Share this page
a hannun mutane ya danne. Haduwarsa da Uwani da amincinsu ne yasa ya rage rarakar aljihun wasu. Bai taba shan wahala ko ta anini ba wurin tatsarta. Ita take kawowa tana bashi, shi kuma yana gina kansa. 'Algungumi, an dai fadi ba nauyi' ya ambaci maigidanta Salihi dashi a lokaci guda yana jan tsaki. Duk shi ne ya bata komai da ya far masa kamar ita ta aiko shi. Tunda ya san gaban kansa yake yi gara ya gaggauta guduwa kauyensu har kura ta lafa. Manyansa a harkar magudi ba za su bari ya rasa aikinsa ba. Yanzu ma daya daga cikinsu ne ya ce ya biyo ya karbi rabonsa na wasu kudade da suka yi kashe mu raba da hakkin talakawa. Hagu da damansa ya waiga don yana ji kamar ana kallonsa sai dai bai ga bakuwar fuska ba. Hakan yasa shi sakin jiki ya shiga office din mutumin. Yana rufo kofa wani masinja ya kira wayar DPO Yahaya kai tsaye ya sanar dashi shigowar Habibun. "Ka san yadda zaka yi ka rike min shi idan kaga zai tafi har mu iso." "Yallabai kada ku dade domin da jaka na ganshi" "In sha Allahu ba za mu wuce minti ashirin zuwa talatin ba." Masinja ya cika aiki kuwa. A matsayinsa me da ma'aikacin da aka fi gani tare da Habibu, DPO Yahaya yasa aka kai shi station. Bayan guntuwar tsoratarwa suka gano da gaske bashi da hannu wajen ha'incin Habibu. Ya dai san yana yi kuma kamar yadda ya dinga yi musu rantsuwa yana yawan yi masa fada. Alakar tasu ba wata mai zurfi bace sama da yawan musayar yawu game da bambancin ra'ayin siyasa. "Muna so ka bamu hadin kai ka taimaki abokinka ya daina cutar mutane" abin da DPO din ya fada masa kenan da ya bashi lambar wayarsa. Bai fi minti bakwai ya rage a lokacin da Masinja yake tsammanin isowar 'yan sandan ba sai ga Habibu ya fito yana fara'a. Masinja ya karaso suka gaisa ya soma jansa da hira. Idanun Habibu akan gate yana daddaga wuya ya zaro dari biyar "sauri nake ga wannan ka sha ruwa" "Yi hakuri ka saurareni Habibu. Matsala ce ta taso a unguwarmu." "Ka ganni nan? Garin zan bari yau dinnan. Ka nemi gidan Dagaci ko Mai unguwa ku kashe matsalar" Masinja bai hakura ba ya bi bayansa ya rage murya kamar sirri zasu yi. "Na san kana dan taba harkar nan. Ka taimakeni ko wani abu ne sai na biya." Saurin takun Habibu sai ya ragu. Masinja kuwa ya gimtse dariyarsa da yaji me yace. "Wace irin matsala ce? Yadda na dauke ka dan uwa kaima ka san ba zan iya dauke kai akan matsalarka ba" Masinja ya kirkiro labari ya shiga zuba masa. Wai fili ya sayar ba tare da sanin mai shi ba miliyan biyar. An gama biyan kudi amma balli na neman tashi. Shi ne yake neman mafita. Hannu Habibu ya dora akan kafadar Masinja yana murmushin mugunta. "Ina kudin yake yanzu? Allah Yasa baka kaisu banki ba" A madadin amsar Masinja da yake jira sai jiniyar 'yan sanda ta ziyarci kunnuwansa. Saboda tsabar kaduwa, hannun nasa da ya dora a kafadarsa ya kasa saukewa. Jikinsa ya yi sanyi kalau amma haka ya daure domin a zatonsa motar wucewa tazo yi ta unguwar. Dif ya daina jin karar har ya samu damar sauke numfashi. A ransa yake tunawa kansa cewa mijin Uwani a yadda take fada masa yafi kama da