Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
takardar, kudi ne zunzurutu wanda aka biya, na daki da kuma na aikin da aka mata da na treatment, sa dai bataji su a gunsu kudi ne mai yawa. Kallan Inna ta sakeyi dan bata fahimci me takesan nuna mata ba. Inna tace takardar kudin da muka kashema Mahaifiyarki ne. Jalila tace "na gani angode Allah ya saka....." Inna tace " Biya zakiyi." Jalila cikin rashin fahimta tace "bangane ba." Inna tace "kina tunanin kina zaune a gidan mu, mun saki a makaranta, mun kula dake da mahaifiyarki, mun biya mata wannan kudin, sannan kice ba zakibi umarnin mu ba?" Jalila tace "Inna......." Inna ta katseta tace "yaya? Kina da kudin da zaki biya mu dai ko?" Idanunta ne suka kara firfitowa ta fara zubarda hawaye, Inna tace " in har kinfi karfin bin umarninmu sai mu zare hannunmu daga rayuwarku sai inga yanda zakuyi, ina fatan kinada inda zaku zauna da kuma kudin da zaki cigaba da kula da mahaifiyarki harta warke." Jalila tasa kuka tace "Inna dan Allah kiyi hakuri, Goggo tana neman kulawarku dan Allah ki yafemin." Inna ta mike tace " tashi ki fita, na baki daga yau zuwa gobe da safe inhar baki bi umarnin mu ba, zansa a koreta daga asibitin, sannan kubar gidan mu bayan kin biya kudin." Jalila ta zauna tana wani irin kuka mai ban tausayi, Inna tace "tashi ki fita." Mikewa tai tana hawaye ta sauko. Yasmeen na mata magana ko kallanta batai ba ta fito tana hawaye. Bangarensu ta nufa kawai ta zube akasa tana kuka, ya zatai? Uncle ne ya fado mata, da sauri ta janyo jakarta ta zaro wayar nan. Ganin irin kiran da yai mata yasa ta saurin danna kira, ringing take ta yi ba'a daga ba. Shikuwa a lokacin Ummy ta nemi ya rakata store, sai daya shiga mota ya tuna yabar wayarsa a gida. Sai dai ganin ba wani dadewa zasuyi ba yasa ya fita kawai. Kuka ta shiga yi sosai da taga bai daga ba, kira take tayi ba kakkautawa. Ganin ba dama ta cila wayar kan gado ta fito rike da jakarta. Tana tafe tana kuka, drivern na mata magana ko bi takansa batai ba tai waje. Tana tafe tana wani irin kuka. Sai da ta mike layinsu sosai, taje tsalakawa ta titi shi kuma ya taho saura kiris ya bugeta, wani irin burki yaja da karfi sannan ya kifa kansa da sitiyari. Jikinsa ne ya shiga karkarwa, Jalila kuwa ta dauka karshen rayuwarta yazo har ta tsugunna, ganin bai kade ta ba kawai sai taji wani irin kuka yazo mata. Tsananin tsoro yasa zufa ta shiga keto mai, da kyar ya iya fitowa daga motar, kusa da ita yazo yanda yaji tana kuka yasa yaji kansa na wani irin juyawa, dan tabbas ya dauka ya mata illa, dan uwansa ya hango alokacin da matsalar da bazai taba mantawa ba ta faru, numfashinsa ne ya shiga sarkewa, hannunsa yasa a wuyansa yana wani irin abu. Jalila ta dago, ganin mutum na neman zubewa yasa hankalinta ya tashi. Da sauri ta shiga yin ihun neman taimako. Mikewa tai zata nemo mutane, hannu yasa ya riko siket dinta. Juyowa tai da sauri tare da tsorata. Da kyar yace " ba bige nai ba?" Gaba daya ta tsorata dan ta dauka shi aka bige. Siket dinta ta fizge ta tsaya tana kallan sa. Mikewa yai sannan ya matso