ta gatsina fuska sannan ta ce "to dai fada tsakaninmu ya kare. Duba status dina."
Kashe wayar tayi tana dariyar mugunta ta bar Farha da waya a kunne. A ganinta ko ma meye tunda har ta kirata ai da ta fada da baki. Kada kai tayi ta fara laluben sunan Yumnan a jerin sunaye dake bangaren status din.
(Alhamdulillah my lion has proposed. Wedding bells ringing)
Murmushin Farha sai ya koma dariya. Falo ta koma wurin kannenta tana tsallen murna ta nuna musu.
"Korafi ya kare Ya Farha ta shirya da aminiyarta." Cewar Sauda ita ma tana tayata murna.
Mardiyya kuwa rungume Farha tayi "congrats Sis. Ai na san sharrin fada da kawa. Ni da muka yi da Jamila har zazzabi na dinga yi"
Yadda ta fada ya sanyasu dariya. Farha ta zauna a nan inda suke ta kira Yumna.
"Wane lucky guy din (mai sa'ar) ne ya sace zuciyarki? Gaskiya sai nayi review na danna nawa stamp din."
Yumna taji dadin farincikin da ta tsammata daga Farha. Wannan zai taimakawa shirinta na farko wajen soma wargaza gidan. Ita yanzu hatta Mamin da take yiwa kallon uwa bata da sauran gashi a idonta. Mulkin da take zubawa a waje shi za ta dora a cikin gidan don ma kada a sami mishkila. Ba za ta ragawa kowa ba balantana ta bada kofar da wani zai takata a gaba. Wannan shawarar cousin dinta ce wadda suke yawonsu tare.
Numfasawa tayi zuciyarta tana dan dokawa da tsoro ta daure ta ce "sake duba status din na saka hotonsa. Zan dai zo har gida muyi shawara don ya ce nan da sati biyu yake son ayi komai."
"Sati biyu? Lallai ki ce zama bai ganmu ba. Amma kin san mun tashi. Ki bari zan zo kawai sai mu taho tare ki ga gidan."
So take ta ce mata ta riga saka kafa a gidan domin sun zo ita da Alh. Tahir yafi a kirga sai ta fasa.
"To shike nan. Sai na ganki."
Farha ta katse kiran ta koma kan status din Yumna ta sake budewa.
(My Lion and I {ni da zakina}) kadai aka rubuta slide din da ya biyo bayan wanda Farha ta fara gani.
Na gabansa ya sanya zuciyarta mummunar dokawar da bata taba yi ba tunda tazo duniya.
Mahaifinta ne Alh. Tahir sanye da singileti da dogon wandon shadda ya zauna akan wata doguwar kujera. Akan cinyarsa ba kowa bace illa Yumna daga ita sai wasu figaggun kananun kaya. Ga hannuwanta sakale da wuyansa yana dariya. Bidiyo ne na sakan biyar mafi tsaho da ciwo a zuciyar Farha. Mummunan gamo ne wanda ko Suhaib da Lilu bata fatan ganin dayansu da wata mace a haka.
Zazzabi, ciwon kai, tsananin bugun zuciya tare da sanyin jiki suka kamata. Jijiyoyinta suka neme daina kai sako yadda ya dace. Bata ji muryar kannenta ba lokacin da suke cewa ta nuna musu hoton mijin Yumna su gani. Bata ji bata ganin komai sai wannan bakin hoto da ya yi zaman dirshan a kwakwalwarta. Hawaye kuwa kamar ruwan famfo suka dinga ambaliya a saman kuncinta.
"Allahumma ajirni fi musibati....Allahumma. Innalillahi..." take furtawa ta kasa kai karshen ko daya.
A zabure Sauda da Mardiyya suka tashi suna tambayarta abin da ke faruwa bata kulasu ba. Mardiyya ta damke hannunta ta fizge wayar ta duba amma Yumna ta riga ta cire status din. Farha na gani ta danna musu delete.
