Share this page
ba ai kwa kyautata mata a matsayin mahaifiyar Mardiyya. Har abada bana fatan abin da zai zo ya raba kawunanku da kanwarku. Ta taso da kaunarku da girmamani shi ne ku kuma don rashin kunya zaku dinga fadawa mahaifiyarta magana akan idonta? Uwa uwa ce fa. Baku san abin da kuke yi zai iya tunzurata ta koma bin umarninta ko da ya sabawa addini da dabi'a ba? Ku tashi ku je dakinta ku bata hakuri." Lilu da Farha ta bawa wannan umarnin. Suka tashi suna kunkuni gami da hararar Suhaib da ya kawo kararsu. Zuwan nasu da bada hakurin bai canja komai na tsanarsu a zuciyar Mama Nasima ba. Mardiyya kuwa sai ta kara kaunarsu a ranta har ta dinga doka murmushi. Farha sai taji dadi ita ma. Lilu kuwa tana biyo bayansu ya shiga tsokanarta domin ya kara wanke laifinsu. Da hannuwansa duka biyu yake wasa da kumatunta. "An Mardiyya, Mardiyya. Kamota nan kamota nan." Ai kuwa ta kwashe da dariya sannan suka taru shi da ita suna bin Farha tana gudu. "Kamota nan, kamota nan.." Da Alh. Tahir ya shigo ya gansu sun hade su hudu suna bin Suhaib har wata guntuwar kwallar farinciki ya yi. Yana son su, yana kaunarsu. Su ne mafi girman arzikinsa a duniya. * "Mukullan na meye ne?" Anti Jiddo ta katse fadan nasa saboda tana son tashi. Gasar tura hotuna da shigar kece raini ake yi a wani group dinsu na whatsapp. Gabadaya ta rikice tana gudun idan bata tura da wuri ba za a iya zargin bata kai matsayin zaman group din ba. "Na dakunanku ne a sabon gidan. Kowacce bangaren da mukullinta ya bude shi ne nata. Ku fara shiri ranar Juma'a zamu tashi. Kuna da kwana uku na packing." Ya tashi zai fita saboda karar text da ya shigo wayarsa yana saurin zuwa ya bude yaji saukar mukulli akan centre table din. Dan wigowa ya yi sai yaga Mami Khadija ce ta ajiye nata. "Ina son magana da kai." Yadda Anti Jiddo da Mama Nasima suka ci burki sai ka rantse cewa tayi ina son magana daku. Alh. Tahir ya mayar da wayar da har ya zaro daga aljihu ya bude sakon. Baya son rigima shi yasa ya zube musu mukullai amma indai wani bangare take so a ranta zai bata dama. Ta cancanci fiye da haka ma. "Ku kawo mukullan. Idan munje sai a zaba. A fara ta kan babba." "Bar musu kayansu." Tsayuwa ya yi da kyau yana kallonta "to ki dauki naki mana." "Ba zan dauka ba. Maganar da ta kawoni kenan. Na gama gini kayi min izini na koma can tare da yara ko kuma ka sauwake min. Duk wanda ka zaba dai a ciki zan koma gidana ne." Ta ce a hasale ganin ya sake kai hannu ya shafo wayarsa da wani sakon ya sake shigowa. 'Yan mintuna kalilan din da take nema ma ba zai iya bata ba saboda matan titi. Kalamanta sun saukar masa kamar dirar aradu ne. Ba shiri ya mayar da wayar. Hajiyoyin gulma suka dawo abinsu kowacce tana ayyana idan Mami Khadija ta fita zata jidadin korar 'yar uwarta. "Wace irin magana ce wannan Khadija? Kina cikin hankalinki kuwa." Bata zauna ba. Zuciyarta ke tunkudarta akan ta amayar da bacin ranta a yau ko zata ji sauki. Abubuwan da suka yi ta faruwa shekara da shekaru suka dinga dawo mata. Mafi muni a cikinsu bai wuce yadda mijinta ya shafawa idanunsa toka yake tozarta addinin musulunci