Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
late insha Allah, sannan jiya ma tsautsayine.” Yace “ a tare zamu gama, kuna gama exams ni ma ina kammala aikina.” Murmushi tai batace komai ba. Yace “ me kikeyi tsayawa yi in an tashi daga school kullum?” Tace “ Kanena nake jira a tashesu sannan a daukosu sai su biyo ta nan mu tafi.” Yace “Kannenki?” Ita kanta taji abin ban barakwai sai dai ko ma menene ai kannenta ne, tace “eh” Juyowa yai yace “ a wani school suke?” Tace “Crescent International School” Kallan mamaki ya mata sai dai bai kara cewa komai ba sai juyawa dayai, yana tafiya yana mamaki, kannenta na Crescent ita kuma tana makarantar Government? Sai data ajiye mai books din sannan ta fito, tana tafe tana mamakin tambayoyin da Uncle Sagir ya mata. Ana tashi sun fito ita da Zarah, Zarah na ce mata ni dazu me kike nufi? Ban samu munyi magana ba........ Nasir da ta gani a tsaye ne yasa ta dakama Jalila duka a kafada tace “ Jalila kinga!” Jalila ta juya ta kalli yaran dake tsaye daga gefensu tace “ yayanki ne?” Yace “My Nasir ne, da alama ya gaji da missing dina ne.” Jalila ta kalli Nasir din sannan ta kalli Zarah wata dariya ta kirkiro wanda kana gani kasan ta dole ce tace “ Ohh shine Ur Nasir?” Zarah ta hade rai tace “Meye hakan?” Jalila ta girgiza kai tace “Kije naga ya kura miki ido kamar zai daukeki.” Murmushi tai sannan tace “ Kawata kalleni fuskata batai komai ba?” Kamar zatai kuka ta daga kai tace “Eh” Zarah ta fara tafiya cikin canza salo, Jalila kallansu kawai take cikin mamaki, wannan ai da alama makaranta ya samu da wuri amma ta tabbatar baiba Zarah shekara biyu bama, dan ma tace a level 3 yake ne amma lalai da tace sa’ansu ne,lalai ansha yarinta shiyasa. Tab itakam gaskiya bataji zata iya soyaya da sa’anta, ita tafisan saurayi kamar Uncle Sagir, da sauri ta girgiza kai tace “What am I thinking? Ahhhhh lalai banida kai.” #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *AyusherMohd* *No 3* Tana kallansu suna tafe suna rangaji irin na masoya, murmushi tai sannan ta koma gefe ta tsaya. A hankali duk aka yoye tana tsaye, ganin rana ta fara dishashewa ne yasa ta daga kai ta kalli sama, hadari taga yana haduwa abinka da damina kan kace me gari yayi daki, da sauri ta juya ciki ganin iska mai kura tana tasowa. Ji tai ta bugi abu, da sauri ta dago ta kalleshi. Idanunsa na kanta, ta matsa baya da sauri cikin jin kunya, sannan tace "Sorry Sir" Yace "anya yau sorry din nan zai karbu kuwa agurina? Da alama sai na hukunta mai laifin nan." Kallansa tai sannan tace " Wlh ban ku........" Yanda yake kallanta ne yasa ta kasa karasa maganar dake bakinta sannan tai saurin juyawa, dan ji take gabanta na faduwa. Murmushi yai sannan yace "muje in kaiki gida." Tace " Naam" Yace "Baki ji bane ko bakya so ne? Hadari ne a garin in aka fara ruwa kina tunanin yanda zakiyi kije gida? Ko su Kannen naki ne bakyasan ki tafi ki barsu?" Shiru tai tana dan nazari kafin tace " Nagode da kulawa Uncle Sagir sai dai in na tafi ba tare dasu ba fada za'amin." Kamar zai sake magana sai kuma taga ya juya ya koma ciki, tana tsaye ya fito da lema