Share this page
fitowa ba. Wasu magidantan ma basu riga sun koma muhallansu daga masallaci ba. Daga ganin yadda ya ajiye mota zaka san baya tare da nutsuwa. Kasheta kawai ya yi ba tare da ya rufe ba ya fita ya soma doka sallama a kofar gidan. Sallamar tasa ba karamin tsinka zuciyar Salima wadda ko tashi daga kan abin sallah bata yi ba tayi. A hanzarce ta mike suka kusa yin karo da Zara don ita ma ta gane muryar waye. Innayo kuwa iccen da take kokarin turawa a murhu tayi jifa dashi su ukun suka hado a kofar gidan da ko budeta ba ayi ba. "Karbo min mukulli a wurin Alhaji" Innayo ta furta muryarta tana fallasa fargabarta. Babu wani abu ko daya da zai kawo Salihi gidan nan da duku dukun asuba mai dadi. Tare da Alh. Rabi'u Salima ta dawo ya sako babbar riga yana murza idanu don ko sallah bai yi ba. Innayo ya kalla ta jingina da bango zuciyarta tana ta dukan kirjinta. "Aka ce Salihi ne yake sallama." "Ni ne Alhaji" ya amsa daga waje. Nasa hannun ma rawa ya kama yi sai Zara ce ta iya budewa Salihi ya shigo. Daga soron ya durkusa ya gaishesu sannan ya dan sosa keya. Salima da Zara sai suka bar wurin tunda kowa ya fahimci ba tashin hankalin da suke taraddadi bane. "Innayo ki bata hakuri tazo mu koma. Indai akan Ummule ne zan raba musu gida." Alh. Rabi'u ya kalli Innayo kallo na wulakanci sannan ya yi wata irin banzar dariya. "Hajiya Hauwa kenan. Kin nunawa kowa a gidan nan cewa kin fi kowa iya tarbiya da kyawun hali. Rannan har magana ki ka fada mana ni da Asabe akan 'ya'yanki. Sai gashi a tsukin abin da bai kai wata guda ba uku sun dawo gida. Allah Ya kyauta." Wucewarsa ya yi ko waige babu. Salihi kunya ta lullube shi yaji kamar ya nutse a wajen. Numfasawa Innayo tayi ta dube shi da murmushin da ya tsaya a fatar bakinta saboda bacin ran Uwani. "Salihi aure kayi?" Da sauri ya kalleta ba tare da ya iya boye mamakinsa ba. "Uwanin bata fada miki ba?" "Bata fada ba. Allah Ya sanya alkhairi. Sai dai kuma bata zo gidan nan ba." Kansa da ya yi niyar yin kasa dashi ya sake dagowa da sauri hankalinsa a mugun tashe. Jiya bata da aikin kwana. A ka'ida ma kafin la'asar take dawowa a ranaku irin wannan. Sai gashi har bayan isha babu duriyarta. Ya dinga kiran wayarta babu amsa, wanda kuma tana sane don kada ya katse mata jiran mai haihuwar da zata zame mata alkhairi. Abu kamar wasa har goman dare. Nan fa yaji ba zai iya bacci ba dole ya tafi asibitin nemanta. Nos din da suke da aikin kwana ranar suka ce masa ta tafi. Basu san tana nan ba tunda kafin zuwansu ma 'yan yamma sunyi nasu sun tashi. Sai da ya tafi ne daya daga cikinsu ta ganta take fada mata wani yazo nemanta. Haka nan taji a ranta maigidanta ne amma sai taki kiransa. Dole zai yi mata ta dawo gida ita kuwa bata cikin masu wasa da neman kudi. Haka ya koma gida ko runtsawa bai yi ba. Tunaninsa ya tafi akan ko tayi yaji ne saboda zuwan Ummule. Shi ne ya taho gidan da sassafe saboda baya son kowa ma hatta Ummule ta fuskanci da b'araka irin wannan tsakaninsu. "Ikon Allah" ya ce lokacin da yake jin wani irin tsoro a ransa "nima nayi jinkirin zuwan ne saboda tunanin ko ta karbarwa wata aikin kwana ne..." Innayo