yaya sai da muka shiga cikin store din nan naji cikina yana wani kara?"
Nan ma baiko tanka mata ba, ta amshi ledar ta ajiye a kusa da ita sannan ta kalli Ameera datai shiru tana danna wayarta.
Itama jan bakinta tai bata sake cewa komai ba.
Suna isa gida Ameera ta fito da sauri saboda tsoron kar reshe ya juye da ita.
Jalila ta zauna ba alamar fita, kallanta yai yace "me kikeyi?"
Tace "Yaya kaima kasan ba kaifina bane, tuntube nai sannan wlh bawai kula bane banayi"
Yace "kinji nace wani abun?"
Tace "bakace ba amma......"
Ya katseta "sauka inkuma bazaki shiga ciki ba sai ki kulle motar inkin gama zaman."
Kallansa tai ranta yadan sosu ta fito daga ciki ta duba boot ta dauko ragowar ledojin sannan tai ciki.
Kallanta yai harta shiga ciki sannan ya dan saki huci yace " ba saboda ke raina ya baci ba saboda kaina ne."
Idanunsa yadan rufe da hannunsa kafin ya fito daga motar.
Ummy najin motsin shigowarsu ta fito daga dakinta tana cewa "Jalila kun dawo?"
Ameera ce ta taho da gudu ta rungumeta, Ummy tai dariya tace "Auta saukar yaushe?"
Ameera ta kalli Jalila tace "tare muke dasu Yaya Jalilah."
Ummy ta kalli Jalila wacce ta karaso tana cewa "da ita muka je ai Ummy."
Ameera ta kalli Ummy cikin zumudi tace "Ummy kinsan waye ya kaimu?"
Ummy ta kalleta, Ameera ta kara matsowa tace "Ummy karkiyi mamaki........."
"Hassan kun dawo?" Abinda Ummy tace ne yasa Ameera saurin boyewa abayanta, Hassan yace "eh Ummy."
sannan yace "Abba fa?"
Ta nunamai falo tana kallan Jalila wacce tana tsaye yazo ya wuce kamar baiganta ba.
Hassan ya wuce falo, Ameera ta kalli Ummy da sauri tace "Ummy kingani? Ummy yaya ne yake magana haka."
Ummy ta kalleta tace "naji hajiyar magana, akwai baki a dakinki kije ku gaisa."
Ameera tace "baki? Su waye?"
Ummy bata tanka mata ba ta matso kusa da Jalila tace "Jalila wani abun ya faru ne?"
Jalila tai yake tace "bakomai Ummy, Kinga kayan da Yaya ya sai mata."
Ummy ta kalli ledar tace "basai kin ciro ba, angode Allah ya saka masa da alkairi."
Jalila tace "Ameen."
Muryar Abba sukaji yana kiran Ummy.
Ummy ta falo, Jalila kuma ta dau leda tai dakin Ameera.
Hassan na zaune kusa da Abba ta shigo, ta zauna sannan ta kallesu tace "d'a da uba ne suke hirar yaushe gamo?"
Abba yai murmushi yace "nikaina ina jiran wannan lokaci, lokacin da Hassan zai zauna dani muyi hirar duniya."
Hassan bai tanka musu ba, Ummy tace "wani abun ya faru ne?"
Yace "a'a kawai dai sirikarsa ce ta nemi mu barta ta tafi tana kunyar zama gida daya da sirikinta da mu."Ummy tace "hakane munyi laifi da bamuyi wannan tunanin ba, sannan bamu tambayeta ra'ayinta ba."
Hassan ya kalli Ummy yace "Ummy ita so take takoma kauye nikuma ina ganin hakan ba solution bane."
Tace "mekake tunani?"
Yace "gwara a nemarmata gida anan ta zauna karami, can yayi nisa."
Murmushi tai ta kalli Abba tace "gaskiya kam yama Jalila nisa wanda zai sata damuwa."
