Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta mike tana zarya a tsakiyar dakin. Safeena na shigowa ta zari mayafinta tace mata ina zuwa. Fita tai ta hau motar da aka kawo Safeena dan daka drivern ya shigo duba Inna, tace mai gidan Jalila. ************ Hannunsa yasa a cikin kasan rigarta tasa hannu ta rike hannunsa tare da cewa "Yayah?" Yace "wai abin haryanzu bai wuce ba?" Tace "menene bai wuce ba?" Yace "gashinan gaba daya sai wani mazewa kikeyi, kindai san na fiki iya hade fuska ko?" Ta kalleshi tare da cewa "nifa ba hade fuska nake ba." "Ohh tafiya ne bakyasan yi dani ko me?" Tace "Allah ba haka bane Yaya kawai dai bansan yanda zan sauka kasa bane, nasan yanzu Abba ya fadawa Ummy." Yace "ikon Allah! To sai me? Ai ko bai fadaba ni zan fadamata." Cikin shagwaba tace "haba yaya?" Yace "to naji bazan fadaba, Abban ya fada mata shikenan?" Ta kalleshi kamar zatai kuka, da alama Yaya bazai gane ba, agoggo ta kalla tace "oh ya kamata na sauka kasa fa." Ta fada tana neman saukar da kafarta daga kan gado, Yaya ya jawota tare da cewa "yanzun ma fitar za'ai a barni?" Cikin zolaya tace "ko zamu tare? Sai ka tayani?" Ganin yanda ya tsaya yana kallanta yasa tai dariya tare da rufamai bargo ta mikomai littafi tace "malam mai karatu ai karatu dayawa." Ta mike ta fita tana dariya, Yaya kam birgeshi tai, gani nai ya mike ya zura doguwar riga kawai ya sauka. Jalila kam sam batai tunanin zai kawo wani abun a ransa ba, kitchen ta nufa, yau kam tai sa'a Ummy bata fito ba, dadi ne ya kamata ta wuce kitchen tare da tunanin abinda za'ai breakfast dashi. Jan nama ta dauko ta shiga wankewa, sannan ta fara yanka albasa tana dan kankane ido. Jin hannu ta bayanta yasa gabanta ya fadi, a tsorace ta juyo yanda ya riketa yasa tana juyowa ta juyo daf daf da fuskarshi, sumbatarta yai yace "na sauko, da me zan tayaki?" Kallan kofa tai sannan ta kalleshi cikin mamaki tana kokarin zamewa tace "Yaya!" Yace "da me zan tayaki?" Tace "tayani? Yaya in wani ya ganmu fa?" Ta fada tana dan zamewa, yace "ohoo naga ke kika ce na sauko?" Baki ta bude tace "wasa fa nake maka kaima ka sani." Yace "wasa? To ya akai ban sani ba? Sannan banaji kema kincemin wasan nan kikeyi." Baki ta bude tana kallansa tace "lalai yaya, me zance in su Ummy suka ganka anan?" Yace "me zakice kuwa? Kawai mijinki ne yake taimaka miki." Dariya tasa tace "a haka sauki fada." Yace "a can din ma sauki zai.....yi" Yai maganar yana kara jawota, tace "Yaya Allah kar Ummy ta fito." Sumbatar wuyanta yai yace " wasa wasa da ke matsoraciya ce." Tace "naji, nayi surrender, ayi hakuri, hanuna a sama." Ta fada tana daga hannayenta. Murmushi yai sannan ya saketa tare da bude fridge, sannan ya rufe yace "yanzu a haka zan tafi?" Tace "hmm dan Allah yaya jeka ko falo ne,wallahi bansan ya zanyi ba in wani ya ganmu anan." Baki ya tabe sannan yace "za'asan an koreni wallahi." Ya juyo tare da hade fuska. Da sauri tace "yaya?" Tsayawa yai fuska a hade, ta matso ta dan daga kafafunta ta sumbaci kuncinsa, tace "sorry!" Kallanta yai fuska a hade yace "wannan karan wannan bai isa ba." Ya fita, kallansa tai tana murmushi har batasan tasa wuka a kusa