Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne dan ta debe musu kewa da ita da Jalila, dan tasan Jalila na bukatar kulawa, ita kuma saboda gudun tunani da zargi yasa take neman abinda zai debe mata kewa. Haka sukaje sukai siyayya sosai, sannan suka biya shagon wayoyi, Ummy da kanta ta zaboma Jalila waya irin ta hannunta Sumsung ce Note 9. Jalila kam gaba daya ta rasa me zatace, dan itakam batasan ta inda zata fara magana ba. Sagir kam dadi yakeji ganin fuskar Jalila na dauke da murmushin da yake har zuciyarta bawai na iya baki ba. Haka suka isa gida sannan sukai abinci ta dau nasu ta hau sama, yau kam zuciyarta ta ragu da damuwa, sannan ta kara samun karfin gwiwar yima Hassan magana. Bayan isha'i ya dawo ta jawo mai abinci kusa dashi, Hassan ya kalleta yace "nasha yogurt, later." Jalila ta dauke tasa a gefe, zama tai a kan gadon daga inda kafafunsa suke can karshen gado, ta mikomai wayarta. Kallanta yai sannan ya amsa, yace "na meye?" Tace "Ummy ce ta saimin." Ya juyata sannan ya mika mata yace "to." Tace "bakasa number ka ba." Yace "me zakiyi da ita?" Tace " In wani abin ya taso." Ya kalleta yace "kamar me?" Wayarta ta amsa tace "shekenan kawai kace dai bakasan sawa." Kallanta yai yace " kawo dai." Ta mika mai tana dan tabe baki kadan kanta a kasa, ya amsa yace "in zaki harareni ko murgudamin baki, ko tabemin baki ki tabbatar kinyishi ina kallo dan ko ban kallekiba ina sanin inkinyi hakan. Jalila ta kalleshi tace "ni banyi komai ba." Wayar ya mika mata yace "yi saving." Ta amsa tasa "Yayah." Sannan sukai dan shiru, can tace "Yaya me zanyi in taimaki Goggona?" Kallanta yai yace "zancen dazu ne?" Tace "eh, na gane dazu na fara ma magana ne kamar i am hopeless bansan me zanyi ba, bani kuma da plan." Littafin sa ya dauka baice komai ba, saukowa tai kasa ta tsugunna a kusa dashi tace "Yaya dan Allah ka taimakeni." Littafin ya ajiye yana kallanta........... #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *31* Kallanta kawai yake baice komai ba, ta dago tace " Yaya Goggona......" Sai ta kasa karasawa saboda kukan daya kwace mata, kallanta yake baida niyyar tanka mata, balle ya lalasheta. Sai dai yanayin kukan da takeyi ya fahimci lalai she is desperate. Yace "in kuka zakimin zan iya tashi in fita." Ta share hawayenta tace " bansan ta inda zan fadamaka halin da Goggona take ciki ba." Yace "ban tambayeki wannan ba, abinda kawai nakesan naji me kike tunanin yi, sannan me kikeso nayi miki?" Ta mike da sauri tace "Yaya zaka taimakeni?" Kallanta yai sannan ya juya kansa, shiru tai kafin tace " Bansan me zanyi ba." Yama rasa mai zaice hakan yasa ya sa hannu zai dauki littafinsa, da sauri ta rike littafin. Kallanta yai tace "Please!" Yauce rana ta farko a rayuwarta da take roko da neman taimako akan 'yancinsu, aduk lokacin da aka musu abu a da sam bata kawo komai sai takaicin yanda ake wulakantasu, amma bata taba tunanin zata kwaci kanta ba, itadai kullum fatanta tai aure ta dauke Goggonta. Hassan yace " in bakida abin cewa ki bari sai kin samu sai kimin magana, bance zan taimaka miki ba bare kisa ran zanyi, na dai ce