galaba akanta ba hakan ya haifar mata da mummuna tsana da tsamgwama daga gareshi, zata iya cewa shine ya fara hura wutar kiyayya tsakanin sauran kannensa da marigayi wanda suka dauki karan tsana suka dora mata acewarsu itace silar mutuwar dan uwansu, yayinda kiri-kiri suka sheganta mata y'ay'a, y'ay'an da bata san daga ina suke ba, kawai ta bud'e ido ne ta ganta a tare da su.
Ta dauka zuwa yanzu Tanimu ya saduda, tunda shekaru sunja, bata ta6a tunani ko hasashen cewa zai kuma tayar da wannan maganar ba, sai gashi yana sake baiyana mata har yau yana nan da muradin tarayya da ita, wa'iyazubilla.
Ta yi kuka ta yi bakin cikin wannan lamarin don sai da ta kwashe kwana uku tana zazzabi a tsaye saboda jimamin wannan lamari, bata cewa Al'ameen komai a kan lamarin, haka shima bai ce mata ba, sai dai shirun shi ba yana nufin bai damu bane, daurewa kawai ya ke, kullum suna tare da Aliyu shine ya ke don karfafa masa gwiwa da bashi baki, a bangare daya kuma suna nan suna wani shiri shi da Dr Abdul wanda Al'ameen din bai san da shi ba, don tun ranar da Aliyun ya mishi maganar shi suka rabu baran-baran bai kuma ambaton sunan shi ba, wannan kuma umarnin Dr din ne.
Da misalin karfe biyar na yamma yaro ya yi sallama, tsakar gidan Ummi ya sanar da ita wai wani mutum na sallama da ita a waje, a lokacin ita kadai ce a gidan Fatima na islamiyya Al'ameen kuma na gurin sana'arsa, cike da madaukakin mamaki, ta ce "Balkisu aka ce ka kira ko dai Fatima." Yaron ya tabbatar mata da Balkisu ake kira, har ta ce ya je ya ce wanene, sai kuma ta ce ya barshi, ya ce wa mutumin ya shigo daure ya kirata tana zuwa, ta dade zaune tana sake-sake , kamar ta fasa fitar don hankalinta bai kwanta ba sai dai ta dake ta mike ta sanya hijab dinta ta fitan........
Oum ummeetarh
09116099486
[12/29, 2:50 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 43*
Mikiya Writers Association
*Masu facebook ku yi following wannan account Ιin domin samun damar cin giveaway Ιin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*
https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL
βA'uzu billahi minashshaidanir rajimβ Ummi ta furta lokacin da ta yi arba da baβkar fuskar Tanimu a matsayin wanda ke sallama da ita. Dakatawa ta yi daga bakin k'ofa ta kasa k'arasowa cikin zauren, sai bin shi take yi da wani irin mugun kallo, mai cike da tsana tsaba. Zuciyarta cike take fal da tsoro, amma a zahiri sam babu alamar hakan a kan fuskarta. Shu'umar murmushinsa ya saki yana jan dogon gemunsa yana binta da wani kallo, irin ta gogaggun y'an duniya tare da ce mata "K'araso mana Balkisu mai gadon zinare, Alheri ne ke tafe sa ni, na canza shawara domin daren jiya na kasa barci kyakkyawar surarki ce ta dinga yi mini gizo zuciyata ta sake kwadaituwa da son tarawa da ke, yayinda gangar jikina ke sake fallasa mini muradinta na son yin nitso a kogon ni'imarki, shine
na ji a raina gara na zo mu sasanta, idan hagu ta ki sai a koma dama ko na haka ba yar shilata." Ya karashe maganar yana fitar da wata sautin murmushi mai cike da zallar iskanci.
Had'e girar sama da ta k'asa ta yi babu alamaun fara'a ko sassaci ko miskala zarratin a fuskarta, ta ce "Ta Allah ba taka ba mugu fasiki dan Akuya, da yardar Allah baza ka ta6a cin galaba a kaina ba, baza ka ta6a cimma mummunar nufinka a kaina ba har lokacina ya cika na bi bayan mijina, kuma ka fita kabar mini gidana bana bukatar taimakon daga wajenka ko wani naka, Allah da na rike zai kawo wanda zai tallafa mana." Takowa ya shiga yi gareta yana fadin "Haba mana balkisu, ya zaki yi mini haka, wannan harkar fa cudanni in cudeka ne, kan ki kawai zaki mallaka min na rana d'aya, ni kuma na jiyar take dad'in da babu wani namijin da ya ta6a jiyar take irinsa a duniya, tun daga kan kwaratanki har zuwa kan mataccen mjinki, iye yan mata kar ki yi mani rowa mana, nasan ai kema kina da muradi." Ya karashe maganar yana kokarin kai hannusa jikinta.
