Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na sanki, idanunsa kadai sun tabbatar da hakan." Jalila ta kalleta sai dai batace komai ba. Ummy ta dafata tace "Jalila godiya, kina sani farincikin dana dade bansamu ba, ganin Hassan na samun sauki yasa kullum zuciyata nakejinta tass, shikansa mahaifinshi yanzu hankalinsa yafi kwanciya har yake fita aiki ya dade haka."Jalila ta sunkuyar da kai a ranta tace me nayi? Ummy tace "mungode Jalila, sai dai ki kara hakuri sannan ki kara kula dashi, insha Allahu bazaki tabba dana sanin auran Hassan ba." Dagowa tai ta kalli Ummy sannan ta daga kai alamar to. Hassan na fita yaje bakin wani shago yai parkin, fita yai ya shiga ciki. Mai shagon ya tambayeshi abinda yakeso, Hassan yai shiru kafin yace "kawai abashi abunda ya dace." Cikin mamaki mai shagon yace "abinda ya dace kamar me kenan?" Gidan mamar matata zankai, ya fada tare da dauke kai. Mai shagon ya guntse dariyarsa sannan yace "katan din juice fa?" Hassan yace dame? Yace sai ka hada ko da kayan tea ne. Hassan yace "samin to." Nan mai shagon ya laftamai kayan tea dan kana kallan motarsa kasan da akwai kudi, ya sa mai juice kala uku a bayan boot ya cafki kudinsa. Hassan na fita yace "Alhamdulila Allah ya kara kawoka." Hassan ya shiga mota yai gidan Goggo. Ya dade a waje yana tunanin abinda zaice kafin ya shiga. Almajirai yasa suka shiga da kayan. Goggo na zaune tana jin radio ana hada musu wuta a waje ya shiga ciki. Tanaganinsa ta mike fuska dauke da fara'a tana lale lale. Ya zauna ya gaisheta ta amsa cikin farinciki, shidai yai shiru. Kowa ta tambayeshi sai dai yace "lafiya." Data gama tambayar tai shiru shima yai shiru. Can yace "ba wuta ne? Naga kamar da wuta a layin?" Tace "gyarawa sukeyi yanzu, Hassan mungode sosai sosai, Allah yayi albarka ya inganta rayuwa." Yace Ameen Shiru suka karayi kafin ya mike yace zai tafi. Tace "da wuri haka?" Yace "eh." Tace "to mungode." Tana fitowa waje tai karo da kayayaki, nan ta kara mai godiya har ya fita. Mota ya shiga yai ajiyar zuciya, sannan ya tada kota ya juyo gida. Jalila kuwa bayan ta gama komai a kasa, ta daura abincin ran. Yana shiga yaji motsi a kitchen, lekawa kitchen din yai, hangota yai tana aiki, yanka vegetables takeyi, tsayawa yai daga inda yake ya kura mata ido, gaba daya yanayin fuskarsa ya canza. Ya dade yana kallanta har itama jikinta ya bata ta juyo. Ganinsa tai a tsaye da alama ya tafi tunani, ta matso tace "Yayah!" Kallanta yai yaganta a gabansa, tace "yaya naga kana......" Da sauri ya wayance yace "kallan yanda kike aiki nakeyi, kin tabbatar kin wankesu kafin ki fara yankawa dai ko? Dan naga kamar baki wanke ba." Cikin mamaki ta kalleshi, juyawa yai ya fita, da kallonta bishi,, yanzu kam ranta ya sosu, me yake nufi? Haka ta cigaba da aikin ta ranta a bace, dan bakin cikin har kwalla ce tadan zubo mata. Shikuwa yana hawa sama ya bude drawer ya dauko hoton Husain yana kallo, a fili cikin wata murya yace "Husain ya zanyi? Nasan bai kamata ba, bai kamata nai sha'awar rayuwa ta jin dadi da wata ba, ban cancanci yin farinciki ba, ban cancanci a soni ko inso wani ba sai dai bansan meke damuna ba, Husain i am really hurting her, wanda nakeji kamar na fita jin zafin abinda nake aikata mata." "Zuciyata na kwadaitamin yin rayuwa da ita, zuciyata na san ta kyautata mata, inasan ingana cikin farinciki, Husain inajina kamar bani ba." Yai shiru