Share this page
yana numfashi, a komai nata yana tsaye da kafafun shi, ita macece mai raunice abar tausayi da riritawa. Dakyar ya bude baki ya ce mata ya "ya isa haka Fatima na hakura share hawayenki." Hijabin jikinta tasa ta share fuskarta da shi, gaban shi ya nuna mata yace "ajiye kayan a nan." Babu musu ta ajiye, numfashi ya sauke kafin a tausaahe ya shiga yi mata nasiha akan kula da mutuncinta matsayinta na diya mace, sosai ta nutsu tana sauraren shi sai da ya dauke lokaci mai tsawo kafin ya dasa aya. Godiya tayi kafin ta mike ta je kitchen ta dauko mai tuwon shi har zuwa lokacin Ummi na tsakar gidan tana sauraren shirin tsalle daya a radio. Ajiye tuwon tayi a gaban shi tare da ledar yalon da ke damke a hannunta tun dazu, murmushi yayi ganin yalo, ya dago ya kalleta itama sai ta sakar mai murmushi, ya ce "Nagode yar gidan Yaya Ameen" dariya ta saka cike da jin dadin yabawan da yayi da kyautarta, wani dadi yaji ganinta cikin farin ciki sai ya tsinci kanshi da yiwa marigayin mahaifinsu addua wanda har yau ko a hoto Ummi bata taba nuna musu shi ko wani nashi ba, kawai abinda suka sani ya rasu da dadewa. "Yaya sai da safe." Muryarta ya katsemai tunani, ya ce "har zaki tafi baza ki zauna muyi hira ba, ko barci kike ji da wuri haka?" Ta girgiza kai, ya ce "kinci naki tuwon ne ko?" Ta ce "A'a yanzu idan na shiga zanci." "Wanko hannu kizo muci tare." Ta amsa da "to Yaya" tare da shiga cikin gidan danta wanko hannu kamar yadda ya umarceta. Cike da nishadi suka ci tuwonsu cikin kwarya daya suna wasa da dariya, a karshe ya saka katon loma, kukan shagwaba ta saka tana dire kafa, cinyewa yayi ya kara kai hannu da sauri ta dauke kwanan ta cinye guntun daya bar mata, tana tura baki, yana mata dariya da gwalo kamar bashi ne dazu ya rufeta da fada ba, bayan ta kwashe kwanukan wanko hannu tayi ta dawo, nan shiga bata labaran ban dariya yana cin yalo yana yabawa ita kuma dadi kamar ya kasheta, daga karshe ya saurari haddarta. Ummi na tsakar gida tana saurarensu, tsakanin Al'ameen da Fatima sai Allah,ko ita data haifesu bata ce ga tsakanin subab, a haka bata san sanda ta fara gyengyadi ba. Ba su suka ta shi ba sai gurin goma da rabi, shima ganin tana ta hamma yasa ya ce taje ta kwanta, koda ta shigo gida ta samu Ummi tayi barci radio a kunne tashin ta ta yi, suka wuce daki bayan sunyi alwalan kwanciya. Washegarikamar kullum ta gudanar da aiyukanta na safe tayi shirin makaranta, tana ta zuba idon ganin Joy sai dai shiru shiru har ta gama ta fito gida ta kama hanya, yana ta tunanin ko zasu hadu a hanyar amma shiru har ta isa bakin get, bata kara shiga damuwa ba sai da ta isa class ta tarad babu joy babu me kama da ita, haka ta zauna jiki a sanyaye tana tunanin mekefaruwa ne yau, iya Sanin ta Joy bata fashin makaranta, can sa'insar daya shiga tsakanin joy da David ya fado mata, take gaban ta ya yanke ya fadi rassss.......... Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lamabar 09116099486 [12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 7* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* Ranar haka Fatima ta wuni a school babu walwala, sboda rashin zuwan Joy, gaba ɗaya jin school ɗin take yi babu daɗi a haka har suka yi closing, jiki a sanyaye ta kamo hanyar gida cike da tunanin abin da ya hana joy zuwa school, fatan ta Allah yasa dai lafiya. A kulle ta iske gida alamar babu kowa, sai lokacin ta tuna Ummi ta ce mata zata dan fita idan ta dawo ta karɓi key a maƙota. Gidan da ke kallon gidan su ta shiga, shima dai kamar nasun ne, na y'ay'an mallam shehu, sai dai yafi nasu girma da yalwar ɗakuna, sallama ta yi a ƙofar ɗakin Maman Amira kamar yadda suke kiran matar gidan, Amira ce ta fito daga ɗakin tana amsa sallamar, ganin Fatima yasa ta fad'ad'a fara'ar fuskarta, budurwace yar kimanin shekara goma sha bakwai, sanye da wandon uniform dinta na girls day, ta cire rigar ta bar farin singlet da alamar itama dawowarta kenan. Murmushi Fatima ta sakar mata tare da cewa "Yaya Amira ina wuni." Cikin sakin fuska ta amsa da "Ina gajiya Fatima kin dawo ya school." Fatima ta ce "Alhmdllh." "Shigo mana tana ciki." Amira ta faɗa tana kauce mata a hanya, "A'a dama Ummi ce idan na dawo na karbi key gurin Mama." "Ok bari na karbo miki." Ta koma ciki ba jimawa ta fito da key din ta mikawa Fatima, amsa tayi ta fice, bayan tayi godiya, da kallo Amira ta bi ta fuskarta dauke da murmushi a fili ta ce "kamar su daya sak! komai nasu iri daya hatta murmushin, ya Allah ka mallakamin Yaya Ameen kasa ya zama majibancin rayuwata, jin Mama kwala mata kira yasa ta amsa tare da komawa dakin da sauri. Ta tarar da gidan tsab kamar kullum, dakinsu ta bud'e ta shiga ta canza kayan jikinta, ganin Ummi bata nan yasa bata tsaya watsa ruwa ba, don idan tana nan bata yarda ta ci abinci sai ta watsa ruwa tayi sallah. Kitchen ta bude ta dauko Kular abincinta, shinkafa ce garau garau da yaji, a nan tsakar gida ta zauna ta ci abincin, tana gama ci ta mike ta kai kular kitchen, tana fitowa Al'ameen na shigowa bakin shi dauke da sallama, amsa mishi tayi tana mishi sannu da zuwa, murmushi ya sakar mata yana amsawa. Idanunshi duk sun zurma kafafunta shi futufutu, takardun hannun shi ya ajiye kan windon d'akin Ummi, ya ja kujerar ummi yar tsuguno ya zauna yana ce wa "Fatima bani ruwa a buta." Da sauri ta dauki buta ta kai mishi bayan ta zuba ruwa, kafafunshi ya shiga wankewa, Fatima dake tsaye daga gefe ta ce "Yaya tracking kayi ne?" Ya ce "Eh kuma A'a kusan dai haka." Ya karashe maganar yana miƙewa don ya riga ya gama dauraye kafar nashi. Kofar dakin Ummi ya nufa, ganin haka yasa Fatima ta ce "Bata nan Yaya." Juyowa yayi ya kalleta a mamakance ya ce "Bata nan, ina taje?" "Wlh ban sani ba ta dai ce min zata dan fita da safe kafin na tafi school." Gyada ka yayi bai, kara cewa komai ba ya nufi dakin shi, Fatima kuma ta nufi kitchen ta dauki abincin shi tabi bayan shi da shi. Abincin ya ci ya koshi, bayan ya gama yasha ruwan sama, kishingid'a yayi a katifar shi ya lumshe idanu, da ace shi wani dan gata ne da kwanciya zaiyi ya huce gajiyar daya kwaso na tafiya, amma yasan haka ba Abu ne mai yuwuwa ba, idan ya kwanta wa zai basu su ci,wa zai kula da mahaifiyar shi da kanwar shi, wa zai dauki dawainiyar rayuwar su, wa zai biya musu bukatunsu na yau da kullum???, "Babu." Ya ba kan shi amsa a bayyane, shine gatan su da