Share this page
kina tuna ni ko sau daya ne a rana.) Wani abu mai kama da ana yiwa mutum yawo a ciki taji ya tsirga mata a lokacin don dadi. Ita kadai ta dinga zuba murmushi tana kuma jin kunya kamar yana gabanta. Ashe sunansa Auwal ta fadawa kanta kamar da wani take. Sai da ya soma fitar da rai da samun amsa sannan tayi masa reply. (Ban san Auwal ba shi yasa bana tunaninsa) Da wurwuri ya sake turo mata wani (Amma dai kin san Abbati?) Kasa rubuta komai tayi tana dariya kasa-kasa. A bangaren Abbati shirunta sai ya dame shi. Shi fa kaifi daya ne baya son jan rai. Kiranta ya yi kai tsaye ta dauka da wayar da kusa tsinkewa. "Ya Farha baki san Abbati ba?" Yadda ya yi tambayar da damuwa yasa ta fasa cigaba da ja masa rai. "Na san shi." Ta rage murya sannan ta kara da cewa " Kuma ina tunaninsa kullum." Ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe idanu "To ai ni ne Auwal din. Suna na na gaskiya na fada miki." Bata san lokacin da tayi dariya ba har tana tunanin ko dan fari ne. Dariyar da ta dinga kurdawa ko ina a cikin Abbati tana saka shi daukar dumi. Tun yanzu yake fatan idan ya sami Farha Allah Ya bashi ita har aljanna. Da wata irin murya mai dadin amo da tsayuwa a rai ya ce "Ina sonki Ya Farha" Yadda ya dauke numfashi yana jiran amsarta haka ta dauke nata saboda girman lafazinsa. Ta dade kwarai da cire rai da jin wannan kalmar a kanta. "Kin barni da faduwar gaba." "Nima nawa gaban faduwa yake" ta bashi amsa da dukkan gaskiyarta. "To yanzu ya za ayi kenan? Da sai nan da kwana uku zan zo daukar motata amma na fasa. Tunda gabanki na faduwa gobe zan zo in sha Allahu." Kunya ta ji ta sake yin shiru har sai da ya tambayeta me yasa bata son yi masa magana sosai. Bai san hira irin wannan gabadaya bakon abu bane a gareta. Kawar da zancensa tayi ta sako wata hirar daban. "Yaya su Baaba? Don Allah ka ce ina gaisheta." Sai da ta yi dariya ya ce "ba damuwa don kin bagarar da zancen. Gobe kinga sai ki bani amsa muna kallon juna. Kinga ni na huta tunda dama ba iya fada zan yi a gabanki ba don nima ina jin kunya. Baaba kuma tana lafiya. Zuciyata tana ninka son mai mutunta Baaba. Ki gaishe min da Maminmu." Katse wayar ya yi ya barta da murmushin da masana zasu gane na sabon shigar soyayya ne. Sai dai nishadin da take ciki bai dade ba ya rugurguje. Alh. Tahir ne ya kirata sau biyu bata daga ba sai ya kira Mami Khadija ya fada mata sako ta bata. Suna gama magana kuwa ta kirata ta sanar da ita. "Abbanku ya ce ki same shi a falonsa goma na safe." Kuka ta soma tun kafin ta gama jin sakon. "Mami don Allah..." Daurewa Mami Khadija tayi domin ta san abin da zata fada mata shi ne daidai. "Wasan buyar da kike dashi ya isa haka. Kije kiji kiran me yake miki" "Mami?" ta furta da kyar saboda kukan da yaci karfinta. "Sai da safe Farha." Ita ma kukan ne ya taho mata shi yasa ta katse kiran. A daren Farha ta hada kayanta a akwati. Gari na wayewa ta karasa shiryawa. Ita ta tashi Mami Khadija da ta shiga dakinta. "Gidan Mama zan tafi na zauna har a gama bikin Kawu." Ta san za a rina dama. Farha can be stubborn idan abu bai yi mata