Share this page
amma wuyan Shazali da yake neman shakewa yana maganganu a zauce don duk tunaninsa da gaske ana can ana cin zarafin Qibdiyya ya saki farat daya. Idanunsa hawaye suke fitarwa ya tashi a firgice da tsanar aika-aikan da yaso yi ba don an dakatar dashi ba. Da kakkausar murya ya nuna Shazalin dake kwance sannan ya juya ga mutane biyun da suke tsaye a hagunsa. "Kai ne mutum na farko da ya fara sakamu cikin wannan masifa Shazali. Kuma har yanzu ka kasa hakura ka barmu mu koma ga Allah. Idan wani abu ya sami Qibdiyya wallahi zaku ga rashin ...." Bai sami damar karasa maganar ba a sakamakon ido hudu da suka yi da Alh. Tahir. Idanuwansa ne kadai suka kara girma a yayinda wani kololon abu mai daci ya taso daga cikinsa ya tsaya masa a wuya. Cikinsa ya kulle tamau har sai da shiga da fitar iska cikin hancinsa suka soma wahalar dashi. Kafafunsa da yake umarta da su zaga dakunan gidan su nemo Qibdiyya sannan ya fita kuwa suka ki motsawa. 'Zina 'yar aike ce. Duk inda ka turata zata dawo ta isar maka da sako. Bana yi mana fata domin dawowarta gidan nan ba zai taba zama alkhairi ba. Sai dai ina so ka sani koda tayi batan kai da sannu wata rana za a sami mai nuna mata hanya. A lokacin ko bata tuna cikakken sakon ba saboda shudewar lokaci, sallamarta kadai zata hargitsa tunaninmu. Na barka lafiya!' Ga Alh. Tahir kuwa, wannan sakon na Mami Khadija wanda ta tura masa tun washegarin ranar da Yumna ta fallasa komai ga Farha ne ya dawo masa tar. Ko batan wasali bai yi ba wurin tunano kalmomin daki-daki tamkar yanzu yake karanta su. Hantar cikinsa ta buga a tsorace da ya yiwa sakon fahimtar da ta dace dashi. Tun kafin ya bincika yaji ko akwai wanzuwar haramtacciyar alaka tsakanin su Abbati da 'ya'yansa ya gama shiga tashin hankali. Sanin cewa sun taba yin luwadi duk da a yanzu kunnuwansa sun jiye masa nadama da tubansu kadai ba karamin bala'i ya jefa zuciyarsa ba. Ko shi da zina ta gama bin jinin jikinsa ba karamin kyama yake yiwa wannan nau'in nata ba. Haka ya dinga jin kamar ana sassara adda a sassan jikinsa. Bai san wanne daga cikin masifun da suke gabansa ya kamata ya fara yiwa kukan bakinciki ba. Ganin Abbati a wannan gida da sanin waye shi ko kuwa ganin da Abbati ya yi masa da sanin nasa sirrin? Kallon kallo da suka tsaya yiwa juna ne ya bawa Comared damar tayar da Shazali ya zaunar dashi akan kujera. Da yaga kallon yaki karewa ne ya dubesu da mamaki sosai. "Alh. Tahir ko kun san juna ne?" Yawu yaso hadiya domin bayar da amsa amma ya laluba yaji babu danshi a bakin nasa. Kansa yaso kadawa shi ma yaji ya yi masa nauyi. Comared kawai sai ya ce, "Shi ne yaron da aka dauko 'yarsu ai domin ya amince da aikinka." Yana gama magana ya juya ga Abbati "wannan haukan da kayi a gidan nan baka ci bulus ba wallahi. Idan kana takama da zafin kai ka tarar da ubangidansa. Sai na daureka igiya tayi rara." A sanyaye Alh. Tahir ya daga kai ya kalli dakunan dake sama ya ce "Comared a wane daki yarinyar take?" Wani irin duba Comared din ya yi masa sai dai bai iya yin musu ba ya nuna masa kofar da hannu. Abbati ya kalla fuskokinsu duka babu digon nutsuwa. "Daukota ka zo ku tafi" "A'a