Share this page
gama musu kowa na fad'in shi yafi missed d'in dan uwan shi, Fatima ta ce "Ya aka yi Ki ka had'u da yayana, ni farin ciki ma ya hana ni wannan tunanin sai yanzu." Ajiyar zuciya Joy ta sauke ta ce "Friend labarin da tsayi amma bari na takaita miki." Tiryan tiryan ta shiga bata labarin abin da ya faru da ita tun daga ranar da Fatima ta je gidan su, wasikar data aiko mata da replay din data bata zuwanta gidan haduwar ta da Al'ameen da abinda ya wakana, hatta bige shin da suka yi bata boye mata ba, zuwa yadda aka yi ta samu fitowa, sai dai koda wasa ta kasa fad'a mata yadda soyayar Al'ameen ya mata kamun kazar kuku. Mamaki gami da dum6in Al'ajabi ne ya cika Fatima jin wai motar Joy ce ta kad'e Al'ameen, lallai Yaya Ameen yana da kyakyawar zuciya ko da wasa bai fad'a musu cewa itace ta kad'e shi ba, kuma harga Allah bai rike ta a zuciya ba, don ko yan dubiya ne suka zo irin masu kumbar bakan nan idan suna tsinewa wanda ya bige shi yakan ce su bari babu komai shi ya yafe, kuma suma ba da gangan suka yi ba. Ranar Fatima da Joy kamar karsu rabu. Dakyar ta yadda Fatima ta rakata ganin karfe shidda ya gota,Fatima kuwa tsoron Mom ya riga ya gama cika ta, shi yasa ta dinga kora Joy akan ta tafi amma ba wai don ta gaji da ganinta ba, ita bata ki Joy ta dawo gidan su da zama ba su dinga kwana suna ta shi tare, Ummi na yi musu dariya suka ta fi, ta ce "Teetee mu je na k'ara gaisar da Yaya Alamein, ba tare da tunani kamaj ba Fatima ta ce "Ok muje." A kofar d'akin Fatima ta yi sallama, shiru babu amsa, hakan ya sa ta lek'a wayam baya ciki, dagowa ta yi ta kalli Joy ta ce "Ya fito." Kwa6e fuska ta yi ta ce "Ina ya je." Dariya Fatima ta yi ta rik'e ha6a tare da cewa "Iyeeee, wannan sabon salon fa." Sai lokacin ta fahimci mai ta yi, Itama dariyar ta yi ta ce, "Ina son ganin dat his cute face kafin na tafi.Teetee mu jira ya dawo sai na tafi." Zaro ido Fatima ta yi kafin ya ce wani abu sai gashi yana shigowa, fatima ta ce "Yawwa Yaya zo kaji." Da sauri joy ta kai hannu ta rufe mata baki, tana zare ido, bata yi zaton yana kusa ba, jingina ya yi da bango ya yi folding hannayesa a kirji ya ce "Menene sister gayamin, gulma na FARHAT ta yi ko." Girgiza kai Fatima ta yi, ya ce "To menene." Kallon Joy ta yi tana dariya da sauri ta girgiza mata kai, sai kawai ta ce "Yaya babu komai." D'age kafada ya yi ya ce "Ku kuka sani Ku bani hanya na shiga dakina." Kaucewa suka yi ya shige bayan sun yi sallama da Joy. Har inda suka yi da David zasu hadu Fatima ta rakata, a wurin suka tarar da shi shima isowar shi kenan, kallo Fatima ya yi yana murmushi ya ce "Fatima my classmate." Harara ta watsa mashij, ya kyalkyale da dariya ya ce "Yau ina cikin farin ciki don haka bazan kulaki ba, amma zamu jone, muje Joy time ya wuce sosai." Ya karashe maganar yana kallon agogon dake daure a hannun shi........... 09116099486. [12/29, 2:44 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 30* Ga link domin shiga group na Littafin *JOY* kai tsaye. https://chat.whatsapp.com/EhPtIfeNaTtCC2GS6SvOnW Tun daga wannan ranar k'awancen Fatima da Joy ya dawo d'anye sharrr!shak'uwa da soyayya da sukewa juna ya sake nunkuwa, abin har mamaki ya ke ba Al'ameen sai ka ce wasu tagwayen da su ka fito mahaifa d'aya. Kusan kullum sai Joy ta zo gidan su Fatima daga school ba tare sanin Mom ba, yanzu bata da wata matsala ko shamaki da yin hakan, dama can David ne matsalar kuma yanzu ta yi