Share this page
yayi da zaro handkerchief daga aljihun shi ya mika mata, kin Karba tayi sai ta samu kanta da dan zumbura baki. Zaro ido yayi ganin abin da tayi, sai kuma ya samu kanshi da sakin murmushi wanda shi karan kanshi bai san ta su6uto ma shi ba, yarintarta yake gani karara idan tayi wani abin San Fatima yake ganinta. A hankali ya kai hannun shi fuskarta da nufin ya share mata hawayen, a razane ta dago idanunta ta karaf! Ya sauka cikin nashi, wani irin lamari ne wanda tunda take a rayuwarta bata taba tsintar kanta cikin shi ba ya afku da ita cikin abinda bai fi kiftawar ido ba, sakone na zuciya wanda ke shiga ba tare da neman shawaran mamallakinta ba bare izini. Samun kanta tayi da Kasa janye idanunta daga cikin nashi duk da irin duguden da zuciyarta keyi, shima bai dauke idanun shi ba a haka kuma bai fasa goge mata hawayen da yayi niyya ba. Murmushin daya Dakar mata ne ya fargar da ita yanayin da da ta shiga, da sauri ta kawar da fuskarta daga gareshi, tana jan numfashi da karfi don ji ta yi numfashinta na shirin daukewa, bata dawo hayyacinta ba ta tsinci muryar shi a kunnenta cikin shigar rarrashi yana cewa "I'm sorry! Ban yi don na cutar dake ba." Maimakon ta amsa mishi sai kawai ta juya da gudu gudu ta bar shi a tsaye rike da handkerchief. Ya fi minti goma yana bin inda ta bi da kallo, shi karan kan shi bazai ce ga abinda yake kallo ba, Me yasa ta wuce ta barshi ba tare da amsa mishi ba, ko dai bata hakura ba ne, "Ya ilahi!" Ya ambata a baiyane. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yayi amfani da dakakkiyar zuciyar shi wajen yi fatali da abinda raunatacciyar zuciyar shi ke shirin ingiza shi a kai. ******** Lokacin da Amira ta samu sakon Al'ameen, ruwa ne kawai bata zuba a kasa ta sha ba saboda farin ciki abin har saida da ya ba Fatima mamaki, duk da karancin Shekarunta sai da ta diga mata ayar tambaya. A daren ranar kuwa bata ko daga kafa ba tana idar da sallar isha sai gata dauke da tarin littafanta, Al'ameen din ma shigowar shi kenan daga masallaci yana dakin sa ko abinci bai kai ga ci ba. Yana jin sallamarta ya bata rai shi har ga Allah zata takura mashi. A gaban Ummi dake zaune a tsakar gida ta zube cike da girmamawa ta ce "Barka da dare Ummi."Fuska a sake Ummi ta ce "Yawwa Amira maraba, har kin shigo karatun ne?"Eh wallahi Ummi." "To madallah! Allah yayi jagora, shima Yayan Fatiman yanzu ya shigo gidan." "Allah sarki, to ko na koma in dawo anjima kafin ya gama kimtswa." "A'a yi zamanki yar nan idan ya ganki zaune zaifi maida hankali ya kimtsa da wuri."Ta amsa da "To Ummi."dadi fall ranta don dama ta dai fada ne kawai ba don ya kai zuci ba.Dan waige² tayi, kafin ta ce "Ummi Fatima bata nan ne.". "Tana daki ina ganin sallah take." Hira su ka shiga ta6awa da Ummi, a haka Fatima ta fito ta same su. Da fara'a ta ce "Laaa! Anty Amira har kin shigo." Ta ce "wallahi Fatima ba shigo." "To bari na sanarwa Yayan yana dakin shi." Duk yana jiyo su a ranshi ya ja karamin tsaki, ya rasa me yarinyar ta taka da suke rawan jiki da ita dhi shiga harga Allah bata kwanta mashi a rai ba. Sallamarta Fatima ya katse mai tunani, a dakile ya amsa mata don haushin Amira ya shafe ta, tura net door din tayi ta shiga, ta same shi zaune yana latsa waya, da zumudi a muryarta ta ce "Yaya Anty Amira ta zo karatu." bai dago yakalleta ba ya ce "Na sani, ki kwaso littafanki kema Ku jirani tare zaki dinga karatun." Ta amsa da " To Yaya." Yana jin ta tana gaya musu sakon shi. Said