Kare tsuke fuska yai yace "Ummy me kike....."
Katseshi tai tace " ni ba da komai nake nufi ba."
Abba ya kalleta yace "wani abun kike tunani?"
Tace "a'a shawararce naga tayi, me zai hana a gidan da ka siya kwananan wanda ke tarauni a maidata can? Naga gidan karami ne sannan ga yarinya ma mai kula da ita."
Abba ya jinjina kai yace "hakan ma shawara ce, kinga Allah ne yasa bamu sa haya ba dan har an fara tambaya, Hassan sai ka dau Jalila kunduba gidan sai a sai abunda ya kamata."
Yace "to."
Bai jira wani abu ba ya mike, yanasan yama Abba godiya sai dai bakinsa bazai iya furatawa ba, harya kai kofa ya juyo yace "Ummy na hau sama."
Tace "to Hassan."
Ya juya ya fita, Ummy ta kalli Abba tace " Ya kagani?"
Murmushi yai yace " tunda na dawo kullum Hassan sai ya bani mamaki, lalai dolene muje muyina doctor godiya ba shakka shawararsa itace babban magani a tattare dashi."
Ummy ta sake yin murmushi.....
Jalila kuwa tana shiga daki inda Goggo take ta hau nuna mata kaya, Ameera kam tana gefe tana mamaki, kenan mahaifiyarta ce ta asibitin nan? Me yasa a lokacin bata nuna mata itace mahaifiyarta ba? Goggo ta kalli Jalila tace "Jalila garin yaya kika barshi ya kwaso kaya haka? Kudi fa aka sa aka siya."
Ameera tai dariya tace "Goggo ashe ke tayo, shiyasa takasa bari na dau kaya ko daya wai tsada, sai da yaya yazo."
Goggo ta kalli Ameera tace "ke kuwa yar nan ina zan kai kayan nan?"
Jalila ta kalli Goggo wani abu ya tsirga mata na tausayi, tunda Goggo take bata saka kaya masu tsada haka ba, ba ta tana samun kaya kwatan yawan wannan ba, gaba daya kayanta......."
Idanunta ne suka ciciko ta kalli Goggo tace "yaya ya fadamin abinda kikace."
Tace "ya sanar dake?"
Jalila ta daga kai, Goggo ta riko hannunta, Ameera tai saurin fitowa daga dakin.
Goggo ta kalli Jalila tace "Jalila kiyi hakuri, nasan burinki ma shirme nasan ganin mun zauna tare bayan kinyi aure sai dai ko a da can jinki nakeyi dan bazan iya zama da sirikina ba."
Jalila ta daga kai alamar ta fahimta dan batasan tai kuka.
Goggo ta kalleta tace "shiyasa a koda yaushe ake cewa Allah ba azallumin bawansa bane, Jalila ban taba tunanin zakiyi aure cikin gata irin wannan ba, gaba daya mutanen gidan nan zuri'ace ta albarka, dolene mu gode ma Allah akan baiwar daya miki ta samun dangin miji irin wannan."
Jalila ta kalleta idanunta suka zubo da kwalla, Goggo tai murmushi tace "nikam wannan yaran kanin mijinki....."
Da sauri Jalila tace "oh Ya Sageer? Oh Goggo kinsanshi ne?"
Kallanta tai taga ba wani alama ta wani abun tace "a'a na dai ganshi a asibiti."
Jalila tace "oh haka ne."
Sundanyi hira kafin ta mike ta fito.
Tunda ta shiga daki taganshi a kwance ta fito ya dawo falo ta zauna, yunwa ce ta sata shiga dakin a hankali ta dauko tiren abinci ta fito falo taci ta zauna tana danne danne a waya, daga baya ma ta sauko kasa sukai girki ta koma gun Goggo sukai hira da Ameera.
