Share this page
gaba da shi ba. Washegari, da wurwuri ya shirya ya fice daga gidan bayan yayi sallama da su Ummi akan ya tafi school, sai dai yana fita ya dauki hanyar, S Alto special hospital, duk da sammakon da yayi sai da ya tarar da layi, zama ya yi a waiting area har layi ya iso kan shi, a hankali ya tura office din doctor ya shiga, kamar kullum kyakyawan matashin likitan wanda a kalla zai kai shekara talatin da takwas da haihuwa ya dago ya zubawa Al'ameen idanun shi dake sanye da farin glass kur kamar zai cinye shi da idanu, hannun da Al'ameen ya mika mishi ya dawo da shi hayyacinsa, hannun ya mika mishi sukayi musabaha, tare da nuna ma mishi wajen zama, zama Al'ameen ya yi a kujerar dake facing din *Dr Abdul Hafiz S Alto* Dr da har lokacin idanun shi na kan Al'ameen ya ce " Muhammadul-Ameen Husain ko?" Al'ameen ya gyada kai yana murmushi, Dr ya ce "Sai yau ka waiwayeni ko? To ya jikin naka, dama nasan zaka dawo ai domin wannan matakin daka za6a ba mai bullewa bane." Al'ameen Ya ce " Kayi hakuri Dr ba laifi na bane na gayaka tun farko a kwai nauyi a kaina bazan Iya hada taura biyu ba, jiki kuma sai godiyar ubangiji." Gyada Dr ya ce ya ce "well! yanzu meke tafe da kai?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kwashe abin da yaji jiya game da shakar kamshin turaren Amira da ya yi, ya d'aura da "Na ji tsoro sosai Dr kar ace matakin ciwon nan ya kara karfi a jikina kamar yadda ka fada zai iya faruwa, Dr I can't hold my self idan abin ya fi haka, bazan Iya ba I'm so scare." Dr dake kallon shi tun dazu ya ce "Then ka yi AURE mana Al'ameen shekarun ka sun kai ai, U ar 25 years by now." Da sauri Al'ameen ya dago ya zuba mishi idanu, Dr ya daura da "Tun a baya na sha fada ma ka dat is d only solution of ur prlm. Duk wani tablet ko injection da zan baka,bazai taba zama total solution a gareka ba, sai ma ya janyo maka wata illar ta dabam, halittanka ne a hakan, wanda ya hade maka da lalura, a halin yanzu abin ya taka mataki na gaba ajikin ka, wanda idan ka bari ya kuma karawa gaba daga haka, to tabbas komai zai Iya faruwa ina tabbatar maka da bazaka iya controlling kanka ba." Kamar zaiyi kuka ya ce "Dr ka taimaka min bazan Iya rike mace a halin da nake ciki a yanzu ba, bani da wannan karfin a kwai nauyi a kaina ni maraya ne."kallon shi Dr S Alto yakeyi cike da nazari, "pls Dr dan Allah ka taimaka min." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce , "Naji zan taimaka maka amma kafin nan, kamar kullum yauma ina son sanin who ar u Muhammadul-Ameen." Kallon shi cikin ido Al'ameen yayi ya e "Bazan gaji da gaya maka cewa ni mayara bane. Bayan hakan bansan komai a kaina ba." Dr ya gyada kai cike da nazari ya ce " For now ka koma ka ci gaba da amfani da wannan tablet din, idan abin yayi tsamari dole akwai wani injection da zan maka, wanda kuma yin shi is very risk ga lafiyar mazan takar ka, idan akayi either a dace kokuma a ta6e." Godiya Al'ameen yayi mishi gwiwa a sage ya mike ya nufi barin office din, har ya kama handle Dr S Alto ya kira sunan shi, jiyowa ya kalle shi ba tare da ya amsa ba, Dr yaci gaba da cewa "Kayi tunani sosai akan shawarata AURE shine magananin matsalar ka, kaje duk abin da ka yanke ta waiwayeni." Murmushin yayi ya fice ba tare da ya amsa ba. Da kallo Dr Abdul Hafiz S Alto ya bi bayan shi har ya kule, ajiyar zuciya ya sauke zuciyar shi cike da wani irin