ba shiri tayi 'yar dariya tana cewa "banda abinka Salihi yaushe zaka dinga magana kamar yau ka san Uwani? Ita da ba wasu kawayen kirki ba ai da wuya ne ta karbarwa kowa aiki." Murmusawa ya yi shi ma. Wayar suka sake kira shiru dai ta ma daina shiga. Innayo daurewa kawai take yi amma gabanta sai faduwa yake yi. Salihi yana tafiya taje ta ballo magungunan hawan jininta tasha. Sun yi dashi zai koma asibitin ya sake dubawa. Idan an tabbatar masa ba a nan ta kwana ba zai kirata ya sanar da ita su san matakin dauka na gaba. Jiri ne ma ya yi mata sallama dole ta nemi wuri ta kwanta. * Wuraren bakwai da rabi Metiron Uwani ta fito daga dakin Haj. Salma wato matar CMD. Bakinta kamar gonar auduga domin Hajiyar tayi mata alkawarin idan aiki ya yi kyau tana da mutane a kalla shida wadanda zata hadata dasu. Duka kawayenta ne a cewarta da suka hayayyafa ana neman tayar da komad'a. Kudin aikin kowacce sun tsayar a dubu talatin. Nuna mata tayi duka matan manya ne sannan ai suna sayen kayan gyara na sama da wannan kudin sosai. Kai tsaye dakin da suke kwanciya ko ajiye kayansu ta nufa ta dauko wayarta. Tabe baki tayi ganin yawan kiran da Salihi ya dinga yi mata. Da yana sonta ba zai munafunceta ya karo aure ba ta ayyana a zuci. Kiransa tayi yana bakin danja zai karaso asibitin. "Naga missed calls ne" ta ce dashi da ya dauki wayar da yanayi na nuna kosawa da kiran nasa. Haushi ya kama shi ya daure ya boye fushinsa. "A ina kika kwana?" "Wace irin tambaya ce wannan bayan ka san ina zuwa aiki? To ina asibiti yanzu zan taho gida." "Sai kin dawo" Yau kam ya yi niyar nuna mata idan ma da gangan take wannan rashin hankalin to bashi da juriyar cigaba da dauka. Ace ko kadan bata ma san tayi masa ba daidai ba? Ta kwana a waje ba waya ba text sai amsa waya da gadara. Wayar Innayo ya kira ya fada mata sun yi magana sai ta roke shi da ya kawo Uwanin gidanta idan ta koma. Ita kuma Uwani wayar kafintanta ta kira cikin sa'a kuwa ya dauka. Kayan gado da kujerun da ta saya a wurinsa ta ce tana bukatar aje a kafa mata yau. Dama ta saya ne saboda tayi gyaran daki idan ta dawo daga Hajji. "Idan kun kusa titin Kofar Famfo ga nambar dana ku kira zai kaiku gidan." Bayan ta gama dashi ta kira mai labule shi ma ya dinka mata ne na iya falo da dakin baccinta. Karin yadi ta ce ya nema irin wadancan za ta zo bayan la'asar suje ya auna labulen sabon gidan a kara. Kafin nan ta san masu gado sun yi nisa a nasu aikin. A son ranta a gama komai cikin kwana biyu ta tare. Ginin da kuma wadannan kayayyakin da ta saya su suka cinye mata kudade. Dalilin da yasa ta shiga rudani kenan akan bacewarsa sarka da kudadenta na daki. Shawarar da ta yanke tun kwana biyu da bacewar kudin ce ta sake fado mata taji kwarin gwiwa. A jikin Salihi za ta fanshi kudinta komai runtsi. Da wadannan lissafe lissafen ta kama hanyar BUK oldsite inda Mubashir yake karatu. Da ta kira shi a waya tsorata ya yi da farko sai yaji ba zancen kudinta bane. Haduwa suka yi ta bashi mukullin gidan nata da bayanin abin da zai yi. Saboda halin rayuwa ta jima da nuna masa gidan tun yana fuloti. Daga nan gida ta nufa zuciyarta kamar an