Share this page
ba ne ya saka Zahra ta shiga kitchen bayan ta idar da sallar la'asar ta shiga kitchen Fried rice ta girka masu ta wanda ya ji kayan haɗi da hanta. A dinning table ta jera komai. Daidai lokacin da Jam'i da ya fita ya dawo, don haka nuna jin dadinsa ya yi mata godiya. Tuna cewa Alexandra na gidan ya saka Jamilu canza fuska, kallion Zahra ya yi tare da cewa. "Ƙanwata ki kai wa Yayanki da baƙuwarsa na su a daki, saboda ba na son ta fito, ɗin a zahirin gaskiya ba na ƙaunar ganinta." Ya ƙarasa faɗa yana yin tsuki Ba musu Zahra ta samu madaidaicin flask ta ta zuba masu na su, ta haɗa da soyayyar naman kaza. Sai Lemun kwakwa da ta haɗa duka ta jera su a tire. Ta saka plate da cokula. Kai tsaye ta nufi ɗakin da ta san ya sauka. Sallama ta yi ba'a amsa ba, har sau uku shiru. Hakan ya saka ta shiga kai tsaye tun da ta san ba ɗakin ma'aurata ba ne, kai tsaye ta shiga ciki. Kanta a ƙasa ta ajiye tire a saman table dake ɗakin. Ɗagowa ta yi ta sauke idanunta akan su. Zaune yake akan doguwar kujerar mai zaman mutum uku, yana sanye da wando dogo babu riga a jikinsa. Alexandra tana zaune a saman cinyarsa babu kaya a jinkinta daga ita sai pant ko bra babu a jikinta. Suna tsotson bakin junansu. Zaro idanu Zahra ta yi tare da furta kalmar. "A'uzu billahi minash shaiɗani raƙumi." Da sauri ta fito cikin yanayin firgici. Jamilu dake falon ya kalle ta . tafe da cewa. "Zahra lafiya?," Ba ta iya cewa koma ɗakin ta sauka Da hanzari ya nufi ɗakin ganin abin da koro Zahrah, shi ma ganinsu ya yi kamar yadda Zahrah ta gansu . Take ya tsuke fuska ya fito ransa a ɓace, zama ya yi a Wajan cike da takaicin Hilal. Bayan m Kamar muintuna ashirin sai ga kiran sallar magrib. Jamilu ya mike kenan sai ga Hilal ya fito sanye da farar jallabiyarsa da alama alwala ya zai je masallaci. Kallo ɗaya ya shi ma Hilal ya masa ya ɗauke kai . Masallaci ya nufa yayin da shi ma Jamilu ya ɗaura alwala ya nufiadallaci don gabatar da sallar magrib. _Zahrah_ Tun da ta shiga ɗaki ba abinda take dai sai aikin kuka, kuka ba take yi sosai don hankalinta ya tashi da abun da ta gani, mace kusan tsirara tana zaune a saman cinyar Yaa Hilal tana tsotson bakinsa. Dama haka halin Yaa Hilal yake ba ta sani ba. "Yaa Hilal me ya saka ka zaɓe wannan ƙazamar rayuwar ne? Dama da gaske ne da nake ji cewa wai sojoji suna da neman matan banza da shan giya? Shin kai ma kana shan giyar ne?" Haka ta dinga riskar kuka kamar ranta zai fita. Jin har an tayar da Sallah ya saka ta tashi da sauri ya nufi bathroom. Wanka ta yi sauri-sauri ta ɗauro alwala, rigar barci ta saka riga da dogon wando farare. Ta sanya Hijabi har ƙasa ta fara gabatar da sallar magrib. Tana nan zaune ha tana addu'o'i har aka kira sallar isha'i. Sai da ta yi sallar sannan ta hau kan gadon bayan ta naɗe sallayar da hijabi ta ajiye. Kwanciyar ta ke da wuya sai ga Sumayya ta turo ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Amsa mata Zahra