Bata san tafiya take yi ba. Yaushe ta je bakin kofar bangarensu? Allah Masani. Ta dai tuna lokacin da ta mika hannu da nufin bude kofar domin ta fita. Daga nan komai ya dauke cak sai ihun Mardiyya da Sauda suna kiran sunanta.
BABI NA SHA BIYAR.
"Ya naga kun yi carko carko kamar masu barin gari, lafiya?" Alh. Rabi'u ya ce idanunsa na binsu daidai da kallo. Baki ya saki da ya hango alamun jariri ne a hannun Maimuna ba kunshin kayan da ya zata da farko ba. Tambayar mai haihuwa cikinsu ya yi Uwani ta nuna Zara.
"Shi ne ki ka taho nan maimakon ki wuce gidan mijinki daga asibitin? Me za ayi miki a nan wanda ba za ki sami dubunsa a gidan Alh. Unaisu ba?"
Innayo tayi kwafa hade da murmushi mai ciwo.
"Dama me za ta samu a gidan uban da bai san ci da shanta ba tun zuwanta duniya bare a kai ga batun hidimar aure?"
Magana ce irin wadda bai taba ji daga gareta ba, shi yasa shigarta kunnuwansa ta gigita shi. Sake kallonta ya yi ko zai ga ta inda ta kuskure da wadda ya sani mai hakuri da kawar da kai tsayin shekaru. Ita kuwa Zara ta kalla.
"Ki kira mijinki ko direbanki ko ki tura a samo miki abin hawa ki tafi."
Zara ta sake fashewa da kuka ta koma rokon Alh. Rabi'u.
"Baba ka bata hakuri na zauna a nan kamar yadda su Hajiyan Fatakwal suka ce. Idan na tafi yanzu wallahi matsala zan samu. Sun ce lallai sai na zauna nayi wankan jego..."
"Laifi kika yi? Ko sakin ki ya yi?" Ya tambayeta cikin tashin hankalin kalamanta da na Innayo.
"Saboda na sake haihuwar mace.." ta fada a kunyace murya a kasa.
Maganar ta shigi Innayo sosai don ji tayi kamar da ita ake. Ita ce ake gorantawa haihuwar mata.
Alh. Rabi'u sai ya yi nufin burge Innayo yau daya dai tunda ya fahimci ranta a bace yake. Fada ya soma ba ji ba gani.
"Amma wannan yaro anyi dan iska. Ita macen ba 'ya bace?"
"Ta ina mace take 'ya? Ai ka barshi ya wulakanta matarsa yadda aka yiwa uwar da ta raina lokacin da take ta haifar mata. Ita kuma ka barta ta koma inda ya fi gidan mahaifinta dadi. Banda abinka ai duniya tafi bagaruwa iya jima."
Juyawa tayi ta shige dakin baccinta ta barsu a tsatstsaye su da mahaifinsu. Yana son cewa wani abu domin kallon neman agaji suke yi masa sai dai bai saba ba. Matsayinsa a gidan suna ne kawai. Ba ya bi ta kan yaran sai bukatarsa ta tashi kamar yadda ya yiwa Salima da Hasiya.
Basu bar wurin ba wani almajiri ya ce ana sallama da Zara. Alh. Rabi'u sai ya leka a zatonsa mijinta ne. Maimakon ya ganshi sai direba ya gani an aiko shi da kayan tea, ruwan roba da maltina masu yawa. Zuciya ta kwadayi sai ya basu hanya suka fara shigo dasu. Kafin su gama Munzali ya dawo. Tasa motar ma shake take da duk wani kayan bukatar maijego.
"Meye wannan?" Ya ce da yaci karo da ledar kayan tea din. Madara da milo manyan gwangwani bibbiyu. Sugar na kwali guda hudu sai su ruwan.
Alh. Rabi'u da sauri ya ce "Mijin Zara ne ya aiko mata. Ku shiga dashi falona saboda 'yan barka kada su gani ayi ta hada shayi ba kai ba ...."
Ai kuwa Munzali ya hasala. A iya saninsa yana bawa mahaifinsa kudin da bai ci ace gwangwanin madara zai daga masa hankali ba. Da karfinsa kuwa yasa kafa ya yi ball dasu. Direban da ya kawo da almajirin daya taya shi shigo dasu suka saki baki. Maimuna da Hasiya kuwa hakan ya musu daidai.