maganin shi ta hanyar sakar mishi kud'i, tunda ta fahimci halin shi, sai ta ci maganin zama da shi. Daga ita har Fatima yanzu hankalinsu a kwance ya ke sai walwalarsu suke kamar basu da sauran damuwa. A halin yanzu zaman Fatima a gida shi ya fi tayar musu da hankali, kullum cikin zulumin school d'in da Al'ameen zai kaita su ke yi. Joy har ta fi Fatima shiga damuwa da tashin hankali a kan hakan, zama suka yi suka yanke shawarar zasu same shi su bashi hakuri a kan ya barta ta ci gaba da zuwa tsohon school d'inta kar ya canja mata. Har daki suka same shi, karo na farko da Joy ta fara shiga d'akin shi, sosai ta yaba da kyawun d'akin duk da ba wasu abin azo a gani ne a ciki ba, yar katifarsa ce, sai karamin wardrobe na kayan shi, sai yar duruwar da yake zuba littafai, sai hanga dake sama ta bangon gabas d'in dakin,sai ko dan tarkacen da baza'a rasa ba, iyakarsu kenan sai dai ko ina tsab kamar ba d'akin namiji ba sai daddad'an kamshin room freshener ke tashi. Yana daga kishingide cikin damuwa, ya yi nisa cikin duniyar tunani, suka yi sallama sanye yake da singlet da short kasancewar a kwai zafi a garin ga babu wutar nefa, ga dai hadari d'ankare a sararin samniya, amma kuma rana ake kwallarawa kasancewar daminar na gaf da wucewa, ganin su yasa ya yi sauri ya ja bargon dake kan katifarsa ya rufe daga kwankwasosa zuwa k'asa, ya ta shi ya zauna da kyau fuskarsa babu walwala saboda yanayin damuwar da ya kwana ciki. Bakin katifarsa Fatima ta laluba ta zauna, Joy kuma ta zauna daga gefenta a k'asa, kallo d'aya ta mishi ta d'auke kai ganin shi sanye da singlet gaba d'aya surar mazantakarsa a bayyane ga wani kwantaccen bakin bashi luf a kirjinsa, duk sai ta ji wani iri a jikinta, hakan yasa har suka gama gaisawa bata iya d'ago kai ta sake yi masa kallo na biyu ba, sai da ta tsinci muryar Fatima na cewa; Yayana dama Joy ce ta ce na rakota tana son yin magana da kai. A zabure ta dago jin kullin sharin da Fatima ta mata, dai-dai lokacin ya mai da kaifaffun idanunsa kanta, carat idanuwansu ya sark'e da na juna, da wani irin sauri ta kawar da kai don ji ta yi gabanta ya yi wani irin fad'uwa, zuciyar ta kamar zata faso kirji ta fito, Fatima ta zungura da itama tsabar kwarjinin shi yasa ta kasa fadar bukatarsu kai tsaye. Dagowa Fatima ta yi ta kalleta, Suna hada ido ta watsa mata harara tare da yi mata kallon ya zaki mini haka, alamar ki fad'a ma shi, Fatima ta mata da ido, ta sake watsa mata harara tare da make kafad'a ta mata alamar ke ki fad'a. Duk abin da suke yana kallonsu, ganin suna neman 6ata masa lokaci yasa ya yi gyaran muryar duk d'ogowa suka yi suna kallon shi, idanunsa a kan Joy ya ce "Uhummm! FARHAT ina jin ki." Cikin inda-inda ta ce "Daa da dama! Mun zo ne, mu rok'e ka a kan ka yi hakuri kabar Fatima ta ci gaba da zuwa school, kar ka canja mata wani' ko Fatima ai haka ne ko?" Ta fada tana kallon Fatima da sauri Fatima ta girgiza kai ta ce "E, e, Yaya haka ne don Allah ka yi hakuri ka bar ni na ci gaba da zuwa can d'in." Duk da yanayin damuwar da yake ciki sai da suka so ba shi dariya; ji yadda suke abu kamar uban wani ya turosu, ba su suka gama tsara abinsu ba, ji adanun Fatima kamar wacce ta yi wa sarki k'arya, ita kuma kawar cin mushenta ji nata kwala-kwala kwalan idanun kamar fitulun mota. A zuciyarsa yake musu wannan tsiyar, dakewa ya yi ya ce, to shikenan na ji kuje sai na yi shawara, har suna had'a baki wurin cewa "To Yaya mun gode." Suna