Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana wani magana, har na tsawon minti goma sha biyar, kafin ta tsugunna jin kafarta na dan zafi, ji tai ya saki hannunta. Kallansa ta sakeyi sannan tace "Yaya jikin ne ko wani abun ne ya faru?" Bai kalleta ba, sai dai yanzu ya mike daga kasan da yake ya zauna akan gado. Sannan ya kalleta, idanunta na kansa ta kara cewa "yaya!" Kallanta yai sannan yace " are u worried about me? Or are u scared?" Ta kalleshi tace "Yaya dan Allah kadaina min tambayar nan, dan bansan me zance ba." Yace "okay, jeki to." Tace "naam?" Yace "ba fita zakiyi ba na tsayar dake?" Kallansa ta sakeyi tace " Yaya." Kallan daya mata ne yasa ta mike tai waje jiki a sanyaye. Zama tai a falon tana tunanin abinda ya faru yanzun nan, ya riketa sannan yace jeki, mekenan? Itakam tana kasa ganeshi wani sa'in. ********** A Abuja kuwa Abba na gama waya ko kallan Hafiz baiyiba ya fada motarsa yai gaba hankali a tashe, kayansa kawai ya dauko a dakinsa sannan yai check out ya fito tare da ajiye motar. Airport ya nufa dan hankalin sa a tashe yake, yana zuwa yai sa'a akwai jirgin da zai tashi karfe 3:00pm zama yai yana jira sai dai zuciyarsa ta kasa nutsuwa. Lokaci nayi kuwa ya mike da sauri, ba nisa daga Abuja zuwa kano a jirgi kan kace me sai gasu sun sauka. Bai tsaya neman Mamman ba kawai ya hau taxi zuwa gida. Ummy na kwance a falo, tayi shiru tana tunanin Hassan, tana jiran dawowar Sageer daga gun Dr. Jin an taba kofa ne yasa ta mike da sauri dan ta dauka Sageer ne. Da sauri ta bude kofar tana cewa “Sageer me Dr din ya.......” Ganin Abba yasa ta tsaya da maganar tana kallansa, kafin tace “ Sannu da zuwa.” Kallanta yai jiki a sanyaye yace “Yauwa, sannan ya fara kokarin shiga ciki.” Hannu tasa ta amshi jakarsa tai gaba fuskarta ba walwala. Kallan falon yai sannan ya kalli hanyar sama, kafin yace “ina mutanen gidan?” Tace “Ameera tace sai jibi zata dawo, Sageer ya fita.” Yace “Jalila fa?” Tace “Tana sama.” Yace “Hassan fa? Ya jikin nashi?” Kallansa tadanyi kamar zata fadamai sai tace “da sauki.” Sannan tai gaba. Ba abinda yakesan ji ba kenan, so yake yaji ko wani abun ya faru dashi, sai dai baisan ta ina zai fara ba shiyasa yai shiru. Ummy tana ajiye mai jaka ta juya zata fita, har takai kofa yai sauri yace “ kinje taron kuwa?” Kallansa tai tace “banje ba.” Yace “Naga kamar bakya farinciki da dawowata.” Wani murmushin takaici tai kafin tace “banasan musu ko fada dakai daga dawowarka, mu bar maganarnan, kai wanka kafin ma shiryama abinci.” Kallanta yai hartabar dakin, zama yai a bakin gadon sannan ya sa hannayensa ya rufe fuskarsa. Jalila kam ganin hankalinta ya kasa kwanciya yasa ta mike ta kara turo dakin a hankali. Yana zaune yasa farcensa yana karzar bayan hannunsa, idanunsa nakan bango yana tunani, idanunsa da fuskarsa a hade suke. Jalila ta shigo ciki, har taje kusa dashi bai san tazo ba, hannunsa ta kalla taga yana ta karza har yaji ciwo ga jini nan. Kallan tsoro tamai sannan tasa hannunta agun dayake karza, tana kallansa. Dagowa yai ya kalleta sannan ya kalli Hannunta sannan ya kalli nasa hannun, sake kallanta yai sai dai yanzu idanunsa sun