Alh. Tahir, bangane ba. Ya zaka sallamesu batare da shawarta ta ba?" "Nawa ne zai fanshi uba da 'yar Comared? Nawa zan baku ku kyalesu har abada?" Sakin Shazali Comared ya yi ya taso har gaban Alh. Tahir cike da dumbin mamaki. "Alhaji ka san shi din da gaske?" "Da ne a wurina. Iyaka abin da zan iya fada maka kenan" Kai Comared ya kada alamun ya amince Abbati ya hau saman. A gurguje kuwa ya haye ya bude dakin da aka rufe ta waje amma key na jikin kofar. A tsakiyar gadon ya sameta ta dukunkune jiki tana bacci. Kwalla mai zafi ta zubo masa a lokacin da ya rankwafa ya daukota. Jikinta zafi rau da zazzabi. Yana dorata a kafadarsa yaji dumin zafin yana nasar nasa jikin. Ba shiri ya dagota ya dorata akan kafar damansa da ya dora a bakin gadon. "Qibdiyya. Bude idonki Papa ne" Da kyar ta bude idon saboda gajiya, yunwa da kuma aikin maganin baccin da Comared ya dura mata. Yadda kanta yake kifewa da kansa kamar 'yar maye ya sake daga masa hankali. Jikinta yabi da hannu daya ya mammatsa domin son ya farkar da ita. A nan ne kuma yaji ya tabo wani abu mai dan tauri a kugunta A razane ya dan daga rigarta ya ciro shi daga cikin siket dinta. Bakinsa da kyar ya iya hada tambayar wayar waye gareta. Cikin yanayin rashin kuzarin da take ta ce masa, "Cewa ya yi na baka" Aljihunsa ya tura wayar ya mayar da ita kafadarsa ya sauka. Idan ta dawo daidai zai tambayeta waye ya bata. Da ya sauko babu wanda ya kalla haka ya fita daga falon. Sai da ya isa bakin motar har ya kwantar da Qibdiyya a baya sannan yaji an ambaci sunansa da murya mai rauni sosai. Gabansa ya yanke ya fadi domin bai san da wane ido zasu kalli juna ba balle har su yi bayanin fidda kai. *** Minti goma sha biyar da isar Alh. Sadisu Nakano makarantarsu Abdul ta hargitse kamar ana cin kasuwa. Tun daga Principal har Masinja babu wanda bai shiga sahun zagaye makarantar ba ana neman Abdul. Principal din yafi kowa rikicewa don sai yau ya san akwai dan Alh. Sadisun a makarantar. Tun lokacin da yasa aka kawo shi makarantar dama ya bukaci a boye ko dan waye. Kudin da yake turowa domin kulawa dashi kuwa bai bambanta da wanda wasu iyayen kan yi ba sai ta adadi. Malamin ajinsu wanda kudin ke biyowa ta hannunsa yana isar da sako tare da yin tasa bushashar son rai. Daya daga cikin masu gadi ne ya ruga ya sanar da Principal bakon da suka yi tun kafin su shigo ciki. Principal din ya tashi da sauri ya shiga kankanta ofishinsa domin yana da labarin zuwan bazata da Alh. Sadisu ya kan yi makarantu. A zatonsa yau sallarsa ce ta kama don yasa rai da samun wani abu mai nauyi daga babban bako. Bai tashi shiga tashin hankali ba sai bayan sun gaisa Alh. Sadisu ya bukaci a kira masa dansa. Dan aike wato Masinjansa ya dawo da mummunan labari cewa wai washegarin dawowarsu makaranta ya koma gida bashi da lafiya. Daga nan aka soma diramar! Tashi Alh. Sadisu yayi tsaye cikin fushi da kaduwa ya hankada teburin Principal din dake gabansa. Ji kake kiyyyy, ya tafi ya daki bango. Abubuwan da suke kai wadanda suka yi zaman dakin kishiyar da ba a shiri da ita suka rufto kasa. "Bana son zancen banza da hofi. Yaron wajena nake nema Abdul. SS2 B