Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kuka san sunanshi, kallan Ummy yai yace “Ummy bari na dan shiga toilet it’s urgent.” Dariya tai tace “to a fito lafiya.” Ya juya da sauri, yana cewa gwara mu mata bayani kafin ta fada cikin mutane. Ummy tana turo kofar taji Goggo na cewa “Jalila aure kamar ya? Aure bansani ba? Auran dole aka miki?” Cikin mamaki Ummy a karasa tace “meke faruwa? Bangane aure mahaifiyarki bata sani ba, meke faruwa Jalila?” Jalila ta kalli Ummy idanunta fal tace “Ummy.” Ummy ta kalli Goggo sannan ta kalli kafarta dake ciwo, tace “muje ciki sai muyi maganar a nutse. Goggo bata musa ma Ummy ba suka shiga ciki. #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) _Should i start with sending my special greetings? Special greetings to u all my fans, thanks alot for the love and support, a sincere thanks to you all from the bottom of my heart 💕Luv u all._ *42* Ummy ta zauna akan gadon kusa da Goggo akwai abubuwan da takesan ji, sai dai ta tabbatar matarnan ba lafiya ce ta isheta ba, dan ga kafartanan. Kallan Goggo tai tace “ki kwanta ki huta dan Allah karkiyi tunanin komai har sai hankalinki ya kwanta.” Goggo ta kalli Ummy tace “Hajiya ta ina zan kwantar da hankalina, aure? Bansani ba?” Ummy ta kalli Jalila ta mata alama da ta fita, sannan ta kalli Goggo bayan Jalilan ta fita tace “ sai yanzu na fahimci me yasa yarki batada walwala duk kuwa da yanda naso ta saki jikinta da gidan nan, na fahimci an cutar dake, an munafurceki, sai dai bayanda za’ai a maida hannun agoggo baya, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, inkin huta anjima sai muyi magana, sai kiji abinda ya faru nima naji abinda ya faru, amma yanzu ko saboda ‘yarki da kwanciyar hankalinta kiyi hakuri, lafiyarki itace abin dubawa a wannan lokacin.” Goggo kallanta kawai take tana mamakin yanda mace mai kudi, mai aji, mai kyau haka take magana cikin sanyi da nutsuwa, da alama Matarnan macece mai tsananin imani, da kaunar jama’a da sanin darajarsu. Kasa musama Ummy tai ta daga mata kai alamar fahimta, Ummy tace “nagode, ga toilet nan in zakuyi amfani dashi.” Ta fada tana kallan Lantana. Goggo tace “Angode.” Ummy tai waje ta turo kofar. A waje taga Jalila a tsaye, murmushi ta mata tace “me kike anan?” Jalila ta kalleta da idanunta da sukai raurau tace “Ummy kiyi hakuri, sannan nagode....” Ummy tai murmushi tace “wanda zakima godiya daban bani bace.” Sannan ki barta ta huta zuwa anjima, amma meke damunta?” Tace “hawan jini da diabetes.” Ummy ta kalli kofar dakin cikin tausayawa sannan tace “shikenan mu barta ta huta.” Jalila ta daga kai alamar to sannan tai hanyar sama. Hannu tasa tana neman bude kofar dakin, tsayawa tai tana rike da hannun kofar amma bata bude ba, tana tunanin abinda zata cemai, da wani bakin zata fara mai godiya? A hankali tai ajiyar zuciya sannan ta tura kofar, a kwance ta ganshi kamar mai bacci, kusa dashi taje ta tsugunna tana kallansa, hawaye ne yazobo mata wanda batasan ya diga akan kuncinsa ba, a hankali ya bude idanunsa. Kallanta yai tana share hawayenta, a hankali ya ke magana yace “Menene? Wani abun ya faru ne?” Hawayenta ta karasa gogewa da sauri sannan ta girgiza kai tace “bakomai.” Yace “and