ya mika mata bai jira tace komai ba ya hau mota yai gaba. Da kallo ta bishi yau da mota yazo? Hmm ita kadai tasan cin zarafin da za'ama mahaifiyarta in har ta tafi. Tana tsaye aka fara yayyafi da sauri ta bude lemarta ta shiga, kan kace me ruwa ya tsuge, ruwa ake mai karfin gaske wanda tana cikin lemar ma amma ba tsira tai ba, komawa gefe tai ta rakube. Kamar motar zata tsaya sai taga ta yi gaba da gudu, cikin tsananin tsoro ta kalli motar tare da kwalla kara da karfi tace "Safeen ina nan fa......" A cikin motar kuwa wanda Safeena tacema Malam Auwal da alama ta tafi ganin hadari, wanda akasan ranta ta tabbatar bata tafi ba, tsabar mugunta ce. Haka ta rakube dan tsoro takeji ta koma cikin makarantar ita kadai, ganin a tsayen ma tsoro ya kamata kawai ta fara tafiya tana tafe tana kuka mai sauti, sai dai kasancewar karar ruwa bai sa tasan da karfi take kukan ba. Yana zaune a cikin motarsa daga gefen titi wanda shi dama yafisan gurin shiru inda ba mutane, shiyasa mafi akasari zaka sameshi ne a zaune a cikin motarsa ya zuge glass kawai ya kwanta. Jikin motar ta tsaya da taga ruwan ya dan yi sauki duk jikinta ya jike jagaf, ga lemarma sai lankwashewa takeyi saboda iska. Juyawa tai ta kalli glass din motar, da yake motar mai tints ce sai ta shiga kallan kanta tana kara wani kukan,sam tunaninta bai kawo mata da wani a cikin motar ba. Kallanta kawai yakeyi sai sharar kuka take wiwi. Komawa yai ya maida kansa ya rufe idanunsa kamar mai bacci. Kara juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai, kamar dama neman kukan takeyi, haushi duk ya isheshi kamar a kansa take kukan, kofar mazauninsa ya bude, a tsorace ta kalli motar, kallansa tai a tsorace, sannan ta kalli motar . Kallan tsoro tamai tace "Hmm hmm." Hannunsa ya dago ya mata alama da ta matsa daga gun, tace "Ban gane me kace ba." Alama ya sake mata da hannunsa akan tai gaba, sannan ya maida kofarsa ya rufe, da harara tabi kofar motar sannan tace " wannan kuma wani kwarantancen dan duniyar ne? Maganarce yafi karfin yimin ko kuwa tsabar rashin mutumci ne?" Harara ta sake yi sannan ta juya, kallan motar ta sakeyi sannan tace "irin motar jiya" Taja tsaki tace " da alama duk masu hawa irin motar nan basuda mutunci." Sam ta manta da kukan da takeyi saboda masifa, tana tafe yayafi na digar mata tana yan mitocinta, sai da ta gama gajiya ligif sannan ta isa gida. Goggo kuwa duk ta kasa zama saboda tsoro ganin yanda ake ruwa ga har yanzu bata dawo ba. Tana shiga Goggo ta kalleta cikin tsananin tausayawa. Jalila fadawa tai jikinta duk da jikarta ta sa kuka, idanun Goggo suka ciciko sai kanta kawai da take shafawa. Jalila ta dago tana kuka tace ""Goggo Allah nasan da sanin Safeena, ai tasan ban taba tahowa ba." Goggo tace "Kiyi hakuri" Jalila tace "Goggo sai yaushe ne zaki daina cewa inyi hakuri? Gaba daya rayuwarmu ni dake a hakuri ta kare, nikam ina takaicin cewa ma Dadyne mahaifi......." Marin da Goggo ta mata ne yasata yin shiru, kallan Goggo tai kuncinta a rike,Goggo ta kalli hannunta cikin dana sani sannan tace " taya zaki dinga kushe abinda Allah ya hada?" Jalila tace "kiyi