ta yi tare da yi mata sannu da zuwa. Amsawa ta yi cike da jin dad'i tare da yi mata godiyar girki. Murmushi ta yi tare da cewa. "Ba komai kada ki damu." ""Na sha Allah Allah, ina ganin girki har yawu na tsinke wa Sai da oga ya ce kafin na ci sai na kira ki kema kin ci." Gaskiya na ƙoshi yanzu." "Me kika ci?" "Ba komai ba na jin cin komai ne." . "Akan me gaskiya ban yarda ba tashi mu tafi " Duk yadda ta so ƙin fita Sumayya dai da ta takura mata suka fito. Jamilu na zane a dinning table yana jiransu, daidai lokacin da Hilal ya dawo daga masallaci. Sallama ya yi wanda idan ba wanda ya kalli bakinsa ba zai san ya yi wata sallama ba. Kasancewar sun kalli kofar ya sa suka amsa. Sumayya ce ta gaishe shi cike da kulawa, ya masa mata a takaice ya nufi bedroom ɗin da yake ciki. Jamilu da Zahra ba wanda ya ce masa uffan. "Ka kira abokinka mana ya zo ya ci abinci. Ko ƙanwarsa ta kira shi ne?" "Kada ki damu an kai masa nasa a ɗaki kasancewar yana tare da baƙuwarsa." "Baƙuwa ya yi ?" "Eh" Ya bata amsa a takaice. "Okay ai da ta fito mun yi dinner tare." Tsuke fuska ya yi tare da cewa. "Ki bar su kawai." Ita ta yi sevin nasu suka fara cin abinci, Zahrah dai abin da ta gani ya tsaya mata a rai. Duk da yau ranar farin ciki ne amma abin da ta gani ya shafi farin ciki da walwalar da take ciki. Har Allah take gari ya waye su kama hanayar komawa gida. Nan suka dinga cin abinci suna jan ta da fira suna ta yaya ta murna na samun nasara tare da mata fatan alkhairi. Bayan sun kammala ne ta yi masu sallama ta shiga cikin, duk da sun so a ce ta tsaya sun yi fira da ita. Kwanciya ta yi ta bayan ta ɗauro alwala ta yi addu'ar kwanciya barci. Ƙarfe biyu na dare ta farka ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallar nafilfili. Sai asuba ta idar tare da yin addu'o'i. Har aka yi assalatu ta yi sallar asuba. Azkar ta yi sai da garin ya fara haske ta fito zuwa kitchen. _Hilal_ Akan hanyarsa ta dawowa daga masallaci suka jero tare da Jamilu. Bayan Jamilu ya bashi hannu sun yi musabaha ya kalle shi ya ce. "Hilal" Bai kalle shi ba amma ya san ya ji shi. Don haka ya cigaba da cewa "Nan fa Nigeria ne ba U.S ko London ba, irin rayuwar da kake yi a can kada ka ce za ka yi shi a nan. Domin Addininmu da Al'adar mu ya sha banban da ta su. A can don ka rungume mace ka sunmbace ta ko yi abinda ya fi haka ba wanda zai kalle ka. Amma anan ba haka ba ne. Yanzu har ya kai ka kira ɗaya daga cikin matan da kake harka da su don su zo su same ka a ƙasar ka?" Yau za ku tafi ina za ka kai ta?" "Gidanmu." Da mamaki ya kalle shi don ya san in dai ya fadi abu sai ya aikata. Don haka ya ce. "Allah ya kyauta. Amma da zan baka shawsra ka ɗauka ko da sai na ce . Ka auri yarinyar nan Fatima Zahrah." Wani banzan kallo ya yi masa tare da ɗauke kansa. "Na yi maka kwaɗayin samun nagartacciyar matar aure ne ya da na baka wanann shawara. Don idan ka aure ta to tabbas ka nema wa yaranka uwa ta gari abun