Share this page
"Mallam ashe har an kammala, to mungode Allah ya saka da alkhairi, ga wannan ayi hakuri." Cewar Ummi tana mai mika mishi naira dubun dake hannunta, amsa ya yi, ya ce "Nagode Hajiya, an kammala an daure kafar nan da kwana hudu zan zo a kwance, an ma yi sa'a baiyi tsami sosai ba ku ka kira ni, Allah ya bashi lafiya." Da "Amin ya Rabbi!." Ummi ta amsa mishi, suka yi sallama ya tafi. Jiki a sanyaye Ummi ta tura kofar dakin ta shiga, cikin hukuncin Ubangiji barci ya dauke shi, sai dai kallo daya zakasan barcin azaba ne, duk ya hada uban gumi. Labulen window ta dage ma shi don ya samu iska, daga haka ta fice daga dakin. Awa biyu ya kwashe yana barci kafin ya farka, zuwa lokacin zafin da bacin ran dake tattare da zuciyarsa game da abinda Dr Abdul ya yi masa ya ragu kaso hamsin cikin dari. Shiru ya yi yana tunanin abinda ya faru da shi yadda accident din ya afku da abinda ya biyo bayan afkuwarsa, bai san dalili ba sai ya samu Kansa da sakin tattausar murmurshi a fila ya furta "Matsociya." Sallamar Fatima ya katse ma shi tunani, ganin shi a farke yasa ta saurin karasowa cikin dakin, a gabashi ta zauna tare da cewa "Sannu Yayana ka farka ya jikin?" Murmushi ya yi mata a hankali ya ce "Alhmdllh kanwata." Mikewa ta yi tana cewa bari na gayawa "Ummi ka farka." Tare suka dawo da Ummi, gefen katifar shi ta zauna, cike da tausayawa ta ce "Amintacce ka farka, yaya jikin?" Ya ce "Ummina da sauki." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Garin yaya kaji ciwo haka?" Shiru ya dan yi kafin ya ce "Accident na samu mota ce ta kade ni, amma ba wani mugun kadewa ba kawai dai abin yazo da tsautsayi ne." Girgiza kai ta yi cike da alhini, ta ce "A ina ne?" "A cikin unguwa ne, na kamo anya ina dawowa gida." "Asshha!Ubangiji ya kara kiyayewa." Ranar Al'ameen a gida ya wuni Ummi da Fatima na jinyar shi ko kwakkwarar tari ya yi su yi ta rige -rigen tambayar shi lafiya me yake bukata, tausayinsu ya kara lullube zuciyarsa, ya kara tabbatarwa duk duniya bashi da kamar su. *********** *Amira* Yinin ranar haka ta yi cikin rashin walwala da faduwar gaba, kullum da tunanin shi ta ke wuni, sai dai yau duk sanda ta tuno shi sai gabanta ya yanke ya fadi, yau kimanin kwana uku kenan rabon da ta saka shi a idanunta, takan shiga gidan kullum kamar yadda ta saba sai dai ta lura kamar yana kaucewa haduwar su da gangan ne, yau kam tana jin idan bata saka shi a idanunta ba baza ta iya rintsawa, hakan ya sa ta shirya abin da zata fada a gida don a barta fitowa. Misalin karfe takwas na dare ta yi sallama a tsakar gidan, Fatima na wajen Al'ameen don haka Ummi kadai ta tarar a daki, zama ta yi a saman dardumar da ke shimfide a tsakar dakin, a mutunce kamar ko da yaushe ta ce "Barka da dare Ummi mun wuni lafiya." "Lafiya kalau Amira, ya dare ya exam." "Alhmdllh Ummi, an gode Allah." "To Allah ya dafa ya bada nasara." "Amin Ummi nagode." "Ya su Maman Amira, da sauyan yan uwa." "Duk suna nan kalau." "Ma sha Allah kya isar min da gaisuwa." Daga haka su ka zauna shiru na dan mintoci, Ummi ta yanke shirun ta hanyar cewa "Ya akayi ne Amira naga kamar ki na son yin magana." Kasa ta yi da kai ta ce "E Ummi dama wajen Fatima na zo kuma naga kamar bata nan." "Ayyo Fatima na wajen Yayanta, da yake dazu ya samu tsautsayi a kafa." Rass! Rass! Haka gabanta ya yanke ya fadi, bata san sanda ta dafe girji da sauri ba, cikin