nake ga kar yaga kamar na cika gajen hakuri." Zainabu ta ce "Bana ganin zai ce haka a yadda kike dan bani labarin halayensa, ni nama fi zargin mantawa yayi."
Amira ta ce " to shikenan yau zan mata gamana sai mu ji mai zai ce, amma wallahi ni kunyar sa nake."Tsaki zainabu tayi ta ce "wannan kunyar naki wallahi shi zai kasheki Amira." "Hmmmm wallahi kawa dan dai baki san shi a zahiri bane, kamar zaki haka ya ke da kwarjini bashi da wasa baya daukar wargi at all.".............
Ga masu bukatar shiga group
09116099486
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
*PAGE 16*
Da gudu ta k'arasa d'akinta ta fad'a kan bed d'inta tana sakin wani irin numfashi mai zafi, can kuma sai ga hawaye shaaa! kamar an bud'e famfo, wani irin tafarfasa zuciyar ta ke mata. Yanzu shikenan Mom ta yaga mata wasikarta, shikenan Mom ta rabata da letter n ta, ji take kamar wani part na jikinta aka yaga mata ba fallen takarda ba, tana jin son latter n nan sosai a ranta shi kadai me debe mata kewar Teeteenta. Ranta ya matukar baci da abin da Mom ta mata yau, tun da take bata ta6a ja'inja da ita ba amma wannan karon ta lashi takobin ko zata yanka ta baza ta bi ta Oshogbo ba suna tsaka da shirin fara text, Ai ba dole ba ne sai anyi tafiyar da ita, zabura tayi ta mi'ke tare da d'auko wayar ta dake yashe kan madubi, bata damu da waya ba don sai tayi sati bata ta6a wayar ba musamman idan Papa yana gari, idan baya nan dai dama kullum da safe zai kiranta ya ji lafiyarta ko ita ta kira shi.
Lambar Papa da tayi saving da My blood ta laluba ta dannawa kira, lucky ringing biyu ya d'aga, ta na jin muryar shi ya ce "He'll my lovely princess my Joy." Ta daddage ta fashe da wani irin kuka mai k'arfin gaske, kamar yadda ta tsammata a rud'e ya shiga tambayar ta "Menene ? Mekefaruwa ? waya ta6aki? Kina ina ne yanzu? Ina Mom dinki?" Babu d'aya data amsa sai ma k'ara sautin kukanta da tayi, aikuwa Papa dake zaune a office d'in abokin shi Mr Jack dake kasar Canada ya mike tsaye, ya shiga safa da marwa yana mata magiyar ta yi shiru ta daina kuka haka, sai da ta bari ta gama rud'ashi sannan cikin wani irin shagwabebben muryar mai hade da shesshek'a ta ce "Papa Mom ne." Wani irin kankance idanu yayi don bai ta6a tsammanin Mom ce ta saka mishi tilon yar shi irin wannan kukan ba, tausasa murya yayi dan kar ya kara daga mata hankali ya ce "Mom din ki kuma? Me tayi miki." Sai da ta gama jan majina ta ce "Ta ce wai gobe in shirya muje Oshogbo kuma On Monday zamu fara test." Cikin danne bacin ranshi ya ce "Ki ce mata bazan kije ba." "Na ce mata ta ce wai ban isa ba." Zazaafar huci ya fesar ya ce j "Ok haka ta ce, To ki kwantar da hankalin ki ni nace baza ki je ba, yanzu dai ki share min hawayen ki bari na kira Mom din naki muyi magana." Ta amsa da "Toh Papa." Tana share hawaye.