marasa wayo. Ita kuma tunda bata san ainihin me ya mata ba da wuya tayi kararsa. Wayar da tayi masa da asubar ranar dama ita ta kara saka masa son guduwa sai kura ta lafa. Yana can yana zancen zuci sai ji ya yi an damki hannuwansa. Ya zabura ya kalli masu rike shi yaga duka kayan gida ne a jikinsu. Wannan kuwa dabarar DPO Yahaya ce domin kada Habibu ya farga ya yi tunanin gudu. "Lafiya? Ku su waye? Satar mutane kuma da safiyar Allah a gaban jama'a?" Daya daga cikinsu ya dauko ID card ya nuna masa "mal. Habibu, ana tuhumarka da satar kudin Uwani Rabi'u ta hanyar yaudara" "Bangane ba!" Da ya fada a tsorace ta nuna cewa ya gane tsaf. "Idan mun station za ayi maka cikakken bayani. Muna neman hadin kanka ko mu tafi da kai ta karfin tsiya" Mutanen da suka fara tsayuwa kallo ya kalla sai kawai ya hakura yabi su. Bai san da sa hannun Masinja ba tunda gefe yaja ya tsaya. Ana tafiya da Habibu station DPO din ya sanar da Salihi. Shi ne ya bukaci ya zo da Uwani domin jin ta bakinta. A lokacin ya tafi gidansu daukarta sai yaci karo da ita a bayan mashin din Kukun su Munzali. Hawa mashin ba dabi'arta bace. Ganin da ya mata ya tayar masa da hankali. Ko dai fitar da tayi ta son zuciyarta ce ko kuma ta emergency ce na abin da ya shafi wani. Zuciyarsa sai tafi karkata da tunanin farko tunda ya santa da son kai. Babu bata lokaci yabi bayansu har gate din gidan Munzali. Akan idonsa ta dira da sauri don saura kiris ta fadi ta tura karamar kofar jikin gate ta shiga da gudu gudu. Shi ma sai ya kashe motarsa ya bi kukun da sauri ganin an bude masa gate zai shiga da mashin din. "Me yake faruwa ne a nan? Ni ne mijin matar da ta shiga yanzu Uwani." Kuku ya ce "Alh. Munzali ne babu lafiya" *** A cikin dakin Munzali kuwa a kwance yake yana rawar sanyi. Zazzabi yayi masa mummunan kamu. Har ta kai yana jin kamar ana kwankwatsa masa kasusuwa. Ciwon kai kuwa bai san daga wane bangare yafi sukarsa ba. Tunani barkatai sun addabi zuciyarsa. Mafi girma a ciki bai wuce jin tsoron ko tubansa ne bai karbu ba. Da tubansa ya karbu da babu wanda ya isa ya ketawa Qibdiyya haddi. "Da tubana ya karbu da Allah Ya tsare min ke ko bana raye" ya furta a kasan makoshi yana shafa kan Qibdiyya. Sake nanike mahaifinta tayi ta ce "Daddy har yanzu Papa bai zo ba" Kwalla ta taho masa ya yi saurin riketa saboda kallon kurillar da take yi masa. "Zai zo. Watarana zai zo...in Allah Ya yarda" saboda bai dade da gama wayar da ta kara masa ciwo da Baaba Mari ba. "Daddy..." Wata tambayar ce ya riga ya sani. Tun safe take faman damunsa. Da yace ta fita saboda ciwon kansa sai ta kulle kofar da mukulli maimakon ta bude bisa kuskure. Shi kuma azabar ciwon kai ya hana shi tashi. "Kaina ciwo yake don Allah kiyi shiru" Can gefe ta koma ta dauki biskit da juice wanda ya zame mata abinci tun safiyar yau din ta cigaba da ci. Wasa-wasa sai ga Munzali yana zubar da hawaye saboda ciwo. Komai ya jagule har yana tunanin rayuwarsa ce ta zo karewa. Sai dai yana tsoron tafiyar ba tare da sanin ko akwai nakasu a tubansa ba. Duk masu kwankwasa masa kofa ana kiransa