rudewa ta ce "Subhanllahi! Na shiga uku! Meya same shi, Allah yasa ba mummunar rauni ya ji ba?" Shaf ta mance da Ummi take magana. Ganin yadda Ummi ta zuba mata idanu yasa ta ji wani kunya ya lullu6eta, da sauri ta yi kasa da kai don gani ta yi kamar Ummi taga abinda ke zuciyarta, basarwa Ummi ta yi ta ce "Wallahi d'azu ne yana dawowa gida mota ta kade shi har ya samu targade a kafa, amma da sauki an gyara an daure kafar." Dakyar ta iya ce wa "Allah sarki! Ubangiji ya ba shi lafiya." Ummi ta amsa da "Amin." Daga haka shiru tayi zuciyar ta ya raunata ji take kamar ta zubar da kwalla amma ta daurw saboda a gaban Ummi take, ranar kasa sakin jiki ta yi suyi hira da Ummi kamar yadda su ka saba ta yi,duk da yadda Ummin ta dinga kokarin jan ta da hira, ita kanta Ummi ta fahimci tana cikin tashin hankali. Zaman mintuna ka dan ta kara ta mike ta na cewa, "Ummi bari na je." Ummi ta ce "Har zaki tafi, to shike nan Amira sai da safe, ki biya dakin Yayan Fatiman, Bintan tana can daga nan ma kya gaishe shi da jiki." "To Ummi nagode." Ta fada tana ficewa. Ta kusa minti biyar a bakin kofar dakin ta kasa shiga, dakyar ta yi ta maza ta yi sallama a hankali Kamar wata mai koyan magana, karfin jin da yake da shi yasa ya jiyo ta, Fatima kam bata ji, a kan labbansa ya amsa, haka kurum ya samu kan shi da da faduwar gaba. tsoron shi daya kar ace ta fesa wannan shu'umun turaren na ta. Minti biyu ta kuma kwashewa kafin ta sake yin wata sallamar ta karo na biyu, wannan karon da dan karfi, sai a lokacin Fatima ta ji, amsawa tayi , tare da ce wa "Anty Amira ce Bismillah! Shigo mana." Kamar wata munafuka haka ta bude kofar net din ta shigo, daga dan nisa da shi ta samu waje ta zauna, idanunta na kan kafafun shi dake daure, wani irin tausayi shi ne ya lullu6eta, ji take kamar ta zubar da hawaye, a sanyaye ta dago ta saci kallon fuskar shi, cikin sa'a su ka hada ido, da sauri ta dauke idanunta daga cikin na shi, ta mayar kan kujewar dake gefen fuskar shi, don baza ta iya jurar ci gaba da kallon kwayar idanun shi ba, a haka ta bude baki dakyar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen, ya jiki, ashe abin da ya faru kenan Allah ya sauwake yasa kaffara ne." A jere ta yi gaisuwar ba tare da ta jira sai ya amsa ba. Kusan hada baki suka yi shida Fatima wajen amsa mata da "Amin ya Allah." Daga haka su ka gaisa da Fatima, tana kara tambayarta ya mai jikin, ta amsa mata da "Alhmdllh." Zaman shiru na yan sakanni ya gifta, Fatima ce ta katse shirun ta hanyar jan Amira da hirar islamiyya, kasa sakin jiki ta yi su yi hira kamar yadda su ka saba. Al'ameen na jin su, amma ya lumshe idanu kamar mai barci, a zuciyarsa kuwa hamdala ga Allah yake da bata feso wannan bakin turaren na ta ba. Hirar bai yi wani tsayi ba ta mike ta ce zata wuce, Fatima tace "Kai Anty Amira tun yanzu, ki dan kara zama mana yanzu fa 8:30 ta yi." Kin zaman ta yi don jin ta take duk a takure. Ba don Fatima ta so ba su ka yi sallama, sake satar kallon shi ta yi ganin idanu I a lumshe ta samu karewa kyakkyawar fuskarsa kallo, har da dan sakin ajiyar zuciya irin mutum ya samu relief din nan, sai da tayi ma'ishi sannan ta mike tana cewa "Fati ya samu barci in ya farka kya kara gaishe shi, sai da safe." Duk abin da take yana kallon ta ta kasan ido har ta fice daga dakin. Bayan tafiyarta Fatima kimtsa mi shi dakin ta yi ta kashe mishi wuta ta fice