Share this page
akwai wani kwamtaccen abu na bacin rai tsakanin uban da d'ansa. Bai bar tunanin ma ya zauna masa ba ya kawar dashi ta hanyar sakin fuska suka karasa wurinsu shi da Munzali. Da fara'a ya tarbesu ya kuma dinga jansu da hira. Dama ransa a bace yake daga office amma ganin yaransa kadai ya wanke masa komai. Wata sabuwar ma'aikaciya suka dauka shi ne daga zuwanta ta fara nuna masa alamun tana so su kulla mu'amala. Matsalarsa da Farha ta janyo masa rashin kwanciyar hankalin neman yarinyar duk da ya kwadaitu da ita tun farkon zuwanta. Abin da ya bashi haushi kuwa bai wuce kukan da ta saka masa a office ba bayan ta gaji da dabarunta ya daka mata tsawa ya ce ta fita. "Amma sauran duk sun ce ba haka kake yi musu ba. Ni me na rasa?" Wannan magana ta hana shi hadiyar yawu a lokacin saboda dacin da ya taso masa. Sauran da take nufi ba wasu bane illa matan kamfanin nasa da ya nema a baya. Kenan duk kudaden da yake kashe musu da gargadin su rike bakunansu ya tashi a iska. Suna hirar da juna harda yi masa cune...in ba cune ba ta ya akayi yarinyar ta san ta nemi jan ra'ayinsa tunda ba shi ya fara nemanta ba? Har suka iso gida yana tunanin mutum nawa aka fadawa? Mutane nawa ne suke yi masa kallon tsirara mara kima ba tare da ya sani ba? Farha da baya tsammanin gani a cikinsu ya tambaya Sauda ta fada masa tana gidan Mama. Ba shi kadai yaji babu dadi ba harda Abbati da suka yi alkawarin haduwa yau. Alh. Tahir murmushi ya yi ya ce "ta fi ku dokin bikin nan naga alama." "Abba bata fada maka za ta tafi ba?" Mardiyya ta tambaye shi don tayi mamakin tambayar tasa. "Yau meeting muka yi tayi amma naga missed calls dinta zan kira." Sallama ya yiwa su Munzali ya wuce nasa bangaren kafin a kara wata tambayar da za ta fallasa karyar da ya musu. Abbati kam jikinsa ya yi sanyi tunda bata sanar dashi ba kuma ta san zuwan a yau dominta ne. Farha ta fi karfinsa ta kowacce fuska idan ya dubi tarayyarsu. 'Yar masu kudi duk da dai ya san indai don kudi ne ba zai wahala ba. To amma cikakkiyar 'yar boko ce mai tsaftataccen asali. Sirrin rayuwarsa ya sanya bai sami damar jin bacin ran kin fada masa ba. Zuciyarsa dai ta raya masa cewa bashi da wannan matsayin. Tunani ne ya yi masa yawa sai kawai ya yi sallama dasu Suhaib ya shige mota bangaren direba . Munzali dake son magana da Mardiyya sai ya fasa ya ce zai kirata. "Mutumina kayi hakuri. Karshenta inda taje din ba za ta iya haduwa da kai ba shi yasa bata fada maka bata nan ba ko ta ce ka biyota" Munzali ya fadi a kokarinsa na kwantar masa da hankali bayan ya zauna. Da sanyin jikin da bai so ko Munzali ya gani ba ya ce "Kar ka damu." Suna tafiya Suhaib ya tafi wurin Mami Khadija. Albishir ya yi mata don yafi kowa sanin damuwarta akan Farha. "Amma Mami yarinyar nan don wulakanci sai ta tafi gidan Mama bata fada masa bata nan ba? Wallahi duk yadda yaso boyewa sai da na gane rashin jindadinsa." "Ai kuwa zan gamu da ita. Ta barmu da damuwa Allah Yasa ba ita take korarsu ba muke tunanin su suke kin zuwa." Zancen yana da mata da kuma