canza. Idanunta ne suka ciciko tace “Yaya wani abun ne yafaru ko? Menene dan Allah? Ko akan abinda na fadama ne?” Hannunsa ya janye sannan ya mike daga kan gadon zai nufi toilet. Tace “kayi hakuri dan Allah, laifinane dana sani ban tsaya naji abinda suke cewa ba, sannan dana sani ban fadama abinda ke faruwa ba, kayi hakuri dan Allah, it’s all my fault.” Tafada tare da share kwalla. Juyowa yai ya kalleta kanta na kasa, tana share hawaye, ya dade yana kallanta kafin yace “ ba akanshi bane, sannan in ma shine ba laifinki bane laifinane tunda ni na matsa miki sai kin fadamin.” Kallansa tai sannan tace “ akansa ne ko?” Kai ya girgiza mata alamar a’a sannan ya shiga toilet. Kallansa tai sannan tai ajiyar zuciya tace “Goggo ya zanyi? Inaji nayi laifi ga wanda zai taimakeki, na tambatar da ban fadamai ba kila yau zai dauke ki daga asibitin sai dai da alama wannan bakin nawa ya ja min........ ************** Inna ce ta kalli Dady tace “Abakar!” Kallanta yai sannan ya amsa, tace “ sai yaushe zaka gidan Jalila?” Yace “so nake sai Taura ya dawo, naji ance yayi tafiya.” Tace “meye damuwa ta da haduwarka da Taura?” Dady yai kasa dakai yana cewa “ai kinga ya kamata mu sake mai godiya da taimakon daya mana.” Inna tace “wace godiya bayan abinda muka aikata yana neman wargajewa saboda shirmanka.” Dady yace “Inna ni......” “Dalla rufemin baki, so kake kace ba laifinka bane? Ka tabbatar ka lalabata da mijin nata, dan kafi kowa sanin dayan plan dinmu da mukesan sake bude wani branch dinmu, ka kuma tabbatar inba da taimakon Taura ba abin nan bazai yiwu ba, ya kamata kasan abinyi, kafin ni insa hannu, kasan in nasa bazata ma kyau ba.” Dady yace “To inna.” Ta kalleshi sannan tace “tashi kaje, ka kuma tabbatar kaje gun Jalila, dan a yanda na ganta da yaran nan ina tsoro karta fadamai komai, wannan yaran idanunsa kadai zaka kalla zaka fahimci ba kara a idanunsa balle ya mana.” Yace “to sannan yai waje. Shiru tai tana sake wani tunanin, yanzu me ya dace tayi?????? (Nace “ kya tambaye ni😏”) ********* Sageer ne ya kalli Dr yace “kana nufin hakan alamu ne na samun nasara? Dr ya kalli Sageer sannan ya jinjina kai yace “Sageer kasan Hassan yana dauke da trauma ne wanda shikadai yasan abin da kuma faruwar abin, tunda abin ya faru ka taba gani yayi ihu ko fada da karaji?” Sageer yace “a’a sai dai zafin rai, rashin magana da kadaicewa, sai kuma rashin nuna emotion na farin ciki ko na tsantsan bakin ciki a fuskarsa, a koda yaushe fuskarsa a hade take wanda yake nuna alama ta bakin ciki ba alama na canji.” Dr yace “Good, yau kuma fa?” Sageer yace “ yau yayi kara sannan kana kallansa kasan ransa a bace yake wanda bacin ran ne da alama yasashi yin karan.” Yace “Very Good, ka gano improvement?” Sageer yace “na fahimta Doctor, a da yana fada sai dai bawai da jikinsa yakeyi ba, ko zuciyarsa yanayi ne da fuskarsa da bakinsa.” Yace “Very Good ka fahimceni yanzu?” Sageer ya daga kai cikin gamsuwa da jin dadi yace “nagane Dr, na kuma gode sosai. #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *38* Saukowa kasa tai, tana matatakalar karshe, taha an bude kofar dakin Ummy, tsayawa tai tana jira Ummyn ta