ki fadamin ne kawai inji ko zan iya, i hate meddling in someone's life." Bata saki littafin ba tace " Ban taba tunanin nima har akwai lokacin da zan nemi taimakonka ba, ganin halayenka, sai dai kai kadai ne a duniya a yanzu da zaka iya taimako na, Yaya dan Allah." Yace " bai dameni ba, Ita mamar taki haryanzu suna tare da wanda ya haifeki ne?" A ranta tace "ina laifin kace mamanki da babanki?" Amma a fili tace "eh sai dai bansan wani irin zama ake ba wanda maganar mutunci bata hadasu." Littafinsa ya kwace yace " to meye matsalar?" Tace "naam?" Yace menene matsalar ta koma gidansu mana." Jalila ta kalleshi jiki a sanyaye, kallanta kawai yai wanda hakan ya nunamai can din ma dai ba magana. Ya dade baice komai ba wanda har jikinta yai sanyi kafin taji yace "ki shirya gobe muje ki dubata." Da sauri ta kalleshi sam hankalinsa baya kanta ya maidashi kan littafi, kamar bashi yai maganar ba, Tace "Bansan asibitin da suka canza mata ba." Bai tanka mata ba, tace "Yaya in mun dubata sai me zamuyi?" Yace "later." Tana shirin magana ma sai taga ya mike ya wuce toilet, ajiyar zuciya tai tace "kai wannan matarka ta shiga uku." Sai tai shiru tace au ahh ashe fa nice ko? (Nace kila nice.......lol) Mikewa tai ta fito tana cewa "da alama bai fahimci ina na nufa ba, ni ba dubata nakeso ba, darajarta nakeso su sani balle har su kara tunanin rainata." Haka ta fito ta sauka kasa, tana san yima Ummy saida safe. Tasa hannu zata bude kofar taji muryar Ummy tace " wai meke damunka ne? Bansan me yasameka ba yanzu komai sai ka fara neman yin fada, scammers ka hadu dasu ne ko me?" Yace " ke ce yanzu bansan meke damunki ba, bansan yaushe kika fara takura haka ba, dolene sai naci abincin......? Jalila ta juya da sauri a ranta tana cewa " mekenan?" Komawa tai sama da sauri, bayan sunyi sallah sannan taga yadanci abinci kadan, a ranta tace "in mace tayi ba wani abu amma namiji?" Hassan ya hau kan gado ya zauna ya dau jornal dinsa, a ranta tace "wai baya gajiya? Daga zama da karatu sai fita?" Wayarta ta dauka tana dan lalatsawa, lalai ta kosa gobe tayi ta nunama Goggo wayarta, amma zasu ganta kuwa? Bayan basusan sunan asibitin ba? Kallansa tai tanasan kara mai magana amma ta kasa. Meya faru tsakanin Ummy da Abba? Ta fada mai? Can tace "hmm wannan mutumin? Salan yace gulma naje yi?" Kafa yasa ya tura bargon dake kan gadon zuwa kasa. Jalila ta kalleshi, ganin ba alamar shi yayi yasa ta dauko bargon ta na neman maidawa kan gadon, yace "in kinaso kiyi amfani dashi." Da sauri ta kalleshi tace "dagaske?" Bai tanka kata ba, ta dauka tana murmushi ta shimfida, ta hau ta luluba da bedsheet ga pillow yaukam kwanciyar ta mata dadi, wayarta ta dauko tana kara latsawa. Haka tai ta latsa wayarta har tai bacci. Juyowa yai ya kalleta, gani nai ya kura mata ido daga inda yake, kamar yana nazari akan wani abu. Can sai naga ya gyara ya kwanta, bai dade ba bacci yai gaba dashi. Washegari ma Alhamdulila anyi sa'a abin nasa bai tashi ba, bayan yayi alwala yasa kafa ya dan buge ta dan dama haka yake tashinta. Idanu ta bude ta kalleshi, kallanta yai sannan ya mata alama data