kusa da ita, matsawa ta dan yi. Ya kara matsowa fuskarsa a hade, kara matsawa tai cikin tsoro. Yace " meye dalilinki na tsugunnawa akasan motata da sa mun kuka?" Jalila ta kalleshi tace " motarka ce?" Yace "tambayarki nake?" Ta kara kallan motar sannan ta tuno abinda ya faru da irin mai motar, da alama duk masu irin motar nan basuda mutunci. Tace " na dauka ma hakuri zaka bani, tunda kasan na tsorata." Baya san magana amma yanda tai maganar yasa ransa ya baci yace " me? Hakuri?" Ta daga kai, kallanta yai, harzai sake magana sai kuma naga ya fasa, motarsa ya koma ya shiga ya fizgeta da gudu. Jalila ta harari motar, ta cigaba da tafiyarta tana matsar kwallarta. Da alama yau gaba daya ranar bakin ciki ce a gareta. #ONELUV💕 [08/10, 02:08] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 17* A hankali ta tura kofar dakin, Tana kokarin shiga nurse din na kokarin fita, jiranta tai ta fito maimakon ta shiga sai tabi nurse din. Tana gaisheta, Nurse din ta tsaya ta amsa, Jalila ta matso tace " Aunty ya jikin Goggo?" Tace "da sauki, ya akai? Kina tsoro ne?" Jalila ta goge kwallarta tace " Aunty kina ganin kamar kwanaki nawa zamuyi kafin kafar Goggo ta samu sauki?" Tace "maybe 3 to 4weeks" Jalila ta zaro ido tace "da tsayi haka?" Tace "Umm." Jalila tai shiru, Nurse din tace " ba wata tambayar?" Jalila tace "in tabar asibitin fa?" Nurse din cikin mamaki tace " ta ya za'ai tabar asibitin tana cikin wannan state din? Ko asibitin kuke san canzawa?" Jalila ta runtse ido can tace " Aunty kudin ne......." Muryar Sultan taji yace "me kike anan?" Idanunta ta bude da sauri, Nurse din ta wuce ganin kamar bazata iya magana ba. Sultan ya karaso yana kallanta. Ya kara cewa "me kike anan?" Jalila bakinta ne ya shiga rawa ta kasa magana, Hannunta ya rike yace "meye hakan?" Kamar ya tabota kawai tasa kuka, mamaki ya kamashi can yace " Mumy ce?" Kai ta girgiza, yace "Dady ne?" Nan ma kai ta girgiza, sam bai kawo Inna ba saboda ba kasafai take shiga harkar rayuwar gidan ba, yace "Jikin Goggo?" Hawayenta ta share tace "Sultan ya zanyi?" Yace "name?" Tace "tsakanin rayuwata data mahaifiyata." Yace "wace irin tambaya ce wannan, sannan in amsa kike so ai ke yarinya ce mai kuma lafiya, ita kuwa Goggo ba lafiya ne da ita ba." Jalila ta shiga daga kai tana cewa "haka ne, Goggo itace gaba da komai." Kallan mamaki ya kara mata, ta kakaro murmushin takaici tace "nagode Sultan." Leda ya miko mata yace "gashi, Ni bari na wuce." Tace "kai kadai?" Yace " inada kudi a jikina, nan ya zaro dubu biyu yan dari biyar biyar, mika mata dubu daya da dari biyar yai ya maida dari biyar aljihunsa yace " gashi ko zaki sai wani abin." Ta amsa tamai godiya, juyawa yai ya fita, da kallo ta bishi sannan ta goge fuskarta ya tura kofar dakin. Goggo na zaune shiru ta shiga, Jalila ta karasa tana cewa "Goggo a zaune kike?" Goggo ta kalleta tace "kin dawo?" Tace "eh." Jakar hannunta ta kalla tace " baki daukon kaya ba?" Jalila ta bude baki tace "wayyo, wlh na sha'afa sam, ni fa dama jakar nan kawai naje daukowa." Goggo ta kalleta cikin zargi tace " me ya samu idanunki? Abubakar ya miki wata magana ne?" Ta zauna kusa da ita tace "Kai Goggo, ni ko ganinsa ma banyi ba." Goggo tai ajiyar zuciya tace " sai yaushe zamu bar asibitin nan?" Jalila tace "tab aima ki gyara zama goggo, dan wlh yanzu Nurse take cewa sati uku zuwa hudu." Goggo cikin mamaki tace "Wannan asibitin mai tsada? Kina tunanin zasu biya mana kudin?" Jalila tai murmushin takaici tace " karki damu da wannan, ke dai ki kwantar da hankalinki, kinji dai mai likita yace jiya." Goggo tai murmushi, Jalila ta bude ledar da Sultan ya miko mata, ruwa ne mai sanyi faru tace "ruwa kika aikeshi?" Tace "Allah sarki Sultan cewa nai ya bani ruwa in akwai, ashe wai babu shine naga ya fita." Jalila a ranta tace "dama sai a dinga kawo abinci ba ruwa." Haka tai ta kokarin boyema Goggo damuwarta. ********* Sagir na komawa gida ya hau sama dan dauko wayarsa, ganin irin kiran da Jalila tamai yasa hankalinsa ya tashi, nan ya shiga buga mata waya shima, sai dai duk yanda ya kira No Answer kawai ake rubutamai, Fitowa yai ya shiga mota ya tafi makarantar su, ba ta nan, ya akai baiyi tunanin amsar address din ta ba? Wai shi yana ganin yasai mata waya, kwatancen gidansu bazai zamarmai wahala ba. Kai ya shafa cikin takaici, ina ne gidansu? Haka ya dawo gida jiki a sanyaye. Abba ne bayan Magrib ya shiga d'akin Hassan, yana zaune rike da littafi a hannunsa yana karantawa, Jornal ne. Yana ganin Abba ya rufe littafin sai dai baiyi motsi ba daga inda yake bai kuma yi magana ba. Abba ya shiga ya zauna kusa dashi, Shiru ne yadan ratsa dakin, can Abba yace " Me zakayi gobe?" Hassan ya mai kallan mamaki, me zaiyi? Shi daka rayuwarsa ai kullum iri daya ce, Abba ya kalleshi yace "Gobe da yamma ko bayan magrib kuje kai da Sagir ku ga yarinyar." Kallan Mahaifinsa yai cikin mamaki yace " inje ince mata me?" Abba yace "kaje ku gaisa ta ganka, ka ganta." Hassan yai shiru can yace " Ai wannan tun a farko ya kamata kuce naje, Abba abinda ya kamata kuyi tun farko kenan, ta ya zaku sa rana ba tare da yarinya ta ganni ba?" Abba yace "Hassan bakasan me nai ba akan samar maka abokiyar zama." Hassan ya kalleshi yace " me kake nufi?" Abba ya mike yace "Ka taimaka gobe kuje kai da Sagir, wannan rokone uba yake ma dansa." Hassan yai shiru baice komai ba, fita Abba yai tare da rufe mai kofa, shiru Hassan yai yana tunanin wannan abun, shi gaba daya ya kasa hasko rayuwarshi da wata mace, macen ma wacce bai sani ba. ********** Wajen karfe d'ayan dare ta mike daga kwanciyar datai dan dama ba bacci take ba, fitowa tai daga dakin ta zauna a kasan matatakalar benin, shiru tai tana tunani, ya zatai? Gaba daya duk yanda taso ta canza shawarar dake zuciyarta in ta auna lafiyar mahaifiyarta wacce ta rayu cikin bakin cikin da namiji bataji zata iya canza wata shawarar, rayuwar mahaifiyarta itace gaba da komai a rayuwarta. Kanta ta kwantar akan gwiwowinta tana tunano rayuwar da sukai da Sagir da irin rayuwar da tai fa mafarkin yi dashi. Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, a wannan rana bacci baiga idanunta ba. Wajen karfe 1o aka kawo musu abinci sannan drivern yace mata "Inna na jiranki." Ta fahimci me yake nufi, kallan Goggo tai tace "Goggo zanje na kwaso kayan, akwai abinda kikeso?" Nan ta fada mata abubuwan da takeso ta taho mata dashi, har zata fita sai ta dawo da sauri ta rungume Goggo idanunta na neman kawo kwalla. Goggo tace "Jalila menene? Badai jiya karya kikamin ba? Ance miki wani abun a gidan ko?" Dagowa tai tana dariya tace "Goggo kenan, kema kinsan bana iya boye miki komai a dunia, me zaisa in ki sanar dake? Inaji fa ganin kin kwanta yasa jikinsu yayi sanyi da zancen." Goggo tai tsaki tace " duk yanda naso in zauna dasu lafiya in har suka sake suka miki zancen hadin aure wlh sai sunsha mamaki." Jalila tace "ni inada ke a duniya me zaisa inji tsoro Goggona?" Murmushi sukai a tare, Jalila ta juya ta fara takawa a hankali, daga sanda tasa kafa tabar dakin nan ta shiga motar ta tabbatar rayuwarta shikenan ta canza, bazatai dana sanin fita daga dakin nan ba kuwa? Ai dana sani tun kafin ta fita tasan rayuwarta lalai tana cike da danasani, domin kuwa batasan wani irin zama zatai ba. Sai data kai kofa ta juyo tama Goggo murmushi sannan ta fita. Mota ta shiga tai shiru tana kallan waje, mutane take ta kallo kowa yana nasa rayuwar, haka har suka isa gidan. Sai dayai kusan minti biyar da parking sannan ta bude kofar ta fito. Inna ta kalli Mumy dake leken window ta dakinta, Mumy da sauri ta juyo tace "ta iso kuwa Inna." Inna ta kalli Dady tace " sai ka kyautata mata kai kuma, ka tabbatar bata nunama mijin nata tsana ba." Dady yace "to." Mumy ta matso tace "Dadyn Yasmeen let us try our best." Murmushi yai mata na dole sannan ya mike. Inna tace " in zaku siyo ragowar kayan gida kudinga daukanta a asibiti." Yace to, sannan yai waje. Yana isa falon tana shigowa, tsayawa tai tana kallansa, wai mahaifinta? Wanda hakkinta ke rataye a wuyansa? Dady ne ya matso kusa da ita, ya sa hannu a aljihunsa yace "Jalila ya mai jikin?" Kallansa kawai take batace komai ba, sai idanunta da sukai ja, bata amsa mai ba. Yace "me kike tunani?" Kai ta girgiza alamar bakomai tace " kawai ina tunanin yanda Allah ya rataya wa uba hakkin dansa a wuyansa ne." Dady yai shiru, zaiyi magana Mumy ta karaso tace "Jalila, yanzu muke shirin zuwa asibiti." Jalila tai shiru a ranta tace "tunda kunsamu abinda kukeso ai dole." Nan ta haura sama batare da tace komai ba. Inna na zaune sai data zauna sannan tace "YA YA? Kin yanke shawarar?" Jalila ta kalleta dan tana tsananin shakkarta ta daure tace "Amma kimin alkawari biyu." Inna tace "inajinki." Jalila tai shiru kafin tace " da farko zaku kula da Goggo, zaku samo mata wacce zata dinga taimaka mata, sannan na biyu karku fada mata komai har sai ta samu lafiya." Inna tace "duk ba matsala bane, Jalila ta kalleta a ranta tace me zata samu da take bin ta kowace hanya dan ganin ta min auran nan?" Dagowa tai da sauri datai tunanin wani abu tace "Inna tsoho ne?" Inna tace "a'a saurayi ne" Jalila cikin tsoro take kallanta, anya? Me suke tunani? In har ba wata matsalar mai zaisa su bar yarsu su