tare da rutse idanunsa, ya koma ya jingina da jikin drawer din, a ransa yace "Husain zan sanar da ita komai, dan abinda zuciyata ke rayamin kenan, in har na sanar da ita zan barta tai deciding abinda taga ya dace, inhar tana tunanin rabuwa dani shine mafita shikenan, in kuma....." Sai yai shiru, tare da kara runtse idanunsa,shiru yai ya dora hannunsa akan goshinsa yana tunanin abinda ya faru a baya. Baisan hawaye sun zubo mai ba. ********** Mumy ce ta kalli Dady bayan ta amshi hular dake kansa tace "Dadyn Yasmeen! Inna ta yarda." Yace "dame?" Tace "bazata daurama laifin abinda ya faru ba." Yace " meyasa kike takurama kanki? Nacemiki bakomai, zan iya yin komai indai a kanku ne." Ta ajiye hular ta rungumeshi tace " karka damu, na fadama it's my turn to protect you" Kallanta ya shafa sannan yace " nine ya kamata nai protecting dinki ke da yarana." A tare sukai murmushi...... #OneLuv💕 [12/7, 9:54 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔️ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) Thanks alot for the love 😍May Allah Subhanahu Watta'ala always help and guide us👏🏻 *52* Yanajin motsin shigowarta ya mike ya maida hoton sannan ya fito daga dakin, da kallo ta bishi tace "yaya!" Ko kallanta baiyi ba bare tasa ran zai amsa mata, saukowa kasa yai ya zauna a garden. Ita kuwa ganin yanda ya giftata ko kallanta baiyi ba tace "me kuma nai? Ni Habiba?" Abba ne ya dawo, yana sauka daga cikin mota ya hango kan Hassan, gunsa ya nufa. Jin motsin tahowar mutum yasa Hassan juyowa. Ganin Abba ne yasa ya juya yana kara tunani, Abba ya karaso ya zauna daf dashi. A hankali yace "sannu da zuwa." Abba yai murmushi yace "Eldest me kake tunani? Naga ka dade banganka anan ba." Hassan yai shiru sai dai ya kalli Abba. Abba ya sa hannu a kafadarsa kamar abokinsa yace "Mata ne?" Da sauri ya kalleshi. Abba yai murmushi yace " na canka kenan." Yai saurin cewa "a'a ko kadan." Abba yai dariya sannan ya sauke hannunsa daga kafadar Hassan, yadan yi shiru. Hassan bai kalleshi ba yace "ina yarinyar? Ka daina tunaninta?" Abba shima yana kallan kasa yadan hade hannayensa gu daya yadan matsa, yace " ba kamar da ba." Hassan ya dan kalleshi yace "kana tunanin santa kake?" Abba yace "yanzu gaskiya kakeso na fadama ko kuma abinda nasan zai kwanta maka?" Hassan yace "gaskiya!" Abba yadanyi murmushi kadan yace " inayi sosai, sai dai kamar yanda mahaifiyarka tace zanyi kokari ganin na cireta a raina, dan ina ji a jikina ni kaina ba san daya kamata nake mata ba." Hassan yai shiru kafin ya jinjina kai yace " nagode Abba da kake kokarin cire ta aranta dukda abin ba mai sauki bane." Abba ya riko hannunsa yace "kasan yanda hankalina ya tashi? Lokacin da naga kana fada akan abin? Nayi tir da zuciyata nayi dana sani wanda bazan iya misaltamaka ba." Hassan ya kalleshi sannan yace "bansan nima sanda na hau haka bane....." Abba ya kalleshi yace "naji dadi a kasan raina, at least inada wanda nasan zai hanani, kaga kamar Sageer na tabbatar bazai dage akan abinda nakeso ba, balle Amira, kai kuma ba lafiya ce dakai ba, balle ka hanani abinda zuciyata ke neman jefani, sai dai bansan har jikinka yayi sauki haka ba ina can ina shirme." Ya karasa maganar jiki a sanyaye. Hassan yai shiru kafin yace "Abba a koda yaushe ka dinga tuna wacece Ummy a garemu, in har wannan tunanin na zuwa maka na tabbatar ba abinda zai gifta zuciyarka." Kai ya jinjina yace "ni kaina bansan ya akai zuciyata ta nemi kawomin shirme haka ba, bayan nasan irin kaunar da kakema Mahaifiyarka, bayan kai din kaine rayuwata." Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi na tausayawa. Can ya dauke kansa da sauri saboda kwallar dake neman taruwarmai a ido, ya juya kansa da sauri. Abba ya sake dafa kafadarsa yace "ya ya? Fada kukai da matar taka shine kai yaji?" Hassan ya kalleshi sannan ya dan murmusa kadan. Cikin tsananin mamaki Abba yace "Hassan murmushi kai?" Yace "wa? Ni?" Abba yace "sosai ma kuwa, na tabbatar kayi murmushi yanzun nan. Hassan ya mike da sauri, Abba ya jawoshi ya zauna ya riko hannunsa yace "nagode Hassan." Hassan ya kalleshi yace "name?" Yace "na komai ma, kai d'a na ne wanda na haifa sai dai ban taba alfahari da komai a rayuwa ba kamar ka."Jiki a sanyaye yake kallansa kafin yace "bancancanci samun wannan matsayin ba." Abba ya dan harareshi yace " in tuno ma?" Da sauri Hassan ya mike dan ya fahimci abinda yake nufi yai hanyar ciki, Abba na cewa "in ban tuno ma ba na tunawa matarka." Da sauri ya shiga ciki, Abba ya bishi da kallo cikin tausayawa, har idanunsa suka dan canza, ya juyo tare da dan runtse ido yace "Alhamdulila!" Tana kasa taga hawansa sama, da kallo ta bishi, shigewa yai. Bata hau sama ba sai bayan magrib, dan sunatare da Ameera da Ummy bayan ta dawo daga makaranta, bayan magrib din ma Ummy ce tacemata dare yayi. Ameera tai dariya tace "kai Ummy ba kara?" Ummy tasa hannu tadan kwadeta tace "zaki fara ko?" Mikewa tai ta hau sama, Ummy ma ta mike tace "ke kuma sai kiyi ta zaman gulma. Ameera tace "bari na jira Ya Sageer ya dawo muyi hira, tunda dai ni kowa ya watse ya barni." Ummy tai tafiyarta tana cewa "bari ma na kirashi naji naga ya dade bai dawo ba." Jalila tana hawa sama ta ganshi a kwance, yau ba karatu yake ba sai dai a kwance kawai yake shiru, ta shiga da salama. A hankali ya amsa wanda ita kanta bataji ba, shiga ciki tai tana kallansa. Yaci abinci, a ranta tace yau ba jira?amma rannan harda jin haushinsa. Hartana neman zama a kan kujera sai ta juyo ta fito falo ta zauna, ta kunna Tv. Shiru tai tana tunani, meke damunshi? Ko bashida lafiya ne? Da sauri ta mike ta shiga dakin, tazo jikin gado tace " Yaya? Bakajin dadi ne?" Kai kawai ya girgiza mata alamar a'a idanunsa a rufe. Tai shiru kafin ta juya, har zata fita sai kuka ta shiga toilet. Tana rufo kofar ya mike, ya kalli kofar toilet din. Mikewa tsaye yai ya dau makullin mota ya dau wayarsa. Tana fitowa ya kalleta ya mika mata hijab dinta, kallansa tai tace "me?" Gani tai yayi gaba, da kallo ta bishi tace "yau maganar ma wahala take?" Fitowa tai dan ta fahimci ta biyoshi yake nufi. Haka ya fita, tana kokarin fita Ameera ta fito jitai tace "Amarya sai ina?" Harararta tai tace "inda kika aikeni, kicema Ummy zamu fita." Da gudu Ameera ta taho tace "ina zaku? A daren nan?" Jalila ta in fada miki? Tace eh ina? Ta fada tana matso da kunne Jalila tai dariya tace "inda Ameera ta aikemu." Tai saurin yin waje tana dariya, dan tana tsoron karta dade a tsaye tai laifi. Yana cikin mota harya tada ta bude gefensa zata shiga yace " shiga baya." Komawa tai baya ta shiga tana yan kunkune, tana rufe mota yaja suka fita. Suna fita motar Sageer na shiga gidan. Tafiya yake, ba mai magana a cikin motar, ita kuma haushin ce mata dayai ta shiga baya yasa batai magana ba. Kanta ta sunkuyar, jin