Abincin ranarsu ma data kai taga yana kwance ta diba ta fito falo taci ta koma kasa sai da suka gama abincin dare ita da Ameera sannan ta dauko nasu ta hawo sama.
Yanzu kam a kasa ta ganshi kan sallaya yana karatu, gefe ta koma ta zauna tana sauraran kartun nashi, tana lumshe ido saboda dadi, tana bala'in sha'awar taga tana rera karatunn qur'ani haka.
Hassan na nan zaune har aka kira isha'i sannan yai sallah, itama tai.
Sai binshi take da kallo tanasan tamai magana amma ba fuska.
Mikewa tai ta zubo mai abinci tace "Yaya ka sauko kaci abinci."
Kallanta yai yace "ban dade dacin na rana ba."
Ta mike daga zaman datai a kasa ta matso kusa dashi jikin gado tace "Yaya dan Allah menene? In laifi na maka dan Allah kayi hakuri."
Idanunya kura mata, a ransa yace "me kika min? Haushin kaina nakeji da duk abinda zanyi tun dazu sai naji kina raina, haushin kaina nakeji nasan na ganki kusa dani, haushin kaina nakeji na rashin sanin abinda ke damuna a kanki."
Jalila ta kalli yanda ya kafe ta da ido kana gani kasan tunani yakeyi, tace "Yaya?"
Littafinsa ya dauka baice mata komai ba.
Tsayawa tai shiru kafin ta zauna taci abincin nasa data zuba, kadan ta iyaci dan ya mata yawa.
Har dare Hassan bai kula ta ba, itama haushi yasa ta dauke kai daga kansa tai kwanciyarta, kankace me bacci yayi gaba da ita.
Kwanciya yai ta saitinta yanda yana hangota daga kan gado, ya kura mata ido, what are u to me?
Gani yai tayi juyi ta juya mai baya.
Mikewa na ga yayi ya dau pillow dinsa ya kwanta akan kujera yanda zai ganta dan kusa da kujerar take shimfida.
Ajiyar zuciya yai ya kalli bargon data shimfida yace "wannan bazai sata ciwon baya ba? Kullum kwana a kasa? Gata ba jiki ba?"
(Nikuwa nace waye ya sata🤨)
Ya dade a haka yana kallanta har bacci ya daukeshi.
Yauma Alhamdulila bai farka da ciwo ba, wajen asuba ya farka, da sauri ya mike yana mamakin kansa anan ya kwana? Ahh wai Hassan hankalinka daya kuwa?
Alwala yai sannan yazo kusa da ita, ya saba sa kafa ya tasheta yau sai gani nai ya sunkuyo yasa hannu yadan bugi kafadarta tare da cewa "Jalila?"
Idanu ta bude cikin bacci ta kalleshi, mikewa yai.
Ta mike itama tai alwala...........
Tunda ta tashi take jinta ba dadi, ba sabon abu bane tasan period dinta ne ya kusa, ita kuma gashi duk sanda zatai al'ada sai tasha azaba na ciwon mara, a gida Goggo sai ta sata tasha dauri, ko ta siyo panadol......
***********
Inna ce tasa aka kira mata dady, yana zama mumy ta shigo taja ta zauna.
Inna tace "Fatima meye hakan? Magana zamuyi."
Mumy tace "kome zakuyi kuyi agabana, sannan nima magana nazo fadamiki."
Inna ta kalleta tace "maganar me?"
Tace "kiba Abubakar mukamin Chairman na company ke kiyi resigning, dama ai kin dade kina cewa zaki bani ke kuma ki sauka."
Inna ta kalleta cikin tashin hankali sannan ta kalli Dady wanda shima yai alamar wai mamaki, tace "Abakar kai ka zigata?"
Da sauri Dady ya kalleta yace "Menene hakan? Ce miki nai inasan shugabanci na company din? Meyasa kike neman sa Inna taga kamar nine nake saki abu? Banasan irin wannan abun."
Mumy ta kalleshi tace "Dadyn Yasmeen."