alfahari ga...." Ɗaga masa hannu ya yi alamar baya son maganar, don haka ya yi mumrmushi tare da cewa. "To ni zan yi ta biyu da ita in sha Allah ba zan bari ta kufce mani ba." _Zahrah_ Tana shiga kitchen ɗin sai hayaƙi da ƙauri ya turnuke ta. Sakamakon manja da Sumayya ta bari a wuta ya ƙone ta fita zuwa ɗakinta don ɗauko green pepper da ta dawo da shi jiya daddare sai ta ajiye a bedroom ba ta kawo shi kitchen ba. Zahra na shiga ta shaƙi hayaƙin, da sauri ta kai hannu ta kashe gas ɗin cikin ƙarfin hali. Tana fita ƙofar kitchen ɗin numfashinta ya fara ɗauke wa. Kafin ka ce ne har ta zube a wajen. Ƙoƙarin tashi take yi don ta je ɗaki amma ta kasa. Cikin wannan halin Sumayya ta rugo da gudu sakamakon tuna Abinda ta bari a wuta. Ganin halin da Zahra ke ciki ya saka ta yi ihu daidai lokacin da Hilal da Jamilu suka iso . Wajen suka nufa in da suka yi kanta, cikin tashin hankali Jamilu ya ce. "Meke faruwa?" Cikin kuka Sumayya ta ce ba ta sani ba. Halal dake tsaye hannunsa a cikin aljihun wandonsa ya ce "Ina ga wanann hayaƙin ya saka ciwonta ya tashi." "Wane ciwo?" Jamilu ya tamabaya ciki n damuwa. "Athma" Ya faɗa yana kallonta. Juyawa ya yi ya nufi ya nufi bedroom ɗin da ta sauka. Handbag ɗin ta ya buɗe, ya duba Inhelar ya ciro daga cikin jakkar ya fito. Fitowa ya yi ya nufi in da take durƙusawa ya yi a gabanta ya shaƙa mata Inhelar ɗin. Zuba mata idanu suka yi suna kallonta. Numfashinta ya fara daidaita. "Ki yi hakuri don Allah ban sani ba " Sumayya ta faɗa cikin rauni. Sannan Jamilu ya kalle ta da cewa. "Gaskiya duk wanda zai suna da ke sai ya kiyeye abinda zai iya jefa rayuwrki cikin hatsari, shawarar da zan bashi kenan ko?" Ya faɗa yana kallon Hilal. "Ko ba haka ba abokina?" Taɓe baki Hilal ya yi tare da cewa. "Ko kuka ka bashi shawarar ya nemi gida kusa da asibiti ya tare saboda ko da ta ɓaci ba su da nisa da asibiti ba sai ya yi ta wahalar sintiri ko wace rana ba don zuwa asibiti ba, idan ma da gida a asibiti nan ta kamata ya tare da ita." Yana gama fadar haka ya wuce abinsa. Da kallon mamaki suka bishi, Zahra wacce numfashinta ya dawo daidai tsabar mugayen kalamansa ya sa ta ji shi kamar saukar aradu ƙirjinta kamar an ɗora mata dutse, zuciyarta kuwa kamar an watsa mata garwashin wuta. Su kansu ba su ƙi dadin kalamansa ba, don gara kalmar da ya yi mata shekaranjiya in da ya ce ba ya kallonta a matsayin mace. Ba ta da banbanci da namiji a idanunsa. Tsabar ɓacin rai ya saka ta fashe da kuka mai cike da ƙunar rai. Take kuma numfashinta ya ɗauke. 🤔 _Tofah ga Jidderh can ashirinta zai tonu a toilet garin taimakon Asadullah. Ga Zahra na cikin wani hali saboda mugayen kalaman Hilal, ko ya za ta kaya?