Share this page
bebin bane a hannunta sai ya zaro kudi. "Dakta ga tukwicinki inji Imran dani babansa. Mungode sosai." Dan dagowa tayi ta kalleshi da kyau "wane Imran din?" 'Yar dariya mai fallasa tsananin farincikinsa "jaririna na ciki" "Oh..ashe fa Nos din bata fada muku ba. Ai mace ta haifa. Ko ba Zara Rabi'u ba?" In sun tanka to lallai kujerun wajen ma sun tanka. BABI NA SHA UKU. Kafin isowarsu gida kishiyar Zara ta sanar da duka maaikatan gidan uwargidan Alhaji ta haifi da namiji. Labari da dumi duminsa yazo gareta daga wajen kanwar Alh. Unais wadda ta kasance aminiyarta cewa mace aka haifa. Dariyarta ta sha a daka harda rawa sannan ta fito rama wulakancin da Zara ta dinga yi mata da cikin. Dama saboda doki Alhajin da kansa ya tuka su zuwa asibiti ita da Hajiyan Fatakwal bai bari direba ya kaisu ba. Hancin motarsa na shigowa katafariyar farfajiyar gidan 'yan dattijan masu aikin gidan mata suka soma guda. "Allah shi raya Imarana magajin Alhaji Unaisu" inji mai girkin gidan. "Aminnnn" sauran suka amsa a tare. Hajiyan Fatakwal ta fito fuska a hade ta daka musu tsawa. "Ku matsa ku bani wuri duk kun cikawa mutane kunne. Waye ya ce muku namiji ne?" Sai suka yi tsuru-tsuru dasu. Hajiyan Fatakwal ta shige bangarenta ko waige babu balle ta sake kallon Zara. Jaririyar ma bata karbeta ba tun a asibitin ita suka bari ta dauko abarta. Ko tausayin yadda take daga kafa da kyar Alh. Unais bai ji ba ya ce tazo su tafi tunda kalau take. Hutun da ake yi bayan haihuwa tayi a gida don bai ga dalilin zama ba. Kasa magana tayi saboda yadda suka canja mata lokaci guda. Gashi ta sha dinki irin wanda ba a taba yi mata ba duk haihuwarta amma dole ta sauko jiki ba kwari. Alh. Unais bin bayan mahaifiyarsa ya yi suka barta da masu aiki. Laurat kishiyarta ta dubeta ta tabe baki. "Ya aka haihu a ragaya uwar Imran? Bari na dauko wayata don har na canja muku suna ke da maigidan zuwa Abu wa Ummu Imran." Tana dariyar shakiyanci ta wuce. Masu aikin ma ganin kamar Alhajin cikin fushi yake sai aka rasa mai karbar 'yar. Akwatin kayanta kawai aka daukar mata. Sai da kowa ya fice daga dakin ta kwantar da jaririyarta ta sami damar fashewa da kuka. Kirjinta har wani irin dokawa yake saboda bacin ran abin da aka yi mata tun daga asibiti har gida akan haihuwar mace. Bata yi mamakin ganin haka daga surukarta ba amma ta zata Alh. Unais yana sonta ko da bata taba haihuwa ba ma. Cikin radadin ciwo ta tashi ta tara ruwan zafi bayan kimanin minti talatin da ganin Hajiyan Fatakwal bata shigo ba. Jikinta ya yi tsami sannan 'yar ma tana bukatar wanka. Setin robor wankar jaririyar ta dauko ta ajiye a dakinta daga bangaren da yafi kusa da bandakin. Haka ta dinga dibar ruwa tana takawa da kyar har ta ajiye komai a wurin. Ta tashi za ta dauko bebin kafarta ta turgude ta tale gabadaya. Wata irin razananniyar kara ta saki lokacin da dinkin da tasha wuyarsa ya kece kyat! A wurin ta fadi jini na zuba cikin dan kankanin lokaci ta fice hayyacinta. Maryama da kannenta sai karfe shida suke tasowa daga islamiyya. Basu da masaniyar Mummyn tasu taje asibiti har ta haihu. Bakwai da rabi suke tafiya makarantar boko daga can su