Ya hade rai yace "Taya zaki yanke hukunci ba tare da kin sanar dani ba?"
Tace "gani nai...."
Inna ta kalleshi lalai yaran nan me? Ce miki akai inasan shugabanci?????
Tai wani murmushin takaici.......
#Oneluv💕
[12/7, 9:53 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔️ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
*48*
Ummy ce ta kalli Jalila tace "Jalila lafiya? Naga tau kamar bakyajin dadi?"
Tace "lafiya ta kalau Ummy."
Ummu tace "da ina tunanin ko in dau Goggo da Ameera muje dakanmu mu siyo kayan gidan muje a saka, kamar zaifi dan nasan halin Hassan bazai shiga gun kayan ba, kinga kuma ke kadai abin bazai yiwu ba, sai da babba."
Jalila tace "to Ummy."
Ummy tace "ko kinfiso kije da kanki? Ko mu tafi tare?"
Da sauri tace "a'a wlh Ummy hakan yafi, ni me na sani a wannan harkar?"
Ummy tai murmushi ita kuma bataso subar Hassan shikadai dan Abba ya fita duba wani aiki.
Jalila tace "me za'a dafa da rana?"
Ummy tace "komai ma duk abinda miki."
Jalila tai murmushi sannan tace "to Ummy nagode Allah ya saka da alkairi."
Ummy ta kalleta cikin kulawa tace "Hassan fa?"
Jalila tace "yana daki."
Ummy tace "nasan yana daki ai haryanzu bai sauko ba?"
Jalila tace "Ummy kema harkin gane? Ni na rasa me namai."
Ummy ta guntse dariyar dake neman zuwa mata tace " da alama dai kin mai babban laifi tunda har nima na gane."
Jalila tai ajiyar zuciya tace "na kasa gane me namai, kuma shima ya ki fadamin."
Ameera da ta fito tasa dariya tace " ba kunya?"
Jalila ta kalleta sannan tai saurin mikewa, sai yanzu ta fahimci bai dace ba.
Ummy tasa hannu ta rikota ta makama Ameera harara tace "to uwar sa ido, menene damuwarki? Ni bana sirikanta da ita 'ya ta ce."
Ameera ta kara yin dariya tace "hmm nayi shiru ai."
Ummy ta kalleta tace "kicema Goggo ta shirya zamuje wani guri."
Ameera tace "ina zaku bani?"
"Ko shirya dake zamuje kema, in muka sai kayan farko sai ke da Lantana da Goggo akaiku gidan ni da Sageer sai mu karasa siyan abinda ya kamata."
Ameera tace to, tai ciki da sauri.
Haka suka shirya Jalila na kusa da Goggonta, Goggo sai tambayarta take wai ina zasu? Itakam Jalila cewa kawai take nima ban sani ba Goggo.
Haka suka fito Sageer ya daukesu a mota, Jalila ta baishi da kallo duk ya canza da dai ba haka tasan Uncle ba, mutum ne faran faran dasan tsokana, yanzu kuwa ya rage sannan duk yadan rame.
Tana tsaye har motar tasu ta bar gidan sannan ta dawo ciki.
A falon kasa tadan kwanta dan mararta ciwo take mata daurewa kawai takeyi, mikewa tai can ta hau sama dan tana san shiga toilet.
Hannu tasa ta bude kofar dakin dakin ta shiga, yana zaune a kasa yana cin abinci da alama baima dade da tashi ba.
Tana shigowa ya kalleta, itama kallansa tai ta tsaya sannan tace "Yaya ka tashi?"
"Umm, dazu." Ya fada idansa na kanta, ta dan tsaya kafin tace "hmm su Ummy sun fita tare da su Goggo."
Yace "okay."
Tadanyi shiru kadan sannan tace " duk tare suka fita."
Yace "nagane, kina nufin daga ni sai ke kenan ko?"