zabeta? Inna tace " ki tashi ki sauka kasa, bayan kinyi aanka kinci abinci ki shirya, ance bayan la'asar zaizo." Jalila ta mike ta fito zuciyarta fal da tunani kala kala. Bangarensu kawai ta nufa ta kwanta, karar wayarta taji. Da sauri ta jawota, ta daga. Muryar Uncle ne ya daki kunnenta, ji tai wasu zafaffan hawaye sun zubo mata. Sagir yace "Jalila ina kika shiga haka? Ba dai wani abin bane ya faru ko?" Kasa magana tai, hankalinsa ne ya tashi. Ya shiga tambayarta, can ta daure tace "Uncle yaushe zamu hadu? Akwai maganar da zamuyi dakai." Yace " ko yanzu ma in kinaso." Tace "a'a banda yau." Yace "nima na manta yau zan raka yayana wani gun, gobe fa?" Tace " to, Allah ya kaimu, zan kiraka goben." Haka kawai tace ta kashe wayar saboda yanda taji zuciyarta ta karye. Tana kashewa kuwa tasa kuka. Shikenan Uncle, soyayyar da muke ma juna ashe anan zata tsaya......... Sagir na kashe wayar shima yai shiru, tabbas akwai abinda ke damunta...... #Oneluv💕 [08/10, 02:09] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 18* Sake kwanciya tai, ta kwantar da kanta akan katifa, itada take burin auren soyayya? Yanzu me kenan? Idanunta ta bude a hankali, tana kallan dakinsu, rayuwarsu da mahaifiyarta ne ta shiga dawo mata, rayuwace wacce sukai ta talauci da tsana, sai dai a tsakaninsu rayuwace mai cike da dinbin kewar juna da shakuwa, zata iya rayuwa ba tare da Goggonta ba? Haka tai ta saka da warwara har bacci yai gaba da ita. Sai wajen karfe uku ta farka, shima mafarki ne ya tasheta wanda ya sata razana da sauri, sai dai me? Duk yanda taso ta tuno wani mafarkin tai ta kasa sam, wayarta ta dauka da sauri ta yima Sagir text. Uncle please mu hadu a makaranta ko na minti goma ne, i really want to talk to you. Ajiye wayar tai ta mike, gaskiya dole ta sanar ma Uncle abinda ke faruwa taji me zaice. Mikewa tai ta kalli kayan da aka kawo mata ta saka, nan tai wanka ta saka ta fito sidif sidif tai waje. ***** A can gidansu Hassan kuwa, Sai da Ummy ta mai magana ya kimtsa, da kananan kaya ya saka tasashi ya koma ya sako manya kaya. Fitowa yai daga dakinsa sanye da dakakiyar shad, cyan color wanda mukafi sani da bluegreen, shadar ta mai kyau sosai, dan shi dama bai fiya sa manyan kaya ba, daga kanana sai jallabiya, Abba ne baya gajiya da dinkamai. Ameera da kanta ta d'aukomai hula ta mikamai. Hassan kallansu kawai yake dan bayasan magana ya amsa. Takalmi ya saka sannan ya sauko kasan, Sagir sai janshi yake da tsokana wai kai Yaya gaskiya wannan kyan kamar ranar auranka. Hassan ko kallansa baiyi ba bare ya tankamai, shima Sagir din manyan kaya ya saka. Ummy ta jawo Sagir tace "Sagir ka taimaka kar a samu matsala, kasan halin yayan naka." Sagir ya daga kai yace "Karki damu Ummyna, ki bar komai a wuyana." Murmushi tai tace "godiya nake dan lele na." Haka suka fito kowa yana farinciki, Ummy ta mikama Sagir gift din da zasu kai mata. Aina'u na jikin dakin Ameera tana kallansu, komawa tai cikin dakin ta kwanta ranta ba dadi. Motar Hassan suka nufa, Hassan na shiga ya rufo kofa, Sagir ya zagawa ta bangaren kusa da driver