Share this page
ya kara bashi tabbaci. "La haula wala quwwata illa billa. Abba? Ya Yumna?" A gigice ya mike da ya tuna ma'anar sakon karshe. Indai Yumna ciki ne da ita kenan komai ma ya faru tsakaninsu. Zuciyarsa a take ta tashi saboda kyamar hakan da yaji. Ya fada bandaki ya amayar da duk abin da ke cikinsa. Baki kawai ya kuskure bayan ya gama ya fita daga dakin. * Duk gidan Alh. Tahir babu wanda Jiddo ta tsana a tsukin kwanakin nan kamar Suhaib. Da can da baya shiga shirginta mantawa ma take dashi. Iyakarsu da juna idan zasu wuce kuma suna kusa taji sautin tsakinsa. Tsakin da tun aurenta da ubansa take ji kuma bai taba damunta ba. Ba kuma wani abu ne ya janyo yake yi mata shi ba sai kamasu da aka yi a daki wanda shi ma yaje wurin. Abubuwan da suka biyo baya da auren nasu sun taimaka kwarai wurin dasa masa tsanarta. Sai gashi bayan shekaru sun shude ta sake bude kofar sabunta zarginta a zuciyarsa. Alal hakika bai yi wani mamaki ba lokacin da yaga tana shirin barin wurin dinner da makaniken nan. Sanannen abu ne cewa indai bawa ya kulla aminci da zina to ba makawa sai ta kawo masa ziyara watarana. Mahaifinsu yace yaji ya gani wurin sabon Allah. Dolensa kuwa ya girbi shukar da yayi ko ba dade ko ba jima. Shi dai adduarsa kullum bata wuce Allah Ya tsare masa mahaifiyarsa da kannensa. Sallama hade da kwankwasa kofa ya yi da ya isa bangarenta. Mai'aikinta ce ta amsa ta bude masa. A hakimce kan two-seater yaganta tana waya. Ganinsa a tsakar falonta ya mugun firgitata. Lafiya ko rashinta basu taba kawo shi inda take ba. Yau da yazo ta san lallai akwai matsala. Wayar faduwa tayi daga hannunta ta kuma gyara zama ba shiri. "Nambar makaniken nan zaki bani." Cewar Suhaib, fuska babu annuri. Jiddo sai ta daburce duk saboda gudun tonon asiri. A haka ta cije ta harare shi. "Rashin kunyarka ta isheni Suhaib. Idan ban ci darajar shekaruna ba ai ya kamata in ci na matsayina a gidan nan." Surutunta bashi da gurbi a kwakwalwarsa balle yaci darajar neman ta maimaita domin ya fahimta. "Zan samu ko in tafi?" Rainin wayonsa ya sake bata haushi. Wato ma bai ji abin da tace ba bare ta san ran zai yi aiki dashi. Yatsina fuska tayi ita a dole bata san me yake nufi ba ta ce, "Wane makaniken?" Wannan karon Suhaib ne ya hango rainin wayonta. Sai da ya dage girarsa daya sama ya murmusa. Harsashi zai hada mata a wurin Alh. Tahir don ranar tada bom din bata zo ba. Wannan ba aikinsa bane. Lokaci da talalar Ubangiji ga bawan da ya dage akan aikin sabo zai cimmata wataran. Wata irin murya ya yi amfani da ita sai a rantse sangartaccen da ne a gaban mahaifiyarsa yana zuba shagwaba. "Don Allah ki bani Anti Jiddo." Ita kanta da taji muryar sai da ta kara tsorata fiye da farkon zuwansa. Ta san dole akwai abin da yake nufi da haka. Ba dai ta zata maigidan ne da kansa ya shigo falon ba tare da ta kula ba sai yanzu. Ran Alh. Tahir fari kal kamar takarda yau ga Suhaib a bangaren Jiddo. Yadda yake magana ya nuna masa sun jima da daidaitawa. Ya dinga zuba murmushi kamar sakarai har yana mantawa da halin da yake ciki. "Wato kin saka danki a daki yana ta shagwaba aka rasa wanda zai amsa min sallama