alamun an tsaya yasa ta dago. Gidan Goggo? Kallan gidan tai sannan ta kalleshi cikin mamaki. Kashe motar yai sannan ya kwantar da kansa jikin kujera. Jalila cikin mamaki tace "gidan Goggo?" Shiru yai har tana tunanin bazaiyi magana ba, cikin wata murya taji yace. " Jalila?" A tsorace tace "naam." Shiru ya sakeyi na wasu lokuta kafin yace " Zan fadamiki abinda ke damuna, abinda na aikata wanda a koda yaushe dana saninsa shike hanani sukuni, a duk sanda na tuno da abin ko cikin bacci ne nakan ji kamar nima na mutu, nakanji gaba daya duniyar ta zamarmin bakinkirin, nakanji komai na cikin duniyarnan ba abinda yake birgeni, zan sanar dake a gaban gidan mahaifiyarki idan harkinga bazaki iya zama dani ba, sai ki bude kofar ki shiga gida gun mahaifiyarki, in kuma har........."Sai yai shiru, dan bayasan yasa ransa akan abinda bazai samu ba. Shiru ne ya kara ratsa cikin motar, ita kam Jalila tayi tsuru tsuru. " Abdullah Taura shine mahaifina, tunda ya tafi karatu kasar Egypt suka rikeshi ya fara musu aiki a can, gaba daya mutum ne mai tsananin san aiki, hakan yasa ba ruwansa da mace balle aure. Ganin yanda bashida niyyar yin aure yasa mahaifinsa ya masa kamun mata, wacce take 'yace ta abokinsa. Amininsa ne tare suka taso, yanada 'ya'ya dayawa sai dai duk maza ne su uku ne mata. Babbar yarinyar Uwargidan ce, su kuma biyun matarsa ta tsakiya ce ta haifesu, dan matansa uku. Babbar tanada mijinta sai aka bashi ta tsakinyar mai suna Hauwa'u suna kiranta da Jidda. Daga can aka sashi ya dawo, yana zuwa ya ganta ya aminta da ita akai aure a sati biyu da zuwansa dan dama sun shirya komai, anayi ya dau matarsa suka koma garin Egypt. Bazaka taba tunanin auran hadi ne tsakaninsu ba dan suna kula da kaunar juna. Basu dade da aureba Allah ya bata ciki. Irin girman cikin yasa hankalin Taura ya tashi, ba shiri ya ajiye takarda akan yana bukatar hutu mai yawa suka taho. Gidansu ya kaita dan hankalinsa da nata sai yafi kwanciya. A lokacin da suka iso dama ana ta fama da bikin kanwarta, ganin yanda Yayarta ke shan wahala yasa sam hankalinta ya tashi, tana kuka muraran aka kaita gidan miji, haka aka gama biki lafiya ta tare, aka dukufa da mata rubutu da kula da ita, saboda cikin yasata ta kumbura sosai. Taura a koda yaushe yana gidan, kai abin makulashe, magani da duba jikinta, har Allah ya kawo lokaci. Satinta daya tana nakuda wanda ya kara wahalar da ita, aka dauketa aka kaita asibiti aka bata gado. A wata ranar asabar aka yanke hukunci yi mata tiyata dan abin yaki karewa. Kanwarta a rikice tazo asibitin dan labari ya kai mata, kuka kamar ranta zai fita, haka aka shiga da ita tiyata tana rike da hannun kanwarta. A dakin tiyata ana zaro 'ya'yan nan biyu ana kokarin yi mata dinki tace ga garinku nan. Tashin hankalin da suka fuskanta a asibitin nan ba'a magana. Kowa ka gani hankalinsa a tashe yake, haka duk sanda aka kalli jariran nan biyu sai an zubar musu da hawaye. Haka aka kaita gidanta, Taura kamar zaiyi hauka, dauriya kawai yakeyi ba magana, dan inya tuno da jariran yaran nan wadanda ko ganinta basuyi ba sai aji hankalinsa ya tashi. Kanwarta ita ke kula dasu dan ko gidanta bata koma ba, dayake mijinta shima na gida ne, a karshen layin ma ya kama gida. Jin ance ta koma gidanta yasa tace itakam dasu zata tafi, duk yanda akaso ta hakura amma taki, kuka ma tasa tace itakam abarta dan bazata iya barinsu ba. Haka aka hakura