why?” Tace “bansan me zance maka bane, kawai sai naji hawaye....” Idanunsa ya lumshe kansa na sarawa yace “ it looks like it’s ur hobby.” Tace “kukan?” Ya lumshe ido kawai, kallansa tai sannan tace “bakajin dadi ne?” Bai tanka ba sannan bai bude ido ba, hannunta tasa a kansa wanda ke mai ciwo kamar zai tsage, jin zafi rau akan tai, da sauri ta kai hannu wuyansa, nan ma zafi a rikice tace “Yaya bakada lafiya, zazzabi ne a jikinka, jikinka zafi.” A hankali ya bude idanu yace “why? Are u worried about me?” Da sauri tace “sosai ma, ka tashi muje asibiti.” Ta fada tare da mikewa tana kokarin dagashi, hannu tasa ta riko hannunsa tana neman dagashi. Jawo hannunta yai, ta fada jikinsa, shiru ne ya ratsa dakin, ita kuma zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, a hankali ta kalleshi, idanuwansa a rufe suke, sai cewa yai “ sai yaushe za’a daga ni?” Ta kalleshi ta kalli kanta data danneshi, neman dagawa tai sai taji hannunsa na rike da ita gam. Tace “to ai.....” Idanu ya bude a hankali ya kalleta, a hankali tai kasa da idanunta. Saketa yai ta mike ta zauna a gun, bata tashi ba tace “Yaya dan Allah muje asibiti.” Yace “bana zuwa asibiti, sannan ni nasan jikina kawai nayi abinda bansaba bane shiyasa, karki damu.” Idanu ta kuramai bayan ya maida idanunsa ya rufe, a hankali tana kallansa tace “Yaya nagode, ban taba tunanin wannan ranar ba.” Bai tanka mata ba, idanunta ne suka ciciko tace “Kayi hakuri Yaya nagode sosai har bansan ta ina zan fara ba.” Yace “hakurin me?” A ranta tace “da na dauka kai mutum ne mara tausayi da mutunci.” A fili tace “for everything.” Idanunsa ya bude a hankali sannan ya kalleta, itama kallansa takeyi, sai dai da sauri ta maida idanunta gefe. Yana kallanta yace “ya zakiyi?” Tace “name?” Idanunsa na kanta tana kallansa taga ita yake kallo ta dauke idanta da sauri, yace “ya zakiyi insu Ummy sun tambayeki?” Tace “ bansan ya zanyi ba, wata zuciyar na sanar dani in fadi komai, wata kuma na tunanin abinda zai faru da Dady dan na tabbatar Inna bazata barshi ba.” Kamar bazaiyi magana ba, dan harta mike zata nemomai maganin zazzabi ragowar tata wanda takaima Ummy taji muryarsa yace “ kiyi abinda ya kwanta miki a rai.” Juyowa tai ta kalleshi tace “In na tuno abinda yama Goggo tundaga haduwarsu zuwa yanzu, sai naji kome zai sameshi bazan damu ba sai dai bansan meke damuna ba, I wish nima inada dauriyar zuciya ko rabin taka ce.” Alama yamata da hannu akan ta matso, matsowa tai gunsa, ya mata alama data kara matsowa, nan ma ta matso takai kunnenta saitin bakinsa, a hankali yace “in fada miki sirrin?” Kai ta daga da sauri, yace “kisa Goggonki a saman komai.” Abinda ya fada kenan yai shiru tare da juya mata baya ya rufe idanunsa, tsayawa tai tana kallansa me yake nufi? Tace “yaya!” Shiru yai baice komai ba, itama shiru tai tana tunanin me yake nufi. Ta dade a tsaye kafin ta daukon mai maganin, ta dauko ruwa a karamin fridge din dake dakin, tazo kusa dashi tace “Yaya tashi kasha magani.” Bai bude idanunsa ba, ganin bashi da alama ne yasa ne ta kara cewa “Yaya Please, ko in fadama Ummy?” Idanunsa ya bude yace “wato kina neman kiyi amfani da weakness dina ko?” Dariya tai tace “ inkaki tashi yanzu sai na sanarma Ummy.” Yace “eh lalai kinga gadon bacci na...” Ta kuntse dariyarta tana nunamai gadan da yake kwance akai, harararta yai sannan ya mike zaune ya fizgi ruwan hannunta ya mikamata dayan hannun ta. Zubamai maganin tana dariya. Sha yai sannan ya kwanta. ********** Ummy na shiga falon Abba ya kalleta yace “meke faruwa? Nifa na kasa gane abinda ke faruwa.” Tace “ni kaina bansani ba sai dai na tabbatar Hassan yasan me yakeyi, kafi kowa sanin halinsa a da can inyai abu ma to akwai dalili, daga baya kuma da matsala ta faru gaba daya ma yadaina shiga rayuwar kowa inba tasa ba, kaga yanzu dayai abin nan kasan zuciyata dadi takeji dan na fara ganin Hassan dina na da na shirin dawowa.” Abba yai murmushi yace “na fahimta sannan nasan wanene Hassan, sannan ni koma menene ya faru ba wani abun dan ni dama ita na gani sannan ni ita na zaba, ko da a lokacin zasu nunamin wata ba lalai zuciyata ta amince da ita ba.” Ummy tai murmushi itama tace “ maybe suna tunanin sun cuceta ne da alama sunyi bincike akan Hassan..........” Karar wayar hannunta ne yasa ta kalleshi, kashe kiran tai sannan ta kalleshi, yace “ Sim dina na wayarki ne?” Tace “eh, da na cire sai kuma nai tunani kar san zuciyata yasa wasu dasuke nemanka ko na taimako ko na aiki suyi ta nemanka, shiyasa nasa Sim din a wayata.” Shiru yai tare da maida kansa gefe can yace “Kiyi hakuri.” Tace “ kadaina fadar haka, kaddara ce ta zo mana, sai dai mu roki Allah akan ya taimakemu yasa mu wuce kaddarar nan.” Abba yai shiru bai sake cewa komai ba...... ********* A can gidan Inna kuwa, Dady cikin takaici ya dawo gida, bakin cikinsa ko waya bai fita da itaba bare yasa a zo a daukeshi, rabansa da taxi haryamanta amma haka yahau ransa a bace. Yana isa gida ya wuce daki cikin zafin rai, Mumy dake kitchen tana bada umarnin abincin da za’ai ta taho da sauri ta shiga ciki. A tsaye ta ganshi tace “Abban Yasmeen lafiya?” Juyowa yai rai a bace yace “ kinsan yaran nan......” sai kuma yai kwafa. Ta matso da sauri tace “ya kukai? Yadauke Goggon Jalilan?” Yace “ya dauketa mana, yaran nan yana abu kamar shine gaba dani, kinga yanda yake wulakantani, amatsayina na uban matarsa?” Mumy tai shiru can tace “nikaina yaran nan yaban tsoro, wai garin yaya kukaba Jalila yaran nan? Bakusanshi ba? Na dauka kunyi bincike.” Cikin masifa yace “bincike? Abinda Inna ke bada umarni mu ina mukaga ta cewa?” Mumy tai tsaki tace “ai gashi nan ta ja mana masifa, ita kanta yanzu abun ya dameta, gashinan abinda take tunanin samu ma ba samu zatai ba, wanda take dashi ma yana neman wargajewa.” Dady yace “wai yaran nan ni zai kalla yacemin wai inada kudi a jikin? Sannan ya mikon wai 1000 wai na hau mota shi bazai kaini ba?” Mumy tace “mene?” Yai kwafa cikin takaici yace “ni nama rasa ma me zance, kamar ni????” Mumy ta rungumeshi tace “cool down Dadyn Yasmeen, zamu san mafita, bari Mu sanar ma Inna.” Yai tsaki cikin takaici, tace “Safeena ta kira, ta isa Paris lafiya.” Yace “Wai paris taje dama?” Tace “eh can Inna tasa a nemar mata skul.” Yai shiru baice komai ba.... Inna gaba daya tunda Hassan ya fita ta kasa tsaye t kasa zaune gaba daya ta kasa samo mafita, cikin takaici ta kira Sani tacimai mutunci akan kin yimata binciken daya kamata akan