ko? Wai ma mene ne yake faruwa zan yi alkalanci." Suhaib ya yi saurin bashi amsa kafin ta sami damar juya zancen. "Nambar makanikenta na Kano nake so Abba shi ne taki bani wai sai na yarda gobe zan rakata shopping" Wohohooo. Alh. Tahir da shi ma ba wani samun hira daga Suhaib din yake ba duk irin son da yake masa sai yaji kansa ya yi gingirin. Murmushi yaki yankewa a fuskarsa. "To ai sai ka amince dan Jiddo" 'I reject it! Tuff, tuff' cewar Suhaib a zuci yana jin tsigar jikinsa na tashi saboda an kira shi dan Jiddo. "Na amince. Don Allah ki bani" Tsabar mamaki sai ta kasa cewa komai banda kai da take gyadawa kamar kadangaruwa taga manja. Sunan Danliti ta lalubo tunda Alh. Tahir ya musu karan tsaye yaki tafiya. Dama al'adarsa ce shiga bangaren kowa idan zai fita ko ya dawo. Bayan Suhaib ya kwafe nambar ne Alh. Tahir yake tambayarsa me zai hada shi da makanike a Kano. "Wani case ne babba ya taso tsakaninmu dashi." Alh. Tahir ya dan bata fuska "Ban gane ba? Wani abu ya yi maka?" Suhaib ya yi hanyar kofa yana cewa "a'a, motar Anti Jiddo yaso lalatawa ba don Allah Ya kaini wurin da suke ba da wuri." Sautin cikin Jiddo har kunnuwansu saboda tsoro. Suhaib kuwa ya fice yana jin Alh. Tahir na tambayarta me ya sami motar har aka nemo makanike shi bai sani ba. Rantse rantsenta kadai ya jiyo ya kara gaba don bashi da lokacin jin karairayin da zata yi. * Lilu kuma da ya fito bai zame ko ina ba sai bangarenta Mami Khadija. Ya yi zaton samunta ta kwanta ko shirin kwanciyar kamar kowa sai yaga sabanin haka. Laptop ce a gabanta ga tulin takardu ta soma barbazawa tana aiki. Gaban table din da aka yi mata musamman saboda aikinta yaje ya mika mata wayar. "Ga wayar mijinki idan ya dawo ki bashi." Tun shigowarsa take kallonsa amma furucinsa yasa ta koma yi masa firgitaccen kallo. "Mijina? Mijina fa ka ce Lilu. Ko dai nice ban ji ba da kyau?" Ta furta a sanyaye. Lilu ya cije lebe cikin bacin ran tuna abubuwan da ya gani. "Mijinki maigidan nan nake nufi." Laptop din ta tura gefe ta tashi tsaye tana dubansa. "Ko agolanci nazo da kai gidan nan bana tunanin za ka iya budar baki ka kira wanda nake aure Mijina." Duk shashancin Lilu bai taba zina ba. Mami Khadija ta dasa musu tsananin kyamar wannan laifin tun basu san kawunansu ba. Yafi kowa fitina a gidan amma akwai iyakokin da ko a mafarki bai hango kansa da ketaresu ba. Kalaman Mamin murmushi suka saka shi. "Mamina kinfi karfin haka a wajena. Wallahi indai mai mutumci wanda ya san darajar kansa data iyalinsa kika aura ni mai tayaki yi masa biyayya ne." Da ya gama maganar ya dora wayar a kusa da tata ya fice da sauri. Zama a gabanta karyar masa da zuciya zai sake yi ya kaishi ga kuka. Tausayinta yake ji sai dai kuma jikinsa ya bashi ta jima da sani. A hanyar zuwa dakin ya dinga tuno irin nasihunta da fada da suna yara har kawo ga yanzu. Kusan komai yafi ta'allaka akan zina. 