Tace "hmm can gidan zasu."
Yace "duk na fahimta."
Juyawa tai ta nufi toilet kafin ta kara juyowa tace "Yaya!"
Ya kalleta tace "abincin bai huce ba?"
Yace "me kikesan ji? Da alama wadannan maganganun naki akwai abinda kike san ji."
Tace "bakomai." Ta shige toilet.
Da kallo ya bita ya dade kafin yacigaba da cin abincin.
Tana fitowa yana gama cin abincinsa, tadan tsaya a jikin kofar saboda ciwon da mararta yakeyi gashi daga bayanta yake tahowa.Da kyar ta taka ta zauna akan kujera tadan tukunkune.
Mikewa yai daga kasa ya juyo ya kalleta, bai kawo komai a ransa ba ya dauka dai kwanciyar tai ko toilet din data shiga ne ya sa ta.
Komawa yai ya zauna ya dau littafi, dan nishin datai kadan ne yasa ya juyo da sauri ya kalleta.
Yace "Jalila!"
Dagowa tai ta kalleshi a hankali tace "naam."
Ganin haka yasa ya sauko da sauri yazo kusa da ita inda take a kwance, kusa da inda kanta yake ya zauna sannan yasa hannu ya dagota.
Kallanta yai itama ta kalleshi yace "menene?"
Tace "bakomai yaya..."
Yace "menene kikeyi to hakan?"
Tace "me nayi?"
Idanu ya kara kura mata sannan yace "menene? Karkisa na sake tambayarki."
Ta kalleshi tace "marata"
Yace "ciwo?"
Ta daga kai alamar eh.
Yace "kinayi ne ko yau ne kika fara?"
Tace "inayi dama."
Shiru yai yana kallanta yace " menstrual pain?"
Kallansa tai sannan ta saukar da idanta kasa.
Yace "ko muje asibiti?"
Tace "a'a yaya zai daina zuwa dare."
Idanunta tadan runtse dan abin karuwa yake yi.
Sa hannu yai ya dagota ya kawota jikin gado yace "kwanta."
Kallansa tai sannan ta kwanta.
Zama yai kusa da ita yana kallanta, ita kuma idanuwanta a runtse suke tasa hannunta kan kasan cikinta.
Wayarsa ya dauko ya shiga google ya rubuta how to relieve menstrual pain.
Nan ya shiga dubawa, kallanta yai sa hannu ya gyara mata kwanciyarta zuwa rubda ciki.
Juyowa tai ta kalleshi yace "menene?"
Kai ya girgiza alamar ba komai sannan ta gyara kwanciyarta.
Shiru yai yana tunani, massage lower back and abdomen? Ta ina zai iya?
Mikewa yai tsaye da sauri ya koma kan kujera ya zauna dan jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri.
Jalila kam abin ne ya kara motsawa juyawa tai ta kara dukunkunewa tana dan nishi kadan.
Kallanta yakeyi sai dai hankalinsa duk ya tashi.
Ya mike ya taso kusa da ita ya gyara mata kwanciyarta zuwa na dazu, idanunta ne suka ciciko ta kalleshi tace "yaya hakan bayamin dadi."
Yace "na sani daurewa zakiyi."
Tace to sannan ta gyara kanta tana runtse ido.
Jitai hannunsa akan kasan bayanta inda yake mata ciwo, kallansa tai, ya kalleta shima fuska a hade yace " ki kwanta ba wani abin zan miki ba."
Shiru tai ta kwanta, janye rigarta yai yana neman kaita wajen kirjinta, da sauri tasa hannu ta rike sannan ta kalleshi.
Kallanta yai idanunsa na kanta ya sa hannu ya zare mata hannunta, shiru tai tana kallansa.
Sai dayakai rigar saman cikinta sannan ya tattareta a gun.
Hannu ya saka a bayanta yana mata tausa da hannayensa suka biyun.