ba. Haram haram ce babu ruwanta da jinsi. To akan me za a dinga yiwa maza uzuri akan zina? Sabon Allah ne fa! "Duk abin da ka dauka game da hankalina daidai ne. Zaman gidanka ne na gama." Ya kankace idanu da mugun bacin rai "saboda ke butulu ce? Sai yau, washe garin ranar da ki ke ganin kin sami duniya za ki fito da wannan maganar? Me ma aka yi miki?" Rashin kunyarsa bata bata mamaki ba tunda ance zina tana daukewa dan Adam kunya. "Wanda ka yi min na yafe amma bari na tuna maka kadan a cikinsu. Ka ha'inceni. Ka cutar da lafiyata. Kaci amanata. Lalura ta sameni a rasa mai zabar min abin da ya dace sai wadda na kama ka akan gado da ita? Wannan wulakancin yafi komai yi min ciwo. Ni Nasima tasa aka cirewa mahaifa." Idanu jazur ta kalli Mama Nasiman "da yake Ubangijina adalin sarki ne sai ya barki da taki mahaifar Ya kuma hana wani dan kwanciya a ciki. Gashi nan da bakinsa yake fada min asibitoci da kudaden da ku ke kashewa wurin neman haihuwa." A haukace Mama Nasima ta kalli Alh. Tahir ranta a bace. Ta yaya zai dinga fallasa sirrinta a wurin matarsa. Ga wata shewa da Anti Jiddo tayi tana tafa hannaye. Ita kam a bangarenta komai zam. Duk su bar mata gidan ta ci karenta ba babbaka. Tashin masifar Mama Nasima ko dis bai shiga kunnuwan Alh. Tahir ba. Zantukan Mami Khadija ne suke kai kawo a kowanne sassa na jikinsa. Don yana bin mata sai me? Mata nawa ne zaune da maza irinsa? Wasu ma kannensu ciki daya mazajensu suke bi kuma ayi sulhu a zauna lafiya. "Meye ban miki ba Khadija? Wace irin kyautatawa ce ban yi miki ba a tsayin rayuwar aurenmu? Karatun da kike son fara yi min takama dashi waye sila?" Ba taso ya ga rauninta ba amma hawaye ne suka balle mata. Yau daya ta daga muryarta sama da ta mijinta. Ta gaji da hakurin gaibu. Babu abin da kokarinta a kansa ya haifar na canji sai kara tabarbarewa. "Kai har kana da bakin goranta min akan abin da kayi min? Ni da aka datsewa farinciki aka rabani da masoyina saboda ana neman shiriyarka in ce me? Kamar yadda mahaifiyata ta yiwa Baba biyayya ta amince da aurenmu haka nima na dinga yi maka. Ni ce shan banza da hofi duk domin ka sami gamsuwar da za ta rabaka da matan titi. Wani abin na sha na kwana na wuni gudawa, wani ya kulle min ciki, wani ya sani jiri amma duk a banza. Har yau ban dace da maganin infection ba saboda zama da kai. Ban gajiya da zuwa kunshi da gyaran kai saboda ance idan na dage da kwalliya zan karkato da kanka. Kai kanka ka sani babu irin kwalliyar da bana yi maka. Ka tara min abokanka nayi ta dora tukunya ina saukewa bana nuna maka gajiyata. Ladabi da biyayya har bayan na kama ka da mai aikina ban daina ba. WALLAHI MAZA IRINKA SUNA DAGA CIKIN MASU KAI MATANSU WUTA. Ba don kariyar Allah ba da tuni na dade da fara gurfana gaban malaman tsibbu ina karbo asiri. Kuma duk da na dade da kudurin barinka amma wallahi inata kyautata maka zato. Fatana ka shiryu mu cigaba da rayuwa da 'ya'yanmu har karshen rayuwarmu. Haba TAHIR! Idan ka tsarkake kan ka daga dattin zina ba Khadija ka yiwa ba. Bani da wuta da aljanna. Kanka kadai za ka taimaka da 'ya'yan da kake ikirarin so. Su ne