Share this page
ciki, duk da haka ta kasa kallon shi cikin ido , sai Aliyu ta kalla ta ce "Barkan mu da yamma." Kamar yadda shi take kallo take magana haka zalika shi ya amsa mata da cewa "Yawwa barkan ki dai." Ta ce "Sunana Zainabu, kaqar Amira, idan babu damuwa ina son yin magana da Al'ameen." Sai lokacin ya sake kai kallonsa gareta gabansa ne ya shiga faduwa jin ta ambaci Amira, kallon shi Aliyu ya yi, yana jira ya ji ta bakin shi, ganin bai tanka ba yasa ya ce "Bismillah! Yana saurarenki bari na baku wuri" ya fada yana kokarin mikewa, da sauri Zainabu ta ce "A'a ka zauna zan yi maganar a gabanka ka zama sheda don naga kamar kai abokin shi ne." Ya ce "Ya ce OK to shikenan." Shiru ta yi na yan sakanni kafin ta yi karfin halin d'agowa ta sauke kallon ta a kan shi shima ita yake kallo har lokacin ta ce, "Shin kasan cewa wannan ciwon da amira ke yi ciwon sonka ke ne? Kasan cewa idan ba ka kawo dauki gaggawa a gareta ba tabbas soyyarka zata zama ajalinta? Nasan duk baka sani ba, to yanzu na sanar maka, Wallahi Al'ameen idan ka rasa Amira ka yi asarar masoyiya, ka dubi girman Allah ka amshi soyayyar ta kodon ceton rai, wallahi muna gaf da rasata kuma idan ka bari hakan ta kasance sai munyi Sharia da kai a kotun Allah." Ta karashe maganar tare da fashewa da matsancin kuka, kasa tsaywa ta yi da gudu ta bar wajen ta shige gidan su Amira, Fatima da ta yi suman tsaye ne tun da ta kunnayenta suka jiyo mata maganganun Zainabu ta fito zata shige gida ne, ta karaso gaba su da sauri cikin kidima da rawar muryar ta ce "Ya Yaya da gaske ne ciwon soyayarka ne ya mai kwantar da Anty Amira? " Kallon ta yake yi kamar mutum mutumi ya kasa koda gyada kai ne, hawaye ne suka Shiga gudu a fuskarta, da sauri ta mike tana girgiza kai sani kuma ta juya da gudu ta shige gida tana kwala kiran sunan Ummi, sai lokacin ya Ankara da tashin ta "Fatimahhhh!" Ya kwala mata kira amma ina! Tuni ta shige "Innalillahi wa inna ilaihinr rajiun." Ya fada yana dafe kanshi dake Sara mishi kamar zai rabe biyu.......... 09116099486. [12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€ ~FARHAT~ *PAGE 32* Tana kaiwa dai dai tsakiyar zauren gidansu ta jiyo muryar shi cikin wani irin sauti kwala kiran sunanta, cak! Ta tsaya ta kasa ci gaba da gudun, sai dai kuma ta kasa dawowa gare shi, sai samun kanta tayi da durkushewa a zauren ta sake fashewa da wani irin kuka mara amon sauti, kukan tausayin Amira, dama ta dad'e tana zargin wani abu a tattare da Amira game da Yayanta sai dai bata ta6a tunanin lamarin har ya kai haka ba, take ranar da ta ga Amira ta fito daga d'akin Al'ameen tana kuka ya shiga dawo mata. A can kofar gida kuwa, dafa kafad'ar shi Aliyu ya yi, a hankali ya d'ago kaifafun idanunsa da lokaci guda su ka canza launi ya watsa ma shi,kallon cikin idanun juna su ka yi na y'an sakanni, Kafin Aliyu ya lumshe ido ya bud'e tare da cewa a sanyaye "It's time 4 prayer, muje masallaci." Bai amsa shi ba, don baya jin zai iya bud'e baki ya yi magana, mik'ewa