Idanunta ta rufe gaba daya jikinta yai sanye, Hassan kam tausa yake mata sai dai daurewa kawai yakeyi.
Kallanta yai yace " kinajin sauki? Naga haka suka rubuta haka akeyi."
Ta daga kai idanunta a rufe dan bazata iya kallansa ba.
Hassan ya cigaba da yi mata, tun tanajin abin har bacci yai gaba da ita.
Ganin alamar bacci takeyi yasa ya kalleta, kusa da ita ya matso ya sa hannu akan gefen fuskarta yadan shafa kadan, meyasa kike sani yin abubuwan da ban taba tunani ba?Ganin motsin idanunta sun canza da alama nauyin baccin nata ya fara raguwa, komawa yai ya sa hannu ya cigaba da yimata.
Sai can ya tsaya ya kalleta tana bacci hankalinta a kwance, murmushi yai wanda shikansa bai sani ba.
Sannan ya mike ya cire kayansa ya daura towel ya shiga wanka.
Bai dade ba dan yana tunanin karta tashi, a hankali ya bude kofar ya fito ya zo zaisa kaya.
Wayarta ce tai kara da sauri ya matso ya dauka, number Ummy ce ya daga a hankali yace "Ummy."
Cikin mamaki tace "Hassan?"
Sageer dake kusa da ita ya kalleta, Ummy tace "Hassan kaine? Ina Jalilan?"
Yace "bacci takeyi bata danjin dadi ne."
Da sauri tace "lafiya? Me ya sameta?"
Yace "ba wani abun bane Ummy sako ne?"
Samun kanta tai da wani murmushi tace "a'a bakomai kace kartai abinci ta kwanta ta huta."
Yace to ya kashe wayar.
Da kallo yabi wayar sannan ya kalleta, me nakeyi hakan?
Ajiye wayar yai ya zo ya saka doguwar riga ta jallabiya sannan ya zauna akan kujera ga dau littafi wanda ya kasa karanta ko layi daya.
Sai kallanta da yakeyi, duk motsin datai a kansa.
Can ya daure ya koma ya maida kansa kan littafin, motsinta yaji, ya mike ya zauna a bayanta ya dan fara yi mata tausa a gun.
A hankali ta bude idanunta kallansa tai, yace "kin tashi?"
Da sauri ta kalleshi tace "yaya, bansan nayi bacci ba wlh yahkuri."
Mikewa yai tsaye yace "ya jikin?"
Tace da sauki sosai, yace "ki tashi ki sake wanka amma yanzu kiyi da ruwa mai zafi, sannan kisha ruwan tea black ne."
Tace "to."
Juyawa yai da sauri ta riko rigar jallabiyarsa.
Juyowa yai ya kalleta, yace "menene?"
Tace "yaya nagode, sannan kayi hakuri."
Shiru yai yana kallanta, yace "kin gode dame?"
Tace "taimakon dakamin."
Yace "karkiyi tunanin wani dalili ne yasa na taimakeki, I really hate naga wani bashida lafiya, ko wanene na gani cikin wani hali ko ba ke bace zan taimaka mai."
Kallansa tai jiki a sayaye sannan ta sakar mai rigarsa, ai dama batace dan ita special bace, me yasa wai yaya baya magana da sanyi?
Ta dan saukar da idanunta tace "nasani, duk da hakan nagode, sannan kayi hakuri da laifin da bansani ba."
Ya sake kallanta yace "nagane tashi kiyi abinda nace, kina mace amma bakisan menene zai taimaki lafiyarki ba, na rasa me yasa gaba daya baki damu da kanki ba."
Jalila ta kalleshi tadan canza fuska zuwa shagwaba tace "to ni ya zanyi?"
Yace "ba ni zaki tambaya ba."
Ya juya ya zauna.
Mikewa tai tana mamakin yanda taji sauki, dan ta saba in har ta fara da safe to fa sai dare, in kuma da daddare ta fara sai safiya.
