Share this page
kwasan dariya. Al'ameen bashi da aboki sama da Ali don shi ba mai yawan kwashe kwashe bane , tare suka yi makarantar primary nan IBB Inda bayan sun gama suka wuce maitunbi secondary school tun jss 1 ajin su daya har suka kammla gasu kuma yan unguwar kusan daya, hatta iyayensu sun san da zaman juna, yanzu da aka gama secondary kowa ya kama gaban shi shine zumuncin yayi wuya duk da suna tare a waya Bini Bini saduwace dai sai a hankali. Fira ce ta barke sosai, Aliyu ya siya musu awaran waken auya da pure water suka ci, sun sha fira sosai suna ba juna labarin makarnata da karatu, shi shi Aliyu direct university ya tafi yanzu haka FUTmin yake zuwa yana 200 level yana karanta languages, inda Al'ameen ke juwa JEFLA yana karantar bangaren Islamic low shima yana year 2 ne kamar dai Aliyu, sun Dade suna hira kafin Al'ameen ya mike yace zai wuce ganin biyar da Rabi ake nema. Taka mishi Ali yayi suna tafe suna ci gaba da hira, sunzo dai dai get din stadium wasu yan mata su uku suka fito daga cikin wajen kowaccenau cikin matsatsen JC kai ba dankwali daya da jakar baya goye a bayan ta dayar kuma hannunta kwallo ne suna tafe tana buga shi fa titi tana cabewa, da ka musu kallo daya zaka san yayan arna ne. Tsaki Al'ameen yayi tare da dauke kanshi a zuciya yana ambaton Allah da neman tsari daga shaidan, kallon shi Aliyu yayi ya ce "Ustaz namu har yanzu kanan nan da tsantsenin ka akan irin wadan nan matan." Al'meen yace "To ina amfanin wannan Abu haka don suna yayan arna sai su rika yawo haka suna fidda tsiraicin su, kamar wasu awaki, ya kamata gamnati ta dauki mataki don naga abin masgaba yake kara yi." Aliyu ya ce "waya gaya maka a zamanin yanzu yayan arna ne kawai suke irin wannan dressing, yanzu ai abin babu arna babu musulmai, don idan kaga wata yar musulman sai ka zubar da hawayen takaici yanzu haka wadan nan ma in ka bibiya musulmai ne." Da sauri Al'ameen ya ce "kai haba Allah ya sauwake, wadannan yayan arna ne babu hasken musulumci ko kadan a tare da su." Kafin Aliyu ya kai ga amsa musa suka jiyo muryar d'aya daga cikin yan matan bahaushiya rass tana cewa "Aisha, maryam pls Ku jirani na sai ruwa." Dariya Ali yayi yana cewa "you see ustaz me na gaya maka." Takaici da bakin ciki ya hana Al'meen amsawa, Aliyu ya ce "Hmmm alamarin yanzu duk sai a hankali fa kalli wasu ma." Ya Nuna mishi wasu yan mata dake sanye da atamfa amma ya matukar matsesu kamar in suka yi kwakwaran nishi zai barke, girgiza kai Al'meen yayi cikin takaici da wannan yanayin suka rabu da Aliyu ya kama hanyar gida. ***** Tunda Joy ta bar dakin Mom ta komawa dakin ta kan bed ta fada yana kuka ga ba ci ba sha, har kusan karfe biyar na yamma hakan ya saukar mata da zazzafan zazzabi mai hade da ciwon kai kafin shidda na gamma ta gama fita hayyacinci dkyar take sauke numfashi, Abu ne da bai taba faruwa da it's ba run tasowarta jinshi take yi sabo a gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin vta Mom kulawace na musamman da Nina kauna haka ma Papa shiyasa duk ta wahala ta kasa sukuni...... Share pls kuma a dan ringa taba comment ko babu yawa, ta hakan ne zan gane kuma bite dani ko A'a Me bukatar shiga group a tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:30 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 5* Da takaicin wad'annan y'an matan Al'ameen ya kamo hanyar gida, daf magriba ya iso k'ofar gidan su, ganin ana shirye shiryen yin salla yasa bai shiga ba ya nufi masallaci, koda suka idar bai tashi ba zama yayi a cikin masallacin yana addu'o'i tare da neman Allah ya kareshi daga sharrin ta'bar'barewar zamani, bai fito daga masallacin ba sai da aka idar da isha'i, daga nan kuma bai zame ko ina ba sai gida. A tsakar gida ya samu Ummi zaune kan shimfidar babbar tabarma, tana sauraren labarai a redio kasancewar mace mai yawan sauraren labarai, zama yayi a gefen tabarmar bayan Ummi ta amsa mishi Sallama, "Ummi sannu da gida." Ya fad'a yana gyara zaman shi da kyau, "Yawwa yayan Fatima ka dawo dama yanzu nake zancen ka a zuciya, ashe kana tafe." "Eh Ummi na tsaya na yi sallah ne gaba d'aya." Ummi ta ce "yayi kyau. ya karfin jikin." Ya ce "Alhamdulillah Ummi naji sauki sosai, da nayi sallar la'asar ma na kaima Aliyu ziyara ne." Ta ce "Allah sarki Aliyu yaron kirki makaranta ya boye shi, yana lafiya." "Yana lafiya Ummi yace yana gaisheki sosai, " "Allah sarki Aliyu d'an gidana ina amsawa ." Murmushi Al'ameen ya yi tuna tsakanin Aliyu da Ummi. Fatima Ummi ta kwalawa kira, daga can kuryar d'aki ta amsa tana tasowa daga kwancen da take har zuwa lokacin riga da skirt din nan ne a jikinta, ji ta yi Ummi na ce wa "Ki zo ki kawowa yayanki tuwon shi ga shi ya shigo." Jin haka yasa da d'aukinta ta koma d'aki ta d'auko ledar yalon data siya mai d'azu a hanyar makaranta ba ta samu ta ba shi ba, ta fito fuskarta washe da fara'a, tana ji dadi zata farantawa yayanta, hankalin shi na kan daddana yar wayar shi buttus, ya tsinci muryar Fatima na cewa "Yaya sannu da dawowa." 'Dagowa ya yi yana amsa mata da "Yawwa Fatima ya gi." Sauran zance ya ma'kale lokacin da ya sauke idananun shi a kanta, ran shi ne ya baci ganin shigar dake cikin ta, ta ke ya had'e rai yana binta da wani irin kallon da yasa gabanta fara dokawa. Lokaci daya fara'ar dake fuskarta ya juye zuwa tsorata, ta ke ta fara ja da baya, bata kaunar ganin wannan fuskar na yayanta, firgitata yake yi, ya kan mata irin wannan kallon ne a duk sanda ta yi wani abu ba dai dai ba, tunda ta ke da shi bai taba d'aga hannu ya duke ta ba, sai dai ya kan ladabtar da ita da hanyoyin data gwammace gara ya faffala mata mari akan su. Ummi bata san meke faruwa ba hankalinta na kan rediyonta tana kokarin canza channel ta tsinin ci muryar Al'ameen cikin kaushi ya na cewa "Zo nan Fatima." Ya karashe maganar yana nuna mata gaban shi. Bata iya mishi musu run tasowarta, hakan yasa ta shiga matsawa a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, nesa kaɗan da inda yake nuna mata ta tsuguna, ta re da duƙar da kanta kasa, a banza ma wani lokacin bata iya haɗa ido da shi balle yana cikin iri wannan yanayin. Ummi dai da ido ta bisu su bata tanka ba a ranta tana kunfi kusa. Ciki muryar shi mai dauke da amon bacin rai ya fara cewa "Fatima wannan wacce irin shiga ce kika yi haka kina yar musulmai," tsuru tsuru ta yi tana zare ido, cigaba yayi da cewa "Ashe ba na hana ki saka