fito sai ta karaso. Ganin Abba tai ya fito daga dakin, mamaki ne ya kamata da sauri ta karaso dan yana fitowa suka hada ido, tsugunawa tai ta gaisheshi. Kallanta yai bayan ya amsa yace " Jalila Hassan yana sama ne?" Tace "eh." Da sauri ya wuce ta ya nufi sama, bata kawo komai a ranta ba kawai ta wuce falo. A kitchen taji Ummy nan ta nufi gunta, tanashiga tace "Ummy ashe Abba ya dawo?" Ummy ta juyo tace "eh, ya jikin Hassan din?" Jalila tace "da sauki." Ta fada tare da karasawa gunta tana neman taimaka mata gun rufe kullar da ta gama zuba ma abinci." Ummy tace "dauki abincinku la'asar har tayi ba wanda yai lunch." Ta amsa da to. Abba kam dakin ya karasa yai knocking din kofar, Hassan daga ciki ya fito daga toilet kenan daure da alwala ya bude kofar. Tsayawa sukai yana kallansa hannunsa rike da kofar, fuskarsa kuwa ya kara hadeta tamau, Abba ya kalleshi yace " Hassan baka ganni bane?" Hassan ya saki hannun kofar baice komai ba ya wuce ciki. Abba ya shiga dakin sannan ya maida kofar ya rufe, yace "Kayi mamakin ganina ko? Bayan dazu mukai waya." Hassan bai kalleshi ba balle yai magana, Abba ya zauna akan sofa sannan yace "Hassan!" Hassan ya juyo ya kalleshi da jajayen idanunsa, yace "How can u? Of all people?" Abba ya runtse idanunsa cikin takaici sannan ya mike ya kamo hannun Hassan suka zauna akan kujerar. Hannayensa na cikin na Abba yake kallansa, Abba yai shiru kafin yace "Hassan." Hassan ya kalleshi cikin takaici sannan ya zare hannunsa daga nashi yace "Zina kake?" Abba cikin mamaki ya kalleshi yace "Hassan wani irin magana kakeyi haka? Taya zaka cemin ni mahaifinka? Ka kalleni kace zina nake?" Hassan ya mike tsaye tare da dan matsawa daga inda yake yace " Ni kaina ina fatan hakan ya zama laifi ne na aikata." Abba yai shiru yana kallan Hassan, gaba daya ma ya rasa ma mai zaice. Muryar Hassan yaji yace "wacece?" Abba yai shiru tare da shafar fuskarsa, Hassan ya juyo ya kalleshi cikin bakin ciki yace "Budurwarka ce?" Abba yace "Hassan ni kaina ina mamakin kaina, wai nine nakesan........" So? Hassan ya kalleshi ya sake cewa, so? Abba so kace?" Abba yace " Hassan wai me yasa kake kokarin juya kalamai na zuwa abinda ranka ya raya maka?" Hassan cikin dan daga murya yace "ta ya bazan fassara ba? Ta yaya Abba zaka kalleni kacemin wai so? Ta yaya zaka furtamin kalmar so, sannan kalmar san bawai akan Ummy kake yinta ba, ta ya........" Kasa karasawa yai saboda numfashinsa dayaji yana seizing. Abba ya mike da sauri yazo kusa da shi yace "Hassan menene?" Hassan ya zare jikinsa daga rikon da Abba yamai ya dan ja baya cikin takaici yace "ni danka ne, banida ikon hanaka abinda kai niyya, sai dai wlh Abba kamar yanda na fada in dai had ina numfashi bazan taba bari ka tozarta Ummy ba." Kofar dakin aka bude, Abba ya kalli kofar shikam Hassan kai ya juya cikin takaici dan yayi tunanin Jalila ce. Muryar Ummy yaji tace "Hassan!" Juyowa yai da sauri ya kalleta, Ummy ta share kwallarta data zubo mata sannan ta matso kusa dashi dariya yaga tanayi tana share hawayenta, tace " Hassan yanzu Sageer ya kirani, Dr yace sauki ne ke samuwa a gareka, ya gama min bayani naga bazan iya hakuri