da bakinta ba sai dataji warin albasa sosai yasa tai saurin sauke hannunta tana dariya. Yaya ma yana fita yadan harari kitchen din sannan yace "chance din ramawa ya samu." Yana kokarin bakin falon Sageer na fitowa, kallansa yai yace "Yaya? Daga ina?" Yace "hmm na fito gaida Ummy ne naga batanan." Sageer Yace "oh wallahi da sassafe suka fita itada Abba, sunje Bauchi, ka duba wayarka har text ta maka kai da Jalila." Yace "Bauchi? Wani abun ya faru ne?" Yace "wallahi ban sani ba, inaji dai zasu je gun dangin Baffanane, sannan kila akwai abin aiki da ya kaisu daga nan." Hassan yace "Shine baka bisu ba?" Sageer yace "kasan halinsu, in Ummy taje sai sun mata gori, gwara ni naje daga baya." Hassan ya jinjina kai yace "Hakan yayi, kace kai kadai ne a gidan kenan?" Yace "hmm amma nima anjiman nan zan fita zanje office din Abba akwai abinda ya sani." Hassan a ransa yace "kenan sai mu kadai?" Amma a fili yace "hakan yayi, ya kamata ka dinga fita ko ka samoma Ummy wata surikar tunda dai kaga ni tafiya zanyi." Sageer yai dariya yace "kar ka damu an kusa." Hassan yace "haba? Ka gano wata ne?" Sageer ya matso sai tin kunnensa yace "na gano amma bansan ko inada chance ba." Hassan yasa dariya zaiyi magana sukaji ana knocking din kofa. Sageer ya karasa ya bude. Mumy ce tsaye a gun, Sageer ya kalli Hassan sannan ya kalleta. Ganin haka yasa Hassan din matsowa. Kallan mamaki ya mata kafin yace "Bismillah." Mumy ta shigo jiki a sanyaye. Abinda takeyi hakan ya dace kuwa? Anya kuwa ta kyautama Abubakar? Zama tai a kasa sannan ta kalli Hassann da Sageer. Hassan ya kalleta yace "lafiya?" Kallansa tai sannan ta hada hannayenta biyu tace "Hassan ku taimaki Inna ta da ni kaina da kuma Mijina, ku duba girman Allah. Bawai abinda muka aikata ba ku taimaki rayuwarmu." Yanda take magana da karfi yasa Jalila lekowa. Ganin Mumy yasa ta tsaya tana kallanta, Hassan ya kalleta sannan ya kalli inda Jalila take, Sageer ka ya kalleshi. #OneLuv💕 [12/30/2018, 10:07 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *71* Mumy ta kalli Hassan idanunta sun ciciko, idanunta duk sun koma kalar tausayi, ta kara daga hannunta alamar tsananin neman taimako, tama kasa magana sai hannunta kawai datake ta murzawa. Hassan kam Jalila ya kafa ma ido yana kallanta, wacce tai tsuru tana bin Mumy da kallo. Sageer ne ya kalleshi yanda yaga yana kallan Jalila ne yasa yace “Yaya?” Hassan ya kalli Sageer sannan ya kalli Mumy, daurewa yai yace “meke faruwa?” Mumy ta kara kallansa idanta duk ya canza zuwa tausayi, kallan inda Jalila take tai a hankali tace “Jalilah?” Jalila wacce gabanta ke ta dukan uku uku tana tsoron kar ace wani ya mutu, tsoron matsowa takeyi, Mumy ta kara cewa “Jalila!” A hankali Jalila ta fara takowa zuwa inda take, tana tafe gabanta na wani irin faduwa, kusa da Hassan ta matso ta tsaya a hankali itama tace “Mumy menene?” Mumy ta kalleta tace “Jalila ki rokarmana mijinki da mahaifinsa su taimaka su dakatar da mahaifinki.” Cikin rashin fahimta ta kalleta tace “dakatar dashi kamar ya?” Nan mumy ta kwashe abinda ke faruwa ta sanar musu sannan ta dora da cewa “bawai hanashi company din nakesan yi ba, dan ni