Bayan ficewar Joy daga garden da wani irin mugun harara Mom ta raka bayanta, a bayyane ta ce "Ya zama dole mu tafi Oshogbo tare gobe goben nan kamar yadda bokanta ya umarta bazan yi sakacin da aikina na shekara goma sha biyar zai lalace ba, zan Iya kawar da duk wanda ya ce zai min shamaki da wannan burina kowaye, Ta karashe maganar tana huci kamar kububuwa. Daga haka kuma tabi bayan fuuuu Joy, sai dai kuma kafin kai ga karasawa dakin Joy wayar ta ya dauki ruri, ganin lambar Papa yasa gabanta faduwa kar dai ace yarinyar nan ta kira Mr James ne, shaf ta manta da hakan da kwace phone din ta, dakewa tayi ta daga cikin kissa ta ce"He'll My O..... Kafin ta kai ga karashe maganar ta ya dakatar da ita ta hanyar ce wa "Alice!!!!!" A tsawa ce. Diriricewa ta yi don tsawar ya shigeta, don bata ta6a tsammanin hakan ba,Rabon da ya mata irin wannan tsawar tun kafin su dawo Niger state da zama, kafin ta dawo hayyacinta ya rude da fada akan me zata saka mishi d'iya kuka Akan me zata tilasta ui. Abinda bata so, sai da ya.mata tatass ba tare da ya bata damar amsawa ba ya daura da kuma "Ban amince miki ki fita ko bakin get da ita ba, ki je duk inda zaki je na lamince miki amma ban amince ki tafi min da Y'ata ba wannan umarni nake baki, idan kuma kika ki ji." Ya yi kwata! Bai jira cewar ta ya katse kiran, ya sake kiran Joy ya ci gaba da rarrashinta.
Daskarewa Mom tayi a tsaye a inda take, tana zazzaro idanu hankalinta a kololuwar tashe, kar dai a ce aikin da ta sha bakar wuya aka yi mata akan Mr James lalace, tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, hannu na rawa ta lalubi lambar bokonta Kubal. ta danna mishi kira, cikin sa'a ya daga muryar na rawa ta shiga kwashe abin daya faru tana zayyana mai, tsawa ya faka mata shima , a kausashe ya ce "Na gaya miki matukar baza ki rabata da wad'an nan ahlin ba ba kiga komai ba, duk wani abu da kika binne ina mai tabbatar miki sai ya tonu." Hankali ta she Ta ce "Na rabata da su Kubal duk wani tsaro da takumkumi na saka mata, na shata babbar layi a tsakanin su." Dariya ya kece da shi mai ban tsoro lokaci daya ya gimtse sannan ya daura da "Wannan bai isa ya raba alakar jini da jini ba, kizo da ita garemu kizo da ita garemu kizo da ita garemu zamu rabasu rabuwa ta har abada." Ta ce "Mr James ya hana kubal. ka taimakeni bana son na rasa aurena ba tare da ba samu ci kar burina ba, ka taimakeni da kai kadai na dogara, tsoro nake ji kar Mr James ya rabu da ni." Boka Kubal ya a tswace ce "ki taho ke kadai da gaggawa, zamu canza kalar aikin namu, ki taho da gaggawa." Ka fin ta bashi amsa tuni ya yanke kiran.
A gurin ta zube ta daura hannu akai, ta san idan har asirin data ma Mr James tsohon shekara sha biyar ne ya karye kashinta ya bushe tabbass kashinta ya bushe, bata ga ta zama ba, idan ba haka ba ta tabbata zata kare rayuwarta a prison madadin ta zama daya daga cikin matan da suka yi ficce suka shahara a duniya kamar yadda take buri, zabura tayi kamar zautacciya ta bar gurin a guje, dakin ta ta shiga ta fara hada kayanta.
Ranar daga ita har Joy basu samu barci mai kyau ba, Joy kukan bakin cikin rabata da letter n ta, ta kwana yi, yayinda Mom tsananin tashin hankali ya hanata rintsawa.