Da sauri ta ja baya hankali tashe take fad'in "Tanimu kar ka ta6a ni, ka fitar mini daga gida ni ba fasika bace irinka." Dariya ya kece da shi, ya ce "to muje cikin gidan mana ai nasan babu kowa daga ni sai ke sai Allah, kinga sai na cika tsohon muradina a kan ki ko ta karfi ne." Yana maganar yana dariya.
Jin hakan ya matukar daga mata hankali, take ta sake k'amk'ame hijabinta tana sake ja da baya, yayinda shi kuma ya ci gaba da biyota har suka shiga cikin gidan.
Zuciyarta ta dinga bata shawarwari shin ta juya ta runtuma da gudu ne zuwa dakinta ta datse kofa ko kuma ta nemi makami ta illata shi ko kuma dai ihu zata yi mashi.
Kamar ya shiga zuciyarta ya ga abinda take kitsawa sai ji ta yi yana cewa " Kina tunanin yi mini ihu ko? To bismillah, idan kika yi mini ihu na rantse miki da Allah k'aik'ayi ne zai koma kan mashek'iya don sai kin gwammace mutuwa da irin Sharrin da zan kulla miki."
"Mugu azzalumi dan Akuya Allah ya fika." Murmushi ya yi ya ja gemunsa ya ce "Balkisu taurin kai! Ni wallahi ko a yanzu kika bani kan ki na minti ashirin na miki Alkawarin a yau zan je na nemawa dan ki aure kuma na tsaya masa babu wanda zai san shege ne balle ayi masa gori, ba sai munje da nisa ba a tsakar gidan nan ma sai mu yi mu ta shi don ni ba bakon zafi bane." Ya fad'a yana murmushi tare da bin tsakar gidan da kallo.
Wannan kalle kallen daya tafi ne ya bata damar zarar wuka a jikin rufin din kitchen Inda suke ajiyewa, cikin zafin nama ta kai mishi yanka cike da shammata, da sauri ya saka hannu sa ya tare yankan hakan yaba wukar damar yankarsa a tafin hannu mugun yanka kuwa, take jini ya balle, razananniyar kara ya saki tare da rike hannun, tuni idanunsa sun kada sunyi jajur, rigar jikinsa tuni jini ya bata shi kaca-kaca.
Ganin yadda mini ke zirara kamar an yanka karamin dabba yasa jikin Ummi ya fara karkarwa take ta sake wukar dake hannunta, don ta tsorata ainun, tunda ta taso ita mai taushin zuciya ce ko kiyashi bata kashewa da gangan balle ace wai yau ita ce ta yanki mutum da wuka haka jina na zuba, hakan ya tayar Maya da hankalin ainun.
Bata yi aune ba taji ya shaki wuyar hijabinta tare da hed'e ta da bango kafin ya shiga wanka mata mari a fuskarta, karfi ya saka ya yage hijabinta jikinta ya damk'i wuyarta ya shake, a zuciye cikin zaro jajayen idanunsa yake cewa " Ni zaki jiwa ciwo! Ni za ki yi wa lahani! Wato don kinga ina bin ki ina da lalla6a ki ko, to bari na turmushe ki ta karfi da ya ji muga ta tsiya." Yana maganar ne cikin fitar hayyaci da tsananin fusata, yayinda ya shiga kokarin keta dogon rigar atamfar dake kijinta.
Babu zato wani irin wawan naushi ya sauka a gefe fuskasa wanda sai da jini ya yi tsartuwa daga bakinsa ya famtsama a fuskar Ummi, babu shiri ya sake ta tare da tallafe gefen fuskarsa ya furzar da miyan bakinsa mai gauraye da jini, saiga hakora uku turame sun biyo.
Kafin ya gama tantance meya faru, Al'ameen ya yi wa wuyarsa wata irin muguwar shaka, idanunsa a waje cikin tsananin fusata ya shiga dukansa ba tare da ya tsaya tantance wanene ba.
Cikin yan dak'ikai ya hada mishi mi shi jini da majina, nan ya zube kasa warwas kamar gawar sababi, bai bar shi ba ya zauna a ruwan cikinsa ya ci gaba da duka yana fadin "Mahaifiyata, Uwata ita za ka yi wa fyad'e kai waye, wallahi wallahi, sai na kashe ka, ni Muhammadul-Ameen yau sai an kashe ka."