hakuri Goggo bazan kara ba" Hannunta ta kamo tace " na sani, na sani sosai abinda ke ranki Jalila sai dai bayanda zamuyi da hukuncin Allah, sannan komai zaiyi ko kowa zai zageshi to lalai banda ke, domin shine silar zuwanki duniya." Tace "Na daina Goggo kiyi hakuri." Goggo tai murmushi tace " yi maza ki cire kayanki." Mikewa tai ta shiga dan dakinsu. Tana cire kaya tai sallah sannan ta mike tace "Goggo bari naje" Goggo tace abinci fa? Naga da safe ma a tsatsaye kikaci, shiyasa kullum gakinan kamar a hure. Tace " Goggo in na dawo naci" tace ban yarda ba sai dai ki tafi dashi can kici, ina zaki jira sai wajen magrib kici abinci? Jalila tai murmushi sannan tace " to in na gama ma rana zam deba inci a namu." Goggo tace "kin tabbatar?" Tace eh karki damu Goggo na Tana isa ta tadda Safeena a falo tana kallo, wata banzar harara ta maka mata sannan tace " da kuka taho kuka barni sai kuma gashi mai rai da lafiya yayo gida da kansa." Safeena tace " au da gaske kina can dama? Ni danaga ana zabga ruwa sai naga ina mai hankali zai tsaya a cikin ruwan nan?" Jalila tace " mai hankali kikace ai ni kuwa ina na ganshi?" Ta karasa maganar tana harararta, jitai ance " Uban wa ya baki damar cimata mutunci?" Gabanta ne yai wani irin faduwa, duk gidan ba wanda take tsananin tsoron ya mata fada irin Inna, a tsorace ta kalleta idanunta sun firfito, bakinta ne ya shiga rawa tace "In nn nna......" Kallanta tai sannan ta kalli Safeena tace " ke kuma Jalila matsayinku daya da zaki dinga zama tana fada miki kalamai irin haka?" Jalila ta hadiyi wani miyau me daci tace " in na bahaka bane......." "Dake nake magana?" Jalila gabanta sai faduwa yakeyi. Sultan ne ya fito daga kitchen rike da jarkar ruwa na faro yace " Inna ita Safeenar itace da laifi bai kamata ku dinga yanke hukunci ba tare da bincike ba." Kallansa tai tace " Sultan shiga daki" Baice komai ba ya wuce ciki, Jalila kuwa kamar wacce aka tsunduma a wani ruwan haka takeji, muryar Dady ne ya ratsa falon wanda maganganu Inna ne suka sa shi fitowa, da sauri yace "Hajiya ki mata afuwa ni zan hukuntata da kaina." Kallansa tai a wulakance tace " kai har wani hukunci zaka iya? Ka saisaita yarinyarka in ba haka ba daga ita har uwarta zasu bar gidan nan, karka kuskura ka manta gida da dukiyar wanene kake mora daga kai har su." Mumy ce ta rike hannunta tace " Kiyi hakuri ki bari dan Allah." Ta fada tare da jan hannun ta zuwa dakinta. Suna shiga tace "Inna sai yaushene zaki daina disga Abakar cikin yaransa? Karfa ki manta 'ya'yansa sunanan kuma suna jin zafin abin." Kallanta tai tace " ke meyasa bakida hankaline? Kin nace sai kin aureshi dake da mahaifinki, bakya tunanin wannan cin mutuncin da nakemai shine dalilin da yasa yake nuna miki kulawa haka?" Tace " Wlh Inna ke kike ganin haka Abbakar na sona kamar yanda nake sansa, dan Allah ki daina wulakantashi." Ta karasa maganar cikin lalashi. A falo kuwa Dady a zuciye ya sa hannu ya fizgo Jalila ya kaita kitchen, cikin fada yace " sai yaushe ne zakiyi hankali kisan darajarsu Safeenan kikeci ke da uwarki?" Kallansa tai cikin rawar baki tace " Dady itace........" Cikin