_ *A gaskiya rashin comments naku ya saka bana yin typing kullun. Domin sai na yi zaman awanni biyu ko uku ina typing ne ya sa comments na minti biyu ba za ku iya ba? Idan har ba ku canza ba to ba za ku samu update kullum ba wata kila ma na ce na mayar da shi paid book. Don idan paid ne ba zan damu da rashin reactions ko comments ba*😒 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣2️⃣ Tsabar ɓacin rai ya saka ta fashe da kuka mai cike da ƙunar rai. Sumayya ce ta taimaka mata ta tashi, har zuwa bedroom ta ta raka ta, a bakin gado ta zauna. Nuni ta yi wa Sumayya da handbag ɗin ta, ganin haka ya saka ƙarasa ta ɗauko mata. Cikin ƙarfin hali ta ɗauko magani a ciki, ganin haka ya saka Sumayya ta ɗauko mata robar ruwa a fridge ta buɗe sannan ta miƙa mata. Amsa ta yi bayan ta saka maganin a bakinta ta haɗiye. Karɓar sauran ruwan ta yi ta ajiye. Yayin da ita kuma ta koma ta kwanta. Zafi kawai kalamansa ke yi mata a zuciya, don Yaa Hilal ya ci mutumcinta ya mata tozarci da ba wanda ya taɓa yi mata ba. Duk da zafin da zuciyarta ke yi sai ta dinga karanto addu'o'i a bakinta, ba jimawa barci ya ɗauke ta. Ganin ta yi barci ya saka Sumayya fita daga cikin ɗakin. Tana fita kitchen ta koka don karasa sauran aiyukan nata. Cikin ɓacin rai Jamilu ya nufi bedroom da Hilal yake ciki. Ko sallama bai yi ba ya kutsa kai ciki. Hilal dake rike da waya a kunnensa ko kallon ƙafar bai yi ba ballantana ya kalli wanda ya shigo. Sai da ya gama wayarsa fuska a tsuke ya kalli Jamilu wanda shi kuma yake kallon Alexandra dake kwance saman gadon cikin bargo, barci take ji hankali kwance. "Yanzu abin da kake yi wa yarinyar nan ya dace?" "Ni ba abinda na mata kada ka ɓata Mani rai da safen nan." Cikin ɓacin rai Jamilu ya ce idan dai har ba za ka taba canza wa ba ko? To ko don ka saba take haddin mata ne ya saka ba ka ganin ƙimar mace. Ba tare da ya kalli Jamilu ba ya ce . "Ban taɓa keta haddin ko wace mace ba ka sani, kai kanka shaida ne. Ko da wasu sun fadi haka kai mai iya ƙaryata wa ne. Ban taɓa aikata fasikanci ba duk tsiya ta sai dai na ragewa kaina zafi amma ba na wuce gona da iri ba." Shiru Jamilu ya yi yana kallonsa, don ya san halin abokin nasa tun suna secondry school har suka tafi ƙasar waje karatu. Ko a zaman su a ƙasar ya dai san sauran abokansu na dake can suna sheƙe ayarsu da mata, suna lalata da mata. Sai dai shi Hilal bai taɓa aikata lalata da kowace mace ba, sai dai yana romancing da su ya rage zafi amma ko da wasa bai taɓa gigin aikata zina ba. Iyakarsa rungume-rungume da sumbace-sumbace har sai ya ji ya rage zafi. Duk da akwai baƙaken fata da suke sonsa a can sai dai iyakarsa da su ragewa juna zafi. Duk da wasu sukan na ce akan ya biya buƙatarsa da su baya yarda. Idan mace ma ta nace amsa akan haka to rabuwa yake yi da ita. Alexandra ita ce Baturiyar da ya daɗe yana mu'amala da ita ba tare da ya rabu da ita ba kamar sauran ba. Don sun kai shekara a tare, amma ganin irin son da take masa ne ya saka ya kasa rabuwa da ita. Don tana masa so ne sosai wanda ko wata mace ta gansu tare sai ta yi kamar za ta yi hauka take yi. Don ta kusa kashe wata baturiya mai suna Juliet akan Hilal. Mumrmushin takaici Jamilu ya yi