baya. Farha kuka kawai ta fashe dashi. Lilu ya tsayar da daya daga cikin motocin yana yi musu bayani cewa ba Abbati ne ya dauke yaron ba.
"Yaro ka kama bakinka ko kai ma a tafi da kai wallahi." Wanda ya bashi amsa ya kallo gate din ya ce da direbansu "ga Alhajin nan ya fito muje"
Su Mami suka juya a tare. Alh. Sadisu ne ya fito yana tafiya da sauri kamar zai tashi sama. Ga 'yan kazanginsa da securities da malaman makarantar suna biye dashi a baya.
Kwakkwaran kallo guda Mami tayi masa ta kara sauri tun kafin ya shige motar da aka riga aka bude masa.
"Alh. Sadisu?"
"Don Allah ku rabu dani" ya amsa a fusace don ya gaji da amsa mutane. Burinsa ya gan shi a station din da aka kai mutumin da ya kira shi a waya.
Da ta fahimci da wuya idan zai juyo balle ya kalleta ne ta kara da cewa "Alhaji Khadija ce, Maman Suhaib"
Ai kuwa da saurinsa ya leko kansa ta taga.
"Hajiya Khadija me kike yi a nan?" Ya yi wa direbansa alama da su tafi yana cewa da ita "Za dai mu yi magana daga baya, yanzu ina cikin tashin hankali ne wallahi"
Da sauri ta ce "na sani.Abdul aka dauke ko? Manemin 'yarka ne aka kama yanzu. Ba shi ne ya dauke shi ba"
Kallonta ya yi a tsanake sannan sautin Innalillahi da Farha take ta ambato cikin hawaye ya soma shiga kunnens.
"A mota kuke?"
"Eh"
"To ku biyo mu don Allah."
Suna shiga mota tasa Suhaib ya kira mata Munzali. Ita da kanta tayi masa magana ta kuma umarce shi da ya boyewa su Baaba Mari kafin a san me yake faruwa. Sai dai tuni hankulan iyayen ya tashi tunda ya amsa wayar ne a gabansu. Suna gama wayar suka nemi jin ba'asi. A dole ya sanar dasu. Haka suka tashi babu wanda ko ruwa ya shiga bakinsa tun zuwansu suka bishi.
A hanya ya kira Alh. Tahir. Yana can gidan Comared har lokacin bai tafi ba. Ya yi bakincikin rashin zuwa da direba gidan saboda har yanzu babu kuzarin tuka mota a tare dashi. Kansa ya rufe ruf ya rasa zaren kamawa tun tafiyar Abbati.
Da yaji kira kamar ba zai dauka ba yadda ya yiwa sauran kiran da suke ta shigo masa. Sunan mai kiran da ya gani ne ya sauya masa tunani. Abokinsa ne da suka hadu ta dalilin ayyukan kwangila. Duk zafin zuciya da kwarjinin da Alh. Sadisu yake yiwa mutane sai tasu tazo daya dashi. Har ta kai suna ziyartar juna a gida.
"Alhaji kaji labarin na shigo Kano ne?" Ya ce da kokarin kawo raha tsakaninsu.
"Kana ina Alh. Tahir? Don Allah duk inda kake ka taho police station din Gadon K'aya. Akwai matsala an sace Abdul kuma muna tare da iyalinka Haj. Khadija."
Satar Abdul din da yaji ta firgita shi. Sai dai ko kusa bata kai kidimar da ya shiga da yaji sunan Mami ba. Ya nemi jin cikakken bayani amma shi ma Alh. Sadisun bashi da abin cewa.
Mukullin motarsa da waya kadai ya dauko ko hula da babbar rigar da ya cire bai tuna ba ya fito. A harabar gidan ya tarar da Comared da Shazali kowa rai a bace suna ta musayar yawu. Comared ya dora masa laifin duk abin da ya faru shi kuma Shazali yana cewa ba zai fita ba sai an bashi kudin da aka alkawarta masa ko ya baza sirrinsu a ahafukan sada zumunta.