Hassan kawai yacemata bashida lafiya alhalin bai bincika wani irin ciwo na kwakwalwa yake ba.... ************ Kuka Zaliha take sosai tana cema Yayarta ita wlh kome zata yi tayi amma itafa kawai ta aura mata Taura in ba haka ba wlh barin gidan zatai ta shiga duniya... Hankalin yayarta ya tashi tace “ kar ta damu dan dole zata koma Niger.” #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *43* Inna tana zaune tananin mafita Mumy ta banko kofa da sauri, Inna ta kalleta tace "naga sanda hankali zai ratsaki ki daina buga kofa haka, yarki ta kai a mata aure amma haryanzu inkina wani abu kamar karamar yarinya." Mumy ta zauna da sauri tace "ni Inna ki bar fadanki zuwa anjima yanzu akwai matsala." Gaban Inna ne ya fadi ta kalleta tace "Abakar ya dawone?" "Ya dawo sai dai yaran ya dauke Goggo" Inna tai shiru hankalinta ya tashi, ta kalli Mumy tace "yanzu kenan da alama sunsan komai ko?" Mumy tace "me zai hana? Shiyasa Inna ni dama na kasa gane dalilinki na......." Wani kallo data mata ne yasata yin shiru, Inna tace "kinsan menene yake bakantamin rai?" Bata jira amsartaba tace " rashin wayau da auna tunaninki, daga ni har mahaifinki munada saurin tunani da kwakwalwa amma ke ni bansan ina kika dauko ba, da farko kince yaran ubanki zaki aura yaran da ko A bai sani ba lokacin, dole da ganin bamuda wani da bayan ke yasa muka jure, sannan kikasan wannan yaran ya munafirceki ashe har aure gareshi, amma tsabar rashin kwakwalwa kika dage ke sai shi, sannan abin bakin ciki duk yanda nai dake akan kiyi aiki a company din da muka gina nida mahaifinki amma kinki, kin dage sai dai mijinki yai, sannan yanzu kice me?" Mumy tai kasa dakai sannan tace "Inna wai dan Allah sai yaushe ne zaki amince da Abakar daro bisa dari? Mutumin nan na miki ladabi wanda ko ni bana miki, sannan ya a sona san da ba wanda yakemin irinshi..." Inna tai tsaki tace "ni tashi ki bani guri nasan mafitar data dace damu dan zamanki anan bakomai yake karamin ba sai bakin ciki." Mumy ta mike tai waje rai a bace.... Inna tai shiru tana tunani kafin ta dau waya ta kira Abakar. Yana zaune a falo Mumy na gefensa itada Yasmeen, Sultan na daki yana ganin kiranta gabansa ya fadi ya kalli Mumy yace da alama Inna tagama shawara. Mumy tace "muje tare." Yace "karki damu ki zauna bari naje." Nan ya mike yai sama......... ********** Inna ta tashi tayi wanka, Ummy ta kawo mata kayanta tace ta saka, dan itakam ta kula kayan dake jikinta da wanda aka dauko a leda san ba magana, itada Jalila ne sukaje BQ dan ganin yanayin gun. Jalila ta kalli Ummy tace "Ummy kije ciki zan gyara." Ummy tai murmushi tace "Jalila ko dai ince masu aiki gidannan sundinga kwana ne?" Jalila tace "saboda me?" Tace "da alama aikin gidan ya karu, sannan zai yi yawa, tunda akwai bangarensu ina tunani gwara mu tambayesu, in zasu dinga kwana to, in kuma bazasuyi ba kinga sai mu samo wasu." Jalila tai shiru can tace " Ummy gani, ga Lantana ina tunanin ba wani abu." Ummy tai murmushi tace "baki fahimceni ba kenan." Jalila ta mata kallo mai alamar tambaya tace "ban....." Ummy tai dan dariya tace "so nake kibama Hassan kulawa 80% dan na kula ina hanaki kula dashi." Jalila da sauri ta juya tana tattare kaya dan kunya, Ummy ta