yake. Sunan form master dinsu Sir Balarabe. Hostel dinsu kuma Sardauna House. Ya ce min a kwanar da gadonsa yake akwai Victor da Faisal" Jinjina kai Masinjan da Principal suka yi na mamakin yadda ya rike komai da ya shafi dansa. Direbansa da PA da suka zo tare basu dauki hakan komai ba. Saurin rike abubuwa suna daga cikin manyan jarinsa da suka kawo shi inda yake yanzu. "Ranka ya dade zauna bari naje ajinsu da kaina na kirawo shi. Ina jin sakon ne bai fahinta da kyau ba." Principal dai bai sami damar dawowa ba sakamakon matsalar da ya tarar. Lokacin ba a tashi daga aji ba. Yana zuwa Monita da sauran 'yan aji suka tabbatar masa da cewa kamar yadda aka bukaci su dawo asabar saboda damina ana bukatar gyara makaranta, Abdul ya dawo amma ba a wayi garin lahadi dashi ba. "Me yasa ban san labarin nan ba sai yau?" Cewar Principal yana gumi tare da tsare malamar dake ajin tana koyarwa a lokacin. "Ranka ya dade Mal. Balarabe ya kamata ka tambaya. Nima ban san komai ba" Tare da Monitan ajin da Assistant dinsa ya tafi staffroom din malamai maza. Yana shiga ya kira sunan Mal. Balarabe sai dai nan take aka sanar dashi baya nan shi da wasu malamai biyu abokansa. "Bangane ba? Ina ya tafi ana cikin wannan yanayin?" Wani malami ne ya bashi amsa da cewa "babu yadda za ayi ya zauna alhalin duka makaranta ta dauka cewa dan Alh. Sadisu ya bata." "To shi ya batar dashi da zai gudu?" Ya tambaya a fusace. Malaman dai basu ce komai ba tunda basu san me yake faruwa ba. Haka ya koma ofishinsa da yaran nan biyu cike da fargabar yadda zai fara yiwa Alh. Sadisu bayani. A inda ya barshi tsaye ya dawo ya same shi yana kai gauro da mari. Yana ganinsa kuwa ya ce ina Abdul. "Yallabai ka zauna kaji daga bakin yaran nan. Daga nan sai mu san abin yi." Rainin wayo Alh. Sadisu ya dauki zancen Principal din. Sai dai kuma ance idan rakuminka ya bata ka duba har cikin hudar allura. Bisa wannan dalilin ya saurari Monitan wanda ya maimaita sak abin da ya fadawa Principal. "Yanzu kai baka ji kunyar cewa na tsaya jin wannan wasan yaran ba? Cewa zaka yi makarantarka babu tsaro har ana shigowa a sace 'ya'yan mutane. To wallahi banda dana. Kai, ina tsammanin baka gane ni ba ko? Suna na Alh. Sadisu Nakano kuma ko uban mutum ne yake mulkin kasar nan bai isa ya hanani koya masa hankali ba." Ya nuna kofa da hannu "kaje ka nemo maigadin da ya kwana ranar asabar din. Da malamin ajinsu duk inda yake..ku hadu ku nemo min dana" Da Principal da mataimakansa biyu tare da malaman da suka yi cirko-cirko a kofar ofishin kowa hankalinsa ya tashi. Alh. Sadisu ma dauriya kawai yake domin zuciyarsa tuni ta fara karanto masa sunayen abokan hamayyarsa wadanda zasu iya dauke masa da a matsayin fansa ko garkuwa. "Sir?" Kowa juyowa yayi don jin wa dalibin dake matsayin mataimakin monita yake kira. Kai tsaye Principal din nasu yake duba ya ce, "Ina jin fa ba bata ya yi ba. Tun kafin hutu yawanci da daddare ranar juma'a Sir Balarabe yana zuwa kiran wasu a hostel. Yawancinsu da safe suke dawowa. Wasu kuma sai lahadi..." Ya kalli monitan "ba shi ne muke cewa ko lesson ake musu banda mu ba?" Da ace kunnuwa suna jin gaibu yau da ofishin