tsoron kada a sami matsala a gaba ta fara yi masa suka shiga wata hirar daban. A waje kuwa sai da kowa ya tafi sannan Lilu ya nufi dakin Abbansu da kayansa da ya dauko a mota. Tunawa ya yi da katin daurin auren wan abokinsa a dakinsa ya juya. Ya san ba zuwa zai yi ba tunda rana daya ne da na kanin Mami da za ayi a Kano. Duk da haka amintarsa da abokin nasa tasa yana son Abban nasa ya sani kuma ya kira baban angon ya masa fatan alkhairi. Akan gadonsa ya ajiye kayan Alh. Tahir ya bude durowar gaban madubi ya dauko envelop din katin. Jakar office din ya fara dauka sannan wayoyin. Ya dago babbar rigar biruka da wallet suka fado daga aljihun jakar. Guntun tsaki ya yi na bata lokaci ya duka ya daukosu. Hannu kawai ya zura a aljihun ya mayar dasu sannan ya kama zip din zai ja sai yaji ya rike yaki motsawa. Jibge kayan hannunsa ya yi ya juyo da jakar yadda zai ga zip din da kyau. Abu ne kamar takarda ya makale yasa taki zuguwa. A lokacin da ya zube kayan hannunsa akan gadon ne wayar Alh. Tahir wadda yake amfani da ita wurin kiran 'yan matansa ta fado daga aljihun babbar rigarsa. Lilu bai kula ba ya gama gyara zip ya kwashe wayoyin da yazo dasu a hannu ya yi gaba. Alh. Tahir bai tashi sanin wayar bata nan ba sai dare bayan Jiddo mai girki a ranar tayi bacci. Hankalinsa kuwa a take ya tashi. Ko a office ba zai so barinta ba saboda gudun fadawa hannun da zai ji kunya, ballantana kuma gida. A daren nan wurin daya saura ya fita yaje motar ya dudduba tunda ya san a hanya ma ya amsa waya da ita. Motsin wucewarsa Lilu yaji a lokacin yana kallo ya tashi ya leka taga. Ya yi mamakin me Abban nasu yake nema a mota a daren. Kamar ya fita tambayarsa sai yaga ya koma. Laptop dinsa ya kashe ya kade bargonsa ba tare da kula da wayar da ta fado daga kai ba ya haye gado ya kwanta. Wurin karfe tara ya fito zai tafi makaranta yaga Alh. Tahir tsaye da jallabiya ga direbansa yana ta bankade mota yana dube dube. Karasawa ya yi ya gaishesu duka. "Abba me ake nema ne? Jiya ma cikin dare na ganka kana duba motar nan." Murmushin dole Alh. Tahir ya yi saboda kada ya nuna ya damu da wayar. "Babu komai jeka abinka" ya ce masa. Shi kuma direban ya ce "wayar Alhaji" a lokaci guda. "Abba ka duba. Jiya duka wayoyinka na kawo maka daki." Kamar gaske Alh. Tahir sai ya saki fuska "bari naje na duba. Sai ka dawo." Ana rufe gate din gidan ya dawo da idanunsa da suke nuna tsantsar bacin rai ga direbansa. Hankalinsa ya matukar tashi. "Idan wayar nan ta fada hannun wani saboda sakacinka a bakin aikinka." Direba cigaba da bincike ya yi yana mamakin wannan abu. Shi ko kalar wayar ba zai ce ya sani ba amma an dora masa laifin batanta. Ana gobe zasu tafi Kano Mami Khadija ta kafa sharadin duk wanda bai gyara dakinsa ba babu inda zai je. Kamun amarya ne wanda aka hada da mother's eve da dinner za ayi a Kanon. Babu mai son a barshi da kallon hotuna yana cizon yatsa. Ita kanta ta san da wa take dama. Lilu ne dakinsa sai tayi da gaske yale gyarawa. Alh. Tahir ya so masu aiki su dinga gyara musu ta ce sam bata