********
Kamar yadda suka tsara da Zainabu hakan ce ta kasance, washe gari kamar yadda ta saba ta shiga wajen Ummi bayan ta tabbatar Al'ameen ya fita, a tsakar gida ta samu Fatima na wanke wanke Ummi na daki, dakin ta nifa ta durkusa har kasa ta gaida Ummi cike da lababi,cikin fara'a Ummi ta amsa tana saka mata albarka daga haka ya fito ta saka hannu tana taya Fatima dauraya suna hira, cikin hiran Amira ta ce "Wai ni kam Fatima Yaya Ameen na nan kuwa." Fatima ta ce "Yana nan mana yanzu bai dade da fita ba." Amira ta ce "Ikon Allah wallahi na kwana biyu ban gansa bane, duk zato na yayi tafiya ne ." Fatima ta ce "A'a yana nan wallahi." Shiru Amira ta dan yi can kuma ta ce "To kodai ya manta ne?" Fatima ta kalleta cikin rashin fahimta ta ce "Ban gane ba Anty Amira." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wallahi rannan nan mama ta saka na tambaye, wai ko na kawa past question na waec ya dinga koyamin kafin namu jarabawar ya kara so, ya amsa min da to zai ne me ni idan ya shirya amma na ji shi har yanzu shiri shi yasa nayi yunanin ko yayi tafiya ne, Ashe yana nan, shine nake tunanin ko ya manta ne." Fatima ta ce "abin ya kai kwana nawa yanzu." "Ummm! Ina ga yafi sati fa." Cewar Amira, "kai anya kuwa! Yayana bai cika mantuwa haka ba, amma dai ki kara tuna ma shi kiji, zai Iya yuwuwa mantawar yayi" marairai ce murya Amira ta yi ta ce "Fatima dan Allah ki taimake ni ki tuna mishi yau idan ya dawo." "To me zan ce ma shi?" "Ki ce Yaya Anty Amira ta ce wai ya maganar da kuka yi ran nan na karatu. Haka kawai zaki ce masa nasan zai tuna." Fatima ta ce "to shikenan in sha Allah idan ya dawo yau zan dasa masa."
Haka ko akayi a ranar da dare bayan Al'ameen ya dawo suna zaune a tsakar gida kamar yadda suka saba, Fatima ta ce "Yawwa Yaya Anty Amira ta ce wai na tuna maka ya maganar da kuka yi ran nan na karatu, wai har yanzu ta ji shiru daga gareka." Dan ya mutsa fuska yayi, jin abinda Fatima ke fada, sarai yana sane da ita shareware yayi don shi a halin yanzu yana tsoron kebewa da wata mace wacce ba muharramarsa ba, bai manta da abin daya faru ranar da tazo tambayarsa ba, common turarenta na neman zamar masa masifa. Ummi kam jin an ambaci Amira, tuni ta maido hankalinta Kansu ta ce "Binta me ya samu Amiran?" Fatima ta ce "A'a Ummi babu komai, ta aikoni wajen Yaya ne akan maganar da suka yi da shi, wai ta tambaye shi zai koya mata karatun jarabawan su dake gabatowa, ya e mata to zai neme ta amma yau kusan sati bata ji daga gareshi ba, shine ta ce idan ya dawo na tuna masa." Kallon Al'ameen Ummi tayi dai dai shima ya kallota suka hada idanu, da sauri ya sauke kai. Ta ce "Yayan Fatima idan da hali ka koya mata dan Allah, Amira yarinyar kirki ce." Shiru yayi kadan kafin ya amsa da "Toh Ummi." Sannan ya dago ya kalli Fatima ya ce "Fatima ki CE mata gobe idan na dawo da daddare tazo sai mu fara karatun." Yana kallon Ummi ta gefen ido yadda fuskarta ta yalwatu da fara'a. Fatima ma taji dadi don ba karya tana son Amira kamar dai Ummi.
*******
Washegari Sunday da sassafe Mom ta fito da trolley dinta, cikin shirinta na tafiya, sai da ta daidaita komai batta driven da zai kaita airport yana zaune a mota yana jiranta sannan ta nufi dakin Joy, tura kofar tayi da karfi, taga ya bude, bata zaci a bude kofar ya ke ba, shiga ta yi, a kwance ta sameta idanunta a rintse kamar mai barci sai dai ba barcin take yi ba, hasalima jin motsin mom din ne ya saka ta rintse idanu, tsayawa a kanta Mom ta yi ta kare mata kallo, sai da tayi mai isarta, sannan ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce "Daughter zan wu ce." Sai lokacin Joy ta bude kumburarrun idanunta amma bata ce komai ba, Mom ta sake cewa "Ba yan school ban lamunce miki zuwa ko ina ba, zuwa anjima Madame Esther zata zo ta zauna dake kafin na dawo." Daga haka ta juya ta fice Joy ta rakata da kallo.
Bani da isasshen lahiya banyi editingπ
Ga masu bukatar shiga group Ku tuntubeni.