wuce islamiyyar. Mas'uda ce ta fara shiga falon Zara daukar wani abu taji kukan jariri. Da gudu ta karasa ciki ta hango jaririyar akan gado tana ta tsala ihu ga mahaifiyarsu kwance a kasa. Kanta tayi ta dinga jijjigata amma ta kasa tashi sai da kyar ta ce ta kira Hajiyan Fatakwal. Kafin wani lokaci dakin ya cika da 'ya'yanta sai Alh. Unais da Hajiyarsa. Masu aiki ne suka taimaka mata tayi wanka da kyar jikinta babu kwari. Duban yanayinta Hajiyan Fatakwal tayi gami da yin karamin tsakin da ya shiga kunnuwan mutanen dakin. Zara bata da hankali a ganinta. Irin maganganunta na rannan a waya su suka tabbatar mata da haka. Tayi mata lamuni ne dama albarkacin cikin da namiji da ake tunanin za ta haifa. Amma tunda abu yazo da haka ta sami damar raba danta da bakar kadara irin wannan. Dinbin asarar da Zara ta saka Alh. Unais akan hasashen gaibu ba kadan bane. Bakin gadon ta samu ta zauna ta dora kafa daya kan daya. Hannuwanta dake dauke da zobban gwal ta dauko guda ta nuna Zaran dashi. "Wai har yanzu baki sanar da kowa haihuwarki cikin danginki bane?" Gabanta ne ya yanke ya fadi ta kalli Hajiyan a tsorace "zan kirasu." "To ya dai kamata. Ba zai yiwu bane ace duk haihuwa sai dai ayi miki komai a nan. Dubi yadda ki ka fadin yanzu har dinki ya bude. Ya dace iyayenki su dinga tabuka nasu kokarin komai talaucinsu." "Umhumm" Zara ta furta kamar taci madaci. "Da dai nayi wa Unais magana akan daga can su samo miki mai zama har kiyi arba'in, to amma tunda ga wannan lalura da dole sai an sake miki dinki gara ki tafi gida. Kira min maman taki nayi mata magana." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Zara ta furta da dan karfi hannunta akan kirji "gida fa ki ka ce Hajiya?" "Akwai matsala ne? Gidanku fa nake nufi." Zara ji tayi ta gwammaci kar a turo kowa tayi aikin komai na jegonta da kanta akan dai ta koma gida. Ta zauna da Innayo a wannan dakin da iskarsa ma bata mata dadi? Tunanin kadai ya sake dagula lissafinta. "Hajiya ki barni a nan zan iya..." Hannu ta nuna mata fuska a hade "bana son wata magana. Ko akwai magana ne?" Ta dubi danta. Kai ya girgiza don shima haushinta yake ji "yauwa to ki shirya direba sai ya mika ki yanzu. Kar ki manta da batun dinkin dai." Jikinta ya yi sanyin da ko baki ta kasa motsawa. Wane irin wankan jego zata je gida haihuwa ta biyar? Anya ba za a zata auren ya mutu bane? Babu sarki sai Allah dolenta ta shirya 'yan kayanta ta lallaba zuwa dakin maigidan. Tare da Laurat ta same shi ta nuna tana son magana dashi ya ce Bismillah. Laurat ta kalla ya hade fuska kuwa. "Kin kuma yi kadan ki zo ki sameta kiyi tsammanin zan ce ta fita saboda ke." Laurat ta murmusa tare da mikewa. "Kila sirri ne bari na baku guri." "Dawo ki zauna nace." A fakaice ta yiwa Zara gwalo ta koma kusa dashi ta zauna. Kirjin Zara ya dinga harbawa saboda tsananin bacin rai amma haka ta danne. "Uhmm dama cewa nayi kayan bebi din kadan ne unisex duk na maza ne. Ko za ka bani kudi...." "Ba zan yi asara ba. Ki saka mata duk wadanda aka farke kafin na sami sararin sayan na matan" Gyada kai tayi tana kokawa da hawayen da bata son zubarwa a gaban kishiya. "To in dauko maka ita