'Ba halinsa bane!' shi ne abin da Mami Khadija ta fara fadawa kanta a lokacin da taji kamar ta kwashe shi da mari. Kwalla ce ta taho mata saboda jikinta yana bata da wuya idan ba sirrin boye ne ya fito fili a wurinsa ba. Yadda Farha ta sani bayan Suhaib gashi yau shi ma ya sani. A ranta ta dinga tsarkake Mulkin Ubangijin da ya haramta zina. Hakika wannan kaba'ira tana zubar da mutumcin mai mutumci. Yau Lilu da bakinsa yake kiran mahaifinsa da wani suna ba Abba ba. Kallon wayar tayi sau daya ta kawar da kanta. Alh. Tahir na shigowa bangarenta daga wurin Jiddo ta damka masa wayar daga bakin kofar da ta tare don kada ya shigo ciki. "Lilu ne ya kawo" Gumi a take ya tsatstsafo akan goshinsa. "Ya ce wani abu ne?" Mami Khadija ta kalle shi ido cikin ido ta ce "ya ce ga wayar mijina na bashi idan ya dawo" Alh. Tahir ya karkata gefen fuskarshi gareta yana son tabbatar da abin da ta ce. "Mijinki? Dani yake?" Cikin ko in kula ta ce "a iya sani na ba." Daga haka ta rufe kofarta ta barshi a wurin yana jinjina girman abin da yake samunsa a tsukin nan. BABI NA GOMA SHA UKU. Naji korafe korafe kai tsaye da ma na aike kala kala game da dorawa Lilu laifin da ba nasa ba. Na so kamewa daga bayar da amsa sai dai ku gani a rubuce. To amma wasu har ikirarin barin karatun suke. Jama'a idan kun barwa Batul labaranta ina ta kama? Sakon da nake fatan Allah Ya bani ikon isarwa bai je ko ina ba kenan. Ya zama dole na magantu. Kafin na fara wanke kaina, ina so inyi amfani da wannan damar wurin yi muku godiya. Akwai gajiya matuka idan marubuci yana daukan dogon zango kafin ya yi post. Sai dai kamar kullum hakuri dai zan cigaba da baku. Ba da gangan bane. Yau da gobe ce wadda take nukurkusar daukacin al'ummar kasar duniya ba ma kasar nan ba. Allah Mabuwayi Ya kawo mana saukin lamura. Amin To mu koma ga labarinmu. Kwanakin baya korafin akan yawan wahalhalun Innayo da rashin cin moriyar guminta ne suka yi yawa. Wasu har suna ganin kamar zan sagar musu da gwiwa wajen kulawa da amanar da Allah Ya bamu ta zuri'a. Ko daya ba nufina ba kenan. Labarin nan kacokan ban yi shi domin tsantsar nishadi ba. Wasu lamura nayi ta nazari a rayuwarmu shi yasa nake son yinsa ta yadda zaiyi kamanceceniya da zahirin rayuwa. Akwai Innayo bila'adadin a cikin al'ummarmu. Mace ta wahaltawa miji ta kuma wahaltawa 'ya'ya. Amma a karshe haka zata koma ga Allah da bakincikin dukkansu. Ta rayu a talauce ta mutu cikin talauci. To amma fa shafin rayuwarta ba zai kare a wurin Maqaginta ba muddin ta koma gareshi tana mai gaskata kadaitar mulkinSa. Daga lokacin ne ma zata fara shan romon ladan ayyuka da hakurinta har zuwa tashin qiyama. Sai dai taji ance ta wuce Aljanna gidan dauwamamen farincki. Game da Lilu kada mu manta su waye iyayensa. Uba mazinaci wanda har yanzu babu wata kwakkwarar nadama a tattare dashi. Shin idan zina bata dawo masa a inda zai yi masa ciwo ba kuna ganin zai san Annabi ya faku? Zai ji ciwon da iyayen 'ya'yan da ya mu'amalanta suka ji? Zai yi nadamar ayyukansa har ma ya tuba? Sanin tsohuwar sana'ar maneman 'ya'yansa ba ta da babban tasiri indai ba an riga an daura aure ba. A yanzu kam ba zai wuce ya soke auren ba ya cigaba da yawonsa. Wanda kuma duk ya yi zina da ahalin wani shi ma sai anyi da nasa. A gefe guda kuma mahaifiya ga Lilu mace ce tagari. Uwa ce da ta amsa sunanta wurin tarbiyya da yawan yiwa 'ya'yanta addua. Ga Ubangijin da take mikawa