don duk a tunanin ta barcin gaske yake. Ya dade yana tunane-tunane kafin barci gasken ya yi awon gaba da shi, koda ummi ta zo sake duba shi itama ta tarar ya na barci ne, gyara mishi rufa tayi ta yi addua'a ta tofa mishi sannan ta fice ta kulle kofar gidan tunda yau me kullewar na kwance babu kafa. Daga nan itama ta wuce ta naimi makwanci asuba ta gari. ******** *JOY* Daga wurin da accident din nan ya faru direct gida su ka wuce don dama akan hanya komawa suke, ta je shopping ne. Har su ka iso gida kuka ta ke yi, Peter duk ya rude sai hakuri yake bata, zama tayi a mota dakyar ta samu ta tsaya da hawayenta, ta goge fuskarta sannan ta fito ta nufi Cikin gida, tuni kayan shopping dinta sun isa ciki, daki ta ta yi niyar shigewa ba tare da ta bari sun hadu da Mom ba, sai dai hakan bai su ba, don a main parlor ta tarad da Mom, a rude mom da yanzu take nuna mata wani irin soyayya mai karfi, ta tare ta ganin yadda manyan fararen idanunta su ka rune su ka kankance, sai dai tambayar duniya ta mata ba amsa data takura mata sai hawaye, a rude Mom ta sama aka kira mata Peter, a bakin shi take jin abinda ya faru, amma bai gaya mata cewa Al'ameen ba ne, ba tare da nuna alhini ko tausayi ba take tambayar ina wanda su ka bige din, nan ya kwashe yadda su ka yi da mutumin ya gaya mata, kuma ya tabbatar mata dan unguwar nan don ya san gidan su. Cike da jin haushi Mom ta ja tsaki ta ce "Mitsiyacin banza shi ya sani ai, ya yi wa kansa" daga haka ta ci gaba da rarrashin yarta. Wani irin yini ta yi ranar mai matukar azabtuwa ga ruhinta, a duk sanda ta tuno lamarin kukanta saboda fil yake komawa, hakan ya haifar mata da ciwon barin kai, sai dai ta yi ta dauriya bata bari Mom ta sani ba gudun kar ta saka mata ayar tambaya, dakyar da rarrashi ta iya tsakarar abinci haka ta wuni a kwace kamar ruwa. Bata gane lamarin ya girmama a gareta ba sai da dare ya yi, kememe barci ya kauracwa idanunta, don a duk sanda ta rintse idanu shi take gani,cikin raunika da yadda yake dingisa kafa cike da azaba, haka ta kusa raba dare tana hawaye, dakyar barci barawo ya saceta, sai dai ko awa biyu bata cika ba ta farka a firgice ta yi mafarki wai Al'ameen ya mutu, ta shi ta yi daga kwance ta zauna da duwawunta a tsakiyar gadon ta rafka tagumi tana ta tsiyayar hawaye ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta je taga halin da yake ciki, ya zama dole gobe ta je ta duba ba shi idan ba haka ba hankali ta bazai taba kwanciya ba............. Gashi nan harda na jiya😬 Gamai bukatar shiga group ya tu tubeni kai tsaye. 09116099486. [12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 26* No editing ayi ta hakuri🙏 Washegari haka Ummi da Fatima su ka tashi da hidamar Al'ameen, abin ma yazo musu da d'an sauk'i ne saboda shi d'in jarumi ne, bai sakar musu ragamar komai ba, yakan yi iya k'ok'arinsa, idan ya kasa sannan ya naimi taimako, yanzu ma Fatima ce ta yi sallama d'auke da abincin karin kumallon shi a hannu, ga mamakinta a tsaye ta same shi yana bin bango zai fito waje har ya kai bakin k'ofa. "Subhanallah! Yaya ina zaka je?" Murmushi ya sakar mata, ya ce "Na gaji da zaman d'aki ne k'anwata zan fita tsakar gida in sha iska." Kwa'be fuska ta yi ta ce "Shine baka kirani in taimaka maka ba, idan ka fama ciwon ka fa?." Ta karashe maganar tana k'ok'arin rik'e shi, ya ce "No Barshi Fatima zan iya, ki je ki shimfid'a mini tabarma