cewa "Na yi rayuwa a gidan nan cikin mawuyacin hali, tamkar mujiya haka na kasance a wajen mutanen gidan wata irin zazzafan kiyayya suke nuna min, kanne Husain mata har daki suke biyo ni su daka wani lokacin harda uwarsu sannan su hanani kuka, ko kishi zai kashe ni babu mai bani ruwa a gidan bare abinci, aikin gidan karakaf ni ke yin shi, Al'ameen kuwa ba shi da ikon raban koda karen gidan ne bare yaran gidan, a bangare guda kuma Tanimu ya uzzirawa rayuwata, bibiyata ya ke yi ido rufe yake neman mutuncina amma na ki ba shi hadin kai, hakan yasa ya kara tsanata kasancewarsa babba a gidan ya yi amfani da wannan damar wajen kara rura wutar kiyayyar dake tsakanina da yan uwanshi, duk da haka bai barni ba ya sha biyo dare don yi min fyade Allah na tseratar dani daga sharrin sa.
Tsamgama da wulakancin da suke mini baya daga min hankali kamar yadda suke kiran Al'ameen shege dan zina ya ke daga min hankali, na kan shi ga mugun yanayi a duk sanda hakan ta kasance, dai dai da sekon daya ban taba ji a zuciyata cewa maganarsu gaskiya bane, duk da bazan iya tunawa ba, ina ji a gangar jii da zuciyata cewa shi jininane kuma shi dan halak ne ba shege ba.....
[1/18, 12:39 PM] +234 803 069 9057: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 46*
A cikin wannan hali na kwashe shekara d'aya har da watanni a gidan Mamman kura, har zuwa lokacin babu abin ya canza dangane da muguwar k'iyayya da kyarar da na ke fuskanta daga ahlin gidan sai ma abin da ya 'karu.
A bangaren Al-husain tuni tausayi ya rikad'a ya koma sassanyar soyayya mai cike da dumbin kulawa da kyautatawa, sannan ga wata shakuwa mai tsanani minallahi daya k'ullu tsakaninsa da Al-ameen, har ta kai ga shi Ameen ke kallo a matsayin mahaifi, yayinda ni kuma a bangarena nake matukar ganin mutuncinsa na ke girmama shi na dauke shi tamkar wa na wanda muka fito ciki d'aya.
Hankalina ya tashi, ranar da Al-husain ya bayyana soyayyar sa a gareni, take jikina ya d'auki rawa, fatana Allah yasa wani bai ji mu ba, don nasan akan wannan lamari tsab ahlin gidan nan zasu iya cinna min wuta da raina, kuka na fashe mi shi da shi na shiga rokansa akan ya yi hakuri ya janye wannan maganar a tsakaninmu, take ya lashi takobi tare da tabbatar min da matukar na aminta da shi babu wanda ya isa ya hana shi aurena koda kuwa Dada ce (Mahaifiyarsa)
Ranar tsabar fargaba da zazzabi na wuni, wasa wasa ciwo ya kwantar da ni sosai, hakan baisa Dada ta ji tausayina ba bare y'ay'anta basu raga min da komai ba sai ma k'arin tsangwama ganin bana gama aiyuka da wuri kamar yadda na saba yi.
Al-husain ne kadai ya damu da halin da na ke ciki, bai βbata lokaci ba wajen siyo min gamungunan zazzabi a chemist na sha, sai dai sam babu sauki sai ma canza salo da ciwon ya yi, na shiga amaye-amaye babu abin da nake iya ci sai ruwa, ga kasala da yawan barci, cikin kwana biyu na kara ramewa na yi wani irin haske na d'anyance.
Har d'aki hajiya Dada ta biyo ni, ta kama tafukan hannuna ta duba ta kware idona shima ta duba, sai kawai ta kwantsama salati tana tafa hannaye, take d'aki ya cika abinka da gidan gandu, duk da lokacin hantsine mazan gidan basa nan, ta fashe da kukan kissa tana cewa "Dama na sani tsintacciyar mage bata mage, yanzu da abin da za ki saka mana ke nan, cikin shege a gidan Maman kura." Nan duk kowa ya shiga tafa hannaye ana sallallami, "Wallahi ciki ne da yarinyar nan, ku duba ku gani." Ta fada tana finciko ni tsakiyar d'akin, nan take suka yo caa! A kaina mai zagi na yi mai dunguri na yi, hajiya Dada kuwa sai cewa ta ke "Wallahi yau sai kin bar gidan nan ko na ubanki, baza mu ci gaba da zama da bara-gurbi ba, munafuka annamimiya." ta shiga kwasan y'an kayana da basu da yawan arziki tana watsi da su a tsakar gidan y'ay'anta na taya ta.