ya yi jikinsa a matuk'ar sanyaye, su ka nufi masallacin kusa da gidan. Bayan sun idar da sallah, hannaye Al'ameen ya d'aga sama ya shiga kai kukan shi ga mahalici, ya dad'a yana kwararo addu'o'i har sai da kusan kowa ya watse a masallacin, bai sauke hannayensa ba. Aliyu na daga gefen shi yana amsawa da amin duk da ba jin abin da yake fad'a yake yi ba don a zuciya yake yi. A tare suka shafa addu'ar, shi ya fara mik'ewa ganin haka yasa Aliyu ya biyo bayan shi. Tafiya suke yi a jere sai dai babu wanda ya ce wa d'an uwansa kanzil, daurewa kawai Aliyu yake yi ya hana kansa magantuwa ganin halin da abokin nasa ke ciki, amma bakinsa fal! yake da tarin tambayoyi, Kansa gaba d'aya a k'ulle ya ke. Mazaunin su na da suka koma suka zauna, shiru ne ya gifta a tsakanin na wasu mintuna, Aliyu dauriyarsa ya k'are don gabansa fad'uwa kawai yake, har ya bud'e baki da nufin magantuwa, Ya tsinkayi muryar Al'ameen cikin wani irin amo mai nuni da cewar tabbas maganar da zai fad'a mai girma ce, ya ce"Aliyu! Banda Allah mahaliccina, bayan ni kaina da kuma likitan daya d'aurani a kan magani, Kai ne mutum na uku da na za6a kasan sirrina, hakan kuma zai faru ne saboda na yarda da kai, na dauke ka d'an uwa amini abokin kuka wanda hausawa kan ce ba'a boye masa mutuwa." Gyada kai Aliyu ya yi cike da gamsuwa da bayanansa, shiru Al'ameen ya yi na wani dan lokaci, kafin daga bisani ya sauke kakkarfar ajiyar zuciya a hankali ya bud'e baki tiryan-tiryan ya shiga bawa Aliyu labarin ciwonsa tun daga lokacin daya fara fuskantan matsalar har zuwa kan yanzu da larurar ke mataki na biyar a jikinsa. Dagowa Ali ya yi idanunsa jajur yace "Wacece Amira? Menene alakar ka da ita." Nan ma bai yi k'asa a gwiwa ba wajen zayyanewa Aliyu wacece Amira da alak'arsu tun daga farko har zuwa yau , ya daura da cewa "Aliyu ban sani ba cewa akan soyayyata ne ta ke wannan ciwon, ban yi zaton lamarin ya kai girman haka ba, abin da na sani kawai bana son ta." Shiru ne ya biyo baya, gaba d'aya jikin Aliyu ya yi la'asar, lamarin ya sosa ransa fiye da zaton mai zato, gaba d'aya tausayin Al'ameen da ahlinsa harma da Amira ya gama cika masa zuciya, a iya hasashensa babu wata mafita data wuce wacce Dr Abdul ya fad'a, to amma ta yaya hakan zai kasance. Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya d'ago ya ce "Abokina na tausaya maka kwarai, sai dai naga zallar wautarka, shin me yasa ka za6i ka kassara rayuwarka akan ka yi Aure, kula da Ummi da Fatima kadai bai isa hujja ba, ka gwammace ka mutu a tsaye a kan ka yara sunnar ma'aiki, wallahi na tabbata idan Ummi ta ji wannan maganar sai ta zubar da hawayen bakin ciki da takaici, kana fa da ilmin addini daidai gwargwado, kana da tabbacin zaka iya rike kanka har zuwa lokacin da ka yanke wa kan ka yin aure, kana da tabbacin kwayoyin maganin da kake sha zasu ci gaba da rike ka har zuwa lokacin da ka d'ibarwa kan ka?" Girgiza kai Al'ameen ya yi ya ce "Ba ni da tabbas abokina yanzu menene mafita." Aliyu ya ce "Da gaske ka dauke