Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Dariya tai tana kallanshi tace “lalai yaya! Nikam bansan ya nakeyi ba.” Hade fuska yai tare da sakin ajiyar zuciya yace “ya zanyi? Da alama sai na jira.” Tace “sai ka jira me?” Kallanta yai tare da kara hade fuska yace “ ya na iya?” Shiru suka danyi har sukai tafiya mai dan nisa kafin yace “Jalila haryanzu bakiyi tunanin komai akan maganar Abba ba?” Yai maganar yana murza hannunta.” Ta kalleshi cikin kulawa tace “ko kara kawoshi a raina ma banyi ba, ai na fada ma duk yanda kace haka za’ayi.” Iska yadan furzar kadan yace “ina san mubar gida mu zauna mu biyu amma bana sha’awar barin kasata, sannan banasan tafiya nabar family na.” Shiru tadanyi kafin tace “ka duba kaga abinda ya dace, ni duk abinda ka yanke daidai ne a gurina.” Kallanta yadanyi kafin ya karkatar dakan mota kan layinsu, yace “ nagode Jalila, na tabattar akan dukan lamurana yanzu am not alone.” Murmushi tamai tare da saukar da idanta kasa. Cikin gidan suka shiga yai parking din motarsa tare da kashe ta, kallanta yai yace “muje ko?” Tace “hannuna...” Yace “au.” Sannan ya saketa, kallansa tai tace “na dauka yanzun ma cemin za’ai, kin tabbatar ba ke kike san na rikeki ba?” Tai maganar yanda yake magana, girman idanunsa yadan rage yace “haka nakeyi?” Tace “eh mana.” Yace “sakemin naga?” Tai gyaran murya kadan tace “kin tabbatar ba ke kike san........” Bakinta ya sumbata tai saurin zaro ido tare da kallansa, sannan ta waiwaiga wajen window, yace “ya akai? Kunya kike?” Tace “yaya? In wani ya ganmu fa?” Yace “hmm to menene a ciki? Mukai a wajen gidan goggo ma bare cikin gida?” Da sauri tasa hannu ta toshe ma baki tace “oh ni Habiba!” Kafadarsa ya daga alamar ko a jikinsa kafin ya nunamata bakinsa da hannu. Sakarmai baki tai ta turo bakinta tace “yaya dan Allah ka daina zancen wajen gidan Goggon nan tun kafin mu fada a inda za’aji.” Yace “ahh ta ya za’ace indaina zancen rana datake special a gurina?” Idanu ta kuramai kamar zatai kuka yace “kinaso na daina?” Da sauri ta daga kai alamar eh. Yace “tam sai kin min abu goma wanda nace inaso.” Tace “abu goma?” Yace “eh! A duk lokacin danacemiki inasan abu sannan na hade hannayena haka to dole kimin, kin yarda.” Dariya tai kafin tace “lalai yaya tun daga yarintarka kakesan fanshewa, wannan fa abin yara ne.” Yace “sosai, ai dama na fada miki ki shirya, kuka kika ce kin shirya.” Tace “to naji.” Bude mota yai ya fito yana Murmushi, itama ta bude ta fito tana murmushi. Ba kowa a falo da alama kowa yana daki, sama kawai ya wuce ita kuma tai dakin Ameera. Kanta tasa a jikin kofar tace “Ameera!” Ameera ta taso ta bude da sauri tace “matar yaya an dawo daga hotel din?” Tace “hotel? Nan mukace zamu dama?” Ta dan daga mata gira tace “ai na gano.” Jalila ta daka mata duka tace “wallahi ke yar duniya ce, uban hotel mukaje ba hotel ba.” Ameera tasa dariya tace “wasa nake miki wallahi, kawai so nake naga na tsokaneki.” Jalila ta harareta tace “su Ummy fa?” Tace “sun tafi daki, ya Sageer ma haka, abincin ku na kitchen.” Jalila tace “ai mun koshi amma bansan ko Yaya zai kara ba.” Ta juya tace “sai da safe.” Ta hau sama. Hassan ya cire riga kenan