lamuranta Mai ji ne ga kukan bayinSa. Al Hayyu, Al Qayyumu ba zai bata kunya ba. Gamu ga Sarkin da baya saba alkawari. Mahaliccin da Adalci ya kasance cikin suffofinSa. Duk da cewa labari ne amma ina son tunatar damu uwaye karfin addua. Tabbas alkawarin Allah na dawowa mazinata da sharrinsu ta hanyar da zasu koka ba zai tashi ba. Sannan kuma adduar Uwa ta gari ga 'ya'yanta wannan kaifiyan ce. Indai haka ne kuwa to lallai Alh. Tahir sai ya yi kuka akan sharrin da aka yiwa Lilu. Sannan Mami Khadija sai ta kara mika wuya ga Allah a yayinda Ya kubutar mata da danta daga dabaibayin da bai isa ya kwance ba. Ya Rabbi ka karawa Annabinka daraja, Ka azurta shi da kololuwar daukaka. Amin. *** Mami Khadija kiran Lilu tayi bayan ta rufe kofarta. A zatonta Alh. Tahir ya bar wurin ashe yana tsaye. Kafafunsa sun yi masa nauyi ya kasa dagasu. Lalacewarsa bata yi kamarin da zai iya cigaba da jure juya baya daga tsatsonsa ba. Bazuwar zancen nan zuwa kunnuwan ragowar 'ya'yansa ba karamar barazana bane ga mutumcinsa a idanunsu. Shi kuwa zai iya komai domin kare wannan martabar. A tsarinsa miji ko mata kada ya fishi girman masauki a zuciyarsu. Yana son ya zama babban amininsu kamar yadda suka faro tun kuruciya. Wannan dalilin ne ma yasa Farha da Lilu suka ji ciwon laifin nasa fiye da yadda zasu misalta. Muryar Mami yaji cikin dakiyar da ya saba gani a tare da ita tana magana da Lilu. "Ina ka tafi?" Bai ji amsar ba sai abin da ta mayar masa. Yadda tayi magana babu alamun wasa ko wargi. Umarni ne take bayarwa domin ta kare dan nata. "Yana daga cikin rahamomin Ubangiji garemu da Ya halatta mana yin abota. Lokuta da dama suna maye gurbi ko ma su fi family dinmu tsaya mana akan matsaloli. Sai dai kuma ba kowacce irin matsala ya kamata a fadawa aboki ba. Wani abin sirrinka ne har lahira. Idan yau kaje wurin abokai da damuwar nan har ka fada musu komai ka cuci kanka. Ba kai kadai ba hatta 'yan uwanka ka tozartasu a idon duniya. Saboda haka duk mummunan sirrinka da Allah bai tona ba kada ka zama mai fitar dashi. Zai zama tamkar ka cakawa kanka wuka ne da kanka. Shi mahaifi sutura ne ga zuri'arsa. Abu kadan idan ya faru wanda ya dauke uba daga muhallinsa a wurin 'ya'ya sai kaji ana kiransu 'ya'yan mace. Kuskure guda daya tak zasu aikata sai a kusa shekara ana goranta musu duk don babu uba kuma babu madadin uban. To ina ga kai da kanka ka tona halin naka? Abokanka karshenta suyi maka tayin kayan maye. A halin da kake ciki na san karba zaka yi" Shiru suka yi na 'yan dakiku kafin Mami Khadija ta ambaci alkunyarsa wadda mutane suka bar kiransa da ita. "Khalil?" "Na'am" ya amsa da muryar da ta makale a makoshi saboda damuwa. "Ina fata sunanka zai jagoranci hukuncin da za ka yanke domin ni kam bani da sauran abin cewa gareka. Banda iyayena dominku nake komai. Don Allah kada ku sa bayan kukan miji na dora da na 'ya'ya." Lilu sai ya fashe da kuka. Mami Khadija ta dinga rarrashinsa da kalmomi masu dadi. Ba don gargadin da tayi masa ba tabbas idan yaje wurin abokan nasa sai ya farkewa mahaifinsa laya. A ganinsa hakan ba zai zama komai ga mutumin da bai iya daraja kansa ba. Ya manta bayan shi akwai 'yan uwansa. 