Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mutane ma na fara ji." Jalila ta dan shagwabe fuska tace " kice kowa kallona kawai yakeyi?" Zarah tace "ah to mu ai yan kallo ne." Jalila ta rufe fuskarta tace "bari in rufe fuska ta inje a haka." Zarah tai dariya tana cewa " u are so Naive." Jalila tana ta wani nuku nuku a haka har ta fita dan dama jiya ma a waje suka hadu gaban makarantarsu kadan, wani dan lungu. Sai data dan laleka kafin ta gangara wai ita a dole batasan a ganta. Sagir na kallanta yana murmushi har ta karaso, yace " me kike ta lekawa?" Tace "Uncle ya zamuyi? Duk fa ansan menene tsakanin mu." Yace "to sai akai ya?" Tace "qx Yace "nace sai akai ya?" Tace "hmm hmm" Murmushi yai yace " kin manta kin gama skul? Sannan ba yaudara ko wasa muke ba balle muce bamasan a sani, ya zakiyi in sukazo auranmu? Ko gidan mu?" Idanu ta zaro sai kuma ta rufe idanta da sauri, yace "oh ni wai sai yaushe ne za'a daina min kunyar nan?" Sauke hannu tai tace "ni in kai wata maganar ne sai naji kunya ta kamani." Yace "to da alama zan tattara maganganun dake cina sai munyi aure." Murmushi tai, sun dade tare kafin tace zata tafi, dan yau ita kadai za'azo dauka tunda Safeena tana gidan kanin Inner tun last week tacan take zuwa makaranta. ******** Abba ne ya kalli Ummy yace " ya kamata yau na sanar ma Hassan abinda ke faruwa." Ummy tace " ni kam tsoro nake kar abin nashi ya dawo." Abba yace " sai yaushe ne zaki bari a fadamai? Tun wancan satin kike sani nake jan lokaci ko so kike sai abin ya zo zai sani?" Tace"shikenan ka fadamai yau." Abba ya mike yai sama........... #ONELUV💕 [07/10, 21:30] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *NO 12* Hassan na sa kaya yaji Abba na knocking, da sauri ya karasa sa rigarsa sannan ya murda makullin ya bude dakin. Abba ya matsawa ya shiga cikin dakin, kallan dakin Abba ya shiga yi yana jinjina kai, gashi dau duk lalurar dake damun Hassan amma bazaka taba ganin dakinsa da datti ba, yadan murmusa dan tabbas bai manta lokacin yana yaro ba kafin abin nan ya sameshi Hassan mutum ne mai tsafta da tsantsani, sai dai dakin bai musu karami ba? Ko sagir zai maida kasa? Dan dama saboda Hassan ne ya dawo nan kusa da dakinsa. Ganin Abba na ta dubs dube yasa hassan ya koma kan sofa ya zauna. Abba ya kalleshi sannan ya koma kusa dashi shima ya zauna., Matsawa kadan Hassan yai dan Abba ya zauna daf dashi. Abba yai murmushi yace " Hassan yada matsawa?" Bai tanka ba dan dama Abban yasan ba tankawar zaiyi ba. Sunyi shiru sai karar fanka dake kadawa a cikin dakin, sai sanyin A.C, Abba ya rasa ta ina zai fara, can ya daure ya maida hankalinsa kan Hassan yace "Hassan!" Kallansa yadanyi baice komai ba. Sai daya dan kara yin shiru kafin yace "Hassan ke kake tunani game da aure?" "Aure? Aure kamar ya?" Abba yace "baka tunanin aure?" Cikin rashin fahimta yace "ban fahimci aure ga mara lafiya?" Abba ya danyi shiru kafin yace " Hassan mubar zancen lafiya da rashinsa, kafi kowa sanin halin da mahaifiyarka take ciki a kanka, ka kuma san yanda tasha wahala akan rashin dan uwan............" Kallan sa Hassan yai idanunsa har sun kada, bakinsa ne ya fara rawa, hannunsa ya sa a wuyansa yana dan kakari, cikin lokaci kankani Hassan ya rikede, hankalin Abba ya tashi sosai rungumeshi kawai yai dan ya rasa ma mai zai mai. Da kyar numfashinsa ya daidaita sai dai zufa da ta keto masa, Abba jikinsa ya kara yin sanyi tsananin tausayi dan nasa ya kara kamashi. Ya dade sosai kafin ya dawo daidai, Abba ya mike zai fita, Har yakai kofa Hassan