Jin shirun Al'ameen ya yi yawa yasa Aliyu dake jiransa a kofar gidan ya miko masa sak'o, ya gaza hakuri ya kutso kai cikin gidan, tun daga Zaure ya fara jiyo sambatun Ameen hakan yasa ya k'arasa cikin gidan a guje, abinda ya tarar ne ya saka shi zare ido tare da runtumawa da gudu ya shiga kokarin bambare hannun Al'ameen a wuyar mutumin da yake duka kamar Allah ya aiko shiz sun yi kokawa sosai kafin ya samu nasarar daga shi daga kan mutumin.
Jijjigashi Aliyu ya shiga yi , yana fad'in" Ameen menene haka ka dawo cikin hayyacin mana." Sam Al'ameen ba ya jinsa, sai yunkurin kwacewa ya ke daga rikon da Aliyu ya yi masa yana kokarin sake kaiwa Yaya babba cafka, ganin haka yasa Yaya babba mikewa a daddafe ya fece daga gidan ba tare da ya tsaya ko neman takalmansa ba.
"Ka sake ni Aliyu, wallahi sai na kashe shi , bazan barshi ba, sai na raba shi da numfashin sa." A tsawace Aliyu yace "Ka nutsu Ameen, ka kalli halin da Ummi ke ciki."
Jin haka yasa shi saurin juyawa gareta, a kwance take sharaf a kasa kamar bata numfashi, da wani irin sauri ya karasa gareta ya dagota yana jijjigata tare da kiran sunanta, da kyar ta bud'e idanunta dake lumshewa ta kalle shi a kan la66anta ta furta "Ka kula da Fatima Ameen na bar maka ita amana nasan za ka iya.... Bata karkareba idanunta suka lumshe numfashita ya dauke cak! " Ummi!!!!!!!! Ya ambata da Iya dukkan karar muryarsa..............
Kunfa rage comment mutanen Joyπ¬
Oum ummeertah
09116099486
[12/29, 2:51 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 44*
Mikiya Writer's Association
Cike da tsananin tashin hankali Al'ameen ke safa da marwa a bakin d'akin bada agajin gaggawa na karamar asibitin dake unguwarsu, in da suka yi gaggawar kai Ummi bayan sun fahimci suma ta yi ba mutuwa ba, tunda suka kai ta kimanin awa hudu a tsaye yake kamar mashi, a k'ofar d'akin sallar magriba da ishsha ne kadai ya kau da shi daga wajen, Fatima na zaune a kan d'aya daga cikin bencinan da a ka tanada domin zama, sai kuka take yi idanunta sun kumbura sun yi jajur, dawowarta daga hadda ta tarar da wannan tashin hankalin ko gida bata kai ga shiga ba ta ga an fito da Umminta a sume kamar gawa, hakan ya daga mata hankali, a guje ta kutsa kai cikin napep din da aka sanya Ummi ta kamkameta tana kuka, tun lokacin take rusar kuka har zuwa yanzu da ake neman karfe goman dare. Yau dai kam kasa rarrashinta Al'ameen ya yi, Aliyu da Maman Amira wacce ta biyo su asibitin daga baya ne suke kokarin bata baki idan suka ga kukan nata ya yi yawa.
Likita ne ya fito daga d'akin , da sauri suka yi caaa! A kan shi kowanne na jeho mishi tambayar da ya zo bakinsa duk a game da Ummi, kallonsu ya yi cike da tausayawa ganin yadda hankalinsu ke tashe, murmushin kwantar da hankali ya sakar musu, ya daura da cewa "Ku yi hakuri yaran Ummi, Ummi tana lafiya, firgicine ta shiga shine ya haifar mata da daukewar numfashi ta yi, dogon suma, yanzu dai Alhmdllh mun bata taimakon da ya dace ta farfado tun dazu,sa dai mun yi mata allurar barci domin kwakwalwarta ta samu hutu, zuwa safiya in dan Allah ya kai mu zamu sallameta.
Hamdala Aliyu da Maman Amira suka shiga jerowa, Al'ameen ku wa rintse idanu ya yi shima yana jero hamdala a zuciyarsa, wani irin farin ciki da kwanciyar hankali na maye gurbin fargaba da tashin hankalin da ke dankare a zuciyarsa. Yayinda Fatima ta rungume Mama ta na shessheka tun da dama cikin kuka take.
