Share this page
tafasa, murmushi Mom ta yi, ta saki joy ta rungume Eshart tana cewa "Oh! I'm Sorry my dear sister. Na yi kewarta sosai ne shiyasa." Daga haka ta rungume David da shima yake mata sannu da zuwa, hannunta sarke da na Joy suka shiga mota, Joy na kwance a jikinta har su ka iso gida. Duk da izza da dagawa irin na Mom, ma'ikatan gidan sunyi murna da dawowarta, daga yadda suka dinga zuwa kwasar gaisuwa kowanne baki har kunne zaka tabbatar da hakan, ko ba komai zasu rabu da masifar Esther. Ranar Joy na makale jikin Mom din ta, tana lelenta kamar yar five years abinda ta dade rabonta da gani daga Mom din hakan yasa ta saki jikinta sosai ta wuni da farin ciki, koda lokacin barci yayi har daki Mom ta rakata ta tayata shirin barci ta kwantar da ita ta kashe mata wuta sannan ta barta ba yan ta yi kissing forehead din ta tare da shafa kanta. Mom na fitowa daga d'akin Joy ta tarad da Esther tsaye tana Binta da wani irin kallo, hannunta Mom ta kama ta jata su ka bar wajen, d'akinta ta nufa da ita sunan shiga Esther ta fisge hannunta daga na Mom, tare da watsa mata wani lalatatcen kallo, ajiyar zuciya Mom ta sauke a tausashe ta ce "I'm sorry Esther. Ba abinda kike tunani ba ne." Cikin daga murya ta ce "Ta Yaya zan tabbatar da haka ba yan kina aikata sabanin abin da kika sanar min, na gani lokaci yayi da ya kamata ki cika alkawari." "Calm down Esther ki saurare ni." Daga mata hannu ta yi a zafafe ta ce "Bazan saurare ki ba, zan bar gidan nan don bazan zauna bakin ciki ya kashe niba." Daga haka ta tuya ta fice daga dakin fuuu! A fusace. Dabass Mom ta zauna tare da rafka tagumi. Washegari da duku duku safiya Anty Esther ta fito da jakar kayanta ta bar gidan. ********** *Al'ameen* Kwata kwata babu sauki a cikin lamuran sai ma kara tabarbarewa da abubuwa ke yi I zuwa yanzu tab! biyar yake sha kafin ya samu relief........ Ga mai bukatar shiga group. 09116099486. [12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 23* *AL'AMEEN* Kwata-kwata babu sauk'i a cikin lamuransa, sai ma kara ta6ar6arewa da abubuwa ke yi i zuwa yanzu tables biyar yake sha kafin ya samu relief, yana cikin matsanancin damuwa, tuni ya fara rama a tsaye. Ba Ummi ba hatta fatima sai da ta fahimci Yayanta na cikin damuwa, don gaba d'aya ya sauya mata, ko magana yanzu bai cika yi ba, haka firan dare, da ya dawo zai shiga d'aki ya kulle ya kwanta da safe ya fito da idanu jajur kamar gauta a kumbure idan ta tambaye shi ya ce babu komai, tuni duniyar ya fara mata zafi, take kewar aminiyarta ya dawo mata sabo fil dama shi ke dauke mata hankali akanta ba wai don ta manta da ita ba. Ummi kam damuwar da ta shiga ba'a magana, matsayinta na uwa lamarin ya shigeta matuk'a gaya, tsoranta Allah kar ace shaye shayen nan na zamani Al'ameen d'in ta ya fara, a duk sanda ta yi wannan tunanin, takan shiga kololuwar ta shin hankali, har ta zubar da hawaye, ta zauna da shi ba sau daya ba ba sau biyu ba cikin lalama da dabara ta naimi jin damuwarsa, amma ya ki fad'a mata, sai dai ya girgiza kai ya ce mata "Babu komai Ummi, kawai gajiyan aiki da karatu ne, sai mura da ta saka ni gaba a yan kwanakin nan ki taya ni da addu'a." Ba dan ta yarda ba, dole take hakura, ta san tunda ya nace a haka bazai fada mata ba ne, ta fi kowa sanin halin zurfin cikin shi tun yana dan kankanin yaro. Da misalin karfe takwas na dare ya