tana turo kofa, kallansa tai da sauri ta nemi fita daga dakin. Da sauri yace “Amarya ina zaki?” Ta juyo tace “ na manta akwai abincin mu ne a kasa.” Takowa yai inda take kawai ya maida kofar ya rufe sannan yasa hannu ya rikota. Tace “Yaya....Abinci....” Yace “ai kinsan a koshe muke ko?” Tace “hmm na dauka...” Saketa yai sannan ya koma ya dauko yar shara sharar shirt ya saka sannan yasa wando three quarter bata taba ganin ya kwanta a haka ba dan da doguwar riga jalabiya yake kwanciya. Kallansa tai kallan mamaki, yace “ya akai? Kyau na miki?” Tace “nagane...” sai kuma tai shiru, yace “da can ma dan karki takura ne yasa nakesa jalabiya amma dama haka nake kwanciya ta.” Jalila tace “yanzu fa?” Takowa yai kusa da ita, tadan yi baya kadan yace “yanzu na san mun zama daya ba maganar takura.” Kallansa tai kawai tai yake sannan ta zauna akan kujera. Yace “ ina kinyi sallah a gidan Goggo?” Tace “eh!” Yace “to ki taho mu kwanta dan bacci nake ji.” Tace “ zan danyi tilawa ne tukunna.” Yace “okay to ki shirya ki matso sai muyi tare, ta kalleshi kafin tace “to.” Yaka ta shige cikin mayafi ta canza kaya cikin dabara sannan ta shiga toilet, pant dinta ta wanke ta shanya sannan tasa wanda ta shigo dashi daga falo. Bazata manta ba a makaranta Zahra take bata labari haka taga yayarta nayi in tazo gida ko a gidanta. (Mata ba wai sai kince ke bazaki iya wanka ba in dare yayi ba, ko kice inkinyi wanka ma miji zai saki ki sake wani, ko baki yi wanka ba at least change ur pant, wannan abu nada mahimmanci, Please karki sa pant tun safe har washegari yanada babbar illa.) Jalila na fitowa ta dauko qur’ani sannan ta matso kusa da gadon ta hau, sai data biyamai yamata gyara inda ya dace sannan ta rufe qur’anin ta ajiye. Jawota yai jikinsa suka kwanta, luff tai a jikinsa tanajin duminsa, a hankali taji yace “zan daure.” Dagowa tai ta kalleshi tace “da me kenan?” Kwanciyarsa ya gyara yace “ba komai.” Yanda yai maganar yasa ta murmusa. Yace “dariya kikai?” Dagowa tai ta kalleshi tace “ni? Yaushe kenan?” Da sauri ta maida kanta jikinsa tare da jan bargo. Shima rufa bargon yai har kansu yana cewa “inji da kunene acemin ba’ai ba?” Dariya tasa tace “da gaske fa Yaya ba abinda nai......” (Jinai suna dariya nace hmm bari nai nan kafin Hassan ya fara tunanin wani abu har ya makoni......) ************** Mumy sam ta kasa bacci daga ya dauketa take farkawa, balle dataga Inna taki farkawa, abinda likita tace mata take tunowa. “Fatima sai dai addu’a, da yardar Allah mun samu numfashinta ya dawo sai dai bamuda ikon sawa ta bude idanunta, sai dai mu dage da addu’a sannan a kula da ita sosai, kar a dinga hayaniya a inda take, da alama wani abu mai tsananin mamaki ya faru da ita ne har yasa ta shiga shock haka.” Mumy ta kalli Dr hankali a tashe tace “ba wani abu da ya faru da ita.” Dr tace “ bazai yiwu ba, dan alama ce ta taji wani abu wanda ya girgizata har ya santa cikin wannan halin, karfa ki manta bawai faduwa tai ba ko kuma dama batada lafiya ne.” Mumy tai shiru tana kallan Inna, a hankali ta goge hawayenta. Jitai an dafata ta baya, juyowa tai ta kalleshi hawaye suka zubo mata. Dady ya tsugunna tare da rungumota jikinsa, yana shafa bayanta alamar lalashi. Itakam kuka kawai takeyi. Washe gari suna zaune a asibiti wajen karfr hudu na yamma, Sultan ne ya fara shigowa. Ajiye basket din da suka kawo kato dauke da kuloli kala kala yai sannan yace “Mumy!” Kallansa tai tace “Sultan Yasmeen fa?” Yace “tana tare da Dady.” Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar. Safeena ce ta shigo da gudu ta karaso ta rungumeta kam, atare suka sa kuka, tare da kankame juna. Mumy ta dagota tace “Safeena? Jiya fa mukai waya.” Tace “Mumy dama na riga ma na sai ticket lokaci, da bakice na taho ba da wani gun zanyi.” Mumy tasa hannu akan fuskarta tace “ya naga kin rame?” Safeena ta share kwallarta tace “Mumy ya jikin Inna?” Tace “gatanan sai addu’a Safeena na ma rasa ya zanyi.” Sultan dake tsaye ya juya kansa saboda hawayenn da suka zubomai...... ************** Ihun da ake yi ana bin motar da gudu ne yasa na ruga da gudu nima dan ganin meke faruwa, kauye ne sosai dan haryanzu mota ba shiga take kauyen ba sai da dalili, dan basuda mutane masu mota. Goggo ta kurama kauyen ido itakam bataga wani canji ba da aka samu, yana nan kamar yanda ta barshi, duk tsawon shekarun nan kuwa. Tuno rayuwar datai a kauyen mara galihu ne yasa ta yin shiru tana bin yaran dake bin motar da kallo. Ita da kanta ta dinga nuna layin, har suka je. Katon gida ne na gaske amma fa ba katon da kuke zato ba, kato na yawa nake nufi. Duk wanda zaiyi aure a cikin gidan yake zama. Mata gasunan kacha kacha, yara kusa kamar kaje wani taron. Ganin mota ta tsaya a kofar gidan wasu da ke cikin masu bin motar wadanda suka kasance a gidan suke suka kwalkwala da gudu gidan dan sanar musu. Kankace me sai ga mata manya ana leka katanga dan ganin abinda ke faruwa, yara maza kuwa har sun gangara gona da gudu wasu sunyi majalisa dan kiran iyayensu maza dan suzo suga abinda ke faruwa a garin nasu. Abba mota ya bada makekiya mai masifar kyau motar da ko a birni inkaga mutum da ita to fa lalai ya isa ne, shikansa Abba ba hawanta yakeyi sosai sai inza’ai abu mahimmi yake hawanta. Goggo ta kalli matan dake ta lekowa ta katanga duk bata sansu ha sai guda biyu wandanda suka kasance matan yayanta maza ne. Mamman ya juyo yace “nan ne ko?” Tace “eh nan ne, sannu da kokari mungode fa.” Yace “karki damu Hajiya, ki shiga kiyi abinda zakiyi a nutse inyaso da yamma sai mu koma.” Tace “har yamma? Kai kuma fa?” Yace “karki damu dani, zan gangara garin misau na samu abinci naci na jira ku, in kun gama sai ki kirani.” Tace “to, ta mikamai wayar tace “ samana lambarka ko?” Ya amsa ya saka, yai saving sannan ya nuna mata taba Lanta tace Lantana ki kalla yanda ko na kasa ganewa zaki nunamin, tace “to.” Ta amsa ta gani sannan ta bata. ************* Baki a sake ya tsaya yana kallan titi, me ya gani yanzu? Anya kuwa ba gizo idanunsa suke masa ba? Yanzun nan Yasmeen ke damunsa akan ice cream sun fito shiyana tunanin yanda zaiyi ya kwaci matsayin da yakeso a company dinsu, ya tsaya a gun bada hannu kawai yaga daga gefensa wata katuwar mota. Kallan motar yai saboda kyan datamai, daidai lokacin da aka dan zuge glass din baya kadan, hakan kuma yayi daidai da bada hannun da akai, sai dai