Ga gashin kan san nan yayi wani irin askin gefe da gefe anyi lowcut, tsakiya ya tara gashi kamar kan zakara. Ita dai ta san ba buzu ta haifa ba amma idan ka ganshi banbace shi da buzu tabbas zai baka wahala. Gashin gaban ne ya wani nannade ya kwanta luf luf yana sheki. Wannan ne dalilin fadan su a daren jiya. Tayi tayi ya fadacmata me yake shafawa haka, har tana ce masa idan ma relaxer ya fara sawa to Allah ya tsinewa mai kamanceceniya da mata. Sannan ta ce idan zai zo taron convocation din to ya tabbatar ya aske kansa askin mutunci.
To gashi dai yazo babu askin da alama kuwa har ya fita nuna farinciki ma yadda yake ta shewa da abokai.
Bayan shi kuma sai autar ta Sauda. Ita yanzu suke shirin gama secondary tare da Mardiyan Nasima, don tare aka saka su makaranta.
Sanda aka saka Sauda, duk da Mardiya bata kai shekarun shiga ba haka Nasima ta nace sai an sakata tsabar masifar kishi dake azalzalarta. Matsalar Sauda shi ne raina duka matan Abbansu. Bata ragawa kowa indai zai shiga gonar Maminta. Amma Allah Ya hada jininta da Mardiya. Nasima tayi kokarin ranasu har ta gaji. Sannan sabanin yayarta Farha da ta rasa manema, ita kuma har sun mata yawa. Shi yasa Allah Allah take ma ta gama makaranta ayi mata aure kafin masifar Tahir ya rabe ta. Tunda manema ne da ita ta ko ina babu babba babu yaro kowa Sauda. Ita da ta haifo su ma bata ga da me saudat din ta dara Yar uwarta ba to amma abu na ubangiji baka da ta cewa se Hamdala.
A gefensu kuwa Mardiya ce a tsaye tana murmushin yake. So take ta karaso wurin Mami amma tana jin nauyi. Sauda ta figo hannun kanwarta suka taho tare ta rungume su daya bayan daya.
Mardiya ita ce babban misali na rayayye ya fita a cikin matacce. Iyayenta basu da halin yabo ko daya amma ita dabi'unta ababen burgewa ne. Tana son 'yan uwanta da mahaifi sannan a gefe tana yakin boye mummunan halin mamanta Nasima.
Su biyar Abba Tahir ya mallaka. Ya dauki son duniya ya dorawa 'ya'yansa. Hatta Suhaib da shi kadai ya san boyayyen halinsa yana son abin sa. Duk wani so da gata da barin kudi ba ta inda ya ragesu. Tunda ya yi kudi arziki ya habbaka.
Bayan gama daukar hotuna iyalin suka hadu a motoci biyu. Ta Alh. Tahir ce ta fara fita saboda takura da ya yi da kallon da Suhaib yake watsa masa. Dayar kuwa Lilu ne ya ja su zuwa gida...
Kaddarar shekarun da Alh. Tahir ya diba yana tafka ashararancinsa da 'ya'yan mutane a yau ne za ta rabi dukkan 'ya'yansa. Domin a wannan rana ne Munzali da Abbati suka shigo garin Kaduna akan hanyarsu ta zuwa Kano.
TAKWAS GOMA BA BIYU.
Tun kafin ta iso bangaren da 'yan kunshin suke zama wanda yake hanyar kofar fita Anti Hasiya ta san takun waye. Sautin kwas-kwas da takalminta mai mugun tsini yake yi har tsakar kan mutane ake ji. Dunduniyar duka takalman ta cire wurin tsinin sai qusa ke kartar fasassun tiles din da aka saka a wurin . Budurwa ce da take cikin ganiyar shekarun 'yan matancinta. Tana da kyaun kirar jiki da na fuska. Kayan jikinta sun matseta don siket din sai da ta dinga tsalle tana jan shi sama kafin ya shiga. Rigarta kuwa ko anyi rantsuwa babu kaffara kana gani ka san da kyar take sauke numfashi. Ga rabin kirji duk a waje haka ma bayanta. Kanta babu dankwali sai wani yalolon mayafi sa ta yane kan dashi. Ana ganin zara-zaran kalbar da tayi da zaren lilo a cewarta shi ba haram bane.