da ya kwashe minti sha biyar kafin ya taso. Ummi ya gaisar, kafin ya samu guri ya zauna, a sanyaye Amira ta ce "Ina yini Yaya Ameen." Sai lokacin ya kalli side din da take, ya amsa mata da "Lafiya." Ummi ta ce "Fatima kawo mishi abincin shi yaci tukunna kafin Ku fara karatun." Da sauri ya ce "A'a Ummi bari mu gama tukunna." Bata ce komai ba, ya kalli Fatima da Amira ya ce "Ku matso" Matsowa sukayi ya kunna fitilar wayar shi ya haska, ya dauki daya daga cikin papers na past question da Amira ta zo da shi ya bude ya dan dudduba sannan ya dan kalleta ya ce "Bismillah ko." Da kyar ta iya dagowa ta saci kallon shi, ta re da gyada kai. A tsanake cike da baiwa da basida ya shiga yi mata bayanin kowani question dalla dalla, duk da kasancewarta ba mai kaifaffan brain ba, tsaka tsakiya take, hakan bai hanata dan ganewa ba, wai damma ta fi maida hankali ta akan kallon kyakkyawar fuskar shi, tana sakin murmushi tare da kiyasto abubuwa da dama a ranta. Sai gurin goma saura ya dakata, tare da rufe paper ya dago ya kalleta ya ce "Zamu dakata a nan said Allah ya kaimu gobe, idan kina da tambaya kiyi akan abinda baki gane ba." Da sauri ta girgiza kai, ya ce "ok shike nan gobe idan muka karkare subject din ni zan miki tambayoyi tunda kince kin gane ko?" Ya karashe maganar da tambaya da sauri ta sake gyada ka ya ce "To sai da safe." Ba don ranta ya so ba ta amsa da "To sai da safe Yaya Ameen nagode sosai Allah ya saka mata da alkhaiti ya baka mata ta gari." Ummi da Fatima ne suka amshi, shi kuwa kasa amsawa yayi don jin addu'an yayi banbara kwai. Bayan tafiyar ta ya yi wa Ummi sallamarta tare da umarta Fatima ta kawo mishi abincin shi daki, daga haka ya wuce dakin shi....... *********** Tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, a bangaren Joy ranar kusan yadda taga dare haka taga rana, duk da bata san so ba, zata iya kiran abinda take ji game da AL'AMEEN da zazzafan soyayya wanda tayi wa zuciyar ta daurin goro a farat daya... Wata sabuwa inji yan caca hmmmm! Joy ina raraki da, kinsan dai Mom kamar yunwar cikin ki, atoh ni dai babu ruwana, masoyan Joy Ku bata shawara. Pls kuyi ta manage da guntayen page insha Allah komai ya kusa dawo min normal muyi mu gama book din nan don ni na fara gajiya da shi saboda rashin comment dinku. yasin. Ga masu bukatar shiga group Ku tuntubeni kai tsaye 09116099486. [12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN 👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN 👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 19* Washegari Monday da shirin school ta tashi hakan ne ya d'an d'auke mata hankali daga tunanin Yaya Ameen data kwana yi, jiki a sanyaye ta gama shiryawa, sai kuma ta nema waje ta zauna ta rafka tagumi, ta yaya zata je ta zauna ta zana jarabawa ita kad'ai ba tare da Fatima ba? ta ina zata fara? Me zata rubuta? Ko dai ta je gidan su ne, wata zuciyar ta bata shawara, yayinda wata zuciyar ta hane ta da aikata hakan. A karshe hankalin ta yafi karkata akan ta bari idan sun yi closing ta je, Haka tayi ta zaman gawon shanu har na kusan 30 minutes ba tare da ta ankara ba. Ringing d'in wayar ta ne ya dawo da ita hayyacinta, da kyar ta mik'e ta isa ma'ajiyar wayar, sunan Mom ta gani yana yawo a fuskar wayar, gabanta ne ya yanke ya fad'i, tunda Mom ta wuce basu yi waya ba. Jiki a matukar sanyaye ta kara wayar a kunne ta ce "Gud morning Mom." Daga daya 6angaren Mom dake cikin matsananin tashin hankali ta ce "Morning." A