Share this page
ke zuwa tare da shi. Da kuma wuraren da da yake zuwa shi kadai ba tare da kowane guard ɗin sa ba. Bayan sun tattauna Dad yana ƙoƙarin koma ciki sai ga Uncle Adam ya karaso wajen. Bayan sun gaisa ne y ce " Dama part ɗin ka zan tafi. Ya ake ciki ne har yanzu ba ka ji motsin Asadullah ko labarin ƙasar da ya tafi ba?" Girgiza kai Dad ya yi cikin damuwa ya kalli ƙanin nasa ya ce. "Adam har yanzu ba wani labari bai taba yin tafiya ba tare da ya sanar da Ni kasar da zai tafi ba, ko kuma ya tafiay bai yi Mani sallama ba sai dai wannan karon na ga sakon message da ya tura mani ta waya wai ya tafi wata ƙasar sai ɗauki lokaci kafin ya dawo." Jinjina kai Uncle Adam ya yi tare da kallon Sulaiman ya ce. "Har da kai bai sanar da kai ba?" "Bai sanar da ni ba, kuma abun da ya bani mamaki mun dawo daga kamfaninsa ASADULLAH GLOBAL RESOURCES." "To da kuka dawo sai aka yi yaya?" "Sai ya shiga gidan sauran guard ɗin suka tsaya a harabar gidan kamar yadda suka saba, ni kuma na ɗauki laptop da wasu file da ya dawo da su na taka shi har part ɗin sa, na ajiye masa a falonsa na fito. To tun daga ranar ban sake ganinsa ba har yau." Wani banzan kallo Uncle Adam ya masa tare da cewa. "Wannan ai zance banza ne , ta yaya kuka aikin kula da mutum ku ce b ku san lokacin da ya fito ba, barci kuke yi ko me?'" "Alhaji ba barci kuke yi ba, sanin kanka ne ko dare yayi akwai security da basa barci, sai dai su yi ta zagaye gidan nan har gari ya waye kafin wasu su karbi aiki. Amma wallahi ba wanda ya ga fitowarsa a cikin gid..." "Shut up! Me za ka ce kana nufin yana. Kwance a ɗakinsa ne ko me kake nufi? 6)To je ka kira shi." _Fatima Zahrah_ Fitowa ta yi zuwa dinning area kamar yadda Sumayya ta sanar da ita. Suna zaune su uku, Hilal, Jamilu da Sumayya. Bakinta ɗauke da sallama ta karasa wajen, tana sanye da hijabi wanda ya rufe mata jiki. Amsa mata sallamar suka yi ta karaso ta zauna. Abinci Sumayya ta zuba mata jallop ɗin cuscus da ya ji kayan lambu da kuma lemun ta zuba mata a kofi da ruwa. Sai farfesun kaza. Kaɗan ta ci ta kasa sake wa ganin irin kallon da Jamilu ke yi mata . Tashi ta yi bayan ta ɗan ci kaɗan ta sha ruwa, kallonta Jamilu ya yi tare da cewa. "Me kika ci?" "Alhamdulillah na ƙoshi." "Ban yarda ba, nan fa kamar gidanku ne, ina zuwa Katsina fa a gidanku nake sauka kuma ina sake jikina kamar gidanmu. Duk da ban taba haduwa da ke ba, sai dai ina tunanin ke ce mai fita kullum da niƙab ko?" Murmushi ta yi sannan ta sunkuyar da kai. "Okay na gane kullum idanunki kawai ake gani, nima yanzu na gane ki ne saboda wannan kyawawan idanun naki." Wani kallo Sumayya ta masa ya wayance ya cigaba da cin abincinsa. Wayar Hilal ce ta yi ƙara ya duba ALEXANDRA ce ke kiransa a waya. Ɗagawa ya yi suka fara magana cikin yaren ƙasar Spain. Tun da ya fara magana Jamil dake jin me yake cewa ne yake masa wani mugun kallo da harara. Su kam Sumayya da Zahra ba sa jin yaren sai dai idan ya ambaci Nigeria ko ya ambaci U.S ne suka san me ya kira. Bayan Hilal ya gama wayar ne Jamil ya kalle shi rai a ɓace ya ce. "Kana nufin goben nan za ta bar ƙasar U.S ta biyo ka Nigeria?" Kallonsa Hilal ya yi kamar baya jin me yake cewa, ya cigaba da danne-danne a wayarsa. "To ai sai ka bari idan ka koma can Katsina ta je ta same ka, amma ba gidana wacen shegiyar za ta zo ba." Sai a lokacin ya kalli Jamilu ya ce. "Gobe za ta zo kuma duk in da