yace "Wani abu ya samu Ummy ne?" Abba ya juyo daga inda yake a tsaye cikin raraunar murya yace " Hassan in har ka damu da halin da muke ciki ka amince ka auri yarinyar da mukesanka da ita." Mamaki me ya kara kamashi yace" tambayar abinda ya samu Ummy......." Yanzu Abba ya canza muryarsa daga alamar tausasawa zuwa dan bacin rai, yace " akwai wani abu dake damunta ne a duniya daya wuce matsalar da kake ciki? In har kanasan hankalinta da nawa ya kwanta ka yarda da auren da muke kokarin yi maka." Hassan shima cikin dan zafi abinda rabon da yai magana mai tsayi haka harya manta yace " Taya zaku nemi min aure bayan kunsan halin da nake ciki? Sannan ni a rayuwata kunfi kowa sanin banasan zama inba ni kadai ba, ya zakuyi kuyi tunanin hadani da wata? Bayan kunsan daga ita har ni hakkin mu zaku shiga?" Abba ya dan matso yace "wannan halin da kake ciki shine yasa muke tunanin ma auren kota wani hali, halin zama kai kadai, halin kin fadar in baka da lafiya, halin nunkufarci da rashin fadar matsalar ka, halin kin yima kowa magana, halin rashin kula da kanka, wannan kadan ne daga cikin dalilan dayasa mukesan ma aure." Hassan har zaiyi magana yaji kansa yayi gingirin gim dan gaba daya dama baya iya magana mai tsayi, mikewa yai ya shige cikin toilet ya rufo kofar. Abba ya juya ya fita, Ummy na tsaye a falo a kasa sai zagaye takeyi tana ganinsa ta matso tace ya kukai? Yace "kema kinsan bazai yarda ba daga bugu daya ba." Tace haka ne, yace "ke zaki mai magana gobe, dan inyaga kin damu kema kinsan zai yarda." Tace "amfani dani da tsauyi da kaunar da yakemin zamuyi?" Abba yace "ba haka nake nufina, hakan dai shi kadai ne haya." Shiru tai batace komai ba. Jalila kuwa tana zaune kusa da goggo suna dan cin abinci duk ta dameta da labarin film din India data kalla mai suna Vivah tana ta fada mata yanda saurayin ciki da budurwar ke san juna can tace "Goggo kinsan abin mamaki? Matarfa ranar auransu ta kone a jikinta amma saurayin nan dan tsabar san da yake mata ya nuna shi wannan ba komai bane, Goggo a asibitin fa ya aureta......" Goggo tace " nikan Jalila sai yaushe ne zaki kyalemu muci abinci shiru? Bafa asan mutum na cin abinci na magana, sannan ni na rasa me yasa baki da aiki sai zancen soyayya, wani irin so kikema Sagir din nan dayasa kika koma haka?" Jalila tai dariya tace "Goggo karki damu yanzu tunda muka gama makaranta zaki ganshi tunda kinga gobe za'ai taron yaye mu, kinga kuwa kila ma jibi ki ganshi dan bazai iya dadewa bai ganni ba." Goggo ta girgiza kai cikin mamaki tace "yaran zamani wato ba kunya, sannan ya san gidan nan ne?" Tace "gobe zan kwatantamai." Goggo ta tabe baki tace " da alama dai kinfi sanshi ma." Jalila tau dariya tace " tab Goggo ai ni bansan wayafi san wani a tsakanin mu ba." Ya isheni haka nan. Ta fada tare da tsame hannunta dan ta rasa me yasa takejin kirjinta na mata nauyi sosai sannan sai tafi kanta na sarawa. Jalila tace " Goggo ki bari kawai na kusa daukeki mu koma gidan aurena." Harararta Goggo tai tace " to sannu, nidai na fada miki ki kiyayi kanki karkije ba shine mijinki ba." Jalila tai dariya tace "tab lalai Goggo kina tunanin zan kara san wani bayan Uncle? Ai nni har mafarki nayi na auranmu." Goggo tace "to uwar surutu ya isheni haka nan, ba wanda yasan mijinki a duniya sai Allah sai dai a koda yaushe ina miki fatan miji na gari wanda zai soki kamar ransa ya kuma kula dake kulawar da baki samu ba a rayuwarki." Jalila batace komai ba sai cigaba da cin abincinta datai tana murmushi dan itakam tasan mai so da kula da