Share this page
"Miss Joy ar u in luv wit him?" Ya fad'a a d'arare. Tsittt! Kukan ta ya d'auke, ta zuba ma shi rinannun idanunta na yan sakanni, can kuma ta girgiza kai ta ce "Noooo! Babu wani abu makamancin haka a zuciyata game da shi, kuma kar ka sake yi min irin wannan tambayar." Daga haka kuma ta juya da sauri sauri gudu gudu ta bar gurin. Ajiyar zuciya ya sauke ya san ta fad'i son ran ta ne kawai amma shakka babu tana son yaron nan, shi daga ita har yaron tausayi suke ba shi, yasan wannan abu ne da ba zai ta6a yiwuwa ba ko a tastuniya balle a zahiri. Alice fa! jinin Alice da soyayya da musulmi tabbas akwai k'ura, shi dai zai saka su a addu'a shine k'adai taimakon da zai iya mu su. Ta d'auka sanin halin da yake ciki zai sama mata sauki a zuciya, amma ina! Babu wani sauki sai ma k'ara mata damuwa da tashin hankali da ya yi. kamar jiya daren ranar sai barci 6arawo ne ya sace ta bayan ta gama tsara yadda za ta yi gobe ta samu fita ta je ta gan shi ko a sace ne. ******** *AL'AMEEN* Kasancewar sa jarumi kuma sam ba shi da k'an jiki yasa nan da nan ya fara samun sauki, a Washegari rana ta uku da samun tsautsayin ya soma taka k'afarsa, tuni kumburin ya sa6e sai dan abin da baza a rasa ba. A ranar ma haka Amira ta sake had'o lafiyayyan karin kummalo ta aiko ma shi. Sam bai ji dad'i ba, a ganin shi ta cika zak'ewa, hakan yasa ya kuduri aniyar taka mata birki, yau kam bai ci abincin ba duk irin magiyar Ummi, ya fake da cewa shi ba cimarsa ba ne, shi kunun zai sha, kasancewar Ummi tasan hakan yasa bata tsaurara masa dole sai ya ci ba. Wainar shinkafa ce da miyar taushe yaji tantakwashi da man shanu, Ummi da Fatima ne kad'ai suka ci. Yau kam a d'aki ya yi zaman shi bai fito tsakar gida ba kasancewar akwai wutar nepa. Wuraren karfe goman rana Amira ta yi sallama tsakar gidan, direct cikin gida ta nufa don bata za ci yana d'aki ba, a kitchen ta samu Ummi, kamar kullum a mutunce ta gaisheta tare da tambayar mai jiki. Ummi ta amsa da "Mai jiki Alhmdllh yana samun sauki, sannu da hidima Allah ya saka da Alkhairi Allah ya yi Albarka." K'asa ta yi da kai tana d'an murmushi ta ce "Amin Ummi." D'aukar tsintsiya ta yi ta tattare hijabinta tana "Ummi bari na tattara gidan naga ba'a riga an share ba." Kallon ta Ummi ta yi ta ce "Kun gaisa da mai jikin ne?" Ta girgiza kai tare da cewa "A'a Ummi." Ummi ta ce "kije Ku gaisa yana d'akin shi." Ajiye tsintsiyar ta yi ta kama hanyar d'akin ,zuciyarta na dokawa da mugun gudu. A sanyaye ta yi sallama a bakin k'ofa. Ya amsa mata yana daga zaune a bakin katifarsa, duk a tunaninta zata tarar da Fatima a d'akin kamar ran nan sai dai ga mamakinta shi k'adai ne zaune a sanye da singlet da dogon wando, kallo daya ta yi masa ta yi saurin yin kasa da kai, take jikinta ya dauki rawa, kasa zama ta yi don gaba daya gani take ya cika dakin tsabar kwarjini. Shikam a tsanake yake kare mata kallo, Sam! Bata da makusa sai dai ita zuciya ba'ayi mata tilas. Ganin bata da niyyar yin magana gashi ta doje a bakin k'ofa ita ba ta koma ba ita ba ta k'arasa shigowa yasa ya yi gyaran murya. A diririce ta dago su ka had'a ido sai kawai ta zu6e gwiwowinta a k'asa a nan inda ta ke tsayen cikin dan rawar murya ta ce "Ina kwana Yaya Ameen ya karfin jiki." Maimakon ya amsa gaisuwarta sai ya cewa "Amm! Amira." Da sauri ta dago tare da amsawa da "Na'am." Ya ce "Na ga sa'kon ki nagode, sai dai ina rok'on ki daga yau kar ki sake wahalar da kanki wajen