a gurina yafi kowa dacewa daya mulki company din, sai dai ina tsananin tsoron kar san zuciya ya jefashi cikin wani halin, sannan bansan me yake kitsimawa a ransa ba, ance yanata duba takarda a gida, da farko ban kawo komai a raina ba sai dai bayan na taho ina hanya na fahimci me yake nema, takardun gidan da muke ciki yake nema, dan dama tun shekara uku da suka wuce nasa aka canza sunan gidan daga sunana zuwa nashi, saboda na kwantar mai da hankali, kenan korar mu zaiyi daga gidan, ni duk na rasa me Abubakar yake kitsimawa a kwakwalwarsa.” Hassan wanda ko kadan baiyi mamaki ba yace “yanzu halayen mijinki kike sanar mana anan? Ko kuma halin da kuke ciki ke dashi?ni na kasa fahimta.” Mumy tace “Hassan ka dubi girman Allah ka taimaka mana, na tabbatar in wani abu ya samu company din Inna wallahi mutuwa zatai.” Yace “Rai a hannun Allah yake, in lokacinta yayi banaji ke ko ni mun isa mu dakatar dashi.” Ya fada tare da juyawa ya wuce sama. Mumy ta bishi da kallo kafin ta matso kusa da Jalila, hannunta ta riko tace “Jalila?” Jalila ta kalleta, idanunta sun ciciko itama, Mumy tace “Jalila na san bamu kyauta miki ba ko kadan, ke da mahaifiyarki, mun wulakantaku daidai wulakanci, sai dai inaso ki dubeni ta fuskar fahimta bawai dan ke akayima ba, a’a ki dubeni a matsayinki na mace, ya zakiyi idan wanda kike masifar so rana daya yazo miki da mace sannan da tsohon ciki? Ya zakiyi in mijin da kike masifarso ya nemi ku barsu su zauna a muhallinki? Ya zakiyi in kikaga mijin naki baisan darajarsu ba, basu isheshi kallo ba bare ya nuna damuwarsu akansu?” Jalila tai shiru tana kallanta, Mumy tashare kwallarta tace “Nasani bazaki fahimceni ba, na kuma san ban kyauta muku ba daga ke har Goggonki ko da Abakar bai nuna damuwarshi akanku ba ni kuma baikamata na maidaku kamar masu aiki ba, sai dai Jalila ki dubeni a matsayin ba kowa ba, dan Allag ki ceshi mai neman bukata, Jalila Inna tana cikin wani mawuyacin hali.” Jalila tai shiru tama rasa me zatace muryar Sageer taji yace “ Please in kin gama ki fita.” Shima ya wuce ciki dan shikam gani yake ko kadan basu cancanci a taimaka musu ba. Mumy ta kalli Jalila ta kamo hannunta tace “Jalila!” Jalila ta daure tace “Mumy zan shiga ciki.” Ta karasa tana dan zare hannunta. Jalila ta juya zata tafi,muryar mumy taji “Safeena ta dawo.” Cikin mamaki Jalila ta juyo ta kalleta tace “ta dawo daga Abujan?” Mumy ta girgiza kai tace “ba abuja taje ba, fita da ita abroad mukai karatu sai dai alhakinki ne inaga yasa gashi ta dawo ba karatun ba kuma jin dadin, ta fita a banza mun kashe kudi a banza sannan me makon ta dawo cikin farinciki ta dawo cikin kunci.” Jalila tai shiru tana kallan Mumy, kafin Mumy tace “kinga yanda rayuwa take Jalila, a da bamu daukeki a komai ba, yar mu kawai muka sani yanzu gashi kece a matsayin komai, ki duba darajar da Allah ya baki, ki rokarmana Sirikinki da mijinki su taimaka mana.” Jalila tai shiru, sai dai ya zatayi? Ko da ace naman jikinta suka dinga yanka, yan uwanta ne, duk duniya batada kamar Safeena, Sultan da Yasmeen, dan jini ba wasa bane. Yanda Mumy ke kara rokarta ne yasa tace “bari na mai magana, sai dai ko da wasa