shi suka dogora da Allah suka dogora, tunanin yadda yasha gwgwarmayar zuwa da dawowa school yau ya shiga yi, zai Iya cewa daga zuwan har dawowar kusan da kafa yayi saboda halin babu, duk abin da ya roro ba ta kan shi yake yi ba, ta Ummi da Fatima yake yi, sune a gaban shi, da wannan tunanin ya yunkura ya mike ya canja kayan jikin shi ya fice daga dakin. Cikin gidan ya shiga ya ma Fatima sallama sannan ya fice, daga gidan, direct unguwar Sayako ya nufa gidan Alhaji bala baka shot, in da yake zuwa daukar keke napep, ya na fatan Allah yasa akwai keken a kasa, cikin sa'a ya samu har biyu a kasa, take aka bashi wani form yayi singing, singing din da kulli yaumin idan zai yi sai gaban shi ya fadi ya rasa dalili, amma haka yake daurewa domin bashi da wata hanyar da zai samu kudi a saukeke sai wannan, yana dan tana sana'ar hannu, amma aikin nashi ne ba ko wani lokaci yake samu ba, haka ya dauki keke daya ya kama aiki da bismillah. Tafiyar Al'ameen babu dadewa Ummi ta dawo,dauke da buhun bakko, Fatima ta tare ta ta amsar mata kayan, tana mata sannu da dawowa "yawwa Fatima sannu da gida," ta karashe maganar tana zama a kan kujera, " matso da bakkon nan Fatima mu gani." Matso mata da shi gabanta tayi, kwancewa tayi ta shiga fito da kullin ledodi a kasa buhun kuma ta fito da doya manya guda uku, kallon Fatima da tayi kasake tana kallonta tayi ta ce "kwashe wannan ki kai mana kitchen wannan kuma ta fada tana nuna mata ledodin gabanta ki bud'e robar da muke ajiye kayan abinci ki sassakasu ciki shinkaface da wake, Fatima da mamakin Ummi ya gama kasheta tace "Ummi kasuwa kika je? Ita kanta bata san sanda tambayar ya subuto mata ba ganin dai tunda suke Ummi bata tana zuwa kasuwa ba komai yayanta ke kawowa, komai za'a siya shi yake siyowa dagowa Ummi tayi ta kalleta kafin ta ce "ba kasuwa naje ba." "To ina kike je waya baki wadan nan kayan abincin?" Ta fada a zuciyarta a zahiri kuma ta ce "Oh ai na dauka can kika je na ganki da kayan abinci." Ummi bata amsata ba, sai ci gaba da kokarin kwance ledan shambo da tarugu da take yi ta juye a kwando. Cefane Ummi ta dawo da shi ba na wasa ba , harda su mai da maggi da busasshen kifi, sai da suka gama Adanawa tsab ta kalli Fatima ta ce "ba na son yayanki yayanki ya san da maganar kayan abinci nan ko da wasa." "To Ummi amm....." "Kinji abunda na fada ko baki ji ba." Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "naji Ummi insha Allah bazai ji ba." Murmushi Ummi tayi ta ce "yawwa fateetee ngd,." Fateeteen data fada yasa Joy ta fado mata a rai, cike da dan damuwa ta ce "Ummi yau joy bata zo school." Ummi ta ce "Allah sarki kila ta samu wani uzurine yau din." Fatima ta ce "ummi Joy fa bata fashin makaranta, ni dai ina ji a jikina kamar bata lafiya, tun dazu da na tuno ta gaba na ke faduwa." Ummi ta ce "Assha! To kiyi ta addua, koma menene Allah ya takaita." "Amin Ummi" Fatima ta amsa yana mikewa zuwa kitchen dan ta hada wutar sanwar dare. Karfe Tara dai dai Al'ameen ya maida keke nape gidan Alhaji bala baka shot, kamar yadda yayi singing sanda zai dauka haka yayi singing da ya mayar bayan alhajin da kan shi ya duba lafiyar keken, yaga babu wata matsala, 3k