'Yan uwan ma mata masu rauni. Gashi babu wadda tayi aure. Wane dan mutumcin ne zai so auren 'yar mutumin da aminiyar 'yarsa take ikirarin yayi mata ciki? Da wannan tunanin ya sauyawa shawararsa akala. Alwala ya dauro ya sanya dogon wando da tsaftatacciyar jallabiya ya dauki littafi mai tsarki ya soma karantawa. (Babu wani abu mai canja kaddarar bawa ko ya sassauta ta kamar addua. Duk takun da bawa zai yi domin kusanta kansa da Mahalicci, Sarkin da bashi da wa'adin zamani zai zo gareshi da fiye da wannan.) *** Shi kuwa Alh. Tahir kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ya bar kofar dakin. Kamar da wasa haka ya shigo tariyo wasu kazaman mu'amala da ya yi da mata daban daban. Tunanin kuwa yayi sanadiyar radadi mai azaba a cikin zuciyarsa. Yana cike da tsoro matuka a wayi gari duka 'ya'yansa suna yi masa kallon fasiki. Wannan rana ya tabbata zata fi kowacce muni a gareshi. Ba zai jure kallon kyama irin wanda Suhaib da Farha suka bishi dashi ba daga dukkansu. Shi bai ma san soyayyarsu tayi masa irin wannan kamun ba sai yau. Har musu ya yi da zuciyarsa akan cewa yanzu son da fargabar kiyayyarsu ya ninku sau adadin da bai sani ba a ransa. Zazzabi ya soma ji tun kafin ya isa nasa bangaren. Tunani ya sha masa kai bai ga isowar Suhaib gabansa ba sai muryarsa wadda ta dawo dashi hayyacinsa yaji. "Ina son zuwa Kano gobe in sha Allahu." Alh. Tahir ya ware idanunsa sosai da son dawo da nutsuwarsa jikinsa. Bashi da lokacin zurfafa tambaya ko binciken me dan nasa zai je yi a Kano daga dawowarsu yau. Ya dai aminta dashi ya san ba shashanci ne zai kai shi ba. 'To ma idan shashancin ne ai a wurinka ya gada' wani sashe na zuciyarsa ya tuna masa. Shi dai Suhaib yanayin sanyin da ya gani a wurin mahaifin nasa ya bashi mamaki. Domin Alh. Tahir mutum ne mai yin komai da kuzari. Sai ya sami kansa da kasa sharewa. "Abba lafiya dai?" Alh. Tahir yayi murmushin jindadi har hakoransa suka fito. Yau shi ne Suhaib yake nuna damuwa akan damuwarsa. "Lafiya kalau. Kaina ke ciwo shi yasa ma na dawo da wuri. Anjima kazo in kara maka guzuri" "Na gode. Kuma Allah Ya kara sauki" cewar Suhaib yana yin gaba. Wurin Mami Khadija ya wuce don baya son sai dare yaje yace zai yi tafiya da safe. Tunda taji sallamarsa bata yarda ya karaso dakin ya sameta a yanayin da take ciki ba. Fuska ta saki har ya shigo ya fada mata zancen tafiyar. Ba karamin dadi taji ba kuwa saboda ko kadan bata so ya fuskanci abin da ya faru. Tafiyar tasa tamkar rage karfin rikicin da take gudu ne. Dagula komai zai yi da fushinsa da zuciya. "Allah Ya kiyaye hanya. Kwana nawa zaka yi?" Suhaib wani irin kallo ya yi mata na rashin gamsuwa. Maminsa mai bin kwakkwafin yara normally cewa zata yi me zai je yi. "Mami lafiya kuwa? Ko baki da lafiya?" Fahimtar inda ya dagota da tayi yasa ta nemo murmushi ta dora akan fuskarta. "Wai don kaga ban tambayeka komai game da tafiyar ba?" Kai ya gyada kawai yana yi mata kallo na son gano inda baraka take idan akwai ta. Murmushi ta sake yi sosai ta ce "jikina ne ya bani kamar surukata daga Kanon zata zo. Ko dai wurinta zaka je ko kuma idan ka tafi yau