aiko min da wani abu ko yi min girki please bana buk'ata, wani irin tunani iyayenmu zasu yi idan suka ga haka, to dan Allah wannan ya zama na karshe, and maganar wasika shima daga yau na kashe please kar na sake gani bana so, sannan ina mai jan hankalinki da ki zama mace mai kamun kai domin mazan yanzu basu da tabbas wani zai iya yin amfani da wannan irin damar ya sabauta rayuwarki. Wani irin tafarfasa zuciyarta ya shiga yi, tun kafin ya dasa aya tuni hawaye sun gama wanke mata fuska. Meye laifinta don ta nuna masa soyayya, dama duk tsawon lokacin nan aikin banza take, Ashe kallon sakarya mara kamun kai yake mata, ji ta yi zuciyar ta ya dake duk wani tsoro da kwarjinin daya cika mata ido ya kau. Dagowa ta yi ta kalle shi, ta ce "Shin laifi ne don na nuna maka soyayya da kulawa, ka sani nima ba yin kaina bane kuma bani na daurawa kaina ba, don Allah na rokeka ka daina min kallon sakarya mara kamun ka wallahi ba haka na ke ba, sannan don Allah ka ta ya ni da addu'a Ubangijin daya sanya mini soyayyarka ya yaye min, na maka alkawarin daga yau bazan sake gwada maka wani abu makamancin soyayya ba, zan yi kokarina na taushi zuciyata, amma ka sani bazan daina sonka ba har karshen numfashina." Ta kai karshen maganar tare da fashewa da wani irin kuka wanda ya taso mata daga can k'asar zuciya, to she bakinta tayi da hijabinta saboda kar sautin kukanta ya fita har Ummi ta jiyo ta da sauri ta mike tare da ficewa daga dakin da gudu. Karo suka yi da Fatima a k'ofar d'akin, bata tsaya ba ta ra6a ta gefenta ta fice daga gidan. Kur!: ya kurawa hanyar da ta bi idanu, rana ta farko da wani abu mai kama da tausayi game da ita ya tsirgar ma shi a zuciya, me ya aikata kenan ya salam! Ya fad'a tare da dafe kai. ************ *JOY* Safa da marwa kawai take yi a d'akin ta ganin karfe ukun rana ya gota babu wata dama da ta samu na fita, babu irin tunaune da bata yi ba ciki har da da haura katanga, sai dai ta san ko cikin maye take bazata iya ketare katangar gidan ba. Cak ta tsaya lokacin da zuciyar ta ya hasko mata mafita "David." Ta fad'a a saman lab'b'anta, da sauri ta rarumi wayar ta, ta lallatsa tare da karawa a kunne. πŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆ kunya duk ta isheni na rasa da bakin da zan baku haΖ™uri ma yasin😬 😬😬 in sha Allah hakan bazai sake faruwa baπŸ™πŸ™πŸ™ Ku tayani da addu'a aljanun kiwar yin typing ne su ka kusa sauka a kainaπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ 09116099486 [12/29, 2:43 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€ ~FARHAT~ *PAGE 28* "He'll who ix on d line" David ya fad'a bayan ya daga wayar, a sanyaye ta ce "David." Murmushi ya yi, sannan ya ce "So is u, ba gizo idanuna ke min ba dana ga call d'in ki a wayata." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "David I need ur help." Wata irin shegiyar dariyar ya saki kafin ya ce "Big gal yau kuma a wajena ki ke naiman taimako? Any way ni d'an uwanki ne bazan 'ki taimaka miki ba, fad'i muji ko zan iya." Jim ta yi kafin ta ce "David fita nake son yi daga gida amma Mom ta hana ni." Ya ce "uhumm! To ni meye nawa a ciki? Me kike so na yi miki? Ko so ki ke yi zo na ce ma Mom dole ta barki fita, a beg obey ur mother." Kamar ta fashe da kuka tsabar takaici amma ta dake don mai nema baya fushi, ta ce "Ba haka nake nufi ba, so na ke kazo ka ce mata zamu fita tare zuwa wajen wani taro na school d'in mu nasan idan ta ji daga bakin ka zata