yarda ba. Tana barin wurin ya fice daga gidan. Shawarma ya siyo guda biyu manya manya da robobin yoghurt ya shige wurinsu Sauda. Mardiyya ce ta fara jin kamshin shawarmar ta tashi da murna za ta karbi ledar ya boye abarsa. "Kun dai ji me Mami ta ce. A gyara min palace dina a ci dadi. Bari na saka muku yoghurt din a fridge kafin ku gama." Da gudu gudu suka bi bayansa. Wasu kaya ya dauka a leda ya tafi dakin Suhaib ya shirya. Dinner din gidansu abokinsa ya tafi. Sauda ta fada toilet aka bar Mardiyya da uban shirgin kayansa. Tana cikin ninki taci karo da waya a kasan gado. Lilu bai san da ita ba balle ya kula da faduwarta. Daukewa tayi ta jona masa tunda taga chaja a jikin bango. Da suka gama aikin ta kunna masa kafin ta fita. Shi kuma da ya dawo ko bi ta kan wurin bai yi ba ya kwanta saboda gajiya. Da safe bayan sun gama shiri sun dauki hanya Yumna ta dinga kiran wayar. *** HUƊU ƘAFAFFUN... *** Flashing ya kai shida Danladi ya yiwa Ayaah. Tsabar kwarewa wasu a ciki ma bata jin karar wayar sai dai taga haske kamar walkiya ya bace. Hakura tayi da son dauka ta kira shi da kanta. Abin da ya fara cewa yana daukar wayar shi ne, "Gaskiya kuna da matsalar netwok a unguwar nan. Zuwana nan na kira ki ya fi sau goma. Har na fara tunanin turo yaro a kira min ke tunda ba zan iya tafiya ban ga murmushinki ba." Da sanyin murya ya yi magana. Cikin wani irin yanayi mai sa mutum ya ji kamar ya aikata gagarumin laifi. Ayaah taji babu dadi ta shiga bashi hakuri duk da a bangare guda tana cike da farinciki game da kalamansa. Da ya nuna mata kamar komai ya wuce sai ta ce ya ajiye mota a bayan layinsu za ta zo nan ta same shi. "Yanzu Babanmu ya kira Anti cewa yana hanya tare da bako. To ban sani ba ko bakon da zai kai ciki ne ko mai tsayawa a soro. Kuma kaga baku taba haduwa ba zai fi kyau ku hadu yana shi kadai." Cije lebe Danladi ya yi ransa na kuna. A soron nan nasu mai dan duhu ya so ya fara koya mata gurbatacciyar soyayyarsa. Gashi bai sami motar da tayi masa a garejin ba. A ina zai sami wannan damar idan suka hadu a filin Allah? Da muryarsa da ya kware wurin kwantarwa domin ya sanyawa 'yan mata tausayinsa ya yi mata magana. "To babu komai Ayaah. Ba zan so na takuraki ko na sanyaki cikin yanayi mara dadi ba. Banda zuciyata da ta kasa sukuni saboda tunaninki da na hakura sai lokacin da kike so na zo." Numfashi taja wanda ya bashi damar yin murmushin samun nasara tun kafin ta furta ta bakinta. Yadda yaso haka ta ce za ayi. Duk da tana jin nauyi haka ta daure taje ta fadawa Hasiya za tayi bako. Murmushi Antin tasu tayi gami da 'yar tsokana. "Gilashi zan saka domin na tantance ko ya cancanci zama surukina. To amma wani hanzari ba gudu ba. Ki bashi hakuri ya jira zuwa gobe. Kinga Babanku yana hanya da bako." Ko kadan Ayaah bata son batawa Dani rai. A tunaninta zai fassara rashin sauraronsa daidai da abin da yake fada mata matarsa tana yi. Zai shiga damuwa idan basu hadu ba kuma bata son haka. "Anti ko inje gidan Mal. Tasi ya sameni a can sai na bashi hakuri tunda ya riga ya