ta tafi dasu, sai Taura ya hadata da kanwarsa wacce take shekara 14 suka tafi tana taimaka mata. Gaba daya Taura ya canza, kullum sai yaje ganin yaran nan hankalinsa ke kwanciya, kowa ya gansu bazai taba cewa basuda uwa ba dan sosai take kula dasu, kowa jinjina mata yakeyi dan yarinyace sannan ko haihuwar fari batai ba. Duk wani bukatunsu Taura ya dauke musu, sannan ya kasa komawa ma gun aikinsa. Har yaran nan suka shiga shekara guda, suka fara tafiya, kowa ya gansu abin sha'awa." Hassan yai ajiyar zuciya yace "A wata rana mahaifinta da mijinta sunyi tafiya sukai hatsari wanda ya dauki rayuwarsu. Taga tashin hankali ga mutuwar miji ga kula da yara biyu, sannan gashi batasan tanada karamin ciki ba. Gashi duk yanda akai yaran nan su barta taji da abinda ke damunta sunki dan su itace mahaifiyarsu ita kadai suka sani. Ita ma ta nemi a barsu, haka ta sha wahalar wannan lokaci duk ta rame ta fige. Taura tsananin tausayinta yasa ya umarci dauke yaran sai dai kuka tasa ta nemi a barmata wai mijinta ya tafi kar a rabata da 'ya'yanta. Haka ya bar mata su, har Allah ya kawo mata nata haihuwar ta haifi danta namiji aka sa mai Sageer." Ajiyar zuciya yai yace "Kin fahimci labari na kashe na farko?" Jalila wacce idanunta ke zubar da hawaye tace "Kune yaran kanana, sannan wacce ta rikeku wato kanwar mahaifiyarku Ummy ce???" Hassan yace "eh, Ummy ce." Haka muka taso mu uku, sai dai nu biyu mun girmi Sageer da shekara biyu, dangin mahaifinsa suka daukeshi saboda takaicin yanda take kula damu. Haka muna kuka aka tafi dashi, bayan mun dawo gidan mahaifanta ne aka yanke shawarar hada auransu. Da harta ki amincewa sai dai ganin za'a kwacemu yasa ta amince. Tunda take bata taba nuna tanasan akawo mata danta ba, duk kuwa da kowa yasan zuciyar uwa. Haka Abba ya daukemu muka koma Egypt, zamansu zama ne na kara bawai na aurataya ba, har a hankali suka fahimci mahimmancin junansu. Shekararmu takwas a garin muka dawo nigera, na taso da tsananin kaunar Ummy wanda ko hawaye ko damuwa naga tanayi sai na yi tayin kuka, ganin yanda take zama tai shiru wani sa'in tana kallan hoton Sageer yasa nai ta kuka nace a dawo Nigeria adauko mana shi. Tundaga lokacin Ummy ta ajiye hoton ta daina daukowa, shima Abba ganin haka yasa ya ajiye aikinsa muka dawo. Husain nada magana sannan akwai saukin kai, muna tsananin san Ummy sai dai shakuwar dake tsakanina da ita daban ce. Muna dawowa nace Abba na yaje ya dauko Sageer. Haka mukaje suka hanamu, gashi a kauye suke sun tubure akan dansu bazaiyi agola ba. Sai da Abba ya daukeni mukai zuwa kauyen nan sau kusan goma kafin su amince. Haka suka bamu shi muka kawoma Ummy shi, tayi kuka sosai dan bata taba tunanin za'a bata shi ba. A kuma lokacin ta dauki alkawarin bazata taba banbantamu da Sageer ba." Cikin tsananin mamaki Jalila ke jin wannan labarin, to meyasa Uncle yace bazai ko dan abinda su Hassan suka mai bazai iya musu butulci ba? Saboda daukoshi da sukai? Hassan yai shiru kafin ya dan runtse idanunsa, wani abu na ratsashi......... [12/7, 9:54 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* ✔️ote me on Wattpad : *Ayusher Mohd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (_D home of expert and perfect writer's_💡) *53* Wata irin muguwar shakuwa ce tsakanina da Ummy wanda ko mahaifina banajin kaunarsa haka a raina, ita kanta ko yaya naji ciwo kafin nace da zafi fuskarta ce zata