a tsakar gida." Cike da mamakin karfin halinsa ta ce "To Yaya." Ta fi ce. Kici kicin shimfid'a tabarman da ta ke yi ne yasa Ummi dake kitchen lek'owa "A'a Fatima ya haka kuma?" Cewar Ummi sanin ba wai sun saba zaman tsakar gida da safe bane. "Yaya ne ya ce na shimfid'a mi shi zai fito yasha iska wai ya gaji da zaman d'aki." Kafin Ummi ta ce komai sai gashi ya shigo da bin bango da dabara ya ke lalla6awa, da sauri Ummi ta zo ta rik'e shi, ta na cewa "haba Amintacce, ai da ka yi magana sai a taimaka maka." Da murmushi ya ce "A'a Ummi zan iya ai." Ita dai bata yarda ba sai da ta rik'e har kan tabarman da Fatima ta gama shimfid'awa ya lalla6a ya zauna, yana rintse ido lamar yana jin azaba, cike da tausayawa Ummi ta ce "Sannu Yayan Fatima Allah ya sauwak'e, ka yi k'o'kari ma wallahi zaman da'ki babu dad'i ga namiji, zaman dak'i ai sai mata, Allah dai ya ta shi kafad'a yasa kaffara ne." Ya amsa da "Amin Ummi." Kayan tea Fatima ta jera a gaban shi da flask d'in ruwan zafi ta shiga had'a mi shi, kallon ta ya yi ya kalli Ummi ya ce "Ummi yau kuma tea zamu sha, babu kamun ne." Ta ce "A kwai naga baka da lafiya ne, kamar zaka fi son shayin shiyasa na bada kudi ta siyo buredi da sauran kayan hadin tunda shi kokon naga kayan fitsari ne." Yamutsa fuska ya yi alamar baiso ba, amma bai ce komai ba, sai kallon Fatima da ya yi ya ce "Sister ka d'an za ki hada shayin." Ganin yanayin shi yasa Ummi cewa "ko a dama maka kunun ne? Naga kamar baka son shayin." Baya son bata wahala , sai kawai ya ce "A'a Ummi ki barshi kawai zan sha." Kafin Ummi ta ce wani abu Aysha kanuwar Amira, ta yi sallama a tsakar gidan. A tare suka amsa mata, ummi ta ce "Aysha ke ce tafe." Ta ce "E ni ce, ina kwana ummi ya mai jiki. " "Alhmdllh da sauki." Juyawa ta yi bangaren Al'ameen shima ta gaishe shi tare da yi masa ya jiki, ya amsa da " Alhmdllh." Basket mai dan girma dauke da kuloli da flask ta fito da shi daga hijabinta, ta ajiye gaban Al'ameen tare da ce wa "Yaya Ameen wai gashi, in ji Anty Amira ta ce na kawo maka wai tana gaishe ka da jiki." Share Aysha ya yi kamar bai ji abinda ta ce ba, wani banbarakwai ya ke jin lamarin, amma yarinyar nan bata da hankali mai take tunanin Ummi da Maman Amira zasu zata idan suka ga haka. Ummi kam murmushi ta yi ta ce "Lallai an gaida Amira harda hidima haka ki ce mata Amintacce yana godiya." Fatima murmushi take yi a ranta tana lallai Anty Amira kin zurma da yawa Allah dai ya tabbatar da wannan lamarin. Sallama Aysha ta yi musu Ummi ta ce "Tsaya ki amshi tukwuici." Tana kwance habar zani da sauri Aysha ta yi hanyar waje ta na cewa "A'a Ummi wallahi ki barshi nagode." Yi ya yi kamar bai san an ajiye wani basket a gabansa ba, ya yi kicin kicin da rai, Ummi ta kalle shi, sai kawai ta yi murmushi, ta ce "Fatima bude abincin nan mu gani." Barin hada shayin ta matso ta fara cirowa kula guda biyu ne tuwo da miya, sai jug, babban kulan ta fara budewa kosai ne an yi shi manya manya jan suya gwanin sha'awa, ta bude karamin shi kuma farfesun kayan ciki ne a ciki da romo kadan sai turiri yake da kamshin kayan yaji jug din kuwa kunun tsamiya ne hadadde shima da zafin shi. Rike haba Ummi ta yi, ta ce "Umm! Lallai Amira, to angode Allah ya yi albarka." Kollonta ta kai kan shi ko kallon side din abincin bai yi ba, ta ce "Amintacce ga abin kari in ji Amira." Ya ce "Angode kuci kawai Ummi, Fatima mikomin