mike, Jalila ta tashi ta dauke da bargon daga gun, ga fili nan a dakin amma shidai anan yake sallah. Toilet ta shiga shi kuma ya tada sallah. Sai wajen karfe 7 ta tashi ta kasa ma baccin saboda ta matsu ya tashi su tafi gun Goggo, saukowa kasa tai dan fara aikin abinci saboda yana tashi itakuma ta gama komai sai tafiya. Ganin dakin Ameera tai a bude, a ranta tace "ta dawo ne?" Dakin ta nufa ta kara tura kofar, me zata gani? Ummy ta gani a kwance tana barci. Meke faruwa? Badai fadan da sukai jiya bane haryakaisu ga haka? Gyara kofar tai ta juya a hankali tabar gun ta nufi kitchen. Aikin breakfast take amma sam hankalinta nakan Ummy, ta rasa meyasa batasan wani abun ya bata mata rai sam. Tana aiki har masu aikin gidan suka zo, suna fara kwankwasawa ta fita da sauri ta bude musu kofar, bataso a tashi Ummy. Gaisheta sukai sannan suka fara aikin shara da gyare gyare, saboda girman kasan. Sagir ne ya fito ya hangota a kitchen tana ta aiki, tsayawa yai yana kallanta inama matarsa ce? Da yanzu zuwa zaiyi kawai ta bayanta ya rungumeta. Da sauri ya fara a'uziyya saboda neman tsari daga shaidan, komawa ciki yai da sauri ya zauna a gefen gado sannan ya kwantar da kansa kan pillow. Ummy kam sai wajen takwas da kwata ta farka, kallan agoggo tai cikin mamaki, wani irin bacci tai haka? Shiru tai tana tunanin abinda ya faru itada Abba a daren jiya. Bayan ya dawo tanemi ya fito falo yaci abinci, tunda haka suka saba. Kallanta yai yace mata "bayajin yunwa." Tai murmushi tare da ajiye jakarsa tace "haka ka koshi a waje ne da alama." Ganin sun saba irin wannan abin bata daukeshi a komai ba, sai cewa yai ban gane na ci a waje ba? Me kike nufi? Gun wata naje ta bani ko me? Mamaki ya kama Ummy tace "meye hakan? Ai kafi kowa sanin ba hakan nake nufi ba." Ai kuwa ya kara hawa wai ta rainashi, nan ya fara masifa ta inda yake shiga bata nan yake shiga ba. Haushi yasa ta fito tabar mai dakin, ajiyar zuciya tai sannan ta mike, ta fito falo. Tayi mamakin ganin masu aikin har sun gama shara suna mopping. Can tai tunanin Sagir, murmushi tai sannan ta nufi kitchen. Jalila ta hango tana aiki, da sauri ta karasa tace "Jalila?" Jalila ta juyo tace "Ummy ina kwana?" Ummy tace "Jalila? Yaushe kika tashi haka?" Jalila tai murmushi tace "kije ki zauna Ummy na kusa gamawa ma." Tace " banyarda ba bari naje na dawo dai." Ta juya ta nufi dakinta. Shikansa bai samu barcin arziki ba, dan bayan ta tafi abin duniya ya dameshi, ya rasa mai yasa yake saurin hawa akan kome ta masa wanda ya tabbatar basai wani abin bane, ya rasa meke damun zuciyarsa da yanzu duk abinda Ummy tai matar da yake ganin kimmarta a rayuwarsa bata birgeshi yanzu. Zaliha....... Duk sanda wannan sunan yazomai saurin mikewa yake yana girgiza kai, bai isa ba, ta ina zai fara yima Ummy butulci? Yasan bazata taba hanashi aure ba dan macece mai class da sanin rayuwa wacce sam batasan fada balle musu, to amma yarinya sa'ar danta? How can he? Yana kallanta ta shigo ko kallansa batai ba ta shiga toilet, can ta fito ta bude wardrobe ta dau abu zata fita. Yace "Hajiya! Ina tunanin zuwa Bauchi gobe." Tace "Adawo