9116099486
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 17*
Tana tsaye jikin windon d'akita tana kallo har motar Mom ya bar compound d'in gidan, ko kad'an bata ji wani damuwa ko alamar kewa a zuciyarta game da tafiyar Mom ba , sabanin hakan sai ma wani irin sanyi da farin ciki ta ji yana huda zuciyarta, wani tsalle ta daka tare da fad'awa kan tattausar katifarta, yau jin ta take yi kamar sakakkiyar tsuntsuwa, rasa irin murnar da zata yi yasa ta ci gaba da jumping akan bed d'in tana tambul da adungure, sai da ta ji ta fara gajiya ta dakata tana sauke numfashi, bayan ta dan huta daga tsalle tsallen murnanta, ta mik'e ta fad'a toilet ta shek'a wanka, tana yi tana wake wakenta alamar cikin farin ciki take, gaban mirror ta tsaya daure da mini tawul, tana kallon fuskarta, Zum6ura baki tayi ta kwa6e fuska, bayyane ta ce "Ji duk yadda nayi baki kamar bani ba, duk Mom ta gama ramar dani da jidalinta." Kwafa ta yi ta harari mirron kamar dai Mom d'in na cikin madubin ne, kallon kayan kwalliyar dake shake kan mirron tayi sai kuma ta saki murmushi ta ce "Bari nayi wa My Teemah kwalliya." Kujera ta ja ta zauna, cikin gwanancewa ta shiga fesa kwalliya a kwakkwayar doguwar fuskarta.
Bata cika yin makeup ba, shi yasa duk sanda tayi yake zama special a fuskarta, lallausar gashinta ta tattara tayi paking din shi gefe ta zubo da jelar ta gaba har kafad'unta, ta yi kyau sosai matuk'a gaya kamar wata y'ar tsanar roba. Mik'ewa tayi ta isa gaban wardrobe din ta ta wangale kofofin shi, tsayawa tayi tana kallon kayyayyakin ciki, kaya ne shake a ciki ba na wasa ba, wasu ma batta taba sakawa ba sai dai duk kanana ne babu wani na mutunci a ciki, idanuta ne sauke akan wani kaya da Papa ya taba kawo mata daga America lokacin da yayi wani tafiya, kaya ne masu matukar kyau da tsada irin ta yayan masu jajayen kunnuwa, bata taba sakawa tunda ya bata ta jera su a sif, zarowa ta yi ta warware kayan. Straight skirt ne mai dauke da dogon tsagu ta baya red colour da riga karami mai hannun bes White colour mai V neck a gaban rigar an rubuta JOY cikin wani irin design mai kayatarwa ya sha stone sai walwali yake, sai dan karamin jaket kalar skirt din, iyakar shi kasan boobs yana da igiya daga kasa da za'a d'aure ta gaban.
A tsanake ta shirya cikin kayan tsab! Duk da kasancewarta bera dan yanzu take shiga sha biyar hakan bai hana kyakkyawan surarta kayatuwa cikin shigar ba, siririyace sosai sai tsayi, sai dai akwaita da faffadan gudu, hakan yasa take da shape kayatacce, idan ka dauke hakan babu wani abu jan hankali a jikinta, dan y'an boobs dinta basu fi girman lemon tsami ba samsam basu da girma shiyasa bata fara saka bra ba.
Takalmi half cover ta saka fari ta daura agogo a tsinstiyar hannunta, daga haka ta fito daga d'akin ta da sauri har tana had'awa da d'an gudu, direct get ta nufa ko tsayawa ta yi breakfasts ta kasa, sai dai tana isowa, d'aya daga cikin security d'in dake bakin get, ya ce "Miss kiyi hakuri madam ta ce kar a bari ki fita, in dai ba school zakije ba." Bata san lokacin da ta kwaso wani irin mugun kallo ta watsa mashi ba, take ta fusata kasancewarta dama gwanar saurin fushi babu wuya ta hassala sai sai tana da saurin sauka. A tsiwace cike da gadara ta ce "Na ce Ku bud'e min get zan fita." K'asa yayi da kai ya ce "I'm sorry Miss sai dai Ki kira madam ki sanar mata." A tsawace ta ce "Bazan kirata ba! kuma ina umartanka da ka bud'e min get kokuma yanzu wallahi a bakin aikin ka." Tsorata yayi ganin yadda ta ke huci yar karamar yarinya da masifa kamar wata babba, shikam bazai so abinda zai raba shi da wannan aikin daya samu mai maik'o ba, jiki na rawa ya shiga bata hakuri, ko kallon banza bai isheta ba, dsauri ya bud'e mata karamin kofar yana mata a dawo lafiya tana fita ya lalubi lamabr Mom don ya sanar mata, sai dai wayar tak'i shiga kasancewar jirgin su ya riga ya lula.