yana ji amma ya kasa daga koda hannunsa ne. Ita kuma Qibdiyya bacci ne ma ya dauketa. A wannan halin Uwani ta iso gidan. Da sassarfa ta hau saman tana buga kofa amma shiru. Ana haka Salihi ya shigo Kuku yana yi masa jagora. Kiran da bugun da take yi ne ya kai hankalinsu gareta. Salihi yabi bayanta da sauri. Shi da Kuku suka hadu suna bugun kofa amma ko gezau taki motsi. "Qibdiyya" Munzali ya tabota da muryarsa da ta dashe bata fita sosai. Gyara kwanciya tayi abinta ta juya masa baya. Ya sake kai hannu ya tabata idanunsa na fitar da kwallar azabar ciwon kai. Da kyar ya samu ta farka tana zuba masa magagi. "Jeki ki bude kofa" Zuwa tayi ta kama mukullin tana ta murda shi ba daidai ba. Hamdalar Uwani da Asabe da bata jima da isowa ba ta tsaya a dalilin rashin buduwar kofar. Salihi ne ya yi dabarar cewa a miko mukullin ta kasa. "Na kasa cirewa" ita ce amsar Qibdiyya saboda ta kasa murda shi ya koma yadda zai fita. Sai da suka kwashe kusan minti goma sha biyar ana kwatanta mata yadda zata yi tana kasawa. "Ina babanki?" Asabe ta tambayeta a firgice. "Yana kwance. Kuma kuka yake yi" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. A zaton Asabe ya ma mutu. Cigaba da juya mukullin Qibdiyya tayi har ta gaji. Ta cire hannu kenan Munzali ya taso da bin bango ya bude kofar. A tare Uwani da Asabe suka tura kofar ya fado gabadayansa akan Uwani saboda ita ce a gaba. "Munzali? Munzali tashi. Na shiga uku na lalace. Ku taimakeni" Zantukan Asabe kenan tana faman jijjiga shi bayan Salihi ya daga shi daga jikin Uwani. Da ta tashi jakarta ta dauko a kofar dakin ta soma auna shi. Jininsa ya hau ta yadda ita kanta ta tsorata sosai. "Asibiti zamu kai shi" Ta ce da Salihi tana mikewa tsaye. Ko tunanin daga ina yake ma bata yi ba. Shi da kukun dai suka saka shi a motarsa. Asabe, Uwani da Qibdiyya kuma suka shige bayan mota. Hayaniyar fitarsu ce ta taso Hanne har ta leka ta taga. Akan idonta aka sanya Munzali a mota. Jiki na rawa ta sami abin fadi ta dauko wayarta ta kira Abbati. Rabonta dashi tun yana shirin tafiya daurin auren kanin Mami Khadija. Tunda akwai kudi a hannunta bata ga dalilin kiransa ba. Shi ne mai kokarin kiran duk inda yake koda sau daya ne a rana saboda hakki. Neman kudi kadai ke sanyata kiransa. Yau da yake gulma ce sai bata ji kyashin kiran ba. Yana dauka ta saki baki ko tauna magana babu. "Yanzu naga an dauko Munzali an saka shi a mota kamar matacce" Razanar da yayi zai rantse ko tonuwae asirinsa bata sa yaji makamanciyarta ba. "Me kika ce?" Ya tambayeta da muryar da take fita kamar ba tasa ba. Sai kuma ta dan yi jim da ta hango wautarta "bani da tabbas fa" Kashe wayarsa ya yi ya sake kiran Kuku. A nan yaji cikakken bayani. Tashin hankalinsa ba zai misaltu ba. Allah Yasa lokacin suna Jogana. Daga nan tafiyar bata da yawa sosai za a shigo garin Kano. Bayan minti arba'in Abbati ya shiga wani babban asibitin kudi wanda suke zuwa tare da iyalansu shi da Munzali. Sai dai ya daki gurbi domin kuwa ba nan aka kai shi ba. * Bangaren A & E na asibitin Sir Sunusi Salihi ya nufa. Sai lokacin