lafiya." Ta fita. Adawo lafiya? Ita kuwa tana fita tai kitchen gun Jalila, tare suka karasa aikin. Jalila tace "Ummy bari na hau sama." Ta fada tare da saurin yin saman. Hassan ya farka ta turo kofar dakin, kallansa tai tace "ina kwana?" Bai amsa ba, tace "bari na shirya." Ya daga kai alamar to, juyawa tai tadau towel tai cikin bandakin sanye da kayan jikinta. #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *32* Kallansa tai bayan ta fito cikin zumudi tace "Yaya na fito ka shiga wanka." Yace "in nayi wanka me zan miki? Ko dama ke kike sani yin wanka?" A ranta tace "hmm wannan mutumin?" Amma a fili tace " a'a gani nai zamu fita." Yace "zuwa inafa?" Ya fada yana gyara gadan daya kwanta dan shi kam badai gyara muhalinsa ba." Jalila da sauri ta fara tayashi ta dayan bangaren tana cewa "jiya fa kace yau zamu." Yace "yau din ta kare ne?" Baki tadan turo mai mutumin nan yake da ita? Hassan ya matso kusa da inda take a tsaye, hannu yasa ta bayanta ya dauko wani littafi sannan ya koma kan kujera ya zauna. Jalila ta tsaka sakato tana kallan ikon Allah, amma mutumin nan.... Cikin takaici ta fita waje tana wata irin tafiya, bugo kofar tai sannan tabi kofar da kallo, dama ita tasan ba lalai ya taimaketa ba. Da alama Uncle kawai zata fadama, haka ta zauna a kujera ta kuna Tv. Shikuwa tunda ta fara cika tana batsewa yake kallanta ta gefe ido, da ta fara wata irin tafiya kuwa tsayawa yai yana kallanta harya banko kofar. Mai zan gani? Hassan naga ya murmusa sannan ya girgiza kai. Shikansa bai fahimci murmushin yai ba saboda rabansa dayai murmushi ko dariya har ya manta. Amma tabas yau kam da saninsa ya kular da ita, dan ya fahimci wani sabon zumudi da takeyi. Ajiye littafin yai sannan ya mike ya shiga toilet, yana fitowa ya dauko jeans da shirt yana shirin sawa, baisan msi ya tuna ba sai naga ya cire ya dauko farin yadi mai shara shara ya sa. Bayasa hula dan haka ko dubata ma baiyi ba. Zama yai ya bude tiren data ajiye. Kallan plate biyun dake gun yai, kenan bataci abinci ba? A falo taji yunwa ta kamata ta turo kofar daki fuskarta a hade, kallanta yai sannan ya dauke kai kamar bai ganta ba. Ganinsa a gaban abinci yasa ta tsaya turus tana kallansa. Kallanta yai yace " Kin fasa zuwa ne?" Da sauri tace "zamu?" Kallan abinci yai sannan ya kalleta, da sauri ta matso tana dariya, duk yanda taso ta boye farin cikinta ta kasa. Shikam ya hade rai yana kallan ikon Allah, shi ta fara zubama sannan ta zuba nata. Dan kadan taci ta fara neman mikewa, kallansa tai taga shima kallanta yai fuskarsa a daure. Da sauri ta koma ta zauna tana kara cin abincin. Yana mikewa kuwa itama ta mike, gani tai ya koma ya zauna akan gado. Tace "Yaya na......" Kasa karasawa tai sai ta wayance tace "Yaya naga bakasha tea din ba, ko na kawoma ruwa?" Yace "later." Juyawa tai ta fita, kallanta yai sannan ya mike ya dau key din mota ya dau wayarsa. Sannan ya sauka, bata falon sama shiyasa ya wuce kasa. A kitchen ya hangota, ita da Ummy da alama wanke wanke suke. Tsayawa yai yana kallansu, bai san me take cewa ba yaga Ummy na dariya. Matsowa yai yana san yi mata magana, kuma