ita ba kowa bane sai Uncle dinta. ******** Abba ne ya kira Sagir ya tambayeshi labarin jarabawa dan shi ba sanin abinda ake ciki yai ba, nan Sagir ya sanar mai ai an gama Neco. Yana kashe wa ya kira Inna, bayan sun gaisa ne yace mata "Inna yara sun gama jarabawa ko?" Tace "eh sun kammala nima dama ina jiran kiranka." Abba yace " sai mu hanzarta ko?" Tace "ba laifi ai ku muke jira." Yace " To Alhamdulila insha Allah jibi sai mata su kawo lefe." Tace "hakan yayi , Allah ya kaimu." Nan sukai sallama, kallan Mumy tai tace " yaushe kike tunanin ya kamata asanar mata?" Mumy tace " duk sanda ya dace kinsan bata isa bijirema maganar mu ba tunda tasan Uwarta a karkashinmu take, sannan in muka mata barazana da rayuwar ta ba shiri zata aminta da duk abinda muka gindaya mata." Inna ta jinjina kai tace " hakan yayi, yanzu mu bari sai jibinbin ankawo lefe dan na tabbatar bazai wuce sati biyu ba bikin dan da alama Taura ya kosa." Mumy tace "mu ko yau yake so menene damuwar mu? Shiyasa ma nace Safeena ta cigaba da zama a gidan kawu daga nan ta wuce Egypt hankali a kwance." Inna tace " da nace kibi mijinki Abuja yau kin binsa kikai ko?" Tace "Inna dan Allah ki kyale Abbakar, sai yaushe ne zaki barshi yai aikinsa cikin nutsuwa?" Inna ta girgiza kai tace "haryanzu baki da hankali, ke wai a naki haukar har yanzu kina tunani tsabar so ne yasa yake kula dake haka? Yake kuma wulakanta matarcan?" Mumy tace "Hajiya." Inna tai tsaki tace "Ke kika sani, ni dai company din ku bazan taba yarda na barmai gaba daya ba dan kina kallan idanunsa da yanda yake aiki zakisan akwai tsantsar greediness." Mumy ta mike tace " Zan sauka." Inna ta kalleta ta girgiza kai, tace ba da dan ina nuna mai matsayinsa ba kina tunanin zai ci. A da darajaki ne?" Mumy tai shiru, Inna tace "jeki ke kika sani." Mumy ta sauko ranta ba dadi. ******* Ummy ce ta turo kofarsa dan tajita ba a kulle ba, yana zaune a kasa yayi shiru sai ma ka rasa me yakeyi shi kadai kullum a zaune, ta shiga ta ajiye tiren abincin sannan ta zauna gefensa kadan tace "tunani kake?" Kallanta yai bai ce komai ba, tace "Dazu Abbanka yama magana ko?" Yanzun ma baice komai ba, tace "Hassan mu iyayenka ne wandanda duk duniya duk wani mai sanka sai dai ya biyo bayanmu, ka fi kowa sanin bazamu zabama abinda zai cutar dakai ba, bazan kuma nemi takura maka ba, sai dai abu daya zan fadama wannan auran ni na fara amincewa akai sannan shine babban burina wanda nakesan ka taimaka ka cikamin shi." Ta danyi shiru kafin ta mike tai waje. Da kallo yabi bayanta sannan ya runtse idanunsa, Ummy ya takeso yai? #ONELUV💕 [07/10, 22:19] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *Sisters Always Ask Questions, Borrow Clothes, Tell You When Your Hair Doesn't Look Good, Always Fight but Never Drawn Apart, Love You Always, Encorage You When You Are Dawn...* _A Small Quote For My Sister Love You Always Ameenah😍_ *NO 13* A rayuwar Jalila indai tana gaban Goggo jinta takeyi kamar yarinyar goye, shiyasa duk wata tabata da shirme juyema Goggo takeyi, suna kwance zasuyi bacci duk ta isheta da neman sanin asalin labarinta. Goggo tace "to ya isheni haka nan yanzu sai ki kwanta ko kin manta gobe kunada taro a makaranta?" Jalila ta juyo inda Goggo take tace "Goggo kinsan yanzu addu'ar da nake yi yanzu?" Goggo tace "ya wuce shirmen soyayyarki?" Jalila ta girgiza kai tace "A'a addu'a nake Allah ya kara miki lafiya da tsawan kwana muyi rayuwa tare, banaji zan iya kwana d'aya a duniya in bakyanan." Goggo ta hade rai tace "Jalila nikam sai yaushe ne