kayan da zasu bayyana surar jikinki ba, ina duk tarin suturunki na mutunci da nake dinka miki? Shiru tayi ba amsa ya cigaba "Ok na gane tarayyarki da yar arna abin yayi 'kamari har kin fara kwaikwayon dabi'u da shigarta ko?." Tuni Fatima ta fara girgiza kai tana kuma jin abin da me fitowa daga bakin yayanta, "ina tambayarki baki bani amsa ba kina kuka, nace tarrayyarki da yar arna abin yayi kamari har kin fara dauka dabi'unta ko, to wlh ba a nan gidan ba, kuma zan yi wa tufkar hanci, tunda ke naga alamar bakin jin magana, don bazan zuba ido ke kadai yar uwata da nake da ita a duniya ta lalace ba, zan dauki kwakkwaran mataki akan ki dake da ita wannan yar arnan, domin hakkinane na kula da tarbiyarki." Ya kai minti ashirin yana mata fad'a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba haushi da takaicin daya kwaso na yan matan da ya gani a hanya, da kuam haushin kawancen ta da yar arna da yake ji, duk Sai da ya sauke mata su, kafin ya tsagaita yana kallonta yana huci. Zuwa lokacin kuka Fatima keyi kamar ranta zai fita, daga yadda take jin amaon sautinsa tasan ba karamin baci ran shi yayi ba,ko daman bashi hakuri bata samu ba, jin yayi shiru yasa cikin shessheka ta ce "Yaya ka yi hakuri walla..." Dakatar da ita yayi da cewa "rufe min baki mutuniyar kawai, kuma ki bace min da gani." Dasauri ta tashi tana toshe bakin ta saboda sabon kukan da ke shirin kwace mata, ta kai bakin kofa ya d'aga muryar ya ce "kuma ki ciro kayan ki kawo mi yanzu yanzu." Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, bata ce komai ba, a ranta Sai hamdala take da tasbihi ma ubangijinta tasan ko yau ta fadi ta mutu Fatima baza ta tagayyara ba in dai har da Al'ameen a gefenta, kallon shi tayi shima ita yake kallo, kallon tuhuma, saukar da kai kasa yayi cikin taushin muryar ba irin wanda yama Fatima magana da shi ba ya ce "Ummi kinga abinda nake gaya miki, kinga abin da nake so ki hango amma kin kasa hangowa Ummi tararryar Fatima da yar arnan nan wlh na tabbata babu alkhairi a cikin sa, Sai sharri Ummi ki buba wannan lamari dan Allah." Murmushi Ummi ta yi a ranta ta ce "yaro yaro ne kuma duk abinda babba ya hango akace yaro ko ya hau rima bazai hango ba." Jin Ummi bata ce komai ba sai bin shi da kallo da take yi yasa ya mike ya nufi haryar zaure ran shi duk ajagule. ********* Joy na barin dakin Mom dakinta ta koma, ta fada kan bed ta cigaba da kuka har zuwa lokacin ko takalmin makaranta bata cire ba bare uniform haka ta wuni a daki ba ci ba sha, har wurin karfe biyar na yamma hakan kuwa ya saukar mata da zazzafan zazzabi mai hade da ciwon kai, kafin shidda na yamma ta gama fita hayyacinci dakyar take sauke numfashi ko idanunta bata iya budewa. Abu ne da bai taba faruwa da ita ba tun tasowar ta, jin shi take yi sabo a gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin ta da Mom kulawa ce na musamman da nuna kauna duk girman laifin da zata yi cikin rarrashi ta ke nusar da ita, haka ma Papa shiyasa ta ke ganin abin da girma. A bangaren Mom kuwa rudanin da take ciki ya shallake tunaninta, hakan yasa bata bi ta kan Joy ba. Karfe shida da rabi dai dai motocin Papa suka yi parking a counpound din gidan, fitowa yayi