ni amini abokin shawara kamar yadda ka fada?" Gyada mashi kai Al'ameen ya yi ba tare da ya iya bud'e baki ya amsa shi ba, "To mafita shi ne ka jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya." " Kamar yaya?" Ya tambaya cikin rashin fahimtar inda maganar Aliyu ya nufa, kallon shi ciki ido ya yi ya ce "Ka Auri Amira." "Na auri Amira?" Ya maimaita maganar cikin sigar tambaya, Aliyu ya ce "E ." girgiza kai ya yi ya ce "Bazan iya ba zan dai taimaka mata ta wata hanyar." A harzuk'e Aliyu ya ce "Ya zama dole ka iya, dole ka auri yarinyar nan Ameen." "Akan me zan aureta ba bayan bana son ta, ita fa zuciya ba a yi mata tilas." Ya amsawa Aliyu shima a fusace, mikewa Aliyu ya yi ya ce "Na sani Ameen zuciya ba'ayi mata tilas, amma ka sani a wannan ga6ar ba maganar so ko kiyayya ake yi ba, magana ake ta ceton rai da rai " Yana gama fad'in haka ya juya ya kama tafiya ba tare da ya sake kallon Al'ameen ba. Da kallo Al'ameen ya bi shi, zuciyarsa na harbawa, shin ya tsayar da shi ne ko ya k'ale shi? Ya fi minti goma yana bin haryar sa Aliyu ya bi sa kallo, a zuciyarsa yana taraddadin mai Aliyu zai yi? Ya fi kowa sanin Aliyu, ya san dai tunda ya ce dole yana nufin dolen ne, sai dai komai zai faru ya faru, fatan shi dai kar Ummi ta ji wannan batu, Rass! Gabansa ya fad'i lokacin da ya tuno da Fatima, a hargitse ya mike, shaf! Ya manta cewa ta ji, ya tabbata ya zuwa yanzu Ummi ta san da maganar, da sauri ya nufi cikin gidansu, sai dai tuntu6en da ya yi da abu a zaure ya dakatar da shi, kafin ya gama tantance da mai ya yi tuntu6e shesshekar kukanta ya cika mishi kunne, "Fatima!!!" Ya ambata a tsorace, yana kokarin haska tocilar wayarsa, itan ce kuwa kamar yadda ya yi hasashe, da sauri ya d'ago ta yana cewa; Menenen Fatima me ya faru, ina Ummi?" A rud'e ya shiga jero mata wad'annan tambayoyin. jikinsa ta fad'a tare da sake rushewa da kuka, k'ofar d'akinsa ya bud'e ya ja hannunta a su ka shiga, ya mai da k'ofar net d'in ya rufe. Zaunar da ita a bakin kafitarsa ya yi ya tsuguna a gabanta, ya ce "Fatima Menene?" Cikin shessheka ta ce "Yayana Anty Amira, da gaske ne?" Gabansa ne ya fad'i, k'ura mata idanu ya yi, kafin ya ce "Kin fad'awa Ummi ne?" Ta girgiza kai. Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa; Kar ki gaya mata kin ji kanwata hankali ta zai tashi sosai." Gyad'a kai ta yi alamar to, sai kuma ta hade hannayenta alamar rok'o ta ce cikin kuka; Yaya dan Allah ka so ta, dan Allah ka tausaya mata ka kaunaceta wallahi tana son ka matsanancin soyayya Yaya ina tsoron kar mu rasata ta dalilinka, idan ka yi haka ka yi ceton rai, kuma na tabbata Ummi zata fi kowa farin ciki da hakan, idan kuma ta samu labarin ciwon Amira na da alaka da kai na tabbata zata fi kowa bakin ciki, Yayana don Allah karka ce A'a, ko dan ni da Ummi ka kaunaci Anty Amira baza ka yi nadama ba.." Hannayenta dake hade ya kama ya rike gam! da hannyensa yana jin maganganunta na ratsa kwakwalwarsa take idanunsa suna karasa rinewa, cikin matsanancin