bazai iya ba. Juyawa kawai yai yana neman komawa sama, Sagir yace "Yaya kaine a falo?" Hassan ya kalleshi sannan ya juya zai hau sama, Jalila najin ance Yaya ta juyo da sauri tana hangoshi ta tsame hannunta a ruwan dauraya tai gunsa da sauri. Ko bi takan Sagir batai ba tasha gaban Hassan tace "Yaya ina zaka?" Kallanta yai yace " fita ma inzanyi sai an tambayen?" Tace "au yahkuri, in fito?" Juyawa yai ya fita waje bai bata amsa ba, da gudu ta haura sama ta dauko hijabinta, da wayarta. Da gudu ta fito ta sauko, Sagir kallanta kawai yake, Ummy da mamaki ya sa ta tsaya tana kallansu, Jalila ta karaso gunta tace "Ummy zamu fita, na tafi karya fasa." Ummy mamaki yasa ta kasa ma magana, yau Hassan ne zai kai wani unguwa? Kallan Sagir tai da sauri wanda yai shiru yana kallan Jalila wace yaga ko kallansa batai ba tana zumudin fita da miji. Ummy tace "Sagir ka ga Hassan?" Kallanta yai ya kakaro murmushi yace "naganshi Ummy, ni kaina mamaki nake." Ummy ta fadada murmushinta tace " Sagir da alama Hassan ya fara canzawa, ko?" Sagir ya jinjina kai yace "sosai Ummy." Ummy ta juya cikin tsananin farin ciki. Jalila kam da sauri ta bude gaban mota inda yake ta shiga. Tana hakki, Hassan ya kalleta yace "meye hakan? Gudu kikai?" Tace " tsoro nake karkai zuciya." Hassan ya tada mota ya ja, suna tafi motar shiru ba komai sai sanyin AC din da ya kunna, ita ta dinga nuna mai hanya da suka shiga unguwar. Suna zuwa kofar gidan tace "nan ne, amma yaya kana tunanin zasu nuna mana inda Goggon take?" Bai kula taba yai horn, mai gadin gidan ya fito da sauri ya leka ganin Jalila yasa ya koma ya bude. Shiga sukai yai parking, sannan ya kashe motar ya kalleta yace "ki shiga." Juyowa tai ta kalleshi tace "in shiga?" Yace "ko ni zan shiga?" Tace "a'a ban dai fahimceka bane, ba tare zamu ba?" Yace " a yaushe mukai hakan dake?" Jalila ta tsaya tana kallanshi tace "Yaya kaifa kace zaka taimaken." Yace "a yaushe kenan?" Jalila yanayin fuskarta ya canza tace "Amma....." Yace " ki shiga ku gaisa, in kuka bakida niyya mu juya." Kallansa tai tama rasa me zatace " Hassan ya dau wayarsa yana duba abu." Idanunta ne suka ciciko ta bude motar ta fita, ta nufi gidan zuciyarta a dagule. Amma mutumin nan anyi mara mutunci. Shikuwa yana kallanta har ta shiga. Dady na zaune yana hada wasu takardu yana waya ta tura kofar tare da yin sallama. Dady ya juyo jin muryar Jalila. A daidai lokacin Mumy ta fito ita da Yasmeen, Mumy na rike da plate dake dauke da kayan marmari. Da yake yau asabar ba aiki. Kallanta sukai sai suka zubo mata ido, Yasmeen ta rugo da gudu ta rungumeta tana mata oyoyo. Jalila ta kalleta tace "My Yasmeen ya makaranta?" Yasmeen ta rike hannunta tana zuba mata shagwaba, nan Jalila ta dauketa. Dady ya kalleta yace "Jalila! Kece?" Mumy ma tace "Jalila shigo mana." Jalila ta shigo jiki a darare ta zauna a kasa, tana gaidasu. Mumy ta amsa sannan tace "banyi tunanin ganinki ba daga aure." Jalila ta kalleta sannan tai kasa dakai ita duk ta rasama me tazo yi. Knocking din kofa sukaji, Dady ya kalleta yace " bake kadai bace?" Kallan kofar tai da sauri tana cewa "eh