ba. "Da izinin wa za ki tafi?" Zubewa tayi a gaban gadon ta marairaice mata. "Don Allah ki barni in tafi Mami. Idan naji zuciyata za ta iya daurewa inyi magana da Abba zan dawo." Tayi maganar kwalla na zubo mata. "Au...bama ki da niyar dawowa in an gama bikin kenan?" "Please Mami" "Naji. Allah Ya tsare. Kada dai ki manta duk dadi ko rashinsa ba a canjawa tuwo suna." Kai ta gyada ta mike. Har ta fita bata bar fassara kalaman Mami na karshe ba. Jinjinawa mahaifiyarta ta tayi domin ta fahimci ko da bata fadi me ta gani ba ita ma ta san ko meye. Ita kam bata son fasiki kuma bata jin zuciyarta tana da kwarin daukar cin amanar namiji. Kofa a bude take yayi aure amma banda yawon bin matan titi. Bata fatan abin da zai zo ya gifta har ya sata hakurin zama da mazinaci! UKU DUWATSUN... *** Da mukulli Jiddo ta rufe kofarta bayan mai yi mata aiki ta fita ta shige daki. Missed calls din Sarauniya sun fi goma. Sai sakwanni wadanda tun bata bude ba ta san kwanan zancen. Surutu ne da zagi duk akan rashin hadasu da Danladi. Kayanta ta cire bayan ta rurrufe tagogi ta haye gado ta dauki hotuna kala kala wanda muninsu yafi na farko. Ta dai tabbatar bata hada da fuskarta ba. Wayar Danladi ta kira yana gani bai dauka ba sai kawai ta tura hotunan tare da sakon magiyar ya amsa gayyatarta. Ta kara da fada masa nemansa da Sarauniya take yi. (Ta bani dubu hamsin na baka kayi kudin mota zuwa Abuja. Ladan aikinka zai iya fidda kai daga talauci. Ni da kai duka zamu karo da abin da za ta biya. Sai naji shawarar da ka yanke.) A kwance yake ya gama karewa hotunan kallo ya karanta sakon nata. A gigice ya tashi har ya barar da dan kofin silba din da matarsa ta ajiye masa ruwa a ciki. Dubu hamsin kuma kudin mota kadai?! Hannunsa kaikayi ya kama yi yana son kiranta amma wata zuciyar ta hana. Wai kada ya nuna mata shi din kwadayayye ne. Jiddo kuwa da ta tabbata yaga hotunan sai ta kira shi. Da irin salonsu na gogaggun mata take masa magana. "Danladi mata aka sani da jan aji amma sai gashi lokaci guda kana ta dagula min lissafi. Shin ko dai abin da na turo bai burgeka bane?" Sai da ya hadiyi yawu da kyar saboda muryar ta tuna masa irin hotunan sannan ya dan yamutsa fuska ya amsa mata kamar ba ya so. "No ba haka bane. Kawai ina busy ne." Jiddo ta murmusa. Dan hannu ne babu tantama. Kyale shi za tayi ya ja ajin sannan ta fadi bukatunta. Danladi ya gama kwanakwanarsa ya mika wuya. Ba wai son zuwa ne baya yi ba tun farko dama. Kawai dai yana tsoro ne ganin cewa matar manya ce. In bai manta ba, motar da ya gyara musu da kayan jikinta babu alamar talauci ko kadan a tare da ita. "Ku sa min rana amma banda satin nan." "An gama" cewar Jiddo cike da nishadi. Jan shi ta dinga yi da hira har ya dan saki jiki. Suna gama wayar hankalinsa ya karkata kan Ayaah. Ita ce irin macen da ya dade yana muradi. Irinsu Jiddo sai dai aje aci kudi kawai a dawo. Ayaah kuwa su ake kashewa kudin idan akwai su. Dakin matarsa Raiha ya shiga tana zaune da yaransu biyu tana basu kunu. Aikin sa yana kawo masa rufin asiri daidai gwargwado amma saboda karya da yawon bin 'yan