yanayin mai wuyar fahimta, ganin yana shirin shiga wani yanayi yasa ya ba next patient damar shigowa don ci gaba da aikin shi. Cike da wani irin damuwa ya fito daga asibitin, tafe yake akan hanya amma kwata kwata baya cikin natsuwar sa jefa kafa yake yi kawai duk inda ya samu ba tare da ya ankare ba, kamar wani karatu haka ya rin ga maimaita Kalmar AURE a zuciyar shi, gaba daya kalaman Dr sun rikita shi har yana neman rasa nutsuwar sa, shin ta ina zai fara jajibo aure a halin yanzu? Shin wa ma zai aura, da wani ido zai Iya fuskantar Ummi ya gaya mata zai yi aure bayan bata da masaniya akan larurar shi, kai ina impossible, yana bukatar shawarata, lallai yana bukatar shawarata da gaggawa, wa zai fadawa matsalar shi ya bashi shawara, Aliyu! Aliyu ne ya fado mai a rai, a fili ya furta "Yesss! Aliyu ne." Daga nan direct gidan su Aliyu ya nufa, ba tare da sanin yana gidan ko baya nan ba. ******** Joy kwana tayi rungume da takardan da AL'AMEEN ya bayar aka kawo mata a matsayin Fatima ce ta bayar, wani irin magadisu ne a cikin takardan dake janta kamar magnet, ta rasa dalili ta rasa dan mafari, sai kawai ta dangata hakan da kasancewar takardar ya fito daga hannu Fatima ne. Ta ki yarda ta baiwar zuciyar ta damar cewa rubutun Al'ameen ne bana Fatima ba, hasalima duk sanda tayi wanan hasashen gabanta faduwa yake yi......... Wallahi Ku ringa comment ko kuma sai na bari labari ya dakko dadi Ku nemi sama da kasa Ku rasa, kun san dai halin , hayyaratata in ji me mata tara😬 Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar amma in kinsman idan kin shigo baza ki ringa comment ba karki fara yi min magana 09116099486 [12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€ *PAGE 14* Ban yi Editing baπŸ™ Daga hospital kai tsaye Al'ameen gidan su Aliyu ya nufa, yaro ya samu ya aika cikin gidan kiran shi, sannan ya lalubi dakalin kofar gidan ya zauna, babu jimawa yaron ya dawo ya ce "Wai an ce Aliyu baya nan yayi tafiya." Jim Al'ameen yayi, kafin ya amsawa yaron da "Ok nagode." Agogon hannun shi ya kalla, sha biyu saura, ya san kafin ma ya isa school yanzu an gama lecture yau, kuma baya jin zai iya fita aiki a halin da yake ciki yanzu don haka kawai ya kamo hanyar gida. Kamar yadda ya zama wa Amira jiki cikin yan kwanankin nan kusan kullum sai ta shiga gidansu Al'ameen , yau ma cike da zakuwa ta shiga fuskarta dauke da madaukakin farin ciki. Jiya da dare dakyar barci ya dauke ta saboda farin cikin Yaya Ameen ya amince zai ringa koya mata karatu, ko babu komai zata samu lokaci ta ke6e da shi, zata samu wani dama wanda kuma ta daukar wa kanta alkawari iya wuya zata yi amfani da shi, zata yi kokarin fahimtar da shi halin da zuciyar ta ke ciki game da shi, ta hanyar kissa irin ta diya mace idan ta kama zata iya kauda zara ta kauda wata ta bude baki ta furta mashi kalmar so, domin kuwa ita kadai ta san irin azabtuwar da zuciyar ta ke yi akan shi. Tana tsaka da jan ruwa a rijiya, ta cire hijabinta ta rataye a igiyar shanya, kasancewar gidan su biyu ne ita da Fatima Ummi bata nan, ya shigo bakin shi dauke da siririyar sallama, gabanta ne yayi wani irin faduwa jikinta ta bi da kallo sanye take da riga da skirt na atamfa dinkin zamani abinka da budurwa ta yi das da ita kanta babu adiko kananan kitsonta a bayyane, wani irin kunya ne ya lullubeta, ga shi ta riga ta zura guga a rijiya,ji tayi kamar ta saki gugan sai