Aliyu da Ameen ne suka kwana a asibitin, Mama da Fatima kuma suka tafi gida, bayan sun shiga sun duba Ummi, tana barci kamar yadda likita ya fada.
Bayan tafiyarsu ne Al'ameen ya samu damar baiwa Aliyu labarin abin da ya sani game da abinda ya faru, yana ba shi labarin zuciyarsa na kara daukar zafi yana sake cin alwashi a kan kassara rayuwar koma waye wannan mutumin, shi kan shi Aliyu ran shi ya baci, zuciyarsa ta tashi har yaso yafi Ameen daukar zafi a kan lamarin, ko da wasa bai ta6a kawo hakan a ransa ba, ya ciji yatsa ya fi sau shurin masaki a kan rike Al'ameen da yayi har mutumin da ko sunan sa basu sani ba ya samu damar guduwa, karshe Ameen ne ya koma tausarsa.
Washegari karfe goma a ka sallami Ummi, a lokacin Fatima da Amira ne ke tare da ita don Aliyu tun wuraren bakwai ya tafi gida da zummar kimtsawa ya dawo, Al'ameen ma ganin sun zo yasa ya tafi gida don yin wanka.
Sosai makota da abokan arziki sukai ta shigowa yi wa Ummi sannu, yinin ranar bata samu kanta ba, kallo daya zaka san bata cikin walwala amma haka ta daure ta saki fuskarta ta dinga amsa gaisuwar yan dubiya.
Ranar da matsanancin damuwa Al'ameen ya kwana, bai iya rintsawa ba, burinsa ya ji daga bakin Ummi 'shin wanene wannan mutumin, domin baya jin har duniya ta nade zai iya yafe mishi.
Washe gari da safe ko da ya je gaisheta bata ce masa komai game da batun ba, haka ya shirya ya tafi makaranta jiki babu kwari, da yamma tare suka shigo gidan da Aliyu ya biyosa don ya sake gaida Ummi duk da jiya ma yazo, kuma mahaifiyarsa da matar kawunsa harma da kannensa sun zo suma a jiyan.
A falonta suka same ta zaune a kan dadduma, carbi a hannunta tana lazumi, zama suka yi suna jiranta, itama ganin shgowarsu yasa ta yi sauri ta kai karshen lazumin, Aliyu ne ya fara gaisheta da jiki ta amsa cike da kulawa, Al'ameen ma ya sake gaisheta.
Daga haka duk zama suka yi jugum-jugum daga yanayin fuskokinsu ta fahimci da magana a bakunansu, ajiyar zuciya ta sauke dama ta san ko ba jima ko ba dad'e wannan ranar zata zo, bata gama tunanin da take yi ba ta tsunkayi muryar Al'ameen yana cewa.
"Ummi don Allah da manzonsa ki gaya mini wanene wannan mutumin? Kallonsa ta yi sai kuma ta yi shiru, ba tare da amsa shi ba, ganin haka yasa Aliyu kar6ewa da " Ummi don Allah ki daure ki sanar da shi, domin yana cikin matsanancin damuwa ni shaida ne, saboda ni amininsa ne, muna da kusancin da bazai iya boye min duk wani damuwarsa ba, nine na ba shi shawara a kan ya zo ya tambaye ki, shi kuma ya ya dauko ni don na taya shi rokon ki, Ummi don Allah ki fad'a masa menene hadin ki da shi."
Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu, ta ce "Dama ko baka tambayeni ba Yayan Fatima yau ne na yi niyar sanar maka su wanene ahlin Alhussain a gare ku da nima baki d'aya." Aliyu ya ce "Alhmdllh Ummi, Ameen ya dade yana tsumayen wannan ranar tsayin shekaru." Ya k'arashe maganar cike da tsantsar farin ciki kamar shine Ameen d'in. Murmushi Ummi ta yi tana sake jinjina amintar dake tsakanin Aliyu da Ameen, kamar dai Fatima da Joy.
Fatima ce ta shigo d'akin daga hadda take, ganin yayyinta yasa fara'ar fuskarta k'ara fad'ad'a, ta gaishesu baki d'aya a ladabce, ta wuce uwar d'aka ta ajiye hijabinta da jakar haddarta ta fito zata wucesu, har ta kai bakin k'ofa, Ummi ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Fatima! Kema zo ki zauna." Bata musa ba ta dawo ta samu guri kusa da Yayanta ta zauna, zuciyarta na tsinkewa haka kurum take jin gabanta na fad'uwa.