dak'ile ta d'aura da "Thank u 4 what u did, nagode sosai kin nunwa duniya ban isa dake ba, na ce karki je ko ina amma sai da kika fita saboda ke mai kunnen k'ashi ne, to baki isa ba, kin yi karya, kin yi kad'an, ni na haifeki ba ke kika haifeni ba don haka baki isa ki juyani, kuma zan nuna miki." Cikin rawar murya ta ce "Kiyi hakuri Mom " Mom ta ce "No don't sorry me, sorry 4 ur self akwai ranar karbar result yana nan tafe. Kuma me kike yi a gida har yanzu, ko ba yaune kika ce zaku fara test ba?" A sanyaye ta ce "Yau ne." "To zaman me kike yi?" "Kiyi hakuri mom na shirya yanzu zan wuce." "Da kyau, ki fita waje driver na nan da zai kai ku kuma zai jira har ku tashi ya dauko ku, idan ki ga dama kar ki bishi,Duk abinda kika yi zan samu labari." Kit ta kashe wayar ta. Wayar ta bi da kallo kafin ta ce "Zai kai mu ni da wa?" Bata da mai bata wannan amsar hakan yasa ta saki ajiyar zuciya a bayyane ta ce "kiyi hakuri Mom ba yin kaina ba ne." Jiki a sanyaye ta jawo jakarta ta sakko downstairs, babu kowa a main parlour, ko kallon 6angaren dining bata yi ba don bata jin zata iya saka koda ruwa ne a cikin ta a halin yanzu. Tana fitowa compound idanunta ya sauka akan wata bak'uwar mota fake a gaban plat din Mom daf da kofa, bata gama mamakin su wanene a ciki ba aka bude kofar motar, David ne ya fito sanye da uniform d'in shi irin nata fuskarshi dauke da murmushin mugunta, kafin ta gama mamaki aka bud'e d'aya 6agaren mahaifiyar shi ce ta fito Mrs Esther fuskarta a had'e kamar hadarin gabas! cikin wani irin takun isa da tak'ama ta iso gaban Joy, kallon sama da k'asa ta mata kafin a gadarance ta nuna mata motar data fito, da hannu ta mata alamar ta shiga. Sai lokacin ta fahimci jam'in da Mom keyi d'azu wata ita da David za'a kai school tare me hakan ke nufa? Kar sai Mom Anty Esther ta fito ta zaua da ita kafin su dawo da kuma ta shiga ukunta. Sai da ta hadiyi wani busassshen yawu kafin, ta kimkimi jakarta jiki a sanyaye ta nufi motar ta bud'e baya ta shiga, David dake tsaye shima ya bud'e inda ya fito ya koma ya zauna, driver yayi ribas ya fice daga gidan. A rayuwarta tana matukar tsoron Anty Esther, macece masifaffiya ta karshe, uwa uba kuma bata kaunarta ko miskala zarratin, tun bata mallaki hankalin kanta ba ta fahimci hakan, ko kadan jininsu bai hadu ba. Bata san school ba sai da ta ji k'arar bud'e kofa David, dagowa tayi yana tsaye daga jikin windon suna had'a ido ya d'age mata gira tare da sakar mata murmushin keta ya ce "Muje ko." Harara ta watsa mai kafin ta 6alle murfin motar ta fito a fusace ta nufi cikin school ba tare data kula shi ba, tana jin shi yana biye da ita yana fito kasa-kasa. Ko a class kasa concentrating ta yi akan abin da ke gabanta, tana kallon sauran student na d'aukan notebooks din su suna dubawa kafin shigowar invigilator, amma ita ko kwakkwaran motsi ta kasa, har zuwa lokacin da aka shigo yi musu first paper wanda English ne, bayan suna babu abinda ta iya rubutawa a script dinta, ajiyewa tayi akan desk ta rafka tagumi, ta fada komar tunani, rintse idanu tayi take kyakkyawar fuskarsa ya shiga yi mata gizo, komai nashi na dawo nata dallah-dallah, especially moment din su na jiya a tare. Bata san iya adadin time din data kwashe ba sai sai ta ji ana cewa everybody submint, tana kallo aka d'auke script din ta ba tare da ta iya rubuta koda kalma d'aya ba. Koda suka fita break kasa fita tayi, kwanciya ta yi kan desk, duk da irin yunwar dake nukurkusarta. A haka har