tare da cewa. "Na sani wannan ɗin ma Allah ya yafe maka." Daga nan ya nufi ƙofar fita har ya rike handle ɗin ƙofar har zai fita ya tsaya ya ce. "Ina neman auren Zahra fatan dai za ka shige Mani gaba har burina ya cika." "Ka bar wannan zancen kawai matukar kana son abotarmu ta ɗore Gajeren murmushi Jamilu ya yi tare da cewa. "Shikenan idan na za ka taimaka Mani ba na san hanyar da zan bi." Yana gama fadar haka ya fice ba tare da ya sake yin wata magana ba. Ba jimawa dai ga shi ya sake shigowa ta tire a hannunsa. Breakfast ne aka jera a ciki. Kamar yadda Jamilu bai ce komai ba haka zalika shi ma bai ce masa komai ba ya tashi ya shiga bathroom don yin wanka. Tsawon mintuna talatin ya ɗauka kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa. Sai wani karami dake hannunsa yana tsane gashin kansa . Ƙarasa wa ya yi zuwa bakin gadon yana tayar da Alexandra. A hankali ta bude idanunta tare da sauke su akan ƙyakyatawar fuskarsa. Allah ya jarabe ta da son Hilal a zuciyarta fiye da kowa da komai. Kuma ba ta da burin da ya wuce ta ga ya yi sex da ita amma hakan ya gagara. Don ya faɗa mata gaskiya ba zai taba iya yin sex da wata mace ba matukar ba matarsa ba ne, addininsu ya gane su da aikata hakan. Lokacin da ta ji ja sanar da ita haka sai ta nuna masa cewa ya aure ta mana, ya nuna mata hakan ba mau yiwuwa ba ne, familyn da ba za su yarda ba, musamman yadda ya san yanayin kakansa Baffa . Don haka ta hakura ta kyale shi amma ta sawa ranta dole wata rana sai ya yi sex da ita ba za ta iya haƙura ba kamar yadda sauran ƴan matan suka haƙura. Don duk iskancin da yake yi da mace sai dai ita ta yi tsirara a gabansa amma shi sai dai ya cire riga da wando amma bexer na jikinsa ba zai taba barin ya yi tsirara tare da mace ba. Akwai wata mace mai suna Rahama ƴar wani attajiri ne suka tsaka da iskancin su ta ha kamar hankalinsa baya jikinsa dai ya fara ƙoƙarin tura hannu cikin gajeren wandon dake jikinsa, rike mata hannu ya yi tare da girgiza mata kai. Ba ta hakura ba ganin kamar baya cikin hayyacinsa ta fara ƙoƙarin tura hannu a cikin wandon nasa hakan ya saka ya hankaɗe ta tare da yi mata gargaɗi. Kuma tun daga ranar bai dake kula ta ba ta yi bi ta nada hakuri bai saurare ta ba. Kallon Alexandra dake kwance ta zuba masa idanu kamar ta cinye shi yake yi, kafin daga bisani ta saki murmushi tare da yi masa alama ya zo gare ta . Juyawa ya yi yana magana. "Ki tashi ki yi wanka mu bar garin nan." "Kana nufin yanzu za mu je garinku?" Kai kawai ya ɗaga mata ba tare da ya yi wata magana ba. Ganin haka ta tashi da sauri don ta ga ko walwala babu a fuskarsa. Ko da ta fito wanka ya har ya shirye ya saka ƙananan kaya. Ba zai ci komai ba don haka ya duba iya abinda Alexandra za ta iya ci. Coffee ya haɗa mata ya bata biscuits yayin da ta gama shirya ta karaso wajen. Sanye take da riga mara hannu iya guiwarta ta tsaya. Direbansa dake hotel ya kira ya sanar da shi ya zo za su