"Kai karamin kwaro ne Shazali. Karyar rashin mutumci kake shi yasa har ka sami kwarin gwiwar mayar min da magana. Harma da barazana. Amma yanzu zan tuna maka waye ubangidan kuma waye bawa."
Kira ya kwala da karfi wasu garadan maza biyu suka fito ya umarcesu da su kulle masa Shazali a store din gidan. Da yake jikinsa ya riga ya yi tsami saboda dukan da Abbati ya yi masa sai ya kasa kwatar kansa. Alh. Tahir yana gani aka ciccibe shi aka yi ciki dashi. Da Comared ya nemi jin ina zai je da sauri haka kin fada ya so yi. Sai kuma ya tuna cewa ta dalilinsa ya hadu da Alh. Sadisu. A takaice ma dai yana cikin yaransa na hannun dama. Saboda haka babu bata lokaci ya zayyane masa iyakar abin da yaji daga bakin Alh. Sadisun. Comared ko cikin gidan bai koma ba ya kira direbansa suka tafi tare.
***
Kafin su Alh. Sadisu su iso har an fara dukan Abbati a cell. Lokacin ya daina kokarin kare kansa daga zargin da ake yi masa balle dukan. Irin tunanin Munzali wanda yake ta kwabarsa a kai ne ya shige shi. Kokwonto da tsoron ko tubansu bai karbu ba shi yasa da an toshe kofa daya sai wata daban ta bude ta bakin ciki.
Ba su suka sarara masa ba sai da wani ya leko ya yi musu magana.
"Kai Sergent, ku taho da shi ofishin DPO yanzun nan ana jira"
Suna jin haka sun san cewa Alh. Sadisu ma ya iso. Jiki na rawa saboda kwadayin samun wani abu suka fito. Dukan da suka yi masa ma dama don su burge shi ne in yaji dadi ya yi musu ihsani.
Hankada shi su ka yi har ciki. Tausayinsa ya sake tsirga zuciyar Farha da taga yadda ya koma cikin kankanin lokaci. Fita taji tana son yi daga office din saboda ba za ta iya jurar kallon sa a a cikin wannan yanayin ba. Tana share hawaye suka hada ido sai ya yi murmushi yana yi mata alama da ta bar kuka.
Bai ankara ba yaji an kai masa wata mahaukaciyar a wuya. Yana kici-kicin kwacewa sai saukar duka a gefen idonsa. Farha ta sake saka kuka yayimda Lilu da DPO suke kicikicin kwace Abbati daga hannun Alh. Sadisu wanda yake ta ihun a fito masa da dansa.
Da kyar bayan an rabasu DPO din ya ce da Abbati "Malam ina mai baka shawara da kada ka wahalar da kan ka da mu ka fada min yadda aka yi ka dauke dan Alh. Sadisu da dalilinka na daukarsa"
Zai fara bayar da amsa su Munzali suka shigo suka same su. Hankalinsa ya kara tashi da yaga yadda aka sab'a masa kamanni a lokacin. Wannan abu fa a dalilin dawo da 'yarsa ya same shi. Shi kadai yaga ribar zama da Abbati yayinda Abbatin yake shiga tarin matsaloli tun farkon haduwarsu. Baaba Mari da Mal. Inuwa suka rasa abin cewa saboda tsananin tashin hankali. Mal. Sa'idu ne ya hau bayanin cewa dansa ba zai taba cutar da wani ba balle a kai ga sace shi.
DPO ya tambayi matsayinsu tare da yiwa Sergent din da ya shigo dasu fadan cika mutane a wurin. Jin cewa iyayen wanda suke tuhuma ne sai ya ce lallai a ragu. Office din ya rage daga Alh. Sadisu sai Mal. Inuwa, Munzali (a matsayin mahaifin yarinyar da ta kawo waya) da Abbati. Su Baaba Mari, Hanne da Mami Khadija da su Asabe duka suka koma reception. Mal. Sa'idu kuwa jinjina kai ya dinga yi. Duk takamarsa akan 'ya'yan 'yan uwansa yana ji yana gani DPO ya ce ainihin mahaifin Abbati kadai ake bukata. Wannan ya kara karya lagonsa da yaga ko kara babu Mal. Inuwa ya ce shi ne uban.