Principal dinnan ya cika da bugun zukata. Duk wani mai hankali a cikin wurin tunaninsa ya karkata daidai da na uban yaron da ake nema. Wannan kuwa ba bakon abu bane tunda akan ji labarai makamantan haka a makarantun kwana. Cijewa Alh. Sadisu ya yi ya daure ya tambayi yaron ko mutum nawa ne suka bar makaranta rana daya da Abdul. Babu musu kuwa ya lissafo masa su biyar. "Amma sauran hudun duka ranar lahadi suka dawo da daddare. Shi kadai ne Sir Balarabe ya ce gida ya koma" Cikin karaji da gigita Alh. Sadisu ya ce "A nemo min Balaraben da masu gadi" "Sir Balarabe ya fita" "Mal. Bawa maigadi baya nan" "Malaman dake abota da Sir Balarabe ma basa nan" Wadannan ne amsoshin da suka biyo bayan umarnin da Alh. Sadisu ya bayar. Da aka gama fada dariya ya kwashe da ita. Wata irin dariya mai dauke da bakinciki da bacin rai gami da tsoro. Kamar yadda ya fara ta kuma a bazata haka yayi dif ya daina lokaci guda. Kallo mai ban tsoro yabi mutanen da suke gabansa sannan ya daga waya ya kara a kunne. "Ku fara aikinku" Cikin kankanin lokaci gabadaya makarantar ta kasance a zagaye da 'yan sanda. Wasu suka shigo aka fara yiwa duk mai ruwa da tsaki tambayoyi. Ya kira su ne tun kafin Principal din ya dawo daga binciko masa me ya faru. Ma'aikatan jarida kama daga na gidajen rediyo zuwa tv suma suka soma dafifi. Alh. Sadisu ya tsaya a kofar ofishin Principal da na'u'rorin daukar magana kala kala a saitin bakinsa ya ce, "Ba roko nake ba shawara ce. Na bada awa biyu kacal a dawo min da dana inda aka dauke shi." *** Ayaah, Murja da Ummita ne suka tashi daga gaban mahaifinsu da Abdulkarim bayan sun gaishe shi. Kafin su fita ya sake jajantawa Ayaah abin da ya faru jiya tare da shawara gareta da 'yan uwanta akan tsare mutumci saboda gurbacewar zamani. Bayan sun koma wurin Anti Hasiya aikin gabansu suka cigaba. Ayaah kuwa kusa da antinta ta koma ta kwanta ta rufe ido. "Dalla can tashi, ai kin san yau kece da wanke-wanken safe" Baki Ayaah ta turo ta tashi rai a bace za ta soma gunaguni Anti Hasiya ta ce ta koma ta kwanta. "Haba Murja! Yanzu har kin manta abin da ya sameta jiya kike kira mata wanke-wanke? Duka duka yaushe garin ma ya waye?" Murja da Ummita suka dubi juna suka bushe da dariya. Karfe goma shadaya harda minti bakwai. Shi ne Antinsu take cewa yaushe gari ya waye. Sannan bata tashi ba Ayaah da Murja suka yi fada kamar zasu ari baki a kofar bandaki. Ita kuma tana tasowa ta cigaba da lallabata. Labarin fadan suka bata ta koma yiwa Ayaah kallon tuhuma. Amma da yake ba a cinyeta da baki sai da ta magantu. "Dauriya ce fa kawai nake Anti amma har yanzu ban dawo daidai ba. Kuma bana son ki shiga damuwa shi yasa nayi kokarin dawowa daidai." "Yanzu tsiwa ce daidai dinki Ayaah? Allah nagode Maka" cewar Anti Hasiya tana dariya. Raharsu suka cigaba da yi cike da so da kaunar juna. Anti Hasiya ta dubesu daya bayan daya ta sake mika godiyarta ga Allah. Irin wannan zaman na ahali daya kuma da zuciya daya tayi ta buri. Sai gashi lokaci guda Allah Ya amsa addu'o'i'nta. Kan yaranta ya hadu sannan ita ma ta sami rabon da zata kira nata. Uwa uba an Abbas yana shirin samun lafiya da yardar