nake dole nan za ta zo, ba ka isa ka hana ta zuwa in da nake ba. Don da na yi niyyar kama hotel ai hana ni ka yi ka sa dole na sauka a gidanka. Don haka duk in da nake nan ALEXANDRA za ta kasance baƙuwata ce." "Baƙuwarka amma ba bakuwar arziki ba ne don haka ka je ka kama maku hotel kai da ita, Zahra za ta zauna a nan har ta kammala abinda ya kawo ta ." "Wallahi ba ka isa ba, yadda ka hana ni da farko na hanu yanzu ba ka isa ka saka ni ba." Yana gama fadar haka ya tashi cikin takunsa na ƙasaita ya nufi bedroom ɗin da ya sauka. Da kallon mamaki suka bishi wanda sam Jamilu bai yi mamaki ba don ya saba da halinsa. Zahara kam mamakin isa da gadara da yake da shi take yi. Washegari gari kasancewar da safe ne za'a gudanar da musabaƙar ya saka Zahra tun da ta yi sallar asuba ta yi azkar sai ta nufi kitchen. Don ba ta saba da barci safe ba. Ruwan tea ta dafa da ya ji kayan ƙamshi sananne ta yi farfesun kayan ciki ta soya dankalin turawa da plantain sai ta soya ƙwai . Lokacin da Sumayya ta fito har ta gama komai ƙamshin da ta ji ne ya bata mamaki Suka gaisa tana mata maganar ta wahalar da kanta tana girki, murmushi kawai ta yi tare da komawa ɗakinta. Kasancewar karfe takwas ta yi ne ya saka Zahra ta gama shirinta. Lokacin da Sumayya ta shigo kiranta har ta sanya hijabi. A tare suka fita in da suka tarar da Hilal da Jamilu suna cin abinci. Hilal kam ya shanye farfesun kayan ciki ya masa dad'i . Don bai ci komai a wajan ba tun da ya ji ƙamshin farfesun. Jamilu kowa har santi yake zubawa yana cewa. "Sweetheart wanan girkin na yau na musamman ne, gaskiya ya yi dadi." "Ba ni ba ce na yi Zahrah ce ta yi." Cak Hilal ya tsaya tare da ture bowl ɗin gabansa ya bar wajen. Da kallon mamaki Jamilu da Sumayya suna bishi, Zahra ko kallonsa ma ba ta yi ba, ba ta da riko amma abinda ya mata jiya ya tsaya mata a rai.zama ta yi inda Jamilu ya daga murya yake ce wa Hilal. "Ba ka birge ni ba har sai ka amayar da abun da ka ci sannan zan san ka yi abin kai." *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣0️⃣ "Ba ka birge ni ba har sai ka amayar da abun da ka ci." Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ba tare da ta nuna ma ta san yana yi ba. Nan Jamilu da Sumayya suka dinga jan ta da fira da yaba irin daɗin da girkin nata, har ta saki ta fara dariya. Ganin saura mintuna arba'in a fara ne ya saka Zahra hankalinta ya fara tashi, musamman da ta ga Hilal baya da niyyar kai ta. Lura da yanayinta ne ya saka Jamilu cewa. "Ƙanwata lokacin ya kusa ko?" Murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana. Don haka ya cigaba da cewa. "Bari na yi masa magana ya shirya, ai tare da ni za ku tafi. Don direban nasa na ce ba sai ya kira shi ba, ya bar shi s hotel ɗin za mu tafi da motata." Yana gama faɗar haka ne ya tashi tare da nufar ɗakin da Hilal yaƙew. Bayan kamar mintuna goma Jamilu ya fito ransa a ɓace. Da alama sun samu saɓani da Hilal ɗin. Jikinta ne ya yi sanyi ganin yadda ya fito, sai ya yi murnushi tare da cewa. "Ƙanwata muna ina zuwa please." Jinjina kai kawai Zahra ta yi ba tare da ta ce komai ba. Suna nan zaune ita da Sumayya sai ga Jamilu ya fito, sanye yake cikin wata yadi mai ruwan ƙasa, sai zuba ƙamshi yake zubawa. Kallon Zahra ya yi tare da cewa. "Fatima Zahrah ta shi mu tafi Yayanki baya da niyyar tashi kada ki makara." Kamar ba za ta je ba sai kuma ta yi wani tunani, saboda Ya