kayi mata huduba?" "Idan kin je gida kakanta ya yi mata ya kuma saka mata sunan da yake so." Hannuwanta ta dunkule har suka soma zafi saboda rashin gudun jini. So take ko ta halin yaya ta farka daga mafarkin da take yi. Lokaci guda mafarkinta ya sauya game da haihuwa. Ta saka rai za ta haihu su dawo gida miji yana nan nan da ita sai gashi ko mutum daya bai karbi jaririyar ba cikinsu. Duk rashin kunyarta bata san da idon da za ta kalli Innayo ba. Asibitin da ta haihu ta ce da direban ya ajiyeta suna fita. Da kafarta ta kai kanta wurin likitar da ta gama yiwa rashin kunya ta nemi a dubata. Duk irin haushinta da likitan take ji sai da ta tausaya mata. Mirgina kai kawai ta dinga yi hagu da dama tana hawaye da ake sake yi mata dinkin. Azaba ce kan azaba don ta gwammace ace sake haihuwa tayi akan wannan wahalar da bata da na biyu. Ana cikin yi tana jin kukan jaririyar da har yanzu ko wanka ba ayi mata ba. "Wai ina 'yan uwanki ki ka dawo ke kadai?" "Wayata ce babu chaji shi yasa ban kirasu ba" ta iya cewa tana kawar da kanta don kar a gano karyarta. Likitan bata takura ba amma jikinta ya bata akwai wata a kasa. Boye mamakinta tayi lokacin da Zara ta ajiye kunya a gefe ta roketa ta bata gado ko da na kwana biyu ne. Tunda file dinsu kudi kawai Alh. Unais yake sakawa bata da matsalar biyan kudin komai. Kudin hannunta ko dubu biyar basu kai ba saboda baya basu kudi a hannu sai dai ka gani a kasa. *** "Wai Ayaah ta zo inji Dani." Muryar wani dan almajiri ya karade tsakar gidan Honorable. Murja ce ta amsa masa saboda tana wanki a wurin. Dakinsu ta shiga ta sami Ayaah ta tura earpiece a kunne tana fama da koyon turanci a gidan rediyo. Makarantar gwamnati suke zuwa turancin babu sosai gashi tana son cigaba da karatu. Shi ne ta daukarwa kanta sauraron wani shiri da ake darusan turanci a gidan rediyo. "Helflesslyyy" "Aimlesslyyy" "Hofelesslyyy" Take ta maimaita kalmomin da ake fada da kokarinta na ganin ta tace turancinta. Sai karya murya take tana magana da hanci. Duka Murja ta daka mata a cinya ta tashi a zabure. "To tashi alhudahuda ana kiranki a waje. Ki je ki kore shi kafin Baba ya dawo wallahi" "Daga sallama sai kora saboda ba wurinki yazo ba?" Ta maida mata a tsiwace. "To kar ki kore shi. Ki bari Baba ya dawo ya tarar da kasurgumim kafiri a kofar gidan nan ki sha mamaki." "Kafiri?" Ayaah ta ce tana kai hannu kirjinta ta dafe. Murja bata amsa mata ba sai ta janyo hijabi ta dora akan rigarta ta fita da sauri. Ko ba Baban nasu ba bata so Anti Hasiya ta dawo daga wurin Innayo da ta sake tafiya yau ta ganshi. Karshenta ta fadawa baban nasu don ayi mata fada tunda ba kaunarta take ba. Tuno fadan da tayi mata rannan tayi ta dan yi murmushi. Ita bata ma san laifin da Antin tayi musu ba har ta tashi da tsanarta. Lallabawa zata yi ta soma yi mata biyayya ko don kayan daki... Ido, baki da hanci duk ta bude tana kallon Danliti a kofar gidansu. Bai tashi zuwa kawo jakar ba sai da aka sake samun rantsatsiyar motar kece raini a garejinsu. Ya sha shadda mai kyau sai daukar ido take. Kan nan nasa a kwance luf yana sheki ya sha man alayyadi wanda ya hada da ruwan turare dan d'uri domin ya