shigo gida kamar yadda ya saba, sunan zaune jigum jigum a tsakar gida, duk yadda Ummi take da son sauraren redi'o yau rediyon nata a kashe yake carbi ne rike a hannunta tana ja, Fatima kam notebook din ta ne a gabanta data dauko zata yi karatu amma ta kasa, ta ajiye ta rafka tagumi. Kallo daya Ummi ta mishi ta kauda kai gefe, sai ga hawaye shaaa! Duk yadda taso ta kauce kar ya gani abin ya ci turo. Da sauri ya kara sa shigowa, zubewa yayi a gabanta hankali tashe, ya ce "Subhanallah! Ummi." Daga mai hannu ta yi ta ce "Karka kira sunana Al'ameen ni ba Umminka ba ce, ka tashi a gabana." Ta karashe maganar tare da fashewa da kuka mai karfi, Fatima da maganar Ummi ya dawo da ita hayyacinta, rarrafowa tayi ta fada jikin Ummi ta fashe da kuka itama, cikin kuka ta ke cewa "ki yi hakuri Ummi, ki yi hakuri ki yi shiru." Rungumeta Ummi ta yi su ka ci gaba da rera kukan a tare. Kololuwar tashin hankali Al'ameen ya shige shi, zuciyar sa tuni ta shiga wani irin tsalle kamar zata faso kirgi ta fito, rasa abin yi yasa shi fara zubar da zazzafar hawaye da , sai kawai ya rungume su gaba daya, cikin zubar hawaye da kunar rai ya ce "Ki yi hakuri mahaifiyata ki dena zubar da hawayenki a kaina, na tuba nabi Allah na bi ki." Kalmomin da ya dinga maimaitawa ke nan kamar karatu. Sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin Ummi ta tattare d'an jarumtarta ta danne zuciyarta, ta zame su daga jikinta ta dago ta kalle shi cikin ido ta ce "Al'ameen shaye shaye ka fara?"da wani irin sauri ya kalle ta yana girgiza kai, ta ce "Karya ka ke yi, idan ba haka ba kuma ka sanar dani damuwar ka, don na tabbata a kwai abin da ke damunki ji yadda ka koma gaba daya ka lalace cikin yan watanni, bazan jura ganin ka haka ba Aminullah." Shiru ya yi yana kallonta bazai iya yi mata karya ba, kuma bazai iya fitowa kai tsaye ya sanar da ita damuwar shi ba, duk da yasan bashi da kamar ta duk duniya, yana matukar jin nauyinta, kasa ya yi da kai ya ce "Ki yi hakuri Ummi, bazan iya yi miki karya ba, kuma bazan iya sanar miki damuwata ba, amma wallahi tallahi bana shaye shaye, ki taya ni da uddu'a Ummina." Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke ko babu komai ta samu saukin kaso ashirin cikin damuwarta kashi dari. Sai dai ko da wasa bata nuna a fuska ba, mikewa ta yi ba tare da ta kalli gefen da yake ba ta shige daki. Fatima ma mikewa ta yi zata bi bayanta, har lokacin kuka take yi, da wani irin raunatacciyar murya wanda basu san shi da shi ba ya kira sunan ta "Fatima." Dakatawa ta yi da tafiyar ta juyo tana kallon shi tana shesheka, girgiza mata kai ya yi tare da cewa "Shiiiiii!" Alamar ta yi shiru, sai kuma ya yi mata alamar ta zo da hannu, da sauri ta karasa gareshi ta fada jikin shi, ta sake fashewa da kukan da dama ba wai ta dai na ba ne. Rumgumeta ya yi, wani irin rauni na kara kaiwa zuciyarsa farmaki. A yau ya kara tabbatarwa, shine cikin farin cikin yar uwarsa tilo, da kuma mahaifiyarsa wacce itace komai na shi a rayuwa. Muryarta ne ya katse masa tunani, cikin shesheka take cewa "Yayana ka canza, yayana ka dawo kamar yadda ka ke da don Allah, da ni da Ummi muna cikin damuwa kai ne haske ka jagoran rayuwar mu." Bubbuga bayanta ya shiga yi, ba tare da ya iya bude baki ya amsa mata ba, sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin ya samu ta yi shiru, sai ajiyar zuciya