ana zuge glass din nan ya hango wata mace kai kama da Goggo, bai kara kare mata kallo ba motar tai gaba. Kansa ya girgiza da sauri tare da cewa “lalai na fara haukacewa.” Yasmeen tasa kuka kallanta yai yace “menene kuma?” Ice cream dinta daya zube ta nunamai tana kuka tare da bua kafa, haushi ya kamashi yace “dan ya zube shine zaki dinga kuka haka?” Ganin yanda yake mata fada abinda bai taba yi ba yasa ta sa kuka sosai. Yanda yaga ana kallansa ne yasa yai saurin daukanta yana cewa “sry muje a siyo wani, shikenan?” Kwanciya tai a jikinsa tare da ajiyar zuciya. A ransa yace “yara duk an batasu da sakalci.” (Nace kuma🤔?) #OneLuv💕[12/30/2018, 9:50 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *67* Dady yana tuki yana tunani harya isa asibitin, Mumy na zaune akan kujera kusa da Safeena tanata tambayarta rayuwar datai, jefi jefi Mumy na share hawayenta dan tausayin yarta, tace "kiyi hakuri Safeena, ni a guna gata muka miki, sai dai daga baya na gane ba gata muka miki ba." Safeena tana kuka tace "yanzu Mumy ina Jalilan?" Mumy ta kalleta tare dayin ajiyar zuciya na takaici tace "Jalila tafi karfin mu, tafi karfinki, yanzu tana wani matsayin da muke neman alfarma da taimako a gurin ta." Safeena cikin mamaki tace "ban gane ba Mumy?" Shigowar Dady ne ya hana mumy bada amsa, Yasmeen ta rugo gun Safeena da gudu tare da fadawa jikinta, Safeena ta kankameta tana hawaye. Dady ta kalla sannan ta mike tazo kusa dashi ta rungume shi tana kuka. A hankali ya dagata sannan yace "Saukar yaushe?" Tace "dazu na iso shine akace su Mumy nanan muka taho da Sultan." Ya kalli Mumy sannan yace "ya mai jikin?" Kai kawai ta girgiza alamar ba labari. Ya kalli Safeena yace "ki huta zanje na dawo." Ya janyeta ya fita waje, yana fita ya tsaya a jikin katangar dakin yai shiru, ba dai yanzu opportunity bane ya bude mai bai sani ba? Kila Allah ne ya dubi zuciyarsa da yanda yai musu wahala ko shiyasa Allah ya kwantar da ita dan ya samu abinda yake so? Lalai yanzu kam ya gama sanin Allah ne yake sanshi da rahama. Da sauri ya dau waya ya kira babban board director na company dinsu. Yana dagawa yace "Abakar ne." Cikin mamaki yace "Abubakar kana lfy?" "Lfy kalau dama kira nai na fadama Hajiya ba lfy she is unconscious." Fuskarsa dauke da mamaki yace "Subhanallah garin ya ya?" Cikin muryar damuwa yace " wlh sai Allah, muna asibiti." Yace "ba kanta, gashi munada meeting jibi monday." Yace "bansan nima ya za'ai ba." "Tunda kaine sirikinta sannan next in line ai kawai sai kai kazo." Yace "ta inaxan zo, kamar bai kamata ba." "Bai kamata ba kamar ya? Dama Hajiya ai ta girma akan running din company yaci ace tun yaushe tayi resigning, sai mun ganka." Kafin Dady yai magana ya kashe. Dady yai dariya yace "ikon Allah! Cikin sauki haka?" Ya sake wata dariyar, hada ido suke da wata nurse sai ya wayance ya fito daga asibitin. ********** Goggo ta shiga cikin gida ta zauna, matar babban yayansu sai kallannta takeyi. Goggo ta kalleta tace "Yaya an wuni lafiya?" Cikin mamaki tace "Hajiya ai ban gane bane." Goggo tace "nice Laraban Meero (haka aka dinga kiranta lokacin tana yarinta)" Idanu ta zaro cikin mamaki tace "inalilahi wa ina