nake jiyewa kada hakkin alfasharka ya fara bibiya." Zuwa yanzu fuskar Alh. Tahir a tamke take baya ma gani da kyau. Wai shi matar da yake kokarin ganin ta tsallake kowa a matsayi da mukami ce take gasawa maganganu haka. Da ya rasa abin cewa sai ya yi mata tambayar da yayi nadamar yi saboda amsar da ta soma bashi. "Duk wata nasara ta rayuwarki ba a jikina ki ka samu ba?" Shekeke ta kalle shi har lokacin idanunta suna zubar da hawaye "nasara? Dama akwai nasara a auren wanda baya tsoron Allah? In dai auren irinka nasara ce ga mata to ina fata Allah Ya hada 'ya'yanka da maza irin..." "Kina hauka ne?" Ya ce da dukkan karfinsa. Sannan ya dauketa da mari, wani abu da bai taba shiga tsakaninsu ba. Idanunta sun rine da bakinciki shi kuma da bacin rai. Da ya barta ko kadan bata da niyyar karasa addu'ar ita ma. Ko ba ita ta haifesu ba ba za ta musu wannan addu'ar ba. Marin bai sakata kuka ba sai dariya. "Ashe dai kana sane ka ke take sanin. Da na dauka kallon waliyyai ka ke yiwa masu halinka shi ne zan rokawa zuri'arka" Da dan allinsa ya nunata cikin fushi yana kumfar baka "ya isheki haka nan. Kuma babu inda zaki je. Ki hada kayanki jibi zan turo mota." Ya karashe a kufule. "Idan ta kama na kaika kotu ne zan kai ka. Babu wani dalili na shari'a da ya ce wajibi ne zama da kai." Nan yaji zuciyarsa ta dan girgiza. Dama ta fada ne don ta tayar masa da hankali. A daidai lokacin kuma waya ta shigo masa a wadda tun dazu ake turo masa sako. Wayar taki tsahirtawa duk da anji bai dauka ba. A kira na hudu yana faman babatun nuna mata wajibcin bin sa tunda shi ne namiji ya amsa kiran da sauri. "Zan kira ki...ka anjima" Bai ankara ba Mami Khadija ta warce wayar daga hannunsa. Katse kiran tayi da rawar hannu duk jikinta yana tsuma. Ace har a wannan matakin akwai wata tsagera a waje da ba zai iya hakura da bacin ranta ya shawo kan iyalinsa ba. Ta sake jin alamun shigar sako a lokacin da ya hayayyako mata da fadan ta bashi wayarsa. Daga Anti Jiddo har Mama Nasima sun kula da yanayin tsoratar da ya yi. "Ki bani wayata na ce." Bata saurare shi ba sai hannu da ta daga masa tana yi masa alamar ya dakata daga matsowa kusa da ita. Da daya hannun ta bude bangaren sakonnin whatsapp wanda ta tabbatar dashi suke hirar. (Mr Rufus) Ta gani a sama alamun shi ne wanda ya turo sako mafi kusa da lokacin da suke ciki. Da kyar ta mallaki nutsuwarta ta bude. "Khadija, Manzon Allah SAW ya ce wata tajassasu" ya fada muryarsa na karyewa. "Ya kuma isar da sakon Allah SWT da Ya ce Wala taqrabuzzina." (Gasu nan su tayaka bacci yau. Idan kuma dattijan gidanka sun barka fitowa ka tsaya a bayan layinmu ka daukeni.) Shi ne abin da aka rubuta na karshe Mami Khadija bata so bude hotonan da suka fara bata tsoro ba tun a haka ma sai dai biyun da ya bude a sama sun kadata. A guje ta bude daya ta dago kai ta kalle shi a sanyaye. She felt disappointed. Lalacewar tasa har ta kai nan? Me yasa maza masu wannan halayyar basa tsoron Allah ne? Ina hakki zai kai su? Mika masa wayar tayi jikinta a sake "Yumna? Yumna aminiyar Farha. Tahir ita ma baka bari ba? Ita kadai da iyayenta suka mallaka sai da ka lalata musu 'ya? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Fita tayi ko gabanta bata gani da kyau tana jiyo hayaniyarsa da amarensa. *** "Daddy ni Papa ne zai bani." Cewar wata karamar yarinya da bature ke yiwa lakabi da cute. Duka duka bata fi shekara biyar ba. Tana sanye da kayan bacci riga da wando na cotton. Kanta sabon kitso ne yiri-yiri anyi mata shuku biyu hagu da dama. Ko a haka ka kalleta sai ta shiga ranka balle idan surutunta ya hadaku. Bata da haske sosai kamar mahaifiyarta domin Munzali ya dan fi ta haske ma. Amma akwai idanu dara dara da dan karamin baki daidai fuskarta. Hancinta yana da dan tsini kamar na Munzali. Rike take da plate din indomie da kwai wanda mai girkin gidan Audu ya dafa. Daga bakin kofar kawataccen wurin cin abincin (dinning area) a tsaye Iya Kande ce dattijuwar dake kula da ita. "Daddy ka kira min Papa pleaseeee." Munzali ya dora hannu a ka kamar ya yi ihu. Kwata kwata ta hana shi baccin safe ga gajiyar da suka kwaso jiya. Kuma suna isowa Kano suka wuce gidansu Zakiyya mahaifiyarta suka daukota. Dama ita ma ta sani indai Munzalin na gari a gidansa Qibdiyya take zama ko lokacin makaranta ne su suke kaita. Bai yarda rabuwar auren ta kawo gibi tsakaninsa da ita ba. Yanzu breakfast suka zo yi karfe bakwai da 'yan mintuna saboda sammakon tashin da tayi amma take yi masa rigimar sai ya kira Abbati. "Papa bacci yake yi idan ya tashi zai shigo. Ki ci wannan sai a sake dafa miki wani abincin idan ya zo." Ya ce da sigar lallashi. Noke kafada tayi "ni dai a'a. Iya ta bude min kofa naje wurinsa." Ransa ya soma baci ya zaro mata ido "zan zaneki fa Qibdiyya. Ki zauna ki ci abincin nan nace kafin ya tashi." Sai kawai ta fashe da kuka kamar dukanta ya yi "Daddy sorry. Daddy ka ce ka hakura. Daddy..." "Na hakura" ya ce a kagauce da gajiyar magiyarta "zauna ki ci." "Kayi dariya" "Hihihi" ya yi yak'e kansa na sarawa. Gadonsa yake muradin hayewa ya nutse cikin lallausan bedsheet.... Murmushinta tayi masa jin ya hakura don ita bata son ana fushi da ita "yauwa Daddy to in dauko maka waya ka kira Papana? Pleaaasee" Ido ya tsura mata ya saki murmushin da bai yi niyya ba. Tana tsaye a gabansa tana rangwada kai gefe da gefe. Duk wanda ya san Qibdiyya zai shaida manyance da tsantsar wayonta. Idan ma akwai tashi a hannun kaka wato Gwaggo Lami kanwar Asabe harda halinta. Wani abin idan tayi shekara goma ko ma fi za ka bata. "Daddyna please fa nake ta cewa" ta dan turo baki alamar gajiyawa. Daukota ya yi ya dorata a cinyarsa "ki zo na baki don Allah ki ci mu je mu kwanta." Ita ma hakurinta ya kare tana ganin ba za ta sami abin da take so ba. Tafi son kwana a gidan Abbati amma tun bayan ya tura Hanne Kirikasamma sai ya ce ta dinga kwana a gidan Munzali tare da Iya Kande. "Ni Papa. Papanaaaa" Tun Munzali da Iya na rarrashi har ya koma fada. Bata yi shiru ba sai ciwon kai da ta kara masa. Wayarsa ya tashi ya dauko ya kira Abbati ba shiri. * Tun farkon kwanciyarsa har bayan asuba da ya koma bacci mafarkin Farha yake yi. Sunanta kuwa ya ambata a mafarkin da kuma a farke yafi a kirga. Wayar Munzali