Allah. * "Ina ta sa ran jin ka tambayeni me yasa na nacewa gidanka naji shiru" Abdulkarim ne ya yiwa Honourable tambayar bayan sun gama gaisawa sannan ya fada masa daren yau ake bukatar kwantar da Abbas a asibiti. Washegari ake sa ran yi masa aikin da safe. Likitan da zai jagoranci aikin ya iso Kano. Da yake Honourable ya fishi kwarewa a sakin magana sai cewa ya yi "Wata kake so cikin 'yan matan gidana ko?" Yadda ya yi maganar kai tsaye ya bawa Abdulkarim mamaki domin bai yi maganar da kowa ba sai zuciyarsa. Zaro idanun da ya yi ba tare da ya ce komai ba yasa Honourable bude baki. "Don Allah wai da gaske kake?" Kwarjini Honourable ya yi masa fiye da kullum amma ya san ranar wanka ba a boyon cibi. Tunda dai Ummita ba za ta aurar da kanta ba dole ne ya fadawa mahaifinta. "Da gaske nake" Honourable ya gyara zama yana dariyar kunya da takurar da yake gani a tattare da Abdulkarim. "Murja dai an kawo kudinta. Ya rage Ayaah da Ummita" Abdulkarim ya dan tura hularsa baya kadan ya ce "Umminmu din nake so. Allah Yasa wani bai rigani ba. Kuma don Allah kada ka sako zancen shekaru wallahi da sauran tafiya kafin nayi hamsin ma." Dariya sosai ta kama Honourable. Farincikinsa ba zai misaltu ba. Wato da gaske bayan kowane tsanani akwai sauki. Sai dai wani hanzari ba gudu ba... " Abdulkarim anya baka yiwa Ummita nisa ba. Ba batun shekara nake maka ba. Ina nufin a zamantakewa ta wayewar rayuwa da arziki. Ina jin tsoron kada ku sami rashin daidaito a dalilin ..." Dakatar dashi Abdulkarim ya yi ya nuna masa rashin jindadin furucinsa. "Ka sanni kafin na zama wannan Abdulkarim din. Duk abin da na samu a sakamakon kusanci da kai ne a lokacin da nima ban dace da kusantar mutum irinka ba. Amincewarka nazo nema domin na nemi soyayyarta. Ba zan so ayi mata fin karfi ba saboda wani abu da na samu na takaitaccen lokaci" Fuskar Honourable dai babu komai cikinta sai annuri. Tashi ya yi ya ce masa idan sun gama shiri anjima zasu tafi asibitin zai kira shi. Abdulkarim sai ya shiga rudani ya ce "maganar Umminmu din fa?" Wata dariyar Honourable ya sake yi "Naga dai yanzu ba lokacin tadi bane da rana tsaka amma dai bari na turota kwashe kwanuka." Kunya ce ta kama Abdulkarim amma abinka da manya sai ya fuske. Ba jimawa kuwa yaji sallamarta a kofar falon. Da ya amsa ya yi zaton zata shigo amma shiru har kusan minti biyu. Ga alamun tsayuwarta a bayan labule yana gani amma taki motsi. Babu mamaki babanta ya fada mata yadda suka yi. Banda haka me zai hanata shigowa don yana ciki? "Nifa dan gata ne a gidan nan. Idan baki shigo da kafafunki ba ko Ayaah na kira zasu hadu da Murja su daukoki a ka" Ja da baya tayi cike da tararrabin me ya kamata tayi. Bayan kusan sakan talatin ta matso jikin labulen ta damke shi da hannu ba tare da ta bude ba ta ce, "Ni wallahi kunya nake ji" Murmushi ya sami kansa da yi ya taso ya dawo bakin kofar ya tsaya ta yadda suke iya ganin shatin juna. Ummita bata ma san ya iso wurin ba sai da taji amsarsa a kurkusa. "Banda abinki idan baki ji kunyata ba ai sai ki sa na fara kokwonton zabina" A wautarta ji tayi amsar tasa bata cika ba. "Ni kadai ce mai jin kunyar?" "A iya