nuna tanajin zafin abin, hakan yasa ko banida lafiya banfiya nuna mata ba, Husain nada kawaici sannan baifiya makon uwa kamar ni ba, da farko bamu taba sanin ba Ummy bace ta haifemu saboda yanda muke, har saida muka dawo daga Cairo, mu kawai mun dauka kanin mu Sageer ne kawai babansa daban. Sageer shikansa baisani ba shi sai da yaje ziyara gun dangin mahaifinsa, sai dai koda wasa bai taba nuna mata ma ya sani ba, duk wani tunani da zakiyi akan yanda Uwa zataso danta Ummy na mana wannan san, Aunty Nana itace yayarsu Ummy amma mahaifiyarta daban, halayenta ba irin na Ummy bane sai dai itama ko da wasa bata nuna mudin ba 'ya'yan Ummy bane, har yau babu wanda na taba ji yace mu ba 'ya'yanta bane sai wanda ya sani tun fil'azal. Yai shiru sautin numfashinsa ya canza kafin yace "haka rayuwarmu ta taso cikin farinciki da kaunar juna har zuwa shekara 13, a lokacin mu muna shekara sha uku shi kuma Sageer na shekara 11, wannan lokacin ma aka kara samun matsala dan 'yan Uwan mahaifinsa daga zuwansa hutu suka rikeshi wai sun kula Ummy ba ta kawoshi duk hutu da alama so take ta daukeshi. Hankalinmu ya tashi dan ni da Husain har zazzabi mukai, sai dai ganin Ummy ta watsar da komai yasa muka ware muma. A wata rana wacce ta zamarmin ranar bakinciki a tarihin rayuwata, a lokacin kanin Abba yazo shida matarsa da 'ya'yansa sunzo gida tayamu murna na suna dan Allah ya albarkaci Ummy da samun 'ya mace ya wato Ameera. Dukansu mata ne sai Sudais kadai wanda yake namiji sannan shine karami dan shekararshi shida a lokacin, yan uwa da dama sunzo tayamu murna. Da yake ni duk inda taro yai yawa ba sanshi nake ba hakan yasa na fito daga cikin gida. Har nayi waje Husain ya kwallamin kira na juyo, yace "ina zaka?" Dayake akwai shaguna a karshen layin mu nace shago zani, yace "bari inzo muje." Nan ya taho da sauri, muna fita kofar gida mukaga Sudais, nace "Sudais daga ina?" Yace "alawa na siyo." Ya nuna mana alawar hannunsa, Husain ya amshi daya ya bude muka taho mu uku, muna tafe munata hira wanda ni kaina a yanzu na manta hira me mukeyi. Har mukaje karshen layin, hango wasu maza mukai a kan titi suna kan doki gashi mutane sai kallansu akeyi, abinka da yarinta kawai sai muka kutsa ciki kuna kallo. Daga tsallaken titi na hango wata mota kamar ta Abba, nace "Husain kaga motar Abba." Ni a guna nasan ba motar bace zolayarsa nakeyi, shikuma yana gani ya yarda yace "ai kuwa muje." Nace ka bari su gama wucewa. Nan muka tsaya har suka wuce nace to mu tsallaka, Sudais sai tsalle yake wai ya hango Abba, wanda ni a guna mugunta na shirya inata dariyar yarinta. Kamar zamu tsallaka titin, harna fara tafiya dasu na dawo baya ina dariya, ina cewa ba Abba bane ziraku nayi. Husain na rike da hannun Sudais ya juyo shima yana dariya yace "amma lalai Hassan, wallahi ni harna yarda Shikuma Sudais, duk ya damu a karasa karshen titi, Husain ya kamo hannunsa suka juyo da shirin dawowa. Gaba daya bamuyi auni ba ina kallansa shima yana kallona muna dariya sai gani nai anyi gaba da.......... Numfashinsa ne ya sarke, wasu zafaffan hawaye ne suke zubomai, karar faduwarsu kawai mukaji. Sam bamu kula da tahowar mota ba, mutanene suka taho gun a rikice, jini....... jini....... Numfashinsa ne ya shiga fita da sauri da sauri. Kansa na wani irin sarawa, yace " Tsoro da fargabar abinda na gani na fara ja da baya da baya, ina kallan jinin da ke zuba daga kansu. Inaji