dai ta daure ta, dukar da kanta kasa tare da amsa mashi sallamar da yayi cikin dan rawar murya, kallo daya ya yi mata da dauke kanshi, yana amsa gaisuwar da ta mishi da " Lafiya." Ya wuce ta zuwa dakin Ummi, Fatima na kwance ta na game da wayar Amira, ta ji sallama, amsawa tayi da sauri tana mikewa zaune, ya shigo akan wayar hannunta idanun shi suka sauka, zama yayi akan kujera daya tal dake falon 2 sitter, cike dan in'ina ta ce "Yaya sannu da dawowa." Bai amsa mata ba sa cewa da yayi "Wayar wa ye a hannunki." Ta ce "Na Anty Amira ne." Ya ce "Ki kai mata abinta ki ce na ce ta rufe gashin ta." Da to ta amsa tare da mikewa ta fice, wayam ta Tatar da tsakar gidan babu Amira babu mai kama da ita, da mamaki ta shiga kiran sunanta amma shiru, hakan ya tabbatar ma Fatima bata cikin gidan. Dawoqa tayi da wayar a hannu ta ce "Yaya ban ganta a tsakar gida ba ganin ta wuce." Ba tare da wani damuwa ko daukar lamarin da muhimmanci na ya ce "Ki kai mata gidansu, kuma kar na kuma ganin ki da wayar wani, idan lokacin ki rike wata yayi ni dakaina zan siyo miki." Ta amsa da "To Yaya." Tana zura hijabinta a jiki, har ta kai bakin kofa ya ce "Ummi fa? Ko ta kwanta ne." Juyowa tayi a sanyaye ta ce bata nan da mamaki a fuskarsa ya ce "Ba ta nan?." Ta ce "Eh." "Ina ta je." Ta ce "Bata fada min ba." Ya ce "ya ce ok je ki kai wayar ki dawo." Ta amsa da to ta fi ce. Da sallama Fatima ta shiga gidansu Amira, da sauri Amira da ke zaune a tsakar gida ta rafka tagumi ta mike tsaye, Fatima ta karaso ta ce "Anty Amira sai kika wuce babu sanarwa, Yaya ya ce na kawo miki wayar ki kuma ya ce na gaya miki ki ringa daura dankwali." Wani irin zaro ido da tayi sai da abin ya ba Fatima dariya, ta ce "Da gaske haka ya ce Fatima?" Fatima na mata dariya ta ce "Wallahi haka ya ce." Amira ta ce "Na shiga uku." Ba tare da tasan ta furta ba duk ta bi ta ruda kanta, Fatima cikin dariya ta ce "Wallahi ke babbar matsoraciya Anty Amira." Ta ce " Hmmm! Baza ki gane bane Fatima, wallahi naji kunya sosai yadda Yaya Ameen ya tarar da ni daga ni sai Riga da skirt babu ko dan kwali wallahi kamar na nutse a kasa saboda kunya, sai naga ma kamar ya harareni" Sa ke kwashewa da dariya Fatima ta yi ta ce "Bari na je na gayawa Yayana wagga batu." Da sauri ta juya zata fi ce, Amira tayi wuf ta rikota, cikin yanayin tsoro ta ce "Dan girman Allah Fatima kar ki gaya mishi." Fatima ta ce "To sakeni Anty Amira bazan fada ba." Ta ce. "Ki rantse." Sai da Fatima ta mata rantsuwa sannan ta saketa tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi gudu, cike da al'ajabi Fatima ta fito gidan ta shige nasu, koda ta koma Al'ameen ya fice data dakin su alamar ya tafi nasa ganin haka ta gane baya son hayaniya don tafi kowa fahimtar shi, bata nemi shi ba ta shiga kitchen ta daura musu sanwar rana kamar yadda Ummi ta bar mata sallahu. ********* Karfe biyar dai dai Dr Abdul Hafiz S Alto ya danna hancin motar shi cikin kyayataccen compound din gidan sa dake unguwar Brighter, bayan parking kai tsaye ya nufi asalin cikin gidan, da sallama dauke a bakin shi, da sauri yan yaran da ke zaune a falo suka kwaso da gudu suna ga Daddy ga Daddy, Daddy oyoyoo Daddy oyoyoo, suka rungume shi, jin hayaniyar su ya fito da matar gidan daga kitchen, matashiya ce mai kimanin shekaru 28 zuwa 30 fara tass da ita kyakkyawa, da fara'a ta karaso ta na mishi sannu sa zuwa, tare da dan