ilaihi raji'un, kece?" Nan fa ta matso ragowar matan suka baza ido, dayar matar yayan nata ma ta taho da sauri. Maza da suka iso daga gona kowa ya shiga mamakin jin wacece. Goggo ta kallesu bayan sun gaisa tace "Innata fa?" Nan akai shiru kowa na kallan dan uwansa. Jikin Goggo a sanyaye tace "batada rai?" Babban yayansu yace "ta rasu shekara biyar da suka wuce, har ta mutu sunanki ne a bakinta." Goggo idanunta ya ciciko, tace "Baffa fa?" Sukace yana kwance ba lafiya yafi shekara yana fama da ciwon ko waje baya fita." Goggo ta kallesu nan aka shiga yi mata introducing din kowa, nan ta Nuna musu tsarabar data kawo, mamaki ne ya kamasu, ganin buhun shinkafa kwalin taliya biyu da macroni, katan din sabulun wanka guda biyar, katan din omo guda hudu, katan din sabulun wanki guda biyu, ga jarkar mangyada irin katan nan. Nan fa aka shiga godiya da ban hakuri akan abinda aka mata, haka akai ta bata labarin yanda mahaifiyarta tai rashinta. Goggo ta share kwallarta kafin ta shiga gun mahaifinta. Shikam harda kukansa wajen neman yafiya agunta, yayi dana sani kara kuka ma yai a lokacin data ajiye kudi dayawa a gabansa, sannan ta fito tare da neman a rakata gidansu Abakar saboda mahaifinsa. Sa albarka agun Baffa har ta bar dakin, mahaifin Abakar yasha kuka daya ganta, yai ta neman yafiya shima a gunsu, ta ajiye mai kudin data kawo da katan din omo da sabulun wanka tai sallama ta fito. Bata wani zaga gari ba saboda kafarta, sai dai dakansu mutane sukaita zuwa da wanda ya santa da wanda baisanta ba, kowa yanajin tazo kawai sai dai kaga yazo. Haka tai ta rabasu an kudi har ta samo ta baro garin.... Zuciyarta cike da tausayi da alfahari da yanda rayuwa ta juya musu.... *********** Yanda taga yana bacci hankali a kwance yasa ta zuba mai ido tana kallo, ko da wasa bata taba kawo rayuwarta nan gurin ba. Idanunta na kansa sam batasan murmushi takeyi ba, jitai ance "zan iya bude ido?" Mamaki ne ya kamata da sauri ta dauke ido daga kansa tare da neman dankwalinta. Ya bude idanunsa tare da sa hannunsa ta ratsinta ya sa kansa a kasan bayanta yace " angama kallan nawa?" Tace "wai ba bacci kake ba?" Tai maganar tana dan juyowa kadan saboda rukun daya mata har jikinta takeji. Fuskarsa ya dago kamar me sanyin bacci yace " kina tashi na tashi, kawai banasan farkawa ne." Murmushi tai tace "ga alama nan, idanka ya nuna." Matsowa yai yasa kansa akan cinyarta yana kallanta yace "idan kara kadan?" Yanda yai maganar ne yasata murmushi tace "a nan?" Kai ya daga tare da rufe ido yace "kinga sai ki kalleni da kyau ba takura." Tace "ni fa ba kallanka nai........" Fuskarta ya nuna da yatsarsa ba tare da ya bude ido ba, tace "kasa fa?" Bai bude ido ba yace "yau Saturday kowa na gida, Ameera ma nanan." Tace "to........" Juyowa yai yasa kansa a cikinta wanda ya hanata magana, jitai har numfashinta sai daya amsa. Ta kalleshi idanunsa sun firfito a hankali tai murmushi. Hannuntantasa a cikin kansa tana mamakin rayuwa yanda ta juya musu daga ita har shi. Kamar yasan me take tunani, dan ita ta daukama ya fara bacci sai taji yace " Jalila!" A hankali tace "Naam!" Yace "mu bar kasar nan." Fuskarta dauke da mamaki tace "mubar kasar