"Ka dauka ka mayar ka fada musu nan ba gidan matsiyata bane. Zara kuma ta dawo gida kenan. Ita dashi sai ya zo gaban mahaifiyarta ya bata hakuri. Ka ce masa wannan sakon UBAN Zara ne!"
"Ni?" Alh. Rabi'u ya ce yana dan ja da baya. Wannan ai sanadi zai masa ya toshe kofa daya ta arzikinsa. Ya kalli direban ya ce "kai wallahi ban fada ba. Alh. Unaisun nan ba wani ganin girmana yake ba za ka janyo min matsala dashi" ya kare yana hararar Munzali.
Kallon tsanar da bai yi niyya ba ya jefawa mahaifinsa sannan ya kalli Zara.
"Ke malama ki fa daina wannan kukan. Idan kin ga kin koma gidan wannan mara mutumcin to da yawun Innayo."
Ransa na kuna ya fita ya nemo masu taya shi kwashe kayan tasa motar aka shiga dasu ciki. Uwani na kallon wannan dirama yadda Innayo ta tsame hannu akan Zara da kuma irin rokon da Maimuna, Munzali da Hasiya suka yi ta fama har ta kyaleta. Hada kayanta tayi ta shiga motarta ta bar gidan kafin a gama daidaitawa. Ita kadai a motarta take magana kamar sabon kamu.
"Dole ma na karasa gini saboda bacin rana. Ji yadda Innayo take mata kamar ba 'yarta ba. Ita ma Zara banza. Da tana da hanyar samun kudi wallahi tafi karfin wannan wulakancin. Hummm. Ba gashi Munzali na shiga maganar Innayo ta sauko ba?"
Allah Sarki Innayo. Duk barazanarta bata fatan kora Zara inda bata da daraja. Tabbas ranta ya baci amma tauna tsakuwa kawai take yi. Ta jira asa baki a bata hakuri domin Zaran ta gane da gaske take yi ne. Magiyar su Munzali taje mata akan gaba ne ba wai don nauyin aljihun dayansu ba.
***
'Yar karamar jakarsa mai cin kayan da basu fi seti uku ba ya zuge sannan kamar wanda ya yi aikin karfi ya zauna akan gadon a gajiye. Rashin kuzarin zuciyarsa ne ya harbi duka gabobinsa har ya haddasa masa wannan yanayin kamar na mai ciwo. Babu sauran jirgi mai zuwa Abuja yau. Shi kuma halin da yake ciki ba zai barshi yaji dadin tuka mota zuwa Abujan ba. Kansa yaji ya sara kamar an buga guduma lokacin da Hanne ta shigo dakin ta buga kofar da karfinta. Damuwa ce fal a ransa ya rasa wanda zai iya fadawa domin ya sami mafita.
"Ashe daki ka shigo ina ta faman jiranka na zata kana wurin Munzali."
Kansa ya rike da hannu biyu saboda magana ma kara masa ciwo take ga wayar Shazali dake shigowa babu kakkautawa. Hanne bata kula da yanayin nasa ba ta soma fada masa tasa an kawo mata mai-aiki ya kawo kudin sallamar wadda ta kawota.
Da kyar Abbati ya iya bude bakinsa ya ce "yaushe muka yi dake zaki dauki mai-aiki da har zata zo ban sani ba?"
Tabe baki tayi kafin ta ce "tohhh, daukar mai aikin ma sai na fada maka? Naga ba sabon abu bane tunda dama akwai tafiya tayi."
Abin da ke ransa yafi karfin wata rashin kunya da Hanne za ta yi masa. Kada kai kawai ya yi ya bata kudin da ta tambaya sannan ya tashi.
"Abuja zan tafi yanzu. Ban san kwana nawa zan yi ba amma bana sa ran yin sati in sha Allahu."
"Adawo lafiya" Hanne ta ce hankalinta yana ga kudin da take kirgawa.