Shi Abbati Allah kadai Ya san irin ciwon da kansa, jiki da ruhi suke yi masa a wannan lokacin. Idonsa daya har ya tara jini don ya kasa bude shi sosai. Ya daure ya fada musu iya abin da ya sani
DPO ya bubbuga kan bironsa akan tebur ya sake yi masa wata tambayar.
"To kai me yasa ya dauki taka 'yar? Sannan ina ya kaita har ta hadu da Abdul?"
"Ban san inda ya kaisu ba. Kamar yadda na fada maka ya yi amfani ne da abotarmu ya tafi da ita daga hannun kakarta a asibiti." Abbati ya amsa masa cikin wani irin yanayi na kosawa da komai.
"Wannan bayanin naka bana jin ko alkali ka fadawa zai karbi uzurinka balle ni."
Munzali ya galla wa DPO din harara ya ce "Karya kake so ya yi maka ko me?"
"Kaga DPO a mayar dashi cell mana a dauko Shazali din" Alh. Sadisu ya fada ganin lokaci na tafiya an kasa cimma matsaya guda "idan wani abu ya sami d'ana ku ma da kuke ta jan kafa ba tsira zaku yi ba" ya kare magana yana tashi tsaye. Fita ya yi da waya a hannu yana waya wadda da alama da wani babba cikin 'yan sanda.
DPO din da kansa ya taso Abbati a gaba zai mayar dashi cell. Suna fitowa duka jama'ar da ya zata sun fita waje suka taso lokaci guda. Kowannensu da irin tambayar da yake jefowa domin son jin ko ya kubuta ne.
"Naga alama kana da tarin masoya" cewar DPO ya mayar da hankalinsa garesu "ku bashi shawara ya fadi gaskiya. Wallahi akan yaron nan case din yafi karfin tunaninku. Komishinanmu ma yana hanya kuma ko shi bai isa ya ja da umarnin Alh. Sadisu Nakano ba."
Jiki sam babu kwari Abbati ya dubi DPO din ya ce "iyakar gaskiyata na fada muku. Bani da zabi idan baku yarda ba sama da na cigaba da addu'ar neman taimakon Allah. A cikin kwanakin nan ina cikin jarabawar Ubangiji. Abubuwa suna ta tasowa wadanda suke barazanar rabani da duk wani abu da nake so. Babban burina bai wuce in rufe ido ko da na minti biyar bane idan na farka in ga ashe duka kwanakin nan mafarkinsu nayi."
Sai ga Mami Khadija da Asabe suna share kwalla. Farha ta fita ta sami wani dan dandamali ta zauna tana kuka. Ana dawowa daga rufe shi Alh. Sadisu ya dawo. Munzali ya tari gabansa ya ce shi ya san gidan Shazali.
"Me yasa baka fada ba tuntuni? Officer a hada shi da mutane mu tafi"
Basu bar wurin ba Alh. Tahir da Comared suka shigo reception din.
Mami Khadija da 'ya'yanta suka fara kallon kofa da tarin mamakin me ya kawo shi nan. Tana yin ido hudu da Comared taji zuciyarta ta tsinke. Babu ko tantama abin da suka saba na tara 'yan mata a guest house a kwana ana sharholiya ne take jin ya hadasu. Takaici ya sake kama ta da ta tuna cewa duba dansu fa suka zo yi amma ya kare da zuwa wurin Comared.
"Ina Abbatin yake?" Ya fara tambayar Munzali.
"Kai kuma waye?" DPO ya tambaya ganin shima nasa hankalin a tashe yake.
Alh. Sadisu ya bashi amsa da cewa abokinsa ne.
Shi kuma Alh. Tahir ya ce da DPO su shiga office dinsa yana da magana.
Alh. Sadisu ya yi saurin cewa "A'a ka bari tukunna. Gidan wani Shazali zamu je Abbati din ya ce wai 'yarsa a can ta hadu da Abdul."