nan?" Juyowa yai saitinta yace "Uhmm, I really want to see us alone." Tace "nan ma ai mu kadai ne." Sai kuma can tace "kana nufin ka yanke hukunci?" Idanu ya lumshe mata alamar eh sannan yace "yanzun nan!" Tace "yanzu ka yanke?" Yace "Umm haka kawai naga barin mu nan shikadai ne zaisa mu kebe, kinga kafin mu dawo sai na fadawa Abba a nemo mana gida." Dariya ya bata, pillow din data daura hannunta akai shita dauka ta sa a saman fuskarsa tana dariya tace " gaskiya yaya ba kunya a harkarka, saboda haka kawai kake san tafiya?" Pillow din ya turo yasa hannunsa a saman wuyanta ya jawota daf dashi yace "bakya tausayina Jalila?" Tace "Tausayin me kuma?" Ya kara marairaice fuska yace "bakya tausayawa zuciyar dake san ganinsa manne da matarsa?" Tana dariya tace "mene?" Yace "nikam tafiya zamuyi, Allah yasa kafin mu dawo Sageer yayi aure ya tare saman." Jalila tana dariya tace "wato shi ya zauna kai ka gudu ko?" Yace "a'a shima yadan dana kadan sai mu gudu dukanmu." Jalila ta girgiza kai tana dariya tace "ni dai gaskiya so nake na sauka kasa Allah kunya nakeji aga ban sauko ba." Ya daga ta tare da hade fuska ya koma ya kwanta akan pillow. Hannu tasa ta taboshi tace "fishi kai?" Ya kalleta yace "abani cin hanci na fita ko kuma inje in nemi izinin zama da matata." Jalila tai dariya tace "kace me?" Yace "mu gwada mu gani?" Da sauri ta sumbaci kuncinsa tace "inje?" Kai ya daga mata yana murmushi. Ta kalleshi sannan ta fita. Tana rufe kofa ta kalli dakin sannan ta murmusa tace "Yayah!" Sannan ta sauka. Kunya ta kamata dataga Ameera da Ummy sun gama aikin breakfast harsuna jerawa akan dinning cikin kunya ta karasa tace "Ummy ina kwana?" Ummy tace "Jalila kin fito? Ai da kinyi zamanki ma Ameera anjima zata kaimuku abincinku." Jalila da sauri ta amshi kayan hannun Ummy tace "a'a Ummy." Ameera ta guntse dariyarta. Jalila ta shiga maka mata harara...... Bata dade da fita ba ya mike daga kan gadon ya gyara sannan ya dau wayarsa ya sauko. Tana kokarin hawa sama ta kirashi sai gashi. Ummy ya gaida tana amsawa Abba ya fito daga daki ya gaisheshi. Sageer ma ya matso suka gaisa yana cewa "jiya nikam bansan sanda ka dawo ba." Hassan ya harareshi sannan yace "Ummy nikam a sama zanyi breakfast." Da sauri Jalila ta kalleshi. Ya dauke idanunsa yana kallan Abba wanda ke cewa "gaskiya ne, a basu abincinsu in yaso juma'a sa dinga saukowa." Ummy tace "kuma hakan yafi ko saboda ma Jalila bazata sake anan ba." Hassan ya kalli Jalila yaga yanda tai tsuru tana kallansa. Dariya ya kamashi ya guntse ya kalli Sageer yace "Malam gauro aci abinci lafiya." Sageer yai dariya yace "gauron ma ya kusa yin zuciya ya kama nasa." Hassan yai sama yana dariya. Ameera ta kalli Jalila tace "Aunty Jalila ga naku nan dama Allah yaso Ummy ta ware muku." Ta matso kusa da Kunnenta tace "oh su yaya ba kunya." Jalila tasa kafa ta taka ta. #OneLuv💕 [12/30/2018, 10:06 PM] El-hajj: 🗯 *JALILAH* 🗯 Written By : *AYUSHER MUHD* Wattpad: *Ayusher Muhd* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* *68* Tana ajiye tiren abincin ya sa hannu ya jawota ta fada jikinsa, kallansa tai tace "Yaya?" Yace "me? Bakiso na fadi haka ba?" Tace "taya zakace