Dai dai lokacin Yaya Tanimu ya shigo gidan jin abinda ke faruwa ya harzuka shi, take ya zare belt ya shiga tafta min cike da bakin cikin hanashi cika muradin shi a kaina da na yi na baiwa wani cen banza har yana min ciki a cewarsa, duka na yakeyi a haukace yana furta "Uban wa ya yi miki ciki? Uban wa ki ka baiwa kanki?
Sam bana iya Kare kaina daga mugun bugun da Yaya Tanimu ke min, bare na samu damar amsa mishi tambayar shi, domin tun lokacin da Hajiya Dada ta furta cewa ciki ne da ni kaina ya sara tashin hankalin wannan furucin yasa duk abin da ke faruwa bana wani fahimta, ta yaya zan yi ciki,shin ana shan ciki a ruwa ne? Sune tambayoyin da suka dinga yawo a kwakwalwata.
Rashin samun amsa daga gareni ya k'ara harzuka Tanimu, shakeni ya yi da hannu biyu idanu jajir ya ke cewa a tsawace " Wa ya mi ki ciki Balki! Wallahi idan ba sanar min wanda yayi miki ciki ba sai na kashe ki! Uban wa ya miki cikin na ce!"
A guje ya shigo d'akin yana haki, ganin abin da ke ya faruwa yasa ya ya yi kukan kura ya cakumi Tanimu tare da yi mai wata irin shaka wanda yasa dole ya sake ni ba shiri, na zube a wajen kamar matacciya da dudu Al-meen ya fada kaina na yana girgizani tare da kiran sunana yana kuka.
Dakyar Yaya Tanimu ya kwaci kanshi, daga mummunar shakar da d'an uwan nasa ya yi masa.
A matukar fusace cikin daga sauti Al-husain ya shiga cewa, "Ba wanda ya yi mata ciki ku ke son sani ba! To ni ne na yi mata, d'ana ne a cikinta ni ne Uban cikin dake jikinta, kuma babu in da zata je zama a cikin ku yanzu ta fara shi domin ni zan aureta!"
Tasss! Hajiya Dada ta dauke shi da wani wawan mari, "Baka da hankali ne Usaini! A gabana ka ke furta cikin jikinta na ka ne, kuma za ka aureta! To bismillah shege ka fasa tsanin ni da kai, wallahi akan wannan tsintacciyar mahaukaciyar ina daf da daga maka nono."A fusace ta juya ta bar d'akin,Tanimu ya rufa mata baya yana 'kwafa tare da girgiza kai cikin tsanin bakin ciki.
Da sauri ya yo kaina ya dagoni hawaye kawai ke bin fuskata, da shakakkiyar murya na fara girgiza kai ina ce masa " wallahi ni ba fasika ba ce, ban taba kusantar wani d'a namiji ba." Ya ce "Na sani Balkisu ke ba mazinaciya ba ce, ni shaida ne ki kwantar da hankalin ki nasan ba ki da wani ciki sharri su ke miki." Ganin yadda na galabaita yasa ya ce na yi kokari na taka zuwa mota muje asibiti, ban iya ni kadai a dole sai da ya tallafa min.
Gado Dr ya bani ganin mawuyacin halin da nake ciki, a office ya rufe Al-husain da fada akan me za'a yiwa mace me karamin ciki irin wannan dukan, kasak'e Al-husain ya tsaya yana kallon Dr ke nan dai ta tabbata cikin ne da ni, ta ke zufa ya shiga karyo masa.
Hakuri ya shiga bawa Dr, daga bisani ya sanar da shi dukkan abin da ke faruwa, shi kan shi Dr ya kad'u da jin labarina ya tausaya min matuka, sannan ya tattabarwa Al-husain tabbas a kwai ciki a jikina d'an wata biyu, lamarin da ya kara jefeshi cikin tashin hankali, me yasa balkisu zata yi masa haka?