Uwani ta farga da ina suke. Kaddara za a kira shafewar tunaninta a game da hukuncin da CMD ya yanke mata har aka shigo. Ta dade da gane hanyar nan din Salihi ya dauko tun a baya amma tunanin an dakatar da ita daga aiki bai zo ba sai yanzu. Da ta fito daga motar sai taji kafafunta tamkar ba za su iya daukar nauyin jikinta ba. Shi kuwa Salihi tunda bai san halin da take ciki ba sai cewa yayi, "Shiga kiyi musu magana mana a zo a dauke shi. Idan ke ki ka shiga na san ba za a bata mana lokaci ba" Sati biyu da suka gabata da ita ce ta shiga tana da yakinin cewa a lalace mutum biyar su biyo bayanta. Idan kuwa aka san cewa kaninta ne to Allah kadai Ya san irin kulawar da zai samu. Sai gashi a dalilin son zuciyarta yau ta zo amma tana kunyar shiga. Labari ya risketa daga masu kiranta jajen gaske da na karya cewa kowa ya san an dakatar da ita. Matron Uwani Rabi'u sananniya ce a asbitin sosai. Akwai kwazon aiki da shige shige. Ga masifa kamar da Alh. Rabi'u aka gina asibitin. Shi yasa ta tara makiya da yawa masu son ganinta a kasa. To yau ga ranar. Taimakon wadanda take nunawa dagawa ne zai sa kaninta ya sami kulawar da ta dace. "Matron Uwani me kike yi a nan?" Da sauri ta juya suka hada ido da wata Matron din. Kallo daya ta yiwa Munzali ta dubi matar. "Wallahi kani na ne babu lafiya. Yana bukatar emergency care." "Ai kuwa nan dai cike yake da jama'a saboda an kawo masu accident." "Innalillahi. To don Allah Matron ki taimaka min don yanayinsa ba zai yiwu mu fita dashi ba" "Sai dai ki fara kulawa dashi kafin likita ya zo" Har ta fara murmushi ta sake tunawa da suspension dinta. Amma haka ta daure tabi bayanta tana cewa su shigo dashi. Da gaske wurin a cike yake. Wheelchair (kujerar guragu) wani sub-staff (karamin ma'aikaci) ya kawo za a dora shi sai yaja baya da ya hada ido da Uwani tana kokarin sokawa Munzali allura a hannu inda za a kara masa ruwa. "Matron? Ko ba Matron Uwani bace?" Ya furta da karfi har aka fara kallonsu. "Nice. Don Allah yi sauri ka kawo ya zauna" Mutumin ya dakata yana yi mata kallon biyu-ahu "In baki kiyi aiki aji dadin korata?" Ya kara daga murya ya kira Matron din da ta shigo da ita wurin yana cewa " da alama dai baki san an dakatar da matar nan har na tsahon wata shida ba ko? To wallahi babu ruwana don dokar daga sama aka aiko da ita. Uwani ta kalli Munzali ko tsayuwa ya kasa yi. Yana tsakiyar Salihi da Asabe ne sun rirrike shi yana neman faduwa. Harbawa zuciyarta ta kama yi ta dubi mutumin rai a bace. "Wannan ba patient din kowa bane nawa ne. Kanina ne wallahi. Don Allah ka bani kujerar a zaunar dashi" "In na baki Allah Ya tsinan..." Ya tabe baki "ko doka bata hau kanki ba Matron wallahi yau dai sai dai wani ya taimaka miki. An fada miki na manta tarin rashin mutumcin da kika yiwa matar kanina a labour room ne? Ga kuruciya gashi haihuwar fari ce amma kika dinga yi mata tsawa kamar wata baiwar da kika saya da arha." Daga bandakin bangaren emergency din wata dattijuwa mai aikin shara da wanke bandakuna ta fito. Duk zancen da ake yi taji kuma ta kara da nata. "Ashe ba