Share this page
In dai kura na maganin zawo to shakka babu yau zan wa kaina magani ta fada a ranta tare da cusa kai cikin gidan A falo ta iske Tahir ta gaishe shi a ladabce tare da fada masa Nasima ce ta aiko ta yin girkin asibiti. Bai ce mata komai ba sai tunanin irin wannan karfin hali nasu, dan me ba za suyi a nasu gidan ba sai a nashi. Hanyar kitchen ya nuna mata ya kau da kai ya cigaba da abun da yakeyi. Kafin ta wuce sai ta cire mayafi ta aje kan kujera, ta wani hau yarfe gumi daga su wuya da kirjinta. Jujjuya jiki ta dinga yi na daukar hankali. Tahir kamar baisan tana gun ba, ita ko bata fasa ba har sai da ta tabbatar ya waigo ya kallo inda take nan ta juya masa baya ta wuce kitchen din. Bata jima da shiga ba ta saki wata kara har sai da Tahir ya dan firgita ya taho da azama zuwa kitchen din dan ganin me ya faru. Tsalle ya sameta tana yi tana direwa ita nan a dole hannun ta ya kone. Sai ya tuna da lokacin da Nasima ta fara rungumar sa a cikin gidan da irin wannan sigar. Sabanin Nasima, ita Jiddo bata nufo shi ba. Yayi dan murmushi a ransa tare da yi mata sannu ya juya zai fice kawai ta saka kuka. Hakan ya sashi dawowa. "Naga hannun" ya umarceta. Kamar jira take ta mika masa. Yasa hannu ya riko hannun nata ba kunya ba tsoron Allah. Daman yaya lafiyar kura balle yaga abin da rai ya biya. Ya hau hura mata yana kallon cikin idonta, ita kuma tana wani sussune kai. "Ko muje daki na shafa miki magani ne." Ta sunkuyar da kanta tana matse ido wasu hawayen na zuba "A'a ka barshi ma ba zafi." "To kukan na meye?" Ya tambaya hannunsa a bayanta yana shafawa. Suna hada ido ya kanne mata nasa yana murmushin 'yan duniya. "Babu komai" ta ce baki na rawa. Dakinsa ya ja ta tana binsa kamar bata sani ba tana kuka. Rarrashinta ya yi ya sake tambayar dalilin kukan. "Hannuna zugi yake yi min da wuya na iya girkin. Idan na koma haka kuma Nasima da Laraba ba kyaleni zasu yi ba." "Kar ki damu. Muje na saya musu sai ki kai." "To ai za ta yi min fada idan taji kai ka saya." Ta ce a shageabe. "Zan yi mata bayani." Godiya ta dinga yi masa har suka bar gidan. Da dai bai yi niyyar zuwa asibitin ba amma tunda yana son samun kan Jiddo sai ya bi a sannu. Da suka isa asibitin shi ya dauko ledojin abincin tana biye dashi a baya. Ta bude masa kofar kafin ya shigo Nasima ta soma zaginta. "Uban me ya tsayar dake daga zuwa girki bayan babu nisa." Hawaye ta sake tarawa a idon tana rawar murya ta bata hakuri. Tahir kuma yaji ransa ya baci. Ita da Ladidi suna ganinsa suka fara murna. Duk da Nasima taga abinci ya kawo amma sai da ta tambayi Jiddo ina wanda ta dafa. "Konewa nayi Nasima. Shi ne Abban Mardiya ya ce na barshi zai siyo." Mantawa tayi da yadda take ladabin kura a gabansa ta hau zazzaga mata bala'i. "Wani salon karuwancin ne wannan ko me? Gidana na tura ki? Me ki ka je yi?" Ai sai Jiddo ta fashe da kuka "Naji kin ce naje gida nayi girki. Na zata gidanki ki ke nufi." Sake bude baki tayi Tahir ya mike a fusace sai tayi shiru tana taune lebe saboda bacin rai. Ta fi Jiddo iya bariki. Idan ta ce za ta shiga huruminta sai