mai motar na tambayar waye ya sansu amma bakina ya kasa magana saboda numfashina da yake hawa da sauka, kaina na wani irin juyawa saboda jinin dake kwaranya....... Kansa ya matse da karfi wanda ke mai wani irin azaba, Jalila kam hawaye duk ya gama jika mata fuska. Matsowa tai tasa hannunta akan kafadarsa tace "Yaya?" Hannunta ya dan ture tunda ya fara labarin sai yanzu ya juyo ya kalleta fuskarsa gaba daya ta canza, bata taba ganin Hassan haka ba, yace "Nine sanadiyar rasa rayukansu, wanda haryau kanin Abba Allah bai kara bashi haihuwa ba, wanda ranar sunan Ameera ya zama ranar rasuwar yayana, wanda nai sanadiyar mutuwar daya daga cikin farin ciki Ummy, farincikin mahaifina sannan farinciki na, bancigaba da makaranta ba saboda na dade a asibiti a kwance, sai dana samu sauki ne Abba ya kawo wani gida yana koyamin, a haka da kyar Ummy ta sani nai exam din waec daga nan ban cigaba da komai ba. Nine sanadi, Taya zan samu farinciki a rayuwata? Taya zanyi murmushi a rayuwata, tunda abin nan ya faru har yau basusan nine sanadi ba, sai dai kowa tausayamun yake akan rashin dan uwa nane yasa ni canzawa haka? Na lalata farincikin kowa na lalata.......:" Kansa ya kifa akan sityarin mota yanajin wani abu na ratsashi. Ya dade a haka kafin yace " ki shiga gun mahaifiyarki, bancancanci samunki ba, bancancanci samun farinciki ba." Shiru tai tana kallansa sai hawaye dake zubo mata wanda kamar korosu akeyi, hannu tasa ta bude kofar motar ta fita. Idanunsa ya runtse da karfi yasan za'ai hakab sai dai zuciyarshi ce ta sake zafi dayaji ta fita, hakan shine daidai shikuma yanzu rayuwarsa sai tafi tada dan ta riga ta shiga rayuwarsa wanda yanzu ya tabbatar cireta babbar gibe ne a gareshi. Jiyai ta sake bude motar, dagowa yai ya hade rai sannan ya kalleta. Yanzu kam gaban mota ta bude gefensa ta bude, kallanta yai sai dai baice komai ba, Jalila ta shiga ta zauna sannan ta rufe motar, kallansa itama tai sannan tace " Inyi magana?" Kallansa yai kallan mamaki, tace "ka fadi duk abinda ke ranka ni baka barni na fadi nawa ba." Yace "kamar ya kenan?" Shiru tai kafin tace " yaya kana tunanin dan Uwanka abinda yakeso kenan?" Kallan tambaya ya mata, tace "yanzu in yasan saboda shi ka maida rayuwarka haka kana tunani zaiyi alfahari da hakan?" Idanu ya kura mata, tace "yaya kana yaro lokacin sannan ba da saninka bane......." Da sauri ya juya kai ya bude kofa yana neman fita, da sauri tasa hannu ta riko hannunsa. Juyowa yai ya kalleta tace "inhar kanasan in tafi zan tafi, sai dai inhar akan dalilan nan ne hujjajun basu karbu ba." Kallanta yakeyi, murmushi tamai tace "wace irinn rayuwa kai zuciyarka na dauke da abubuwan nan?....." Batai auni ba ya jawo hannunta ta fada jikinsa, kankameta yai tsam, yanajin wani abu na ratsashi, duk da gabanta dake faduwa a hankali tace " meyasa kake tunanin su Ummy zasu ga laifinka akan abinda ya faru?" Idanunsa ya lumshe kawai, bayansa tadan shafa alamar lalashi tace "Yaya kaine abin tausayi ba su Husain ba, su kansu na tabbatar da zasusan abinda ka aikatawa kanka bazasuji dadi ba." A hankali ya dagota daga jikinsa kallanta yai, ita kanta kallansa takeyi, sai dai ganin kallan da yake mata yasa ta saukar da idanunta kasa, ya rike fuskarta da hannayensa yace "Jalila kinfi kowa sanin halina, inada dizgi? Shariya? Rashin san magana? Rashin iya magana? Rashin iya hulda da mutane?

Chapter 24 of 38