yayyafa ruwan sanyi. Tana tura gate din suka yi ido hudu da Salihi. "Fita zaka yi ne?" Tayi masa tambayar rainin wayo a zuwan ita har lokacin bata san tayi masa laifi ba. "Ke nake jira" Kallonsa tayi shekeke ta wuce ciki tana cewa "wai meye ne kake ta wani bata rai don na kwana a asibiti kamar wani bakon abu?" Dan tunani tayi ta dawo da baya ta ce "Idan saboda ban kiraka bane aiki ne ya min yawa. " Tsabar takaicinta bai bashi damar amsa mata ba. Daki ta wuce tayi wanka ta fito ta sha shayi a gurguje saboda kada Haj. Salma ta kirata bata gama ba. Tana tashi Salihi da Ummule suka fito daga dakinsa. Dakin nata ya bita shi kadai ya sameta tana sauko da akwatuna. "Lafiya?" "Lafiyar kenan" ta ce a yayinda ta dauko wata leda da 'yan mukullaye a ciki. Kwancewa tayi ta dauko wasu masu guda hurhudu ta cirar masa d'ai-d'ai ta damka masa. "Gasu nan mukullin gate ne da na kofar gida. Idan kayi kwanakin cin amanarka a nan sai ka dinga biyoni nawa muhallin ranar girkina." Mamakinta yana neman zarta bacin ransa. Sam ya kasa fahimtar inda ta dosa. "Ban fahimceki ba." Kugu ta rike da hannu daya bayan ta turo dauri gaban goshi. "Na gama gini na ina shirin saka 'yan haya kazo min da waccan abar wai kishiyata kuma kana sa rai na karbeta mu zauna a nan. Sai dai ina so ka sani cewa nafi karfin wannan wulakancin. In Allah Yaso ba zan kara sati ba a gidan nan zan koma nawa. Ba kuma zan yafe maka hakkina ko daya dake kanka ba." "Yanzu Uwani har gida ne dake ban sani ba?" Kwaikwayonsa tayi tana dariya "yanzu Salihi har aure ne da kai amma sai da matar tayi ciki na sani?" Ganin ya kasa cewa komai ta dora da cewa "da ne maza suke taka mata su zauna lafiya amma yanzu kan mage ya waye. Ko an fada maka kudin da nake nema ina yi ne don na mutu ku ci gado kai da 'ya'yanka?" "A tare lafiya Uwani" Daga yanayin fitar muryarsa ma ta gane ba da niyya ya yi mata adduar ba. Shi yasa ita ma ta amsa masa yadda zai ji haushi. "Amin dai. In ka sami sukuni sai ka kawo kudi ko ka sayo gadon da zaka sa a dakinka na can." Ya daina mamaki kamar yadda ya daina jin bacin rai. Hukuncinta sai ya zauna ya yi shawara da kwakwalwarsa sosai. Tafiya ya soma yi ta biyo bayansa da sauri. "Af...baka ji ba. Na ce akwai lissafin da zan maka na abubuwan da bakuwarka ta sace min." Dage gira taga ya yi sai ta hau bayanin cewa ranar da ya kawo Ummule gidan bata ga alamun bakunta a tare da ita ba. Shiyasa rake ganin ba ranar ya fara zuwa da ita ba. A takaice tana zargin ita tayi mata satar kudi da sarka. Katse zantukan da yake ganin matsalar kwalwalwa ce ta kawo mata su ya yi "Idan kin gama shiryawa ki zo muje Innayo tana nemanki." "Ina da uzuri zan biya idan na gama. Maganar sark...." "UWANI!" Hadiye sauran maganarta tayi ba shiri saboda karfin tsawar da ya daka mata. "Ki dauko mayafinki yanzun nan ina jiranki a mota." Bata gama dawowa daidai daga firgicin da ta shiga ba Mubashir ya kirata. Saurin dawo da nutsuwarta daga tunanin me ya sami Salihi tayi ta amsa wayar. "Umma gamu a bakin gate amma KNUPDA sun yi alamar a dakatar da aiki a gidan." Kwakwalwarta ce ta toshe na 'yan dakiku ta dinga maimaitawa