Dan ma tayi sa'a tanajin yanayin nan ta sanar ma Ameera ita kuma ta bata pads, ta boye a cikin basket na laundry din dake cikin toilet din.
Ruwa mai zafi tasa ta gasa jikinta ji tai jikinta ya sake warewa ta tsaya a toilet din, sanye da toilet, taya zata fita? Shiyasa fa daga ta tashi takeyin wanka in kuma batai da wuri ba sai ta bari ya fita takeyi, tunowa tai jiya daya ganta tana sa bra.
Shiru tai tana tunani, ta kalli kayan data cire wanda tasa a ciki basket din laundry.
Ganin ba yanda zatai ne yasa tadan bude kofar kadan ta leko kanta.
Shikuma yana jin alamun bude kofarta ya kalli gun.
Suna hada ido ta komar da kanta.
Mikewa yai dan ya fahimceta.
Agoggo ya kalla, yaga azahar tayi ya mike ya tada sallah.
Ita kuma tana komawa ciki ta jingina da kofar toilet din, massage din daya mata dazu ta tuno, da sauri ta girgiza kai.
Sake lekowa tai taga yana sallah, a hankali ta fito tazo jikin wardrobe ta bude ta zura hijab.
A cikin hijab din tasa bra sannan ta zura skirt ta sa riga sannan ta cire hijab din ta matso jikin madubi ta shafa mai sannan ta fesa body spray da turare.
Kallansa tai yana zaune akan sallaya ta lalaba tai waje.
Tana sauka ta hada tea kamar yanda ya sata tasha, sannan ta koma kitchen ta bude fridge ta dauko nama zata sa tafashe.
Bayan ta fita ne yai tunanin yanzufa sai ta tafi sa abinci ko?
Mikewa yai ya sauko kasa, kitchen ya nufa, ya taka ciki ya shiga.
Raban da Hassan ya shiga cikin kitchen shikansa ya manta, ko magana zaiyi sai dai ya tsaya daga falo, ko kofa.
Juyowa tai jin motsin shigowa, kallansa tai cikin mamaki tace "yaya!"
Me zance? Abinda zuciyarsa ta tambayeshi kenan.
Hade rai yai yace "ruwa zaki bani."
Tace "ruwan sama har ya kare?"
Yace "a'a ba sanyi ne."
Cikin mamaki ta mikomai robar ruwa tana cewa ko na kashe fridge din?
Mikamai ruwan tai yasa hannu zai amsa, kan hannunta hannayensa suka taba, kallansa tai shima ya kalleta.
A hankali ta zare hannunta ta dan juya.
Ya amshi ruwan kafin yace "me kike? Ke da ba lafiya ba?"
Tace "abinci zanyi kaga ba kowa a gidan."
Yace "dan ba kowa sai akace mara lafiya yai abinci?"
Ta juyo tace "ba haka nake nufi ba, kaga sanda zasu dawo ne a gajiye zasu dawo."
Yace "in ance bakya kula da lafiyar ki kice ba haka ba, to Ummy ce tace karkiyi."
Ya juya ya bar kitchen din.
Da kallo ta bishi, tadan yi ajiyar zuciya tace "oh ni, yanzu ma laifi na sakeyi?"
Maida namantai cikin fridge din sannan ta fito.
A falo ta sameshi tace "Yaya!"
Ya kalleta yace " kin warke ko na kaiki asibiti?"
Tace "Allah na warke har mamaki nakeyi."
Ya juya ya hau sama.
Shiru tai tare da binsa da kallo.
*******
Ummy kuwa tana kashe waya ta saki wani murmushi, Sageer ya kalleta yace "Ummy wani abun ne?"
Tace "a'a bakomai, kawai dai abin ne kemin dadi, dan na tabbatar yanzu Hassan ya fara san matarsa."