zaki girma? Na dauka in mutum ya tashi cikin wahala yana hankali amma wani sa'in in kikai wani abun sai inta mamakin ki." Jalila tai murmushi tace "Goggo a koda yaushe in ina tare dake ji na nake kamar yarinyar goye, kece kawata, mahaifiyata, mahaifina, sannan kuma yar uwata, Goggo yanda bana boye miki komai dan Allah kema kidinga sanar dani komai na rayuwarki." Kallan tausayawa ta mata dan tabbas tana ji a jikinta wani babban ciwo na cinta domin wasu sababbin canjin da take fuskata a jikinta tasan da matsala,, sai dai fatan Allah yasa abin ba babba bane. Jalila tace "Goggo!" Goggo tace "shikenan Jalila na miki alkawari a daren gobe zan sanar dake komai na kafin a haifeki, yanzu dai ki kwanta." Tace "yauwa Goggona, saida safe." Goggo ta daga kai, sannan ta zuba mata ido, kankace me Jalila ta tafi bacci. Goggo a dade tana kallanta har batasan sanda hawaye suka gangaro mata ba, hannu tasa ta share sannan ta gyara mata bargo ta juya ta fara bacci. Da safe bayan ta gama gyara bangarensu ta fada wanka, an dade ana saba jiki kai kace fatar tata zata canza, ta fito ta bude drawer dinta ta saka kayan makaranta sannan ta shiga duba sababbin dinkin da aka mata, nan ta zabi wani lace mai an karan kyau yasha duwatsu, ta fara kokarin sawa a jakar hannunta da aka sai mata. Goggo ta bude labule tana kokarin shigowa, kallan Jalila tai tace "ke da zaki makaranta me zakiyi da kayan gida?" Ta karasa shigowa da kyar ta samu ta zauna. Jalila tai murmushi tace "Goggo yau fa ake yaye mu." Tace "to sai akai ya?" Jalila tace "Ana gama taran ai zamu kwabe mu shiga kayan gida ai shagali." Goggo ta tabe baki cikin rashin gamsuwa tace " Wai yaushe aka fara haka a makarantar Gomnati ma?" Jalila tai dariya tace " ina kike fita balle ki sani?" Goggo tace "Hmm amma ai kyaci abinci ko?" Jalila tace " Ni bana jin yunwa sannan za'a kawo abin saidawa a makaran........." Kallan da Goggo ta matane yasa ta zauna da sauri tare da bude kular abincin, tea ne da bread da farfesun naman kai." Jalila ta dade kafin ta bude bread din, har goggo tace "menene?" Jalila tai yake tace "rayuwa kawai nake tunani Goggo, wai yanzu mune ake bamu abinci ba tare da munyi musu aiki ba, Goggo kin manta sanda muke musu wanki? Mu musu komai na gidan?" Goggo tace " rayuwa kenan Jalila, insha Allah wahala ta kare miki a rayuwa." Jalila tai murmushi sannan ta fara cin abincin, bazata cemata iyaye suna zuwa ba dan ta tabbbar zataji ba dadi, gashi ita ba lafiyar kafa ba." Tana gamaci ta fito, Sultan ta gani yana kokarin shiga mota, tace "Sultan?" Tsayawa yai har ta iso, tace "ina zaka?" Ta dauka cemai akai ya rakata saboda gama makaranta da zasuyi. Jitai Yace "In an kaiki makaranta ne zan wuce gidan kawu in amso sako." Sakon me? Yace " kamar wai lefe za'a kawo." Jalila cikin mamaki tace "lefe? Lefen wa za'a kawo?" Yace "ina na sani?" Ya fada tare da shiga motar. Jalila ta shiga tana mamaki, bikin Safeena za'ai? Amma bataji labari ba, to ko amsar kayan za'ai kawai a gidan?" Ganin batada amsa yasa ta share. Yau yan mate dinsu Jalila ansha uban kwalliya, sai iyayi akeyi. Haka aka fara programs kowa iyayensa da yan uwansa sai zuwa sukeyi, Jalila tana zaune dan tasan ba wanda zata gani. Zarah ce ta tabata tace "Jalila Yaya yazo dasu Umma." Nan sukaje suka gaishesu, Jalila tana zaune daga inda take tana hango Uncle Sagir, insuka hada ido sai suyi ma juna murmushi. Ganin Uncle ne ma yasa ta cire komai a ranta har aka gama programs. Nan sukaje suka canza kaya kowa yasa kayan gida suka dau kwalliya, masu waya