da take saukewa jefi jefi. Dagota ya yi daga jikinsa ya shiga share mata hawaye, yana yi yana cewa "Kar ki sake yin kuka My luv na miki alkawarin zan dawo muku da farin cikin ku ke da Ummi. Al'ameen din Ku zai dawo Yaya Ameen din ki zai dawo kin ji ko." Ta gyada kai ya ce oya wuce kije ki kwanta, Babu musu ta wuce shi jiki a sanyaye, sai da yaga shigewarta daki sannan ya kwashe tabarman ya jingine, kamar mara laka haka ya nufi dakinsa. Ranar damuwa biyu ne ya hade masa, ga na azababbiyar ciwonsa gana tunanin halin da ahlinsa suka shiga a dalilin sa, bazai iya jurar ganin su cikin wannan yanayin ba, bazai iya jurar zafin zubar hawayen uwa ba, ya san wata kila Ummi ta na fushi da shi, dole ya tsayar da mafitar da yake ganin ita ce dai-dai. Ranar yadda yaga rana haka yaga dare. Da safe kamar yadda ya saba gudanar da komai haka ya gudanar, hankalinsa ya kara tashi lokacin da ya hada idanu da Ummi, bai taba ganinta cikin irin wannan kamar ba, gaba daya idanunta sun kumbura sun yi jajur, sai dai bata nuna masa wani sauyi a fuska ba, ya san ta kwana cikin damuwa, abin da ya fi daga mai hankali ganinta da ya yi kwance a dai-dai lokacin da kullum yake samunta zaune ta na lazumi tabbas! Bata da lafiya, kuma yasan shine sila, shikam ina zai kai girman sannan zunubin uwa tafi gaban wasa,zai iya sadaukar da komai domin ganin farin ciki ta, a koda ya tambayeta ko bata da lafiya ne, cewa ta yi kalau ta ke. Ko breakfast bai iya tsayawa yi ba, ya shirya afujajan ya nufi asibitin Dr Abdul Hafiz S Alto don a nan ne kadai yake ganin zai samu total solution. Lokacin da ya isa Dr bai iso ba, zama yayi a waiting area shi da sauran patient din da ke nan. Sun dauki almost gud 2 hours kafin Dr Abdul ya iso, tun daga nesa ya hango Al'ameen, boyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tuna wayar da su ka yi da Aboki, shekaran jiya. Sama sama ya amsa gaisuwar ma'aikata ya shiga office ya fara duba patient dinsa, gefe guda kuma zuciyarsa cike da fargabar da me yaron ke tafe fatansa Allah yasa ya zabi cancanta kar ya zabi son zuciya. Mutum bakwai ya gani kafin layi ya iso kan Al'ameen, tun da ya turo kofar office din Dr Abdul ya dago yana kallon shi, shima jemammun idanu shi na kan Dr din. Guri ya samu ya zauna a inda aka tanada don zama, da wani iron cool voice ya ce "Dr na dawo gareka ka taimaka ka yi mini wannan alluran da ka ce shine zabina." Rasss! Rasss! Haka gaban Dr Abdul ya yanke ya fadi, ya san za'a rina dama. Shiru ya yi yana kallon Al'ameen din ba tare da ya amsa shi ba, gajiya da zaman shirun ya saka Al'ameen sake cewa "Don Allah Dr ka taimakeni ina cikin matsanancin damuwa." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Wacce irin damuwa ce sannan data saka ka kake shirin kashe rayukar a tsaye." Ya ce "Duk abinda kaga ya koro bera daga rami har ya fada wuta to hakika yafi wutar zafi, ni dai don Allah ka taimake ni." "Ta yaya zan maka injection irin wannan mai hatsari alhalin ban san matakin ciwonka ba, kar ka boye min komai ka gaya min gaskiya mekefaruwa?" Tuni idanun Al'ameen suka kara kadawa, a raunace ya shiga labartawa Dr halin da yake ciki, ba tare da rage komai ba kamar yadda Dr ya roka. Tun kan ya kai kar she tuni Hankalin Dr ya ta shi, ranshi yayi mugun baci, bai taba sanin akwai mutane kidahumai ba a duniya sai yau. Cike da wani irin bacin rai ya katse shi ta hanyar jiran sunan shi a tsawace "Muhammad!!!! "........ 