zo?" Katangarsu daya da ta gidan Mal. Tasi din. Yadda ta marairaice fuska sai Hasiya ta amince. Dakin Abbas ta koma suna hira da Murja mai bashi abinci. A zuciyarta take tunanin lallai Ayaah tana son bakon nata. Za ta sanar da Honorable tun wuri ayi binciken da ya dace. Ayaah kuwa da saurinta ta sake kiran Dani ta fada masa inda zasu hadu. Ba haka yaso ba amma ya fiye masa waje. Tana cikin gaisawa da matar Mal. Tasi tare da fada mata abin da ya kawota taji sallamarsa. Wani iri ta dan ji tunda ta zata zai kirata ne. Da babu alaka mai kyau tsakanin gidan da nasu kuma ba ayi mata izini ba haka zai zo kenan? Ta tambayi kanta. Haka nan dai ta tashi da ledar da ta sako madaidaicin filas din da ta zuba masa abinci. Tana doso soron kamshi ya dinga hawa kanta. Yau ma turaruka 'yan duri ya bulbula sai dai hannu ya so zarcewa. Kamshin ya yi yawa har yana neman sakawa mai shaka mak'ak'in wuya. Suna hada ido ta manta da komai sakamakon murmushin da ya sakar mata. Yana da nashi kyawun amma babban abin da ya zame masa jari bai wuce yanayin jikinsa ba. Ga tsayi ga kaurin da bai kai a kira shi kiba ba. A idonta gani tayi kamar ya fad'a. Haushin matarsa ya kamata. Ta yaya mace za tayi sake mijinta ya dinga ramewa saboda rashin kulawa da abinci? "Mom dina tana gaishe ki" Rausayar da kai tayi gefe tana murmushin jindadi ta ce "ta sanni ne?" Dariya ya yi mata yana mai cewa babu wani abu nasa da mom din bata sani ba. "Idan ta dawo daga Dubai har gida zamu je ki gaisheta." Ayaah sai tayi murmushi. Ina ita ina zuwa gaishe da uwar saurayi? Ba Anti Hasiya da Babansu ba ko su Anti Fati da kakarta Larai sai sun kusa yankata. Yawo ba tarbiyarsu bace. Idan ya sake tayar da zancen a gaba za ta kirkiro hanyar fitar da kanta don babu inda za ta je. Ledar hannunta ta mika masa ya dinga godiya da shi mata albarka. Harda cewa wai ya akayi ta san yana jin yunwa? Filas din wan can karon da na yau ya yi mata alkawarin kawowa duka a washegari. Wurin karbar ledar ne ya samu ya hada da hannunta ya matse. Gabanta taji ya yi mummunar faduwa taja hannun da sauri amma ta kasa kwacewa saboda ya rike gam. Ja ta sake yaki saki sai ma wani irin shafawa da ya dinga yi a hankali yana mai bin kwayar idanunta da kallo da nasa da suka yi alamun tausayi. Ilahirin jikinta babu inda baya rawa kamar mazari. Cikin dabara ya rage tazarar dake tsakaninsu. "Ki dago ki kalleni Ayaah" ya ce a kasalance. Kasawa tayi sai girgiza kai da take yi tana son cewa ya saketa. Danladi sai ya saka yatsunsa biyu ya dago kanta. Runtse idanu tayi da sauri taji ya yi karamar dariya. "Kunya ki ke ji? Gashi ni kuma mutum ne mai son kulawa. Kulawar da na rasa a gida. Ina fata da addu'ar ki cike min wannan gurbin ki hanani tunawa akwai kowacce mace bayan ke. Idan kin amince min zan yiwa Mom magana kawunnai na su zo ganin Baba." Runguntsumi sunan abin da Danladi ya yiwa Ayaah domin yaji dadin isar da mummunan kudurinsa. A lokacin da yake son bude mata ido da haramtacciyar mu'amala ya kama zuciyarta a hannu ta hanyar nuna mata yana