haka bayan kasan yanda su Ummy kijin dadin cin abinci dakai?" Ajiyar zuciya yai mai sauti yace " nikaina ba haka naso ba, to amma ya zanyi? Na kasa jurewa." Tace "ka kasa jure me?" Jawota yai ya kara rungumeta yace "nafisan na jimu shiru." Dagowa tai ta kalleshi tace "yaya? Nikuma tsoro nake ai." Yace "tsoron me?" Tace "naji ance duk ma'aurata farkon aure ne kawai miji ke nuna musu so, amma da zarar sun shekara daya, biyu zuwa uku zai canza mata, wani maganar mutunci ma ba samu zatai ba." Yanda yake jinjina kai yana tabe baki ne yasa tace " Da gaske haka ake cewa." Ya karkata kai yace "ohhh haka ne kenan?" Tace "mene?" Yace "ban taba ji ba amma yanzu da kika fada da alama na fahimta." Kallansa tai a tsorace tace "me ka fahimta?" Dagata yai daga jikinsa ya zauna gaban abincin da ta kawo, ya nuna mata tare da cewa "matso muci abinci, yunwa nake ji." Kallansa tai jikinta duk yai sanyi, a hankali ta matso ta zauna tace "Yaya bakace komai ba." Yace "me kikeso nace?" Tace "Hmm abinda ke ranka." Yace "bakomai a raina." Kallansa tai tace "bakomai?" Yace "sosai, saboda labarin rayuwar wasu can daban kika bani wanda banida hadi dasu." Tace "yaya Goggo....." Yace "Jalila?" Yanda ya kirata ne yasa tace "naam." Yace "ya sunana?" Tace "Ya..." Yace "ba wannan ba ya sunana?" Tace "Hassan?" Yace "gud, mahaifinki fa?" "Abubakar." Yace "toh, banaso a rayuwata dake ki dinga hadashi da rayuwar wasu da kikaji ko kika gani, koda kuwa rayuwar mahaifinki ce, ni nine, sannan ke kice, bansan mace ba, ban taba magana mai tsayi da wata mace ba bayan mahaifiyata, ko Ameera kina ganin yanda muke magana, ke kadai na sani, so Please inaso ki daukeni a yanda na daukeki, nasan haryanzu baki saki jiki dani ba wanda nasan a hankali ni zan canza wannan, amma banaso ki dinga sako rayuwar wasu a cikin tamu. Bazan miki alkawarin rashin canzawa ba ko wani abu makamancin haka, i am a human being wanda baisan ke zai faru dashi anjima ba bare gobe, amma i will try my best to love and protect you." Kallansa kawai takeyi batasan kwalla ta tarun mata a ido ba, sai jitai ta gangaro mata, kai ta jinjina tana sharewa tace "nagode yaya, insha Allah bazan sake ba, sannan nima zanyi kokarin cire duk wata kunya dake damuna, sannan nima i will try my best to love and protect you." Murmushi yai sannan ya miko mata hannu, itama mikomai nata hannun tai ya jawota kusa dashi, yasa kansa akan kafadarta yace "Baby yunwa, yunwa nakeji." Murmushi tai cikin kunya tace "yanzu zakaci abinci." Zuba musu tai a plate, chips ne da soyayyan kwan sai farfesun kaza. Fork ta mikamai, kai ya girgiza mata alamar a'a tace "kace yunwa kakeji?" Yace "sosai ma." Ya karasa yana rike ciki. Tace "to naga kaki amsa kuma?" Yace "hannuna ciwo." Tace "hannu? Garin ya ya?" Yanda tai maganar a rikice ta kara matsowa tana duba hannunsa ne yasashi yin wani lalausan murmushi. Ahhhhhhh abinda taji ya fada kenan, kallansa tai rike da hannunsa tace "Ahhhhh?" Ya daga kai yana kara bude baki, wato shine ya sa hakalinta ya tashi? Tace "ok, ta sa fork ta debo tace Ahhh Bude bakin yai tare da rufe ido, jin shiru ne yasa ya bude idansa ya kalleta. Gani yai tana

Chapter 31 of 38