Sai da ta fito gida sannan, ta ji wani tsoro na shirin kamata sabanin da da take cikin farin ciki, da wani ido zata kalli Fatima, da Ummi, uwa uba Yaya Al.......kasa karasa tunanin tayi don bata fatan hakan takasance fatan ta Allah yasa zuwa yanzu baya gida, duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta yi, karfe goma har ta gota, ta tabbata zuwa yanzu ya fita, dakewa tayi ta ci gaba da tafiya.
Tana kusantar gidan gabanta na faduwa, duk taku daya karfin bugun zuciyarta na karuwa, sanda ta fara hango gidan ji tayi kamar ta koma saboda yadda zuciyar ta ke luguden daka kamar zai fado kasa, ita kanta baza ta ce ga dalili ba, ta san dai ba tsoron Fatima ta ke yi ba, haka Ummi akwai kyakkyawar alaka ta mutunci a tsakanin su, dakewa tayi ta karasa kofar gidan, babu kowa a layin kasancewar shi karamin layi.
A hankali ta tura kofar gidan ta shiga da sand'a kamar barauniya, a haka ta wuce kofar dakin Al'ameen ta isa kofar shiga cikin gida, la6ewa ta yi jikin bango ta kasa shiga, can ta jiyo muryar kamar na Fatima tana magana hakan yasa ta leka kanta a hankali.
Al'ameen na tsaye a bakin kofar dakin shi cikin shirin shi na fita ya na makala links a hannun rigar shi, ya ji an turo kofar gidan, shiru shiru ba'a shigo ba, ba, a koma ba hakan yasa ya dago kai ya kallo waje ta raga ragar net door din dakin shi, mamaki ne ya kusa kashe shi lokacin da idanunshi ya sauka a kanta tana tafiya cikin sand'a kamar wacce ta shigo sata, kwafa yayi a ranshi lallai yarinyar nan, uwar me ta zo yi gidan su bayan irin wulakancin da sukayi wa Fatima, kamar zai dakatar da ita sai kuma ya dakata yaga Iya rashin kunyar ta, yana kallo ta la6e a jikin bango ta lek'a kai cikin gidan.
Shiru shiru bata d'ago ba hakan yasa Al'ameen yin gyaran muryar daga bayanta, kiriss! Ya rage ta saki fitsari lokacin da sautin muryar shi ya ratsa dodon kunnenta, da sauri ta d'ago kai ta zubawa kofar dakin shi idanu batta hango shi saboda duhun net amma shi yana iya ganinta.
Bud'e net door d'in yayi ya fito fuskar shi a had'e kamar hadarin gabas, Sai lokacin ya samu damar ganinta da kyau, wani irin wulakantaccen kallo ya shiga wurga mata ganin irin dressing d'in dake jikinta a rayuwarshi ya tsani yaga mace da shigar banza koda kuwa arniya.
Shesshekar kukanta da ya ji yasa ya kai kallon shi ga fuskarta, zaraf idaunsu ya sarke dana juna, a tare zuciyoyinsu ya yi wani irin girgiza, bude baki ta yi da nufin yin magana, da sauri ya daura hannunta shi akan leben shi ya ce mata "Shiiiii!!!." Tsit! tayi tare da hadiye shesshekanta tana wurwurga manyan idanunta da suka kada saboda tsorata.
Ya sake yi mata alamar ta zo ta fice da hannu, baya son ya yi magana ne don yasan su Ummi na tsakar gida zasu jiyo su.