sunata yin hotuna, Zahra ma ta zo musu da waya sai hoto ake tayi. Wata monitor din Jss3 ce ta shigo ajin nasu, nan ta nemi inda Jalila take ta tabata. Jalila ta kalleta tace " Hadiza ya akai?" Mika mata wata yar karamar jaka ta kwalli tai tace "gashi inji Uncle Sagir." Jalila ta amsa tana bude jakar. Kwalli ta gani ta jawo,Zahrace ta matso ta fizgi kwallin tana cewa " me muka sa......" Ganin waya yasa ta kalli Jalila tace " yeee!" Jalila ta harareta sannan ta fizge wayar tace " muga." Ganin Wayar ne ya sa ta kallan Zahra, hannu tasa cikin jakar ta zaro wani karamin card. Bude shi tai taga ansa _To u my dear!_ _Congratulation on your graduation, here is my small gift, hope you will accept it._ Zarah ce ta kara amsar wayar ta bude ta, wayace mai tsananin kyau Sumsung Note 5 ce. Kan kice me Zarah ta fara haska Jalila wacce tai tsuru tana kallan ikon Allah. Fitowa tai daga ajin ta shiga nemanshi, can ta hangoshi cikin mutane. Tsayuwa tai dan bata san ya zatai ba, juyowa yai kawai sai hangota yai daga nesa. Yaune rana ta farko da ya ganta cikin shiga haka mai kyau dauke da kwalliya, sannan wannan ne rana ta biyu daya ganta ma da kayan gida a iya zamansu, na farko sanda ya fara ganinta sai kuwa yau. Kasa dauke ido yai daga kanta wanda har hakan yasata tsarguwa. Juyawa tai da sauri ta shiga class din. Zahra ta matso tana nuna mata hotunan da ta mata. Jalila kam bata kula taba dan hankalinta nakan Uncle dake waje. Daina hangoshi tai hakan yasa ta fito daga class din tana lekensa. Zarah ce ta miko mata wayar da sauri tace "Zarah Yours na kiranki." Jalila aji abin banbarakwai, kallan wayar tai a jiki an saka MINE dariya tai sannan ta kalli zahra tace ya ake daga wa?" Mamaki ya kama Zahra sai dai kafin ta farga Jalila tana gwadawa kawai taga yaja hakan yasa Zahra tai tunanin iskanci take mata. Jitai yace "Banga kwalliyar nan ba, tunda ba'a ganni ba sai a taimaka azo inda muke haduwa." Murmushi tai sannan tace "to." Kallan Zahra tai sannan tace "ina zuwa." Nan ta fara tafiya. Yau a kan mota ta ganshi, karasawa tai fuskarta dauke da murmushi da kuma kunya. Tana isa ta gaisheshi, yace "Irin wannan kyau haka ai sai kisa in rasa gane hanya." Kallansa tai tace "Uncle wannan gift din yayi yawa, bana tunanin zan iya amsa, Goggo ma fada zatamin" Yace " to Jalila ya kikeso muyi? Kingama skul nima na gama service a ina kikeso indinga jinki? Ke ba waya ba? Sannan ko zuwa zan dinga yi kina tunanin za'a barni nazo kullum?" Jalila tace kullum? Yace sosai in har bazaki amshi wayar ba sai dai ki amince kullum nazo muyi awa uku tare. Da sauri ta zaro ido dan tasan wannan inaa bazai yiwu ba. Ji tai yace "bazai yiwu ba ko? To kinga kawai ki hakura." Jalila tace "Amma....." Yace "mu bar maganar nan please." Kallansa tai dan batasan me zata ce ba.......... Hira suka shiga yi ta masoya masu tashen soyayya, Kiran wayarsa da akai ne yasa ya kalli wayar mamaki yai dayaga Mine a jiki dan number Jalila ce. Nan ya daga yana cewa wayarki na gun wa? Tace Zahra Zahra na dagawa tace "Uncle wai Jalila tazo anzo daukarta." Uncle ya kalleta yace "wai anzo daukarki." Mamaki ya kamata tace "amma nace sai bayan azahar, gabanta ne ya fadi badai wani abun bane ya samu Goggon ta?" Kallan Uncle tai a tsorace tace "Uncle bari naje gida." Zahra na tsaye kusa da motarsu, wayarta ta mika mata ta bata jakarta, nan Jalila ta sa a cikin jakar ta shiga ciki sukai gaba, addu'a kawai take Allah yasa ba wani abun bane ya samu Goggonta. *£*£********* Goggo tana zaune wajen karfe 12 Yasmeen tazo