sonta. Banda haka ya hada da maganar aure da mata ke so a wannan zamani. Sannan ya rufeta ruf da ya nuna mata cewa za ta zo gidansa a matsayin mai share hawaye. Wannan tunani ke sanya mata mugun tausayin namiji da ganin ba zai rayu babu su ba. Da kyar ta iya mallakar tunaninta ta ja jikinta baya. Muryarta ko fita bata yi sosai ta ce, "Ka sakar min hannu don Allah. Kaga babu kyau." "Nima ba zan so yin abu mara da ke ba. Kiyi hakuri" ya ce yana sakin hannun. Ko sallama bata yi masa ba ta fita daga soron. Ya kwashe da dariya "Kin kusa samuwa." Ficewa ya yi abinsa da ledar abinci ya tafi gida. Yana zuwa ya bawa Raiha yana wani cin magani. "Sai ki saki ran ai. Baki san irin kokarin da nake domin samar muku abinci ba. Don na karbi darin dazu ki ke ta kumbure kumbure. Ki zuba min ku ci sauran" Bude filas din tayi ta ganshi shakare da abinci sai kamshi yake. Cikinta ya bada wani uban sautin yunwa. Da sauri ta samo faranti ta dibar masa sannan ta taso yaranta tana basu tana ci. Tambayar inda ya samo abincin bai zo mata ba don ta zata sayowa ya yi. * A dakin Abbas iyalin Honorable Habu suka hadu ya nuna su ga Abdulkarim wanda tausayin Abbas ya kusa saka shi kuka. Addu'ar samun lafiya ya yi masa tare da jaddadawa Honorable lallai ranar litinin a mayar dashi asibiti. Duk abin da ake ciki a sanar dashi. Hasiya tsabar farinciki sai da tayi kuka. Da zai tafi tayi masa tayin abinci sai ya ce a zuba masa ya tafi dashi. Dan filas din da yake madaidaici mai kyau shi Ayaah ta kai wa Danladi. Aka yi neman duniya aka rasa. Murja sai rantsuwar ta wanke shi take yi. Hasiya ta ce babu komai su bar maganar kada bakon yaji. Na maigidan ta saka a leda aka bashi. Bayan tafiyarsa ne ta rutsa Ayaah a kitchen ta tambayeta inda ta kai shi. "Lokacin da zaki fita wurin bakonki na ganki da leda da abu kamar shi sai dai ban zata abinci ki ka diba ba shi yasa ban miki magana ba." Sunkuyar da kai Ayaah tayi. Hasiya ta daure fuska saboda bata so hasashenta ya zama gaskiya ba. "Na zata mun wuce wannan matakin Ayaah. Kin sani sarai rowa ba halin gidan nan bace amma ba zan lamunci yiwa saurayi girki ba! Wato dalilinki na karbar girkin Ummita kenan? Bai ji komai ba ya karbi abinci a hannunki ko mahaifinki bai taba gaisarwa ba?" Tuni zuciya ta soma tunzurata. Ba za ta iya jure kalamai marasa dadi a kansa ba. Idan ba a tayata tausayinsa ba ai bai dace a aibata shi ba. "Anti matarsa ce fa bata girki. Shi ne na zuba mishi ba roka ya yi ba. Bata yi masa komai ko ya roka sai taga dama." Hasiya sai ta hadiye fadanta ta kirkiro murmushi ganin abin ya girmi abincin da ta bayar. "Kin kyauta da ki ka taimaka masa amma nan gaba ki dinga tambayata kinji ko? Kuma ki ce lallai zuwa na gaba ya zo mu ganshi." Ayaah sai murmushi. Tasa hannu ta rufe fuska sannan ta tashi a guje tana yiwa Hasiya godiya. Ita kuwa bayan tafiyar Ayaah daki ta koma ta rafka tagumi. Gabadaya saurayin bai yi mata ba daga jin furucin Ayaah. Maza masu tonawa iyalansu na gida asiri ba mazan kwarai bane mafiya yawan lokuta. Ta kuma fuskanci ya riga