tafi. _Fatima Zahrah_ Har lokacin barci take yi hankali kwance . Tana lullube da bargon da Sumayya ta lulluɓa mata lokacin da ta dawo duba ta ne ya lulluɓa mata bargon da rage gudun AC . Kamilu da Hial na zaune a falon bayan sun gama yin breakfast sai ga Hilal ya fito hannunsa rike da janar kayansa da kuma Jakar Alexandra. Cikin fara'a Sumayya ta gaishe shi ya masa mata ba yabo ba fallasa. Fita ya yi direbansa dake wajen mota ya hange shi ya ƙaraso da sauri. karba ya yi ya ki bayan motar. Yana komawa ne Sumayya ta ce. "Ga Zahra na barci har yanzu." Bai ce mata komai ba ya ciro kudi masu yawa a ajiye mata a gabanta ba tare da ya yi magana ba ya nufi ɗakin. Godiya ta yi masa amma bai amsa ba ya shiga ɗakin da Zahra ke ciki. Kallon Jamilu Sumayya ta yi tare da cewa. "Wannan abokin naka halinsa sai shi, ina tausaya wa matar da zai aura." Mumrmushi kawai Jamilu ya yi ba tare da ya y magana. Yana shiga har lokacin tans barci.kallo ɗaya ya yi mata ya san cewa ta ji sauƙin ciwon da yake damunta. Pillow da take kwance ya daka, ta bude idanunsa tare da sauke shi a fuskarsa, shi ma ita yake kallo fuska a tsuke. "Kin san yau za mu tafi tsabar wulakanci ya da kuka kwanta kina barci ko? waye yaronki da zai zauna zaman jiranki?" "Ka yi haƙuri kai na ke ciwo ne shi ya sa na kwanta." Tsuki ya ja sannan ya ce. "Na baki mintuna biyar ki haɗa kayanki ki same ni. Mota." Yana gama fadar haka ya fice zuwa ɗakin da yake. Kiran Alexandra ya yi suka fito tare sallama suka yi wa masu gidan suka fita. Da kallo suka bi su Sumayyaa ce ta iya amsa masu. Ɗakin da Zahra take ta shiga, ta same ta tana hada kaya. Jamilu ya yi sallama suka amsa sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga. Ganin tana hada kaya ya ce. ",Ai ba ki yi wanka kin shirya ba." Sumayya ta ɗora da cewa. "Ko breakfast ba ta yi ba." Jinjina kai ya yi ya ce. "Ki kwantar da hankali ki yi wanka ki ci abinci." "Mintuna biyar ya bani, kuka yanzu saura mintuna uku ." Ta fada tana saurin tattare komai nata. "Ba in da za ki tafi har sai kin yi wanka kin ci abinci." "Ku yi hakuri idan na ce gida zan yi." "Awa nawa za ku dauka a hanya, ba zai yiwu ba." Ƙwalla ta goge tana cewa "Kada ku damu ba na jin yunwa." Duk yadda suka yi sam ta ƙi ganin haka ya saka Sumayyaa ta yi saurin komawa kitchen. Abinci a flask ta kawo mata da karamin flask na ruwan zafi da bread ta haɗa a basket. Daidai suna fitowa Jamilu na rike da Jakkarta. Suka bita har wajen motar. Direba na gaba Hilal da Alexandra na baya, ta kwanta a ƙirjinsa. Bayan Jamilu ya daka kayanta a bayan motar. Ganin yadda suke manne da juna ya sa ta shiga gaban motar. Ba wanda ya hana ta don sun san gara ta zauna can ya fi mata. Sumayya ta miƙa mata breakfast nata a ta ce. "To idan na tafi da kayan waye zai kawo ki barshi kawai." "Na baki duka har da kayan." Godiya ta yi tare da yi masu sallama suka tafi. Jamilu ko kallon Hilal bai yi ba haka shima. Direba ya ja