Suna cikin wannan tararrabin wayar Al-husain ta yi kuwwa ya duba ya ga Mallam ne wanda yake bani taimako har zuwa lokacin, bayan sun gaisa Mallam ya sanar dashi, yana neman shi akwai maganar da yake so su yi mai muhinmanci.
Bai bata lokaci ba ya tafi bayan ya baiwa Dr ajiyar Al'ameen.
A zauren Mallam bayan sun gaisa, ya dube shi da kyau ya ce " Yau kimanin kwana biyar, daya daga cikin aljanan da aka yiwa Balkisu asiri da su, ya bayyana a gareni, ya sanar da ni shine wanda aka wakilta ya danne yaron cikin da ke dauke a mahaifarta ya hana shi ci gaba da girma ma'ana ya kwantar mata da cikin, cikin hukuncin ubangiji muka tattauna da shi, mun yi maganganu masu yawa wanda na daukar masa alkawarin bazansanar wa kowa ba, a karshe ya shaida min shi ya tuba ya bi Allah bazai kara cutar da ita ba, don haka ma ya sakar mata cikinta zai ci gaba da girma, a mahaifarta daga in da ya tsaya."
Kakkarfar ajiyar zuciya Al-husain ya sauke a take ya shiga jerowa Allah godiya da kirari, daga bisani ya kwashe labarin halin da suke ciki ya sanarwa Mallam, Mallam ya jinjinawa iko da sarauta irinta mabuwayi Allah, ya kuma baiwa Al-husain wasu shawarwarin da zasu taimaka masa daga haka suka yi sallama.
Lokacin daya dawo asibitin na farka, ina ganin shi na fashe da kuka ina tambayarsa me likita yace game da cikin shin da gaske ne ina da ciki? Cike da tausayawa ya ce, "ki kwantar da hankalinki Balkisu, likita ya tabbatar min babu wani ciki a jikinki."
Wannan magana nasa ne ya kwantar min da hankalina ya samar min da natsuwar zuciya.
Kwanana hudu a kwance Al-husain ke jigila da dawainiya da ni shi kadai, ya yi da kudinsa ya yi da jikinsa, sai Dr wanda ya dauki nauyin kawo mana abinci daga gidansa kullum safe, rana da dare , ko Kare bai zo dubami daga gidan Mamman kura ba bare mutum........
[1/18, 12:39 PM] +234 803 069 9057: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 47*
A rana ta biyar Dr ya sallameni, bayan ya shimfid'a min dokoki, da abubuwan da zan kiyaye don gudun samun wata matsala.
Kaina ne ya 'kulle da jin irin jawaban da Dr ke min, Al-husain ya ce min Dr ya ce bani da ciki, yanzu ga Dr na min wasu irin maganganu da ba na wani fahimta sosai.
Har muka shiga mota nazarin maganganun Dr na ke yi, na yi nisa cikin tunani don banzan iya tantance a ina muke ba, tsayuwar motar ne ya sa na d'ago da kaina dake d'uke, ga mamkina ba gida muka iso ba, gefen hanya ce ya yi parking, kallon shi na yi, ya juyo ya fuskance ni sosai a nutse ya ce "Balkisu ki saurareni da kyau ki nutsu ki ba ni aron hankalinki za mu yi magana ne." Jin haka yasa na tattara duk wata nutsuwa da hankali da ke jikina na bayar gare shi, kamar yadda ya nema.
A nutse ya shiga warware min zare da abawa game da halin da nake ciki a yanzu.
Kaina ne ya shiga juyawa, duhu na neman mamaye ganina, jikina ya dauki rawa kamar mazari, na tabbata ba don a zaune nake ba babu abin da zai hanani fad'uwa, muryarsa na tsinta a kunnena yana fad'in "ki ambaci Allah Bakisu ki kira Ubangijinki" samun harshena na yi da maimaita Kalmar " Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!" Ban san iya tsawon lokacin da na d'auka a haka ba, kafin na yi 'karfin halin d'agowa na kalle shi ido cikin ido abin da bai ta6a faruwa a tsakaninmu ba tun haduwarmu, cikin rawar murya na fara cewa " Shin wani laifi na yi wa Ubangiji ne Yaya Husain? wannan jarabawar ta yi tsauri a gare ni bazan iya cinye ta ba, ya Ubangiji gara ka kashe ni kawai na huta." "Kul Balkisu! Ki dawo cikin hayyacinki, idan hankali ya gushe da hankali ake nemo shi,Ubangiji ba abin wasa bane, bazai ta6a daurawa bawa abin da bazai iya ba, ki yi maza- maza ki tuba gare shi." Kalaman da suka ratsa kunnena kenan wadanda suka yi saurin maidoni kan mizanin hankalina da ya gushe, da sauri na shiga furta "Astagfirulla! Allah na tuba Astagfirullah!! Allah ka yafe min." Sai lokacin hawaye suka samu damar fara kwaranya daga idanuwa.