"A haka zaki fita?" Cewar Anti Hasiya ganin tana niyar fita kai tsaye.
Maimakon amsa Ayaah gatsina fuska tayi ta nufi kofar gidan gadan gadan za ta fita. Anti Hasiya tayi murmushin takaicin wannan hali nata. Wani salon fitsara da rani bata tunawa dasu sai taga tsakar gidansu cike da 'yan kunshi. A lokacin take yunkurin taka matar da take matsayin uwa a gareta don kawai ta zubar mata da mutumci. Bukatarta ta dade da biya domin dadaddun kwastamominta kusan kowa ya san tana da 'yar da take neman fin karfinta ba don a tsaye take ba.
Murja dake gefe tana tata sana'ar ta kitso ta saki kan matar gabanta ta taso a harzuke.
"Ba dake Anti take ba?"
Ayaah tayi mata kallon raini tana jujjuya idanu "ai fa tunda ki ka fara kama matsabbai bakinki ya bude. To haka zan fita uwata ko zaki hana ne?"
Wata mata ta kada baki ta ce "ke kuwa 'yan mata idan baki ga girman yayarki ba bai kamata kiyi haka a gaban mahaifiyarki ba."
Dukan kunnuwanta tayi a tare tana murguda baki hagu da dama tare da farfari da ido kamar sabon kamun aljanu.
"Mahaifiya? Tabdi. To ni mahaifiyata tana kasa Hajiya. Wannan matar..."
"HAJARA!"
Ba Ayaah ba kusan duka matan wurin harda Anti Hasiya kuwa sai da tsawar Honorable ta kada musu ciki.
"Baki da bakin amsawa ne?" Ya sake cewa a harzuke yana tsaye a kofar da ta raba ainihin tsakar gidan da barandar da ake zaman kunshin.
"Gani Baba" ta ce da sauri lokaci guda kwalla na zubo mata.
"Share wadannan munafukan hawayen kizo ki wuce mara kunyar banza."
"Baba gidan Anti Hasina (kanwar A'i kuma yaya ga Hasiya) zani."
"Kin wuce ko kuwa?"
Bata jira ya kuma magana ba ta bi ta gefensa ta shige ciki tana kuka. Dan dukar da kai ya yi ya bawa matan hakuri.
"Ai shekarun nan sai an kai zuciya nesa. Allah Ya shirya mana zuri'a." Matar dazu ta furta da dan murmushinta.
Ciki ya koma zuciyarsa tana tukukin bacin rai. Tsakaninsa da Hasiya yafi kowa sanin cewa ba soyayya bace. Ya sakawa zuciyarsa Allah ne Ya kawota cikin rayuwarsu domin ta zame masa bangon jingina. Idan ya tuna yadda har A'i ta rasu bai taba taka kafarsa gidansu ya gaishe da Innayo ba kunya kan rufe shi. Shi yasa baya ganin laifinta da taki goyon bayan auren nasu har yanzu. A yayinda mutane da yawa marasa tawakkali zasu alakanta aurensa da Hasiya a matsayin silar karayar arzikinsa shi alkhairi ya hango. Ya sani sarai cewa ko uwar 'ya'yansa da wuya ta zauna tsahon shekarun nan tana dawainiya dashi. Ba yadda zaiyi ya raba 'ya'yansa da kakarsu Laraba da kannen mahaifiyarsu amma yana bakincikin alakarsu. Yaji dadi da sauran basa daukar zuga amma Ayaah zugar ce ta tadda hali. Da fada yana fitowa mutum kila ba za ta ganu ba yanzu. A kanta ya fara dukan 'ya'yansa amma kullum dada kangarewa take yi. Shekararta goma sha shida da watanni, yanzu take ajin karshe a sakandire.