Shi ma bai kulata ba ya dauki jakarsa ya fice. Sai da ya zauna a mota ya saka wani hadadden bakin gilas sannan ya tayar ya fita daga gidan. Ya kusa Unguwa Uku wayar Munzali ta shigo masa. Gidan mai ya shiga ya bi gajeren layin dake ciki sannan ya gyara murya ya amsa wayar.
Munzali da shigarsa gida kenan "ina kaje ne? Na dawo babu motarka."
Abbati ya dan kaurara murya yana murmushi "kai fa ka fiye naci. Yanzu daga baka ganni ba sai kira. Wannan idan kayi aure matarka ta shiga goma bama uku ba."
"Naji. Ni dai ka fada min inda kaje. Wallahi ina ganin babu motarka gabana ya fadi shi yasa na kira ba wai don na damu da kai ba. Banda ni ma waye zai iya zama da masifaffe. Ka wani zama mafadacin karfi da yaji kwanakin nan. To dai ina kake in zo?" Munzali ya yi maganar yana shiga motarsa.
Dariyar da Abbati bai son yi ce ta kubuce masa har Munzali yaji sautinta.
"Ina hanyar Abuja."
"In kaje ka gaida Zuma rock."
Ya san bai yarda ba sai ya rantse masa tare da fadin karyar da ya shirya tunda Shazali ya kira shi kwanaki biyu da suka wuce.
"Chief Harrison ke nemanmu. Shazali ya yi masa bayanin mun daina yaki yarda. Shi ne yace gara daya daga cikinmu yaje muyi masa bayani baki da baki. Wai a haka yana iya zargin ko hadin baki ne muka yi da abokin nan nasa da suka yi fada."
Saboda yadda yake fitar da maganar daki daki da sanin cewa karya ce ya sharo har wani irin bugu yake jin zuciyarsa tana yi. Da wahala idan akwai watarana da suka taba yiwa juna karya shi da Munzali.
Munzali ya saurari dogon bayanin amma abu daya ne yafi daukar hankalinsa. Hade girar sama da kasa ya yi kamar Abbati na kallonsa ya ce
"Wait! Ba mun ce ko waya ba za ta sake hadamu da Shazali ba? Menene nasa na kiranka yanzu?"
"Na fada maka..." Abbati ya soma fada yana jan motarsa gaban bututun zuba man.
"Yes ka fada naji amma ban yarda ba. Haba Abbati! Shazali dan is** ne kuma gogaggen makaryaci. Ka sani ko wata manakisar ya shirya maka tunda ya san Chief yana mutuwar sonka."
"Nima nayi tunanin haka sai na ce gara naje dai muyita ta kare dasu kawai." Shi ma da yake maganar ba shigarsa take ba saboda raunin hujjar da ya bayar. Da wane baki zai fada masa cewa kwanaki biyu kenan da ya sami alert mai tsoka kuma ana jiran yaje ya yu aikin kudin?
"To amma me yasa baka fada min ba? Me yasa kuma baka jira mun tafi tare ba?"
Abbati sai ya amsa masa da cewa baya so ya kawo masa matsalar da zata sa ya bar 'yan uwansa a yanayin da gidansu yake. Ya dora da nuna masa illar rashin ganin ko mutum daya cikinsu saboda matsayin irin mutanen da suke bi a da.
Munzali tun yana ta kokarin kure shi da tambaya saboda rashin gamsuwa har ya hakura ya amince.
"Don Allah ka kiyaye kar suyi maka wayo don na sanka sarai."
Abbati ya saki rai jin Munzalin ya dauko wasa.
"Ai baka da kunya dama kuma yau tun safe bamu hadu kayi min ba. Zan kira ka idan na kuma tsayawa yanzu zan hau titi."
Sun gama sallama Munzali zai katse kiran ya fasa. Haka nan yake jin wani irin nauyi a ransa.
"Abbati wallahi idan ka bari suka yi wani abu da kai ALLAH YA ISA."
Wani irin radadi ya rike duka jijiyoyin idanun Abbati saboda kukan da yake jin zai iya yi. Tafiyarsa daidai take da cin amanar Munzali, Baaba Mari da tuban da ya kuduri niyar yi.