mata ya kasa wadata gidansa. Yau tashi suka yi babu ko sisi a jikinsa sai makota ta shiga ta karbo bashin kunu. Shi ne suka sha da safe, rana da kuma yammacin yanzu da ya gama sanyi kalau. "Wani abin kake so ne?" Ta tambaye shi a ladabce ganin ya tsaya a bakin kofa yana ta binsu da kallo. Tabe baki ya yi kafin ya ce "bani darin da na baki dazu zan dan fita." Danne zuciyarta tayi ta ciro darin daga cikin riga ta mika masa. Bai ce mata komai ba ya juya abinsa. Ludayin da take bawa yaran kunu taji ya mata nauyi ya sabule daga hannunta saboda bakinciki. Dan kudin da ya bata take cancanawa za ta saya musu awara suci mai dan nauyi da daddare shi ne ya karbe. Kamar kiftawar ido da bude shi don ko gyara zama bata yi ba ya sake shigowa ya wuce dakinsa. Katin naira dari ya siyo ya saka a wayar ya dannawa Ayaah kira. Yaci alwashin yau zai fara dorata akan manufarsa. Ba zai bar gidansu ba sai ya rungumeta. * Wanki take ta kunna rediyo tana sauraron wani shiri da akeyi a tashar Freedom mai suna Sabon Shafi. Shirin yana burgeta matuka domin ana hira ne da mata da suka yi fice a fannoni daban daban. Burinta wata rana ace za ayi hira da Hajara Habu Danmalam, fitacciyar.... Tunaninta ne ya katse ba tare da ta gama tsara matakin da take son kaiwa a gaba ba sakamakon shigowar waya. Daga kai tayi kan dan dakalin da suke ajiye guga inda wayar take taga sunan mai kiran. Da sauri ta goge hannunwanta da zanin jikinta ta amsa kafin ta katse. Sai da tace hello sau hudu Danladi bai amsa ba. Yana jin ciwon tafiyar kudinsa a banza amma dole ya hakura idan yana son cin wannan yakin. Wani jan numfashi ya yi kamar wanda ya yi muguwar gajiya sannan ya kira sunanta da kwantacciyar murya. "Ayaahhhh. Me na yiwa mata suke guduna haka?" Daburcewa tayi da salon maganarsa. A lokaci guda kuma kalamansa suna tayar mata da hankali. Duk yadda akayi matarsa ta kuma guma masa wani abin. "Mata har nawa ke gudunka?" "Wadda kika sani dai ta gidana, sai kuma ke da na daukeki wata babbar jigon rayuwata. Kwana nawa baki ji daga gareni ba amma ko dan tes dinnan ya gagara ki ji lafiyata." Kanta yayi gingirin kamar an dora farantin kwai tana tsoron ya fado ya fashe. Zuciyarta kuwa shawagi ta dinga yi mata a kirji saboda tsananin farinciki. Da tattausan lafazi ta soma bashi hakuri. Da ya san katin yana daf da karewa sai ya katseta. "Na san dai ina takura miki da matsalolina amma don Allah I am sorry. Bana son Mom ta sani. Ke kadai zuciyata ta amince ta dinga fallasawa sirrinta. Idan kina gida zan zo da anyi magariba." Cikinsa a take ya bada wani sauti kamar yana rokon shi ma a kaishi gareta ya sami abinci. Shu'umin murmushi ya yi ya dan daga murya, "Dalin, kin dafa min indomie din ne?" Ya dan yi jim kadan "naji. Allah Ya baki hakuri. Idan na fita zan nema. Kina son wani abu ne na taho miki dashi?" Ana fara warning na yanzu kudin zai kare ya ce da Ayaah "sorry na barki ina magana. Idan nazo zan kiraki." Mace mai tunani za ta fassara hirarsu Ayaah da cewa Danladi (Dani) ya cancanci a tausaya masa saboda rashin samun kulawar iyalinsa. Da kudinsa da komai amma