Sageer ya kalleta wani abu ya ratsomai, ya daure yai murmushi yace "ai Ummy ki daina damuwa na tabbatar Yaya zaiso Jalila yanda bakya zato, tanada halayen da zaija ra'ayinsa."
Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace "sosai ma, na yarda dakai Sageer."
A tare sukai murmushi Ummy tace "ya kukai da Goggo dazu?"
Sageer yace "ai bakiga kukan datake ba nidai har na taho tana kuka akan itakam da munbarta ta koma kauye ina ita ina wannan gida haka?"
Ummy tai murmushi tace "Sageer in na tuno abinda mutanen nan sukayima Jalila da mahaifiyarta sai naji kamar bai kamata mu kyalesu ba."
Yace "hakane Ummy koni abin na damuwa, bansan haka tai rayuwa ba."
Ummy tace "nikaina, sai dai mu barma Allah komai."
A ransa yace "bansani ba Jalila, bansan haka kikasha wahala a rayuwa ba, i am really sorry......."
*******
Suna saukowa Dady ha kalli Mumy yace "mumyn Yasmeen me kikeyi hakan?"
Rungumeshi tai tace "ba sai ka shiga maganar nan ba, wannan shikadai ne hanyar da zaisa Inna tadinga ganin girmanka."
Dady ya dago ya kalli sama, inna ya gani a tsaye tana kallansu, murmushi ya mata sannan ya kankame Mumy tare da sa kansa a wuyanta.
Inna ta dunkule hannunta sannan ta juya, snake yanzu kake nunamin abinda ke boye a kasan zuciyarka, u really try na yanda ka boye fuskarka a cikin mask ba wanda ya fahimci abinda ke tattare da ita.
Tace sai dai ka makaro dan kana tafin hannuna wlh.
(Nace damuwarki😏)
#OneLuv💕
[12/7, 9:53 PM] El-hajj: *JALILAH* 🗯
Written By : *AYUSHER MUHD*
✔️ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
(_D home of expert and perfect writer's_💡)
*49*
Goggo tana zaune tana kara bin gidan da kallo, hawayenta yaki tsayawa, ashe alheri ne a dukulle a tattare da sharrin da aka jefesu dashi.
Ba wani katon gida bane, falo daya ne babba sai 2bedrooms a cikin falon da toilet daya.
Sai tsakar gida kato wanda za'a iya ajiye motoci kananan guda biyu.
Ameera da Lantana dake sa labule ta kalla tama rasa ta ina zata fara, ashe a rayuwa akwai rana irin wannan? Shiyasa mutane ke cewa Allah yasa muci darajar 'ya'yan mu, a da bata fahimtar abinda ake nufi da hakan amma yanzu ta gane dalilin fadan hakan, in kai a rayuwa bakai sa'ar abokin zama ko iyaye ba sai ka nemi sa'a akan 'ya'yanka.
Hawayenta ta share, ko mahaifiyarta da mahaifinta nada rai?
Haka su kai ta aiki, itama tana tayasu, sai yamma su Ummy suka dawo, sun siyo abin kitchen, tv set, toilet, abinci da sauransu, dama zuwan farko aka siyo kujeru, gado da labulaye.
Haka suka taho musu da gashashiyar hanta da juice suka ci suka sha, Ummy ta nunama Goggo kawai komai ta samu tayi. Hamdalla bawai taita kuka ba, hakan yasa ta saki jiki sukaci abinci tanata godiya.
Sai wajen Magrib suka kammala komai, Ummy tace su tafi, sai asa ranar tarewarta.
Goggo tai shiru tana tunani, Ummy ta matso tace "lafiya? Ko kina tunanin zama ne gaba daya?"
Goggo tace " indai hakan zai samu nafisan hakan, dan maganar gaskiya kunyar gidan nakeyi.
Ummy tace "shikenan ai ba wani abu bane, in har hakan yafi kwanta miki a rai, sai dai kamar ba'a gama jan wutar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 38