ta kwashi kashinta a hannu. Daga ranar ta ja mata kunne akan kada ta sake zuwa gidanta ko da wasa. Ladidi ta sake matsa mata. Ba don tana morarta da aiki ba da ta korata inda ta fito. Jiddo ta amsa da to. Aka kwashi kwanaki Tahir baya ganinta. Sai rannan bayan ta gama fakonsa ya hangota a gefen gidansa tana share hawaye. Da sauri ya taka burki ya fita wurinta. "Ke lafiya?" Bai rike sunanta ba. Fashewa tayi kuka ta rike ciki tana matsawa. "Don Allah ka taimakeni. Cikina, cikina." "Muje ciki wurin Nasima. Ko kuma shiga mota bari na kira ta mu kai ki asibiti." Hannunsa ta kamo da sauri tana zubewa a kasa "ni dai la taimaka min ka mayar dani garinmu." Kallon rashin fahimta ya yi mata ta ce masa tun ranar da ya kaita asibiti da abinci Nasima ta hanata shiga gidanta. A can gidansu kuma Ladidi ta matsanta mata. Abinci ma sai da kyar ake bata. Yanzu haka ma ciwon na yunwa ne. Da yake idanunsa sun rufe sai yaga kamar da gaske ta fada. Ransa ya mugun baci ya shiga da ita gidan. Nasima bata nan bai san inda taje ba. Khadija kuma ta zo hutu da yara saboda bikin kanwarta bai san suna ciki ba. Akan idon Suhaib ya shigar da ita dakinsa. Ya koma ya hada mata abincin da Nasima ta ajiye masa ya kai mata. Ta ci ta koshi sannan ya ce ta taso zai kaita hotel ta kwana gobe sai ya kaita gidansu. Khadija ta gama yiwa Sauda wanka kenan Suhaib ya fada mata Abbansu ya dawo. "Amma Mami naga ya shiga dakinsa da bakuwa maimakon ta zauna a falo ta jira ki fito." Gabanta taji ya fadi. Ba abin mamaki bane daga halayyar Tahir amma tayi zaton ya yi hankalin da zai daina kawo tarkacensa gidan aurensa. Yadda fuskarta ta sauya a idon Suhaib ya gane akwai matsala. Da ta ce ya zauna ya kular mata da Sauda tana zuwa sai yabi bayanta ba tare da ta sani ba. Batun zuwa hotel kadai taji a kofar dakin ta kwankwasa. Ya zata Nasima ce saboda haka kai tsaye ya bude. Ganin Khadija a tsaye sai yaji kunya ta lullube shi. "Ko don lafiyarka idan ma baka tsoron Allah Ya kamata ka yiwa kanka fada." Da sauri ya ce "ba fa abin da kike zato bane. Taimakonta kawai nayi." "Hmmm, taimako a uwar daka? Ina jiye maka ranar nadama domin wallahi hakkin duka matan da ka ke lalata dasu ba zai barka ba." Haushi yaji tunda bai yi din ba kuma take gaya masa magana. Kafin ya ce wani abu Nasima da ta dawo ta shigo wurin. Bata san me yake faruwa ba ta taho da gadara da tsiwarta. "Duk jarabar mutum dai yau girkina ne tunda ban san zaki zo ba. Sai ki koma sai gobe." "Ke miji ya dama Nasima. Idan kin shiga kya yi maganar girki da ta ciki ba ni ba." Ai kamar ta watsawa Tahir wuta ya ji takaicin abin da ta ce. Hannu yasa ya janyota za ta bar wurin ya kwasheta da mari. "Wato ban dameki ba? To idan kin isa ki saki kanki." Hannuwa yaji daidai kugunsa aka dage aka hankada shi sai da ya daki kofar dakin ya fadi. Yana tashi yaga Suhaib yana huci kamar maciji. "Ni ka ture Suhaib?" Ya ce da tsantsar mamaki. "Me yasa ka mari Mami?" Yaron ya bashi amsa kai tsaye. Bakinsa Khadija ta doke da sauri tana cewa ya bawa babansa hakuri. "Khadija halayyar da ki ke koya musu kenan?" Za ta