Mumy karkisa ran zasuyi abinda kikeso, ni dai zan yi iya nawa ne, ba kuma dan kowa zanyi ba sai dan Allah da darajar yan uwantaka.” Mumy ta hau gyada kai tana cewa “nagode Jalila, nagode.” Jalila ta shiga kitchen ta rage gas sosai sannan ta fito tai sama, Mumy ta bita da kallo, rayuwa kenan, wai su da sunyi tunanin cutar da ita sukai, sun killace tasu, sai gashi ashe daukakata sukai, hawaye ne ya kara taruwar mata sai yanzu hankalinta kadan kadan yake kai mata manufar Abakar, yanzu kam ta fara tantama ma in har yana santa. Jalila ce ta tura kofar dakin, yanna zaune yana latsa waya ta shigo, kusa da kafarsa ta zauna dan yadan jasu sama. Sa kanta tai saman gwiwoyinsa, ta dan karkato da kanta gefen da wayar take tace “Yaya! Shine ka gudu ka barni?” Kallanta yai tare da ajiye wayar yace “Bansan me zance miki bane, shiyasa na taho.” Ta dan rufe baki kadan kafin tace “me zaka cemin kamar me?” Yace “mahaifinki ne, me zance?” Kanta ta kwantar akan gwiwar tasa kafin tace “mahaifina ne sai dai tunda nake dashi Yaya ban taba zama dashi munyi maganar mutunci ba, duk maganar da zata fito daga bakinsa zakaji san zuciya ne da tsantsan san kai.” Hassan yai shiru yana mata kallan tausayi, murmushi tai kafin tace “ sai dai Yaya duk yanda naso na gane na kasa fahimta.” Ya mata kallan rashin fahimta, tace “wani irin uba ne Dady? Yaya duk yanda naso na kasa gane wa.” Fuskarsa ya sa ko kusa da tata, yace “wanda baisan baiwar da Allah ya mai ba?” Tace “baiwa?” Kiss ya mata yace “baiwar yarinya kamarki mana.” Idanu ta kankance tana kallansa kafin tace “ahh yaya.” Murmushi yai kafin yace “yau kinsan mu biyu ne a gidan nan?” Murmushi tai sannan tace “kafin mu zama mu biyu kadan taimakamin kadan.” Name? Tayaki breakfast din zanyi? Ya fada yana dan kamo gefen cikinta. Dariya tasa tace “kai Yaya!” Yace “ba su bane?” Tace “ka taimakeni kar Dady zuciyarshi tai nisan da bazata taba waiwaye ba.” Yace “kamar ya?” Tace “banaso mahaifina idanunsa ya rufe, ina tsoron halin da zai afka, baya tunanin komai sai kansa, shiyasa nakeso a dakatar dashi haka daga kan san kansa da yakeyi, ya fahimci yanada responsibility’s da kuma abinda yafi shikansa daraja.” Yace “yanzu me kikeso ayi a tsayar dashi?” Tace “dan Allah ka taimaki Mumy, hakkinsu ne company din nan, mahaifinta da mahaifiyarta sune sukasha wahala gun ginashi, taya Dady zai zo lokaci daya ya nemi kwacewa? Bayan na tabbatar da yayi hakuri Mumy yanda take sanshi da kanta ma zata bashi, kaga alama ce ta san zuciyata da tsantsar burin rayuwa ne yake damunsa, wanda ya rufemai ido daga taimakon da aka mai, yake ganin kamar komai ya cancanta ne shiyasa ake mai?” Hassan ya sa hannunsa yaja kumatunta kamar wata baby sannan yace “ohhh wannan babyn da alama ta mike tsaye.” Bai saki kumcin nata ba ta shiga kokarin magana tana cewa “Yaya Please!” Dariya yai yanda tai maganar yace “to ni kinsan bansan kan harkar ba, ta ina zan taimaka miki?” Tace “ muje mumy sai tama bayani, lokaci yana kurewa.” Yace “Hmm umm.” Cikin shagwaba yai tasa dariya tace “da alama in an gama wannan zan kara nema amin abin nan.” Fuska ya hade yace “haka kawai ina murna zamu zauna mu