sake dariya tace "ko nayi sankai?" Jalila tace "a'a kawai ta cigaba da aikinta. Ummy ta kalleta tana murmushi, Lantana ta kira suka gyara gun, Ummy tace "gobe sai a siyo gado da kayan bukata a sa a ciki, wai gadan ciki ya tsufa, da Jalila zatai magana Ummy ta harareta wanda yasata yin shiru. Sageer kuwa a daki hankalinsa duk ya tashi tabbas Goggonta ganshi a lokacin dan har gaisheta yayi, to amma tagane tsakaninsu? Malam Sagir ashe da raban zan ganka. Kalaman Goggo ne suka dawo mai, ajiyar zuciya yai cikin tashin hankali yace " ba zama bane ya dace dani." Mikewa yai ta budo kofar dakinsa a hankali ha sako kai, yana leke. Bakowa a falon, komawa yai ciki ya zauna yana tunanin abinyi, can ya daure ya fito a hankali yai falo, Ummy na zaune rike da littafin addu'oi ya shigo. Ta kalleshi tace "Sageer fitowarka kenan, tun rana sai yamma?" Yace "Ummy ina matar Yaya?" Tace "Jalila? Tana BQ suna aiki, ta dage sai na taho, ya akai? Nemanta kake?" Yai murmushin dole sannan yace "eh, bari naje can." Ummy tace "to, amma Sagir karka tambayeta maganar mahaifiyarta, da magrib in anyi sallah za'a zauna a falon Abbanka." Yace "to Ummy sannan yai waje. Tana kwashe shara ya tsaya a bakin kofar yana kallanta. Kallansa tai sannan ta matso inda yake jiki a sanyaye. Kallan dakin yai, ya kalli Kofar Toilet inda Lantana ke wankewa. Yace "Jalila!" Yace "Uhmm" Shiru suka danyi dan they are uncomfortable in suna tare ba kamar da ba. Can ya daure yace "Goggonki, sanda mukaje asibiti....." Sai a lokacin itama abin yazo mata, ta kalleshi da sauri tace "Ta ganka ko?" Yace "kin manta har gaisawa munyi?" Tai shiru tana kallansa, yace "Jalila, zaki iya mata magana? Dan banasan kowa yasan abinda ya faru a baya." Jalila ta kalleshi tace "ince me? Ince Goggo yayan Uncle nake aure? Ko ince Goggo karki fadama kowa irin san da nakema Kanin mijina? Ko ince Goggo da naso Uncle ashe kanin mijinane?" Yace "Jalila ya kikesan juya maganar da na fada ne? Me yasa bakya yima kalamai na kyakyasar fahimta?" Idanunta ne suka ciciko tace "Uncle ni to ya zanyi? Me zance? Kamar yanda kake tsoron matsala ta afko a dalilinka, matsalar da zata sa hankalin iyayenka su tashi ni kaina a yanzu bana san ace nice silar wargaza farinciki Ummy da Abba, dakai kanka da yayanka, Uncle bansan....." Kasa karasawa tai saboda kuka dake neman zuwa mata dan muryarta ta fara rawa. Sageer yai shiru yana kallanta cikin tausayawa yace "Nafahimceki Jalila, na kuma gode da kaunar da kikema Family na, Please ko Goggonta tambayeki kawai kice mata sunane yazo daya, mu barshi kawai a haka." Ta daga kai, kawai dan batasan itakam me zata kuma cewa ba... Bayan sun gama aiki tai wanka a toilet din ta maida kayan jikinta ta hau sama. Yana kwance yana bacci ta shiga a hankali ta dau kaya ta saka, sannan ta matso kusa dashi ta sa hannunta akansa, jin ba zafi yasa tai murmushi. Da alama yau ma ciwon nasa da sauki, dan bacci yake hankalinsa a kwance. ********* Bayan magrib kuwa Ummy ta kalli Jalila bayan sun gama girki tace "Jalila inkin kaima Goggon ki ajiye sannan ki kaita falon Abba zamuyi magana." Tace to, sannan ta dauki Abincin Goggo, tana shiga dakin ta zauna kusa da Goggo tare da kwanciya a kafadar ta tace "Goggona!" Goggo ta kalleta tace " kin gama gudun?" Jalila tace "gudun me?" Goggo ta tureta daga kafadarta tace "kindauka bansan guduna kike ba? Kar na miki tambayoyi? Shiyasa tunda kika fita kikaki shigowa?" Jalila ta tuntsire da dariya tace "ni? Wlh ba haka bane aiki mukeyi ne bakiga Lantana ma batanan ba?" Goggo tace "ba wani." Jalila fa kara kwanciya a kafadarta tace " Ummy tace inkaiki falon Abba, anan zakiji komai." Tace "kaini dan ni kaina so nake naji." Nan suka fita tare, sai data kusa kaita falon, suna tafe tare sai ga Ummy tace " Jalila barta zamu shiga tare." Ta matso kusa da kunnenta tace "ki je ki lalabo mijinki." Jalila ta kalleta, Ummy tai murmushi sannan ta nuna mata sama da kanta. Jalila ta kalli saman sannan ta nufi matatakalar, anya zai fito kuwa? Gashi bashida lafiya. Kofar dakin ta tura ta shiga, yana kan sallaya yana karatun kur'ani. Zama tai a bakin gado tana jiransa, bai dade ba yakai ayar karshe ta cikin suratul maryam, yana neman dauko wata surar ne dan izu daya yake yi a duk tsakanin sallar magrib da isha'i tai saurin cewa "Yaya!" Tsayawa yai bai fara wata surarba sannan bai juyo ya kalleta ba, tace "Yaya za'ayi maganar." Ya juyo yace "magana?" Ta kalleshi tace "maganar nan.... ba Abba yace sai anjima ba?" Yace "and so?" Tace "shine za'ayi yanzu ka sauko." Yace "in me?" Tace "ka sauko, muje tare." Yace "kinsan me kike cewa? Nine zan sauko inje inda kowa zai zauna ayi magana?" Kallansa tai tai raurau da ido, yace "ki tashi kije, ni ba nayi nawa part din ba? Saurab ya rage naki." Haryanzu kallansa take da idanun kafin tace "Yaya Please" Juyawa yai ya bude kur'ani zai dora daga inda ya tsaya. Da sauri ta sauko ta bayansa ta rike gefen rigarsa ta kafadarsa. Juyowa yai yace "wai........" Bata jira me zaice ba tace " yaya dan Allah ka taimaken, ba wai wani abu zakace ba, inka zauna agun ma ya isa." Yace "in zauna?" Tsugunawa tai ta gefensa tace "Dan Allah yaya." Hade rai yai ya juya, tace "kan ne?" Ya mata shiru, tace "yahkuri yaya, na sani ina takura maka, sannan ina takura maka da neman yin depending akanka akan komai na rayuwata, kayi hakuri nasan bana kyautawa." Ta mike tai waje, a falo ta tsaya tai ajiyar zuciya sannan tace " who do u think u are?" A hankali ta fara sauka daga matatakar, jiki a sanyaye. A falo kuwa Abba da Ummy na zaune daga bangare daya, Goggo na dayan bangaren Jalila ta shigo. Tana shigowa Sageer ya shigo, tunda ya shigo Goggo ke kallansa, inata san fuskar nan? Abba ne ya katseta da cewa "yaki saukowa?" Ta daga kai alamar eh. Jiki a sanyaye ta zauna a kasa kusa da Goggo. Sageer ya zauna a kasa kusa da Abba. Falon ya dan yi shiru kafin Abba yai gyaran murya yace "Sannu da zuwa mahaifiyar Jalila, muna baki hakuri akan abinda ya faru wanda mu kanmu bamusan takamaimai abinda ke faruwa ba, sai dai ina neman sanin dalilin dayasa ba wanda yasan da zamanki a gidan, sannan dalilin dayasa aka munafircemu mu dake akan auran nan, Jalila yar muce a yanzu shiyasa nake san sanin menene ke faruwa takamaimai." Goggo tace "nagode da karamawa, sai dai a yanda nasan mutanen nan ba damuwa sukai damu ba ina mamakin yanda akai suka kawo Jalila cikin gidan karamci irin wannan." Abba yai murmushi yace "mun