abinci ma sai dai ya saya. Mai zurfin tunani kuwa za ta tausaya masa da farko. Idan an gama wayar sai ta koma tunanin dalilinsa na fada mata laifin matarsa. Daga nan za ta gane akwai wata a kasa. Sauran binciken zai nuna mata shi abin yarda ne ko akasin haka. Wankin da Ayaah bata gama ba kenan. Inda Hasiya take tare da 'yan lallenta taje ta durkusa. Sosai alakarsu tana ta gyaruwa yanzu sai dai duk da haka aure Ayaah take so. Ita dai ta bar gidan ta huta da zugar su Anti Fati kannen mamanta da kuma mitar yayyenta. Sannan ta kula baban nasu ba iya biya mata zai yi ta cigaba da karatu yadda take so ba. "Anti me za a dora ne? Naga yamma tayi sosai." Hasiya tayi murmushin jindadi. Canjin da Ayaah tayi yana faranta zuciyarta sosai. "Kin manta yau Ummita ce a kitchen? Kice tayi mana jallof din shinkafa." Ta zaro dari uku ta mika mata ta ce a siyo kifi a saka a ciki. Ayaah ta karba harda godiya ta shiga ciki. Mayafi ta dauko ta tafi ta siyo kifin ko Ummita bata nema ba. Kifin dari biyu da hamsin ta siyo sai alayyauhu da albasa mai lawashi na hamsin. Sauran kayan bukatar duka akwai a gidan. Albasa ma suna da ita sai da mai lawashin take bukata. Wankesu tayi ta yanka tare da alayyahun ta sake wankewa ta ajiye ya tsane. Ta debo wake yadda take bukata ta dora. Sannan tayi jajjagen kayan miya da citta da tafarnuwa ta soya ta tsayar da ruwan abinci. Kamshin ne yasa Ummita lekowa daga daki. Tun dazu take son fitowa dora girkin ciwon kai ya hana. Ta dauka Murja ce ta gama kitso ta zo taimaka mata sai ganin Ayaah tayi. Wani dadi ya shigeta na canjin kanwar tasu tayi mata gofiya ta koma ciki. Da ruwa ya tafasa Ayaah ta zuba shinkafa tare da waken da ya soma dahuwa su dahu tare. Sai da ta kusa gama turara bayan ta rage wutar ta zuba lawashin da alayyahu tare da kifin da ta ciccirewa kaya. Yau ma kafin kowa ya farga ta dibarwa Dani sannan ta kwashe sauran. Tayi sa'ar gama komai kafin a fara kiran sallah. Sai ta fake da alwala ta samu ta wanke fuska taje tayi kwaskwarima. * Honorable yaga ranar taimakawa na kasa a lokacin da bai zata ba. Da suka bar ma'aikatar su Alh. Bala, gidan Minista Abdulkarim suka wuce. Tamfatsetsen gida wanda ko lokacin da yake ganiyar arzikinsa bai taba tunanin mallakar irinsa ba. An kawo masa abinci mai rai da lafiya ga kuma girmamawa ta musamman daga maigidan. Matarsa tana Abuja da yara shi kadai ya zo ganin iyayensa da magana da Alh. Bala. Wannan yasa masu hidimar gidan su ma suka zage damtse anata kai kawo. "Naga kamar umarninka kadai suke bi. Don Allah ka ce kada ta zubawa wallahi na koshi." Furucin Honorable kenan bayan duk abin da yaci kuma aka sake kawo masa farfafesun jelar saniya. Abdulkarim ya dagawa mai aikin hannu da murmushi a fuskarsa sannan ta fasa zubawa. Kallon Honorable ya yi yana mai kara jin tsoron Allah ta yadda rayuwa take jujjuyawa ga bayi. "Gani nayi duk ka rame. Don Allah ka sake cin wani abu." Honorable ya tuntsire da dariya "banda abinka kuma sai aka ce a cin abinci guda zan yi kiba?" Dariya suka yi tare suka taba hira sannan Honorable ya tashi zai tafi. Abdulkarim ya ce