sanina dai mata sun fi son namiji mai karancin kunya akansu." "Wai naga kamar 'ya nake a wajenka" "Wai idan kin dauka kallon 'ya nake yi miki ki ajiye." Hannu kawai Ummita ta kai ta rufe bakinta saboda murmushin da ta kasa daina yi. Gabadaya nauyinsa take ji sannan tana mamakin yadda ya sake abinsa ya ma manta ita wace ce. Duk da cewa ba yau ta fara sanin soyayya ba, wannan tazo mata da salo mai girman da yafi karfin shekaru da tunaninta. Zurfafa da tayi a tunani ya bashi damar kallon irin tsayuwar da tayi. A jikin kofar ta dan jinkina sai gefen labulen da ta rike amma taki budewa. Kusa da inda hannunta yake ya kama bata lura ba sai ganin fuskarsa tayi ta bayyana a gabanta. Ja tayi da baya zata gudu ya girgiza kai wanda yanayin fuskarsa da tayi mata kwarjini ta hanata kin bin umarninsa. "Gajiya nayi da hirar bayan labulen kamar wani mara gaskiya" "To ka koma zan shigo na zauna" "Na yafe. Zan dawo anjima idan za a kai Abbas asibiti." "To Allah Ya kaimu." Ta furta da azama tana son tafiya. "Dawo Aminatu ban sallameki ba tukunna." Dagowa tayi a hankali da niyar kallonsa ta kasa. Ya san mamakin sunanta da ya fada take yi. Shima ya yi mamakin rashin mantawa. Kodayake bai taba manta duk abin da ya shafi Honourable ba. "Nace ba, wai nayi miki kuwa?" "Innalillahi ..." Furta tare da rufe fuska tana dariya kasa-kasa. "Ya kike ja min Innalillahi? Nayi?" Dariyar dai ta cigaba da yi cike da kunya ya ce "in dauki wannan kunyar a matsayin amincewarki kenan?" Da ka ta amsa masa. "Nagode Ummi-ta. In sha Allahu ba zan baki kunya ba daga ranar da zama ya hadamu a inuwar aure." Kafin ta daga kafa har ya fito. Kunya bata barta tayi masa sallama ba. BABI NA ASHIRIN. *** Kan Abbati a kasa ya kasance har Alh. Tahir ya isko shi a bakin motar. A bakinsa wani irin daci yake ji mai naci domin duk yadda ya kai ga hadiyar yawu yaki wucewa. Halin da ya tsinci kansa baki ba zai taba iya fada ko ya kwatanta ba. Zuciyarsa ce kawai take harbawa fiye da ka'ida. Bai ga wata maraba tsakanin sanin sirrinsa da Alh. Tahir ya yi ba da Farha. Tunda uba ya sani, me zai hana 'yar ta sani? So ya yi su rabu asirinsa a rufe. Gara ta dinga tuna shi a matsayin mayaudari akan fasiki...fasikin ma kuma manemin maza. Firgici da tashin hankalinsa ko kusa basu kai rabin abin da Alh. Tahir yake ji a dukkan gabbansa ba. Ko tafiyar da yake ba zai iya cewa ga da yadda aka yi yake iya daga kafa ba. Ya dai dawo hayyacinsa da yaga bai fi taku biyar ya rage tsakaninsu ba. "Abbati..." A tunanin Abbati maganar da Alh. Tahir zai yi masa ba za ta wuce tuhuma akan 'ya'yansa ba. Saboda haka bai bari ya kai karshen abin da zai fada ba ya ce, "Babu abin da ya taba mutumcin su Farha a a hannunmu. Ban kuma kawo kaina da niyyar aurenta ba kamar yadda yake a wurin Munzali sai da muka tuba" ya ciji lebensa na kasa wanda yake nuni da karayarsa yayinda ya cigaba da cewa "mun yi nadama, mun tuba har muna shirin barinsu kafin duniya taji a dalilin barazanar da Shazali yake yi mana...amma ban san me yasa Allah Yasa asirinmu ya tono ba a irin wannan yanayi." "Asirina ne ya tono ba naku ba Abbati. Ni Allah Ya gwadawa IkonSa ba kai ba." Da