shayin da kika hada."Ummi ta ce " Baza ayi haka ba Yayan Fatima, Binta dauko kofi da plate ki zubawa yayanki abinci." Mikewa tayi ta shiga kitchen ta dauko ta zo ta zuba mishi kunun da kosan zata zuba farfesun Ummi ta ce "Bar wannan Binta ya ci anjima." Ta amsa da "To ummi." Tare da mika mishi abincin gaban shi. Dakyar da takurar Ummi ya dauki kosai daya ya yi bismillah ya kai baki ya gutsira, babu laifi yaji dadin shi sosai bai san sanda ya tura guntun a baki ba, daga haka ya shiga ci yana kora kunun sai ga Mallam Aminu ya kar kunu da kosai tas. Ummi da ke mishi dariya a ranta ta ce "A kara ne?", yamutsa fuska ya yi ya ce "A'a Ummi Alhmdllh." Ummi da Fatima ne suka ci sauran ragowar kunu da kosan, farfesun kuwa Al'ameen aka ajiyewa da rana aka dumama mi shi ya sha. Makota na ta shigowa yi mi shi sannu da jiki baga mata da matasa tsararrakinsa ba har da dattijan unguwa, domin shi din mutumin mutane ne, yana da kirki da yawan gaisuwa, Maman Amira ma ta shigo haka kafatanin yan gidan gaba daya. ************* *JOY* Allah-Allah ta dinga yi gari ya waye ta je ta ga halin da Al'ameen ke ciki idan ba haka ba zuciyarta zata iya tarwatsewa, sai dai gaba daya Daren ranar ya mata nisa, dakyar ya iya jumirin jiran har bakwai da rabi ta yi. Duk da tarin ciwon kan da take fama da shi, hakan bai hanata tashi ba, cike da karfin hali ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando kanana as usual, sakkowa ta yi dining ko Mom bata jira ba ta yi breakfast din ta ita kadai duk da iya tea ne kawai ta iya sha. Dakin Mom ta nufa, ta tarar bata tashi ba, ji ta yi baza ta iya jira har sai lokacin da ta farka ba, hakan yasa ta zauna a bakin godon ta shiga dan bubbuga pillow, Mom ta bude idanu cike da barci ta kalleta, ganin yadda idanunta suke har zuwa yanzu a rine gashi sun kara kankancewa fiye da jiya, saboda kwanan da ta yi kuka yasa ta mikewa zaune cike da damuwa ta ce "Daughter, me yasame ki?" Ta kai hannu tana tattaba jikinta, rike hannunta ta yi ta ce "Babu komai Mom tun kukan jiya ne da na yi." "Amma Daughter ya kamata ace tunda kin yi barci kin farka idanunki su dawo daidai ba wai su kara rinewa ba." Shiru ta yi ta rasa me zata ce don kare kanta. "An ya kuwa lafiyar ki kalau, idan kina jin wani damuwa ki sanar min muje asibiti." Girgiza kai ta yi, ta ce "I'm ok" "Well!" Mom ta faa tana gyara kwanciya. Langwabe kai ta yi ta ce "Mom ina son zanje landmark bookshop na duba wani story book da nake nema, da ma wasu books din wadanda nake da su duk na gama karantasu." Tsare ta da idanu Mom ta yi na yan wasu sakannni tana nazartanta, Hankalinta bai kwanta mata da fitar ba, hakan yasa ta ce " Da sassafen nan haka? Ki barshi kawai ba sai kinje ba, ki fadi sunan book d'in zan saka a naimo miki." "Ok Mom Thank U." Ta fada tare da mikewa ta fice a dakin gudun kada kwallan daya ciki idanunta su zubo a gaban Mom. Sarai Mom ta ga yanayin da ta shiga hakan yasa ta kara gaskata zarginta akanta. Da gudu ta fada kan gadonta ta rushe da kuka, ya ya zata yi? Ina zata saka ranta ta ji sanyi? Wani hali Al'ameen yake ciki, shin kodai ya mutun ne da gaske kamar yadda ta gani a cikin mafarkinta, yin wannan tunanin yasakata mikewa zaune zumbur! Zuciyar ta ne ke Ingizata akan ta saci hanya ta tafi . Da sauri ta mike tsaye da nufin tafiyar , sai kuma tsoro ya kamata, idan asirinta ya Tonu Mom ta sani mai zai biyo