danne warinsa. Shi da kansa ya san ya yi barna a zuciyarta saboda yadda ta kasa mallakar kanta a gabansa. "Malama Ayaah sai ki ka ganni a kofar gidanku ko?" Muryar da ya daddage ya kashe domin ta kara dadi ta shiga kunnuwanta wanda tsabar rudewa sai cewa tayi "cewa akayi in zo in ji Dani." Kansa ya shafa da dan murmushi "sorry you know rannan sunanki na tambaya ban samu na fada miki nawa ba muka rabu. Suna na Abubakar amma a gida kakanni suka saka min Danliti. Abokai na kuma suke cewa Dani. Sunan nawa dai na san ba zai miki dadi ba." "Nooo" Ayaah ta cije baki wurin fadar kalmar saboda ya gane ita ma ba baya ba a turancin. "Sunan da dadi mana. Dad dina sunanku daya amma Hon. Habu ake kiransa shi ma." "Nice" inji Danliti. Jakar ya mika mata tare da zuba mata karairayin yadda ya dinga nemanta bayan ya ganta a motarsa. Abin ya so daure mata kai saboda duk lissafinta jaka tana adaidaita sahu. Za ta iya rantsuwa bata shiga da ita motar ba. Saurin kawar da tunanin tayi tunda dai ta dawo sannan ga Dani a gabanta. "Ban san me ki ka yi min ba Malama Ayaah amma tunda muka rabu na kasa sukuni. Zuwa nayi da bakinki kiyi min bayani." Wayyo Allah. Ko balam-balam ba za ta gayawa Ayaah kumburi ba a wannan lokaci. Tsaf ta fahimci inda ya dosa. Jirkita idanu tayi tana masa fari. Zuciyarta fes sai farinciki Allah Ya kawo mata mijin aure tayi ta bar gidan nan. "Ni ban maka komai ba" ta fada tana dan tura baki. Danliti ya kunshe murnarsa zai mata magana wayarsa ta shiga ringing. Saboda rayuwar karya da cutar 'ya'yan mutane da suka saka a gaba wayar mai tsada ce. Dauka ya yi ya kara a kunne maganarsa na fita da sigar rarrashi ga wanda ya kira shi. Ayaah ta kusa kuka da hirar tasa tayi gaba ta gane da wa yake magana. "Kiyi hakuri ba dadewa zan yi ba." "Ba shekaranjiya na tura miki 50k ba?" "To, to...naji kiyi hakuri. Yadda ki ke so Honey haka zan turo." Ya dan saurara kadan sannan ya ce "har dubu dari biyu? Ok zan miki transfer." Wayar ya tura aljihu idanunsa a kanta yana murmushi. "Sorry wife dina ce." "Ok" ta amsa da yanayin ko in kula. Muryarsa a sanyaye ya ce "Ku mata sai da lallabawa. Bakwa son gaskiya ko kadan. Da an so nuna muku laifinku sai ku hau bori." "Wasu matan dai ba duka ba" Dariya ya yi "dama kun saba karewa juna." Wata wayar ta sake shigowa ya dauka murya a sake. "Gambo ka siyo min abincin?" "Yauwa dama cewa zan yi ka biya Yahuza suya tsire ka siyo na dubu biyar saboda tayi baki kuma bata yi girki ba. Abincin kuma duka friedrice mai hantar nan suke so plate takwas. Sai coleslaw da lemon kankana." Yawun Ayaah ya tsinke saboda tsabar yadda ranta ya biya har kamshin abincin kwakwalwarta ta zayyano mata. "Sorry fa na cika ki da waya. Yau Madam dina ke jin rigima shi yasa nace ku mata sai da lallabawa." Daga iya bayaninsa ta fahimci kamar baya jindadin abin da matar tasa take yi masa. Ga kudi zai tura ga abinci zai saya. Kuma a haka aka sake masa flashing ya dauka ya sake bata hakuri yana cewa yanzu zai tura. Danne danne ya yi a waya ya sake yin alamun kira ya ce ya turo. Da ya gama gabadaya ya sake fuskantar Ayaah. "To Malama Ayaah ni zan gudu gashi baki bani amsar