Comared ya ce "Shazali kuma?"
"Ka san shi ne?" DPO da Alh. Sadisu suka yi masa tambayar a jere.
"Kwarai kuwa. Yallabai muje office din naka"
"Comared wallahi ba zan iya sake bata lokaci ba. Ka fadi ko ma mene ne a nan bani da damuwa." Alh. Sadisu ya furta a kagauce.
Alh. Tahir da Comared suka hada ido. Munzali kansa ya tsorata don bai san me zasu ce ba. Jikinsa ya gama sanyi yana jiran a farke musu laya.
"Shazalin nan da ake magana gagarumin kawali ne mai fada a wurin manyan mutane. Yana kai maza da mata duk inda ake da bukata. Bana fata amma indai shi ya dauke Abdul akwai yiwuwar ..."
A hargitse Alh. Sadisu ya ce "kai dakata min nan kada ka karasa wannan maganar banzan da ka dauko."
Baaba Mari, Mal. Inuwa da Mal. Sa'idu sun san waye Shazali da rawar da ya taka a rayuwarsu Abbati. Shi yasa furucin wannan mutumin bai basu mamaki ba. Sun dai kara shiga rudani ne akan dalilin da yasa Shazalin ya dauke Qibdiyya tunda basu sami zama anyi maganar ba.
Cikin lumana DPO ya lallaba Alh. Sadisu da cewa "Yallabai kada muyi saurin katse masa hanzari. Irin wannan abin yana cikin manya manyan matsalolin da muke fuskanta daga makarantun kwana. Lallai zamu je gidan shi Shazali din. Kuma yanzu zan tura mota a taho min da Principal, masu gadi da malaman makarantar tasu."
Gyaran murya Comared ya sake yi ya ce "ina da magana"
"Ina jinka" Alh Sadisu ya bashi amsa rai a bace kamar shi ne Shazalin.
"Ku bani kimanin rabin awa zan kawo muku Shazali har nan."
Alh. Sadisu ya nisa ya ce " kowane sakan guda yana da mahimmanci a gareni. Ni dai na fi son mu rankaya gidan nasa in ga halin da dana yake ciki"
"Ka sanni ba tun yau ba. Abin da ya shafi jininka nima ya shafeni. Ka bani lokacin da na bukata kawai. Komai zai zo karshe in sha Allah. Shazali shu'umi ne. Na rantse maka zai gwammace a kulle shi akan ya fadi gaskiya idan muguntarsa ta tashi."
"To meye alakarku da Abbati da shi wannan Shazalin da ake ta fada?" DPO ya jefawa Comared tambayar da take cin zuciyar kowa.
Alh. Tahir ne ya bashi amsa da cewa "Ni zan baka amsar tambayar nan idan komai ya lafa."
***
Babu wani abu da zai sami bawa face da sanin Mahaliccinsa. A wannan rana taimako ya zo wa Abbati da Munzali a yanayin da basu taba zato ko tsammani ba. Waye zai taba kawowa a ransa cikinsu cewa duk ranar da asirinsu ya tasarma tonowa Alh. Tahir zai zame musu garkuwa? Sai gashi ya zama wata katanga wadda ta tokare bayyanar sirrinsu da tozarcinsu a idon duniya ba tare shi kansa ya shirya hakan ba.
Kamar yadda DPO ya fada, ya tura motoci biyu an taho da duk wani mai kusanci da aji ko hostel din su Abdul daga makarantarsu. Masu gadi ma sai police aka zuba aka taho da su.
Jigum-jigum aka zauna jiran dawowar Comared. Alh. Sadisu kamar zai zare a tsokin lokacin saboda rabin awa ta gota.
Abin da yake faruwa kuwa shi ne da Comared ya koma gida sawa ya yi aka fito da Shazali. Ya kare masa kallo a ransa yana tausaya masa. Indai ta tabbata dan Alh. Sadisu yana gidansa to kashinsa ya gama bushewa. Ta wani fannin ma sune da riba domin duk abin da yake takama dashi na sirrinsu bai isa ta fito dashi ba idan yaje hannu.