barni." Shiru ya mata bai amsa ba, ganin haka yasa ta ce "please David ka taimake ni." Magiya ta dinga yi mai har da kuka. Ajiyar zuciya ya yi ya ce "To shikenan zan taimaka miki, amma a nawa?" Wani firin ciki ne ya ziyarceta jin ya ce zai taimaka mata, cike da jin dad'i ta shiga cewa "Thank u David, thank u very much."ganin kamar bata gane nufin shi ya yasa ya ce "Rike godiyar ki, ki fad'a min a nawa zan taimaka miki." "Ban gane ba?" Ta fad'a cikin rashin fahimta, "Ok ina nufin zaki biya ni ne ba a free zan taimaka miki ba." Ta ce "Ok nawa zan baka." Murmushin cin nasara ya saki, ya ce "Zaki bani 100k idan ya miki to, idan bai miki ba kuka shikenan." Ba tare da wani tunani ba tace "Na amince." Fiton murna ya saki ya ce "gud gal! Ki shirya gani nan zuwa." Daga haka ya katse kiran ya ta shi yana tsallen murna dama yana bukatar kudi abokinsa zai yi birthday ko babu komai ya samu na fita kunya tsuntsu daga sama gasasshe. A bangarenta ma hakan ne, don har ta fi shi farin cikin samun biyan bukata, sai dai bata da kuzarin yin tsalle-tsalle kamar shi. Zama ta yi bakin bed tana sauke ajiyar zuciya, finally yau zata gan shi, ji ta yi kaso goma cikin d'ari na nauyin da zuciyarta ya mata ya kau. Bayan 30 minute David ya iso tuni ta shirya cikin wani Straight gown 3 quarter yar kanti dark blue, ta gyare dogon gashinta da rabonki shi da cumb tun ranar da su ka yi accident, ta yi parking din shi a baya, mai kawai ta iya shafawa sai perfume, ba cin su ko lip gloss bata shafa ba. Direct dakin Mom David ya nufa, bayan sun gaisa ya ce "Mom Joy ta gama shiri kuwa?" Cikin rashin fahimta tace "Shirin me?" Ya ce "Na zuwa taron CRS official da zamu yi a school yau 4 to 6." Mom ta ce "Ai kuwa ta manta bata gaya min ba, dubo dakin ta ka kira min ita." Tana tsaye tsakar d'aki tana kiran tsammani ta jiyo knocking, da sauri ta bude , d'age mata gira ya yi ya ce "I hope kin shirya." Ta gyada kai ya ce "muje Mom na kira. Amma kafin nan in ji alert." Ta ce "Bani account number na yi maka transfer." Wayar ya karba ya saka mata, sai da ta yi mashi transfer 100k. Sannan su ka tafi dakin Mom. Kallon ta Mom ta yi ta ce "daughter dama kuna da irin wannan taro mai mahimmanci shine baki fad'a ba, yanzu da David bai biyi miki barka shikenan ko." "Sorry Mom wallahi Na manta ne." "Ok maza ki shirya ku tafi kar ku makara." "Ok Mom " ta fada tana mikewa, takalmi da wayarta kawai ta dauko a dakin ta ta dawo ta ta yi sallama da Mom suka fito. Waige-waige David ya fara yana naiman Peter, riko hannun shi ta yi ta ce "Da kafa zamu fita." D'age kafad'a ya yi alamar he don't care. Ba su sha wahalar fita ba, don kafin ma su iso Mom ta sanar wa security din ta. Suna dan yin nisa da gidan David ya kalle ta ya ce " To Miss yanzu sai ina." Ta ce "Gidan su Fatima Hussain." "Fatima Hussain!" Ya maimaita sunan cike da dimbin mamaki, juyowa ta yi ta kalle shi cikin ido ta ce "Yes ko kana da magana." Yadda ta tsare shi da manyan idanunta masu kwarjini yasa ya yi saurin d'age kafad'a tare da cewa "Nop! Zan je wani waje na dawo mu had'u a nan." Ta ce "OK ya yi." Gaba ya yi ya barta a tsaye har sai da taga k'ulewarsa. Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta kama tafiya. Cike da karsashi da shauk'in so dake d'ibarta ta dauki hanyar gidan, zuciyar ta na k'ara karfafa mata gwiwa. Sai dai ko da ta iso k'ofar gidan sai ta kasa shiga, tsayawa ta yi tana rarraba ido, sai lokacin wani tsoro da fargaba ya shigeta, ji take kamar ta juya ta runtuma da gudu, amma wani bangare na zuciyar ta na ingizata, kar fa ta shiga ya yi mata wani abin, cewar wani side na zuciyar ta, don warning din shi na ran nan har yau yana nan rad'am a kwakwalwarta. Ta fi karfin mintuna ashirin a haka tana karantar wasikar jaki, ita bata shiga ba ita bata wuce ba, kamar daga sama ta ga an bud'e k'ofar gidan, a daburce ta d'ago manyan idanunta da suke cike da tsoro ta kalli k'ofar don ganin mai fitowa. Al'ameen ne, ya lalla6a ya fito don ya sha iska , yana bude k'ofa ya ci karo da ita, rasa wani yanayi zuciyarsa ta shiga a lokacin da idanunsa suna sauka akan kyakkyawar fuskanta ya yi, farin ciki ne ko kuwa kewa ne oho, sai dai ko da wasa bai bari fuskarsa ta nuna ba, sai ma k'ara tamke ta da ya yi babu fara'a ko kadan, sannan ya zuba mata kaifaffun idanun shi. Numfashinta ne ya dauke na wucin gadi, lokacin da idanuwanta ya sark'e cikin na shi, baki ta ke son ta bud'e ta yi magana amma kamar wacce aka sakawa padlock. Sosai ya hango tsoratar da ta yi a cikin kwayar idanunta, yadda take rarraba idanu tana muymuy!! Da d'an bakinta ba bakaramin kyau ta yi mashi ba, tana d'aya daga cikin mutanen da ko wani irin yanayi suka shiga kyau ya ke musu. Jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa ya ce "You again? Ba nace miki kar na sake ganin k'afar ki a gidan nan ba, babu ke babu Fatima, ok baki jin magana ko?." Da sauri ta girgiza kai a raunace ya ce "Ba wajen Fatima nazo ba, wajen ka nazo." Had'e hannayenta ta yi take har ruwan hayawe sun cika mata idanu, ta ce "Na zo ne na sake baka hakuri akan abin da ya faru ran nan, ka yafe min for God sake, it all my fault." Ta k'arashe maganar tana kallon d'aurarren k'afar shi. Wani irin rauni gami da tsantar tausayinta ne suka shiga ratsa zuciyarsa, shiru ya yi yana kallonta, yana jin wani irin yanayi a zuciyarsa game da ita, kwatankwacin yadda yake ji a zuciyarsa game da tilon kanwarsa. Ganin bai amsata ba bai kuma daina binta da wani irin kallo mai kama da harara ba, yasa ruwan hawayen da take ta kokarin rike wa wanke mata fuska, ta san dama bazai kalleta da idon rahama ba, cikin muryar kuka ta ce "Nasan ni mai tarin laifuka ne a gare ka Yaya Alamein, zai yi wuya ka iya yafe min at once." Ta karsahe maganar cikin kuka da shessheka. Rintse idanu ya yi da karfi. Da tasan yadda kukanta ke tsisstinka jijiyoyin zuciyarsa da ko da wasa bata yi ba. Ita kam bata san abin da ke faruwa ba ganin yadda ya rintse idanu, yasa ta k'ara sautin kukanta wanda kukan da biyu ne, harda na yadda soyayya ke nukurkusarta. "Stop!!!" Ya fad'a a tsawace jin tana shirin tarwatsa masa kwakwalwa. Ta sauri ta had'iye kukanta, tana zare idanu, still hawaye bai bar zubo mata ba, kasa ya yi da murya ya ce "Is ok, na hakura ki dai na kuka, kinji." Yadda ya yi maganar a sanyaye cikin shigar rarrashi yasa ta yin shiru ta na kallon shi. Hannu ya saka aaljihunsa ya dauko farin handkerchief ya mik'a mata ya ce "Oya wipe ur tears." Wannan karon kasa ignoring ta yi duk da wannan time babu sassanyar murmushi nan a fuskarshi kamar wancen karon, sai ma sa6anin hakan. A hankali ta miΖ™a hannunta dake d'an karkarwa ta kar6a, sai kuma ta kasa goge hawayen ta rik'e hankin a hannun tana kallon shi, gyada mata kai ya yi ya ce "uhumm!. a hankali cike da shauki ta kai handkerchief d'in fuskarta, wani irin sassanyar kamshine ya ziyarci hancinta, a ta ke ta lumshe idanu tare da