lokacin second paper yayi, shima dai kamarna farkon babu abinda ta tsinana, da ta kai hannu ma sai ta samu kanta da yin drowning din hearts da arrow ba tare da ta farga ba, a haka lokaci ya tafi, ta yi submit ba tare da ta goge ba. Kasancewar suna test sha biyu suka ta shi, ga mamakin ta David ta ga yazo ya tsaya akanta, a hasale ta ce "what?" Yayi murmushinsa dake kular da ita tare da cewa "Nothing, just let's go." Tsoron Anty Esther ne kawai yasa ta bi bayan shi suka wuce, kamar kuwa yadda Mom ta fad'a a bakin get suka tarar da driver'n daya kawo su yana jiran su, kai tsaye gida ya wuto da su ba tare da ta samu damar zuwa gidan su Fatima ba kamar yadda ta tsara. Cike da fargaba ta bi bayan David suka shiga plat din Mom, a hakimce ta tarar da Anty Esther a falo kafa daya kan daya, ta tara duk ma'aikata gidan a gabanta, ko me take gaya musu oho! A haka suka karasa ciki David dake gaba ya ce "Good afternoon Mama." Ta amsa da "Fine Son kun dawo." Ya ce "Yes Mama." Tare da neman waje gefenta ya zauna yayi balance kamar gidan uban shi. Idanunta ta dawo da shi kan Joy, ta shiga binta da wani shegen kallo mai cike da tsana. Jikinta ne ya d'an dauki rawa lokacin da sukayi hada idanu rasa abin yi yasa ta samu kanta da maimaita abin da ta ji David ya fada ita ma, a d'arare ta ce "Good afternoon Anty." Harara ta watsa mata kafin ta ce "Afternoon." A dakile daga haka bata kara ce mata komai ba sai tsarabar hahara. Ganin haka a sukwane ta kimkimi school bag din ta, ta haura dakinta. Tana shiga ta yi wurgi da jakar, ta fada gado ta fashe da kuka, wata zuciyar ce ta mata, "yanzu haka zaki zauna wannan matar ta yi ta mulkarki a cikin gidanku gidan mahaifinki. Impossible!" Zabura ta yi da nufin ta dauki wayarta ta kira Papa sai dai wayam babu wayar a ma'ajiyarta babu dalilinta, sake fashewa ta yi da sani sabon kukan, ko bata tambaya tasan Anty Esther ce ta daukar mata waya, dan kuwa babu mai ikon shigar mata daki cikin ma'aikan gidan matukar ba ita ta bukaci hakan. Zamewa tayi kasan tiles ta jingina da bed din ta tana matsar kwallah. Tsawar da Anty Esther ta daka mata aka ne, yasa ta mikewa a firgice, cike da masifa ta ce "Kukan uban me kike yi, iye nace kukan Uban me kike yi." Cikin son hadiye kukanta ta ce "Kiyi hakuri Anty." "Rufe min baki munafuka kin zo kin zauna kina kuka saboda tsabar sangarta da fitsara kamar wacce aka daka ko aka zaga, maza ki cire wadan nan kayan ki fito ki yi lunch." Tana tsaye a kanta ta cire uniform ta sauya na gida, daga haka ta tasata a gaba zuwa dining, dinning din shake da abinci kamar wanda mutum goma zasu ci saboda almubazzaranci. Uban abinci tayi serving dinta tuli wanda tasan ya mata yawa, ta tasata a gaba wau sai ta cinye shi, tana ci tana kuka ita kuma tana antayata zagi, "Yarinya duk anbi an sangarta ki, kina yiwa mutane fitsara iri iri, babu tarbiya, to ni nan zan gyara miki zama kafin Mom dinki ta dawo." Da kayar ta iya cin rabin abinci, ta shiga kakarin amai, ganin haka yasa Anty Esther kyaleta, tana sharar kwallah ta mike zata wuce daki, hanata tafiya Esther tayi ta sakata ta zauna ta mata massage. Ranar haka Joy ta wuni cikin wahala da zagi da tsamgwama daga wannan ta shiga wannan , ba ita ta samu kanta ba sai wajajen karfe goman dare, duk wannan wahalar da gajiyar da tayi tana samun hakarkarinta ta kasa tunanin Al'ameen ya mata sallama, Babu abin da yafi tsaya mata a rai irin kyakkyawar murmushi sa, ta tuna ranar da Fatima ke ce mata duk duniya babu wanda ya kai Yayanta iya murmushi, a she da gaske ne. Ta sake tuno daddadar muryar sa lokacin da yake ce mata "I'm sorry! Ban yi don na cutar dake ba." Murmushi ta yi tare da kai hannu ta shafi goshinta dai-dai gurin daya d'an kuje har yayi jini tana sahafawa tana murmushi, bata san iya tswon lokacin data kwashe a haka ba kafin barci barawo yayi gaba da ita... *********** Masu bukatar shiga group na joy su tuntube ni kai tsaye . 