da gudu wai tazo inji Inna. Tayi mamaki sosai dan tanaji tunda take a gidan Inna bata taba nemanta ba haka kawai. Samun kanta tai da faduwar gaba. Haka ta taso da kyar saboda ciwon kafa ta karasa. Tana shiga falon taga Inna, Dady da Mumy a zaune. Faduwar da gabanta ya shiga yi ne kawai ya sa ta shiga yin addu'a dan ta tabbatar ba lafiya ba, shiga tai a hankali. Mumy ta mata nuni da kujerar dake gefe tace "ki zauna anan." Goggo ta zauna sannan ta gaida Inna ta gaida Dady da Mumy. Bayan sun amsa ne falon yai dan shiru. Goggo tace "lafiya?" Inna tace "Gobe za'a kawo kayan lefen Jalila." Abin yazoma Goggo a ba zata wanda yasa tace "lefen Jalila kamar ya kenan? Dan banaji ta taba sanar dani tanada miji." Inna tace " ba sai ta sanar dake tana da saurayi ba, dan kuwa hakkin mahaifi ne ya zaba mata mijin da yaga ya dace da ita, sannan shi Abbakar ya fitar da nasa hakkin na yi mata miji yanzu hakkin 'ya ne tabi umarnin mahaifinta." Goggo ta kalli Dady da sauri tace " Abbakar me kenan?" Yace "hakan da kikaji shine." Cikin daga murya tace "da tunda aka haifeta bakasan da hakkin ta akanka ba sai yanzu? Dama wlh ni jikina yaban mutuncin da kuke mata da wani abin a kasa, ashe aurar da ita zakuyi? Mijin mahaukaci ne ko dan shaye shaye? Ko kuwa barawo ne? Ko kuma nakasasshe? Ko kuma dan fashi ne?" Mumy tace "ya zaki fadi haka, Abbakar fa ubanta ne ta ya za........." Goggo cikin tsawa tace "Ba dake nake ba." Yanda tai maganar ne yasa Mumy tsorata dan bata taba ganin Goggo na fada haka ba. Goggo cikin fada tacigaba " me ka mata a matsayinka na ubanta? Me ka mata?" Dady shim ya kasa magana dan bai taba ganin tana fada haka ba. Goggo fa mike da kyar idanunta sun canza tace " duk abinda kuke ma tunanin ku ajiye dan wlh ba wanda ya isa ya yima Jalila auren dole." Juyawar da zatai taji wani jiri na debanta, kan kace me tayi baya luuuu jikake tim ta fadi a kasa. Da sauri suka mike suna jijigata. Jalila wacce ta shiga bangarensu da gudu taga ba Goggo jakarta ta cilar a dakin sannani ta fito ta nufi bangarensu Mumy dan tambayarsu,ganin Goggo a kasa su Dady da Mumy na kanta yasa ta karasa da gudu jikinta na bari. #ONELUV💕 [08/10, 02:02] ‪+234 803 222 1758‬: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *No 14* Dady a rikice ya nufi daki ya dauko key din mota ganin yanda Goggo take a kwance ga Jalila sai wani irin kuka takeyi. Jiyai ance "ABUBAKAR." Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalli Inna, kallansa tai tace "ina zaka?" Yace "Asibiti." Tace "dawo ka zauna." Tsayawa yai yana kallan Goggo sannan ya kalli Inna. Mumy ce ta kalli Inna tace "Inna kingafa......" Kallan data mata ne yasa ta yin shiru, Jalila a rikice ta jawo gwiwarta ta iso inda Inna take tace "Inna dan Allah ki bar Dady ya kai Goggo asibiti, duk da bansan me ya hadaku da Goggo ba har take nan bangaren sai dai na rokeki da ki yi hakuri." Hannunta ta hada guri daga tana ta murzasu tana kuka alamar tsantsar neman taimako. Ganin Inna batada niyyar kulata yasa ta ja gwiwa zuwa gun Dady ta rike kafaraa tace "Dady ka taimaka dan Allah, karka manta Goggo matarka ce, sannan mahaifiyatace." Gani tai Dady ya kalli Inna, hankalin Jalila ne ya kara tashi ta matso kusa da Mumy ta rike gwiwowinta tace "Mumy ki taimaka min, bazan sake yima Safeena laifi ba, sannan zan cigaba da yi muku aiki, dan Allah ku taimakeni ku kai Goggo Asibiti." Muryar Inna ce ta katseta da cewa " kinaso a ceci ran mahaifiyarki?" Jalila a rikice tana kuka shabe shabe ta shiga daga kai ba kakautawa,

Chapter 6 of 38