09116099486. [12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 24* Cike da wani irin bacin rai Dr ya katse shi ta hanyar kiran sunan shi a tsawace "Muhammad!!! Baka da hankali ashe, five tablets fa ka ce." Komawa ya yi zauna da6ass "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Ya furta tare da dafe forehead. Ganin yadda hankalin Dr Abdul ya ta shi yasa Al'ameen yin k'asa da kai, cikin sanyin murya ya ce "I ha6 no choice, dat is y" Dagowa Dr ya yi idanun shi har sun kad'a ya ce "Ni ka ke gayawa baka da za6i, shin! haka mu ka yi da kai?" Ya girgiza kai. "Then y ka yi hakan, kasan me ka aikata kuwa, hakan fa dai-dai yake da kashe kai." "I'm sorry Dr." D'aga ma shi hannu Dr ya yi , ya ce "Ka rike hakurin ka, ka tashi ka fice min daga office bana bukatar ganin ka, don babu abin da zan iya yi maka a halin yanzu." Jin haka yasa hankalinsa kara ta shi tuno yadda ya baro Ummi a kwance cikin ciwo ya yi, ya sake tuna irin damuwar da tilon kanwarsa ke ciki duk akan wannan matsalar, sannan ya zo in da yake ganin zai samu maslaha amma yana ji yana gani ana neman yi masa sakiyar da babu ruwa. A raunace ya ce "Dan girman Allah Dr ka tausayin min ka dubi maraicina, ka yi mini wannan alluran, na amince da duk abin da zai biyo baya." Kallon zautacce wanda bai san ciwon kan shi ba Dr ke mishi i zuwa yanzu, hakan yasa ya baiwar iska ajiyar shi ya ci gaba da duba tarin files din dake gabansa. Magiya da ro'ko Al'ameen ya shiga yiwa Dr amma yayi kamar bai san da zaman mutum a wajen ba, don ran shi a matukar 6ace yake danne zuciyarsa kawai ya yi don tunzira shi ta ce akan ya ta shi ya dinga sharara ma shi mari, amma yaga alamar yaron na neman kai shi bango. Magiyar duniya Al'ameen yayi wa Dr amma bai kalle shi ba, har k'asa ya duka ya riko kafafusa yana rokonsa, amma kamar da dutse yake, tuni zuciyarsa ta fara tunzira. Mik'ewa ya yi a fusace cikin tafasar zuciya da matsanancin bacin rai ya ce "Kar ka yi min mana so what!" Kalmar da ta doke kunnen Dr da ya sa ka shi dagowa da sauri a kalle shi. Cikin tsawa da rufewar idanu ya ci gaba da cewa "Wacce irin zuciya ce a kirjinka Dr? Shin baka da imani da tausayi ne baka san Allah da ma'aiki ba? To shike nan ka je ka rike taimakon na ka, gari da yawa maye baya ta6a cin kansa! Idan baka taimaka mini ba akwai dubban irin ka da zasu iya taimaka mini, duk duniya babu wanda na yarda ya san sirrina ciki da waje sai kai, na gaya maka abin da ke faruwa ban 6oye maka komai ba, na ce maka na amince da duk abin da zai biyo baya ba shike nan ba, ina ruwanka jikin ka ko jikina rayuwar ka ko nawa? So kake na fifita wani jin dad'i na rayuwana akan farin cikin mahaifiyata, to ka sani UK duniya babu wanda ya isa, bani da kamar ta itace komai nawa, kuma zan iya yin komai dan ganin farin cikin ta, dukan table ya yi da karfi har sai da wasu takardun dake kai su ka watse ya ce " Ni muhammadul-Ameen Idan na haifu dan halak na maka alkawarin baza ka sake ganin kafata a cikin asibitinkada zumar naiman taikamo a wajen ka ba." Daga haka ya juya a fice daga office din tare da buga koda da mugun karfi. Tun da Dr ya kafe shi da ido bai sauke ba har ya fice daga office din. Ya fi minti goma a haka, kafin ya sauke zazzafar huci, fuskar yaron yake sake kallo a idanunsa maganganun