sauri ya daga kai ya dubi Alh. Tahir. Shi ma din Abbatin yake kallo. Idanunsa sun cicciko da kwallar da ya manta rabonsa da yinta. Haka ya cigaba da magana jikinsa yana mutuwa da kowacce kalma. A jikin motar ya jingina saboda babu sauran karfi a tare dashi. Ya daure dai ya fada masa cewa maganin bacci ne aka shakawa Qibdiyya saboda haka ya kwantar da hankalinsa zata dawo daidai nan da awa daya ko kasa da haka kamar yadda Comared ya fada masa. Yana ganin yadda Abbati ya shafa fuskarta cike da kulawa. A ganinsa wannan ita ce soyayyar iyaye da 'ya'ya ta gaskiya ba wadda yake ikirarin yiwa nasa ba. Zantukan da suka biyo baya kuwa ya yi su ba a cikakken hankalinsa ba. "Ban taba tuba ba. Shekara da shekaru Khadija tana kuka tana hakuri dani. Sai yanzu ne ma wani dan dalili yasa ni nadama. Bukatar kawar da wannan dalilin ce ta kawo wannan lokaci. Kafin zuwanka ina tunanin akwai lokaci a gaba da zan sami damar yin hakan in tsufa ya kamani. Ashe lokacin zai biyoni yau? Suhaib ya sani! Farha ta sani!! Lilu ma ya sani!!! Amma hawayen 'ya'yana dana mahaifiyarsu bai sa naji lokacin tubana ya yi ba. Ba don abubuwan da suka faru ba a ciki da yanzu kila na amince anyi..." Karshen maganar nauyi ya yiwa bakinsa dole ya datse zancen. Kamar saukar guduma maganganun suka dinga shigar Abbati. Farha ta san mahaifinta yana zina? Ko shi ne musabbabin ganin canjin da ya yi a gareta kwanakin baya da Alh. Tahir ya dawo gida suna wurin? "Ban taba mu'amala da maza ba. Na yau din ma dalili ne" kamar an matsi bakinsa ya fadawa Abbati abin da yasa ya zo Kano yau da kuma dalilin nadamarsa. Wato sanin da Farha tayi cewa yana neman aminiyarta wanda da ace aurenta yake nema kadai ma da sauki. "Mayafin da ya lullube soyayyar da 'ya'yana suke yi min naso yayewa. Na tabbatar fasa auren Yumna zai iya dawo min da martabata a idanunsu. Ashe Yumna ba ita ce matsalata ba. Ni ne matsalar kaina. Wallahi Abbati ina jin kamar na bude ido naji an shafeni baki daya." Shi dai Abbati kasa cewa uffan yayi saboda shi ma din mai laifi ne. A nutse dai ya saurari dukkan maganganun Alh. Tahir wanda ya sake dauka a matsayin izina. Babban mutum, mai kudi, iyali, da kima a idanun al'umma ya tasa shi a gaba yana ta sumbatu. Ashe idan basu tuba ba nan gaba suna da rabon ganin rana makamanciyar wannan ko ma wadda ta fita muni. Duk wata daraja da kimarsa shi da kansa yake jin sun gudu sun bar shi a dalilin haduwarsa da Abbati a gidan nan. Zuciyarsa har lokacin bata huta da kakkarfan harbin da take yi masa a kirji ba. Wace irin masifa ce tafi wannan? Ya aka yi bai ji girman laifinsa ba a lokacin da 'ya'yan cikinsa suka san sirrinsa sai yanzu a gaban mutumin da bai riga ya zama surukinsa ba? Kalmar surukin da ya ayyana a ransa ita ta sanya shi yin wani tunani. Babu bata lokaci kuwa domin tabbatarwa ya nuna saitin jerin wasu motoci guda hudu ya ce, "Don Allah taimaka ka miko min wayata a cikin mota in kira likitana" Durkushewa ya fara yi wanda hakan yasa Abbati yin saurin zuwa wurin motocin ba tare da ya tambayi wacce bace cikin hudun. Da d'ai-d'ai ya dinga bin tagogin motocin yana lekawa ko zai hango

Chapter 50 of 62