kuka ta ci gaba da cewa "Don Allah Yayana, don Allah pls kar ka ce A'a, ko dan ni da Ummi, ba baka da tam karmu muma bamu da ya kai." Kalaman data yi ta maimaitawa kenan idanunta a rufe tana hawaye har sai da ta ji ya ce "Is ok Fatima, is ok naji na Amince." Cak! Ta tsayar da sambatu da kukan da take yi ta dago ta kalle shi idanu jaga-jaga da hawaye ta ce a sanyaye "Da gaske Yayana." Ya gyada mata mata kai tare da sakar mata murmushin karfin hali. Fad'awa jikinsa tayi tana sakin dariya mai sauti hawayen farin ciki da kaunar tilon dan uwanta na kwaranya a idanunta, tallefe kanta ya yi shima yana jin kamar ya yi wahayen. Sun kusa minti goma a haka, tun tana shessheka har ta koma sauke ajiyar zuciya, jin ana shirin tayar da sallar isha'i yasa ya sake ta, ya kalleta ya ce, "Ina rokonki Fatima ki yara daren yau wajen taya ni neman za6in Allah, ni ma yau zan gabatar da istikhara akan lamarin kome ciki Allah zai dafa mana." Gyada kai ta yi ta ce "In sha Allah Yayana." Mikewa ya yi ya ce ki shiga gida nima zan ta fi masallaci. Koda ta shiga gida bata nunawa Ummi komai ba, alwala ta yi ta gabatar da sallar magriban da batta yi ba ta daura sa ishan da ake kira. Kamar yadda Al'ameen ya roketa ranar daga ita har shi kusan kwana suka yi a bisa sallaya suna kai kukan su ga Mahalicci. Washegari ************** Ajiyar zuciya Dr Abdul ya sauke bayan ya gama sauraren jawabin dan matashin yaron da bai gaza tsaran Al'ameen ba ya gama yi masa, sake kallon yaron ya yi da kyau, ya ce "Aliyu ko?" Gyada kai Aliyu ya yi, Dr ya sake cewa "Thank u Aliyu!" K'arara mamaki ya bayyana a fuskar Aliyu, shi da ya zo ban hakuri da neman taimako ana yi mishi godiya, goron ruwan faron dake kan table Dr Abdul ya dauka ya bude murfin ya kur6a kadan ya mai da murfin ya rufe, kallon Aliyu ya yi ya ce "Nasan kana mamakin dalilin da yasa na yi maka godiya ko." Aliyu ya gyada kai, Murmushi Dr ya yi yace "Saboda ka rage mini aiki, sam! Ban yi fushi da Al'ameen ba domin da baka zo ba ina daf da bin sahun shi, jira nake wa'adin dana d'aukar masa ya cika, sai ga shi kai ka fanshe shi, na jinjina maka lallia ka cika Amini na kwarai kuma ina da tabbacin zaka taimakeni a kan abin da na saka a gaba na alkhairi." Shiru ya yi kad'an kafin ya daure da " Aliyu na fi ka son na taimakama Al'ameen, amma na rasa irin taurin kan shi, sometimes na kan zauna ni kad'ai na dinga tunanin irin karfin hali da taurin zuciyar shi, ko da yake ance ma gaji ma fiyi, ada ni kad'ai na me gwagwarmayar nan yanzu gaka ka shigo ciki, don haka zamu had'a karfi da karfe! Yanzu dai abin da ya kamata mu yi, shine mu samu ya amince da maganar auren domin a yanzu shi ya fi komai mahimmanci, idan muka yi sanya, ina mai tabbatar maka daga nan zuwa ko wani irin lokaci zai iya haduwa da mummunan attack wanda idan ba'ayi da gaske ba zai iya shiga wani mummunan garari ko kuma ya rasa rayuwarsa ma baki d'aya." "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!" Shine Kalmar da Aliyu ya furta a baiyane