zaku hadu." Suhaib dai bai san kujerar da Ayaah ta samu a zuciyarsa ba amma kalaman Mami sun saka shi jin kunya. Shi din ba ma'abocin harkar mata bane saboda tsoronsa na zama tamkar babansa. Faffadan murmushin kama kai ya shiga yi gami da susar keya. Mami Khadija ta mike cike da farinciki tana dariyar da ta bayyana hakora. "Hasashena ya zama gaskiya akwaita kenan. Alhamdulillahi. Na santa?" "Nifa Mami ki ma daina wannan batu don ban girma ba." Kallon ka-ma-rainani tayi masa tana cewa "to bari nayi addu'a ga wadda zaka je wurinta din. Allah Ya kawo mata santalelen miji wanda zai aureta nan ba da jim...." Abin da yayi a lokacin har ya koma dakinsa yana mamakin kansa. Katse addu'ar Mami ya yi da saurinsa yana mai bata fuska. "Ba amin ba." Ta dage gira tana leken fuskarsa da yayi kicin kicin da ita. "Koda kaine mijin?" Shi ma sai sannan ya gano tasa katobarar. Gaggawar fita daga dakin nata ya yi cike da jin kunya yana cewa ba abin da take zato bane. Sai da ta tabbatar ya fita ta iya sauke ajiyar zuciya. Farha ce kuma a ranta yanzu. Yarinyar tana da dauriya fiye da zato da tsammani. Da ta matsa mata da tambaya tabbas ta sanar da ita cewa har yanzu bata ji daga Abbati ba. Bai daga wayarta ba sannan kuma bai nemeta ba. Hankalinta taji ya tashi da tsoron kada zuwansa rayuwar Farha ya zama tamkar lasawa yaro zuma a baki. Da ace abin da ya saka shi komawa gida ya girmama bata jin mahaifiyarsa zata boye mata lokacin da suka yi waya. Tunanin ba zai fissheta komai ba shi yasa ta fita zuwa dakin 'yan matan. * (Allah Ya zama gatanka akan duk abin da baka da iko akansa) Sakon sms da Farha ta turawa Abbati kenan taji an murda kofar dakinta. Mami Khadija ce ta shigo da sallama. Farha tayi saurin gyara zama daga kashingiden da tayi. "Ya naga kowa ido biyu ne? Na zata zan sameku duk kun kwanta saboda sammakon da akayi." Dan murmushi Farha tayi tana cewa kwanciyar zata yi yanzu. Mami sai ta sami wuri a bakin ta zauna. "Farha" ta kirata a tausashe. Ba da baki Farhan ta amsa ba, sai dai ta tattaro hankalinta da nutsuwa ta mikawa mahaifiyarta. Mami Khadija ta cigaba da magana "kafin faruwar abin nan, ina nufin tafiyarsu gida babu shiri ranar da suke ganawa dasu Abbanku kun samu sabani ne?" "A'a Mami" cewar Farha tana danne kwallarta. Kewa da damuwa akan rashin sanin halin da Abbati yake ciki sun yi mata yawa. Karfin hali da dauriyar tata sun kai makurarsu. "Ki kwantar da hankalinki ki kuma yawaita addu'a. Ba komai da muke so bane alkhairi a garemu. Miji kuma babu matar da zata auri wanda ba nata ba" da dan sauri Farha ta dago ta dubeta tana son ta ce ita dai Abbatin kadai take so amma ta kasa. Mamin ma dai murmushi tayi "ke dai ki kasance mai mika wuya wurin karbar kaddara. Mijinki da yardar Allah wanda zaku kama hannun juna ne har aljanna. Bana miki fatan haduwa da abokin rayuwa wanda zaki so tatayyarku ta kare a duniya kadai." Farha ta san da wa Mami take shi yasa ta dinga zubar da hawaye. Duniyar gabadaya sauki ne da ita amma mazauna cikinta suyi ta jajibowa kansu matsaloli ta hanyar sabon Allah. A daren ranar Jiddo ta kira Danliti ta fada masa Suhaib ya karbi nambarsa a