ce ta tashe shi ya yi guntun tsaki. "Idan na shigo sai ranka ya baci. Ka san me ka katse min da wannan wayar kuwa?" "Ba matsala duk abin da zaka yi na shirya in dai za ka dauki 'yarka. Yadda ka san in yi bacci a zaune amma kamar da gangan ta isheni da rigima." Murmushi ne ya mamaye fuskar Abbati yayinda yasa kafa ya shure katon duvet din da ya lulluba dashi. Sanyin dakin ya sauka a jikinsa ya mike da gaggawa ya dora riga mai madauri akan dogon wandon baccin jikinsa. Girarsa ta tattare da fushin da ya maye gurbin fara'arsa "me yasa ka tasheta da sassafe haka? Ko takwas fa bata yi ba. Yara suna bukatar isasshen hutu. Asabar din ma yaro ba zai huta ba to sai yaushe?" "Sannu mai 'ya. Dadin abin dai nima ba daga bishiya aka tsinkoni ba. Haka kawai ta hana mutane bacci ka zo kana yi min fada..." Dariyar da bai yi niyya ba ce ta kama shi. Wani zubin ya kan rasa gane da Munzali da Qibdiyya waye 'ya waye uba. Munzali har kishi yake da ita idan ya ga yaki kula shi. Ba don komai ba kuwa sai don ya tashi da yunwar kulawa irin ta iyaye. Shi ne komai na aminin nasa shi yasa yake ganin lokaci ya yi da zai yi amfani da wannan damar su saita rayuwarsu. A nasa bangaren dole sai ya je gida gobe. Munzali kuwa tunda iyayensa suna gari yanzu zai fara yi masa maganar abin da ya kamata ace ya yi tuntuni. Wannan rayuwar ta ishe shi. Suna bukatar iyali na kurkusa wanda zasu rayu tare. Farincikinsa daya yaki da jahilcin da suka dage sosai suka yi. A lokacin sun yi ne domin samun kasuwarsu ta daga a idon manya. Yanzu zai musu amfani wurin yin kasuwanci a ilimance. Wayewa dai irin wadda mutum zai je ko'ina kai tsaye ya saje sun samu. Haka nan manyan kasa ke biya musu su je kasashen waje domin idan sun iso su amfana dasu. A haka suka sami wayewa sosai idanunsu suka bude. * "Papaaa" Qibdiyya ta ce tana yin tsalle. Abbati ya dagata sama ya juya suna kyalkyala dariya. Munzali na ganin haka ya tashi zai gudu daki. "Malam dawo magana zamu yi fa. Me Audu ya dafa ne?" Ya yi maganar lokacin da ya dire Qibdiyya. A marairaice Munzali ya kalle shi "kayi min rai dan Mariya uban Mariya. Kaina wani yammm yake yi irin na mai shirin zarewa saboda rashin bacci." Kafe shi da ido Abbati ya yi wanda ya nuna masa zaman nasa dole ne. Sai da ya harare shi ya koma ya zauna. "Ka dai ci sa a ina tsoron masifarka wallahi da ba zan zauna ba." Iya Kande ta dube su tayi dariya. Abokan suna matukar burgeta. Tana fatan kowanne ya sami matar da zasu yi zaman lafiya tare. Ta san wani abu cikin zaman Abbati da Hanne mara dadi. Wauta take ganin ta yiwa Hannen yawa tunda duk kokarin Abbatin na son kyautata mata ta 'buge da yi masa sace sace a gida. "Mutum ma yaki zama mana idan ya isa." Cewar Abbatin bayan ya zauna a kujerar kusa dashi. Iya Kande sai ta ja hannun Qibdiyya da dabara suka bar falon. Bread da kwai Audu ya kawo musu domin bai kammala suyar doya da farfesun da yake ba. Ka'idarsu sai wuraren sha daya suke karyawa shi yasa bai fara da wuri ba. "Ni wallahi jikina duk ya yi sanyi. Ka sanni idan an ce za ayi magana amma don mugunta ka tayar min da hankali kafin na ci abinci." "Idan