yaron ne ke sake repeating kan su a cikin kunnuwansa, "Ya Rabbi! Kaga niyyata ka dafa mini." Ya furta a bayyane wayar shi ya dauka ya yi dialing lambar Hayatuttdeen, kamar yadda ya tsammata kiran bai tafi ba, kife wayar ya yi akan table, shima ya kife kanshi tare da lumshe idanu..... *********** Da wani irin fushi hadi da bacin rai ya fito daga asibitin, jefa kafa yake yi duk in da ya samu, idanun shi a rufe, ikon Allah ne kawai ke rike da shi, bai san ina yake nufa ba, don zuciyarsa ce kawai ke jagorantarsa kwkwalwarsa kam ta dau zafi a lokacin da bazata iya tantance komai ba. Wani irin mugun horn ne hadi da taka burki suka ziyarceshi lokace daya, sai dai kafin ya yi aune tuni motar ta ture shi, duk da ba wani mugun turi bane don direban yayi iya kokarinsa wajen kaucewa hatsarin, sai da ya fadi kasa. Gigitacciyar kara ta saki a matukar razane. ba ta san yadda a ka yi ba, ta shiga komar tunanin shi kamar yadda ya zame mata ibada, kawai ta ji direbanta ya taka birki, a firgice ta dogo kafin tayi aune kamar kiftwar idanu taga motarta ya ture shi. Ita da direbanta rige rigen fita a mota suka shiga yi, kusan a tare suka isa inda yake, bata tabbatar shi din ba ne, don duk a tuninta gizon da ya saba mata ne, sai da ta fito daga mortar ta ganshi ra'ayil aini. Cikin rawar jiki Peter ya isa gare shi don ya taimaka mi shi ya mike, abin mamaki da daure kai dakatar sa shi yayi ta hanyar daga mishi hannu cikin karfin hali da jarumta ya dafa kasan titi ya mike tsaye, bai ji mugun rauni ba sai dan kujewa, sai dai ga dukkan alama ya bugu a kafafun shi ganin yadda tsayuwa ta so gagararsa da fari, amma yayi ta maza ya cije lips ya tsaya cak. Tuni ta fashe da wani irin kuka tare da karasawa garesa, a gabansa ta tsaya cikin kuka take cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba daya ta rude bata cikin hayyacinta...... Ku yi manage pls. Masu comment nagode kwarai ina alfahari daku, jiya kun faranta min sosai dana bude data naga ruwan comment na shigowa group di na pls Ku ci gaba hakan shine karfin gwiwata ina sonku sosai masoya mabiya. [12/29, 2:41 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 25* Fashewa ta yi da wani irin kuka, da gudu ta k'arasa gare shi, a gaban shi ta tsaya cikin kuka da kid'ima ta ke cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba d'aya ta rud'e bata cikin hayyacinta. Duk da yana cikin halin ciwo, sai da ya ji Yarrrr!!! A jikinsa lokacin da hannunta ya sauka a kan nasa, da sauri ya saka hannusa d'ayan ya 6an6are hannunta daga nasa. Jin haka yasa ta dago da jikakkun idanuta ta sauke a fuskar shi, karaf! Suka su ka sauka cikin na shi kaifaffun idanun da suke rine, tuni zuciyarta ta shiga wani irin dokawa da wani irin speed,wasu irin sinadarai masu kama da surkulle ke fitowa daga idanun shi suna shiga na ta direct ba tare da wani shamaki ba, kasa janye idanu ta yi daga cikin na shi, duk da irin kaifin da suka mata. Kayataccen murmushinsa ya sakar mata, ya girgiza mata kai, murya kasa-kasa ya ce "I'm ok' ba sai kin kai ni hospital ba thank yhu for Ur care." Daga haka ya juya ya ci gaba tafiya yana d'ingisa kafarsa ta hagu. Kamar a sume kuma ba a sume ba, haka ta dinga jin kanta, bata farga da ya bar wajen ba sai da ta tsinkayi muryar Peter yana cewa "Miss ar u ok." Firgigit ta yi ta kalle shi, ta sake kallon hanyar da al'ameen ya