fitowa "ta zubawa Fatima dundu ta ce " Haka muka yi dake Teetee." Dariya Fatima ta saka ta ce, "To ni kasa fad'a na yi yasin kwarjini ya min." "To kema kenan ina ga ni, amma sai naga kamar bai dauki maganar mu da mahimmanci ba." Fatima ta ce "Wallahi kuwa, tunda kika ji ya ce haka, amma nasan abin da zamu yi da Ummi zamu hada shi nasan idan ta saka baki idan da yuwuwar ya bar ni zai bar ni." Da kyar Ummi ta amince musu zata mishi magana, sai da suka yi ta magiya da bambaki! A ranar kuwa daya dawo da dare ta tuntu6e shi da zance, kallon Fatima ya yi da ta yi saurin yin k'asa da kai ya jefe mata kallon tuhuma, Ummi ta ce "Amintacce kai na ke sauraro, idan da yuwuwar hakan don Allah ka barta ta koma can d'in su k'arata tunda sun kusa kammalawa." Jim ya d'an yi kafin ya ce "To Ummi shikenan, ta shirya zuwa Monday sai na rakata da kai na Allah yawa hakan shi ya fi alkhairi ya kad'e fitina." Ummi ta amsa da "Amin ya Allah." Fatima kam washe baki ta yi tana dariyar farin ciki, Al'ameen ya jefa mata hararar wasa, sake kyalkyalewa ta yi da dariya tare da cewa; Thank u Yayana Allah ya faranta maka kai ma." A tare suka amsa da Amin shi da Ummi. Ummi ta ce "Wai ni kam Yaran nan ko kun ji mini motsin Amiratuwana, yau idan ban yi karya ba kusan kwanan ta goma rabonta da gidan nan, Allah yasa dai lafiya." Fatima ce ta dago da sauri tare da cewa "Yawwa Ummi tun ranar Asabar a hadda Aysha ta ce min bata da lafiya wallahi na manta na gaya miki kwata kwata na sha'afa." Tafa hannanye Ummi ta shiga yi tare da sakin salati. "Haba Fatima, yanzu tun ranar Asabar aka gaya miki amira babu lafiya amma ki ce wai kin manta, Haba haba Fatima amana bai ce haka ba, Amira ai ta wuce haka a gareki, don komin lalacewar giwa ta fi karfin kwandon goro, wato yanzu kin samu Joy shikenan kin rabu da kowa ko? Gaskiya banji dadi ba baki Kyauta min ba, ai hausawa sun ce ka gaida mai gaisheka ko ba zai amsa ba." Haka Ummi ta yi ta mita tare da yi wa Fatima fad'a, can kuma ta ce "Amintacce duba min karfe nawa idan dare bai yi nisa ba yanzu zan shiga na dubo ta yarinyar kirki, ai ko iyayenta ma sai su zageni ba don Allah yasa mutanen arziki ba ne." Shikam Al'ameen shaf ya manta da batun wata Amira, zai iya cewa tun daga ranar da wannan maganar ya shiga tsakanin su bai kuma saka ta a ido ba, agogon ya duba kamar yadda Ummi ta umarta jin tana ta sake tambayar shi karfe nawa ya ce "Ummi goma da rabi ta gota nasan yanzu sun kulle kofar gida ki bari da safe." Badan ta so ba dole ta hakura, amma fa ranar Fatima taga fushin Ummi, itama duk ta yi laushi jikinta ya yi sanyi tabbas bata Kyauta ba, gaba daya cikin yan kwanakin nan Joy ta d'auke mata hankali ita ce kadai a rai da zuciyarta. ************ *AMIRA* Tun daga ranar da Al'ameen ya nuna baya da ra'ayinta ta shiga matsanancin damuwa, a ranar ta yi kuka kamar baza ta daina ba, har sai da ta kwanta zazza6i na kwana uku, tun da ta tashi daga wannan zazza6in gaba d'aya ta canza, a hankali aka fara rasa gane kanta, bata da aiki sai kuka sai tunani, kurmar karfi da yaji ta naimi komawa, don tana iya wayar gari ta wuni ta kwana ba tare da ta cewa kowa uffan ba, lamarin da ya fara d'aga hankalin ahlinta, wa'ec d'in da suka fara bada ita aka kark'are ba, sosai Maman Amira ta shiga damuwa duk a tunaninta iskokai ne suka shigeta, hakan yasa kullum cikin tofa mata addu'o'i take da amso mata taimako a wurin malamai, amma a banza lamarin sai dad'a