runguma,yana murmushi, ya amsa mata da "Uwar gida ran gida, yaya gida ya yara." Ta ce "Gida da yara lafiya kalau sai hamdala." Zame hannun shi yayi daga cikin na karamin yaron shi ke kimanin shekaru biyu, ya ce "Aboki bari na watsa ruwa na dawo ko." Yaron ya gyada kai yana murmushi, daga nan yayi dakin shi, matar shi ta rufa mishi baya, ruwan wanka ta hada mishi kafin ta dawo ta taya shi rage kaya ya shige toilet don ya watsa ruwa. Minti goma ya kwashe kafin ya fito sanye da rigar wanka, bata dakin bai damu ba don yasan kila tana wani uzirin ne, shiryawa ya shiga yi cikin kananan kaya, yana gama shiryawa ta shigo da sauri ta, tana ganin haka tace "Oh shirt! Kayi hakuri wallahi Ina kitchen ne ban gama hada dinner ba shi yasa na barka." Murmushi yayi yace "Babu komai ai na gama." Ta ce "Nasan halinka yanzu zaka baza kaci abinci ba ka riga kaci abinci a hospital, amma duk da haka bari na kawo naka dan abin tabawa." Fita ta yi jim kadan ta shigo dauke da tray da jug cake ne da pineapple juice da ta hada mishi da kanta ta jawo center table ta daura mishi, godiya ya mata ya zauna ya shiga ci, ita kuma ta bashi hakuri ta sake ficewa kitchen, bayan ya gama ya dauki tissue ya goge baki, mikewa yayi daga gaban table din, ya koma bakin bed ya zauna, wayar shi ya dauka, ya lalubo wata international number da yayi serving da suna Hayatudden Aboki. Sai da ya kalli agogon bangon dakin ganin biyar da arba'in, ya tabbatar inda zaiyi kiran yanzu dare ne a wajen su amma haka ya daure ya yi dialling, lambar yayi ringing sosai kamar baza a daga ba can kuma lucky yaji anyi picking, daga can bangaren aka yi sallama da wata irin nutsattsatsiyar murya, kafin a daura da "He'll Aboki." Murmushi Dr Abdul yayi kafin ya amsa sallamar ya daura da cewa "Hi Aboki." Kamar yadda Abokin nashi ya fada, duk murmushi suka yi, kafin su shiga gaisawa da tambayar lafiyar juna, bayan sun gama suka dan taba hira irin ta amintattun abokai, daga nan kuma, Barrister Hayatudden ya ce "How about d boy, ya sake zuwa." Dr Abdul ya ce "Yes ya sake dazu shi yasa ma na kiraka." Cike da wani irin karsashi Barrister Hayat ya ce "Me ya kawo shi? Me ya ce maka? Yaya matakin ciwon shi zuwa yanzu? Ya fada maka shi wanene? Su waye iyayensa." Dr Abdul ya ce "Easy mana aboki, wadannan irin tambayoyi haka a jere, koda yake ba wani Abu bane tunda da cikakken lawya me zaman kansa nake magana." Barrister Hayat ya katse shi da cewa "All, aboki, duka tambayoyin nake bukatar amsarsu daga gareka."............ Ayi hakuri da wannan, yau bani da naji sosaiπŸ™ masu comment ngd sosai na gani kuma na yaba much luv 2 u ppl all INA yinku irin totally. Da iya masu comment kadai fa nake yi atoh! Ga masu bukatar shiga group. 09116099486 [12/29, 2:36 PM] AyshaNalado: πŸŒ€πŸŒ€ *JOY* πŸŒ€πŸŒ€ ~FARHAT~ *PAGE 15* Dr S Alto ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya ya ce "Bai gaya mani komai game da ahlin shi ba, still yau ma ce min yayi shi maraya ne kamar yadda ya saba fada, game da matakin ciwon shi kuwa, yanzu abin ya kai mataki na hudu a gaskiya yana cikin hatsari ." Barrister Hayat cikin sanyin jiki ya ce "Aboki lokaci yayi da zan dawo 9ja koda kuwa ban gama cike wa'adina a nan ba, ya zama dole na san ko wanene shi, jikina yana bani cewa mafarkina yana gaf da tabbata." Dr S Alto ya ce "Aboki ban katsi hanzarin ka ba, sai dai ina mai kara baka hakuri, kayi