ya fara dasa mata wani tunani. Tashi guda idan ta nemi rabasu za a iya samun matsala. Gida za taje suyi shawara da Salima don ta fita fahimtar halayyar yara. Shawarar data bata kwanaki ita ce ta taimaka wurin kara kusantasu da juna. *** Ginin shopping mall din su Abbati ya yi nisa. Hankali kwance komai yake tafiya yadda suke so. Ga tafiyarsu Italy asibiti tana ta matsowa. A lissafi nan da kwanaki goma sha bakwai zasu tashi. Suna fata idan an dace babu wani abu da zai yi saura a tare dasu na bukatar jinsinsu. A gefe guda suna cike da farincikin daina jin motsin Shazali. Tun zuwan da Munzali ya yi gidansa ya masa dukan nan akan tafiyar Abbati bai sake nemansu ba. A zatonsu an rabu kenan... Yau ta kama Alhamis suna site din gininsu tare da masu aiki ana ta lissafin kudaden da zasu kawo domin siyan wasu kayan aikin. Hankulansu sun raja'a kan abin da ke gabansu wayar Abbati ta soma ringing. A hannunsa take ya juyo da ita yaga sunan Farha ya bayyana a screen din. A take zuciyarsa ta doka dan tsalle sai kuma ta koma ta kwanta. Tun zuwansu Kaduna da bai hadu da ita ba yake kiran wayarta a kashe. Yau kwana biyar sannan za ta kira shi. Yana son dauka yana jin tsoron me za ta ce. Muryar Munzali yaji wanda ya zuro kai ta kafadarsa. "A haka dai kamar za kayi abin arziki amma daukan waya ya gagareka. Tsoron me kake ji ne?" "Ni kar ka kara min tension ka matsa ka bani wuri" Abbati ya bashi amsa yana kokarin matsawa gefe domin yaji dadin amsa wayar. "Ita ma fa tana sonka" Tsayuwa Abbati ya yi ya juyo ya kalli Munzali da murmushi kamar Farha da kanta ta fada masa. "Ai fa na kasheka da dadi to dauki kada ta kuma tsinkewa" Munzali ya ce yana kara yi masa dariya. "Kaima ka ce wani abu. Bari na sallameta zan gamu da kai." Gefe ya matsa don idan Munzali ya saka shi a gaba kila hirar ba za tayi armashi da kyau ba. Yana dauka yaji zazzakar muryarta mai taushi tana magana. "Ya Auwal" Shiru...Abbati ya sake nutsewa cikin kogin son Ya Farha. "Ko dai wrong number na kira?" Tayi tambayar da murmushin da yake kan fuskarta tun lokacin da ta yanke shawarar kiransa da sunan gaskiyarsa idan ya dauki wayar. "Ki ka ce baki san shi ba" Abbati ya fada a hankali da ya rasa me zai ce. "Na san shi. Kararsa ma na kawo maka" Sai da ya jingina da bango ya cigaba da sauraron bayaninta. Korafi tayi masa na rashin nemanta ranar da yaje Kaduna a wurin 'yan uwanta. Ta tabbata da ya yi hakan dole zasu kai shi gidan kakaninta. Ita kuma wayarta ce gida na taro aka nema aka rasa a ranar. Ba ita tayi sabuwar waya ba sai da safe kafin su taho Kano. Kin fadawa Alh. Tahir wanda zai saya mata sabuwa a guje tayi. Sai da safen Mami Khadija ta bata kudi ta saya. "Kina nufin iskar gari daya muke shaka? Shi yasa yau nake jina daban." "Uhummm. Wane canji aka samu?" "Iska mai dadi, gari yana kamshi, zuciya kuma sakayau." Farha sai ta kama dariyar yadda yake magana. Kwatancen inda suka yi masauki ya nema ta ce ba za ta iya gane komai a hanyar ba. Wata 'yar uwarsu ta samu 'yar gidan da suke tayi masa kwatancen. Hira