Mubashir tambaya daya kamar mai bitar karatu. "Su waye kuma KNUPDA?" *** Farha bata dago da kanta ba har Abbati ya gama fada mata asalinsa da musabbabin zuwansa Kano. Labarin nasa ya sami sauyi ne a wurin silar arzikinsa inda ya ce mata kasuwanci suke yi amma yanzu sun balle daga jikin ubangidan nasu. Ya fada mata unguwar da suke ginin shopping mall da ire iren kayayyakin da suke son zubawa a ciki. A lokacin da yazo gabar da dole karya ce kadai za ta iya rufa masa asiri sai da ya hadiyi yawu mai daci. Da kansa yake jin tsana da kyamar dabi'ar da suka rayu cikinta. Yana son Farha so mai girma. Burinsa idan har ya mallaketa su zamewa juna tamkar warin takalma masu cike junansu. Yadda bashi da sirri da Munzali yana fatan kusancinsa da ita yafi wannan. Ba don komai ba kuwa face sanin cewa duk matsayin aboki matar aure ta fishi. Ita da mijinta aminai ne, masoya kuma ma'aurata. Kimanin minti uku da yin shirunsa amma har lokacin bata dago kanta ba. Tuni ya fara sarewa yana jin ya rasata kenan har abada. Magana mai girma irin wannan ya so ace a gida aka yita. Sai dai kuma tazo masa bagatatan ne da Farha tayi masa tambayar cikin hirarsu. "Don Allah ki dago kan ki ko sallamata zaki yi kada ki ce ba za ki sake iya kallon wannan almajirin dan kauyen wanda ko kwalin primary bai mallaka ba." Muryarsa ce tayi wani irin rauni mai fallasa ruhi da zuciya tana raurawa saboda tasirin soyayyarta a zuciyarsa. Bai gaji ba ya sake yi mata magana domin ya kagara ya san matsayinsa duk da ya gama sallamawa. "Ni ba tsaran aurenki bane Ya Farha, amma wallahi ina sonki da dukkan zuciyata." Farha bata san yadda zata kwatanta halin da Abbati ya jefa zuciyarta ba da kalamansa na karshe. Zuciyarta kara fadi take a cikin kirjinta tana kuma cikewa da wannan bawan Allah dake gabanta. Kosawa ya yi da rudanin da zuciyarsa ta shiga a sakamakon shirunta. "Ko in tafi?" Sai lokacin ta dago da taji ya dan tura kujerarsa baya alamun zai tashi. "Idan ka tafi kana tunanin tsaran auren nawa zai zo?" Ta ce a raunane. Kansa ya gyada da murmushin da ya tsaya a labbansa. Wurin kawai yake son ya bari kafin ya tsinci kansa a kan gwiwoyinsa yana rokon soyayya. Hawaye ne ya zubo mata ba shiri da ta hada ido dashi. Wannan wace irin zazzafar soyayyace suke yiwa juna haka? Da jikakkun idanunta ta dube shi. "Yazo ya aureni kana ji kana gani?" "Kin yarda idan yazo na kore shi ko waye?" Ita ma kai ta gyada masa amma nata murmushin mai sauti ne da jindadi. "Kina ganin su Mami zasu yarda ki aureni?" Ya tambayeta da sabuwar damuwa. "In sha Allahu babu matsala." Gyara zamansa ya yi gami da sakin ajiyar zuciya. Suka kalli juna suka yi murmushi a tare. Abbati ya kasa dauke ido daga kan kyakkyawar fuskarta. "Kin san me?" "Ina dai so in sani" ta lumshe idanunta sannan ta bashi amsa. "Na dan kware a Ingilishi." Farha bata san lokacin da ta kama dariya ba. "To ko mu kara ne?" "Me ya yi zafi daga wasa" Dariya suka yi tare a idanun Mami Khadija wadda ta zo wucewa can nesa dasu da kawayenta. Murmushi tayi ta dauke kanta kafin su farga cewa ta gansu. Fatanta Allah Ya cikawa 'ya'yanta farincikinsu. A zuciyar Abbati kuwa