hakuri ka zauna ka kammala aikin da ya kaika, kar muyi biyu babu." A dan harzuke Barrister Hayat ya ce "me kake so ka gaya min, wani irin biyu babu, kafin kowa sani na Abdul idan da wanda zai karfafa min gwiwa akan lamarin nan baren ka ne, amma sai naga kamar baka dauki lamarin da muhimmanci ba." Dr ya ce "Ba haka bane Hayat, so nake mubi komai a hankali, ka tuna fa har yanzu, tsammani kawai muke bamu da tabbaci, kuma har yanzu idanunsu ba wai ya dauke akan ka bane, kana dawowa Nigeria ba tare da wa'adin ka ya cika ba, zasu saka maka ayar tambaya duk wani motsin ka zai kasance a kan idanun su, kayi hakuri ka zauna nayi maka alkawari kafin nan da shekaru biyun da suka rage maka ka dawo kasarka zan tabbatar na gama duk wani bincike daya kamata." Ajiyar zuciya B Hayat ya sauke, a sanyaye ya ce "Na yarda da kai Aboki, a duniya bayan y'an uwana bani da wanda ya fi ka, na san zaka iya, na damka maka amanar rayuwata ka kulamin da ita." Dr ya ce "in sha Allah na maka alkwari bazan baka kunya ba." Daga haka ba su yi wani hira ba, suka yi sallama zuciyoyin kowannen su a jagule musamman Barrister Hayat wanda maganar ta yi mishi fami a zuciya. *********** *JOY* Zaune ta ke a kyayataccen garden din gidan su, yammaci ne mai cike da ni'ima kasancewar garin yau kwata kwata basu ga kyallin rana ba saboda ruwan da aka kwana ana tsugawa daren jiya kamar da bakin kwarya. Books ne a gabanta da yawa, ta kwaso domin tayi karatu saboda gabatowar lokacin fara mid term test wanda ya kasance na third term ne, wato na canza aji, d'aya daga cikin books din na rike a hannunta tana dubawa, a zahiri idan ka ganta zaka dauka a gaske karatun takeyi amma a badini kwata kwata hankalinta baya kan karatun, tunani ne fal zuciyar ta, kallo daya zaka fahimci bata cikin walwala ko kad'an, yau kimanin kwana biyar kenan data aikawa Fatima letter, amma har satin ya kare bata je school ba, gashi on Monday zasu fara mid term test, bata yi aune ba sai kawai ta ji hawaye na zuba daga idanunta yana diga kan book din da take kallo, Ta na matuk'ar kewar Fatima ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gidan su, ta ke ta shiga tunano yadda suke gudanar da rayuwarsu a baya, yadda suke nunawa juna tsatanin kauna da kulawa babu kyamata kyashi ko hassada tsakanin su da juna soyayya ce gangariya daga indallahi' ta tuna ranar data fara haduwa da Fatima, farkon shigowar su SS1, wata rana suna zaune a class aka kawo musu new comer Fatima Husain, kallo daya suka yi wa juna a tare suna sakarwa juna murmushi kamar dama sun san juna, lokacin da class Master su yaba Fatima umarnin ta je ta samu sit ta zauna direct ta nufo kujerarta duk da cewa ga sauran empty sit nan a class din da yawa kuma ga musulmai nan yan'uwa ta a ajin, babu musu ko gaddama ta matsa mata ta zauna, ranar ko kalmar A bata shiga tsakanin su ba, sai satar kallon juna da suke yi kamar wasu munafukai, idan suka had'a idanu su sakar wa juna murmushi, tun daga ranar farko da suka fara haduwa zuciyoyin su ya sark'e da soyayyar juna, sun kai kusan kwana uku a haka kullum idan Fatima ta zo sit d'inta ta ke zama suyi ta kallo juna, maganar farko data fara shiga tskanin su a rana ta hud'u maths teacher ya shigo ya yi musu lesson bayan sun gama ya bada class work kowaccensu ta dauko notebook d'inta ta fara solving, Fatima ta gama nata kamar yadda suka saba satar kallon juna ta juya ta