yana cew "Yaya na dauka da Mamman zamuje saboda shi yasan gidan. Jiyai kofar a rufe, cikin mamaki yace "Yaya me kenan?" Hassan ya zuge glass dinsa yace " ka shiga motar ka Mamman ya jaka, ni daga can wani guri zanje." Sagir ba tare da tunanin komai ba ya juya ya shiga motar sa shida Mamman. Haka suka fita da motoci biyu, su Sagir na baya shi yana gaba. Suna tafe suna hira sam hankalinsa baikai kan wayarsa ba domin yanzu harkar yayansa ce a gabansa baya tunanin akwai wani abu da zai ratsa wanda zaiyi distracting dinsa. A kofar gidan Mamman yasa signal sannan aka bude mai gate ya shiga, maimakon Hassan ya shiga kawai sai yai gaba. suna parking Sagir ya juya baiga motar Hassan ba, mamaki ya kamashi da sauri ya fito wajen gidan yana lekawa, sai dai ba shi ba labarinsa. Haka suma mutanen gidan, dan tun lokacin da Mumy ta aika Jalila tazo ta karasa shiryata, taki zuwa hankalinsu ya tashi, ta fito ta duba bangarensu bata ganta ba. Hankalinsu yayi tsananin tashi dan sun duba ko ina basu ganta ba, Mumy kam kamar tai ya ya. Nan Dady ya fito nemanta. Can ita kuwa tana tsaye a inda suke haduwa, tana duba agoggo, taji ance bayan la'asar zaizo shiyasa take sauri Uncle yazo suyi magana ta koma kafin hudu da rabi. Agoggon hannunta ta kalla, karfe 4:30jiki a sanyaye ta juya, lalai yanzu wata zuciya tana sanar da ita Uncle bai damu da ita sosai ba, wata zuciyar kuma neman yi masa uzuri takeyi. Haka ta tako jiki a sanyaye ta tsaya akan titi dan neman adaidaita. Tana tsaye mota tai parkin ta bayanta kadan, kallan motar tai dan ta dauka uncle ne, batai ma tunanin motar waye ba kawai ta nufi motar. Shikuwa yanda tazo saitinsa ne yasa cikin mamaki yake kallanta. Sai dataje jikin kofar sannan tai tunanin ba shi bane, lalai zuciyarta a matse take da san ganin Uncle, baki ta turo sannan ta juya jiki a sanyaye. Yana zaune a ciki yana kallanta, da yake motar tint ce itakam bata ganshi ba. Haka ta tsaya a titi zuciyarta duk ba dadi, sai kara leka hanya take ko zata ganshi. Yana kallanta harta samu mota ta shiga, kai ya girgiza sannan ya kashe motar, yasa kansa akan kujera yana tunani, shikam ta ina zai fara kallan mace da sunan zance? Sannan in tsautsayi yasa matsalarsa ta tashi fa? shikam hankalinsa ya kasa kwanciya, ya san kuma Sagir zaisan me zaice mata. Haka ta samu adaidaita ta hau jiki a sanyaye, ajiyar zuciya taitayi a cikin adaidaitar har suka isa, tana kokarin biyan kudin adaidaitar su kuma suka fito daga cikin gidan. Motar tabi da kallo, taga mutane biyu a zaune sai dai hankalinta ba'a kansu yake ba. Haka ta taho a hankali ta tura gate din gidan. Mumy ta ganina waje itada Dady suna magana, suna ganinta suka juyo suka zuba mata idanu. Dady a zuciye ya fara takowa, ganin haka yasata ta tsorata. Hannu ya daga zai shara mata mari, da sauri ta runtse idanunta, tsayawa yai sannan ya kalleta rai a bace, yatsa ya nuna mata yace "ni zaki cima mutumci?" Mumy ta matso ta sauke mai hannu tace "Dadyn Yasmeen meye hakan?" Kallanta yai yace "yanzu da badan shima dalili ya hanashi zuwa ba fa?sannan da kanin nasa bai