biyu yanzu kuma kinzo da wani zance daban?” Tace “sry yaya.” Ajiyar zuciya yai sannan yai gaba. Da kallo ta bishi sannan tai murmushi, bin bayansa tai. Kasa suka sauko Mumy nata amsa waya tanata magana da Sani. Tana ganinsu ta kashe wayar tare da gyara zama. Hassan ya sauko kofar Sageer ya nufa tare da yima knocking. Sageer da ya bude kofar ya kalleshi. Hassan yace mai “Sageer dan fito plx.” Fitowa yai tare da rufe kofar. Jalila kam na saukowa kitchen ta nufa kawai ta cigaba da harkarta. Duk da hankalinta nakan abinda ke faruwa a falo sai dai ta sa wa ranta abu daya, duk abinda Hassan ya yanke kawai yayi, dan bazata tilastamai akan abinda bayaso ba. Mumy ce ta kalli Hassan wanda yacemata “fado abinda kikeso ayi muji.” Nan Mumy tamai bayani kamar yanda Sani ya mata, tace “duk yanzu kudin dake running a company din 80% kudin Mahaifinku ne, hakan yasa kuna da hujjar kwatar company din kuba wanda kukeso in har bamu biyaku kudin da kuke bin mu ba.” Sageer yace “amma contract din ai kamar lokacin biyan nada tsayi.” Tace “eh, sai dai nunawa zamuyi kamar abin yazo.” Hassan yace “nuna wa zamuyi? Har a yaushe muka zama mu?” Mumy tace “bada wani abun na fada ba, kuyi hakuri dan Allah.” Hassan ya kalleta sannan yace “na kasa fahimtar wani abu, in an amshi company daga hannun mijinki wa kikeso a ba?” Tace “ni kaina bawai so nake ba, saboda koda wasa ban taba burin mulkar company din nan ba, ni kaina shi nakeso aba sai dai bata wannan hanyar ba.” Hassan ya mata wani kallo dan shikam ya dai jitane. Yace “Sageer ya kake gani?” Sageer yace “bari na kira Abba muyi discussing.” Ya fada tareda mikewa. Ganin za’a barsu su biyu yasa ya mike ya shiga kitchen. Ta banyanta ya tsaya tana soya yankanken kayan miya akan frying pan. Tana ganinshi ta juyo tana kallanshi. Karasowa yai ya sa hannunsa ya zagayo da ita ta cikinta ya kwantar da kansa a kafadarta yace “kallanfa?” Tace “ya kukai?” Yace “kawai dai.” Murmushi tai kafin tace “Thanks alot Yaya.” Yace “banasan wani thanks kawai zanbi bashi ne dan sai an biyani.” Murmushi ta sakeyi tace “da alama bashin nan nawa karuwa yakeyi dayawa.” Sumbatar wuyanta yai yace “da alama zamu dan barki a gida ke kadai na dan wata awa daya.” Kai ta daga alamar gamsuwa ba tare da ta tambayeshi ba. Saketa yai sannan ya wuce sama, wanka yai yasa kananan kaya sannan ya sauko, Sageer ya tarar a falon Abba yana rike d wasu takardu yana kuma waya. Yana ganin Hassan yamai alama dayazo, nan sukai magana su biyu kafin su fito falo. A tare suka fita, Mumy ta shiga motarta suma suka shiga motar Sageer. Suna shiga Hassan yace “haka Abba yace?” Sageer ya shiga yimai bayani, Hassan ya jinjina kai alamar gamsuwa yace “shikenan.” ************* Ba wani kato bane main branch din nasu, sai dai dayake ajiyar kayan abinci sukeyi daga baya akwai wani tangamemen fili da akai gini inda ake aikin a ciki. Sani na ganinta ya taso da sauridan dama yana zaune a waje yana jiranta, tanna karasowa ya matso da sauri yace “sun shiga cikin meeting din kamar minti 5 da suka wuce.” Mumy ta matso ta sanarma Hassan. Dakin babban taro na hadaka suka nufa, suna zuwa Sani yasa aka bude dakin. A