ba sai na ganka." Ta kara share hawayenta tace "Hassan bansan yanda zan kwatanta maka dadin da nakeji ba." Cikin takaici ya kalli Abba sannan ya kalli Jalila wacce ta juya ta fita, Hassan ya kalleta yace " Ummy?" Tace " fadanku da Abbanka a kaina?" Ya kalleta cikin tausayawa, tai murmushi tace "karka damu Hassan bakomai, ko ka manta ba mace daya aka halarta ma namiji ha aura ba? Ta yaya zaka nemi mahaifinka ya zauna da mahaifiyarka ita kadai? In mukai haka bamuyi san kai ba? Ko baka ga na fara tsufa bane?" Idanunsa ya rufe cikin takaici yace " ya wani irin zance kikeyi Ummy? Waye zai ga Ummy yace ta tsufa?" Ummy tai dariyar takaici tace "ba wani kai dai sankai zakai, Hassan gashi nan na fara gani." Yace "me?" Tace "samun saukinka mana, rabon da kayimin magana mai tsayi haka har na manta, yau gashi nan kana min magana." Shiru yai kawai yana kallanta, Ummy cikin jin dadi tace "Kar kasa komai a ranka, ka manta da maganar da kukai yanzu, kayi kokari ka dawo Hassan dinka ma da, I really miss that Hassan." Baice komai ba sai kallanta kawai da yakeyi, Abba ne ya share kwallar data dan zubo mai, sannan yai waje da sauri. Ummy ta kalli Hassan tace "Please ka kula da matarka, wannan shi kadai ne abinda ni nakeso, kaji?" Hassan yai shiru, ta juya tai waje. Jalila na zaune a kasa a falo ta sa kanta akan gwiwowinta, gaba daya abinda ke faruwa ya sa tausayin Ummy ya sa ta zubar da kwalla, wannan wace irin macece? Ita lafiyar Hassan ce a gabanta bawai abinda taji ba? Tana kallan Ummy ta fita, mikewa tai ta shiga dakin, gani tai har ya tada sallah. Nan itama ta wuce tai alwala tai sallah, ganin bashida niyar mikewa daga kan sallaya yasa ta fito daga dakin. Abba kam daki ya shiga ya shiga zagaye dakin cikin takaicin abinda zuciyarsa take sashi aikatawa, wani irin butulci ne hakan yake shirin yi? Ummy ce ta shigo dakin tacemai, yallabai ka fito kaci abinci, ko in kawo ma nan?" Jiki a sanyaye yace "muje can din." Ya zauna akan kujera ta zubamai sannan ta turamai abincin gabansa, sannan ta juya tai daki. Da kallo ya bita dan baisan ta ina zai fara magana ba, shi yanda takeyi kamar ma batasan me ake ciki ba shine ya kara tsoratashi, dana sani ya kara kamashi. Jalila kam, sai yamma liss ta samu taci abinci kadan, sam ba fuska agun Hassan, dan ko kallanta baiyi ba bare ta samu damar yi mai magana. Haka tai tayin abinda zatai har dare, shikansa Abba har dare bai samu damar yi mata magana ba. Bayan sallar Magrib ne Sageer zai shigo yaga motar Dady. Nan yasa aka budemai yai parking din motarsa, Dady ya fito suka gaisa, Sageer ya jashi ciki. Yau gidan tsit ba dadi, Hassan na daki, Jalila na falo a kan carpet a kwance tana latsa waya, Ummy na falo shi kuma Abba yana daki. Sageer ne ya shigo ya kalli Ummy yace "Ummy dadyn Jalila me yazo." Mikewa tai da sauri tace "ka shigar dashi falon Abba" Nan Sageer ya shigo dashi yai bangaren Abba. Ummy ta bude dakinsu ta kalli Abba dake zaune yayi shiru abin duniya ya dameshi tace "Abban Ameera ka fito Baban Jalila ne yazo." Abba ya mike tare da cewa to. Ta juya ta fita, Sageer ne ya karaso yace "Ummy na kaishi." Tace "Sageer dan hau sama kama