ni kadai matar nan ta yiwa diban albarka ba. Nifa matar makocin dana aka kawo sai a baranda ta haihu. Kememe Matron Uwanin nan ta dage sai an biya kudin gado wai na gwamnati sun kare saura na kudi. Yaron wajena yazo muka tafi nace mata nima nan nake aiki sai cewa tayi wai tayi ragin dari biyu albarkacina. Su biya dubu tara da dari takwas." "Uwani Rabi'u ake fada muku. Matar da ta kasa biyawa uwar da ta haifeta kudin ganin likitan hakori? Nan asibitin suka zo babarta ko bude baki ta kasa amma Uwani ta ce bata da kudi. Kai ranar naga rashin mutumci ajin karshe. Wallahi sai da na godewa Allah da bai bani haihuwa ba. Da haihuwar dan da ba zai ji kanka ba gara kayi ta shafa fatiha." Uwani ta juya suka hada ido da daya daga cikin nurses din bangarensu na haihuwa. An kirata ne saboda cikin masu hatsarin harda mai ciki. Muzanta da tozarci irin wanda ko a labari bata taba ji ba ne suka saukar mata. Idanu sun fi a kirga a kanta. Ciki harda na Salihi da Asabe. Ga maganganun 'yan kallo harda majinyata ana zundenta tana ji. Jikinta a take ya yi sanyi kalau kamar an jefata a ruwa. Gumi ne kawai yake karyo mata sakamakon zafin da take ji yana bin jikinta. Ta kuma kasa yin motsi don ji take kamar an zare mata laka. Kai ta sunkuyar kasa ta dunkule 'yar robar daure hannun wanda za a sakawa allurar karin ruwa a hannunta da karfi. A hankali ganinta ya ragu a dalilin kwallar da ta cika idanun. Hannu taji a kan na damanta an riketa ana jijjigawa. "Mu fita mu nemi private hospital (asibitin kudi)" Da kyar ta iya daga ido ta kalli Salihi sai ta mayar da kanta ga Munzali. Idanunsa ne suke yin luuu yana shirin suma. Ganin haka bata san lokacin da ta dauko wayarta ta duba nambar Barr. Umma Jibril. Ringing hudu ta amsa kiran. "Matron Uwani?" Ta ambata cike da mamaki. Yawu Uwani ta hadiya mai daci. Bata manta da haushin matar da take ji ba da yadda ta rufta ta a gidanta da sunan dinki za ta yi mata. Bacin ranta ba wai don tana tantamar rashin gaskiyarta bane. Ta san ita din mai laifi ce sosai. To amma yadda aka bi aka kunyata ta duk da ba a gaban mutane bane ya tsaya mata a rai. Ga matsalolin daban daban da suka kunno mata kai lokaci guda. Amma hakan bai hanata jin cewa Barr. Umma ita kadai ce hope dinta ba a yanzu. Muddin ta tsaya girman kai ta ce su tafi wani asibitin Munzali zai iya shiga mawuyacin hali fiye da yanzu. Barr. Umma sai ta ce "Ko ba Uwani bace?" Da taji shirun ya yi yawa. "Nice" ta amsa da sanyin murya tana kallon kaninta. Kanin da ba wani abu na zumunci da zata ce ya taba giftawa tsakaninsu tun kuruciya. Sai gashi a yau tana jin damuwarsa ta danne tata. Ga ciwo ga maganganunsa da bata gane ba sannan ga babbar lamari game da 'yarsa....'yarmu ta gyara a zuci. "Hajiya don Allah ina rokonki da ki taimaka ko na yinin yau ne kisa CMD ya janye dokar suspension dina" Karaya da nadamar da ba a son bayyanawa Barr. Umma take ji daga muryar Uwani. Da yake ba halinta bane sai ta kasa jan zancen ta hanyar nuna mata dama rana irin yau sai ta zo dole. "Me yake faruwa?" "Kanina ne muka kawo gashi babu wanda