lokacin kuwa Dady ne tsaye yana bada speech dinsa na yanda company dinsu wai ke cikin matsalar da suke san akawo mafita dan a kwatota daga ciki, Babban director din yace “Bravo! Gaskiya duk company din nan ba wanda yake sanshi da kula dashi kamar kai, shiyasa nazo da babban shawara akan sauke Hajiya wacce girma ya kamata yasa take neglecting din aiyukanta, a baka kai sirikinta wanda ka sadaukar da komai naka akan company din mu.” Muryar Sani sukaji yace “Investors din da suka taimaki company dinmu sunzo.” Kowa kallan su ya juyo yai, Mumy ta zubama Dady ido wanda gaba daya shima idanunsa na kanta. Hassan ya matso inda Dady yake yace “will you please get down?” Dady ya kalleshi zuciyarsa gaba daya ta rage bugawa yanda ya kamata, Hassan ya kalli Sageer yamai alama dakai akan ya matso. Sageer ya kalli Dady wanda yake saukowa kamar wanda bashida ragowar laka a jikinsa. Sageer ya fara bayani kamar yanda Abba yamai. Takarda ya zaro ya daga sama yace “wannan shine contract din da mukai da company dinku akan za’a biyamu 50% na kudinmu a kwana uku da suka wuce. A cikin wannan contract din munyi bayani time da kuma kudin da za’a fara biyanmu. Sai dai jiya mun nemi Chaiwoman din company din me makon ta bamu sai ma taki daukan wayarmu, wannan dalilin ne yasa muka sauko kasan contract din wanda yace “in har ba’a biyamu kudin mu akan lokaci ba rabin company din zai dawo namu.” Nan fa kowa ya fara kananan maganganu, Sageer ya kallesu yace “ saboda haka daga rana tayau zan zama nine shugaban company din nan har zuwa ranar da za’a biyamu kudin mu.” Nan fa guri ya kachame da kananan maganganu. Hassan kam abin ya birgeshi wani irin dadi yakeji a ransa, lalai ilimi rahama ne. Hannu ya daga ya yima Sageer jinjina. Dady kam ji yai gaba daya wata muguwar zufa na ketomai ta ko ina. Wani daga cikinsu ne yace “ta ina zamu yarda da abinda ke faruwa?” Sageer yace “da farko ga signing din Chairwoman din nan sannan ga yartanan zatai duba, dan tana nan akai komai, sannan zan miko muku ku gani kuma.” Mumy wacce gaba daya dana sani ya gama kamata, jikinta duk ya gama yin sanyi, meke faruwa? Itakam ai ba haka sukai ba, ta dauka ko ita zasu barikon kwarya kafin ta samu Dady ya dawo hankalinsa, ya kamar take ganin anyi amfani dasu? Haka tace ai komai daya fada daidai ne sannan aka mikama kowa ma ya gani, nan fa ba yanda suka iya aka ba Sageer kujerar shigabanci ya zauna akai. Dady kam gaba daya ya koma mutum mara amfani dan jiyai ma dakin kamar ba kowa a ciki ba kuma abinda ake cewa a ciki. Sai zafi da kirjinsa yakeyi...... Mumy kallansa kawai takeyi...... Sageer ya kalli Hassan sukai murmushi, Sageer ne ya tuno kalaman Abba dayace akwai tsuhuwar contract din da suka farayi dama time din da akasa kenan, to shi bai yaga ta ba shine yasa Sageer ya nemo, Abba yace da Jalila tayi nisa a karatu da ita zai sa aba wannan matsayin ko dan mahaifinta ya hankalta. #OneLuv💕 [12/30/2018, 10:08 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *72* Gaba daya haka kowa ya fito daga dakin taron zuciyarsa a cunkushe da wannan al'amari. Ya rage daga Hassan, Sageer, Mumy, Dady sai Sani ne kadai a ciki. Mumy ta kalli