"Me ka ce?"
"Allah Ya isa na ce. Mutumina kayi duk yadda zaka yi ka fito lafiya. Kaga ka jirani in zo mu tafi tare mana" ya kare a raunane yana mai jin tsoron kada ayi amfani da saukin kan Abbatin.
Sai da ya dake ya iya cewa "kaima ka san zan kiyaye. Idan na sami damar ganinsa a daren yau ma to gobe zan dawo in sha Allahu."
"No..a'a fa. Wane irin da daddare? Ka jira gobe ku hadu koda a restaurant ne da rana tsaka kuma a wuri mai mutane. Ka fada masa komai ka. Kuma ka tsaya akan bakanka ka ce musu mun daina duk aure zamu yi." Ya dan sako wasa yana dariya kasa-kasa "Idan kana dawowa ka jirani a Kaduna inje wurin Diamond girl."
"Wai da gaske ka ke akan yarinyar nan?" Kyakkyawar fuskar Farha na dawo masa tar a idanunsa.
"Tausayinta naji ranar nan. Sai nake ganin kamar irina ce ta tashi uwa bata damu da ita ba. Tunda kai ka fasa da yayarta ni dai ina ciki da kanwar. Allah Ya kiyaye hanya."
Daga haka ya ajiye wayar zuciyarsa babu dadi. Abbati kuwa kwalar idonsa ya hana zuba sai zafin dake yawo a ilahirin jikinsa. Dama can sun san haram suke aikatawa amma shaidan yafi karfin zukatansu. Yanzu kuma da suke jin sun shirya komawa ga Allah sai shaidanu suke neman hanasu. Wani irin abu ne ya soki kokon ransa da ya ayyana a ransa ko bashi da rabon tuba ne? Ko dai baya cikin masu dacewa da rahamar Allah? Zuciyarsa sai ta sare. Karfin gwiwarsa ya ragu. Tsoro da fargaba suka mamaye dukkan tunaninsa. Me yasa suka biyewa son zuciya a wancan lokacin? Ya akayi ya zama daga cikin masu raya zunubin mutanen Annabi Luďu AS? Tabbas ya san basu da alhakin dulmiyar da kowa amma idan ya tuna sun rayu kwatankwacin rayuwar karuwa sai yaji ya tsani kansa. Sun bi musulmi sun bi kirista. Manyan masu fada aji a kasar nan duk suna tafin hannunsu domin sun san sirrinsu. Kafin ya isa Kaduna zazzabi ya rufe shi. Tukin gagararsa yake neman yi don sau biyu yana auna arziki bai karawa wani ba. Da tambaya ya samu aka kwatanta masa asibiti mafi kusa da titin da yake bi na fita gari.
DOCTORS HAVEN
Shi ne sunan da ya gani an rubuta kato a jikin bangon dake kallonsa na asibitin.
(Yana daga cikin kokarin Shaidan la'ananne akan bayin Allah ya sarar musu da gwiwa yayin tuba. Ya kan sanyawa mutane hopelessness har kaji kamar tuban ba zai amfaneka ba. A bangare guda kuma Allah SWT zai iya jarabtar bawa da kalubale domin Ya kara masa ladan hakuri da jajircewa wurin tuba. Muhallishshahid shi ne kada mu karaya. Mu dage iyakar dagewa mu tsaya akan bakanmu. Idan Allah Yaso sai mu rayu cikin zunubi kuma Ya saukaka mana tuba da komawa gareShi. Sannan rahamarSa ce idan Ya so ya kawo mana nau'ikan jarabawa akan hanyar tubanmu domin mu kara imani. ALLAH SHI KADAI NE BASHI DA ABOKIN TARAYYA. Ya bamu ISTIGFARI domin Ya daukaka darajarmu rana gobe kiyama. Idan mun tsaya da ikilasi to lallai Allah zai bamu mafita da izininSa.)