Sai da ya bari na yi kuka na sosai na gaji na koma sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara rarrashina daga bisani ya daura sa yi min nasiha mai ratsa zuciya, wanda ya kashe dukkan wani laka dake jikina, ya nusar da ni yin imani da kowacce irin kaddarace ta tunkareni me kyau ko mara kyau matsawar ina son kasancewa cikakkiyar musulma mai cikakken imani, a karshe ya daura da tambayar "Shin kin amince za ki aureni Balkisu!"
Ummi ta kai karshen maganar tana mai ba hawayen da ke cike da kaurin idanunta daman silalowa kan fuskarta, tana mai tunano lokacin a ranta tare da hasko fuskar Al-husain d'inta a idanunta.
Da sauri Fatima ta tashi ta isa gareta ta fad'a jikinta tare da k'ara fashewa da wani sabon kukan da dama kan yi take.
Aliyu kam zamowa ya yi daga kan kujera ya zame hullan kan shi ya na kuka kashirban harda shesheka
Al'ameen kukan zuci ya ke yi wanda ya fi na zahiri ciwo.
Zame Fatima Ummi ta yi daga jikinta ta share hawaye da hijabin jikinta, ta ci gaba da cewa;
Ko mahaukaci ya san hallaci balle mai hankali, ta yaya zan iya kallon tsabar idon Yaya Husain in ce bazan auresa ba, sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, Mahaifiyarsa da kuma yan uwansa na ke tsoro, hakan yasa na yi shiru na kasa ba shi amsa, sai zuciya ta daketa faman luguden dakan uku-uku.
Ganin na yi shiru ban ba shi amsa ba ya yi murmushi ya ce "Shiru ma amsa ce Balkisu, nasan baza ki ni ba, kuma nasan abin da da ki ke ma tsoro, Dada da kuma yan uwana, wannan duk mai sauki ne da zaran mun yi aure zan dauke daga gidan gaba daya sai kin so zasu ganki, yanzu abin da nake so da ke, duk juyin duniya kar ki yarda ki furta cewa cikin jikinki ba nawa ba ne kamar yadda na sanar da su tun farko, da sauri na kalle shi , ya girgiza min kai ya ce " Hakan ma wani makami ne da zan yi gwagwarmayar yakin samun nasarar aurenmu, kuma ma banda abinki ba ni din ne uban shi ba, ko yana da wani uba bayan ni." Da sauri ta girgiza kai tare da cewa "Sunan ka fa Yaya Husain." Ya ce "Ban damu ba Balkisu, Ina son ki kuma zan iya bada rayuwata wajen kare taki rayuwar bama suna ba."
Daga haka bai sake ce min komai ba ya tada mota muka dauki hanyar gida.
Fadin irin gwagwarmayar da aka sha da Dada kafin ta barni na saka kafata cikin gidan da sunan ci gaba da zama bata lokaci , da kyar sai da Al-husain ya hadata da wani kawunta wanda shi kadai ya rage mata a iyaye, kuma shi kadai ta ke jin maganarsa sannan ta amince, amma fa babu tausayi babu saukakawa sai ma karin azabtarwa da tsamgwama.
A haka na ci gaba da rainon cikina da tallafawan Yaya Hussain, a bangare daya kuma soyayya na dad'a karfi tsaninmu a boye ta yadda muke jin baza mu iya rayuwar babu juna ba, idan na nuna damuwata akan yadda zamu samu damar yin aure, sai ya yi murmushi ya ce kar na damu ya gama shiri, haihuwata kawai ya ke jira.