baka ci ba ma maganar sai jibi." Munzali na jin haka ya shiga tuttura abinci yana kurbar tea. Yana gamawa ya ture harda na gaban Abbati dake cin nasa a nutse. "Yauwa fadi don Allah." "Ban koshi ba" "Ba kyau abin da kake yi min." Sai kuma ya dan muskuta tare da rage murya "ko dai ya shafi maganarmu ta jiya? A shirye nake mu daina da gaske." Wannan yanayin na zance mai mahimmanci Abbati ya yi da fuska sannan ya ce "Wannan maganar zamu yi ta sosai amma kafin nan Munzali gidanku kai ne namiji babba ko ba haka ba? Duk yawan yayyenka mata ka fisu iko saboda kasancewarka namiji. Saboda haka alhakin gyara zumuncinku yana wuyanka. Ka nemi 'yan uwanka ka san su sani na jini da jini. Kaga ni dasu Atine bamu da shamaki. Babu wadda ban san halin da take ciki ba duk da suna gidan miji." "Ummakati ce babba kuma tayi aure mijinta yana da abin hannunsa." "Ina ruwan zumunci da abin hannun mijinta? Kuma fa muna tare fa babbar yar ku ta rasu kuma ka ce min akwai wasu." "Wadanda ba dakinmu daya ba su tara ne duka mata." "Sai kuma aka ce sun sauya suna daga matsayin 'yan uwanka don baku fito daki daya ba? Nima muna da 'yan uba kuma duk na hadesu. Magana ta gaskiya Qibdiyya ba mu kadai take bukata a rayuwarta ba. Banda 'yan gidan su Zakiyya bata saba da kowa ba." Kallo sosai na nutsuwa da fahimtar mutum Munzali ya yi masa. Kullum shi ne mai hango masa matsala kuma ya taya shi gyarata. Shi kam ko yau ya bar duniya ya yarda da soyayyar dake tsakaninsu ya san Qibdiyyansa ba za ta taba maraicin uba ba. "Naji zan kokarta. Amma sai ka tayani don ka san Asabe ita kudi kawai take so. Su kuma wallahi idan na bi wata ta gayan bak'a sai na rama." "Ka kwana biyu baka yi muryar 'yan tasha ba ai." "Kut...ni ne dan tashar?" Munzali ya tashi ya yo kansa a guje shi ma ya mike yana neman tsira. Idan ya zauna karshenta sai ya nemi panadol. Gajiya Munzalin zai tara masa don a jikinsa yake fanshe wasan kokawarsa da bai yi ba da kuruciya. "Ka dawo kawai mu gwabza mutumina ko na goge nambar yarinyar nan ta Diamond plaza." "Da gaske ka karbo?" Farinciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskar Abbati lokacin da Munzali ya gyada kai. Bai jira komai ba ya je ya riko shi suka fara gwada kwanji. Yau dai Munzali ne ya ji jiki don bai san me Abbati ya sha ba har yake jin karfi irin haka. *** Sai da ta kusa isa dakinta wani tunani da ya karasa dagula mata lissafi ya darsu a ranta. "Yumna. Yumna aminiyar Farhata?" A guje ta shiga dakin 'yan matan har tana tuntube saboda sauri. "Farha bani wayarki" Ta umarceta fuskarta babu wasa. Bakinciki da taraddadin dake kai kawo a kirjinta kuwa baki ba zai iya kwatanta shi ba. Wani irin sauti kamar bugun kararrawa take ji a kunnuwanta. A tsaye take tana haki amma cike da dauriya ta kai hannunta dake rawa bangaren hotunan wayar. Bata ga komai ba saboda haka ta mika mata "Baki isa ki ha'inceni ba wallahi. Ungo ki budo min wadanda ki ke tura masa." "Shi wa?" Lilu ya tambaya suna shigowa dakin shi da Sauda da Suhaib. Akwati ta kira shi ya zo ya sauko musu dashi daga kan wardrobe. Tun a hanya ya ce ta san ba tsayi gareshi