tsawa yace " so kike in fasa miki baki? Ko me ta miki bazaki hakura ba? Shashashar banza to wlh ki bala'in shiga hankalinki in har kinaso mahaifiyarki dake ku zauna a gidan nan." Yana gama magana yai falo, yana shigowa Safeena taje da gudu da rungumeshi. ************** Yana shigowa cikin gidan ya tadda mahaifinsa a zaune a falo, karasawa yai ya gaidashi sannan ya fara kokarin mikewa. Mahaifinsa yace "Hassan!" Komawa yai ya zauna tare da kallansa, Abba yai ajiyar zuciya sannan yace " Baka manta badai karshen satin nan zamu koma asibiti ko?" Hassan ya kalleshi yace "Abba please ka hakura Abba cikin kulawa yace " Ka taba ganin inda uba ya hakura da dansa? Karka damu insha Allah da yardar Allah wannan matsala taka zata warware sannan zaka samu sauki cikin yardar Allah." Kallan mahaifinsa kawai yake shidai sun kasa fahimtarsa, mikewa yai baice komai ba zaiyi gaba. Kaninsa ne ya dafashi yace " Yaya kace Ameen mana ko hankalin Abban zai kwanta?" Ummy ya kalla wacce ke tsaye ita da Ameerah yai shiru sannan a hankali yadan motsa baki yace Ameeen. Murmushi sukai dukansu m, Sagir ya dafashi yace " Ko kai fa Yaya." Hannunsa yasa ya ture nashi daga kafadarsa yai wuce, Ummy tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Ameera. Kai Ameera ta daga sannan tai kitchen. Faten dankali wanda Ummy ta masa ta zubo a plate sannan ta dau spoon ta fito, sama ta hau sannan ta shiga dakinsa. Yana zaune a kasa kan carpet ta shiga. Gabansa ta ajiye abincin sannan ta ce "Yaya abinci." Kallanta yai yace " BAna......" Tace " Na sani yaya baka jin yunwa dama ko da yaushe zancen kenan, sai dai Yaya ka ci ko dan Ummy ta samu sukuni a ranta." Yace "Naji zanci, ke kuma fita." Ta mike tace " to" Waje tai sannan ta turomai kofar. #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *AyusherMohd* _Gaisuwa mai yawa tare da fatan alkairi a koda yaushe gareki Aunty na ta kaina.....Aunty Goggo Allah ya kareki ya ja da ranki😍 much luv Sister_ *No 4* Da kyar ya tura abincin sannan ya mike ya shiga bandaki, wanka yai tare da dauro alwala. Jalabiya ya zura ya tada sallah, ya dade sosai akan sallayar yana mika rokonsa gurin Allah sannan ya kwanta a kasa, a takure ya kwanta , sam baisan sanda bacci yai gaba dashi ba. Ummy ce ta leko ta ganshi yana bacci, kusa dashi taje ta zauna tana kallansa cikin tsantsar so da kulawa da kuma tausayi, jan numfashi tai sannan ta mike ta dau tiren abincin da yaci tai waje. Gab da magrib yana bacci yaji kamar ana shakemai wuya, wani irin mumunan mafarki yakeyi wanda ya shiga sandarewa yana kankake jikinsa, idanunsa a runtse sai wani irin zufa da yake kwaranya daga jikinsa, numfashinsa ne ya shiga hawa da sauka, shure shure ya shiga yi saboda tsananin azabar da yake fuskanta. Har zai shiga dakinsa yaji alamar motsin Hassan, da sauri Sagir ya tura kofar, ganin Hassan a kankame yasa yai saurin shiga dakin, tabashi yai yana cewa Hassan! Yaya! A firgice ya bude idanunsa tare da jan wani irin numfashi, Sagir ya dagashi zaune yace "in kawo ma ruwa?" Hassan ya daga kai, da sauri ya mike ya dauko mai ruwa, amsa yai ya lafa bakinsa, sai dayasha