gaba ya ke yi, wani irin rama da mugun haske ta yi cikin abin da bai fi wata guda ba, kusan sau uku suna zuwa asibiti ganin likita maganar daya ce kullum; damuwa ce ke damunta." tambayar duniyar nan ta k'i fad'awa kowa damuwar, sai dai ta ce ita babu wani damuwar da ke damunta, har kuka mahaifiyarta ta yi mata ta yi magiyar ta yi nasihar ta yi fad'an akan ta gaya mata matsalarta amma a banza, hakan yasa Maman ta k'ara gaskata zarginta na cewa; Iskokai ne suka shigeta. Da farar safiya Ummi ta yi wa gidan su Amira dirar mikiya, lokacin ko Al'ameen bai dawo daga masallaci ba, wasu masallatan ma ba'a idar da sallah ba, itama tana sallame nata ko tasbihi bata yi ba ta tashi, don jiya dakyar ta yi barci saboda damuwa da tunanin halin da Amiranta ke ciki, yarinyar kirki, babban abin da ya k'ara d'aga mata hankali bai wu ce mummunar mafarkin da ta yi a kan ciwon Amiran ba, kwarai ta tsorata da lamarin, don ita kanta tana tsoron mafarke mafarken da take yawan yi a cikin yan kwanakin nan. Tsakar gidan babu kowa, duk su na d'aki, a k'ofar d'akin Maman Amira ta yi sallama, Aysha ce ta fito tana amsawa, ganin Ummi yasa ta yi saurin risinawa ta gaisheta, ummi ta ce "Ina gajiya Aysha ya mai jiki." "Alhmdllh Ummi tana samun sauk'i." Kafin Ummi ta ce wani abu Maman amira ta fito daga d'akin sanye da hijabi hannunta r'ike da carbi, murmushi ta sakar wa Ummi tare da cewa "Maraba da Ummi ke ce da farar safiyar nan, ina kwananmu ya kwanan iyalai." Ummi ta ce "Ni ce Maman Amira, ya mai jiki, wallahi ban ji sai jiya da dare, da nake cewa yara nikam kwana biyu banga Amira ba, shine Fatima ke ce min wai bata da lafiya, wallahi hankalina ya ta shi, ba dadon dare ya yi ba da a daren zan shigo na duba ta, a addafe na yi barci jiya wallahi." Ta karashe maganar cike da alhini da tausayawa. Maman Amira ta yi murmushin karfin hali ta ce "Allah sarki Ummi Kiyi hakuri wallahi nima harda laifi na da ban aika miki ba lamarin ne da rikitarwa." Ta fad'a damuwa bayyana k'arara a fuskarta ta, hakan ya k'ara daga hankalin Ummi, "Ki shigo daga ciki gata nan." Maman Amira ta fad'a tana juyawa cikin d'akin da sauri tare da d'auke dan guntun hawayen da ya zubo mata ba tare da ta bari Ummi ta gani ba. Salati da sallallami Ummi ta saka a lokacin da ta yi arba da Amira kwance a kan gadon Mama tana barci, wanda sai gabanin asubahin nan ya dauketa cewar Mama "Na shiga uku ni Balkisu! Mai zan gani haka." Sai kuma ta fashe da kuka tana maimaita kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, allahumma ajirni fi musabati wa aklifni khairan minha!" Ganin tana neman fad'uwa yasa Mama saurin rikota tare da zaunar da ita a bakin gadon. Kuka Ummi ta yi sosai, Mama na rarrashinta cikin karfin hali da danne zuciya, bayan ta tsagaita ta dago ta kalli Mama tare da cewa "Hafsatu mai ke damunta haka?" Take Mama ta kwashe komai ta gaya mata ba tare da tare da rage ta da komai ba, itama dai aljanan ta fi baiwa karfi, don ko kusa babu wanda zai kawo wani tunani makamancin soyayya a cikin lamarin. Addu'a Ummi ta sauna ta dinga tofa mata har wuraren bakwai na safe, har zuwa time din bata farka ba, sallama Ummi ta musu a kan zata je gida ta dawo.......... Dan Allah Ku yi hakuri da jina shiru kwana biyu Mamana ce bata ji dadi ba, bana samun zama bare nayi typing dan Allah Ku sakata a addu'a. Ku ci gaba da hakuri da ni littafin Joy yanzu ya fara dadi, Ku dai Ku ci gaba da bibiya. Yan group d'ina *Joy