bi, ji ta yi wani kuka mai karfi ya taho mata from no where, da gudu ta wuce shi ta bude motarta ta fada tare sa fashewa da kuka. Jiki a matukar sanyaye Peter ya bude motar ya shiga mazauninsa, ya tada motar suka bar wajen, zuciyarsa cike da tausayin uwar dakinsa. ************* Karfin hali da jarumta ce kawai da kuma taimakon Allah suka karasa da shi gida, zuwa lokacin tuni kafar ta kumbura, baya son ya tadawa su Ummi hankali hakan yasa bai nufi cikin gida ba ya tsaya dakin shi. Karar taba kofar dakin ne ya jawo hankalin Fatima dake tsakar gida, da sauri ta leko don ganin ko waye tunda dai ta riga ta san yayanta ya fita, kuma muddin ya dawo sai ya shigo cikin gida kafin ya nufi dakinshi, sai dai ga mamakinta shi din ta gani tsaye idanun shi a rintse ya cike lips yana kici kicin soka key a jikin padlock. "Yayana." Ta furta tana karasawa gaban shi, sai lokacin idanunta suka kai ga kujewar dake gefen fuskar shi da gwiwar hannun shi da ke zubar jini, zaro idanu ta yi a rude ta ce "Subhanallahi! Yaya me ya sameka?" Kafin ya bata amsa ta hango kumburan da kafar shi ta hagu ta yi, "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na shiga uku!" Da sauri ya bude rinannun idanunsa jin zata yi masa kwarmato, cikin karfin hali ya yi mata alamar shiii! Da hannu, girgiza mishi kai ta yi tana hawaye sai kuma ta juya ta runtuma da gudu, "Ya Salam!" Ya furta akan labbanasa, ya fahimci gaba daya ta rude ne kuma yasan Ummi zata je ta gayawa, sam baiso ba sanin da ya yi Ummi bata jin dadi yau. Allah sarki uwa! A kwance take amma jin abin da Fatima ke fada tuni ta mike zaune, kafin Fatima ta kai aya, ta mike kan kafafunta, ta yo gaba, Fatima ta rufo mata baya. "Subhanallahi! Yayan Fatima me ya faru haka, innalillahi wa inna ilaihi rajiun!" Ta fada cikin tashin hankali ganin yadda kafar shi ta kumbura, "Fatima amshi makullin ki bude kofar." Fatima dake sharar kwalla ta amsa key a hannun Al'ameen ta bude kofar, dakyar ya iya daga kafa ya shiga ciki, Ummi da Fatima suka rufa masa baya, kwanciya yayi, don bazai iya zama ba, Ummi ta sake cewa "Ko dai asibiti zamu je Al'ameen?" Dakyar ya girgiza mata kai yana cike lips Cike da azaba, sannu suka shiga rige-rigen yi masa. Sake kallon kafar Ummi ta yi dakyau ta ce "Wannan kafar taka akwai targade, Yayan Fatima. Binta yi maza ki je gidan Mallam Surajo mai dori ko yana nan" Da gudu Fatima ta fice, Ummi kuma ta zauna tana yi masa sannu, daurewa kawai ta ke yi kar ta zubar da hawaye. Minti sha biyar Fatima ta yi sallama, Mallam Surajo biye da ita, fitowa Ummi ta yi a dakin suka gaisa sama-sama ta ce "Mallam yaro ne ya shigo yanzu da kafa a kumbure, shine nace ta kira ka ka duba ina ganin kamar targade ne." Ya ce "Assshha! To bari a duba, Allah kiyaye gaba." Daga haka ya shiga dakin Al'ameen din. Kamar yadda Ummi ta yi hasashe targaden ne kuwa. Babu bata lokaci Mallam Surajo ya hau aikinsa, duk da cewa kafar bata yi mugum tsami ba, Al'ameen yaji jiki, rintse idanu kawai yayi yana ambaton sunaye Allah. Ummi kasa tsahuwa ta yi a baki kofar jin hawaye na shirin zubo mata da sauri tayi cikin gida, Fatima kam kuka take wiwi ta aza hannu aka. Bayan wasu mintuna Mallam Surajo ya kammala aikinsa, fitowa yayi ya tarad da Fatima, ya ce "Yan mata ki gayawa innarku an gama." Ta amsa da to , ta shiga ciki, tare suka dawo da Ummi.

Chapter 11 of 22