zai iya duba shi a emergency saboda yawan patients. Ki taimaka min don Allah." Yau wai ita Uwani ce take magana da roko har tana jin taruwar kwalla a idanunta. Ina zuwa taji Barr. Umma ta ce. Ba a yi minti goma ba aka kira babban likitan dake emergency din. Da kansa ya zo inda Uwani take kai gwauro da mari ya mika mata dan akwatin awon bp. "Ki daukar min duk wani relevant detail ki fara kara masa ruwa kafin na gama da wadanda suke kan layi." Murmushin da yafi kama da dariya gami da fitowar kwalla duka suka sauko mata a lokaci daya. Asabe tana ta hamdali yayi da Salihi ya karbe wheelchair din da sub-staff din nan yaki basu da farko ya zaunar da Munzali. Ita kuma ta kama hannunsa ta dauki bp. Sakamakon da ta gani ya tsorata ta sosai. Lokuta kalilan ta taba ganin wadanda jininsu ya hau haka a bangaren haihuwa. Zafin zazzabin shi ma ya haura ka'idar da aka saba. Da taimakon Salihi ta samu ta saka masa ruwa shi kuma ya rike ledar saboda stand din ma babu a kusa. Tayi masa allurai da duk wani agajin da ya dace da halin da yake ciki. Bayan ta gama iya nata ta ruga duk infa likitan nan ya saka kafa tana biye. Bata so ya manta da dan uwanta akan layi. Da ya ce a miko wani abu sai tayi azamar yi duk don idan yazo kansu ya kyautata. Asabe tana tsaye rike da hannun Qibdiyya amma idanunta suna biye da duk takun Uwani. Sanda kwalla ta silalo mata ita kanta bata sani ba. "Innayo bata yi asarar haihuwa ba" ta fada da raunanniyar murya. Salihi ya gyada kai a inda yake tsaye yana kulawa da Munzali wanda bacci ya fara daukarsa. Uwani baudaddiyar mace ce. Shi kan shi bai taba zaton akwai ranar da zai ga tambarin mahaifiyarta a tattare da ita ba. Indai mara kirki wanda ya amsa sunansa mutum yake nema to lallai in yazo kan Uwani ba zai matsa ba. Zai ce ya sami abin da yake nema ne kai tsaye. Inama Innayo tana kusa ta ganewa idanunta. *** "Mami zani Kano gobe in sha Allah" Wayar da aka yi mata daga Kanon ta fasa amsawa ta kalli Lilu da sauri. "Wani abin ne ya faru?" "Ya Suhaib ne ya buge a kafa ba zai iya tuki ba" "Kada ka boye min komai Lilu" ta furta cike da tsoro. Murmushi ya yi kawai ya kira Suhaib a wayarsa ya bata. Da kansa ya fada iya abin da zai iya. Kofar daki ya daka ya bugu a kafar. Hankalinta ya dan kwanta amma ta san Suhaib da dauriya akan abin da yake ganin zai janyo mata damuwa. Ga Lilu kuma shi ma bata jin yana cikin nutsuwar jan mota shi kadai har Kano. "Zan bika amma ka san ni ina son sammako" Dage gira ya yi harda 'yar dariya "dan farin kuma Mami? Ai na zata za ki daure har ya iso gida" " Fita ka bani wuri" ta ce ita ma tana dariyar. Fitarsa keda wuya ta kira Alh. Tahir ta fada masa abin da ya sami Suhaib. Izinin tafiya ya yi mata. Ya kara da cewa shi ma jibi abu mai mahimmanci zai kai shi Kanon. Su jira shi sai su dawo tare. Da ta ajiye wayar kwakwalwarta aikin tunani ta shiga. Lamarin 'ya'yanta yana matukar damunta. Kowa da irin tasa damuwar. Yanzu da tace tana son zuwa Kano bata ce ga dalilinta ba. Indai buguwa ce tabbas abu ne da zata iya jiran a dawo mata da Suhaib din gida. To