tambayar da nayi miki ba." Wayarsa ce ta hau ruri ba kakkautawa tana soma magana. Da sauri ya dauka ya sake bada hakurin cewa gashi nan zuwa. "Madam ta matsa kambon zan tafi sai na sake kawo miki ziyara." Ranta bakikkirin da takaicin wannan mata mai hana ruwa gudu ta ce, "tafiya ko ruwa baka sha ba?" "Kar ki wahalar da kanki akwai a mota." Wata wayar ta shigo wannan karon daga garejinsu. Dauka yayi abokin aikinsa na sanar dashi mai motar yazo dauka amma an fada masa anje testing. Hakuri ya kuma bayarwa yadda ba za ta gane ba. Bayan mutumin ya ajiye wayar ya cigaba da magana ba tare da ya cire daga kunnensa ba. "Don Allah kiyi min tuwon ko leda biyu ne." "Haba Honey. Ko baki da lokacin yin miya ni dai kiyi tuwon zan yi miyar da kaina ko in ci da mai." "Babu komai Allah Ya kaimu weekend din." Ayaah taji tausayin Danliti kamar tayi kuka sannan ga mamakin saukinsa. Ji yadda yake bin matar tana wulakanta shi. Idan ita ta same shi ba zai rasa komai ba. Samun kanta tayi da tambayarsa. "Tuwo ka ke so ne?" "Na cire rai Madam ta gaji." Ayaah taji kamar ta nemota ya shako wuyanta. Sosai take jin tausayinsa. Ji wannan bata show ta hana shi hira da ita ma. Tayi sa'a ya karbi nambar wayarta dai. Yana tafiya don karfin hali ta ce, "Idan na shigo gidan nan sai kin raina kanki." Shi kuwa Danliti yana haduwa dasu Rabilu ya labarta musu yadda suka yi. "Irinsu zuma ne da wuta ake cinsu. Na darsa mata tausayina da yawan arzikina ga hakuri. Indai ba fyade kake son yiwa mace ba to da irin haka sai kayi mata wayo ta kawo kanta har ta roki kayi eh ya ne..." Dariya suka kwashe suna tafawa. Danliti ya kira matarsa da ko shekara basu yi ba ya kasheta da kalaman soyayya da alkawarin taho mata da tsire saboda laulayi da take. "Mugu dan masara. Ka gama da wata ka koma lallaba ta gida." Inji Rabilu "Ta gida ce dahir kaji. Wadannan kawai a samu garabasa ne a wuce wajen. Bari ma na tashi sai gobe." *** "Haba Malam. Wannan irin sakin baki tun ban kira ba." Cewar Munzali yatsansa na laluben nambar Mardiyya "idan ka fiye washe baki zan fasa kira sai gobe. Ina tsoron kar ka zubar mana da girma garin rawar kai" Ba don yana tsoron kar Munzali ya yi masa sanadin rasa abin da zai hada shi da Farha ba da a take zai rama. Kwafa ya yi kawai. "Fadi ko kaji dadi" Munzali ya sake kokarin tunzura shi. Abbati ya nuna masa gidansa ya ce "Ka kira ko ka kwana a waje yau. Ai dai ka san wancan gidana ne." "Gidan Hanne da 'Yashshafa ba." Karar da wayar ta soma yi alamun kiran ya shiga ne ya dakatar da Abbati daga bashi amsa. Mardiyya na taya Sauda tsifa kiran ya shigo. Har yanzu basu san me yake faruwa a gidan ba sama da abin da Suhaib ya fada musu. Wayarta da Saudan ke dannawa ta hau kuka ta mika mata. Ganin bakuwar namba sai ta dan jinkirta dauka har ta kusa katsewa. "Salamu alaikum" ta ce da siririyar muryarta. Munzali ya dan numfasa kafin ya amsa da murmushi "amin wa alaikum salam. Diamond girl ce?" Mardiyya ta tabo Sauda ita ma ta taso don jin waye mai kiran. "Diamond girl kuma?" "Eh. Mardiyya wadda muka hadu farkon satin nan a Diamond plaza Kaduna." "Waye don Allah?" Ta tambaya duk da ta so gane muryar. Sai dai