yi magana suka ji sautin ihun Jiddo ya fada dakin yayin da Khadija taja hannun Suhaib. Amma kunnuwansa sun jiyo masa kalmar 'karuwa' da Nasima ke kiran Jiddo. Lokacin da Khadija ta ce suyi magana da ta ciki ta fada dakin da sauri. Jiddo dama tana jin muryarta ta kwanta akan gado ta kwaye zani har cinya. Bata ma gane ko wace ce ba saboda azabar kishi sai da ta finciko wuyanta. "Jiddo?" Ta ce da rawar baki "ni za ki yiwa haka? Mijin nawa zaki nema saboda ke 'karuwa ce'." "Nasima kiyi hakuri babu abin da muka yi." Ta ce tana kukan munafurci. Idanunta sun rufe ta shiga dukanta ba ji ba gani. Da kyar Tahir ya kwaceta ya kuma tsinkawa Nasiman mari. "Ki je gida sai na nemeki. Zan zo na karbi Mardiya don ba za ta zauna a gidanku na marasa tarbiyya ba." Hauka ne kadai Nasima bata yi ba. Tana ta kokarin sake kamo Jiddo ya shiga tsakani. Da kuka ta bar gidan da alwashin sai taga bayan Jiddo. Ita kuma tana ganin fitarta ta soma kukan rayuwarta ta kare domin ba ita ba hatta mahaifiyarta sai Ladidi ta ciwa mutumci. "Zan baki matsayin da basu isa su tabaki ba." Ya kuwa aikata abin da ya ce! Sati hudu a tsakani sai ga Jiddo ta dawo gidan a matsayin amarya. Dakinsa ya zama nata. Nasima da Ladidi suka haukace wurin bin bokaye da malaman tsibbu. Zumuncinsu da 'yan uwa da yawa ya lalace. Da kyar da sudin goshi bayan wata biyar ya yarda ta dawo gidansa. Kazamin kishi suke bugawa ita da Jiddo kamar zasu ga hanjin juna. Tun daga kan Mardiya bata sake haihuwa ba. Jiddo ta zubar da ciki yafi a kirga a kauye har ya taba mahaifarta. Ita ko haihuwar bata yi ba. Khadija ba ta shiga sabgarsu daga su har mijin da suke rigima a kansa. Tana gama karatu kamfanin da tayi bautar kasa suka riketa. Albashinta ta shiga tarawa har ya isa sayen fili. A hankali ta soma gina kayanta saboda ta matsu ta raba 'ya'yanta da kazamin gida irin na mahaifinsu. Duk da haka tana kokari sosai wurin shanye abubuwa da rufawa Tahir asiri don kada su san halinsa. Kusan babban burinta a rayuwa bai wuce nesanta su daga sanin halinsa da kwatanta aikatawa ba. Sai dai tunda kudi suka sake zama a hannunsa rashin mutumcinsa ga duka matan ma ya karu. Ita da yake ragawa darajar 'ya'ya ma ya daina. Nasima da Jiddo dama basu da wanban darajar. Gida ne tambadadde wanda mai shi ya lalata da hannunsa. Abu daya suka tsira dashi wato makauniyar soyayyarsa ga 'ya'yansa. Su biyar dinnan bashi da na biyunsu. Don ma Suhaib ba ya sakin jiki dashi ko kadan. Tun ranar da ya mari Khadija ya dauki karan tsana ya dorawa mahaifinsa. Da sannu yana kara wayo ya gane halinsa ciki da bai. Sai yake jin inama wani ne can Abbansa ba wannan manemin matan ba. Khadijan da yake yi dominta kuma kullum fada take masa akan ya bi mahaifinsa don neman rabauta ranar lahira. Sai yake ganin kamar cin kashin da ake mata baya damunta. Yana shekara goma sha biyar ya fara zukar tabar wiwi a boye saboda yawan damuwa da halin da iyayensa ke ciki. Lilu kuma ya zama mugun fitinanne mai yawan dauko magana. Duk kaffa-kaffa da Khadija take yi da rayuwar 'ya'yanta saboda mahaifinsu ba zai hana kaddara