Bayan sun shige ciki sai da Anti Hasiya ta dauki mintuna kafin ta ita cigaba da zanawa matar gabanta lalle. Lokuta marasa adadi ta kan ji kamar ta yiwa Ayaah dukan tsiya amma sai ta daure. Maraicinta take dubawa da kuma sanin cewa duk ranar da ta kai mata hannu akwai yiwuwar ta karairayata. Bata iya fushi ba sam. Sai ta dade tana tara mutum kafin ta dauki mataki. Abu na biyu kuwa bai wuce fargabar da take fama da ita akan kalaman Innayo ba. Tana yawan fada mata cewa yadda su A'i suka watsa mata kasa a ido ta tabbatar da wuya idan ba haka su Ummi zasu yi ba. Gashi ita bata haihu ba ma balle tasa rai da samun mai jinkanta a gaba.
'Ba duka aka taru aka zama daya ba. Dan da zai ji kan mutum ba lallai ya fito daga cikinsa ba.' Haka take yawan fadawa zuciyarta.
Daga karfe uku ta rufe karbar 'yan kunshin ranar. Sai bayan la'asar ta gama ta shiga ciki tayi wanka. Ummi tayi abinci ta ci sannan taje ta duba Abbas. Yana yawonsa ko ina sai dai kwakwalwar ce ta dan tabu. Maganarsa ta hankali bata tsayi yake komawa shirme. Kwanakin nan yana yawan tashi da ciwon kai irin wanda yake yi tun bayan hatsarinsu. Ganin har lokacin yana kwance ta koma dakin Honorable.
Kudin da take tarawa ta dauko. Dubu hamsin ne da 'yan kai suka rage bayan sun sayi kayan abinci sannan ta biyawa Ayaah kudin NECO da WAEC. Dubu shabiyar ta cire zata kaiwa Innayo washe-gari. Wata shabiyar din ta bawa Honorable a kai Abbas asibiti. Ashirin din kuma zata rike goma sai goman kai ta siyo kayan lalle. Dama haka take yi duk karshen wata ta raba musu ribarta.
"Hasiya ki bar kudinki. Na yiwa wani abokina dan majalisa magana zai bamu tallafi akai Abbas asibiti a duba shi sosai."
Kin karbar kudin da ya miko tayi, "ka fara kaishi ko magani su bashi na saukin ciwo kafin tallafin yazo."
Da kyar ta samu ya karba a daidai lokacin da suke jin ihun Abbas din cikin azabar ciwo. Da gudu-gudu Honorable ya fita ya samo mai adaidaita sahu suka kaishi asibiti. Sai karfe tara na dare aka sallamosu.
Kafin su dawo saurayin Ayaah ya kawo mata ziyara. Tunda babu idon babba a gidan tayi shiga irin wadda take so ta fita ba tare da sauraron gargadin Ummi da Murja ba.
"Wowwww baby so ki ke ki kasheni ne da wannan kwalliyar? Kin san ina matukar son kwalliya. Ganinki haka ya cire min duk wani bacin rai da na taho dashi." Ya ce tana isowa jikin motarsa.
Kanta taji yayi gingirin ya kara girma saboda tsabar dadin da taji da yabawarsa. Hankalinta kwance ta gillo masa karya da suka soma hira saboda yadda da soyayyarsa da tayi.
"Babanmu ya ce ka fito."
Sarai ya fahimceta sai ya bagarar ya gyara tsayuwarsa.
"In shigo dai ko Baby?"
Kallonsa tayi da rashin fahimta ta ce "ka shiga ina?"
"Oh, ba kina nufin na shiga ciki mu gaisa bane?"
Da saurinta ta gyara masa "nufina ya ce ka turo ayi magana saboda asa rana."
Rabeel sai ya mike tsaye da kyau yadda za ta ga tsayinsa ya daure fuska yana jera mata tambayoyi "amma ba dai ce masa kika yi mun tsayar da maganar aure ba ko? Yaushe muka hadu? Ke da kike karatu me zaki yi da aure?"
Tsoron kar shi ma ya kufce kamar sauran yasa ta kwantar da murya tana bashi hakuri
"Dama ba wai auren za a daura yanzu ba. Kawai dai don ya san da kai ne kafin na gama makaranta."
Kofar motarsa ya kama zai shige yana sababin da ya kwana biyu yana neman damar yi. Ya gaji da gafara sa bai ga kaho ba. Ta kware wurin kwadaita masa jikinta da irin shigarta amma taki bari ya dara daga rike mata hannu. Ya zata a waye take yazo kwasar ganima ashe kidahuma ce. Ga damar sulalewa ya gudu ya samu ba bata lokaci kuwa ya cafketa.