tunani yake kada Allah Ya kawo abin da zai raba shi da Farha. Shi kan shi tsoron girman soyayyar da yake yi mata yake yi. Idan ya rasa ta......baya son sanin halin da zai shiga idan ya rasa ta. * Can daya bangaren inda Munzali da Mardiyya suka zauna suma tasu hirar suke gwanin sha'awa. Hirar irin son da Abbati yake yiwa Farha yake mata tana bashi amsa da tabbacin yayarta ita ma tana kaunar aminin nasa. "Da gaske dai ba sona kike ba ko Mardiyya?" Ya furta daga sama suna tsakar magana. Gabanta ne ya fadi domin tun haduwarsu bai taba kiranta da sunanta ba. Kallon ma kamar tayi masa laifi haka ya tsareta da idanu duk sai ta daburce. "Me nayi don Allah?" Yanayin tsoratar da tayi sha'awa ya bashi. Yarintarta ta fito sosai sai kara shiga zuciyarsa take yi. "Tunda muka zauna nake yi miki zancen su Abbati amma ko ki bata rai ki ce a canja hira. Kamata ya yi nima naci ribar lokacin nan nayi miki hirar zuciyarta da yadda take kaunarki." Sunkuyar da kai tayi tana wasa da wayar hannunta. A haduwarsu da yawan wayarsu ta gane Munzali yana da son wasa da tsokana. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka sa take son sa. "Baki ce komai ba." Mardiyya sai ta zabi ta rama ita ma ta nuna masa wace ce ita. "To ni me zan ce? Ka kebe 'yar karamar yarinya kana yi mata zancen soyayya." Dariya sosai ya dinga yi yana bude baki ya rufe kafin ya ce "kin ce wani abu. Wato yarinya ko? Bari na tashi na nemi daidai dani a cikin taron nan" Hannuwanta ta daga kamar mai addu'a da ya mike ta soma cewa "Allahumma..." Tsayuwa ya yi yana kallonta cikin wani irin yanayi mai kashe jiki "karasa mana." Sai ta daure fuska ta cigaba "Allah Kasa duk wadda Daddyn Qibdiyya ya gani ya yiwa magana ta ce an kawo kudin aurenta." "Diamond girl" ya ce yana dariya sosai "I love you." A guje ta tashi ta bar wurin har tana tuntube da kujera akan hanya. Munzali ya dinga murmushi yana mai mamakin yadda zukatansu suka zama mallakin yaya da kanwarta lokaci guda. * Filin rawa Lilu yaje ya yi abarsa son rai ya dawo inda Sauda take tare da Qibdiyya. Yarinyar ta sake abinta tana ta yi musu hira. Tana ganin Lilu ta gudu wurinsa. Sauda ta ce. "Baban yara ita ma ka sayeta kenan" Ranar har su Abbati suka tashi tafiya Qibdiyya tana hannun Lilu. Kowa sai da ya shaida yadda tasu tazo daya daga haduwa. Da ya zo sakata a mota shi da iyayen nata babu wanda ya kula cewa kiss ta so yi masa a baki. Dama ce bata samu ba saboda tana yunkurowa ya sauketa a jikin Abbati. Kuruciya bata barta ta dauke shi komai ba. Uncle Daddy ne kadai yake yi mata. Sai kuma mutanen cikin ire iren bidiyo da yake kunna mata ya ce tayi masa abin da ta gani. Ta fanin kallo Zakiyya tana matular kokari don ko fim ta daina kallo a gaban 'yarta saboda kaifin basirar yarinyar. Shi yasa bata da aiki sai karatun waya. Sakacinta a bangaren saka ido ne a cikin gida. A zatonta tunda suka fito ciki daya da Daddy ba zai taba cutar da ita ba balle 'yarta. (Ya ke UWA mai dimbin daraja da martaba. Ba a ce ki sanya zargi da kokonto a tsakanin mu'amalar 'ya'yanki da 'yan uwanki ba. Nagari masu sonmu da gaskiya sun ninka shaidanun. Yana da kyau