Hassan tace "amma nikam ai ba haka mukai daku ba." Hassan ya mata wani kallo yace "ke wacece da zaki tsara mana abinda kikeso muyi? Na dauka farincikinki kawai a kwace company din ne daga gun wannan, ba kuma naji kinada wani iko na samu ko hanamu." Dady zuciyarsa takai makura dan dama daurewa kawai yakeyi, jin kalaman Hassann ya kara tunzuro shi, matsowa kawai yai naga ya daga hannu kamar zai gaurawa Mumy mari, sai kuma ya sauke hannunsa yana hucci, kamar wani kumurci sannan ya bugawa Hassan wani banzan kallo. Hassan kam ganin yanda yake kallansa yake muzurai yasa shi yin wata dariya tare da cewa "bani na kar zomon ba, sannan ni na taba ganin wannan karfin halin?" Cikin tsananin fada yace "karfin hali? Karfin hali fa kace, ka san wace irin rayuwa nai har na kawo wannan ranar?" Yadanyi kara cikin karaji yace "who are u? Da har ka isa ka wargazamin abinda nake shiri shekara da shekaru?" Baa mumy taja saboda tsoron da Dady yake bata, Hassan ya hade fuska yace "rayuwar dakai? Wani ne ya saka? Kai fa ka sa kanka, sannan kai tambayar who am i? Nine wanda har karshen rayuwata indai har inada dama bazan taba barinka ka saci abinda ba naka ba." "Sata? Sata nai? Uban waye yacce haka ake sata?" Yace "To sanar dani in ba sata ba menene? Tsabar san zuciya ka wulakanta iyayenka, matarka, yarka, sannan yanzu kake neman ka sace abinda dayan matar da 'ya'yanka ke da shi." Cikin tsananin zafin rai ya matso ya sa hannu da karfi ya hankade Hassan, baya yai saura kadan ya fadi ya rike teburin dake gun. Dady yayo kanshi cikin fada yace "uban waye ya baka damar shiga rayuwata? Uban waye?" Yanda yake yi ne yasa Hassan ya kura mai ido yana kallan ikon Allah, gaba daya ma mutanen dake gun ma kowa kallan mamaki yake mai, Mumy kam hawaye ne kawai ke zubo mata, cikin masifa yake kallan Hassan yace "Uban waye nace? Duk duniya duk wanda ya kuskura yace zai hanani abinda nasa gaba wallahi zan iya mai abinda ni kaina ban san zan iya ba." Mamaki ne ya kara kama Hassan yace "ya zamuyi?" "Dame?" Dady ya fada a harzuke, Hassan yace "dan banaji zan dakata daga nan, har kasa na fara zakuwa naga mai zaka iya aikatawa." Cikin tsananin zafin rai da bakin ciki, Dady yakai hannu ya naushi Hassan, wanda sai da ya fasa mai gefen bakinsa, ya daga hannu zai kara Sageer ya rikeshi, Dady ya juyo cikin tsananin masifa yace "menene hakan?" Hassan ya mike ya goge bakinsa, yace "ya zamuyi yanzu kuma?" Dady ya mai wani kallo, Hassan yace "Sageer baka tunanin ya kamata a koreshi daga aiki?" Sageer yace "ai ba sai ka bata bakinka ba Yaya, Zakai resigning ne ka fita da martabar ka ko kuma kafisan mu koreka?" Dady yace "mene?" Sageer yace "ba dai kana tunanin duk wannan bugun dakai a banza kayi shi ba? Sai dai fa kayi hakuri dan duk na dau video ina jiran naji uzurinka dayasa ka naushi investors din ku." Dady ya zaro ido ya kalli Hassan gani yai Hassan ya mai wani murmushi sannan ya matso ya danyi ajiyar zuciya yace "in zaka saida shares dinka na company in gari yama zafi ka kawo Jalila zata siya." Hassan yai gaba ya barshi a gun, cikin takaicin hali irin nasa, Sageer yace "sai naga resignation letter

Chapter 33 of 38