"Kayi hakuri. Bai kamata na bari bacin rai ya sani tsare ka ba. Sai dai kana sane da matsayina. Ba zan so duk wani abu da zai shafi mutumcina ba"
"Ina iya tafiya?" Kawai Shazali ya iya tambayarsa saboda ransa ya riga ya gama baci. A gefe guda yana ta tunanin Abdul da ya hada da bango kafin ya fito. Ya rasa dalilin da yasa yake ta fado masa a rai tunda aka rufe shi a daki. Bai sani ba ko don son da yake masa ne har ransa.
Da dingishi ya karasa motarsa ya fice daga gidan. Yana tuki ana biye dashi a baya ba tare da ya sani ba. Motar amittacen yaron Comared ce wanda yasa bin Shazali gida. Shi a nasa zaton ma a can ainihin gidansa da kowa ya sani ne ya ajiye shi. Sai da yaron ya kira ya fada masa suna hanyar wata unguwa mai cikowar mutane da yawan gidajen gargajiya.
"Bishi kawai. Gamu nan a bayanku. Ka kwatanta min inda ku ka bi"
Bai yi mamaki ba don kuwa Shazali ya taba fada masa cewa yana da gida a unguwar inda yake shagalinsa. Suna hanya ya kira Alh. Tahir. Shi kuma ya sanar da DPO da Alh. Sadisu. Nan da nan aka yi ayari aka bisu.
Shazali bai san me yake jiransa a waje ba ya shiga gidansa kai tsaye.
"Abdul na dawo"
Shiru babu amsa. Ya murmusa a ransa yana tunanin ko har yanzu fushi yake saboda yanayin rabuwarsu da zai fita da Qibdiyya.
Yana sanya kafarsa a karshen soron ya hango shi kwance cikin jini a inda ya barshi da zai fita. Rawa jikinsa ya dauka tamkar mazari a yayinda ya duka a kansa yana kiran sunansa cikin sarkewar murya.
"Abbbbbduuu...llll?"
Shiru mai hargitsa tunani ne kadai ya bakunci kunnuwansa. A take duk wani ciwon jiki da yake ji sakamakon dukan da yasha ya kau. Ya dago kan Abdul wanda kasansa babu komai sai jini ya jijjiga shi. Jikinsa gabadaya a sake yake. Fuska tayi fayau saboda rashin jini. 'Na shiga uku' ya dinga ambata a ransa don ko sau daya bai tuna da sunan Sarkin da ke warware dukkan matsala ba.
"Mutuwa kayi?"
Ya yi tambayar da bai sa ran samun amsarta ba. Jinin wajen ya sake kallo wani ya bushe ma. A lissafinsa ya yi wajen awa hudu da barin gida. Cikin sauri-sauri ya tashi ya shiga daki ya dauko duk wani abu da zai iya tunawa wanda zai iya tona masa asiri ya saka a wata jaka. Dama ba wasu kayan kirki yake ajiyewa ba tunda lalatarsa kadai yake yi da kananun yara a wurin. Yaran da ko da zata kwabe a gaba iyakarsu nan gidan wanda ya saya da sunan wani dan uwansa na kauye. Kallo daya ya sake yiwa Abdul ya bude kofar gidan da niyar idan ya tafi ya tafi kenan har abada.
Sai dai me???
Ko minti goma bai yi da shiga gidan ba Comared da motocin 'yan sanda wadanda aka ki kunnawa jiniya suka iso tare da Alh. Sadisu. Ba don an rirrike shi ba ma da tuni ya afka gidan.
Idanun kowa akan kofa. Ga wasu 'yan sandan sun tokare kofar gidan ta yadda ko jinjiri ba zai iya wucewa ta tsakaninsu ba.
Shazali yana bude kofa ya yi ido hurhudu dasu. Cikin dimaucewar tunani ya koma ciki da sauri zai rufo kofar. Sai dai tuni mutum biyu sun riga sun sanya hannuwa sun dannota ciki. Na ukunsu ya tura da kafa. Na karshen kuma ya zura hancin bindiga.