Jalila magana, bari na shirya abin sha." Yace to, sannan ya hau sama har zai kwankwasa kofar yaji motsi a falon, nan ya juya ya falon, a kasa ya ganta tana ta latse latsen waya, tv din ma ba'a kunne take ba. Kallanta ya tsaya yana yi cikin tausayawa, sai dai ya taya yayansa murna ta fara samun lafiya, sai dai shikam tausayin kansa yakeyi, anya zai iya san wata kuwa? Jalila ce ta juyo, ganinsa tai a tsaye ta mike zaune tana kallansa, yace "ashe kina nan?" Ya dan sosa keyarsa. Tace "Eh." Yace "Uhmm dama Ummy ce tace nazo na fadamiki Dadynki yazo." Kallansa tai cikin mamaki tace "Dady?" Yace "eh, yana fallon Abba." Ya fada tare da juyawa. Jalila ta mike gabanta na faduwa, me yazo yi? Badai wani abin bane ya samu Goggon ta? A rikice ta shiga dakin tana neman hijab dinta, gashi a gabanta wanda ta ninke bayan tayi sallah amma tsabar hankalinta baya jikinta sam ta rasashi. Hassan dake zaune yana kallanta shine yace "menene?" Matsowa kusa da shi tai kamar dama jiran kiransa takeyi, tace "Yaya! Dady ne yazo, baka tunanin ko wani abun ne ya faru da Goggona? Ko kuma wani abun suke shirin yimata?" Ganin yanda ta rikice ne yasa yace "Dan yazo shine kika rikice haka?" Tace "Yaya bansan........" Tai maganar cikin wani irin murya mai raunin gaske, da yatsarsa ya nuna mata hijab din sannan yace " a haka zaki?" Ta kalleshi alamar rashin fahimta, yace “ bazaki daidaita kanki ba?” Tsayawa tai tana ajiyar zuciya wai tana calming din kanta, baisan yanzun ma bakinsa ya motsa ba saboda yanda takeyi. Yace “yimin magana naji.” Tace “Yaya!” Yace “sake.” Tace “Yaya.” Yace “bai yi ba.” Baki tadan turo tace “dazu amma inasan maka magana ai hade rai kayi.” Ya kalleta yace “ ni yanzu inaji damuwar dake gabanki tafi tawa, ke mahaifiyarki zaki ceto wace take hannunsu, ni kuma i am confidence akan I will protect mine.” Tace “ni ma.......” Sai kuma tai shiru dan tasan she is not confident. Yanzu ma bakinsa sai da ya sake motsawa yace “jeki, bari na jira naga yanda zakiyi.” Ta kalleshi tace “yaya zakazo?” Yace “ina kenan?” Tace “ gun Dady, tsoro nakeji kar ya sani abunda banzan iya bijerewa ba.” Kafada ya daga mata alamar ba ruwansa. Jalila tai raurau da ido tace “Yaya Please!” Samun kansa yai da kallanta cikin wani yanayi sannan yace “ki wuce kije ko?” Ta dau hijab jiki a sanyaye ta fita.......... Da kallo ya bita har ta fita daga dakin, yabi kofar da kallo. #OneLuv💕 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *39* Fitowa tai jiki a sayaye, abin duniya duk ya dameta ga tsoron abinda zai fito daga bakin Dady da takeyi. Tana sauka kasa taga Ummy, Ummy ta nuna mata hanyar falo tare da mika mata tiren dake dauke da juice da cup, Jalila ta amsa tare da yin murmushin dole sannan ta nufi falon. A gefen kofar da zata shiga da ita falon taga Sageer a tsaye, kallansa tai da idanunta wanda suka cika da taoro, yace "Jalila, menene wai?" Kai ta girgiza mai alamar ba komai, zata shiga yankara kasa da murya yace "Jalila?" Juyowa tai ta kalleshi, yace "Bakyasan ganin mahaifinki ne? Naga tunda na fada miki yazo naga fuskarki ta canza." Murmushin yake tai sannan tace " bakomai, nagode." Kawai ta shiga, dan