***
Mami Khadija na daki tana aikin tsara slides (power point) na lecture din da take dashi da 'yan masters sati mai zuwa taji kamar ana kiranta a waje. Gilashin idonta ta tura ciki sosai ta tashi daga gaban teburin aikinta da sauri.
"Sauda? Farha? Mardiyya? Kai waye yake min wannan kiran ne kamar ana kuka?"
Hanyar fita zuwa bangarensu tabi inda take jin muryoyin. Sai da tayo kusa ta fahimci Sauda da Mardiyya ne suke kukan. A bakin kofa taci karo da Sauda wadda ta taho domin kiranta. Nan kuma idanunta suka sauka akan Mardiyya tana girgiza Farha tare da kiran sunanta cikin kuka. Da gudu gudu ta karasa gabansu ta durkusa a wurin.
"Me ya sameta?"
"Bamu sani ba Mami. Daga duba status din Yumna ta fadi." Cewar Mardiyya hannunta na rawa wurin shafawa Farha ruwa a fuska.
Ran Mami Khadija ya baci sosai ta ce "Yumna? Gaya min yadda abin ya faru. Sauda dubo min mazan nan mu kaita asibiti."
Bayan fitar Sauda ne Mardiyya ta fadawa Mami abin da suka sani.
"Na duba banga hoton ba amma na tabbata ganinsa ne ya sumar da ita."
Fuskar Mami tamkar bata taba murmushi ba baŕe dariya ta tashi tsaye. Lilu ne ya shigo lokacin Farha ta bude ido da kyar.
"Ku bani wayata" ta ce a tsorace tana gudun kada su ma su gani.
Yadda tayi ya tabbatarwa Mami Khadija cewa lallai hoton ya shafi mahaifinsu. Wayar ta mika mata don ta sami saukin rai har tana nuna mata kamar ranta ya baci ganin bata da lafiya amma tana neman waya. Farha bata ce komai ba sai kai da ta sunkuyar. Kunyar mahaifiyar tasu take ji sosai da tausayi. Ga wata irin tsana mara takunkumi da take hauhawa a zuciyarta ta mahaifinsu.
Mota ta ce su wuce ta tafi dauko mayafinta a daki. Ta dauko jakarta ta saka wayarta a ciki. Ji take kamar ana caccakarta da allura saboda bakin cikin halin da Alh. Tahir ya sakasu a ciki. Albarkacin 'ya'yan nan yaci kuma yake kan ci da tuni ta bar gidansa. Ba za ta yarda ya lalata mata tasu rayuwar da rashin kamun kansa ba.
Doctors Haven asibitin da suke zuwa duka gidan Lilu ya kaisu. Farha da kafarta ta shiga kuma tana ta rokon Mami akan su koma gida.
"Zan saba miki idan ki ka sake magana Farha."
Bata sake cewa uffan ba har aka kira sunan file dinsu suka shiga wajen likita. Abu na farko da likitan ya fara gani shi ne jininta dake barazanar haure mizanin zaman lafiyar dan Adam.
"Hawan jini nema yake ya tashi daga ciwon manya zuwa na kowa da kowa."ya ce a kokarinsa na yiwa Mami Khadija bayani "ki saka mata ido ta cire damuwa daga ranta kada a gaba ya zame mata ciwo."
"In sha Allahu zan kula doctor. Nagode."
'Yan rubuce rubuce ya yi a takardar gabansu ya mikawa Farha takardar. Magungunan da zasu saya ne ya rubuta.
Shiru suka fito babu mai magana sai hannunta da Mamin ta rike. Gani take kamar idan ta saketa damuwar dawowa za ta yi har ta kuma sumar da ita.
"Jeki mota ki huta na karbo magungunan."
Muryarta can kasa duk tayi laushi ta ce "zan iya Mami ki je ki zauna."