sosai sannan ya kalli Sagir ya mikamai jarkar. Sagir ya amsa sannan yace "akwai abinda kake bukata?" Kai ya girgiza alamar a'a. Cikin tausayawa Sagir ya kalleshi sannan ya mike yace "Yaya kazo dan Allah ko waje ka fita kaji iskar duniya." Bai kalleshi ba haka kuma bashi da niyyar amsamai, Sagir ganin haka yasa ya fita tare da ja mai kofar. Sagir yabi bayan kofar da kallo sannan yace "Allah ya yaye maka ya baka lafiya." Dakinsa Sagir ya shiga kallan kayan da ya cire dazu yai sannan yai murmushi ko a ya ta koma gida? Cikin nuna halin damuwa yace " ba ta dai jike ba ko?" Kai ya girgiza yace " ya za'ai ta jike ga lemar da ya bata sannan ya tabbatar tace ai zuwa za'ai a daukesu." Murmushi yai sannan ya dau wayarsa dayazo dayka ya sauka kasa. ************** Jalila ce zaune tanacin abincin dare ita da Goggo, tunanin abinda ya faru dazu takeyi. Jitai Goggo ta tabata tace " Jalila wani abun ya faru ne dazu?" Jalila ta kalleta tace "Bakomai kawai dai ni akwai abinda na dade ina san tambayarki ne Goggo." Goggo ta kalleta tana neman karin bayani, Jalila tace " Bawai da wani abin bafa nake san ji Goggo, kawai dai tambaya ce." Goggo tace "Ina jinki." Jalila tace " Ni Goggo baki da kowa ne sai Dady?" Murmushi tai tace"Ban gane banida kowa ba sai shi? Kin tabaganin wanda bashida kowa a duniya?" Jalila tace " To ni Goggo na kasa fahimtarki ne sam, na rasa takamaimai ke mukeyi a cikin gidan nan." Goggo ta tsame hannunta sannan tace " Lalai Jalila, muhallin Mahaifin naki kike fadama haka?" "Muhalli? Ai kowa yasan gidan Mumy ne ba nashi ba, sannan ni waye ma yasan ni 'yarsa ce, ko suna a makaranta ni ansa nayi amfani da Auwal wato kakan Dady, dan kawai karma asan ni yar sace." Goggo tace" ya isa to, ke dai ba ruwanki da wannan, mahaifinki da mahaifinki ne, sannan banaji yana da laifi a harkar nan, laifin na iyayenmu ne." Jalila tace "Goggo dama tun can baya sanki" Harararta tai tace"Wai yau me kikesan ji ne haka?" Tace"ni dan Allah ki fadamin tarihinki Goggo." Hannunta ta wanke a robar ruwan da Jalila ta kawo ta dan matsa kadan tace " sai randa hankali yazo miki." Jalila ta dan turo baki tace "ni yau meyasa ake tacemin banda hankali?" Goggo tace " Ce miki akai mara hankali a cikin gida?" Tace "Safeena ce." Goggo tace "Fada kukai kenan?" Jalila ta hade rai tace " ni ai....." Goggo tace "sai yaushe ne zaki dinga hakuri Jalila? Na dauka na rokeki akan kai zuciya nesa?" Jalila ta kalleta tace "Yanzu duk hakurin da nakeyi bakya gani? Wlh a yanda nake ji da wata rana sai na fasama 'yar nan baki, kawai hakuri nake sawa a zuciyata." Goggo tausayinta ya kamata tace"kiyi hakuri, duk tsanani yana tare da sauki, shiyasa a koda yaushe nake miki fatan miji na gari, wanda ke sanki ina tunanin hakan ne kadai zai kawo salama a zuciyata da taki." Jalila tace "ni duk wanda zan aura sai dai in zai iya rikemin ke, dan bazan iya aure na barki ba." Dariya Goggo tai tace "Lalai yarinta na damunki Jalila." Haka sukai ta hira har suka kwanta............. ********* Washegari......... Yau tana gama aiki ta shirya ta fito dan jiransu, dadi takeji yau ta rigasu shiryawa, yanda