Mikewa Aliyu ya yi, da nufin tafiya gida don ya basu waje, Ummi ta dakatar da shi da cewa; Dawo ka zauna Aliyu, domin kuwa kaima d'ana ne, tamkar Al'ameen haka nake jin ka." Bud'e baki ya yi da nufin yi mata musu, sai dai ganin yadda ta tsare gida yasa ya kasa, sai dai bai koma ya zaunan ba kamar yadda ta umarceshi, idanunta ta watsa mishi, irin kallon da take yi wa Al'ameen idan tana son ladaftar da shi, babu shiru ya koma ya zauna.
Sauke kai Ummi ta yi kasa ta yi shiru duk ido suka zuba mata falon ya dauki shiru na tsayin mintuna biyu, a hankali ta dago idanunta da suke cika taf da kwallah cikin wani irin murya mai sanyi wacce basu ta6a junta da irin shi ba ta fara cewa..............
Oum ummeertah
09116099486
[1/18, 12:39 PM] +234 803 069 9057: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 45*
Mikiya Writer's Association
*Assalamu alaikum, barkanku da war haka yan uwa masoya masu kamshin Appleπ Kamar yadda kuka sani sunana Aisha Nalado, marubuciyar littafin Joy. kwanakin baya kun ji shiru kamar Mallam ya ci shirwaπ¬ nasan wasunku sun san dalili wasunku kuma basu sani ba, ga wadan da basu sani ba, hakan ya faru ne saboda arzikin da Allah ya yi mini na samun k'aruwa, ina nufin Allah ya azurtani da haihuwa, shiyasa na dauki hutu, to Alhmdllh ina mai farin cikin sanar daku cewa na dawo, in sha Allah zamu daura daga inda muka tsaya da fatan za ku yi farin ciki da jin hakan.*
Sauke kai k'asa Ummi ta yi, kamar bazata kuma cewa komai ba.
Duk ido suka zuba mata falon ya d'auki shiru na y'an wasu mintoci, a hankali ta d'ago, idanunta cike taf da kwallah ta dube su, da wani irin murya mai sanyi wacce basu ta6a jin ta yi irin ta ba, ta fara cewa.
"Ni kaina bansan wacece ni ba, ban san daga wata duniyar na fito ba, ban san komai game da rayuwata ba abin da na sani kawai shine bani da galihu!" Ta kai karshen maganar cikin wani irin rauni, muryarta na rawa alamar kuka ke shirin kwace mata amma ta yi kokarin danne shi da karfi.
Shiru ta yi ta daga kai sama alamar tana tunano wani abu tare da kokari mayar da hawayen da ya ke daf da wanke mata fuska , ta dad'e a haka kafin ta kalle su ta ci gaba da cewa
Wata ranar Alhamis wacce bazan ta6a mantawa da ita ba, na bud'e ido na tsinci kaina a tare da ahlin gidan Mammam kura, bani da masaniyar abin da ya faru a lokacin domin bana cikin hayyacina amma ina da cikakken labari komai, don Al-husain ya sanar dani komai kafin ya bar duniya kamar haka:
Al-hussain Mammam kura shine wanda ya tsince ni a mararrabar dukko a hanyarsa ta dawowa daga kano zuwa cikin garin Minna.
A kallo d'aya baza a kira ni da mahaukaciya ba, saboda tsab na ke cikin shiga ta kamala ina janye da hannun yaro, wanda ke matukar galabaice ya yi kuka har ya gaji ya yi shiru. Yadda na ke tafiya ina tangad'i, kafafuna futu futu da k'ura ne zai tabbatar wa mutum bana cikin koshin lafiya, Allah kad'ai yasan daga duniyar da na ke.
A dai dai wannan lokacin hussain yayi fakin motarsa a dokar daji ya kewaya domin biyan bukatarsa, bayan ya kammala ya taso domin ci gaba da tafiyarsa. tun daga nisa ya hangi mace cikin tsananin galabaita da fitar hayyaci ta rafka karo da motarsa, "Subhanallahi! Ya ambata kafin ya karaso gare ni kuma yaga na zube kasa sharaf a gurin, daga yaron da na ke ja, da gudu ya 'karaso gurin cikin tashin hankali ya shiga waige waige, ganin babu mataimaki sai Allah yasa ya yi bismillah ya dauke ni ya saka a bayan mota bayan ya fara daga yaron dake kuka zuwa lokacin.