fahimcemu ba fa?" Mumy ta kalleshi tace "tunda dai komai yazo da sauki ba shikenan ba?" Yace "in Inna taji fa? Me kike tunanin za'ace?" Mumy tace "sai muce mata ta ganshi sun gaisa harya tafi." Dady ya kalleta cikin jin dadi, wanda baisan a ranta ba wai damuwa da Jalilan tai ba balle tace batasan a mata fada ne, tayi hakan ne dan abin ya kara karfafa. Jalila ta kalla sannan tace "Hassan din wani uzuri mai karfi ya tasomai a hanya bayan sun fito, dole ne yasashi kin zuwa, shiyasa ya turo kaninsa. Jalila ta dan tabe baki kadan, dan itakam ba damuwarta bane. Mumy ta rike hannunta tace "muje ciki ko?" Jalila tace "A'a Mumy asibiti zan koma." Mumy ta jinjina kai tace "bari mu kaiki." Jalila fuskarta dama a daure take tai bangarensu. Kayan da Goggo tace ta dauko mata ta dauko sannan ta fito. Suna tsaye suna ta wani abu wai su a dole mata da miji, ita Mumy sai wani shagwabewa take, haushi ya kara kama Jalila a ranta tace "mutum ya girma amma jinsa yake kamar yaro." Ta gabansu tazo ta wuce, Mumt ta riko hannunta tace "Jalila tare zamu tafi." Jalila tai shiru tana kallan Dady. Mumy ta bude mata baya sannan ta shiga, ita kuma ta shiga kusa da Dady. A hanya tayi shiru tana kallan waje, wayarta ce ta fara ringing, da sauri ta zarota. Uncle? Da sauri ta daga tace "Uncle!" Jalila i am............ Bata gama jin mai zai fada ba, Dady yai wani irin parking, wanda ya tsoratata, sam ta mantada mutane a motar. Mumy ta fizgi wayar tana cewa "Jalila me kenan?" Jalila a tsorace ta kalleta, sunan da ke jiki ta kalla MINE? Nunawa Dady tai ya kashe wayar yace "uban wa ya sai miki waya?" Idanunta ne suka firfito tai shiru. Mumy tace "Jalila zance kike a bayan idanun mu?" Jalila ta kallesu sai dai ta kasa magana, cikin salo Mumy tace "shiyasa take neman bijerawa maganarka kenan? Lalai samarin zamani sun iya siyan zuciya, da har zasusa 'da ya bijirema mahaifinsa." Dady cikin takaici yace "Uncle? Malamin ku ne kenan? Dama abinda kike a makarantar kenan?" Jalila da hawaye suka fara zubo mata tai shiru tana kallan ikon Allah. Dady yace "wato ina miki magana ma kinfi karfin amsawa ko?" Jalila tace "ba haka bane Dady." Mumy tace " Jalila yaushe kika zama haka?" Jalila jitai hawaye suna gudu a idanunta, wannan shine a dakeka a kuma hanaka kuka. Haka tana kallo Dady ya zare sim din ya karyashi sannan ya cilar waje, sannan ya ajiye wayar cikin motar sa. Jalila tana kuka tana cewa "dan Allah dady ka barni ko magana daya muyi." Dady ko kallanta baiyi ba ya ja motar sukai gaba. Mumy tana cewa "lalai Jalila wato ya baki kima saurayinki magana?" Juyawa tai tana kallan window tana wani irin kukan takaici. #ONELUV💕 [08/10, 02:11] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 19* A kofar asibitin Dady yai parking sannan sukai shiru a cikin motar, Jalila tasa hannu. zata bude kofar Dady yace "Jalilah!" komawa tai ta zauna tana kallansa tare da amsawa. Dady ya juyo yace "Fatima dan bamu guri." kallansa tai kamar zatai magana sai naga ta fasa, kofar ta bude ta fita sannan ta nufi cikin asibitin. Jalila ta kalleshi

Chapter 8 of 38