakewa ta yi ta dauke kai daga kallonta ta mayar kan wayarta, Halin da joy ke ciki yasa bata kula da yanayin yadda Mom din ke rude ba, zubewa ta yi akan gwuiwowinta daga bakin kofar don tana jin tsoron karasawa kusa da Mom, ta hade hannayenta alamar roko sannan ta sake fashewa da kuka Wanda dama cikin sa take, ba ta ce ko mai ba sai kuka da takeyi ba saurarawa. Kiran waya Mom keyi amma gaba daya hankalinta na kan Joy, kukanta na matukar ta'ba mata zuciya, har ta fara daina fahimtar abin da take yi, zuciyarta ce ke azalzalarta akan ta rungume Joy ta jawota jikinta ta rarrasheta ta hanata kuka, sai da ta yi da gaske ta yakice wannan tunanin daga ranta, dan idan yayi wasa ta bari rauninta ya bayyana ta bazan ta comma burinta na taba Joy da Fatima cikin sauki ba, juyowa tayi a fusace ta kalli Joy cikin tsawa ta ce "ki fita ki bani waje Joy bana son ganin ki." Joy data kara tsorata da lamarin Mom ta dago murya na rawa ta ce "I'm sor!!!" Kafin ta karkare fadin abin da zata fad'a Mom ta sake daka mata tsawar data fi na dazu " I said get out from here." Ta karashe maganar tare da yiyowa kanta kamar idanu waje, da gudu ta fice daga d'akin tana rizgar kuka. ********** Ko da Fatima ta isa gida, a daki ta samu Ummi, ta dan kishingid'a akan darduma da alama sallah tayi ta idar, Sallamar ta yasa Ummi da barci ya fara kwasarta ta bude idanu, ganin haka yasa Fatima cire takalmi ta karasa shiga dakin ta na cewa "Ummi sannu da gida." "Yawwa Fatima kin dawo." "Eh Ummi Allah ya dawo dani." "Maza ki debi ruwa ki dauraye jikinki ki kimtsa ga abincin ki nan a kitchen ki dauka. Bayan Fatima ta fito wanka dakin ta shiga ta kimtsa jikinta ta canza pad, wardrobe ta bude ta dauki kayan da zata saka, har ta ciro Riga da zani sai idanunta ya sauka akan wani Riga da siket na kanti da take da shi na gwanjo, ta Dade ma rabonta da sakawa, haka nan ranar taji tana sha,awar saka kayan, cirowa ta yi ta shirya cikin su, kayan sun mata kyau sai dai sun kamata tsam dai dai jikinta sabanin da da suka mata dan yawa yanzu har skirt din ya d'angale mata don iyakarsa 'kaurinta, amma dai sun bala'in yi mata kyua. Abincinta ta dauka ta ci , ganin Ummi ta samu barci yasa ta yi kwanciyarta a daki, tare da Ciro wani story book data amsa hannun Joy ta fara karantawa, tana fara karatun itama barci ya kwashe ta nan ta yada book din ta tintsire. Kiran sallar la'sar ne ya farkar da Ummi, ta shi ta yi ta fito tsakar gida dan ta dauro alwala ta na cikin zuba ruwa a buta Al'ameen ya shigo cikin gidan, shima kiran sallar ne ya tada shi ya shigo don ya daura alwala ya lallaba ya tafi masallaci, "Sannu Ummi." Cewar Al'meen kallon shi Ummi ta yi lokacin ta zuba ruwa ta tsuguna daga bakin makwarari zata fara alwala ta ce "yawwa yayan Fatima ya jikin." "Da sauki Ummi." Ya ce yana shigewa makewayi, koda ya fito Ummi ta idar da alwala ta shige daki don ba Iya kama ruwa yayi ba, sake diban wani ruwa yayi a drum ya tsuguna ya yi alwala, sannan ya fice zuwa masallacin kusa da gidan jin ana haramar tada sallah. Sai da Ummi ta idar da sallar ta tashi Fatima, akan taje ta wura wuta ta daura ruwan tuwo tunda yau alhamis basu da islamiya. Bayan Al'meen sun idar da sallah fitowa yayi daga masallaci, kallon yanayin garin yayi, ko'ina shar haka kawai yaji yana sha'awar yad'an zazzaga, Abokin shi Aliyu ne ya fad'o mai a rai murmushi yayi a fili ya ce "dan duniya nasan yana gida yanzu, bari na mike kafa na kai mishi ziyarar bazata." Kallon jikin shi yayi, ganin, kananan kaya ne a jikinshi wandon jins ruwan kasa da T shirt fari mai layilayi bakin, bai ciki son fita da kananan kaya ba, amma ganin rigar bai matse shi ba yasa ya kama hanyar unguwar su Aliyu a kafa kasancewar basu da nisa unguwa daya ne a tsakanin su. Stadium junction nan ne unguwar su Ali, a kofar gidan ya tsaya ya aika aka mishi sallama da shi, Aliyu ya fito yana waige waige, daga bayan shi yaji an ce "Aliyu timekeeper." Da sauri Ali ya juyo jin muryar da bai zata ba, a d'okace ya nufe shi ya na fadin" A'a ustaz! ustaz! ustaz! ustaz!!!! namu." Hannu Al'meen ya bashi suka kashe suna dariya, Al'ameen ya ce "Babban timekeeper babban timekeeper" suka sake kwashewa da dariya. Sunaye ne da suke kiran junan su tun a makaranta, hakan yasa koda aka gama karatun aka rabu ba'a bari ba, haka suke kiran junan su dama sunan makaranta ya gaji haka, hakan dabi'a ce ta dalibai duk Inda aka had'u komi tswon zamani kuma duk komin munin suna haka za'a kira juna, Ali ya ce "gaskiya ka shammaceni ustaz ban taba zaton kai ba ne." Al'meen ya ce "Ai baka da mutunci Ali, baka da kirki baka zumunci." Ali ya ce "Wai talle ne zai ma Audi gori ba gara ni ba ma ina kira a waya a kai a kai kuma ko last time na haduwar mu ni naje gidanku ko ka manta ne na tuna maka." "A'a fa Ali ka dai sake tunawa." Cewar Al'ameen, haka dai bayan sun gama yar musu as ka gaisa da tambayar ahalin juna daga na suka nemi waje suka zauna kan dakalin kofar gidan su Ali suka shiga hira suna

Chapter 2 of 22