ta cimmusu ba wata rana. *** SHIDA RANAKUN AIKI. *** Kwance tashi ba wuya a wurin Allah, yaran Innayo duk sun girma amma har kawo yau sana'o'in da takeyi babu wanda ta daina. Girma ya soma kama ta, ga wahalhalun ayyukan da takeyi domin ta rufawa kanta da ahalinta asiri. Sannu a hankali lafiyar idanunta ya soma tabuwa sakamakon yawan zama gaba murhun da takeyi. Amma haka nan take daurewa don samar wa yaranta ingattacciyar rayuwa. A kullum burinta Yaranta manyan uku duk sunyi aure Uwani, Maimuna da Salima, saura Zara da Hasiya a gabanta. A yadda rayuwa take gara musu tsugunne bata karewa Innayo ba. Uwani ta gama School of Nursing abinta har ma ta kama aiki a Abdullahi Wase Specialist Hospital Kano wanda ake yiwa lakabi da asibitin Nasarawa. Tana samun kudi sosai sai dai anyi rashin sa'a. Halinta yana neman zarta na mahaifinta. Mugun mako da kyashi gareta. Mijinta yana da rufin asiri daidai gwargwado. Lab Technician ne a asibitin nasu. Bai taba dora mata nauyin da ba nata ba na kula da gida ko 'ya'yansu guda uku. Tana da wadatar da za iya taimakawa mahaifiyarta musamman ta harkar lafiyarta amma kullum cikin kiran babu take. Don ma kada Innayo ta dinga tambayarta kudi sai wata ya raba ta kan leko gidan. Tana zama bata da zance sai na bukatunta wadanda kudin hannunta ba sa su isa ta biya ba. Ita kuma Maimuna lokacin da Allah ya kawo mijin rimi-rimi ya amince za ta cigaba da karatun da take a Legal. Sai dai anayin aure ko wata biyu ba a rufa ba zance ya juye. Innayo tace indai don kudin ne zata cigaba da daukan nauyin 'yarta. Yace yaji ya amince dama kudin ne baya so ya biya. To kuma sai mahaifiyar sa ta ce bata yarda ba ko dai tayi zaman aure ko ta fita taje tayi karatun ta. Nan kuwa yace to sai dai ra ajiye karatun. Maimuna shaukin soyayya na dawainiya da ita a lokacin tuni ta amince da bukatarsa. Innayo taji ciwon wannan abun amma ba yadda zatayi haka ta hakura. Haihuwa biyu duk ta tsufa ta lalace. Babu cima mai kyau ga tashin hankalin uwar miji da talauci. A hankali nauyinta ya sake komawa wuyan Innayo kuma bata yi mata komai da kyashi domin 'yarta ce. Salima kuwa watarana suna zaune kwatsam Alh Rabiu yazo wai yayi mata miji kuma aure nan da nan zaayi ba bata lokaci. Nan fa innayo da Alh Rabiu suka hau suka duro ta dage tana so yar ta tayi karatu ko don gudun abin da ya sami Maimuna amma yaki yarda sam. Karshe dai haka wannan ma ta hakura akai auren. Ashe basu sani ba auren biyan bashi yayi mata ga mijin mashayi ne na bugawa a jarida. Yau duka gobe tsangwama haka dai itama Salima rayuwar ta kare babu wani cigaba. Banda lalurar ido tsabar damuwa da halin da 'ya'yanta suke ciki sai hawan jini ya sarketa. Innayo bata fasa komai ba. Tashi karfe hudu na asuba har jikinta ya saba. Kwata-kwata bata san hutu ba. Zara da Hasiya da suka rage take take fatan ko za a samu wani abu na cigaba a rayuwarsu. To matsalar Zara karya ce sama da kasa take dawainiya da ita. A dole ita sai tayi rayuwar da za'a ce ita 'yar wani ce, ita dai kar a rainata. Hasiya kuwa ba sawa ba fitarwa. Yadda bata son rigima haka take