wurinta. Ta kara da cewa bata san manufarsa ba saboda haka tana mai gargadinsa da ya yi taka tsantsan. Ya kuwa yi mata alkawarin kiyayewa. Sai dai kuma ta riga ta makaro. Tun bayan komawar Suhaib dakinsa ya kira shi. Sauya murya ya yi yadda ba zai saurin gano shi ba ya ce kwatancen garejinsu yake nema. "Kwanaki mun zo tare da wani abokina daga Abuja har ka bashi nambarka. Na shigo gari ne mota take ta bani matsala. Idan zan sami gyaran da wuri ina son kawo maka ita gobe." Kalmar Abuja kadai da Danliti yaji tasa shi bayar da cikakken kwatance harda wata nambar idan bai same shi a wannan ba. A gefe guda kuma maganar Jiddo ta sanya shi yiwa Ayaah mugun tanadi. Indai akwai wata alaka tsakaninta da Suhaib da wannan shirin nasa zai bakanta masa rai. Ita kuma ya zama ladan bata masa lokaci kamar bata san me ya kawo shi ba tun farko. *** Duk wani taimako da Uwani zata iya bawa Qibdiyya tayi a lokacin wanda bashi da wani yawa. Mafi a'ala a kaita asibiti wurin kwakrarren likita domin a dubata yadda ya dace. Shawarar da ta bawa Munzali kenan bayan sun fito daga dakin. Kai ya gyada mata ba tare da ya iya magana ba. Zazzabi yake ji yana bin lungu da sako na jikinsa kamar ana gasawa akan garwashi. Numfashi da iskar da yake fesarwa ta baki ta hanci duk zafine dasu. Daki ya nuna musu a kasa ya ce idan zasu kwana ne ga wuri nan idan sun idar da sallar magariba. In kuma zasu tafi ne shi ma ga kudin mota don ba zai iya tuki ba. Ficewa ya yi daga gidan bayan ya yi tasa sallar a daddafe yana taku kamar a iska saboda rashin nauyin jiki yaje kofar gidan Abbati. Shi kadai kawai yake son fadawa abin da yake faruwa domin ya dauki mataki. Don sai yanzu ya kara yarda cewa Abbatin ya fishi tunani. Duk inda ya laluba sai yaga kamar idan ya taba Lilu sai ya kashe shi. Ya san zafin fyade tunda Shazali ya yi masa a shekarun da suka fi na Qibdiyya ma. Ya san ciwon da rai ke rikewa a yayinda ya san cewa shi ne sanadiyar dulmiyar wani a aikin sabo. Wannan ya tilasta masa yin sanyin da yake ganin yanzu ba muhallinsa bane. Salamar da ya san Abbati zai cusawa ransa ko yaki ko yaso ya tattaro ya sanyawa zuciyarsa. Saboda idan bai nutsu ba yana da yakinin cewa sai ya yi abin da zai yi nadama a gaba. Gara ya nemi uban Qibdiyya ya nemi shawararsa kafin ya zartar da nasa hukuncin. Ya debi kusan mintuna goma yana sallama da kwankwansa kofa kafin Hanne ta bude masa. Yadda ta bude kofar da dankwali a hannu zai sanar da duk wanda ya ganta cewa daga bacci ta tashi. Yatsina fuska tayi da ta ganshi taja guntun tsaki. Murmushi mai ciwo ya yi mata. A ransa yake jin kinsa da take yi tuntuni ba zai rasa nasaba da kasancewarsa sanadiyar bata rayuwar mijinta ba. "Don Allah kin yi waya da Abbati? Na neme shi na kasa samunsa." "Rabona dashi tun ranar asabar da kuka fita tare" ta bashi amsa tana cika tana batsewa. Ganin bai ce mata uffan ba ya juya zai tafi sai ta ce "kayi ka gama munafurcinka na son saka shi ya min kishiya. Ta Allah ba taka ba." Bai ko waiga ba balle ya kalleta. Yana ji ta buga kofa da karfinta kamar za ta balleta. Gida ya koma ya shige daki bayan sallama da su Uwani sun ce

Chapter 40 of 62