cikin tsantsar tashin hankali, "Dr yanzu menene abin yi?" "Ka bi duk hanyar da zaka bi wajen ganin ka tirsasashi ya amince da batun auren yarinyar nan." Cikin tashin hankali ya ce "Zan yi Dr, zan tirsasashi ko zai amince' dole zai amince." "To shikenan Aliyu zan kar6i lamabarka saboda ina son sanin duk halin da ake ciki." Canjen lambar waya suka yi daga haka suka yi sallama Aliyu ya tafi. *************** Washegari ya kama asabar babu school, misalin karfe tara na safe Al'ameen ya shiga d'akin Ummi cikin shirin shi na tafiya wajen neman halalinsa ya sha kyau cikin wani yadi milk, dinkin karamin riga mai guntun hannu da wando babu hula akansa don ba abocin sakawa bane, duk suna falo Ummi ta maida hankali tana sauraren wa'azin Dr jabir mai hula a tashar Afrika TV 3, yayin da Fatima ke zaune daga can sak'on kujera, kallo daya zaka san tana tattare da damuwa, idanunta sun yi luhu luhu alamar rashin barci, sallamar sa ne ya dawo dasu duk hayyacinsu. Ummi ta ce cikin fara'a bayan ta amsa sallamarshi, "Amintacce har an fito." Murmushi ya yi ya ce "E Ummi na fito a yi mini addu'a." Ya karashe maganar yana rage tsawo a gabanta. Kan shi ta dafa ta ce "Ubangiji ya tsare gabanka sa bayanka ya yi maka albarka ya saka maka Albarka cikin neman ka ya jikan mahaifinka." Cikin wani irin yanayi ya amsa da "Amin Ummi." Tare da mikewa tsaye, ya kalli Fatima da itama shi take kallo ya ce "Kanwata muje ki min iso na shiga na dubo jikin Amira." Daga yadda fara'a ta fadada a fuskar Ummi ya tabbata ta ji dadin lamarin sai ya tsinci Kansas cikin farin ciki shima, Fatima kam wuf! Ta yi ta mike fuskarta dauke da madaukakin farin ciki........ Oum ummeetarh 09116090468 [12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€ ~FARHAT~ *PAGE 33* No editing 😀 Cike da zumud'i Fatima ta zura dogon hijabinta, bakinta washe kamar gonar auduga ta ce "Yayana muje." Ya gyada mata kai tare da k'ara yin sallama da Ummi suka fito. Tana gaba yana biye da ita har k'ofar gidan, a nan ya dakata ita kuma ta k'arasa ciki bakinta d'auke da sallama, a tsakar gida ta tarad da Maman Amira da Aysha da sauran k'annen Amira, Mama ta fara gaisarwa tare da tambayar mai jiki, sannan suka gaisa da Aysha wacce suke kusan sa'anni, sauran yaran suka gaisheta. Wuri ta samu ta zauna a dakali, ta kalli Mama ta ce "Mama Yaya Ameen ne yace na mashi iso yana son ya shigo ya duba Anty Amira da jiki." Mama ta ce "Assha! Aminullahi ne da neman iso dan zai shigo gidan nan, jeki maza ki ce ya shigo, ke kuma Aysha gayawa Amiran zuwan Aminullahi." Kusan a tare Fatima da Aysha suka amsa mata da to Mama. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bi bayan Fatima, da ta juya bayan ta isar masa da sa'kon Mama, Bakin sa dauke da cikakkiyar sallama ya saka kansa cikin dan madaidaicin tsakar gidan, dai dai lokacin Aysha ta fito daga d'akin Mama tana cewa; "Mama Anty Amira fa ta samu barci." "Barci kuma? ikon Allah! Yanzu fa na barota ido biyu." Cewar Mama tana kallon Fatima da ke tsaye tana jiran k'arasowar Al'ameen. Sallamarsa ne ya karad'e musu kunnuwa kusan a tare duk suka amsa, gefen Mama ya risina cike tsantsar ladabi da kamun kai ya ce "Mama ina kwana." Da fara'a ta amsa da "Ina gajiya Aminullahi, ya harkoki ya karatu." "Alhmdllh Mama ya jikin Amira." "Hmmm! Jiki da sauk'i Aminu sai hamdala." Ta fad'a muryarta cike da rauni. "Allah Ubangiji ya bata lafiya." "Amin ya rabbi, Mai jikin ma ta samu barci, idan ta farka zan sanar da ita zuwan ka." Ya amsa da " Ayya ba komai Mama, a gaisheta idan ta farka, idan na dawo da wuri zuwa dare zan sake shigowa in sha Allah." "To to!! Aminullahi Allah ya kaimu daren an gode sosai, Allah ya yi Albarka." Da Amin ya amsa tare da mik'ewa ya fice. Fatima ma bata dad'e ba ta yi musu sallama ta tafi tare da Alkawarin sake shigowa anjima. Kamar almara tana fitowa daga gidan ta yi kicibis da Joy. Da fara'a suka tari juna, Fatima ta ce "ya akayi kika fito da sassafen nan, yau Saturday." Murmushi ta yi kafin ta kai bakinta dai dai saitin kunne Fatima cikin rad'a ta ce "Na zo ganin Handsome Yayana ne, na yi masa godiya a kan, turaren da ya siya mana, yanzu zan koma kafin Mom ta nemi ni." Dariya Fatima ta yi, Idan da sabo ta sabo da jin ire iren sunayen nan kala kala daga bakin kawar tata da take kiran Al'ameen da su, sai dai bata ta6a daukarsu da wata manufa ba, ta bar hakan a matsayi kirkin da yake gwada mata shima, yana kula da ita sosai ya daukesu duk daya, sometimes har tsaraba yake musu a tare, tun bayan da hargitsin nan ya lafa ta lura da irin yadda Joy din ke matukar girmama lamarin da ya shafe shi, ko fira suke idan na shi ne ta fi maida hankali, kullum zancen ta Yaya Ameen kaza Yaya Ameen kaza, takan yi mamakin yadda lamarinsu ya juye daga kiyayya da kushe juna zuwa yabo da girmamawa hadi da tsantsar kulawa. "Umh! Wato shi kadai ki ka zo gani ko banda ni, to kin mak'aro yarinya ya fita." Narai narai ta yi da ido ta ce "Da gaske?" Cikin dariya Fatima ta ce "Ah swear!" "Ok bari na tafi, idan ya dawo ki fara Isar min da sakon godiya, kice nace turaren yana da kamshi wai tunda nake ban ta6a jin turaren mai dadinsa, kar ki sanarwa Ummi zuwana pls zan dawo may be gobe." Fatima ta ce "Oh naso kuwa na baki wani labari mai dadi, tunda kina sauri shikenan, kuma labarin ya shafi Yaya Ameen." A d'okance ta ce "Pls ki fara fad'a min Teetee ko Kad'an ne." "A'a ki tafi kawai bana son Mom ta miki fad'a, ranar Monday zan gaya miki a School." Riketa ta yi tamau ta ce "Ban yarda ba, sai kin fad'a min." "Ok to sake ni." Sake ta yi ta ce "Oyo tell me." Shammatar ta Fatima ta yi ta kwasa da gudu tana cewa; Sai Monday." A jigace ta yunk'ura ta mike zaune, lamarin da ya kusa zautar da Aysha tsabar mamaki, saboda rabon da ta iya mik'ewa ta zauna da kanta haka har sun manta, kullum sai dai a kwantar a tayar, bata damu da irin kallon da Aysha ke mata ba ta ce da muryarta wadda bata fita sosai saboda jigata "Da gaske ki ke Aysha Yaya Ameen ya shigo gidan nan duba jikina?" Aysha