bayan daya daga cikin escort biyu dake biye da shi ya bude mishi kofa, fitowa yayi jacket din suit din shi a kafad'a hannushi rike da briefcase din shi, entrance din gidan ya nufa zuciyar shi cike da bege da kewar iyalan shi, ma'aikatan gidan sai kwasan gaisuwa suke yana amsa musu da fara'a, Koda ya shiga main parlour babu kowa bai damu ba, upstairs ya haura yana kiran sunan baby kamar yadda yake kiran Joy, yayi mamakin da har ya 'karasa hawa saman ya isa babban kayataccen falon daya fi na kasan kyau da kayatuwa, baiga ta fito da gudu ta tare shi ba kamar yadda ta saba, to ko dai bata gidan ne? Ya jefawa kanshi tambaya. Bai samu wannan amsar ba Mom ta fito daga dakinta, sakar ma juna murmushi suka yi wanda ita nata iyakarsa la'b'ba, bud'e mata hannayenshi yayi ta fad'a jikinshi suka rungume juna cike da soyayya,cike da kissa take mai sannu da dawowa yana amsa mata da zuciya d'aya cike da kulawa, amsar jakarshi da jacket din shi ta yi ta kama hannunshi zuwa dakin shi. Wanka ta taya shi yayi, ya shirya cikin kayan zaman gida, zama yayi a falon wanda ke hade da bedroom din shi, yana amsa called, fita Mom tayi ta dawo dauke da ruwa da lemon five alive a tray, zuba mishi ta yi ta mika mishi amsa yayi yana murmushi ya ce "thank you Sweetie." Itama murmushin ta yi ta zauna a gefen shi ta maida idanunta kan TV duk da kallo kawai ta ke yi hankalinta baya gurin, sama da minti talatin Papa ya kwashe yana waya da wani tsohon abokin kasuwancin shi wanda suke shirye shiryen had'akar Samar da wani kamfanin sarrafa 'karafina a Lagos. Ko da ya ajiye phone din Mom bata kula ba, muryar shi ta tsinta yana cewa "Hala baby bata nan ne?" Ta amsa mai da "tana nan, tana dakin ta." Murmushi ya yi ya ce "yau mulki take ji baza tazo ta ma Papa welcome back ba kenan, bari to ni naje na ganta." Daga haka ya mike ya fice daga dakin. Tun kan ya karasa dakin yake ce wa "baby where are u, I'm back, your Papa is back." Yana maganar yana murda handle din dakin nata,yana shiga idanun shi ya sauka a kan ta , zaro ido yayi kafin ya karasa da sauri ya haura kan bed din ya shiga jijjgata yana kiran sunan ta, da kyar ta bude idon ta da suka kumbura, murya a shake ta ce "Mom ki yafe Mom kiyi hakuri." Bai jita ba saboda shakewar da muryarta ya yi, a gigice ya ciro waya ya dannawa Dr dake duba su waya, jin yadda Papa ke gigice yasa, ya ce ya bashi fifteen minute gashi nan zuwa. Yana ajiye wayan ya shiga kwala ma Mom kira, bata ji ba saboda tazarar dake tsakanin dakunan, kuma gashi ko ina a kulle, ganin zai bata lokaci yasa yayi amfani da telephone din dake dakin joy ya kira lambar dakin shi da shi. Mom dake zaune ganin kira ta wayar tafi da gidanka abin ya bata mamaki, ta shi ta yi ta dauka, jin yadda Papa ke magana a rude yasa taji gaban ta ya fadi da gudu ta kwasa zuwa dakin Joy.......... Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu🙏 yawan comment yawan tsayin page😬 Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:31 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 6* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* Yadda Mom ta hango Joy a hannu Papa tana kakkafewa yasa ta 'karasa da gudu, a rud'e take tambayar shi me ya same ta, cikin wani irin yanayin yace "Alice I don't no nima haka na shigo yanzu na same ta." "Jesus!!!" Mom ta ce lokacin da ta d'aura hannunta a goshin joy jin yadda ya dau zafi radau, "Mu kaita asibiti honey karmu rasata." Ta fada tana shirin fashewa da kuka, "Na kira Dr solo ya ce yana zuwa yanzu." Papa ya amsa mata, gyada kai ta yi tana share hawaye. Wayar Papa ne ya dauki ruri, ganin Dr ke kira yasa ya daga da sauri, yana cewa "ka iso ne Dr." Dan dakatawa yayi kafin ya daura da "OK ka karaso da sauri Dr ka hawo sama tana dakinta." Cikin kankanin lokaci Dr Solomon ya karaso dakin Joy yana d'auke da jakar kayan aikin shi, ganin yanayin da take ciki yasa ya nemi da su Papa su bashi guri, da kyar suka fita suka tsaya a bakin kofar dakin, Mom rungume jikin Papa tana kuka shi kuma sai bubbuga bayan ta yake yi idanu jajur, Minti talatin Dr Solomon ya kwashe akan Joy, ya gano damuwace da yawan kukan da tayi ya haifar mata da zazzabi da ciwon kai mai tsanani sai ulsanta daya ta shi saboda rashin ci da sha, take ya bata duk taimakon daya da ce, ya mata allurai tare da daura mata drip, barcin wahala ne ya kwasheta kasancewar a cikin alluran da ya mata har da na barci, sai da komai ya daidaita sannan ya fito. Da sauri suka yiyo kanshi suna rige rigen jero mashi tambaya, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga yi musu bayanin abinda ya gano yana damunta, cikin kwantar da murya ya daura da cewa "kuyi hakuri yanzu dai komai zai dai dai ta don na bata duk taimakon daya dace na daura mata drip na mata allurai, yanzu haka barci ya dauketa saboda alluran da na mata masu karfi ne kuma akwai na barci a ciki zaku iya shiga shiga ku ganta." Tare suka koma dakin da Dr , zama kusa da kanta Papa yayi ya kamo daya hannunta da babu canula ya rike yana binta da kallon zallar kauna da tausayawa, Mom kuwa ta wurin kafafunta ta zauna ta zuba mata idanunta mai dauke da danshin hawaye ganin yadda ta rame ta kara haske a cikin yini guda. Gyaran murya Dr yayi duk suka kalle shi ya ce "Mr and Mrs James ni zan koma hospital dan na bar aiki sosai na taho nan, amma zuwa safe zan dawo na sake dubata na kuma kawo magungunan da zata sha, sannan ruwan da na daura mata zai Kare nan da sha biyu na dare, za kuma ta iya farkawa nan da hudun asuba idan ta ta farka Ku tabbatar ta ci abinci kafin na iso." Godiya suka mishi Papa ya rako shi har parking lot na gidan, tare da mai alkawarin kafin ya isa gidan zaiji alert kudin siyan magunguna dana shan mai, shima godiya ya shiga yi, don yasan yau account din shi zai kwana da nauyi. Kusan a kanta suka kwana suna bata kulawa, cikinsu babu wanda yayi barcin kirki, sha biyu ruwan ya kare kamar yadda Dr ya fad'a, Mom ce ta cire mata, bata farka four kamar yadda Dr ya ce ba sai gurin six na safe har sun fara damuwa suna tunanin kiran Dr ta farka. Dishi dishi ta fara gani, kafin a hankali komai ya daidaita, tar ta ware idanunta akan mahaifinta wanda zuwa lokacin shi kadai ne a dakin, da sauri ya karasa kusa da ita ya kamo hannunta yana mata sannu, kura ma shi ido tayi tana kokarin son tunano abin da ya faru, Dai dai time din Mom ta turo kofar dakin ta shigo, motsin kofar