batasan me zatacemai ba. Abba na falon suna ta magana ta shiga bakinta dauke da sallama. Abba da Dady suka amsa, Dady ya kalleta cikin farin ciki yace "Jalila!" Jalia tace "naam sannan ta karasa ta ajiye tiren a gabansa ta gaisheshi. Abba ne ya mike yace "yanzu ba abin business kazo ba, uba ne yazo ganin yarsa, kaga bai kamata na shiga tsakani ba, later mayi magana." Dady ya mike yana godiya har ya fita, kallan Jalila yai wacce ke tsugunne a inda ta ajiye juice din, Dady yace "zauna mana." Ta gyara zamanta tana kallansa, gabanta sai faduwa yake. Dady ya zauna sannan ya kalleta yace "hmm ya gidan?" Tace "lafiya, wani abun ne ya samu Goggona?" Yace "wani abun? Kamar me kenan?" Tai shiru ta kasa magana, yace "dan uba yazo ganin yarsa sai ya zama sai akwai matsala?" Jalila ta kalleshi tace "a'a ba haka bane." Yace "Jalila ni mahaifinki ne, ki daina dararewa da ni." Ta kalleshi kawai bata ce komai ba. Matsowa ya danyi kusa da ita yace "jalila magana nakesan muyi." Kallansa tai cikin tsoro, yace "Nikam ya kukai da mijin naki?" Tace "wani mijin?" Yace "wanda kukazo tare mana, badai wani abun kika fadamai ba ko? Naga kamar baiji dadi ba ranar." Jalila ta kalleshi gabanta na faduwa ta kasa magana, Dady yace "amma yasan Goggo ce ta haifeki ko?" Jalila ta daga kai alamar eh, Dady yace "ya fadama wani ne?" Tace "ban gane ba?" Yace "ya fadama wani kamar mai gidan nan cewar Goggo ce ta haifeki?" Jalila tai shiru, yace "ba dai duk wani sirri na gida kin fadamai ba?" Jalila ta kalleshi yanzun ma batace komai ba, ya kalleta ransa a bace, badai duk wahalar da wulakancin da ya hadiye ba lokaci daya wannan yarinyar zata zo ta ruguzamai? Dan ya tabbatar in har Taura ya kwace kudin daya basu tabbas Inna korar sa zatasa ayi daga company din. Kallan Jalila yai rai a bace yace "Wai Habiba ba magana nake miki ba? Sai dai ki kalleni? Ko kema munafircin uwar taki zaki koya?" Jalila cikin tsoro ta kalleshi, hannunya daga a zuciye zai kai mata mari. Jiyai ance " da alama sararka kenan?" Juyowa tai da sauri ya kalli mai maganar, Jalila ma kallansa tai kawai sai ji tai hawaye sun zubo mata. Karasowa yai cikin tafiyarsa ta isa sannan ya kalleta yace " tashi." Mikewa tai tana kallansa, yace "bakiji me nacemiki ba ne da zaki zo?" Tace "me kace?" Yace “sau nawa zan ce miki ki canza tone in zakiyi magana? Meyasa bakyayi da confidence?” Kallan juna sukai, hawaye ya gangaro mata, juyawa yai ya kalli Dady wanda yai tsuru tsuru. Hassan ya kalleshi yace “ gobe zanzo muje dakai asibiti inda aka kwantar da mahaifiyarta, a gabanka zakasa hannun sallama mu amsheta.” Dady yace “me kake nufi?” Yace “abinda zuciyarka ta baka, u don’t deserve to be a father nor a husband.” Kallan Jalila yai yace “wuce mu tafi.” Kallan Dady tai gabanta na ci gaba da faduwa, Hassan ya kalleta ya mata alama data fara fita, nan ta fita tana waiyaye. Tana fitowa daga bangaren falon taga Sageer a tsaye a jikin bango. Yana ganin ta fito ya matso da sauri yace “ Jalila” Hawayenta ta share sannan ta kalleshi, yace “menene?” Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta juya tai gaba, Sageer yace “Akwai abinda ya faru ko? Naga yaya ya shiga kuma shi bai fito ba.” Juyowa tai ta kalleshi sannan ta juya kawai ta hau sama da gudu. A falo kuwa Hassan ya kalli Dady yace “me ka samu, na saida yarka dakai?” Dady yace “me kake nufi?” Hassan yace “yanda kai da manyanka iyayen gidannka kuke nunawa, kunayi ne kamar kun samu wani abu sosai wanda yasa kuka bada yarku.” Dady ya kalleshi yace “Hassan ta ya zaka ce haka? Kana so kace rashin so ne yasa muka aurar da ita?” Yace “sosai, inba rashin so ba kun taba tambayar ya mijin nata yake? Wasu halaye gareshi? Me nene aikinsa? Ya mu’amalarsa da jama’a take? Duk kunyi wannan tambayar? A matsayinka na uban yarinya?” Dady ya kalleshi yace “Inna tayi bincike ita ce tasan mahai.......” Ya katseshi rai a bace “wacece ita? Menene matsayinta agun Jalila?” Dady yace “bangane ba?” Hassan yamai wani kallo yace “ karka manta gobe zanzo in banzo ba jibi zanzo, in kuma har kukai tunanin yin abinda bai kamata ba, zan baku mamaki.” Ya juya bai jira mai zai ce ba ya fita. Dady haka ya fito gaba daya kansa yayi nauyi, Sageer ne kawai a falon yamai sallama ya fita, yana cemai ya gaida Taura. Mota ya shiga yai gaba. Sai daya je kofar gida sannan yai parking a gefen mota ya kashe motar ya fito yana tunanin abinda zai fi mai mahimmanci, danshi rayuwarsa itace gaba da komai, mai zaiyi dan cigaban sa? Hassan kam yana haura beni kansa na wani juyawa da kyar ya kai kansa daki yana shiga ya kwanta. Jalila na falo tana ganinsa ta taso dan dama ta kasa ko zama ne. Yana shiga a shiga dakin itama, akwance ta ganshi akan gado, taje kusa dashi tana san mai magana sai dai ganin idanunsa a rufe tasan bayasan magana, balle ya juya mata baya. Ta dan dade a tsaye kafin ta fito. Karfe tara tai shimfida ta kwanta, shikam tunda yai sallah ya sake kwanciya bai sake ko motsawa ba balle ta samu damar magana. Shikam takaicin abinda ke faruwa a gidansu ne yake damunshi, meke damun Abba? Meyasa ita wannan rayuwarta take a cude? Meyasa abubuwa ke faruwa haka? Yau ce rana ta farko dayai fada da magana mai tsayi haka, gaba daya kansa wani irin sarawa hakeyi, ya dade sosai kafin bacci ya daukeshi. Jalila kam ta dade a kwance kamar tana bacci, me suka fada da bata nan? Taya uba wanda ya haifeta zai dinga mata haka? Hawayenta ta share data tuno rayuwar da mahaifiyarta tai, lalai bazata bari Goggo ta cigaba da zama dasu ba. Juyawa tai saitin da Hassan yake, ta haska wayarta, ganinsa tai a dukunkune ta mike ta dan rage A.C din dakin sannan ta matso inda yake, kansa baya kan pillow din, in dagashi? Ganin yanda ya kwanta a takure. Hannu tasa a hankali ta daga kansa ta daura akan pillow din sannan ta juya ta kwanta. Shikam tana tabashi yaji ta, har sai data kwanta idanunsa na bude juyawa yai shima saitin da take kwance, duk da ta kashe hasken dakin ba ganinta yakeyi ba, sai dai ya samu kansa da tsurawa gun ido kafin ya maida idanunsa ya rufe. ************* A kasa kuwa, Ummy ce tasa kayan baccinta ta sa hijab tana neman fita daga dakin. Abba ya kalleta yace “ina zaki?” Tace “Dakin Ameera, ni kam kamar munyi kuskure da mun sani dakin can mun gyarashi.” Kallanta yai yanda take mai

Chapter 17 of 38