Hilal na gidan ta san ko zuwa ya yi ya cutar da ita ko aka rasa ta dole shi za'a tuhuma tun da ya san shi. Don haka sai ta miƙe ta ce. "Yaa Jamil ina zuwa, ɗakinta ta koma ta ta ɗauko ƙaramin handbag ɗinta da niƙab, sai ta tuna a ce kada su saka saboda a san su. Don haka ta ajiye ta fito bayan ta rataye ƙaramin handbag ɗin ta. A tsaye ta same su shi da Sumayya suna rike da hannun juna. Don haka gaba suka yi tana biye da su a baya. Ɗaya daga cikin motocinsa dake parking space suka nufa. Ya shiga mazaunin Direba, Zahara ta kalli Sumayya ta ce "Auntu ke ba za ki je ba ne?" Murmushi ta sakar mata tare da cewa. "Sister ta ce ta haihu yau ake suna, can zan tafi ku yi haƙuri." Murmushi ta sakar mata tana cewa "Allah ya raya." Da Amin ta amsa mata yayin da ta buɗe mata murfin motar, ta shiga ta zauna gefen Jamilu. Ɗaga masu hannu ta ta yi yayin da ya yi wa motar key maigadi ya wangale masu gate suka bar gidan. Wajen harabar in da za'a gudanar da gasar karatun Al-ƙur'anin ya cika da mutane. Suna parking kiran waya ya shiga cikin wayarta. Ba kowa ba ne face Mallam Usman, Mallamin islamiyarsu da ke sonta. Ɗaga wa ta yi baya ta yi sallama take sanar da shi sun iso. Wajen da aka tanada saboda parking motoci ya nufa. Bayan ya yi parking suka fito. Mamakin cikar jama'a dake wajen ta yi, duk da an sanar da su da yadda komai zai gudana a wajen, amma ba ta yi tunanin yawan jama'ar sun kai haka nan ba. Taro da ya ƙunshi manyan mutane tun daga kan ƙusoshin gwamnatin zuwa hamshaƙan ƴan kasuwa da ƴan siyasa, sarakuna. Da masu matsayi a gwamnati. Jami'an tsaro kuwa ga su nan cike a wajen suna gudanar da aikinsu. Don an saka matakan tsaro sosai ba waje ne da za ka je kai tsaye a bar ka ka shiga ba, sai an bincike babu wani abu na cutarwa a tattare da kai. Cikin sanyin jiki ta ƙarasa in da ta hango tawagar ƴan jiharsu. Yayin da Jamilu ya zauna ɗaya daga cikin kujeru da aka tanada don baƙi su zauna. Tana ƙarasawa ƴan tawagar su da Mallamansu suka nuna jin daɗinsu da isowarsa. Nuna mata wajen zaman da aka tana da dan su aka yi. A hankali ta fara taku cikin nutsuwa ta nufi wajen zamansu , taka step ɗin take yi cin nutsuwa yayin da ta kasa ɗaga idanunta. Saboda idanun. Mutane da take ji yana mata yawo a jiki. Ɗaya daga cikin kujeru uku da suka rage ba mutane ta nufa. Kowane kujura an rubuta sunan state, kai tsaye ta nufi wanda ta ga an rubuta Katsina state. Saura na Adamawa da Niger state. Su ne da alama ba su ƙaraso ba. Zaman ta ba jimawa sai ga ƴar jihar Niger ta iso Salma Usman Isma'il. Daga kashe sai ga na jihar Adamawa namiji ne shi ma ya ka karaso wajen. Ƙamshin daddaɗen turarensa ne ya daki hancinta. Wanda ya haifar mata da faɗuwar gaba, kamar an ce ta ɗaga kai sai kuwa ta sauke su akansa lokacin da yake shigowa cikin taron. Da Sanye yake cikin wata ɗanyar shadda fara sa sai ɗaukar idanu yake yi, yana sanye da baƙar hula sai bakin takalimi hannunsa ɗauke da tsadden agogonsa. Duk da fuskar nan a tsuke take babu sassauci amma hakan bai hana kyawunsa da cikar haibarsa bayyana ba. Jamilu ne ya karaso wajensa yana masa nuni da in da za su zauna, kamar ba zai zauna ba sau ya bishi suka zauna. Nan Sheikh Muhammad bin Ali shahararren Mallamin da ake alfahari da shi ya yi sallama, tare da bude taro da addu'ar ya gabatar da abinda ya tara su . Tare da yi wa manyan baƙi da kowa barka da zuwa, in da ya gabatar da sunanyen