ta ce "Ya shigo mana Anty zan miki karya ne." Ga mamakinta wani Busasshen murmushi taga Amira ta saki wanda rabon da ta yi irinsa har sun manta sai kuma ga hawaye shar yana bin kumatunta,, murya ciki ciki ta ce " Tabbas ban yi farin ciki da wannan barcin da na yi ba, domin yayi mini shamaki da ganin rayuwata." "Anty mai Ki ka ce? "Ban ce komai ba Aysha." Gyada kai Aysha ta yi wani tunani na zuwar mata a kwakwalwa, da sauri ta d'ago ta kalli Amira ta ce "Yaya ina zargin wani abu, kar dai kice min soyayyace silar damuwarki?" Kura mata ido Amira ta yi, dai dai lokacin Zainabu ta yi sallama a k'ofar d'akin tare da kutso kai, gaban Aysha ta tsuguna tare da dafa kafadarta ta ce "Kwarai kuwa Aysha zarginki ingantacce ne, ranar wanka ba'a boyar cibiya." Ajiyar zuciya ta sauke, tiryan tiryan ta shiga labarta mata komai, tausayin Amira ya saka Aysha kuka kashir6an, cikin shessheka ta ce "Dama na dad'e ina zargin Anty Amira na son Yaya Ameen, amma ban ta6a tunanin shine matsalar larurarta ba, da tuni na bankad' sirrin kowa ya ji, dan bazan yarda na rasa yar uwata ba ina ji ina gani, amma ko yanzu bata 6aci ba." Ta kai karshen maganar tare da mikewa a fusace, riko hannunta Zainabu ta yi ta ce "kar ki yi haka Aysha abi komai a sannun." Komawa ta yi ta zauna tare da dafe kai ta ce "Gaskiya Yaya Ameen bashi da tausayi, ko dubata bai ta6a shigowa yi ba fa Anty Zainabu" "Kar kiga laifin shi Aysha bai san komai ba sai jiya." Nan ta kwashe yadda su ka yi da shi jiya ta fada mata. Ta daura da "Tun sa kika ga ya biyo baya ina ga akwai alamun nasara abin ba sai ya kai ga manya ba." "Allah yasa" Cewar Aysha. kamar almara ranar a zaune Amira ta wuni sa6anin kullum da take wuni kwance, sai gata harda dan cin abinci, Tsabar farin ciki Mama da gudu ta garzaya ta sanarwa Ummi don abokin kuka da shi ake dariya. Hamdala Ummi ta shiga yi, ranar da wannan zancen ta wuni duk wanda ya shigo gidan kuwa da maganar take fara taron shi. Cikin sa'a karfe shidda Al'ameen ya dawo, da wannan zancen Ummi ta tare shi fuskarta a washe, murmushi yak'e ya kirkiro ya yi tare da cewa "Alhmdllh kai na yi murna Allah ya kara mata lafiya." Jiki a sanyaye ya juya ya koma d'akinsa, kimtsawa ya yi, ya tafi masallaci, daga masallaci direct gidan su Amira ya nufa, a lokacin duhu ya fara. Sam ta ki yarda ta sake komawa barci tun bayan wanda ta yi da safe wanda ta yi mishi lakabi da barcin shamaki, tun karfe biyar take ta zuba idon ganin shi amma shiru, shidda ya yi da rabi ya wuce har magrib zuwa lokacin ta fara sarewa, silalewa ta yi ta kwanta ta lumshe idanu hawaye na bin kumatatunta. Kamar a mafarki ta tsinaka yi sallmarsa a cikin dodon kunnenta, kafin ta gama tantance a wani hali ta ke ta sake jiyo muryar Mama tana cewa "Tana d'akinsu, Aysha yi wa Aminullahi iso." Kur! Ta kurwa k'ofar dakin idanunta masu danshi ya yin da bugun zuciyarta ya tsananta.......... Haka so yake d'iba ya maida kai bawa🎢🎢🎢🎢 Allah sarki Amira. Y'an term d'in sannunku hwa

Chapter 15 of 22