amma ki kula da irin shakuwarsu ko tsoronsu da yara ke ji. Idan tayi yawa to wajibi ki bi abin cikin laluma ki gano musabbabinsa. Ita alakar da aka gina da taba jikin juna a waje tana da wuyar bari. Shi yasa ma yaran da ake yiwa fyade ko koya musu mummunar dabi'a ake samun wahalar hanasu. Sai kin dinke baraka tsakaninsu da mai koya musu sai suje suna nema a wurin wasu da kansu. ZINA MASIFA CE GA BABBA DA YARO! Rabuwa da ita sai an dage sosai.) *** KIRIKASAMMA Dakin Baaba Mari babu haske sosai saboda ta gama shirin bacci. A kwance take tana ta juye juye akan gado. Jikarta ta wajen Atine da suke kwana tare sai munshari take abinta. Gajiya tayi da tunanin da ya addabeta ta tashi za ta dauro alwala kamar yadda aka koyar dasu a islamiyya. Babu wani abu da ya gagari addu'a, musamman a hada da qiyamul laili. Alwala taje ta dauro a bandakinta wanda Abbati ya yi mata a falo. Da yake fitilar chaji ta kunna tana iya hango tsakar gidansu sosai. Maigidanta ne har yanzu shadaya da kwata na dare zaune tare da Mal. Sa'adu wanda ya yi uwa ya yi makarb'iya akan bakon da suka yini dashi. Su uku har bakon hira suke suna dariyar wani abu da ya fada. Daki ta wuce ta dauki hijabi da abin sallah. Komai a sanyaye take yi saboda wani kwantacwn abu da bata san a ina yake ba yana fada mata akwai matsala. Ko Munzali bai taba zuwa Kirikasamma shi kadai ba. To me zai sa 'yan satittika da nad'in sarautar Abbati shi wannan Shazalin ya dawo? SHIDA RANAKUN... *** Gari ya waye, rana ta fito tun karfe shida da rabi. Zuwa goma na safiyar Asabar jama'ar dake waje har sun fara jin zafinta. Sai dai wannan zafin ba zai hana masu uzuri a waje fita su gabatar dashi ba. Kamar kowacce rana ga dan Adam, ita ma wannan Asabar ta zo a matsayin ranar kuka, farinciki, dariya, bakinciki, fargaba, alhini da kowane irin yanayi da mutane ke tsintar kawunansu. A safiyar wannan Asabar din ne Uwani ta amsa wayar Mubashir mai tafe da mummunan labari akan gininta. A ranar ne kuma Shazali ya wayi gari a Kirikasamma bayan ziyarar bazata da ya kaiwa gidansu Abbati. Ita ce kuma ranar da Hasiya ta zaba domin kai wa Salima kukanta akan saurayin Ayaah. Duka dai kuma a wannan ranar ne Abbati da Munzali suka je daurin auren kanin Mami Khadija bayan dinner din da suka je ranar Juma'a da daddare. Dinner din da basu baro ba sai da suka tabbatar an sami musayar zukata tsakaninsu da 'ya'yan Alh. Tahir guda biyu. *** Ana kiraye kirayen sallar Magariba Shazali ya isa Kirikasamma. Girkin abokiyar zaman Baaba Mari ne. Tana jin an ce abokin Abbati ne ta fito daga rumfar da suke girki tana fadin maganganu. Ciki har tana cewa "Ban san da zuwan bako ba saboda haka ban girka dashi ba." Baaba Mari ko tari bata yi ba har ta juya ta tafi. Bakinciki da hassada ba bakon abu bane gareta daga wurin kishiyar dake morar arzikin Abbati. Niyarta idan an kawo mata nata abincin ta bashi. Sai gashi an hada masa gara guda daga bangaren Mal. Sa'adu. Atine da Habi su ma ba a barsu a baya ba saboda kada mahaifiyarsu ta wahala. Kowacce ta aiko da abinci. Ashe kusan karfin girkin ma 'Yashshafa ce tayi. Deluwa ta rasa inda za ta saka ranta domin