kin halayyar Uwani da Zara. Maimuna da Salima kuwa tausayi suke bata. Zara ta gama sakandire da wata shida aka kawo kudin aurenta. Lokacin Hasiya tana aji shida ita kuma ita ma ta kusa gamawa. Saurayin nata da ne ga guda cikin mashahuran 'yan kasuwar da Kano take ji dasu a Singa. Alh. Rabi'u kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha. Yadda yake jindadi da mijin A'i haka yake fata daga mijin Zara. Asabe kuwa hadiyar zuciya ne kawai bata yi ba. Hankalinta in ya yi dubu ya tashi wurin nemarwa Ummakati miji na wuce sa'a. An sanya biki wata biyu masu zuwa. Innayo ce zaune a daki da Uwani da Hasiya ga kayan amfanin gida irin su kuka da daddawa da ta siyo tana rabawa gida uku. Uwani dake kashingide akan gadonta ta dago kai. "Ki dan kara min kukar Innayo kin san Usman bai ki kullum na kada masa ba." Murmushi Innayo tayi ta debi cokali bibbiyu a sauran kaso biyun ta kara a daya. A zahiri ita ba da Uwani take rabon ba. Ta san tana da kudin saye. Nata ne da Maimuna da Salima. Ba yadda ta iya ta hakura da natan. 'Yan kudaden hannunta duk sun kare wurin siyayyar auren Zara. Wadannan din ma cikin nata ne ta dibar musu. Dan gyaran murya tayi tana juyayin samun biyan bukata a wurin Uwanin. "Uhmmn. Dama abin da yasa nace ki zo saboda maganar Zara ne." Tashi tayi zaune tana hade fuska "Wallahi indai harkar kudi ce sai dai kiyi hakuri. Na fada miki adashi nake yi kuma sai nan da wata hudu zan dauka." "Yanzu ba za ki iya rokon arziki a baki daukar watan nan ba? Kinga bikin ya matso ko bamu sayi kujeru ba." Tashi Uwani tayi. Da ta san dalilin kiran ma da ta kirkiri dalilin kin zuwa. "Ki nema a wurin Baba ko a rokesu a daga bikin. Ni wallahi yanzu dubu ashirin ma ba zance za a samu a jikina ba. Gobe nake shirin ranto talatin a asibiti. Sai na raba muku ke da Baba kuyi hidimar bikin." Muryar Innayo kamar za ta yi kuka ta ce "iya gudunwamarki kenan a bikin kanwarki? Uwani idan baki tausaya min ba waye kuma zai min? Sauran 'yan uwanki duka abin a tausayawa ne a gidajen mazajensu amma ban taba cewa ki kawo wani abu na basu ba. Na zata kina da hankalin duba yanayin da suke ciki ki ..." Yanzu taji magana. Ta rasa dalilin da yasa Innayo ta kawo ido ta saka akan albashinta. Lokacin da take hana idanunta bacci tana kwana karatu me Maimunan da Saliman suke yi? Basu tsaya sun gina rayuwarsu ba kowace tayi aure. Sai kuma ake tunanin ita za ta dauki dawainiyarsu saboda bata san zafin nema ba. Muryarta a sama ta soma magana. "To ni dai ba zan dauki nauyin kowacce katuwa ba wallahi. Dubu talatin kuma ita kadai zan iya fitarwa saboda nima bani dashi. In don nace ki kara min kuka ne to ki bar abarki. Haba! Ba damar nazo gidan nan kin dinga tasowa da bukatun kudi..." Tasss...taji saukar gigitaccen mari. Da kyar ta bude idonta da ya kanne saboda zafin shigar marin tana neman wanda ya yi mata wannan aikin. Hasiya da Innayo ne a gabanta. Kalaman autar tasu ne ya nuna mata hannun waye ya sauka a kuncinta. "Idan su Yaya A'i sun wulakanta rikon da Innayo tayi musu basa dubanta yanzu ke kina da wata uwar ne bayan