"Yadda bana son a katsewa kannena mata karatu kema ba zan katse miki ba. Na zata Baba zai yarda kiyi zurfin ilimin da zamu yi alfahari dashi ni dake da 'ya'yanmu amma na fahimci ba haka ba. Tunda da wuri yake son aurar dake gaskiya ki nemi wani."
Hankalin Ayaah in yayi dubu to duka ya mike tsaye. Bata da burin da ya wuce tayi aure ta bar gidansu. Gwaggo Laraba dama ta fada mata Anti Hasiya ce ta hana Murja da Ummi aure sannan sun kasa shiga jami'a. Daga mai dinki Ummi sai Murja dake kitso. Ga babansu ta hana arziki ya zauna masa domin ta juya shi. Shi yasa ita ta dage da karatu sosai don ta sha alwashin shiga jami'a. Abin kaddara duk kokarinta bata ci kwalifayin (qualifying) ba shi yasa Anti Hasiyan ta biya mata kudin NECO da WAEC. Ta fara murna wannan saurayin sun yi wata biyu shi ma yana shirin subucewa.
Murmushi ta kirkiro na dole ta ce "Lahhh, wasa fa nake maka. Baba so yake na zama likita ma."
Ai kuwa ya hade girar sama da kasa
"Ayaah ni kam ba zan iya hada inuwa da makaryaci ba. Kamar baki san haramcin karya ba ki kalleni ki yiwa mahaifinki karya da sunan wasa?"
Hawaye ta soma tana bashi hakuri ya shige motarsa yaja. A ransa yana cewa ta fiye bakin naci. Tun satin farko da yazo ya fahimci ita aure kawai take so.
"A nemi wani wahalallen ba ni ba" ya ce yana dukan sitiyari.
Kamar kiftawa da bude ido Ayaah ta neme shi ta rasa. Kuka sosai ta fashe dashi tana mai gasgakata Gwaggo Laraba. Lallai bokan Anti Hasiya ya iya aiki. Yanzu yanzu ta fito yana dariya amma ko rabin awa basu yi ba ya tafi.
Rabeel bai zame ko ina ba sai gidansu abokinsa Danliti wanda ya bashi aron mota. Waya yayi masa ya fito karbar makulli.
"Amma Rabilu yau kayi sauri ko baka sameta ba?"
Dariya ya yi sannan ya kwashe yadda suka yi da Ayaah ya fada masa.
"Kuma sai ka barta?" Cewar Danliti da mugun mamaki.
"To zama kake so nayi a sani auren da ban shirya ba?"
"Kai dai gaula ne. Irinsu ai da sa musu rai da aure ake moresu. Yarinya danya shakaf kamar wannan ka tsallake ka barwa wani?"
Maganar ta shigi Rabeel ya cije yatsa yana maganar 'yan tasha yadda ya saba "ban yi tunani ba Yasin. To yanzu meye shawara?"
Danliti ya lashe lebensa na kasa "sa'arka ta kare saura tawa. Can zani na gwangwaje son rai..."
"Wannan yarinyar kamar kifi ba bari zata yi ka mori komai ba."
Danliti ya shige motar da ya gyara zai mayar gareji kafin ubangidansa ya fahimci bata kwana a can ba "muje ka rakani na mayar da motar nan na baka satar ansa domin gaba."
***
Jirgin Abuja su Munzali suka shiga. A can suka dauko motarsu wadda suka ajiye a gidan shakatawar daya daga cikin mutanen da suka ziyarta a Lagos. Babu bata lokaci suka kamo hanyar Kano saboda shirin bikin nadin sarautar Abbati sati mai zuwa.
"Wai kuwa ya maganar mai yiwa Qibdiyya alkyabba ne? Ka tabo shi mana muji idan ya gama mu tsaya a Zariyan" Abbati ya tambayi Munzali suna daf da shiga Kaduna.
Da sauri Munzali ya dauki waya ya kira mutumin da ya bawa aikin dinkunansu shi da Abbati da 'yarsu. Telan kwarrare a dinkuna irin na kayan sarauta. Kwatanta musu wata plaza ya yi mai suna Diamond plaza.