amma zuciyarta ta gaza sukuni. Kanon dai take son zuwa. BABI NA SHA BAKWAI. Su Innayo basu san wainar da ake toyawa a gidan ba sai da suka dawo ita da Salima. Tambayar inda Uwani ta shiga ta yiwa Zara ta fada mata duk yadda suka yi har fitarta. "Ban san me yake faruwa ba amma tana fita Asabe ma ta fita" Dama da tunanin halin da ta bar Uwanin a gida ta wuni. Wannan labari sam bai mata dadi ba. Duban 'ya'yan nata tayi ta ce daya daga cikinsu ta kira mata Uwanin a waya. Salima ce ta kira da aka amsa ta mika mata. "Ban hana ki fita ba Uwani?" Fita tayi daga dakin da aka kwantar da Munzali don kada ta tashe shi daga bacci. Kofar ma a hankali ta rufeta sannan ta ce, "Muna asibiti da Munzali an kwantar dashi" "Me ya same shi?" "Bayanin ba zai yiwu ta waya ba Innayo" Muryarta babu wannan gadarar da ta saba da nuna isa. Kamar ma da sigar rarrashi Innayo take jin amsoshin Uwani. Da taji a wane asibiti suke sallar magariba kawai tayi ta sake tashi. Sai da Salima tayi da gaske wurin hanata fita bata ci komai ba. A lokacin ne ta fadawa Zara abin da ya faru da Ayaah. Suka gama jajantawa sannan suka fita zasu tafi asibitin. Wannan karon dai Zara sam taki yarda su barta a gida. Ciwon dan uwansu da zai kai Uwani asibiti ko biyanta zai yi ba abin rainawa bane. Innayo ta girgiza kai kawai don bata ga alamun zata ji maganarta ba suka tafi. Basu wani sha wahala ba suka iso dakin da Uwani ta kwatanta musu. Mamakin ganin Salihi a wurin ne ya kama Innayo. Ya gaisheta da fara'arsa sannan ya bata kujerar da yake zaune. Sai da ta zauna sannan ta kalli inda Asabe take tayi lakwas. Ta kira kannin Munzali namijin mai suna Bature akan yazo ya kwana amma kememe yaki. Uzuri mara tushe ya dinga bata. Dama rabonta da ta sanya shi a ido an tasarma sati. Da dai rabon kudi yake ba zai yi fashin zuwa. Ummakati kuma mijinta yace dare ya yi za su zo gobe, duk da lokacin da aka fada mata shida bata karasa ba. A gidanta autarsu mace ta tare saboda kwadayi. Gashi mijin Ummakati yana mata kulle. Sai abin ya shafi kanwar da ya kula tana yawo. 'Ya'yan Innayo mata wadanda kullum take aibatawa tare da yi musu kallon rashin galihu sune a tare da ita. "Asabe ya mai jikin?" "Da sauki, gashi ya sami bacci." Dakin sai ya yi shiru tunda hirar kirki dai bata taba hada duka mazaunan cikinsa a lokaci guda ba. Uwani waya take yi da wata mai shara tana bata sautun irin abincin da za a siyo da adadin mutanen dakin. Jin haka Innayo ta ce, "Mu kam a koshe muke" "Sai a tafi dashi gida. Guda bakwai za ki karbo kinji" ta karkare wayar tana duban Qibdiyya wadda ke faman matse kafa. "Kina jin fitsari ne?" Ta tambayeta. Da ka ta amsa don ta matsu sosai. Tashi tayi domin ta kai ta sai Asabe ta riga. Dakin ya zame mata kamar akurki. Kwarjinin Innayo da zuri'arta yasa ta kara jin kanta kamar wata 'yar kora. Suna fitowa taji ance, "Barka da dare Asabe" Sakin fuska tayi da ganin fuskar da ta sani. "Barkanmu dai dannan. Shiga ciki ga dakin da aka kwantar dashi." Qibdiyya da ya gani tare da ita ya jefa tunaninsa a mizanin aune-aunen hanya

Chapter 46 of 62