tare muke." Mamaki tai dataga Dady ya mike da sauri yana kallan Mumy yace "yi maza kinsanar ma Inna." Mumy tai sama da gudu. Jalila ta tsaya kallan ikon Allah, Dady ya bude mai kofa. Hassan ya kalleshi sannan yace "sannu." Dady ya washe baki yace "shigo mana." Hassan ya shigo tare da zama akan kujera. Dady ha zauna a dayar kujerar yana cewa "ai bamu san tare kuke ba, ke kam Jalila bakyaji akan me da kika shigo baki sanar mana ba?" Hassan ya kalleshi sannan ya kalli sama wanda yaji alamar saukowar mutane. Matan biyu daya gani a gidan su yau ma su ya gani. Kallan Dady yai yace " tanata damuwa akan rashin lafiyar mahaifiyarta shiyasa nace bari muzu." Turus Inna da Mumy sukai akan kasan beni, Jalila ma da sauri ta kalleshi, Dady yace "naam? Me kake nufi?" Hassan ya zubawa su Inna ido yace " Jalila a ina Goggon take? Dan nasan bata cikin su." Ya fada yana nuna su Mumy da kai. Inna wace ranta yakai koluwa gun baci, ta kalli Jalila tana jiran me zatace, Jalila kuwa tayi mamakin kalamansa dan bata taba tunanin haka zai bulo musu gatse gatse ba. Hassan ya kallesu yace " Ina wuni?" Inna bakinta na dan rawa tace "Lafiya." Hassan ya mike ya kalli Dady yace " dan Allah a ina take? Ina sauri ne." Dady baki na rawa ya kalli Mumy da Inna yace "tana primer." Yace "wani dakin?" Dady ya kalli Mumy yace "wani dakin ne ma?" Tace "hmm...." Hassan ya kalli Jalila yace "muje ko?." Jalila tai sakato tana kallan ikon Allah. Ganin yana neman fita yasa ta mike da sauri kar a rufeta da duka tai waje. Suna shiga mota ya ja yai gaba. Jalila ta zubamai ido tana nazari akansa, can tasa wata dariya tace "Yaya kaga idon Inna kuwa?" Kallanta yai yace "wacee hakan?" Jalila tace "kaka ta? Ahh ba kakata ba kakar su Yasmeen." Hassan bai kula ta ba ya juya yana tuki, ita kuwa in ta tuno yanda sukai sai ta kara sa dariya. A haka har suka isa, suna shiga ya nemi a duba musu sunan Goggo. Nan wata nurse ta wuce dan nuna musu dakin, Hassan ya kalleta yace "ina mota." Da sauri ta riko rigarsa ta kasa tace "mota?" Kallanta yai, tace "dan Allah kuje ka gaidata. Batasan anmin aure ba fa?" Ta fada tare da canza fuska xuwa tausayi...... #Oneluv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *33* Hassan ya kara kallanta yace “kina nufin in shiga ciki?” Ta daga kai, ya kara kallan asibitin, batasan nan ma dakyar ya shigo ba? Jalila ta kalleshi tace “Yaya!” Kallanta yai sannan ya fizge rigarsa ya juya. Binshi tai har jikin motar ta tsaya a jikin kofar inda yake tace “Dan Allah yaya kazo muje.” Kallanta yai yace “ wai meke damunki? Ana abu dole ne?” Tace “i am really scared” Kallanta ya sakeyi, tace “bansan a wani hali zan sameta ba, bansan me zance mata ba in ta tambayeni, Yaya dan Allah kazo muje.” Oh God! Wannan wace irin yarinya ce? Yace “to in naje ta tambayeki wanene ni me zaki ce?” Kallansa tai sannan tai shiru, yace “ki je ki fito in kuma in barki anan ne sai ki zauna sai dare.” Jalila ta kalleshi tace “zan zauna anan din.” Yace “ ur choice.” Sannan ya kalleta yace” zan rufe kofa.” Jiki a sanyaye ta matsa daga jikin motar, ya ja yai gaba, ta glass din mota ya