"Kwananmu hudu da kama shago a nan mun baro Zariya. Ban fada maka bane Alh. Munzali saboda idan na gama da kaina zan kawo muku Kanon."
"Ka gama na Qibdiyya? Babanta ya dameni wallahi." Munzali ya ce yana dariyar hararar da Abbati ke jefa masa.
"An hada komai saura takalman."
"Zamu biyo"
***
Sau biyar Mardiyya tana kin daukar wayar Mamanta Nasima saboda tsoron me zata ce mata. A na shidan sai ta tura mata text wanda yasa da kanta ta kira a tsorace.
(Idan baki dauka ba zamu hadu ne a gida. Shashasha mara mutumci.)
Ringing din farko Mama Nasima ta dauki wayar ta fara surfa mata zagi.
"Saboda baki daukeni a bakin komai ba ki ka shirya ki ka bisu ko? Tun ranar da babanki ya fada ban ce babu inda zaki ba?"
Mardiyya sai ta wayance kamar bata ji me ta ce ba "Mama muna hanya"
Rai a bace ta ce "Au, baki ma ji me na ce ba kenan. To ki ce su saukeki a shago yanzun nan."
Mardiyya ta kashe wayar ta taba Sauda dake gefenta.
"Mama tana nemana a shago."
Sauda ta dan zura kanta gaban motar ta ce "Ya Lilu don Allah mu biya shagon Mama a ajiye Mardiyya."
Bai so ba sai dai kuma Mardiyya tafi karfin haka a wurinsa. Tana kaunar 'yan uwanta suma suna sonta ciki kiwa harda Suhaib.
"A ina yake?"
"Diamond plaza" Farha ta bashi amsa.
U-turn ya yi ya koma titin da suka baro domin sun bar hanyar plazar a can baya. Farha ce ta kira Mami Khadija ta sanar da ita inda zasu fara zuwa ta ce babu matsala. Ta ma jidadi domin abin da take son yiwa Alh. Tahir zai fi a bayan idon 'ya'yansa.
Suna shiga harabar plaza din Lilu ya hango wata jar mercedes benz ya daki sitiyari yana dariya.
"O.M.G! Wayyo Ya Suhaib mintsine ni na farka."
Suhaib ya girgiza kai yana dan murmushi "kana da matsala Lilu. Yanzu zaka yi sauri mu ajiyeta ne ko mota zaka tsaya kallo?"
Kallon rashin yarda da maganar da ta fito daga bakinsa Lilu ya yi masa.
"Mercedes benz E class, E dinma 350. Ya Suhaib dream car dina ce fa kake yi mata kallon raini."
Su Farha dake baya suka bushe da dariya don Lilu kamar zai yi kuka.
"Tunda dai iyakarka da ita bai wuce dream din ba ai shi kenan." Ya zura hannu ta taga ya dagawa motar da ta sha tint glass hannu "ke dream car Lilu na gaisheki."
"Ya Suhaib ka sace min gwiwa. Burina na mallakin motar nan kasa kafa ka dagargaza da wannan abin da kayi."
'Yan matan suka cigaba da dariya yayinda Lilu yake ta mita kamar ya ari baki. Kusa da motar yaje ya yi parking yana cewa sai ya shafata ko za ayi kararsa.
"Muje na raka ka Lilun Mami." Farha ta ce hannunta a jikin hannun kofa.
Mardiyya ta janyo hannun Sauda bayan ta fito daga motar.
"Zo ki rakani muma mu taba."
Kamar ba su Suhaib yake kira ba duka kannen nasa suka fice suna dariyar yadda jikin Lilu ke rawa yana zaro wayarsa. Jingina ya yi a jikin motar ya gyara kwalar rigarsa. Farha ya mikawa wayar ta karba tana murmushi.
"Allah Sarki 'yan matan KASU zasu shiga uku da hotunan karya."
Yana zura hannayensa a aljihu idanun Abbati dake zaune a mazaunin direba yana ta dariyar hirarrakinsu suka sauka akan Farha.
"Ya Ladif" ya sami kansa da furtawa a hankali yana shafar sumar kansa da take shan gyara.