09116099486 [12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writers Association* *PAGE 20* Washegari wajajen bakwai da rabi na safe, Anty Esther ta fad'o mata dak'i, tana cikin barcinta mai dad'i wanda ya d'auke ta dakyar gabanin asuba cike begen Al'ameen ta ji an d'ad'a mata duka a cinya, a zabure ta farka zata zunduma ihu idanunta ya sauka akan Anty Esther, tuni ta ja bakinta ta tsuke tana zare ido. Harara Esther ta watsa mata ta d'aura da "Sannu isasshiya, karfe bakwai da rabi kina kwance ki na barci, wa kike jira ya tashe ki. Common get up, stupid girl!" Ta karashe maganar a tsawace tare da mi'ka hannu kamar zata kai mata mari. Da gudu ta mik'e ta fad'a toilet ta rufo kofar ta murza key, jingina tayi da kofar ta fashe da kuka k'asa-k'asa don kar Anty Esther ta jiyo ta, sai da ta yi mai isarta babu mai rarrashi ta samu tayi wankan dakyar, a d'arare ta turo kofa ta lek'o, ganin Anty Esther bata d'akin yasa ta k'arasa fitowa da sauri, sharp-sharp ta shirya cikin uniform dinta ta sakko downstairs dauke da makeken school bag d'in ta mai tayoyi. A dining ta tarar da David gaban shi shake da abincin kala-kala ya ci wannan ya ture ya janyo wannan, Harara ta watsa mishi a fakaice a ranta ta ce "Shege mayunwaci babu a hause anzo an samu na banza." Muryar Anty Esther ta jiyo daga hanyar kitchen tana tahowa,sai masifa take da hargagi da alama da kuku's take yi. Da sauri ta ja kujera ta zauna, cikin dan karkarwar jiki ta shiga kokarin had'a tea, David na kallon ta yana mata murmushin keta. Bata wani ci abin kirki ba ta mi'ke, ganin David ya gama don kar tayi laifi, du k da haka bata tsira ba sai da Anty Esther ta zage ta tas, wai tsabar iskanci ta zuba abinci ta barshi bata ci ba. Kuka take son yi amma babu dama, Tana kallo David ya kwaso kayan kwalama dangin su cake, ice cream, chocolate, ya tula a jaka, sannan su ka fita sabon driver'n Mom ya d'auke zuwa school. A cikin mota ta samu damar yin kukanta, kwantar da kanta a jikin kujera ta yi tana shesshekar kuka kasa-kasa, David dake gefenta ya kalleta yayi murmushi, cike da izgili ya ce "Yarinya ki kwantar da kai a gabana ki roke ni abin da kike so, zan taimaka miki." Harara ta watsa mishi ta dauke kai wani irin mugun haushin shi take ji. D'age kafad'a ya yi ya ce "kin huta." Yau ma kamar jiya babu abin da ta tsinana a school d'in har sukayi closing. Koda su ka koma gida yau ma bata huta ba, haka Anty Esther ta sakata a gaba kamar jiya, ko garden ta ki bari ta fita ta sha iska, wayarta take bukata ta kira Papa amma tsoro ya hana ta tambaya, tana ji a gabanta Anty Esther da Mom suka yi waya, amma Mom bata ce a bata ba, sai ma cewa ta yi wai a ci-gaba da tsareta kar a barta fita ko compound ne idan ba school zata je ba, kuma koda wasa kada a kuskura a bata waya, har sai ta dawo, daga nan kuma suka ci-gaba da wasu maganganu wanda tuni ta daina fahimtar komai saboda kukan da ya ci karfinta. Kamar jiya tana samun kanta tuni ta manta da duk halin da take ciki, ta tsunduma tafkin begen abinda