Asibiti mafi kusa ya kai ni, bayan samun taimakon gaggawa da nayi daga nurs, na farfado, sai dai babu um babu um um! sannan idanuna a juye suke tabbacin ba na cikin hayyacina, tambayar duniyar nan ya yi domin ya samu ya mayar da ni gidanmu amma babu bakin magana, ganin haka yasa Alhussain dauka cewa ma'aikatan asibitin ne basu san aikinsu ba, sai kawai ya nemi sallama, a ganinsa gara ya karasa da ni cikin gari ya kai ni babban Asibiti, babban likita ya duba ni.
Muna shiga cikin garin Minna direct general Hospital ya nufa da ni, na samu ganin babban likitan da ke kan aiki ya kuma rubuta mana test din da zamu je mu yi ciki harda na kwakwalwa don shima kansa a tunaninsa mahaukaciya ce.
Sai dai wani kudirar Ubangiji test din ya nuna lafiyar kwakwalwarta kalau, shi kansa a Alhussain bai za ci haka ba bare kuma likita, hakan yasa ya sake tura mu wani asibitin domin sake yin wani test din, nan ma dai kamar cen, aka sake tabbatar da komai normal, tun daga nan Alhussain ya d'iga wa lamarina Ayar tambaya, kwanana uku aka sallameni , har zuwa lokacin bana iya bude baki bare na furta wani kalma, idanuna a juye hasalima ban san a ina nake ba.
Ya yi matukar shiga damuwa ganin har an sallameni bai ji Daga gareni ba, bare yasan daga ina na fito maida ni gida, hakan yasa dole ya tunkari gidan iyayensa da ni, don ba ya jin zai iya rabuwa da ni a cikin wannan halin, a cewarsa bai san hannun da zan fada ba, bugu da kari haka kawai yeke jin wani feeling a zuciyarsa game da ni, uwa uba a cikin kwanaki ukun nan yayi wani irin mugun sabo da yaron da har zuwa lokacin ya kasa gazgata cewa nawa ne.
Tashin hankali gobarar gemu! An sha gwagwarmaya sosai a gidan marigayi Mamman kura, lokacin da Alhussain ya dawo musu da tsarabar tsintacciyar mahaukaciya kamar yadda suka rad'a min suna, duk bayanin da yayi musu sun ki gamsuwa karshe sai da rayuka da yawa suka baci, an kai ruwa rana sosai tsakaninsa da yan uwansa da kuma mahaifiyarsu kafin ya samu damar ajiyeni a gidan, kasancewar shima kafaffe ne na karshe kuma dai duk cikin yayan gidan shine mai dan abin hannu Allah ya yi masa nasibi, hakan yasa ake daga masa kafa wani lokacin.
Dakinsa dake cikin gidan ya saka ni yayinda shi kuma ya koma Zaure da kwana, babu mai shiga safgata a cikin gidan babu mai ba ni abinci babu mai kula da yarona idan Alhussain baya nan.
Cikin kwanaki goma Alhussain ya dage da neman min magani, inda ya dauko wani babban malami mai bada taimako ya zo har gida ya duba ni ta shin farko ya tabbatar da cewa bakin sihirine a jikina farrak'u ne mai karfi wanda karyewarsa zai yi bakar wahala, sai dai zai yi taimako dai dai gwargwadon iyawarsa da izinin Ubangiji.
Tabbas! Babu abin da ya gagari Allah,Mallam ya yi kokari sosai wajen ganin ya taimakawa min, aiki ya yi tukuru, sati daya cur ya kwashe yana gwagwarmaya , kafin Allah ya nufa na dawo cikin hayyacina, sosai Alhussai ya yi farin ciki da hakan , sai dai kuma da sauran rina a kaba don sam na kasa tuna rayuwarta ta baya, kwakwalwata ta dawo empty kamar dai ace wacce ta samu lost of memory.
An yi an yi na tino koda sunan garinmu ne abu ya gagara, ganin haka Mallam ya bada shawarar akan a bar wa Allah sauran lamarin a dage da addu'a, idan Allah ya nufa wata rana zata zo da da zan tuna ko ni wacece ko Daga ina nake ranar da har yau ba ta zo ba, ranar da nake tsumayen gani kafin Allah ya dau raina" ta dakata tare da share hawayen da sai a sannan ya yi nasarar zararowa daga idanunta.
Zuwa lokacin Fatima kuka take yi sosai kamar ran ta zai fita, Aliyu ma a fakaice ya ke dauke hawaye da handkerchief , ya yin da idanun Al'ameen suka rine jajur kamar an watsa masa barkonun tsidigu.
Dakewa Ummi ta yi ta ci gaba da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 22