bata fatan wata matsala ta taso sakamakon tsayuwarsu yin hoto a jikin motarsu. Abin da ta guda ne ya faru taji ya ce "dama ranar da ku ka yi hoto a jikin motarmu yayana yana ciki. Shi ne ya ce na kira ki zai yi miki magana. Shi ne ma dalilinmu na biyoki shagon." Mardiyya taji cikinta ya kulle. Daga daukar hoto abu na neman zame musu matsala kamar sun saci motar. Jiki a sanyaye ta ce "Hoto ne fa kawai muka dauka." "Mirror din bangaren direba yana rawa, motar ma a gareji ta kwana." Abbati ya zungure shi da gwiwar hannu yana balla masa harara "Sannu kanya uwar zuba. Haka kawai ka ke yi musu karya" Sai da ya toshe kan wayar sannan ya ce "ka kyaleni nayi yadda nake so. Kai dai ba Farha kake nema ba? To za ka samu in sha Allah." Cigaba ya yi da wayar sai yaji murya daban tana cewa "daga cin arziki sai ku ce an taba mirror? Ko an gaya maka ba za mu iya biya bane" "Ke kuma ya sunanki?" "Sauda" ta amsa a tsiwace "ai ba mu ya kamata ku nema ba. Mu ma muna da yayye sai mu hadaku dasu." Munzali ya kunshe dariyarsa. Da gani 'yan matan a tsorace suke amma suna gudun nunawa don kada matsalar ta girmi yadda take yanzu. "Zan ma fi son haka. Hadani da babba sai na bawa yayan nawa." Kashe wayar Sauda tayi ta rike haba "Mardiyya me yasa kika basu nambarki?" "Biyoni suka yi" ta iya cewa ba tare da tayi bayanin abubuwan da Mamanta tayi musu ba. Duk lalacewarta da kunya ta dinga kwaye mata baya. "To mu kaiwa Ya Suhaib?" Mardiyya ta mike da sauri "kina bashi zan tafi na kwanta. Haka kawai ki sa ya shekara yana yi mana mita" Dariya suka zauna yi wayar ta kara shigowa. Da sauri suka kaiwa Farha a kitchen. Takaitaccen bayanin kiran suka yi mata sannan ta amsa wayar da sallama. Sunanta Munzali ya tamnaya tana fada ya maimaita da cewa, "Ya Farha" kamar yadda yaji Mardiyya ta fada kafin ta bata wayar "ga yayana Abbati" ya karawa Abbati a kunne ya tashi. "Ya Farha" Abbati ya ambaci sunan a kasalance. To ita dinma kamar kannenta taji tsoron wannan binbini. "Yanzu shi kaninka da ya hadamu da kai ba arziki bane ace yana da motar da za a dauki hoto a jikinta?" Murmushi ya yi yana jin jikinsa sakayau kamar zai tashi sama. "Ni ban ce daukar hoton laifi bane." "To menene? Su Sauda sun ce wai mirror yana rawa. To ko dai motar gidanku ku ka dauko ta sami matsala ku ke neman kudin gyara a jikinmu? Ko irin 'yan karyar nan ne masu aro mota su je burge 'yan mata? Duk fa mun san halin ire-irenku." Sosai yadda take magana ya sanya shi nishadi. Jinginar da kansa ya yi da bayan bishiya yana sauraron muryar dake zagawa sassan jikina. "Da gaske Ya Farha." "Ka dena ce min Ya Farha ni ba yayarka bace." "Allah Ya Farha?" Abbati ya kuma fadan sunan da 'yar dariya. Ita ma Farha sai ta sauko da ta fahimci kamar zolayarta ma yake yi. "Ya sunanka?" "Kina iya kirana Abbati." "Sai dai in ce maka Uncle Abbati. Wai don Allah me yasa ka kira kanwata." "Neman rigima kawai Ya Farha. Yadda motar ta burgeku shi ne na fito ko Allah zai sa nima na burgeku ayi hoton dani sai kawai ina bude kofa ki ka gudu." Yana son ya kara da cewa ta gudu da zuciyarsa ya fasa. Ba yanzu ba. A gaba kadan za ta gane matsayin da ta taka farat daya