zuciyar ta ke bege. ************** Bayan wasu kwanaki. Sosai Amira ta dage da zuwa daukar karatu wurin Al'ameen, sai dai hakan ba abinda ya kareta da shi sai wani irin mahaukacin kaunar shi, a duk sanda zasu zauna karatu zuciyarta sake narkewa take da soyayyar shi, haka zata yi ta kallon shi wani bin sai Fatima ta ta'ba ta zata yi firgigit ta dawo hayyacinta, zuwa yanzu Ummi ta soma fahimta wani abu game da Amiran sai dai ta bar abin a zuciyar ta a tunda hasahse ne kawai take bata da tabbas. Shi kam Yaya Ameen bai fahimci komai ba, saboda kwata babu wata aba wai soyayya a gaban shi, sai dai ya kan rasa wani irin kallo ne yarinyar ke yawan bin shi da shi haka. Ita kam a bangaren ta sosai lamarin ke damunta, duk wani salo da iyayi da zata yi don Al'ameen ya gane halin da take ciki ta yi amma a banza, hakan yasa ta sake tarar Zainabu da maganar, zee ta bata shawara kamar yadda ta saba, ta yi na'am da shawarar don a yanzu yadda take jin soyayyar shi, bata ki kowa ya sani ba don ta k'una bata tsoron kauri. Yau ma kamar kullum ta shigo gidan bayan sallar isha'i, kasancewar an wuni ruwan sama gari yayi sanyi, yasa Ummi basu zauna a tsakar gida kamar yadda suka saba ba, a falo ta same su gaba dayan su harda Al'ameen d'in da dawowar shi gidan kenan, ya mutsa fuska ya yi lokacin da ya ji sallmarta, baya jin dadin jikin shi tunda rana karfin halin kawai yake yi, ga wani sanyi-sanyi da yake ji yana shigar shi. gaban Ummi ta zube ta kwashi gaisuwa, sannan ta juyo bangaren sa, cikin wata irin narkakkiyar muryar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen." Ya amsa da "Lafiya kalau." Yana dauke kai daga gareta don take kamshin wannan mayataccen turaren nata na ran nan ya mashi sallama, dafe kanshi daya fara Sara mishi ya yi. Fatima ce ta gaisheta, ta amsa cike da kulawa kafin ta samu waje kusa da ita ta zauna, ta saitin shi yadda zata samu damar satar kallon shi hankali kwance. Ya fi minti uku a haka kafin ya dago, carat idanunsu ya sarke dana juna ba tare da ta ankara da zai dago ba, da sauri ta kawar da kanta don bazata iya jurar hada idanu da shi ba, muryar shi ne ya dawo da ita hayyacinta "Amm! Amira ki yi hakuri kike gida yau baza mu saka yin karatu ba, Bana jin dadin jikina." Jin haka yasa Ummi kallon shi da sauri, ta katse shi da cewa "A'a yayan Fatima baza ayi haka ba, tunda ta riga ta zo, ka koya mata ko kadan ne." Shiru ya dan yi kafin ya amsa da "To Ummi." Baya iya mata musu matukar akan abinda bai fi karfin shi ba ne. Mikewa yayi ya kalli Fatima ya ce "Ku muje dakin zaure taskar gida a kwai sanyi." Daga haka ya fice, Ummi ta so tsayar da shi suyi karatun a falonta ganin ya riga ya fice yasa ta kyale shi. Fatima ce a gaba Amira na biya da ita suka shiga dakin bayan ya amsa musu sallama, lumshe idanu Amira tayi lokacin data shaki daddadar kamshin turarensa da take maitar son ji kullum. Dakin tsab da shi a tsabtace kamar ba dakin saurayi ba. Cike da karfin hali da jarumta ya fara koyar da su, sai dai ko minti goma basu dauka ba ya fara neman fita hayycinsa, rintse idanu ya yi, yana jin yanayin shi na canjawa, gefe daya ga wani shu'umin kamshin turaren da yake shaka na neman hallaka shi. Babu shiri ya dakata, ya kalli Amira da kyar ya ce "Amira kije kawai gobe ki dawo, bana jin zan iya karatu yau, na so na koyar da ke kamar yadda Ummi ta saka ni amma bana jin zan iya." Cike da matsanancin tausayin shi ganin yadda idanun shi suka rine, ta ce "Toh Yaya,

Chapter 9 of 22