taga Dady ya fito da sauri ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba tasan lalai da matsala, mota taga ya shiga da sauri, sai ga Mumy ta taho da gudu tare da shiga gefensa itama, nan taga sun fita a guje. Baki ta tabe tace "ko ina zasu haka oho" Su Safeena ne suka fito,Yasmeen na ganinta ta isa gunta da gudu tana nuna mata sabon school bag din da Dadynta ya siyo mata. Jalila tace "inyee lalai tayi kyau." Tafada tana kallan wata yagwalgwalaliyar jakar dake bayanta. Mota suka shiga, Safeena ta kalli Sultan tace "Sultan kamar akwai matsala a company dinsu Dady ko?" Sultan ya kalleta yace" ina na sani, in so kike kiji me yasa baki tambayeshi ba da zai fita?" Haushi ne ya kamata tace " Wai kai meyasa mutum bai isa yai maganar mutunci dakai ba?" Tsaki tai sannan ta maida kanta kan Jalila cikin masifa tace "ke kuma uban me kike kallo?" Jalila tace "Ba ni na kar zomon ba Hajiya." Safeena ta kara kuluwa, da saninta tasa kafa ta tako kafar Jalila, Jalila ta kalleta. Safeena tace " sry fa ban kula ba." Jalila ta kalli safarta wacce ta baci sannan ta kalli Safeena tace " mantawa nai ashe idanunki basa aiki." Ran Safeena ne ya baci tace "mene?" Jalila ta kalli window ganin sun kusa isa, me zata gani? Uncle Sagir ta gani yana parking din mashin dinsa, ga mamakinta murmushi ne ya bayyana a fuskarta, Safeena ce ta kalli inda take kallo nan idanunta suka sauka kan Sagir. Idanu ta kuramai, waye wannan? Batasan a fili ta fada ba, Jalila ta kalleta tace "Uncle dinmu ne na Math." Safeena ta kara kallanshi sannan tace "Driver tsaya anan mana ta sauka." Jalila ta kalleta ta tabe baki sannan ta sauka. Muryarta yaji tace "Good Morning Uncle." Juyowa yai ya kalleta, yanayin fuskarsa kadai zaka kalla kasan ganinta ya sashi farinciki. Jalila ta dan matsa gunsa kadan tace "Sir nayi laifi." Bai ce komai ba sai wani kallo da yake mata, gana kokarin b'oye abinda ke ransa, dan bai manta ita din dalibarsa bace. Ta fara wasa da hannunta sannan tace "Lemarka jiya ta samu matsala." Yace "ta samu matsala ko dai ba'a damu da ita ba an lalatata?" Da sauri tace " ba haka bane, Allah iska ce ta dinga bankareta....." Yanayin fuskarsa ne ya canza zuwa kulawa, yace "ba dai abinda ya sameki ko? Are u okay?" Ganin yanda ya damu da ita yasa taji ta kasa cewa komai, yanda take kallansa ne yai saurin juyawa ya kalli daliban dake ta shiga makarantar yace " Ki wuce cikin makaranta."maganar ya karasa tare da juyawa yana kallan mashin din. Jalila ta fara tafiya a hankali tana mamakin kulawar da yake nuna mata wanda ke kokarin sa zargin so a zuciyarta, anya kuwa? Karfa zuciyarta ta raya mata abinda ba haka ba, Uncle Sagir yafi karfinta, dan mata dayawa na sanshi, sannan da alama dan gidan wani ne duba da yanayin yanda yake zuwa wani sa'in a mota. Wata zuciyarce ta ce mata ina ruwan so da wannan? Juyowa tai bayan tayi tafiya mai nisa, ga mamakinta gani tai idanunsa na kanta, suna hada ido yai saurin juyawa, Jalila ta juya cikin yanayin jin kunya. ********** A company dinsu Dady kuwa suna isa sukaga mutane ancika a waje. Da sauri sukai parking Dady ya fito cikin