'So ne? Wannan ce soyayya?'
Karon farko a rayuwarsa mace ta burge shi. Mace ta dauki hankalinsa. Ganin Farha ya yi tamkar tauraruwar da wata ba ya cika sai da kasantuwarta kusa dashi.
It was love at first sight...
TARA DAGA KE SAI GOMA.
I just published "10" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/ZvVtc6Nojab
UWA UWACE...10
Batul Mamman💖
Allah don isar da tafi kowacce isa
Allah don mulkin da bashi da wa'adi
Allah don rahamar da bata yankewa
Allah don girman zatinKa
Allah don kadaitar mulkinKa
Allah don buwayarKa
Ka karawa Annabi SAW daraja
Ya Rabbi mamallakin sammai da kassai Ka kare mana zuri'a daga dukkan sharri.
Ya Allah Ka karesu daga sharrin masharranta da sharrin kawunansu domin hakika kowane dan Adam akwai dabi'ar da aka halicce shi da ita mai kyau ko akasinta. Ya Allah kar Ka buga misalin Allah wadai damu ko 'ya'yanmu.
Ya Allah Ka azurta iyayenmu da mafi girman daraja da daukaka daga cikin AljannarKa. Allah Ka yafe musu, Ka jikansu, Ka kara musu lafiya, Ka kyautata halayensu, Ka inganta mu'amalarmu dasu da kuma sauran mutane. Amin
RABBIR HAMHUMA KAMA RABBAYANI SAGHIRA
***
Babu sautin da kunnuwan Abbati suke ji sama da bugun zuciyarsa. Sassanyan murmushi ya kufce masa a lokacin da ya dora hannun damansa akan kirji saitin zuciyarsa.
"Ya Farha kawo kema na dauke ki" muryar Lilu ta katse tunaninsa.
"Farha" ya gwada kiran sunan akan harshensa.
Daga wajen murmushi tayi wanda ya kara narkar da zuciyarsa ta ce
"Haka kawai ina tsaya masu motar su fito a tsareni in sha kunya."
Mardiyya da Sauda ya dauka har lokacin Munzali bai fito daga wajen tela ba. Farha ta gaji da surutunsa na rokon ta dauka ta jingina da motar bangaren direba.
"Irin abin nan zanyi kamar nice mai motar na zo shopping."
Hannun ta kama kamar za ta bude, Lilu ya saita ta zai dauka Abbati kuma ya cire lock. Tana dan daga handle din kofar ta bude. Daga ciki ya turota ai sai ta gigice su duka hudun suka kwasa a guje suka nufi shagon Mama Nasima. Suhaib na ganin haka ya fito daga mota da sauri. Wurin Abbati dake tsaye yana dariya ya karasa ya mika masa hannu.
"Don Allah kayi hakuri"
Abbati ya saki fuska sosai "ni zan baka hakuri saboda na tsorata maka kanne. Muje na tayaka kiransu" ya nuna hanyar matattakalar da suka hau.
"Kar ka damu na san inda suka je" Suhaib ya bashi amsa yana hawa benen. A ransa yake ayyana mutumin yana da saukin kai duk kuwa da cewa kana ganinsa tun daga sutura har fatar jiki ka san akwai kudi.
Shagon Nasima da take sayar da kayan kitchen suka shiga. Allah Yaso babu kwastoma ko daya a ciki sai 'yar budurwar dake tayata aiki. Mardiyya ce ta fara shiga ta hau ta da fadan da ta fara a waya.
"Tsinannen yawo da rashin kishin uwarki yasa ki ka bijerewa maganata ko? Wace uwar za a baki a wurin da yasa ki fita da sassafe kafin na tashi?"
Tuni idanun Mardiyya suka kada suka yi ja tana shirin yin kuka. Farha, Lilu da Sauda sai suka yi turus. Mama Nasiman kanta ta dan ji kunyar ganinsu amma sai ta fuske.
Fuska ba wani annuri ta ce "yau kune a nan? Ince dai lafiya."
"Lafiyar kenan. Kanwarmu wadda babu mai iko da ita sama da Alh. Tahir mahaifinta muka kawo" Lilu ya bata amsa shi ma fuska a hade.