wasu manyan baƙi da suka halarci taron. Governor bai samu zuwa ba amma ya turo Wakilinsa ya halarta. Cikin nutsuwa aka fara gabatar da komai, tamabayoyi ne ake masu na alƙu'arni. Maza da mata ana tambayarsa cikin sura kaza aya ta kaza ka karanto su. Ko kuma a yanko aya a tsakiyar surorin al-ƙur'ani a ce ka karanta , har sai ka kai yadda suke so sai a dakatar da kai a sake shiga cikin wata surar a ce a ce cikin sura kaza aya ta kaza ki karanto su. Kina gama kai in da ake so sai a dakatar da ke a sake tamabayarki wata aya cikin wata sura ki karanto su. Kuma an soma kowane harafin ki bashi hakkinsa don ko kaɗan kika yi kuskuren harshe sai na gyara maki. Tun ana yi wa ƴan wasu state har aka zo kan Katsina state in da Zahra ke wakiltar ɗaliban jiharsu. Kowace tamabaya aka yi mata cikin kowane sura aka fada mata lambar ayar kai tsaye za ta fara rero karatunra cikin zazzaƙar muryarta mai saka nutsuwa a cikin zuciyar ma'abota saurarenta. Ta burge mutane da yawa saboda karatun na ta ba'ayi mata gyara ko ɗaya ba, kowane harafin tana bashi hakkinsa. Kuma duk surar da aka yanko mata za ta fara babu tsayawa har sai an dakatar da ita. Ta burge mutane da yawa ga yan jarida da yan gidajen rediyo suna ɗauka, bayan masu ɗauka da wayoyinsu. Tsawon lokaci aka ɗauka ana gudanar da komai gwanin sha'awa, yayin da Zahra ta shiga ran mutane da yawa, yadda duk in da aka aka ce ta karanto za ta karanto take ba tare da sai ta tsaya nazari ko tinani ba. Hakan ya saka jaharta Katsina ta ci wannan gasar. Ita ce ta zo ta ɗaya a cikinsu. In da ta samu manyan kyaututtuka na ban mamaki. Don kujerar Hajji sai da ta samu guda biyar da mitoci biyu. Ga masu ba ta kyaututtukan kuɗaɗe. Tsabar farin ciki kuka ta yi sai hawaye ke bin fuskarta. Sauran ma sun samu kyautar amma ba ta kai ta Zahra ba, ta biyu zuwa na biyar ne suka samu kyautar kujerar Hajji. Farin ciki a wajan Mallaman makarantar ta su ba'a magana. Don sai washe baki suke yi. Haka aka tashi taron cikin farin ciki, yayin da ƴan jarida ke ta ƙoƙarin sun ji ta bakin Fatima Zahrah Salis Tafarki amma abun ya ci tura. Don ta kasa magana sai kuka take yi. Gashi sai hasken Camera ke ta haska ta ta ko ina, wasu saboda ƙwazonta yayin da wasu kuma saboda kyawun da Allah ya yi mata. Kamar yadda tsarin su yake sai an koma state ɗin ta kafin a damƙa wa iyayenta kyaututtukan da aka bata. Haka ma ta kasance. Sallama ta yi wa Mallamansu da niyyar idan ta koma za ta same su a makaranta ita da iyayenta. Tafiya take a hankali ta ji mutane na bin ta a baya za su yi photo. Ba musu ta bawa duk masu bukatar daukar photo da iya dama, wasu kuma ita kadai suke dauka saboda su yi posting a a social media. Jamilu ne ya karaso wajen da suke ya kira ta don ta zo su wuce. Da Ɗaga kai ta yi suka haɗa idanu da Nihal ya watsa mata mugun kallo. Ganin haka ya saka ta bar wajen da sauri don wuce wa. Tana tsaka da tafiya ta ji ana mata sallama. Juyawa ta yi ta kalli mai sallamar. Wani matashin saurayi ne kyakkyawa yana sanye cikin gezna ruwan sky blue ya guard ɗin sa na biye da shi a baya. Murmushi ya sakar mata tare da cewa. " Hafiza barka da wannan lokacin, don Allah ko za'a jiƙaina a bani lambar waya?" Shiru ta yi wanda ganin haka ya saka ya yi murmushi tare da miƙa mata wani kati. Karɓa ta yi ta yi gaba. Tana tafiya cikin sanyin jikinta, wanda har lokacin ba ta daina jin idanun mutane na yawo a