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta fara takowa, ta gaban shi ta bi ta fice daga zauren, minti biyar ya dauka kafin bayanta yabi bayanta, tunanin shi zuwa lokacin ta dan yi nisa da gidan, sai dai ga mamakin shi yana fitowa, ya tarar da ita durkushe a kofar gidan tana sharar kwalla, ranshi yaji yayi mugun baci, wato bata tafi ba kenan don rainin hankali, a hasale ya daka mata tsawa " keeee!" A zarane ta dago ta watsa mai idanunta da suka fara sauya launi, take ya ji duk wani karsashinsa ya tafi, kasancewar sa dakkaken namiji mai dakakkiyar zuciya yasa ya dake ya ce "Me ya kawo ki gidanmu." Shiru ba amsa sai sabbin hawaye dake sake shatata akan dakalin fuskarta, ya ce "Ok na gane yau ma kin biyota har gida ne ki sake ci mata mutunci kamar yadda rannan kuka ci mata matunci a gidan Ku keda mahaifiyar ki ko?" Da sauri ta shiga girgiza kai cikin shirin fashewa da kuka, ya ce "Kul! Kar ki min kuka a nan. Kuma ki bud'e kunnuwar ki da kyau ki saurereni, daga yau sai yau idan na sake ganin wadan nan kazaman kafafunta naki a gidan nan, hmmmm! Sai na lahira ya ciki jin dadi. Oya kafin in bude idanuna ki 6ace daga kofar gidan nan, daga yau babu ke babu Fatima har abada." Rushewa ta yi da kukan da take ta kokarin rikewa tun dazu, cikin magagi ta ce "Pls Yaya Alemin karka raba ni da Fatima wallahi ba laifi na bane laifin Mom dina ne idan ka raba mu, zan shiga tasananin damuwa ku yi hakuri da abinda ya faru rannan Ku yafe min." Ya ce "Ok baza ki tafi ba ko? Ina zuwa." Ya fad'a yana shirin juyawa zuwa cikin Zaure, caraf ya ji ta riko kafafun shi, wani irin shock ya ji a jikin shi wanda tunda yake bai taba jin irin shi ba, hakan yasa yayi wani irin fusgar k'afunshi da mugun karfi, har saida Joy ta fad'i tare da bige goshi da wani dutse.............
Na gode da addu'o inku gareni, na j sauki sosai hannu ma da sauki alhmdllh ngd kwarai da kulawa.
Me bukatar shiga group din joy ya tuntubeni ta wannan Layin.
09116099486.
[12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: ππ *JOY* ππ
~FARHAT~
*PAGE 18*
Yauma ba editing a tai ta hakuriπ
Ba tare da ya kula da fad'uwar da tayi ba ya shige zaure da sauri ya bugo k'ofa. Zafin buguwar da taji yasa ta saki yar k'ara "Acchh!" da siririyar muryarta , hannu ta kai ta dafe goshinta dai dai gurin da ta bige, danshi da ta ji a wajen yasa ta dubawa da sauri, zaro ido tayi a tsorace ta ce "Jini! wayyo my Dad." Sai kuma ta fashe da kuka tana yarfa hannaye, rabon da jini ya fita a jikinta irin haka har ta manta, ji tayi ranta ya mugun baci da abinda Al'ameen ya mata sosai ta kullace shi, dama tun farko bata ta6a mishi kallon mai saukin kai ba, kallon wani irin murd'add'en mutum mugu mara fara'a take mishi, sai gashi yau ya tabbatar mata da hakan, mikewa tayi ta kakkab'e jikinta ta na hawaye ta kama hanyar barin kofar gidan.
Duk abin da take yi yana tsaye daga cikin duhun zaure yana kallo, ji yayi zuciyar shi ya sosu, haka kurum kukanta ke ta6a mishi zuciya, irin abinda yake ji a duk sanda ya ji Fatima na kuka ya dinga ji, gaba d'aya tausayinta ya ji ya kama shi, idan ya barta ta fice haka, anya ya kyauta kuwa, Annbin Rahama ya hane mu rama sharri da sharri, ya gamsu da irin soyayyar da ta ke yiwa yar uwar shi kodan wannan ya kamata ya raga mata, da sauri ya fito ya biyo bayanta, lokacin har ta riga ta bar kwanar gidan, sunanta yake son ya kira amma ya kasa, sau uku yana gwada bude baki sai dai ya mayar ya rufe, hakan yasa ya k'arasa da dan gudu gudu ya isa gareta, jin karan gudu daga bayanta yasa ta juyowa da sauri har zuwa lokacin kuka take, daai dai nan shi kuma ya iso inda take, kasancewar tana cike da haushin sa yasa ko d'ar bata ji ba sai dai ta kasa kallon fuskar shi ko da gigin wasa, a gabanta ya tsaya sai kuma ya rasa me zai ce mata, samun kanshi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 22