k'amk'ame handkerchief d'in gam ta na shakar shi. Duk abinda ta ke yi idanunsa na nan k'em akanta. Minti biyu ta kwashe a haka, kafin ta bud'e idanunta tare da sauke handkerchief d'in a fuskarta ta mik'a ma shi, had'i da cewa"Thank u." Bai san sanda sassanyar murmushi ya ku6uce masa ba, mi'ka hannu ya yi kar6a hankin ya mayar aljihu tare da "gud gal! Don't cry again kin ji" A sanyaye ta gyada kai tare da cewa "Ni zan wuce ina rok'on ka ka mika min gaisuwa wajen Fatima ka gaya mata ina kaunarta kuma ina tsananin kewarta." Tana fad'in haka ta juya ta kama tafiya. Gaba d'aya lakkan jikinsa sun mutu, so yake ya bud'e baki ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta amma kamar last time ya kasa kiran sunan, sai a zuciya yake ta maimaita Kalmar JOY. FARHAT ya fad'a akan la66ansa, tabbas d meaning of d word Joy in Arabic is FARHAT. Sai ya tsinci bakinsa da furta FARHAT da 'karfi, cak ta tsaya duk ta san ba ita yake 'kira ba, amma haka kawai ta ji k'iran ya ratsa har cikin kwakwalwarta. Ganin ta tsaya yasa ga sake furta FARHAT, a karo na biyu, dis time juyowa ta yi, don jikinta ya gama bata da ita yake, daga Inda take tsaye ta nuna kirjinta da hannu ta mashi alamar ita yake kira, kai ya gyada mata tare da cewa "Yes u FARHAT." FARHAT ta maimaita sunan a zuciyar ta, tana tsaye a in da take bata motsaba, ganin kamar bata da niyyar zuwa yasa shi fara d'ingisa a hankali yana nufarta, ganin haka yasa ta saurin takowa itama ta nufo shi, a gaban shi ta tsaya ta zuba mishi ido tana jiran ji daga gare shi. Ya kalleta ya sakar mata murmushin da ke shagaltar da ita, ya ce "Kin nemi yafiyata na yafe miki amma ni har yanzu baki ce kin yake min ba akan abin da na miki ran nan." Shiru ta yi tana son gano akan me yake magana, ganin kamar ta manta yasa a hankali ya kai hannun shi goshinta daidai inda ta k'uje ran nan ya ce "For dis." Sai lokacin ta gane me yake nufi, Karo na farko ta saki murmushi har fararen jerarrun hakwaranta suka bayyana. "Masha Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta." Ya fada a zuciyarsa, muryarta ne ya katse mai tunani cikin sanyi ta ce "Baka yi min komai ba Yaya Alamein, idan ma kayi min ni ban 'rike ka rai ba, I know it fault, duk wanda aka yi wa kanwar shi abinda Mom ta yi wa Fatima in dai yana da hankali zai iya daukar matakin da yafi wanda ka dauka, ka ce wa Fatima ta yi hakuri, kaima kayi hakuri." kallon ta kawai take yi cike da birgewa har ta dasa aya. Ta matukar birge shi kalamanta da hikimarta sak irin na Fatimarsa sai yake ganin kamar ma ita ce tabbas maganar Ummi gaskiya ne a cikin tarayyarasu akwai wani sirri wanda Allab daya haΙ—asu ya barwa kansa sani. A tausashe ya ce "Kina son ganin Fatima?" Bata iya bashi amsa ba sai gyada kai da ta yi da sauri, ya ce "Oya muje na kai ki wajenta." "Da gaske!" ta furta cikin wani irin farin ciki tare da zaro ido............ Harda na gobeπŸ™ˆπŸ™ˆπŸ™ˆ 09116099486 [12/29, 2:43 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€ ~FARHAT~ *PAGE 29* Murmushi ya yi tare da gyad'a mata mata kai alamar da gaske ya ke yi. "Oh my god!!! I'm so happy." Ta fad'a cike da mad'aukakin farin ciki, fuskarta dauke da yalwataccen murmushi. Kallon juna suke yi kowanne zuciyarsa fari 'kal, shima murmushin yake ganin yadda ya wanzar mata da farin ciki, cikin sigar zaulaya ya ce "Miss smiller! Wannan murnar duk na ganin Fatima ne?" Da sauri ta gyada kai, ya girgiza kai tare da ce wa"To