Lilu yana bangaren da aka jere kujeru ya hangosu ya taso. Mami ta ce ya tafi da Farha mota su jirata. So take kawai su bar inda take ta samu ta fito da zahirin halin da zuciyarta take ciki babu rufa rufa. Tana kallo suka sauka daga matattakalar kofar fita waje sannan ta sami wuri ta zauna maimakon sayen maganin. Hawayenta ta bari suka sauko a lokacin da ta sanya fuskarta a kan tafukan hannayenta. Yana daga cikin abin da take gudu ace duka 'ya'yanta sun san halin mahaifinsu. Sai gashi bayan Suhaib ga dukkan alamu Farha ma ta sani yau. Rayuwarta da ta sadaukar saboda karesu tana shirin zama shirme da bacin lokaci muddin aka tafi a haka. Yaranta zasu daina ganin girman mahaifinsu. Tarbiyarsu za ta tawaya domin yana da hakkin matsayin uba a wuyansu. Wace irin rayuwa zasu yi a gaba? Wane irin mutum Allah Ya jarabceta da aure? Yana da damar karin aure. Ga kudi. Kai idan ya so ma ya sake su duka ya sake sabon zubi a gidansa da dai wannan kazamar rayuwa mara fasali.
A cikin motar Lilu ne yake ta damun Farha akan ta fada masa wane irin hoto Yumna ta turo mata. Tausayin yayar tasa yake ji har yana hasashen ko dai mutumin wani ne da Farhan take so a gefe.
Maganar hankali irin wadda bai saba ba yake yi mata tare da ban baki
"Kin san dai babu wanda zai auri matar da ba tasa ba. Ki bar mata shi kawai. Naki mijin fa idan ya tashi zuwa sai Kaduna ta girgiza."
Murmushi tayi wanda ya hade da zubowar hawaye. Za ta barshi ya cigaba da wannan tunanin har zuwa lokacin da kowa zai sani. Iyaka dai bata fata ko kadan wani ya fahimci akwai mummunar alaka tsakaninsu tun a waje.
A lokacin da suke 'yar hirarsu ne kuma idanun Lilu suka kai bakin gate din asibitin. Motar Suhaib ce take shigowa yana waya dasu Sauda masu damunsa yaya jikin Farha. Motar bayansa wanda ya zata mai ita yana jiran ya wuce ne shi ma ya yi nasa parking din ta soma karar horn da karfi.
Tsaki ya ja da karfi saboda anki daina danna horn din "Zan kiraku Sauda" ya jefa wayar gefensa ya kauce.
Har ya gama parking babu sassauci a karar horn din. Mutane suka fara kallon motar ana 'yan surutai. Kimanin minti biyu a tsakani da suka fahimci ko motsi motar bata yi sai hankula suka fara tashi. Suhaib yana so ya shiga ya ga halin da kanwarsa ke ciki ya dakata. Shi ya fara zuwa gefen direban ya kama hannun zai bude yaji a rufe. Gashi gilas din da duhu baya ganin komai. Farha da Lilu da 'yan tsirarun mutanen wurin sun firfito an tsaya a wurin. Ta gilas din gaban motar suke iya ganin kan matukinta akan sitiyarin kuma baya motsi.
"Ki koma mota Farha bari mu gani ko zamu iya balle kofar a fito dashi" cewar Suhaib ganin tana tangadi kamar za ta fadi.
Bata san me ya fito da ita ba kamar yadda Abbati bai san ya akayi ya iya daga kansa dake tsananin ciwo a lokacin ba. Sannu a hankali yake dagawa saboda kwankwasa gilas din da ake yi ta kowane gefe ana cewa ya bude domin a taimaka masa.
Sakan daya, biyu, uku...goma, talatin...idanun Abbati suka sarke cikin na Farha suna kallon juna. Bata tabbatar shi ne na diamond plaza ba amma fuskar ba bakuwarta bace. Abbati kuwa mamaki ne ya kashe shi a zaune. Da ace bai ga Lilu yaron da ya fara tsayuwa yin hoto a motarsu ba, da Suhaib wanda ya bashi hakuri da sai ya ce lallai gizo take yi masa. Kai ya girgiza a hankali ya runtse idanunsa sannan ya sake budewa yana kallon inda take. Fuskar da ta zame masa hoton zuciya ya sake gani ta dan yamutsata tare da dafa gaban motar don kada ta fadi. Rana ce ta take sosai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 62