jinkinta ba. Suna ƙarasowa wajen parking motocin sai wani mutum yana sanye cikin Suit ya karaso, tare da miƙawa Hilal da Jamilu hannu suka gaisa. Kallonsu ya yi tare da cewa "Na so na ji matakin Shari'a don Allah idan ba damuwa ina son na sani wannan sister naku an yi mata miji ne?" Da sauri Jamilu ya ce . "Ƙwarai kuwa nan ba da jimawa ba za'ayi mata aure sai ka yi hakuri." Cikin sanyin jiki ya masu godiya ya tafi. Ita dai Zahra mamakin Jamilu ne ya kama ta. Gefen motarsa wajen me zama banza ya bude mata. Shiga ta yi ta zauna wajen me zaman banza. Hilal ya zauna bayan motar kasancewar ya tura direbasa ya dauko massa ALEXANDRA a airport. "Mallam ina motarka da Direbanka, bai tanka masa ba ya dinga danne-danne a waya. Har suka karasa gidan bai yi magana ba, Sai Jamilu dake ta jan Zahra da fira yana yabawa baiwar ilimin da Allah ya yi mata.ita dai fage uhm sai umm." A parking space suka yi parking ta fito shima ya fito yayin da Hilal ya fito daga karshe. Key ya saka ya buɗe gidan suka shiga. Kai tsaye ta nufi ɗakin da aka sauke ta. Jamilu ya kalli Hilal ya ce. "Abokina gaskiya ina son wannn sister ta ka fatan za ku bani aurenta, hakan ya saka na cewa wancan gayen ta kusa yin aure ya haƙura." Ita ko wayarta ta ɗauka tana kiran Abbi da Umminta, ba su shiga ba don ta lura tun tuni ya dace su dawo amma ba su dawo ba, amma ta ji Yaa Sadik ya ce mata jikin Papa ne ya tsayar da su, amma nan da kwanaki uku za su dawo. Don Papa na asibiti likita na kula da lafiyarsa. Fitowa ta yi da niyyar ta duba ko akwai aikin da za ta taya matar gidan, fitowarta ya yi daidai da shigowar direban Hilal da wata baturiya a bayansa. Tana ganin Hilal ta ruga wajensa wanda ganinta ya sa ya miƙe tsaye ta rungume shi a jikinta tare da sumbatarsa a kumatu. Mumrmushi ya yi mata yayin da Jamilu ya tsuke fuska yana masu wani banzan kallo musamman ALEXANDRA. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣1️⃣ Fitowa ta yi da niyyar ta duba ko akwai aikin da za ta taya matar gidan, fitowarta ya yi daidai da shigowar direban Hilal da wata baturiya a bayansa wanda ganinta ya sa ya miƙe tsaye ta rungume shi a goshinta tare de sumbatarsa a kumatu. Murmushi ya yi mata yayin da Jamilu ya tsuke fuska ya masu wani banzan kallo musamman ALEXANDRA. Kau da kai Zahra ta yi ya nufi kitchen ɗin, tsawon mintuna biyu suka ɗauka kafin ya zame ta daga jikinsa ya fara magana cikin yaren ƙasar Spain. "Dama da gaske za ki zo duk in da nake?" "Ina mai tabbatar maka ko a karkashin ƙasa kake zan bila?" "Anya za ki iya zaman Nigeria kuwa?" "Me zai hana idan ina tare da kai." "Amma da kin jira dai na dawo." "Gaskiya ba zan iya jira ba domin sanin kanka ne cewa ba zan iya hakuri rashinka har na sati ɗaya ba, ga shi kamar ba za ka dawo ba, don haka tare za mu koma ƙafata ƙafarka." Sai a lokacin da ta kalli Jamilu don ta san shi tare da Hilal tare da shi suka yi karatu a can ƙasar. Gaishe shi ta yi ya amsa mata ba wani sakin fuska, duk da cewar ta dade da gane cewa baya son tarayyarta da abokinsa amma ba ta damu ba, saboda shi Hilal yana sonta. Amma duk da ta ji wani irin yadda ya amsa mata sai ta ji wani iri, lakatar hancinta da Hilal ya yi ne ya sa ta lalle shi tan murmushi. Cikin yaren Hausa Jamilu ya fara magana yadda ya san cewa ba za ta ji shi ba. "Dalla Mallam ka ɗauke mani wannan abar a cikin gidana, duk da ba yau za ku koka Katsina ba sai