ita?" Cewar Hasiya lokaci guda tana fashewa da kuka. Muryarta ta dinga yin sama-sama saboda taki yin shiru. "Kullum ki ka zo gidannan kin dinga kiran babu kenan saboda kada ki taimakawa uwar da ta biya miki kudin makaranta. To Allah Ya hadaki da babun nan da kike kira don girman..." "Hasiya kama gabanki. Fita kada ranki ya baci. A gidan wa ki ka koyi rashin kunya haka?" Innayo ta furta da kwalla a idonta. Kwallar ta sake tunzara zuciyar Hasiya. Rainin wayon yayarta ta ya kaita makura. Idan bata amayar da ranta ba tana jin zuciyarta sai ta buga. "Innayo ki barni don Allah. Dubi dakinki don Allah." Ta nuna kowacce kusurwa da hannunta "Dakin da Yaya Uwani ta mayar kemis a gidanta fanka biyu ce da ta bango da ta tsaye. Ke kuwa fankar tsayen ma da kyar take juyawa. Nima tashi nayi na ganta a gidan nan." Bakincikin marin da Hasiya tayi mata yasa ta kasa cewa komai. Duk abin da ta fada gaske ne to amma gaskiya tana tsoron talauci. Idan tana bada kudin sai su koma matsayin da ta tashi a ciki. Innayo ce ta kama hannun Hasiya ta fita da ita daga dakin. Tana juyowa taga Uwani ta saba jakarta tana gyara mayafi. "Uwani." Ta kira ta a sanyaye. Banda kudin bikin Zara da take nema harda na zuwa asibiti. Kwanakin nan sam bata jindadin jikinta daurewa kawai take yi. Dan abin da take dashi idan ta taba a zuwa asibiti dame za ta aurar da Zara? Danginta suna kauye a haka ta fi da yawa rufin asiri. Shi kuwa Alh. Rabi'u bakin hali ya raba shi da nasa sai jefi-jefi. "Innayo sai naci mutumcin Hasiya. Dani take zancen. Kar ma ki bani hakuri don wallahi ba zan hakura ba." "Zan yi mata fada. Yanzu dai ki taimaka min da ko dubu biyu ne in je asibiti gobe. Bani da kudi a hannu duk nayi sayayya dasu." 'Innayo ba dai naci ba' Uwani ta fada a zuciyarta. A ganinta duk abubuwan da take yi sun isa su sa tayi fushi ta daina tambayarta komai. Ba dole su A'i suka gujeta ba. Kila su ma roko ta damesu dashi. Dubu daya da dari biyar ta bata tasa kai ta fita. "Nima ba kudin gareni ba." Hasiya tayi kukan bakinciki a ranar. Bata ga me Innayo tayi da ya cancanci wannan wulakancin daga 'yar cikinta ba. Washegari ta rakata asibiti. Hawan jininta ne ya tashi tana daf da samun stroke idan bata huta ba. Sannan likita ya bada shawarar ta rage damuwa daga ranta. Da ta fadawa su Maimuna babu abin da suka iya zuwa dashi dubiya sai sannu da fatar baki. Innayo din ce ma ta ce ta basu kullin kayan da ta ajiye musu. Zara kuwa bata zama ana ta shirin biki da kawayenta 'yan karya. Da daddare ne ma da ta dawo daga rabon kati ta saka Innayo a gaba da kuka. "Wancan gadon na soro ne gadon da ki ka saya? Dangin Unais raina ni zasu yi. Kuma har yau ban ga kujerun ba. Idan auren ba zai yiwu ba kawai zan ce masa na fasa." Tana jin motsin Hasiya tayi shiru. Tunda Uwani ta dawo ta fadawa Alh. Rabi'u marin da tayi mata itama take shakkarta. Shi kuwa har uwar daka ya kirata ya zazzageta tunda Uwani ta bashi dubu shabiyar tayi mutumci a idonsa. Da maganganun Zara Innayo ta kwana a ranta. Gari na wayewa taje gidan A'i. Tangamemen gida ne na zamani. A wani karamin falo