suka yi inda take fada masa daurin auren kanin Maminsu ne za ayi ta kuma gayyacesu. Hoton IV din za ta tura masa ta whatsapp don bata san unguwannin Kano ba. "Idan kun fita ki dinga kallon hanya tunda zama ya kusa kawo ki." Kunya kuwa ta kamata ta ce "Ni sai anjima". "Mu jima da yawa Ya Farha sarkin kunya. Yau dai tunda bikin na yamma ne ba zan zo ba. Amma gobe da jibi kafin ku koma in sha Allahu zan zo." * Anyi kamu ranar Alhamis din tare dasu Mami Khadija da suka iso ita da sauran yaran. Ranar Juma'a kuma sai bayan magariba za a tafi wurin dinner. Farha ta sami Lilu tayi masa famfo akan ya tambayi Mami ko zasu sami kati guda biyu tunda event din card admit ne. Shakiyanci ya yi mata kuwa son rai tana shanyewa sannan ya tafi wurin Mami. Yana gama fada mata zancen da ya tsara ta girgiza kai tana murmushi. "Dama kai ai ko ba aiko ka aka yi ba nayi tunanin za ka iya nema musu." Shafa kansa ya yi yana dariya "wallahi Mami don ba ki yi musu kallon kwaf bane amma sun hadu." "Allah Ya tsareni da yi musu kallon kwaf" ta ce tana mikewa da dariya. Babu wanda ya san irin farincikin da take ciki sakamakon soyayyar da taji akwai a tsakanin Abbati da Farha. Sun yi sa'ar samun katuna a wadace daga wurin dangin amarya masu shirya dinar. Hakan kuwa ya faru ne saboda suma zasu yi tasu a Kaduna idan an kai amarya. Yadda suka basu da yawa shi ne aka ramawa kura. Guda biyun ta bashi ya tafi yana murna. Suhaib ya kaiwa domin su ji dadin karbar gayyatar shi kuma ya kira ya fada musu. * Kafin lokacin masallaci dama Munzali yake da nufin zuwa dauko Qibdiyya yau. Tunanin zuwansu dinner din gashi Kande bata dawo ba sai washegari sai ya kira Abbati ya fada masa. "Kada ma ka fara tunanin soke daukota zuwa gobe. Ko so kake a fara ganin kamar akwai uzurin da za ka dinga fifitawa akanta?" Cewar Abbati yana tsaye a cikin wani bakery. Duk wani cake da ya san tana so ya saya yana jiran turn dinsa ya biya. Munzali ya sha kunu kamar suna tare ya ce "Ka gama kashewa yayarmu murya ni kuma ka dinga yi min masifa. Ya yi kyau!" Daga inda Abbati yake har hasko fuskar tasa ya yi. Dariya ya dinga yi masa, "Ai kaine da wani zance kawai don za ka je tsara budurwa baka son babyna ta bata show." Shi ma dariyar ya yi "Dadin abun kaima tsarin nan dai zaka je. Tun wuri na fada maka idan mun tafi da ita a wurinka zata zauna ku kare kalau." Da haka suka yi sallama. Munzali ya kira Mardiyya shi kuma Abbati gudun kada Munzali ya shashantar da dauko Qibdiyyan yau ya kira Zakiyya ya ce mata yana hanya. Abu ne da suka saba dama. A wajen kaita gidan ko daukota daya daga cikinsu ke zuwa ko suje tare. Tunda Zakiyya ta san da tafiyar tun kwanaki biyu ta riga ta hada mata 'yan kayanta. A can dinma tana da kaya domin dakinta guda. Hatta uniform akwai koda watarana dalili zai sa ba a mayar da ita da wuri ba. Fitowa tayi daga daki tana kwala mata kira domin ta zo ta shiryata. Duk inda take tunanin samunta ta duba babu Qibdiyya babu dalilinta. Hankalinta tuni ya fara tashi tunda ta tabbatar tare suka

Chapter 30 of 62