gode da karamawa, Jalila inaso ki sanar damu abinda ke faruwa." Jalila ta kalli Abba, ta kalli Ummy sannan ta kalli Sageer. Ummy tace "duk wani abunda kika sani muke sanji, wannan shikadai ne abinda zaisa musan abinda ya dace muyi, kada ki munafurcemu, kada ki munafirci mahaifiyarki." Jalila ta kalli Goggo. Turo kofar da akai ne yasa suka kalli kofar, Hassan ne ya shigo. Kallan Jalila yai wacce itama kallansa takeyi, a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda yana ganin haka ya dauke kansa daga kallanta sannan ya nufi can gefe ya zauna akan kujera shi kadai. Goggonta kalleshi, wannan shine na dazu...... ******** Inna ce ta kalli Dady tace "take all the blame." Kallanta yai cikin mamaki yace "ban gane ba?" Tace "kace kaine kai komai, dama matarka ce da yarka, kaga kome kai dama kaine me hakki akansu, wannan shikadaine hanyar dazamu kwaci company dinmu." Dady yace "ni na kasa fahimta, kenan nine na shirya duk abinda ke faruwa?" Tace "eh ko dama nice na shirya? Ina naga matsayi? Matar data tsufa???? Dady yamata wani kallan tsantsan mamaki........ #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *44* Jalila tai ajiyar zuciya sannan ta kalli Goggo tace "sanda na sameki a bangaren su Dady akwance ba lafiya........................." Haka ta kwashe komai ta sanar dasu, gaba daya falon yayi tsiy saboda tsananin tausayin abinda kunnuwansu yakeji, Hassan na zaune ya kwantar da kansa a saman kujera, idanuwansa na lumshe kai kafe bai san me ake cewa a falon ba, sai dai gaba daya zuciyarsa a karye take da abinda kunnuwansa keji, wannan wace irin rayuwa yarinyar nan tai? Wani irin rashin imani ne hakan? Hannunsa ya matse guri guda cikin tsananin takaici. Jalila ta karashe maganar tana kuka tace Goggo banasan wani abu ya sameki shiyasa na kasa fadamiki, sannan suma sunce min karna sanar dake..... Goggo tana kallanta idanuwanta na zubar da kwalla ta jawota jikinta ta rungume Jalila ta saki wani kuka mai ban tausayi, Goggo tana hawaye tana shafa bayanta tana cewa "kiyi hakuri Jalila duk nice na ja miki abinda suka miki." Ummy ma gaba daya hankalinta ya tashi, tausayin su ya kamata. Sageer kam ba'a magana dan baima san hawaye yana gangaromai ba, sai dayaji ruwa a kuncinsa, ya goge da sauri yana kallanta. Ummy ta kalli Abba wanda yai shiru yana nazarin abinda ke faruwa, kenan bayan yaga Jalila yace yanaso su bawa dansa a matsayin matar Hassan shine sukai bincike akan Hassan, da sukaji bashida lafiya shine suka hadashi da ita, to ina asalin yar tasu? Dan ya fahimci akwai wata. Kallan Jalila yai yace "ya isa haka Jalila, su ne suke tunanin sun cutar dake suna ganin sun yaudare mu, amma ni da matata basu yaidaremu ba ko kadan dan ni dama ke nagani sannan ke kika kwantamin a rai, haka itama ke ta gani sannan ke kika kwanta mata a rai, anci mutuncin mahaifiyarki a matsayinta na wacce ta haifeki ta shayar dake sannan ta reni bai kamata ko menene ba a aura da 'ya bada sanin mahaifiyarta ba." Ummy cikin zafin rai tace "ai muma sun ci mutuncinmu taya zasu nuna mana sune suka haifeta bayan mahaifiyarta daban, tayana dan rashin imani zasu aurar da yarinya mahaifiyarta na kwance ba lafiya? Sannan suyi amfani da rashin

Chapter 19 of 38