saci kallon na Joy, zaro ido tayi ganin yadda ta yi solving wrongly, sai dai ta rasa yadda zata gaya mata, ta zauna tana ta sak'e sak'e , har lokacin data mik'e zata je tayi submit, har ta fita daga sit d'in ta ji an riko hannunta, juyowa tayi suka kalli juna cikin ido, cikin inda inda Fatima ta ce "please can I see ur calculation." "Why not." Ta amsa mata da murmushi tare da mik'a mata, bata ce mata komai ba ta shiga gyara mata inda ta yi kuskuren tana gamawa ba tare da ta kalleta ba ta mik'a mata tare da cewa "ki yi hakuri da shisshigina." Sai lokacin ta kula da kuskuren data tafka, murmushi tayi tare da ce mata "Thanks" Itama ta sakar murmushi ba tare da ta amsa ba. Tuna wannan yasa Joy sakin murmushi ba tare da ta san tana yi ba, still ga hawaye a idanunta, Hannu ta saka a aljihun wandonta ta zaro letter n nan na Al'ameen, daya zame mata kamar wani gold duk inda zata je yana tare da ita da shi take kwana rungume a jikinta duk daren duniya, ta warware pepan tana kallo, sai dai har yau bata sauya zani ba a duk sanda zata daura idanu a jikin rubutun gabanta sai ya fad'i, ba tare da tasan dalilin hakan ba, tana kallo tana ci gaba da hawaye ta ce a bayyane "I missed u a lot my Teetee." ba ta san isowar Mom ba sai jin muryar ta tayi akanta, ta na ce wa "Joy what's wrong wit U? me ya same ki, kukan me kike yi." Da sauri ta shiga goge hawayenta at same time tana kokarin boye letter n cikin inda-inda ta ce "Nothing Mom, abune ya fad'a min a idanu." Mom da ta gama karantar rashin gaskiya k'arara a fuskarta ta shammaceta ta fusge letter n, a bayyane ta karanta abinda ke ciki "THANK YOU." A razane ta kalli Joy data zaro manyan idanunta cike da fargaba ta watsa mata, k'ank'ance ido Mom tayi cike da tashin hankali ta ce "Menene wannan Joy?" Ta ce "Babu komai Mom." Mom ta ce " Wannan letter daga ina." Cikin inda-inda ta ce "Ya dade sosai Mom a cikin textbook dina, yanzu dana dauko su ina dubawa shine na gani." Mom ta ce "To naji wannan kukan kuma na menene shi?" Ta ce "Ba kuka na ke yi ba Mom abune ya fada min a ido." Ko kadan Mom bata yarda da batun ta ba, hakan yasa ba tare da wani dogon nazari ba ta daga letter n ta kekketa shi. Rintse ido Joy ta yi don ji tayi kamar zuciyar ta Mom ke ketawa, lura da haka yasa Mom yin gutsi gusti da shi yadda koda ta tattara pieces din baza ta gane komai ba. Tana gamawa ta ce ki tashi muje ciki kiyi yan shirye shirye, tafiyar gaggawa ta kamani gobe da sassafe zamu bi jirgi zuwa Oshogbo . Cike da mamakin me zai kai su Oshogbo tana tsaka da shirin fara mid term test hankali ta she ta ce "Mom Oshogbo kuma." Mom Ta ce "Yes of course." "Ba sai hutun karshen shekara Mike zuwa ba? Kuma next week Monday zamu fara text." Mom ta ce "dat is not my prlm." Cikin shesshekar kuka tace "Gaskiya Mom ni bazan je ba." Wani mugun kallon ta watsa mata tare da saka mata wata uwar tsawa da gufu ta mike tayi cikin gida tana kuka. ********* Tsawon sati guda Al'ameen bai cewa Amira komai game da batun karatun su ba, iya damuwa ta shiga damuwa gashi tana jin kunyar sake tunkarar shi da maganar, yau a islamiyya, ta zayyane wa Zainabu halin da take ciki, Zainabu ta ce "Ko dai ya mata ne?" Amira ta ce "bana tunanin haka." Numfashi Zainabu ta sauke ta ce "Fatima zaki aika ta tuna masa idan ma mantuwa yayi sai ya tuna." Amira ta ce "nima tunanin da nake yi kenan k'awata.sai dai

Chapter 7 of 22