a zuciyarsa. "Idan na baka hakuri magana za ta wuce? Idan aka ji a gida fada za'a yi mana." "Tun ranar ma na hakura Ya Farha." Dan hade fuska tayi ta ce "nifa ko rabin shekarunka ban yi ba ka ke ce min yaya." "Kin sanni ne? Ko kin san shekaruna?" "Na ganka lokacin da ka bude motar." "Wane irin mutum ki ka gani?" Ya tambayeta da dan tararrabi a muryarsa. "Mai kyau" ta ce kai tsaye. Zuciyarsa dokawa tayi da abin da bai san sunansa ba. Dumi ne ya lullube shi tun daga tsakar kansa har tafin kafa. Ita Farha tunda take bata taba hira makamanciyar wannan da saurayi na shi yasa take fadin duk abin da yazo bakinta. Kalmar karshe ce dai sai da ta fito ita kanta taji nauyinta. A karon farko taji kunya ta mamayeta. Harshenta ya yi nauyi a bakinta da kyar ta juya shi ta sake hada wasu kalmomin da suka fito kamar mai rada. "Ba haka nake nufi ba." "Bani da kyau kenan? Allah Sarki Abbati..." ya furta yana mayar da muryarsa irin ta mai shirin kuka. Da sauri Farha ta ce "kana da kyau mana." "To za ki yi hoton dani? Please Ya Farha." "Idan Allah Ya sake hadamu." Ta ce tana murmushi sosai. "Zai hadamu. Ina ji a jikina in sha Allah idan na sake zuwa Kaduna zan nemeki ki cika alkawari. Wace kala ki ka fi so?" Duk da ta soma rikicewa sa zantukansa amma ta bashi amsa. "Orange" "Ina fatan ganinki cikin kaya masu wannan kalar a haduwarmu ta gaba. Mu kwana lafiya Ya Farha." Da kyar ta iya cewa "Allah Ya bamu alkhairi." Kafin ya ce Amin ta kashe wayar. Juyawa tayi za ta bar kitchen din ta hada ido da kannenta sun zuba mata nasu idanun. "Ya ku ka kare ne Ya Farha?" Cewar Sauda tana kanne ido. "An kare a matakin ina karbar wayar nan in tura number dinta mana" Mardiyya ta bata amsa. Kasa ce musu komai tayi kuma bata ji tana son hana a tura nambarta ba. Bata san me take ji ba har suka fice suja barta. Haka ya karasa daren har ta kwanta tana tariyo hirarsu tana murmushin da bata san dalilinsa ba. Could this be love knocking at her door? Da ta kwanta ranar mafarkin Abbati ta dinga yi a daidai lokacin da ya bude motar nan ya fito suka gudu. Bambamcinsa da haduwarsu ya zahiri shi ne (Ya Farha) da ya dinga kiranta... * Bacci yaki zuwa kamar yadda Shazali ya yi niyya saboda aikin tunani da ya bawa kwakwalwarsa. Neman hanya yake komai kankantarta da zai dauwamar da su Munzali akan sana'ar da ya zama sanadin fadawarsu gareta. Abbati bashi da hankali da har zai tunkare shi da maganar tuba. Dariya ce ma ta taho masa da ya tuna yanayin fuskarsa a jiya da ya fada masa. Idan sun san wata basu san wata ba ai. Shi mutum ne da zai iya komai domin biyan bukatarsa. Da ya ce zai biyosu nadin sarautar tudun dafawa yazo nema kuma ya dace da samu. A sanin da ya yiwa Munzali tun kuruciya ya fahimci shi yaro ne da ya rasa sa ido da kulawar iyaye. Sai aka yi sa a sakacinsu ya cire masa tsoron sab'a musu da kaunar faranta musu. Yana da yakini mai girma cewa ko a gaba kwai ya fashe daga Munzalin har iyayensa ba za su ji ciwo kwatankwacin na Abbati ba. Sudaddiyar habarsa da babu alamun gashi ya shafa, murmushi na mamaye fuskarsa. Ya shiga har falon uwar Abbati. Kirjinsa har dokawa sai da ya yi saboda

Chapter 17 of 62