Cikina ya shiga wata tara ya yi wani irin girma mai ban mamaki duk wani abu da ake tanada na taron Baby Al-hussain ya tanade shi, yadda yake son cikin nan bana tunanin yana son wani abu a duniya haka, cikin kwanakin ya shiga tashin hankali, damuwarsa yaya zamu yi idan nakuda ya taso min sanda baya gida ko cikin dare, idan ya fadi haka sai na yi murmushi na ce "Karka damu Yaya Hussain ka taya ni da addu'a in sha Allah zan haihu lafiya." Da ni da shi haka muka tashi tsaye da addu'a ba dare ba rana akan Allah ya sauke ni lafiya.
Allah maji rokon bawa wata ranar litinin bayan Al-hussain ya min sallama ya fita da zumar amso abu ya dawo, na haifi Fatima, wata irin haihuwa mai ban mamaki da al'ajabi, na shiga bandaki da niyyar yin fitsari marana ya kulle a wajen, ban tashi ba sai da na haihu.
Kukan jinjirar ya jawo hankalin mutanen gidan, amma tsabar bakar zuciya da tsana a cikinsu aka rasa wacce zata iya daidaida yanke cibiya balle daukarta, ina duke cikin jini rungume da babyna da ke ta rusa kuka, babu abin da nake sai hawaye da neman dauki daga Rabbis sawati wal ardi akan ya kawo min agaji.
Daya daga cikin matan makwafta mai suna Hajo ce ta shigo wajen Dada, ta tarad da abin da ke faruwa, dattijuwa ce mai hankali da wadataccen ilmin addinin islama, ita ce ta yanke cibin ta taimaka min na koma daki ta gyara ni sannan ta koma ta gyara bandaki.
A lokacin ne Al-hussain ya dawo, ya sha mamakin jin wai na haihu da sauri ya karaso d'akin da nake don gane wa idanunsa, sai da ya yi arba da jaririyar wacce a take ya rada mata suna Nana Fatima sannan ya yarda, ya rungumeta tsam a kirjin shi yana godewa Allah daya sauke ni lafiya.
Hajo ta fita da zumar hura wuta ta daura ruwan zafi don ta wanke jaririya Fatima da ke ta kuka amma Dada ta daka tsallen albarka ta ce ba da tukunyarta ba.
Wanna dalilin yasa Hajo ficewa da Fatima gidanta a cen ta yo mata wanka ta shiryata cikin kayan sanyi na jarirai mai kyau da tsada.
Ni kam wankan da ban samu yi ba kenan a gidan nan sai dare, don sai da Al-hussain ya sake hada Dada da wannan kawun nata yazo har gida ya mata tatas sannan ta yarda aka aza ruwan wankana a gidan..........
Ya naga bakwa comment ko dai mu ajiye labarin ne sai bayan sallah? Pls in ji ra'ayin ku akan hakan.
[1/18, 12:39 PM] +234 803 069 9057: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 48*
Washegari ma Baaba Hajo ce ta shigo da sasassafe ta d'aura ruwan zafi ta yi wa jaririya Fatima wanka ta shirya ta ta goya, sannan ta kwashe wani ruwan nima ta kai min toilet, ta na tsaye a kaina na yi wankan, duk abin da ban yi da kyau ba ta saka hannu ta gyara, sai da ta tabbatar mun yi tsab, sannan ta koma gidanta ta damo kunun kanwa ta kawo min ta tursasani na sha shi da zafi-zafi, da rana kuma ta tuko tuwo da miyar yauki ta kawo, haka ta yi ta hidima damu ba tare da gajiyawa ba, sai da ta yi mana wankan yamma ta tabbatar na ci abinci ta ajiye min duk wani abin da zan bukata sannan ta yi mana sallama wuraren karfe taran dare.
Har 'kasa Yaya Hussain ya zube ya na mata godiya, ta yi murmushi tare da cewa "ka tashi Al-hussain bana son haka, ai yi wa kai ne, dβa na kowa ne."
Har na kuma kwana na hantse babu d'aya daga cikin 'yan uwan Yaya Hussain da ya min barka bare na saka ran cewa zasu d'auki jaririyar, nan na kara tabbatar da cewa lallai ba karamin kiyayya suke yi mini ba.
Dattijuwar kirki Baaba Hajo ce ta yi ta kula da ni da jaririyata da zuciya d'aya tamkar yar da ta haifa da cikinta koma na ce fiye da haka, ranar da na cika sati d'aya da haihuwa Yaya Hussain ya siyo katon rago ya yiwa Fatima ha'ki'ka, ranar kuwa ya sha bala'i wajen Dada kamar zata yi hauka tsabar ba'kin ciki tsine mishi ne kawai ba ta yi ba.