bai san zance ba. Yana son jin me ya faru dashi tsayin lokaci har rayuwa ta koma haka. Tiryan tiryan ya labarta masa komai. Ba kuma don maula ba sai don dalili guda wanda ya fada masa kamar haka, "Duniya bata da tabbas Abdulkarim. Ba komai ne yake zama tabbatacce ba a rayuwa. Saboda haka ka daure ka rike gaskiya a duk inda ka sami kanka. Idan duniya ta ciyar da kai gaba fiye da nan sai ka dinga kallon kasa kana kara godiya ga Allah. Bana maka fata amma ko da za ta kawoka inda ta ajiyeni to kada ka karaya da samun rahama. Allah ba Ya dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Ba zan boye maka ba da farko na shiga kunci saboda rashin sabo da babu ga Abbas a kwance. Da ilimina na fara hasashen ko auren Hasiya ne ya jaza min talauci. Sai gashi ashe ita za ta rike gidana da 'ya'yana. Duk zafin talauci idan Allah Ya baka mace ta gari to tabbas Ya kwashe maka radadinsa." "Zan so ganinta. Muje da kaina zan kai ka gida." Cewar Abdulkarim, zantukan suna shigarsa da kyau. Honorable ya dage baya so. Shi ma Abdulkarim ya dage sai yaje. Daga nan ya tashi ya bi wata hanya zuwa bangarensa. Da envelop ya dawo ya mika masa. Allah Sarki! Yawun bakinsa ya kafe. Idanuwansa suka kada suka yi ja....a wani shudadden lokaci shi ne yake bawa Abdulkarim. Yau duniya ta nuna masa cewa tables can always turn. (Ya Allah Ka rabamu da talauci da karayar arziki. Duk abin da zai taso mana na kudi Allah Kasa mu fi karfinsa.) "Duk ni kadai? Basu yi yawa ba?" Ya ce da murya tana rawa. Raba kudin ya yi gida biyu ya mika masa rabi. Abdulkarim sai yaji wani abu mai nauyi a zuciyarsa. Honorable Habu yafi karfin wulakanci a wurinsa. Laifin kansa ya gani da ya yi sakaci da zumunci har ta kai bai san mawuyacin halin da tsohon ubangidansa yake ciki ba. Ace har ya kai matsayin da dubu dari za ta kawo masa kwalla a ido. "Kada kayi min haka Honorable. Ban kyauta ba a baya na sani amma ka dauka Allah ne bai shirya haduwarmu ba sai a yanzu da muke sa ran alkhairi ya biyo bayanta." "Haka ne. Nagode.." Godiyar ma katseta Abdulkarim ya yi suka fita zuwa mota tare. Wannan karon daga su biyu a bayan mota sai direba. A hanya ne yake tambayarsa irin sana'ar da yake son yi. Lokaci ya ja babu batun komawa siyasa. Idan an manta da mutum sai ya zo da kwakkwara kuma kyakkyawan shiri tafiyar take sake armashi. In ba haka ba kudinsa kawai zai yi asara. "Zan yi shawara da Hasiya sai na fada maka" Ya ce da murmushi a fuskarsa. Abdulkarim ya kama dariya sannan ya ce "Allah Yasa bata aurar da duka 'ya'yanta ba ta bani guda. Don naga alama idan na auri rainonta kila sai nayi shugaban kasa." Honorable ya girgiza kai "abin kuma harda zolaya?" Abdulkarim bai ce komai ba. Ba kuma zai ce ba har sai yaje gidan ya ga 'yan matan da ya sani a baya tun suna yara. Kudurcewa ya yi a zuciyarsa indai ba rashin tarbiya wanda baya tsammani ya gani ba ko su suce basu son aurensa ba zai nemi guda. *** Mardiyya da Sauda ne tare da Suhaib da Lilu tsaye a jikin motar Abbati. Sun rako su bakin mota shi da Munzali bayan sun shiga sun gaisa da Mami Khadija. Mama Nasima bata nan kuma