"Rashin kunya zaka yi min? Khadija ma..."
"Wallahi kar ki soma. Da fa bamu san asalin balbela bane." Farha da bata da hayaniya ta ce a tsiwace. Ita da 'yan uwanta basa gani su kyale in dai abu ya shafi mahaifiyarsu.
Mardiyya kuka ta saka. Ita ma ta san labarin auren cin amanar da mahaifiyarta tayi da babansu. Ba dai su san da maganar suna neman juna ba amma sun san mai'aikin gidan ce. Haka zalika sun san Anti Jiddo 'yar uwarta ce. Sauda ma kukan take tayata. Ana haka Suhaib ya shigo. Mama Nasima ta nuna masa kannensa cikin bacin rai.
"Ka fita dasu kafin na kira Alhaji. Ba zan yarda ku zo har nan ku min rashin kunya ba."
Da ido kawai ya kallesu suka fice daya bayan daya.
"Kiyi hakuri"
Ya ce da ita bayan sauran sun fita. Maminsu ta gargade shi sosai akan yiwa matan babansa rashin kunya. Mota suka nufa ya karbe mukullin daga hannun Lilu. Bai ce dasu komai ba yaja suka tafi. Suna fita Abbati da Munzali suna shiga shagon Mama Nasima.
Yawun bakinta taji ya kafe ta nemi na hadiya ta rasa saboda ganin matasan masu kudi a gabanta. Komai da komai na suturar jikinsu da ido ke gani iri daya ne. A cikin 'yan dakiku ta gama lissafin tsadar kayansu ta gane sun tsallake raini nesa ba kusa ba. Harara ta gallawa Mardiyya wadda take jin zafin zuwanta a mace gashi bata sake haihuwa bayanta ba. Jikinta na rawa saboda rashin sanin daraja da kimar kai ta matsa gabansu.
"Alhaji me ku ke so? Ke Debora miko musu katalog (catalogue) dinnan su duba kaya."
Kamar wani zai rigata da sassarfa ta ce su biyota office dinta. Wani dan daki ne da aka sakaye daga gefe da kofar gilas. A nan take zama idan ta shigo shagon. Waige waige Abbati ya dinga yi yane neman su Farha. Munzali yana 'yar dariya ya tura shi gaba zuwa ofishin Mama Nasima tana fesa airfreshner.
"Tunda ka kawomu ko kofi ne sai ka saya." Ya rada masa a kunne.
Da suka shiga sun sameta tana goge kujerun zaman baki da dankwalin kanta. Murmushi take ta dokawa ta nuna musu su zauna.
"Mardiyya. Ke Mardiyya kawo musu abin sha. Alhaji me zaku sha? Idan babu sai Debora ta sauka ta siyo."
Sai da Mardiyya ta goge hawayenta ta taho zuciyarta tana zafi. Haka ta tashi ta fahimci mahaifiyarta tana bare-bare da zubar da mutumci gaban masu kudi. Idan ta sansano kudi a jikin mutum to babu ya shi a wurinta. Yaro sa'an Mardiyya ma sai ta duka masa. Neman kudi take kamar tayi sata. Tunda bata da magajin da zai tatso mata da yawa a jikin Alh. Tahir sai ta fake da kasuwanci tana kwasar kudi son rai. Duk da haka tana son kasuwancin domin yana hadata da manyan mutane.
Shigowar Mardiyya keda wuya idanun Abbati suka sauka a kanta. Murmushi ya yi sosai.
" 'Yan mata ashe nan ku ka gudu. Dama ku muka biyo. Ina 'yan uwan maki?"
A darare ta kalli Mama Nasima sai taga ta kyafta mata ido da sauri. Da dariya ta ce dasu "Ba dai Mardiyya ku ka biyo ba? Ikon Allah. Ai 'yata ce ta cikina. Waye surukin nawa a cikinku?"
Mardiyya ji tayi ina ma kasa za ta tsage a lokacin ta shige ciki. Daga ganin mutane ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Ita kuwa Mama Nasima ko amsa bata jira sun bayar ba ta dora da cewa "zo ki zauna bari na kawo lemon da kaina."
Da taga Mardiyyan ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 62