Al'ameen ya bashi cikin cinikin dubu hudu da dari biyu da yayi, amsa yayi yana washe baki sabanin da da fuskarshi yake murtuk yana jiran yaji da wannne ya dawo dan yanzu kafin shi mutum biyu da suka dawo da kekuna har yanzu gasu nan ana kes, daya ya samu accident gefen keken ya lotsa dayan kuma dubu biyu yakawo sabanin dubu uku da yake a ka'ida idan mutum yayi fitar rana zuwa taran dare zai kawo. Sallama yayi musu ya tafi bayan yabar alhaji bala na ta bala'i a biya shi ko ya hada su da polie don shi akan kudi babu sani babu sabo ne. Sai gurin goma saura ya iso gida, a tsakar gida tarad da su, Fatima ta tare shi tare da karbar ledan biredin daya siya musu a hanya. Ummi ya tsuguna ya gaisar kamar yadda ya saba kullum, ta amsa mishi tana "Alhmdllh yayan Fatima jiki yayi warware dama tunda na dawo Fatima ta ce ka fita aiki nace to jiki ya yi dauki kenan." Murmushi yayi ya ce "eh ummi wlh jiki Alhmdllh." Nan ya zauna Fatima takawo mishi abincin ya ci suna ta hira, gefe daya kuma iska na kadawa hadari na haduwu, Sai gurin sha daya saura Ummi ta ce su ta shi haka gobe da makaranta, dari takwas din daya rage mai a aljihu ya kwaso duka ya mikawa Ummi, ya ce "Ummi ga wannan ki rike a hannunki a sai wani abin." Kallon shi tayi tana murmushi ta ce "A'a Amintacce ka bar shi kaima ka rike a hannunka kayi hidimar makaranta ni akwai kudi a hannuna kuma a kwai abincin da zamu ci gobe ka fini bukatarsu, Allah yayi albarka." Tana gama fadin haka ta mike ta shiga daki ta turo kofarta don karma ya tsareta da magiya, Iska da hadarin daya taso gada gadan ne yasa shi sauri ta shi yayi hanyar dakin shi, gaban shi na dokawa wanda shi kadai yasan dalilin haka. Kamar jira ake yi su ta shi a tsakar gidan, take ruwa ya kece da wani irin karfi mai ban mamaki, kudundunewa yayi cikin bargo bayan ya lafta kaya masu nauyi a jikin shi, kwance yake kawai yana jiran tsammani, amma zuciyar shi cike take fall da tsoro, fatan shi daya kar ciwon shi ya tashi, shiru yayi a kwance yana sauraren sautin ruwa da haka barci barawo ya kwashe shi ba tare da sanin shi kasancewar dama a matukar gajiye yake. Kusan raba dare akayi ana tsuga ruwa, can cikin barcin shi ya fara jin sauyi a jikin shi, ji yayi wani irin sanyi na ratsa kasusuwan jikin shi, babu abin da yake bukata a lokacin sai dumi, duk da kasancewar a cikin bargo yake a kudundune, dumi yake bukata ba irin dumin bargo ba, sannu a hankali tsigar jikin shi ya fara tashi, kafin daga bisani wani irin feeling ya lullubeshi, rasa Inda zai saka kanshi yasa ya cusa duka hannayenshi cikin wandon shi, ya matse abin shi dake ta mishi wani irin honkoro, yana ambaton innalillahi wainnailai rajiun a zuciya, magani yake son sha , amma har yanzu abin bai kai matakin da Dr ya ce idan ya kai ya hadiyi maganin ba, kuma baya fata ya kai stage din, sai dai fatan shi bata karbu ba, dan cikin abinda baifi minti biyu ba maran shi tayi wani irin kullewan da yasa babu shiri ya yaye bargon ya mike ya nufi jakar nan, ya zaro sachet din maganin shi balla yayi ya jefa a baki kafin ya bi da ruwan buta ya koma ya kwanta yana nunfarfashi. Da asuba da karfin shi ya tashi ba kamar wancen ranar ba kasancewar