tashin hankali, suna ganinshi sukayo kanshi. Mumy na gefensa, cikin tsantsar tashin hankali yace " gaba daya kayanda muka adana sun lalace?" Cikin damuwa yace " Muje ka gani." Store din da suke adana dukan kayan aikin da sukeyi ya bude. Store din acike yake da kayan ma'a dana na abinci. Gaba daya hankalin Dady ya tashi dan kana gani kasan lalai lalata musu akai. Juyowa yai yace " How can this happen? How......." Mumy ma hankalinta ya tashi ta kalli Dady tace "Yanzu ya zamuyi? Gashi zuwanka Abuja munyi signing da Al-Company zamu aika musu da kayan cikin satin nan." Wata zuface ta karyomai yace "Muje gida mu sanar ma Inna, sai muyi tunanin mafita, dolene mu san yanda zamuyi kafin nexweek." Hankali a tashe suka juya gida. Inna macece wacce tasan kan kasuwanci, dan company dinsu ya bunkasa ne harda tsananin iya kasuwancin ta, shiyasa mijinta yake girmama kalamanta sannan takeji da kanta itama. Har Allah ya mai rasuwa, ta dade tana juya company din da kanta duk kuwa da ganin Dadyna iya nasa kokarin a karkashinta,har sai dataga girma ya kamata tana bukatar Hutu sannan tabar Dady yakejan ragama. Inna wacce yanzu ne ta maida sunanta haka, dan da kowa Hajiya yake kiranta, yanzun ma Sultan ne ya sa mata hakan har kowa ya koma kiranta haka a gidan, amma daga ta fita sai dai kaji ana Hajiya. Tai shiru kafin tace "nawa ne a account dinmu?" Yace "Hajiya mun kwashe rabin kudin mun sai kayan aiki, ba nakawo miki budget din ba?" Hannu tasa ta shafi fuskarta tace "Kudin bazasu kai musai wasu kayan ba kenan?" Kasa yai dakai yace "Gaba dayan mun gama shirya plan dinmu banaji ko kwata zai kai." Ta dade batace komai ba da alama nazari take kafin tace "Sai dai kenan mubi last option din da banaso." Yace "Loan?" Tace " dole zan duba a cikin mutanen Alhaji da nawa wanene na amana sai musan yanda zamuyi, either mu samu loan ko kuma yayi investing." Kai ya jinjina sannan yace "bari a kira board meeting sai a tattauna." Tace "No ka bari sai zuwa gobe in na samu wanda zai tallafa mana." Yace " To Hajiya." Nan ya mike ya fita, wani karamin diary ta d'auko ta shiga duba sunaye tana auna mutane....... #Oneluv💕 [08/10, 19:18] ‪+234 816 365 0557‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *AyusherMohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 5* Yau a staff room yai shiru yana tunanin yanda zaiyi, ya dade yana tunani dan baisan ma sanda wani staff yazo kusa dashi ba yace "Sagir mu mun wuce sai gobe in Allah ya kaimu." Kallanshi yai cikin mamaki sannan ya kalli agoggon dake jikin bango, lalai har an tashi da kusan minti goma ma. Yace "To Sai goben." Nan ya shiga hada kayansa shima, a tsaye ya ganta a inda ta saba tsayuwa, ya dade yana kallanta sannan ya karasa kusa da ita yace "Malamar jira." Kallansa tai sannan ta sunkuyar da kanta tana murmushi dama yanzu take tunanin bata ga fitarsa ba. Jitai yace mata "D'an zo."ya fada tare da fara tafiya, cikin mamaki take binsa har suka shiga wani class. Zama yai a saman desk sannan ya mata alama data zauna daga kujerar dake gefensa kadan. Bata musa ba ta zauna, sai daya d'an yi shiru na

Chapter 2 of 38