yasa ta maids idanunta gurin, idanunta ne ya sauka cikin na Mom, take abin da ya faru ya dawo mata tsab, shesshekan kuka ta fara, ganin haka yasa Mom karasawa da sauri ta kama daya hannunta, girgiza mata kai ta shiga yi, alamar kar tayi kuka, a hankali ta bude baki hawaye na bin gefen fuskarta ta ce "Mom ki yi hakuri ki yafe min." Hannu Mom tasa tana share mata haware, kafin ta ce "Ya isa haka daughter ki daina kuka, kinga baki da lafiya." "Bazan daina kuka ba har sai kin yafe min Mom, bazan iya jurar fushin ki ba." Dauke kai Mom tayi cikin dan bata fuska ta ce "zan hakura amma sai kin mini alkawari babu ke babu wannan yarinyar." Ba tare da tunanin komai ba don a lokacin mafita da sassauci kawai take nema ta ce "Na yi miki alkawari Mom daga yau babu ni babu ita har abada." Murmushin farin ciki da nasara ne ya kwacewa Mom ta rungumeta tana ce wa "nagode daughter ina son ki ina tsananin kaunarki." Dariya ta saki mai sauti cike da jin dadi ta ce "I luv u 2 my Dear Mom." Gyaran muryar da Papa yayi ne yasa Mom sake Joy, kallon tuhumar da yake mata yasa ta yin murmushi, da ido ta mai alamar yayi shiru zata mai bayanin komai anjima, bai ki ta tata ba, kawai yaja bakin shi ya tsuke. Tea Mom ta hada mata, papa ya taimaka mata ta zauna, da kanshi ya ringa bata tana sha har ta shanye, abinci mai saukin nauyi mom ta shiga kitchen da kanta ta samar mata, ganin yadda Mom ta sake da ita yasa ta kwantar da Hankalinta ta ci abincin sosai, kan kace koba sai gata ta gyagyije, da kanta tayi wanka ta shirya, cikin riga pink mai hannun singlet da wando legis fari, Karfe takwas Dr Solomon ya iso ganin yadda patient din shi ta gyagyije yaji dadi sosai, magungunata ya bata ya musu sallama ya tafi. ********* Sai da taci kuka ta koshi kafin ta mike jiki ba kwari ta kwabe kayan ta canza zuwa dogon rigar atamfa, ta dauke dan madaidaicin hijabi ta sanya, ninke wadancen kayan tayi ta kwaso ta fito dakin, ganin baya tsakar gidan yasa ta nufi hanyar zaure, sallama tayi da yar siririyar murya, amsa mata yayi tare da bata izinin shigowa, a bakin kafifar shi ta same shi zaune, har zuwa lokacin fuskarshi a hade babu rahma, daga nisa ta tsuguna, cikin sanyin murya ta ce "Yaya kayi hakuri bazan sake ba." Ta karashe tana mika misha kayan, bai amshi kayan ba kuwa bai amsa mata ba, ganin haka yasa ta sake cewa "Yaya dan Allah da manzonsa ka yafe min, wlh tsautsayine na yi maka alkawarin bazan sake ba" sai kawai ta fara shesshekar kuka. Rintse idanu yayi, jin kukarta yake kamar saukar ruwan zafi a zuciyar shi, yana jin Fatima a zuciyar shi fiye da tunani me tunani, yana mata so irin wanda kafin a same shi tsakanin yan uwa sai an tona, kukanta yakan yi saurin raunata zuciyar shi, matsayi uku yake takawa a rayuwarta UBA, DAN UWA, da kuma ABOKI, sun budi ido ne daga shi har ita basu san kowa ba sai junansu sai kuma Umminsu, hakan yasa suke ma juna wani irin so Mara iyaka, tunda ya fara girma ya fahimci basu da wani gata sai Allah sai Ummi mahaifiyarsu da take tsaye a Kansu dare da rana, ya kudiri aniyar zame mata gata, yadda yake maraicin rashin mahaifi ko wani tsayayyen dan uwa ita bazai taba bari tayi shi ba matukar

Chapter 3 of 22