"Idan ka sake yunkurin rufe kofar nan sai na fasa maka kai da harsashi"
Baya ya yi ya daga hannuwansa sama. Ya nemi yawu zai hadiya yaji bakin a bushe. Tunaninsa ya dauke sai hanya da ya bayar domin 'yan sandan su wuce. Abu daya yake takama dashi. Manyan mutanensa ba za su bari ya rayu a kulle ba.
"Ku bani hanya, ku bani hanya."
Abin da yaji ana fada kenan daga kofar gidan. Ya zuba ido domin ganin mai shigowa sai yaga Comared da Alh. Tahir. Budar bakinsa zai yi musu tambayar abin da ya kawosu nan sai ya hada ido da mutumin da ko baka taba haduwa dashi ba a zahiri to lallai an sha gamuwa a TV ko kafafen sada zumunta. Kai hatta muryarsa ba bakuwa bace.
Wani irin sanyi mai hade da zafi a tare suka fara binsa daga tsakar kansa har tafin kafa. Me ya kawo Alh. Sadisu Nakano gidansa?
Shi Alh. Sadisu ba tsayawa ya yi ba. Ciki ya bi 'yan sandan. Yana zuwa ya gansu akan Abdul suna salati. Kirjinsa yaji ya takure. Gumi ya wanke masa jiki. Gwiwa a sake ya durkusa a gaban Abdul ya janyo shi jikinsa. A daidai nan Shazali ya juyo domin ganin me ake yi. Hoton da idonsa ya dauka da kalaman Alh. Sadisu suka kusa sanya shi hadiyar zuciya. Duk da cewa ko uffan bai ce masa ba saboda rayuwar dansa ce a gabansa tukunna.
"Abdul tashi domin Allah kada ka mutu ka barni. Me zan fadawa mahaifiyarka? Me zan fadawa uwayenka? Wace rayuwa ce kuma za ta rage min idan na rasaka? Kai kadai na mallaka. Abdul ka tashi Baba ne da kansa ya zo"
Da kyar da sudin goshi kwakwalwar Shazali ta bude har yaji a ransa cewa muddin ya cigaba da tsayuwa babu abin da zai hana a dauki tasa gawar. Duk fadin kasar nan babu mai tsaya masa ya bar Alh. Sadisu. Mutumin da shugaban kasar dake kan kujera ma babban yaronsa ne a siyasa.
Kofa ya kalla babu ko tunani ya nufeta a guje ya fita. Kafarsa na fita yaji hanya ta kare. 'yan sanda sunfi biyar da suka cafke shi.
Ana kokarin daukar Abdul a ciki Alh. Sadisu ya ce su bari. Da kansa ya dago shi ya saba shi a kafada. Idanuwansa suna zubar da kwallar da rabonsa da yin irinta tun ranar haihuwar Abdul din ya yi ta farinciki. Hanya aka bashi ya fita da shi ya sanya shi a bayan mota. Ya juya da niyar fadawa DPO cewa gida zai wuce sai yaji an kamo hannunsa. Rikon dai babu karfi saboda rashin kuzari.
"Baba.." Abdul ya furta a hankali.
"Alhamdulillah. Ya Allah Ka bani ikon aikata alkhairin da za Ka yi farinciki dani albarkacin raya min Abdul da kayi"
Wannan shi ne furucin Alh. Sadisu kafin cikin gaggawa su bar wurin zuwa asibiti.
'Yan unguwa suna kallo aka jefa Shazali a bayan mota. Wadanda idanuwansu suka taba ganin lokutan da yake kawo yara sannan bakinsu ya bude suka dinga bada shaida.
Sai da aka gama bawa Abdul taimakon da ya dace kafin ayi maganar 'yan sanda. Alh. Sadisu yasa aka duba masa kuma likita ya tabbatar cewa lallai ana amfani da dansa don har ya dauko hanyar gamuwa da cuta. Kansa kuma ya bugu sannan ya zubar da jini. An matukar auna arziki da rayuwarsa bata salwanta ba.