Mardiyya sai addu'a take yi su yi su bar gidan kafin ta shigo. Sau biyun da ta zubar da kimarta a gaban Munzali bata yi a gaban yayyenta ba. Ba kuma ta son a fara daga yau. Hirar motoci suke yi wadda Lilu da Munzali ne karfinta. Lilu ya shafa motar yana binta da kallon bege "Ni dai ba don yau za ku tafi ba ai da na dana ko zuwa karshen layinmu ne in kashe arna." Keyarsa Suhaib ya kwade ya kuma ce idan bai kama kansa ba sai ya fadawa Mami. Mardiyya da Sauda zasu yi dariya ya hade rai zai yi kaza huce kan dami. "Wai me ma ya fito daku ne? Wurinku suka zo? Ku koma ciki." Munzali ne ya shigar musu domin Abbati kamar baya wurin. Hankalinsa yana kan hanya yana dakon ganin ta ina Farha za ta bullo. Da sauri Munzali ya ce "Ya za ka korar min kanne?" Dan nesa kadan da inda suke tsaye ya nuna da hannu yana mai cewa "In ganki mana Diamond girl." Karashen maganar ya yi ne idanunsa a cikin na Mardiyya. Kawar da kai tayi da sauri gabanta na wata irin faduwa ta daban. Bata san yadda akayi yau take jin Munzali a ranta haka ba. Tun dazu take satar kallonsa sai ta ga shi ma ita yake kallo. Juyawa tayi za ta gudu saboda kunya Sauda ta rike mata hannu. Shi kuma gogan ya basar kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba. Abbati ma dake son tambayarsu game da Farha amma ya kasa sai da yaji kunyar. Wato duk yanzu halinsu yake fitowa game da mata da suka hadu da wadanda suke so. Suhaib ma dai daskarewa ya yi don kusan yafi kanwar tasa jin kunya. Gyaran murya ya dinga yi ba kakkautawa don ya kasa magana. Lilu kuma ya dinga kikkifta idanu na shakiyanci sannan ya ce, "Diamond dai da na sani mai shegen tsadar nan ka kira Mardiyya?" Hannu ya sakalo a kafadarta ya tako kusa da Munzali dake ta murmushi ya tsaya da ita a gefensa. Hannuwa ya hada kamar mai shirin daukar hoto yana aunosu ta cikin zagayen da yatsunsa suka bayar. Ya dawo kunnenta yayi magana kamar rada amma kowa na ji "Baby Sis kin matso mana class wallahi." Ya koma ga Munzali " Kai ma Alh. Munzali ka more. Hummm don ma kada ka ce yabon kai da sai in ce duk 'yan matan Kaduna babu kamar na gidanmu." Hannun Mardiyya ya fara kamawa suka ti musabaha sannan ya saki ya koma kan na Munzali yana faman murmushi gami da nanata kalmar "congratulations." Suhaib ji ya yi kamar ya daga shi a kafada su bar wurin. Lilu ba ya jin magana ya ce a ransa kafin kuma a zahiri ya biyo shi. Zillewa Lilu ya yi bai bari ya kama shi ba ana ta dariya. "Baka da kunya ko kadan." Suhaib ya furta yana fuskantar bangaren Abbati. Nauyin Munzali ne ya kama shi saboda a gabansu yake yiwa Mardiyya wani irin kallo. Gashi sun girme shi sosai balle ya yi irin jan idon nan na yayan budurwa. Abbati kafadar Munzali ya ture da tasa har sai da yasa shi rankwafawa yana mita. "Munzalin ma ai ba kunyar gare shi ba da ya yi mata magana a gabanmu." Daure fuska Munzali ya yi cikin wasa yana hadawa da hararar Abbati. "Ai dama ba ayi maka gwaninta. Sharar fage nayi maka don duk su watse kafin ta fito." "Wa?" Lilu da Suhaib suka hada baki wurin tambaya. "Ya Farha" Sauda da Mardiyya suka basu amsa a tare. Suhaib