gobe tabbas wannan ba za ta kwana a gidana ba, sai dai daga kai har ita ku je ku jama hotel ku kwana, washegari ka zo ka dauki Zahra ku tafi, ko ma da kaina zan iya mayar da ita gidan. Wani kallon baka isa Hilal ya yi masa ba, sannan ya ɗaura da cewa. "Tabbas nan gidanka ne amma ba ka isa ka kore mu ba, har sai gobe idan mun tashi tafiya. Da lokacin da na yi niyyar kama hotel me ya saka ka dame ni akan na sauka a gidanka, duk da ba da shawarar son raina na sauka ba saboda yanzu kana da mata, ni kuka nake ganin kamar zan takura har. Kana fushi da ikirarin ba za ka sauka a gidanmu idan ka sake zuwa garin ba. Dole ba da son raina na zo ba. Sannan yanzu ka kawo Mani wani zancen ba ka isa ba." Yana fadar haka ya ja hannun Alexandra suka nufi bedroom ɗin da y sauka. Muryar Jamilu ya ji yana ce masa. "Nan gidan Sunnah ne wallahi ko da wasa kuke aikata Mani ɓarna a cikin gidana sai na baku mamaki, tun da ta kasa hakuri ka koma can ku cigaba da iskancin da kuka saba." Kamar Hilal bai ji shi ba ya share shi suka shiga cikin bedroom ɗin. "Zahra tana kitchen tana mata goge goge, ta ji maganar Jamilu tana mamaki dama haka halin ya Hilal yake, take ta ji babu dad'i a ranta. _Asadullah Mantson_ Uncle Adam ya cigaba da yi wa Sulaiman faɗa akan me za' ce ba'a san in da Asadullahi yake ba. Bayan shi ne na hannun damansa. Ya kamata ace duk in da yake yana tare da shi. Ko da cikin falonsa ne. Jin faɗar ya ƙi karewa ne ya saka Dad yi masa magana akan ya bar shi don yana iyakar ƙoƙarinsa. Uncle Adam bai saurari Dad ba ya kira duka guard ɗin dake kasance tare da Asadullahi ya masu tambaya, sai dai kowa amsa iri ɗaya suke bashi. Dole ya ƙyale su don ba abinda zai ce masu kuma. _Jidderh_ Tun daga ranar kullun sai ta faki idanun mutane ta nufi ɓangaren da Asadullahi yake, ta je ta bashi abinci ya ci ta bashi ruwa. Sannan take samun nutsuwata a rayuwarta. Kuma kullum sai ta yi masa kuka, musamman ganin yadda ya rame duk da shi ba mai yawan cin abinci ba ne amma ta lura duk ta saci jiki ta kai masa abin da zai ci. Duk da shi ba mutum ba ne mai yawan cin abinci ba ne, amma ta lura kullum idan ta je kai masa abinci sai ya dinga rawar jiki wajen cin abincin. Da alama yunwa yake ji. Hawaye take yi idan tana kallonsa. Su kansu waɗan da suka tsare shi a wajen dau ɗaya sauke bashi abinci. Su kansu sun fara mamakin ganin kwana biyu baya galabaita da yunwa. Don haka suka fara tunanin saka ido a bangaren da kuma mutanen cikin gidan, don sun san tabbas akwai wani abu a ƙasa. Don haka yadda suke barin ɗakin da suka barin ɗakin Asadullah ba tare da sun saka key ba, saboda sun san cewa sun ɗaure shi da sarƙa, ba iya tashi zai yi ba, kuma bugu da ƙari ba wanda yake zuwa ɓangaren da aka aje shi. Don haka ya faɗa tunanin su rufe. Kamar kullum yau ma ko da ya shiga part ɗin bayan Doctor ya tafi ne, ta shigo ɗakin. Sanye take cikin wata doguwar riga baka, ta sanya p cap 🧢 a kanta, sannan ta saka facemask da ban n gallass. Ba wanda ya zai iya gane ko wace ce saboda ta yi shigar ɓadda kama. Tura ƙofar ta yi ta ji ta a buɗe. Jidderh wacce ta gana ba shi meet pie ta tashi da sauri jin motsi ta nufi toilet. Tana. Shiga ana gama shigowa ɗakin jin kamar motsi ya saka ta waige-waige ganin ba kowa ya saka ta nufi toilet ɗin ta tura ƙofar da sauri ta shiga ciki. _Zaharah_ Ganin har yamma ta fara gabatowa Sumayya ba ta dawo

Chapter 11 of 39