Ranar da na cika kwana arba'in da haihuwa aka daura aurena da Yaya Hussain, lamarin da yazo mana a bazata daga ni amaryar har Dada da y'an uwan shi, tun zuwa na gidan ban ta6a ganin tashin hankalin daya kai na wannan rana ba, tsayawa baku labarin irin tashin hankalin da aka yi wanna ranar 6ata baki ne, tun haduwata da Husain, ban ta6a tunanin barinsa ba sai ranar.
A take a wajen Dada ta yi amfani da kambun ta na uwa ta saka ya rubuta min saki d'aya, ta kuma buga rantsuwa akan bazan sake kwana a cikin gidan nan ba, in dai ta haifu cikin uwarta da ubanta.
Ranar raina ya baci zuciyata ta yi mini kuncin da bata ta6a yi ba, ban ta6a jin tsanar wani mahaluki a zuciyata ba irin yadda na ji tsanar Dada da 'ya'yanta a ranar, ina kuka na goya Fatima na kama hannun Al'ameen idanuna ko gani sosai basa yi na kama haryar barin gidan, ina ji Yaya Hussain yana kuka tare da kirana amma na kasa juyawa in kalle shi, haka na saka kai na bar gidan ba tare da nasan in da zan doso ba.
Tafiya kawai na ke yi cikin karfin hali da dakewar zuciya, idanuna a bude amma sam bana ganin gabana, saka kafa kawai na ke yi duk in da na samu ba tare da kula ko kiyayewa ba, a wannan lokacin zuciyata ta kekashe idanunawa sun bushe, dan ragowar burbushin hankalin da ke tare dani na neman gushewa, ina ji a raina dama Allah bai halicceni a duniya ba, ina ji kamar na kashe kaina na huta, sautin muryar Yaya Hussain a lokacin da yake kirana cikin kuka da kururuwa ne kawai ke amsa kuwwa a kunne na,
Al'ameen sai kuka yake haka ma Fatima, yaran kamar sun san abin da ke faruwa.
Na yi nisa sosai da tafiya, ina daf da shnaye kwanar gidan na hau babban titi, na jiyo muryar Baaba Hajo a bayana tana kirana, a duniyata bayan Yaya Hussain Baaba Hajo ce mutum na biyu da nake mutuntawa sama da kaina, dakatawa na yi ta karaso gabana da sassarfa idanunta jajur alamar ta sha kuka, muna hada ido na ji wani rauni ya lulle6e ni, sai kawai na saki hannun Al'ameen na fada jikinta na kamkameta tare da fashewa da wani irin kuka.
Bata dakatar da ni ba, domin ita kanta hawaye take yi, ganin mutane da basa raina abin kallo sun fara taruwa yasa ta yi karfin halin zare jikinta daga nawa, ta dauki Al'ameen ba tare da ta iya ce mini komai ba ta kama hannuna ta fara jana tamkar rakumi da akala.
A cikin d'akinta ta yi mana masauki, raba dare muka yi tana faman aikin rarrashina da bani baki akan na yi hakuri na rungumi kaddrata da hannu bibbiyu shine cikar imanina,bayan ta baiwa Al'ameen tuwo ya ci tuni ya yi barci.
Kwanana uku a gidan Baaba Hajo na kasa daina kuka, har sai da tayi fushi ta yi mini fada tare da nuna mini bacin ranta san nan na fara daurewa na daina yi a gabanta sai dai idan na shiga ban d'aki, na yi mai isata, Yaya Hussain shine rauni na, bansan wani hali yake ciki ba, nasan duk in da yake yana cikin halin matsanaciyar damuwa ina jin hakan a jikina.
Gutsiri tsoma ya barke tsakanin mutanen unguwa, wasu na ganin watau Baaba Hajo data taimakeni suna zaginta yayinda wasu ke shi mata albarka tare da jinjina mata.
Sati na biyu a gidan amma ban taba leka ko zauren gidan bane, sai dai zuwa lokacin na yi tawakkali na mikawa Ubangiji dukkan lamurana na dage da addu'a babu dare ba rana, sai dai har zuwa lokacin na kasa daina kukan rashin Yaya Hussain.
Ranar da na cika sati uku da yammaci
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 22