bai bari ciwon ya shige shi sosai ba ya sha magani, kamar kullum saida ya kwankwasa masu Ummi kofa kafin ya wuce masallaci, koda ya dawo zama yayi ya gabatar da azkar da sauran addu'o'inshi Inda ya roki Allah ya kawo mishi dauki game da wannan matsalar da kullum kara gaba take yi a gare shi, bayan ya gama kuma ya daura da karatun alkur'ani mai tsarki cikin daddadar sautin kira'ar shi wanda ya karade ko ina na gidan hatta da gidajen makota na kusa, Amira tana daga tsakar gidan su ta na aikace aikacenta tana sauraren shi zuciyarta gari tass. Seven fourty Fatima ta gama shirinta na schools, sai dai yau ma kamar jiya har ta fito gida babu Joy babu labarinta, jiki a sabule ta k'arasa class, tana fatan Allah yasa ta cimmata a can , sai dai nan ma wayam, haka ta isa sit din su ta zauna jiki a mace. Yau kan damuwar data shiga yafi na jiya haka kawai jikinta ke bata ba lafiya ba, ta kudiri aniyar zata tambayi David ta ji ko mekefaruwa tun da shi dan uwanta ne bazai rasa sani ba. Da aka buga break time, ta yi sauri ta isa sit din David da har ya mike yana goya jaka da harshen nasara ta ce "Sannu David." Wani banzar kallo ya mata ya dauke, bata damu ba ita dai fatan ta taji halin da Joy ke ciki ta sake ce ma shi "me yasa Joy bata zo school ba kwana biyu." Share ta yayi kamar bada shi take magana ba bata yi zuciya ba ta sake cewa "ko bata da lafiya ne dan Allah ka gaya min na damun sosai da rashin ganinta?" D'agowa yayi wannan karon ya ce "ha'ahh! Wai ke mayya ce ne? To nima ban sani ba kije gidan su ki duba."daga haka ya fice ya barta tsaye a wurin. Haka Fatima ta koma gida cikin wani irin yanayi, tana isa kuwa labarin yau ma Joy batta zo school ba ta fara ba ummi da yadda sumayi da David, tausarta Ummi ta yi akan kar ta damu in sha Allah joy tana lafiya ai lafiya ke buya, ta dai ji ne kawai amma ba wai hankali ta ya kwanta ba. Ranar har Yaya Ameen sai da ya fahimci tana cikin damuwa daya dawo da daddare, shima cikin damuwar yake amma ya danne nashi, koda ya tambayeta damuwarta kin fada ta yi sai hawaye da ta shiga zubarwa sharr! Ummi na jin su bata saka baki ba, don abin na Fatima ya fara wuce makadi da rawa, har kullum bata gajiya da mamakin irin shakuwa da kaunar dake tsakanin Joy da Fatima. Da kyar Al'ameen ya lallabata ta sanar mashi da damuwar tata, tabe baki bayan ya gama sauraranta, shi bai ga abin damuwa akan wannan ba, hakan yasa bai bama damuwar tata mahimmanci ba, sai ma canza akalar hirar tasu da yayi. Washegari daya kama friday ma bata sake zani ba still Joy bata je school ba, zuwa yanzu kuwa ta gama yanke shawaran bin abinda zuciyarta keta azalzalanta akai wato zuwa gidan su Joy ............... Me buƙatar shiga group ya tuntuɓeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 8* ASSALAMU ALAIKUM KUYI HAƘURI DA JI NA SHIRU DA KUKA YI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SABODA WANI DALILI MAI ƘARFI , AMMA YANZU NA DAWO INSHA ALLAH ZAMU ƊORA DAGA INDA MUKA TSAYA, FATAN DAI BAKU MANTA LABARIN AL'AMEEN DA JOY BA KUCI GABA DA BIBIYA AKWAI FAƊAKARWA, WA'AZANTARWA RIKICIN KABILANCI, TARE DA ZAZZAFAN SOYAYYA MAI TAƁA ZUCIYA. A bangaren Joy kam jinye take yi hankali