hangota tana tsaye inda ya barta. Bazai iya shiga ciki ba dan shikadai yasan memory din da yake dawomai in ya shiga cikin asibiti gun marasa lafiya. Jalila ta juya jiki a sanyaye, tana shiga nurse din ta tareta tace “ina yayan naki?” Jalila ta kalleta tace “a ina Goggon take?” Nan tai gaba Jalila ta bita a baya. Goggo na zaune akan gado, ba laifi kafar tata ta samu sauki sosai, tana shiga tai gunta da gudu ta rungumeta ta saki wani irin kuka. Ita ma Goggon kuka ta saka, sun dade a haka kafin Goggon ta daure tace “Jalila ina kika shiga?” Jalila ta dago ta zauna kusa da ita tace Goggo na. Goggo tasa hannu ta share mata kwalla tace “ kukan ya isa hakanan, me ya faru? Ko jikin naki ne?” Jalila ta kalleta tana girgiza kai tace “ba komai Goggo na, ya jikin naki?” Goggo ta kalleta kallon tuhuma tace “Jalila kin tabbatar? Dan nikam tsoron mutanen nan nakeyi.” Hassan har ya fara tafiya naga yayi kwana da motarsa ya dawo asibitin, bude kofar motarsa yai ya fito sannan ya nufi asibitin. Nurse din tana ganinshi ta taho inda yake, tace “ ka dawo?” Hassan yace tana ina? Nan Nurse din ta fara tafiya yana binta a baya. Suna taka steps din gaba daya kawai takawa yake, suna zuwa second floor yaji kansa ya fara juyawa, da sauri ya rike bango, sannan ya tsaya ya rike gefen zuciyarsa. Wani irin numfashi yake fitarwa, juyawa yai da sauri ya sauka kasa, nurse din ta juyo kawai taga bayanan. Hassan ya sauka da sauri ya shiga mota ya ja ya rufe ya fita da gudu. Sai da yai nisa sannan yai parkin ya kifa kansa akan sityarin motar yana maida numfashi. Jalila tai murmushi tace “Allah Goggo ba komai, kawai dai ina bakin cikin laifin dana miki ne.” Goggo tace “laifi?” Jalila ta kwantar da kanta akan cinyarta tace “ ni dai ki yafemin Goggo na.” Goggo ta shafi kanta tace “ba abinda kika min Jalila, na tabbatar ko da kin min ba daidai ba sai dai a rashin saninki ko kuma tirsasaki akai, kawai dai inaso kisan ke kadai ce dani a duniya” Jalila ta share kwallar data gangaro mata tace “ tsoron sanar dake nakeyi.” Goggo tace “ko menene ki fadamin.” Jalila tai shiru can tace “zan fada miki amma sai kin warke an sallameki.” Goggo tai murmushi tace “ shikenan, da alama akan Sagir ne.” Jalila tai murmushin yake batace komai ba. Haka ta zauna makale da Goggonta, Lantana na gefe tana kallansu gwanin sha’awa. ************* Su Hassan na fita Inna ta matso kusa da Dady ta daga hannu ta sharara mai wani wawan mari, da sauri ya kalleta dan sam baiyi zatan abinda zatamai ba kenan. Mumy ta matso da sauri ta tsaya agan Inna tace “ Inna menene hakan?” Inna cikin takaici tace “Uban wa yace ka fadi inda take?” Dady ya kalleta ransa a bace takaicinsa agaban Yasmeen dan wulakanci. Mumy ta kalleta tace “Ta ya bazai fada ba bayan yaran yasan komai, da alama Jalila ta gama sanar dashi duk abinda ke faruwa?” Inna cikin kunar rai ta zauna akan kujera tace “Akace bashi da hankali?” Mumy ta zauna kusa da ita tace “dama Bakiyi bincike ba?” Inna tai shiru kafin tace “ muna cikin tashin hankali, idanun yaran nan ba tsoro ko fargaba a ciki sannan da alama baya ragama wanda ya

Chapter 14 of 38