Bayan komai ya daidaita ya bar Abdul tare da matansa ya koma police station. Abin mamaki babu mutum ko daya da ya tafi cikin wadanda suka zo domin Abbati. Ga kwamishinan yan sanda shi ma ya zo. Alh. Sadisu ya fada masa yana so a gaggauta shigar da makarantarsu Abdul da Shazali kotu.
"Ina gudun daukar mataki a hannuna. Ku yi abin da ya dace da wuri kafin a kira ku daukar gawar da hukuma bata bada umarnin kashewa ba"
Office daban aka ware domin sauraron wannan batu. DPO yasa aka fito da Abbati. A reception din Alh. Sadisu ya taresu ya rike masa hannu tare da raba shi a jikinsa.
"Ka yafe min. Da taimakon Allah da jajircewarka akan wanda baka sani ba dana ya kubuta."
Abbati bai ce komai ba. Alh. Sadisu ya juya ya ce idan yana da uwa a wurin nan a nuna masa ita. Mami Khadija tayi murmushi ta nuna masa Baaba Mari. Akan idon kowa ya karasa gabanta ya sauke gwiwarsa daya a kasa.
"Duk wanda ya sanni zai shaida duk zafina bani da girman kai. Ina rokon gafararki akan tozarcin da aka yiwa danki. Wallahi babu mai gane halin da na shiga dazu da wanda nake ciki yanzu sai wanda ya dandana shi. Don Allah ki roka min yafiyar Abbati. Dalilinsa Allah Ya raya min Abdul. Da ya jinkirta ko bai ma kira ba da karshenta bayana ya yanke kenan har abada"
Duk dauriyarta sai da kwalla ta zubo mata.
"Ya yafe maka har abada ba zai kara kallonka da laifin yau ba"
Tunda uwa ta yafe waye d'a da ba zai yafe ba? Tana fada zuciyarsa ta wanke fushinsa zuwa ga fatan kaffara. Munzali ya riko shi domin bashi madogara. Hanne tayi gaba tana kuka zasu tafi. Alh. Sadisu ya dakatar dasu.
"Ina neman alfarma. Don Allah kafin ku tafi ina son ganinka Abbati tare da baban yarinyar nan da Shazali ya dauka"
"Nima ina da magana dasu game da alakarsu da Shazali da satar diyarsu da aka yi." In ji DPO
A wannan lokacin ne kuma Alh. Tahir ya taka rawar da ta shafe tunanin kowa akan laifinsu na baya.
Office din DPO dai aka koma. Alh. Tahir da Comared, Munzali da Abbati sai kuma Alh. Sadisu da DPO din.
"Dazu Alh. Tahir kayi mana alkawarin warware abin da ya hada samarin nan da wancan matsiyacin. Na dawo da tambayar nan ne saboda ina son a hukunta shi akan Abdul da yarinyar wajenku."
"Wani labarin sirri ne wanda jinsa zai iya cutar da mai shi"
Alh. Tahir ne ya yi magana . DPO kuma ya bashi amsa da cewa rashin sanin gaskiya a hukumance zai mayar da Abbati sahun wadanda ake zargi. Wanda a karshe dole shi ma a kai shi kotu.
Basu da zabi. Kofofi sun toshe. Dole su fadi komai da bakunansu yau. Bisa wannan dalilin suka nemi a shigo da iyayensu. Abbati ya ce a hado da Mal. Sa'idu.
Abbati ne ya fara magana yana duban amininsa.
"Ranar wanka ce yau fa Munzali."
"Na sani. Ba a boyon cibi idan ta zo"
"Wadannan sune iyayena" Abbati ya nuna su Baaba Mari, ya dora da cewa "daga Kirikasamma aka turo ni Kano almajiranci. Da karancin shekaru da rashin wayo na zamewa kaina uwa da uba a dalilin haka."
"Ga nawa iyayen. A gabansu na tashi. A cikin gidanmu. Amma daidai banda wurin kwanciya babu abin da zanyi tinkaho
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 54 Chapter of 62