Oya let's go to her." A hankali ya juya ya fara tafiya yana d'ingisa k'afarsa. Tsayawa ta yi tana karewa bayan shi kallo, ta na zayyana irin kyawun surar shi a ranta, sai da ta ga yana daf da shigewa zaure sannan ta bi bayan shi da sauri. Sallama ya yi a tsakar gidan, kusan a tare Fatima da Ummi suka amsa, Ummi na daga d'aki Fatima kuma na kitchen. Da sauri ta mik'e ta fito tana ce wa "Yayana har ka daw......" Sauran zancen ne ya mak'ale lokacin da idanunta suka yi arba da Joy tsaye a bayan Yayanta, cikin rawar murya ta ce "My Joyyyy!" Joy da tuni ta fara takowa wajenta ta ce "My Teetee!" Da gudu Fatima ta k'arasa gareta suka rungume juna, fashewa da kuka Fatima ta yi tana ce wa "My Joy ke ce da gaske ba mafarki nake yi ba kamar yadda na saba, mai yasa baki zo naima na ba, kika bar ni da tarin kewar ki." Joy da tuni itama hawaye ya wanke mata fuska, at d same time kuma tana murmushi, ta ce "I'm sorry My Teetee, ki yafe min, nima na yi kewar Fatima, I missed u my friend, I badly missed u." Tsabar farin ciki bata iya amsa mata ba, sai zame jikinta ta yi a nata da sauri ta isa wajen Al'ameen dake tsaye yana kallonsu, yana murmushi ta fad'a jikin shi ta rungume shi gam ta kwantar da kanta a kirjin shi, cikin shessheka take ce wa "Nagode Yayana, nagode nagode daka dawo min da walwata da farin cikina, yadda ka faranta min Allah ya faranta maka Yayana." Tsam! Ya saka hannu ya zagayeta, yana bubbuga bayanta, gaba d'aya zuciyarsa ta karye ji yake kamar tana melting, tausayin rayan gaba d'aya ya cika shi, ba dadan shi din jarumin namiji ba ne , da babu abin da zai hana ya zubar da hawaye. Tsayawa Joy ta yi tana kallonsu cike da sha'awa tana murmushi still hawaye na zubar mata. Daga bayanta taji an dafa kafad'arta, da sauri ta waiga, ganin Ummi yasa ta saurin fad'awa jikinta ta 'kamk'ameta. Ummi kam kasa jurewa ta yi sai da ta dauke kwallah a fakaice, murmushi farin ciki kwance a fuskarta, ta shiga shafa kanta alamar rarrashi. Dakyar Al'ameen ya raba Fatima da jikinsa, handkerchief d'in sa yasa ya shiga share mata hawaye, lokaci 'daya kuma yana ce mata cikin rad'a da rarrashi, "Ya isa haka k'anwata, ki yi shiru ko kuma na ce ma FARHAT ta wu ce abinta tunda ba ki son ganinta." Da sauri ta mak'e kafad'a tare da ce wa "inyiiiin!" Cikin sigar shgwa6a ya ce "Oya go to her." Ya k'arashe maganar tare da rik'e hannunta ya soma tafiya, gaban Joy da Ummi suka tsaya, a hankali ya ce "FARHAT!" D'agowa ta yi daga jikin Ummi ta kalle shi, murmushi ya sakar mata, tare da kamo hannunta ya had'a da na Fatima. A hankali ya saki hannayen ya juya ya bar tsakar gidan, Ummi ta kalli Fatima data kamkame hannun Joy gam kamar za'a kwace mata ita, ta ce "Yau kuka da mafarke mafarke da surutan cikin barci ya kare ko?" Zafo ido ta yi ta ce "Laaaa! Ummi ni?" Ummi ta ce "Ke fa, kusan kullum sai kin yi sambatun kiran sunan Joy cikin barci." Duk dariyar farin ciki suka saka, Fatima ta ja hannun Joy ta na ce wa "Friend mu je d'aki ki bani labarin school da bayan rabuwa." Joy ta amsa da "Sai dai na baki labarin irin yadda na yi missed d'in ki." D'akin Ummi suka shige basu tsaya a falo ba har bedroom Fatima ta ja ta. Ganin shigewar su yasa Ummi girgiza kai, lamarin Al'ameen sai shi, ta fad'a a ranta, d'akin shi ta nufa don tana son jin yadda aka yi ya had'u da Joy har ya kawo ta cikin gidan yau dan kan shi. A d'aki kam, hira ce ta 6arke tsakanin kawayen biyu. Bayan sun

Chapter 13 of 22