bai san lokacin da wani irin murmushi mai cike da tsantsar annashuwa ya bayyana akan fuskarsa ba. Farha ce yau da kunnuwansa yaji ance namiji yana jiranta? Ganin murnar na neman yi masa yawa kuma bashi da tabbacin me yake faruwa sai ya ce, "Yanzu duka nan dama zance ku ka zo ba daukar mota ba?" Sauda da Lilu har ma da Munzali sai dariya. "Diamond girl kanwata ce kuma abokiyar shawara ko?" Munzali ya yi magana yana kannewa Mardiyya ido sannan ya dora da cewa "wasu ne dai har a cikin bacci za ka ji suna kiran Ya..." Bakinsa Abbati ya rufe da hannu su Lilu aka sami nayi sai dariyarsu suke. Munzali na kokarin kwatar kansa Abbati kuma yana faman yi masa alkawura akan idan ya kama bakinsa zai cika masa su. "Zan tuka motar har Kano!" Ya fadi abin da ya san zai yiwa Munzali dadi. A take Munzali ya daina kokarin janye hannun Abbatin ya nutsu. Yana sakinsa yasa dariya. Da gaske wautar Abbati bata wani buya lokuta da dama. "Riba biyu kenan. Kaga dai kowa ya fahimci menene baka son na fada. Alkawari kuma dole ka cika tunda ban fada da bakina ba" Mukullin ya dorawa Abbati a tafin hannu ya yafito Mardiyya da hannu. "Kina ta sani dibar kunyar Ya Suhaib kuma kin ki zuwa." * Gate din gidan aka wangale direban Alh. Tahir ya shigo ciki. Wurin ajiye nasa motocin ya dan yi nisa da inda yake hango 'ya'yansa da wasu baki biyu suna dariya. Motar da ya gani a kusa dasu kuma a bude ce tasa ya gane su waye. Mami Khadija bata tauye masa hakkinsa na maigida ba, ta sanar dashi game dasu tun ranar da suka ajiye motar a gidan. "Ga sirikinku nan" cewar Lilu yana yin gaba wurin mahaifinsa. Mardiyya da Sauda ma da sauri suka mara masa baya suna kiran "Abba" tamkar wanda ya yi tafiya. Kafin su karasa ya ware hannuwansa ya rungume kowacce a bari daya. Kirjinsa yaji ya takure saboda rashin Farha. Indai su uku suka zo tarbarsa to ita a bayansa take tsayawa ta riko wuyansa da hannuwanta biyu. Daga nan haka suke raka shi har daki. Wani lokacin ma su taya shi cin abinci. Lilu kuma idan yana gida shi yake dauko masa jaka da wayoyi. Yanzu ma ya dauko harda babbar rigar da ya bari a motar ya ratayota a kafada. Tun tashinsu Suhaib baya zuwa sai suke ganin kamar irin abin nan ne na babban yaya. Farha kuma tunda taga bidiyon nan take kirkirar abin da zai hanata fitowa idan ya dawo ko ya aika a kirata. Yanayin soyayyar uban da 'ya'yansa ya burge Munzali da Abbati matuka saboda basu tashi a haka ba. Gara ma Abbati ya san nasa mahaifin yana dan kokartawa amma babu zancen wata runguma ko sakin fuska makamanciyar wannan. Duk ranar da suka kwatanta haka karshenta Mal. Sa'idu sai ya tsire masa uba. Shi kuwa Munzali ina ma suka hadu balle a nuna an damu dashi. "Manyan yayye basa zuwa oyoyo?" Munzali ne ya tambayi Suhaib amma Abbati ne ya lura da yanayinsa a lokacin da yake bayarda amsa. "Mu ai mun girma an barwa kanana" Ba da niyar nuna musu komai ya yi ba amma bakidaya annurin fuskarsa ya bace. Irin kallon da ya yiwa mahaifin nasa ya kawar da kai Abbati ya kasa fassarawa. Kamar kallon tsana, kiyayya ko jin haushi. Kallo mai nuni da cewa

Chapter 29 of 62