Novel Fans* ina Godiya da addu'o'inku ga Mamana Allah ya amsa, Allah ya sake muku da alkhairi ina matukar Alfahari da ku. Kar a manta da comment and share pls🙏🙏🙏🙏🙏🙏 09116099486. [12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 31* No editing🙏 Ko da Ummi ta shiga gida da Al'ameen ta fara cin karo a tsakar gidan yana wanki, a kid'ime ta fara labarta masa rashin lafiyar Amira, ta k'are da, cewa; Wallahi Amintacce na tsorata da ganin yarinyar nan, hankalina ya tashi, da da k'arar kwana da sai dai na ji mutuwar ta." Ta kai karshen maganar tana matsar kwalla, sosai ya kid'ime da ganin hawaye na kwaranya a idanun ta. Ummi jaruma ce, abin da zai sakata zubar da hawaye haka lallai ya kai abin tausayi, rik'e hannunta ya yi ya kai ta falonta ya zaunar da ita, ya shiga bata baki a kan ta yi hakuri ta yi shiru cuta ba mutuwa ba ne, ta ce "Yayan Fatima dole na koka, kar kaso kaga Amira." Rarrashinta ya ci gaba da yi, har ya samu ta yi shiru, Fatima kam jikinta ne ya yi sanyi tun lokacin da ta ji Ummi na labartawa Yayanta halin da Amira ke ciki, hakan yasa ta lafe a kitchen ta kasa fitowa. Ranar yini Ummi ta yi zirga-zirga tsakanin gidanta da gidan Maman Amira, babu irin tambayar da Ummi bata mata ba a kan damuwarta amma kamar yadda ta saba ta k'i fad'a, da Ummi ta dame ta da tambaya, sai kawai ta fad'a jikinta ta rungumeta ta fashe da kuka, hakan ya k'ara sanyayar ma Ummi da gwiwa kwarai. Fatima ma ta shiga ta duba ta, sai da ta yi kwalla itama. Kamar yadda Al'ameen ya yi alkawarin ranar Monday zai kai Fatima makaranta hakan ko aka yi, ranar ita da aminiyarta sun yi farin ciki kamar babu gobe, dan kar Mom ta sani yasa Joy ta laftawa David kud'i, ai kam ji kake tsit! Mallam ya ci shirya. A bangaren ciwon Al'ameen, babu abin da ya canza, sai ma sake ta6ar6arewa da lamarin ya yi, kusan kullum a cikin damuwa ya ke, sai dai koda wasa bai bari Ummi da Fatima sun fahimta ba , don baya son abin da zai d'aga musu hankali, haka ya ci gaba da shan overdose d'in maganin shi, don a halin yanzu ba shi da wata mafitar data fi wannan, abin da ya fi d'aga hankalinsa a yanzu bai wuce yadda, ciwon ke yawan tayar mishi a kowani irin lokaci ba, babu dare babu rana babu safiya, hakan na nufin ya kai stage 5 kenan a jikinsa, hakan yasa ko ina zai ce maganinsa na tare da shi saboda tsaro. Sau biyu Ummi na kama shi yana kokarin shan maganin, hakan ya firgita shi, sai dai ya yi mamakin yadda bata tambaye shi na menene ba, itakam har ga Allah bata kawo komai a ranta ba don ta yadda da tarbiyar da ta yi ma shi d'ari bisa d'ari. Ana cikin wannan halin Aliyu ya dawo, A ranar ya kira Al'ameen ya sanar mi shi da shigowar shi Niger, kuma a ranar yana ajiye jaka a gidan ya yi wanka ya yi wa gidan su Al'ameen tsinke, don lamarin shi ya tsaya ma shi a rai a kulli yaumin da tunanin shi yake kwana yake tashi. Da yammaci ne misalin karfe biyar da rabi, Aliyu ya iso unguwar Abayi, bai tsaya an yi mai iso ba, ya yi sallama ya shiga don yana son gaisawa da Ummi, babu kowa a tsakar gidan Fatima na islamiyya, Ummi na d'aki. Sake rafka sallama ya yi, daga cikin daki Ummi ta amsa mashi, tare da mikewa ta fito tana cewa; Muryar wa nake ji haka kamar Ali gadanga." Ta karashe maganar tana rike ha6a lokacin data yi arba da shi, risinawa ya yi yana murmushi ya yi ya ce "E Ummi ni ne, Ina wuni." Cike da fara'a ta ce "ina gajiya Aliyu muatanen kano saukar yaushe?." Ba tare da ya mike ba ya