ba kawai ta kira shi don suyi dariya. Da kansa ya kira Suhaib suka taho tare. Mami Khadija ta kallesu ta ce "duk ku jirani zan zo gareku daya bayan daya." Ta mayar da hankalinta ga Farha "idan ba za ki bude ba bani nambarsa ko waye shi in kira." Farha ta karasa rudewa sai kuka take yi tana juya wayarta a hannu. Ran Mami Khadija ya sake baci ta daka mata tsawa nata jikin yana 'bari da tsoro. "Har kin isa ki yaudareni? Ina ta kaffa kaffa daku ashe ni aka mayar shashasha. Kuna can kuna turawa mutanen banza tsiraicinku." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Su duka yaran abin da suka ambata kenan amma sautin muryar Farha tafi ta kowa. Kuka take yi iyakar karfinta Sauda tana tayata. Mamin tasu ta hargitse basu san musabbabin hakan ba. Kirjinta ta shiga nunawa wasu sababbin hawayen suna wanke mata fuska. "Mami ni? Ni din? Wallahi, wallahi karya yake ko waye shi. Saboda gudun fadawa halaka da tsoron bata miki Mami watana biyu bana kula Yumna." Da kyar Mami ta dan saita kanta ta nuna bata san komai ba "ina magana akanki me ya kawo zancen Yumna. Me tayi?" " 'Yar kawunta ce tazo hutu gidansu ta koya mata bin sugar daddies. Nayi ta mata nasiha taki ji shine na rabu da ita bayan ta ce za ta hadani da wani." "Ta hadaki da wani don mugunta? Me yasa ma baki sanar dani ba?" Farha ta share kwalla "ce mata nayi zan fada miki ki gayawa Ummanta sai ta ce min wai in na fada miki sai me? Shi ne naji haushi na kyaleta." A zuci Mami Khadija ta iya cewa 'Ba dole ta ce miki sai me ba tunda mahaifinki ya zubar mana da mutumci?' "Naji kuma na yarda amma na rantse duk ranar da ki ka afkawa irin wannan sharin ki kuka da kanki." Sauda ta nuno da hannu tana labe bayan Suhaib duk ta tsure. "Wallahi Mami bana komai ni. Masu zuwan ma nace su rabu dani sun ki." "Ki daina kokarsu tunda lokaci ne da Allah Ya kawo miki. Na baki kwana uku kiyi shawara da zuciyarki da 'yan uwanki ki fidda wanda ya kwanta miki. Kina gama secondary zan miki aure." Da yake bata ga fuskar musu ba ko tari bata yi ba sai aukin gyada kai. "Kai kuma Lilu idan na sake jin an ce kana bibiyar mata sai na saba maka. Yaro tun baka tafasa ba kana neman konewa. Kar kayi tunanin cututtukan zamani ne kadai sharrin dake cikin yawon banza. Lahirar mutum ce kacokan take gurbacewa. Duniyar ma kuma duk kudinka ba za ka taba samun nutsuwa da jindadin da kamilalle zai samu ba. Wadannan abokan banzan naka ku raba jaha kowa ya kama gabansa. Sai kun fi jindadin shiryuwa." Duk maganganun nan tana yinsu ne cikin haki da kunar zuciya. Suhaib yaji duniyar tayi masa zafi. Kusa da ita ya karaso ya dora hannayensa akan kafadunta ya sallami kannensa. "Ki kwantar ta hankalinki Mami in sha Allahu komai zai daidaita" "Komai zai daidaita a ina? Shaye shayen da kake ka shirya dainawa? Idan kana tunanin kana sha domin batawa mahaifinka rai ne to ka sake tunani. Bai san kana yi ba. Ko ma ya sani babu mai dora masa zunubanka tunda ba shi ya kama hannunka ya kai gaban 'yan kwaya ba" Idanunsa a kanta yana kara samun tabbacin Abban nasu ya yi wani abu mai girma ya ce "In Allah Ya yarda ba

Chapter 14 of 62