motar suka bar gidan suka ɗaya wa Zahra hannu. *Daga alƙalamin*✍️ Maman Ihsan ce *Yawan comments yawan typing* [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣3️⃣ Direba ya ja motar suka bar gidan suna ɗaga wa Zahra hannu. _Jiddrrh_ Jin motsi kamar an nufo toilet ɗin ya saka ta tsaya jikin bango ta bayan ƙofar yadda ko da an buɗe ƙofar ba za'a ji ta ba. Ko da ya tura ƙofar ta shiga sai ta tsaya tana ta waige-waige, ganin ba kowa abun ya bata mamaki don ko tantama babu ƙarar ƙofar ne ta ji. Ganin ba kowa ya saka ta janyo ƙofar ta fito. Tsayawa ta yi tana ƙarewa ɗakin kallo Sosa ganin ba alamar kowa ne ya saka ta yi ajiyar zuciya. Message ne ta ji ƙarar ya shigo cikin wayarta. Don haka ta duba tare da kiran wata lambar. Bayan an ɗaga daga can Muryar namiji ne ya ce. "Wai meke faruwa ?" "Ina jin kamar akwai matsala, na ga ƙofar nan ta ɗan buɗe. Sannan ina shigowa na ji kamar ƙarar rufe ƙofar toilet. Amma na duba babu kowa." Ki tabbatar kin duba da kyau sosai don idan har asirinmu ya tono tun yanzu ba mu kai ga mallakar dukiyar ba akwai ƙura. Don ba ga shi har yanzu haƙarmu ta gaza cimma ruwa." "Wannan shi ne dalilin da ya saka ya kasance a raye ba mu kashe shi ba. Ga shi baya cikin hayyacinsa. Kafin akai wannan matakin wani irin barazana ne ba'a yi masa ba ga shegen taurin kai kamar na uwarsa." Ta fada tana jan tsuki. Fita ta yi daga ɗakin da alama ranta a ɓace yake. Tana fita Jidderh dake cikin toilet ta fito daga cikin toilet ɗin. Kallonsa ta yi na tsawon mintuna biyu hawaye na bin kumatunta. Ganin yadda kyakkyawan matashin saurayi mai ji da kyau ga Naira yadda rayuwarsa ta kasance a yanzu. Kukan tausayinta kawai yake ji. "In sha Allah sai na bi duk wata hanya da zan bi don ganin na kuɓutar da kai daga waɗan nan azzaluman mutanen. Sai dai hanyar da zan fitar da kai ne zai bani wahala dole na nemi taimakon Yaya Isah. Shi kadai zai iya taimaka Mani don kuɓutar kai ." Goge hawayenta ta yi ta fice da sauri don gudun kada wani yazo ya ganta. _Hilal_ Sun isa Katsina lafiya lau, sai dai bai sanar wa kowa na gidan cewa sun taso yau ba, saboda ya san cewa zasu iya zuwa tarbonsa su saka idanau da zarar sun ji ƙarar mota. Don haka ya ɓoye masu sannan ya saka direba ya bi ta bayan gidan ta can wajan garden ɗin gidan. Don akwai ƙofar da za ta sadaka da part ɗin Hilal. Ita dai Zahra kallon ikon Allah take yi dalilin da ya saka ya sa abi ta baya, madadin gaban gidan. Sai da aka ƙara da daidai wajen ƙofar Sannan ya bawa direba umarnin tsayawa. Bayan ya tsaya durban ya fito da sauri ya bude masa masa. Fitowa ya yi yayin da direban ya bude wa Alexandra. Don ya sant da Hilal tun a U.S. Jakar kayansu ya cewa Direban ya fito masu da shi. Kai tsaye ya nufi ƙofar sai a lokacin Fatima Zahrah ta gane dalilin da ya saka ya bi ta baya. Da alama baya son mutanen gidan su san cewa ya zo da Alexandra. Hakan ya saka ya bi don kada a ga shigarsa da ita

Chapter 12 of 39