amsa da "D'azu Ummi." Ta ce "Masha Allah shine barka zauna ka huta ba ka kamo hanya, to ya ka bari yan cen, fatan an iske mutanen gida lafiya." "Lafiya kalau Ummi duk suna gaishe ki." "To madallah! Ina amsawa, ina yawan samun sak’on gaisuwarka wajen Yayan Fatima, har ya ce zai had’a mu a waya Allah ba nufa ba." Ya ce “Allah sarki! Haka ne dama komai sai Allah ya so” "mik’e Aliyu ga kujera ka zauna, d’aki zafi sun dauke wutar su." Ta karashe maganar tana nuna mashi kujera y’ar tsuguno. Zama ya yi, itama ta d’auko tabarma ta shimfid’a ta zauna tana cewa; ga shi Fatima bata dawo makaranta ba da tsoro maka ruwan sanyi amma nasan tana hanya.” murmushi ya yi ya ce " Ba komai Ummi yanzu ma masha ruwa kafin na shigo." Hira suka shiga yi da Ummi cikin sakin jiki da sabo, da alamar a kwai shakuwa a tsakanin tun ba yanzu na, kusan rabin hirar ta Amira ce, Ummi ke mashi, duk da baisan yarinyar ba ya tausaya mata sosai, ya yi mata addu'a da fatan samun sauk'i. Fatima ce ta yi sallama ta shigo ganin Aliyu yasa ta sakin fara'a ta ce "Laaa! Yaya Aliyu Kaine a gidan namu yau." Murmushi ya saki a ransa yana mamakin girmanta ya ce " Ni ne Zahra, kin dawo ya makaranta?" "Alhmdllh Yaya ya su Umma da su Aziza, da sauran y’an uwa?" "Duk suna gida na baro su k'alau." "Madallah! A gaishe su." "Insha Allah zasu ji." "Maza ki ajiye jaka ki amso mi shi ruwan sanyi." Cewar Ummi bayan sun gama gaisawa da Fatima, jakarta ajiye a d'aki, ta amshi kud’in ta je ta siyo pure water mai sanyi a shago ta kawo, ajiye ma shi ta yi, ta ce "Ummi bari na dubo Anty Amira." "Yawwa Binta maza je ki, ni ma naso shiga da dazu sai ga Aliyu, amma idan na yi isha kafin na kwanta zan dubota nima." A zaure ta ci karo da Al'ameen, "Yayana oyoyoo." Ta fad'a tana amsar ledar hannunsa, godiya ya mata, tare su ka shigo cikin gidan, d'akin ummi ta kai ledar ta ajiye ta fice zuwa gidan su Amira. Cike da d'okin ganin juna, suka yi musabaha, "Timekeeper kanawan dabo, gaskiya kano ta kar6e ka abokina, kaga yadda ka yi wani k'ato." Cewar Al'ameen cikin sigar zaulaya, dariya Aliyu ya yi ya ce "Na gode da zagi, kana ga duk na kanjame sai kashin wuya kamar kai, ka ce wani na yi kato." "Allah ba sharri na ka yi dan gwa6i, me ye sirrin." "Kai dai ka sani ni babu wani gwa6in da na yi, kowa cewa ya ke ba rame na yi katon kai." Haka suka yi ta zaulayar juna, Ummi na yi musu dariya daga bisani suka fito kafar gida suka zauna a dakalin gidan su Amira dake kallon nasu. Jiki a sanyaye Aliyu ya dafa kafadar Al'ameen, juyowa ya yi suka kalli juna cikin ido, damuwa da tsantar so da kulawa Al'ameen ya hango kwance a kwayar idanun Aliyu, "Abokina mekefaruwa, ka rame Ustaz kamar ba kai ba ka taimake ni ka gaya mini halin da ka ke ciki." Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke, ya ce " Ina cikin matsanancin damuwa Aliyu! Damuwar da take neman ruguza mini rayuwa, ta hanani farin ciki da kaanciyar hankali dani da ahlina." Ya karashe maganar a sanyaye, agogon hannunshi ya kalla ganin lokacin sallah ya kusa ya ce , "maganar da yawa bari mu yi sallah tukun na." Kafin Aliyu ya amsa suka ji sallama a kansu, a tare suka mai sallamar jin muryar mace. Kallo d'aya ta ma shi zuciyar ta ya bata cewa shine, tabbas bata ta6a gaskata zantukan Amira ba sai yau da ta yi arba da shi, gaba daya duk wani karsashinta sai ya nemi arcewa ya barta, dakewa ta yi ta karfafa zuciyarta, tuna halin data baro Amira a

Chapter 14 of 22