kwance, daga Mom har Papa wani irin so da kulawa suke nuna mata na musamman, sai dai kamar yadda Fatima ta shiga damuwa saboda rashin ganin ta, haka itama ta shiga matsanancin damuwa saboda rashin ganin Fatima, hakan yasa ranar Friday ta shirya don zuwa school amma ƙememe Mom ta hana ta zuwa ta ce ta bari sai Monday badan ta so ba ta haƙura saboda kar Mom ta zargi wani abu, ta bari idan ta wuce aiki sai ta saci jiki ta je gidansu koda Ummi ne ta gani, da wannan shawarar ta koma ɗaki ta cire uniform ta yi shirin zuwa gidan su Fatima, sai dai ga mamakin ta ranar Mom ƙememe taƙi fita ko bakin get har wurin sha ɗayar rana, kamar tasan abin da take ƙullawa, gajiya tayi ta miƙe taje ɗakin ta, a kwance ta sameta bata da alamar fita, zama ta yi a bikin bed ta ce "Mom yau baza ki je aiki ba ne." kallon ta tayi kafin ta amsa da "Yes daughter yau na ɗauki excuse zan huta sai on Monday." har ranta bata ji daɗin wannan lamari ba don ta sani in dai ba yau ba to bata da damar fita daga gidan sai ran monday, ita kuma bata jin zata iya jurewa har zuwa ranar ba tare da ta saka Fatima a idanunta ba, haka ta bar ɗakin Mom jiki a sanyaye, ranar haka ta wuni sukuku duk ranta babu daɗi. Kamar yadda Fatima ta ƙudiri aniyar zuwa gidansu Joy yau, bata yi ƙasa a gwiwa ba, la'asar nayi tayi shirinta na hadda, cikin dogon zumbulelen hijabi ta ruwan toka, ko jiran Ummi ta shafa addu'a suyi sallama da kyau bata yi haka bata biya gidan su Amira su jera da yara gidan kamar yadda suka saba jerawa ba ta wuce. Direct haryar gidan ta kama tana sauri don kar ta ci karo da idon sani.Sai da ta tsaya a gaban tangamemen get ɗin gidan sannan gabanta ya fara faɗuwa take wani irin tsoro ya shige ta, tsoron mahaifiyar Joy , sau ɗaya rak ta taɓa ganin matar wata rana an tashe su school, tun daga irin kallo ɗaya data mata tsoronta ya ɗarsu a ranta, sai dai bata jin duk da haka zata iya komawa batare da ta san halin da Joy ke ciki ba don ta tabbata baza ta iya rintswaba idan hakan ta kasance. Ta fi minti goma kafin ta daure ta miƙa hannu tayi knocking ɗin ƙaramin kofar get ɗin a hankali, bata zata za'a jiyota ba balle har a buɗe mata sai dai ga mamakinta taga an buɗe get ɗin wani baba iyamuri da ko zo in kasheka da hausa bai sani ba ya leƙo. Suna haɗa ido gaban ta ya faɗi amma ganin ya sakar mata murmushi, yasa taji hankalinta ya ɗan ƙwanta, cikin harshen nasara daya caƙude da yaren igbo ya ce "My daughter who ar u looking." da sauri itama cikin harshe da ya mata magana ta ce "I'm looking 4 Joy, ni ƙawarta ce naga kwana biyu bata zo school bane shi ne nazo in dubata ko lafiya." ɗan jim ya yi kafin ya ce "kom in." tare da buɗe mata ƙaramin get ɗin, jiki a saɓule ta bi bayanshi gabanta na dakan uku uku. Gurin zama ya nuna mata daga gefe, ya ce ta jira shi ya na zuwa yama Joy ɗin magana, idan ya shiga wa za'a ce mata, ta ce "Fatima Husain." "Ok." ya amsa mata tare da ficewa. Farfajiyar gidan Fatima ta shiga bi da kallo, bata taɓa shigowa gidan ba sai yau, take ta ji ta raina kanta, ashe girman gidan da tsaruwar shi daga waje duk shafan mai ne akan cikin, baƙauyiya tukuf ta koma tana bin ko'ina da kallo baki sake , tare da

Chapter 4 of 22