aka ajiyeta har A'in ta sakko bayan kusan minti arba'in. "Innayo kece a gidan namu? Nima ina son zuwa kawo gudunmawata ta bikin Zara." Juyawa tayi ta koma sama. Bata dade ba ta dawo da leda mai baka da yalo ta bata. Godiya tayi tun kafin ta bude sannan ta fadi abin da ya kawota. "Don Allah rance nake so A'i. Kujeru zan sayawa kanwar taki da sauran kayayyakin da basu samu ba." Kallon tausayi ta bita dashi kamar gaske "banda abinki Innayo kiyi mata komai daidai karfinki mana. Kodayake naji ance dan masu kudi ne. Zara da rawar kai maimakon ta kawo tsaranta shi ne ta dauko wanda yafi karfinta." Daurewa tayi bata ce komai ba tunda nema take. Wai A'i ce take yi mata haka? Lallai duniya baka shaidar da ko da naka ne bare na wani. Ta sami bashin tayi ta murna ta karba ta tafi gandun albasa inda kafintoci ke kware basirarsu. Ta sayi kujeru aka biyota dasu hae gida. Zara na gani ta tabe baki alamun basu yi mata ba. Innayo sai ta shige daki kawai ta fashe da kuka. "Allah kar kasa 'ya'yana su maye gurbin mahaifinsu wurin wulakantani. Idan nayi kuskuren tarbiyarsu Allah Ka shirya min su. Ya Allah na yafe musu. Da wanda suka yi da wanda zasu yi a gaba." (Haka rayuwa ta kan zo wa bayin Allah. Sai mu wahala akan wani abu da tunanin samun jindadi a tare dashi nan gaba. Idan lokacin girbar dadin ya zo lokuta da dama sai mutum ya kare da shan mamaki. Babu abin da Innayo bata yiwa 'ya'yanta ba na kyautatawa amma har yanzu bata ga wani abin buga kirji game da cigaban da ta jima tana yi musu fata. Duk da su din jininta ne to amma kar mu manta jinin Alh. Rabi'u ne. Basu tashi sun ga mahaifiyarsu tana da kima ba. Wannan zai iya rage mata daraja a idanunsu. A wahale suka ganta kuma dabi'ar dan Adam ce gudun wahala da talauci. Sai mai hankali, hangen nesa, tuna baya da tsoron Allah ne yake jajircewa wurin sakawa iyaye musamman uwa da alkhairi.) Anyi bikin Zara ba yadda take so ba amma dai ta bar gidan kamar yadda ta jima tana buri. Sai jifa jifa take zuwa gidan nasu saboda tana kunyar a ce Innayo mahaifiyarta ce. Ga talauci ga rashin wayewa. Mijinta ko a jikinsa. Bata nuna masa tana ganin girman mahaifiyarta ba shi ma bai ga dalilin girmamata ba. Abu na karshe da ya karasa kashewa Innayo jiki ta fitar da rai daga samun saukin rayuwa shi ne auren Hasiya. Wata uku bayan bikin Zara aka aiko musu da mummunan labari. A'i tayi hatsari ta rasu. Shi kuma babban danta da suke tare ya sami rauni a kansa. Wannan labari ya gigita Innayo ya kusa zarar da Laraba mahaifiyar A'in. An sha koke-koke an hakura. Ranar da aka yi sadakar uku Innayo ta sayar da filin da shi kadai ya rage mata kadara ta biya bashin da A'i take binta na kudin kujerun Zara. Mijinta Hon. Habu ya ce ya yafe, idan ma adadinsu ya shiga gadon 'ya'yansu zai biya a madadinta. Kafin ta isa gida Laraba har ta je ta ce ta bata kudin. Ba musu ta dauko ta bata. Kafin ayi bakwai ashe Alh. Rabi'u yana can yana kulle-kullen yadda zai cigaba da ci daga jikin Hon. Habu. "Ga kanwarta Hasiya ba sai ta maye gurbinta ba. 'Ya'yanka suna bukatar uwa da za ta kula

Chapter 8 of 62