a burge wannan bako. Mahaukaciyar motar da yazo da ita kadai ta ishi bawa shiga rudani. Akan Shazali ita mai iya hakura da Sha'aib ce kamar yadda take kiransa. Kafin lokacin kwanciya baccin da Baaba Mari ta kasa runtsawa Mal. Inuwa ya shigo dakinta. K'aidarsa ce zaga matansa da asuba da kuma bayan Isha. Da murna ya shigo mata yana yabawa baiwar dansu wanda har masu kudi ke ziyartar iyayensa. "Idan aka kirani da Uban Abbati sai naji duk garin nan babu ya ni. Dubi dai ace mutum mai arziki kamar wannan ne a gidanmu..." Kula ya yi hankalinta ba ya gare shi ya bata rai. "To yanzu kuma me ya faru? Tunane tunanenki na banza akan arzikin danki ne ya sake dawowa?" Murmushin yake tayi tare da kawar da kai domin ko za ta kwana tana bayani baya taba fahimta. "Malam kenan." Komawa ya yi ya zauna yana dubanta cikin yanayin da yaki jinin ganinta. "Ki fadi damuwarki tunda nayi imanin akwai. Yau da ace ba Inna Mairo ce ta karbi haihuwar dan nan ba sai ince ba naki bane shi yasa kike gwada masa halin matar uba ko dan riko. Ni ko da wasa ban taba jin uwar da take yiwa dan cikinta bakincikin samun arziki ba sai ke Mari." "Har yanzu kana ganin laifina don na damu da son sanin silar kudin da mu da danginmu muke ci? Daga zuwa almajiranci sai kudi kamar suna zuba daga sama?" Ransa ya soma baci amma ya danne domin baya son rigima a daren nan. "To meye a ciki? Arziki ba na Allah bane? Kuma yana baiwa wanda ya so bi ghairi hisaba. 'Yan kasuwa nawa ne suka fara a matakin da yafi bara kaskanci amma yanzu sun wuce sa'a?" "Cikinsu kuma kowanne idan an tashi zaka ji an cewa abu kaza yake sayarwa ko yake kerawa. Shin ka taba tambayar kanka me Abbati yake sayarwa? Ka taba ganin wani abu cikin kayan sayarwarsu ya kawo gidan nan?" Shirunsa ya bata damar cigaba da magana cikin lumana. "Malam ni da kai mun sani cewa yaron nan duk fadi tashinsa yana yi ne domin ya inganta rayuwarmu. Kafatanin gidan nan babu wanda Abbati bai shiga rayuwarsa ba." Muryarta sai ya karye tun kafin ta fadi abin da ke zuciyarta "dan nan yaron kirki ne ba don ni na haife shi ba. Amma ina tsoron kada haram..." "Ya isa!" Mal. Inuwa ya furta yana mikewa. Zargin ta dasa masa wanda ko kadan bai so ba. A duk lokacin da son bincikar dan nasa ya bijiro masa sai tsoron abin da zai tarar ya hana shi. Amma yau yaji wani irin nauyi ya sauka a zuciyarsa mai tayar da hankali. "Allah Ya huci zuciyarka. Mu kwana lafiya." Daga wadannan kalaman ya shige uwar daka ta barshi. Ya fita zuciyarsa tana ta wasiwasi. Amma yana zuwa wurin Mal. Sa'adu da ya same shi da Shazali suna hira sai ya tura zarginsa baya. Da safe Deluwa har dakin da aka sauke Shazali ta tura 'Yashshafa ta kai masa abinci. Ta hada mata da hudubar kwarkwasa domin daukar hankalinsa. To 'Yashshafa ko kadan baiyi mata ba daga kallon farko. Akwai kudi ta gani daga sutura da motarsa. Bashi da wani muni amma mummuman nufin dake zuciyarsa ya tasirantu a cikin ji da ganinsa. Ko murmushi yake idan ka kalle shi zuciya sai ta harba saboda shaidan ya gama dashi. Da zumbura baki tayi sallama kuma yana amsawa ta ajiye a bakin kofa ta gudu abinta. Gara

Chapter 32 of 62