baya, ta tuna sanda Mom ta juya mata baya lokacin da ta gane tana mu'ala da Fatima, ko kadan baza ta so su koma gidan jiya ba, don baza ta iya jura ba da wanne zata ji. Komowa ta yi dabass ta zauna a bakin bed ta ci gaba da kuka. Wani shawara ne ya fado ranta wanda ya sakata mikewa da sauri kamar an tsikareta, da sauri sauri gudu gudu ta dinga saukkowa stairs, tana fitowa direct boy quarters din gidan ta nufa, bangaren da wasu daga cikin ma'aikatan gidan suke kwana, a kofar dakin Peter ta tsaya ta shiga knocking, da sauri ya fito ko amsa gaisuwar da yake mata bata yi ba ta ce "Peter, ka taimakeni." Ta fada tana hade hannaye hawaye na bin kumatunta, rudewa Peter ya yi, cikin rawar bani ya ce "Miss me ki ke bukata kiyi hakuri ki daina kuka ko meye zan miki matsawar baifi karfina ba." Tunda ta fara zayyano ma shi bukatar ta na tana son ya je gidan su Fatima ya dubo mata wani hali Al'ameen ke ciki, ya ke bin ta da kallon tausayawa ji yake kamar ya zubar mata da kwallah wannan wacce irin jarabta ce, a raunace ya ce "ki yi hakuri Miss na miki alkawarin zan je na dubo miki shi, yanzu dana gama abinda nake yi." Haka suka rabu da Peter ta koma cikin gida tana jiran tsammani. Kamar yadda Peter ya yi mata Alkawari karfe goma sha daya a kofar gidan su Fatima ya mi shi, kasancewar gidan ana ta shiga da fice na masu zuwa gaisuwa bai sha wahala gurin sanin halin da Al'ameen ya ke ciki ba, shi kanshi ya tausayawa yaron da fargaban yadda zai sanarwa uwar dakinsa wannna bakin labarin ya koma gida, bai samu haduwa da ita ba a lokacin, sai wuraren karfe shiddan yamma suka hadu. Kallo daya ya mata ya sauke kai, gaba daya ta fice a hayyacinsa kamar ba Miss Joy daya sani ba, "I'm sorry Miss labarin babu dadin ji." Ya fada a sanyaye. Wani irin Kwalalo ido waje ta yi tare da safe kirji a razane ta ce "Ya mutu ko."............ 09116099486. [12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 27* Wani irin gwalalo idanu waje ta yi tare da dafe kirji a razane ta ce "Ya mutu ko?" Girgiza kai Peter ya yi ya amsa da "Bai mutu ba." "To mai ya same shi?" Ta fad'a cikin shirin fashewa da kuka, Shiru ya yi yana nazarin mai zai ce mata don ba k'aramin tausayin ta yake ji ba, baya so ya fad'a mata abin da zai tayar mata da hankali, muryarta ne ya katse mishi tunani "Na rok'e ka kada ka boye min komai Peter, sanin halin da yake ciki shine kwanciyar hankalina." Ba yadda zai yi hakan yasa ya yi k'asa da kai ya ce "Na samu labarin cewa sanadiyar kad'e shin da muka yi, ya samu targad'e a kafar shi ta hagu sannan......" Shesshekar kukanta ya saka shi dasa aya, da sauri ya dago yana kallon ta, dama yasan za'a rina, an saci zanin mahaukaciya. Cikin muryar rarrashi cike da girmamawa matsayinta na uwar dakinsa ya ce "I'm sorry Miss ki daina kuka zai samu sauk'i soon, naji labarin tun jiya an gyara kafar an d'aure." Cikin kuka ta ce "Saboda mai ka ke cewa kar na yi kuka, bayan nice sanadin raunatar shi? Me yasa bazan yi kuka ba? Kasan yadda na ke ji a zuciyata kuwa?" Ta fad'a tana ta6a saitin zuciyarta, kasa ya sake yi da kai, tare da cewa "I'm sorry Miss." Zuciyarsa gaba d'aya ta raunana, anya zarginsa bai zamo gaskiya ba kuwa? Ko dai uwar d'akinsa ta fad'a soyayya da wannan yaron ne, domin lamarin ya fi gaban tausayi kad'ai. Daurewa ya yi dago ya kalleta tare da jeho mata tambayar da ke kai kawo a ransa,

Chapter 12 of 22