na dawo."
Bai tsaya jiran amsar sa ba ya fita, don shi ma Ammar ɗin baya da niyyar amsa masa. Don ya ji haushin abun da ya aikata.
Dada ta gasa wa Zahra ƙafa sosai sannan suka fito. Mai aikin Dada Inna Ladi ce ta shigo da sallama. Tattare kayan da suka ji breakfast ta yi ta kai kitchen.
Sai sannan Ammar ke jerawa Zahrah. Magani Dada ta bata ta sha sannan ta koma ɗakinta ta kwanta da taimakonka Dada.
Hilal kuwa zuciyarsa wasai ya nufi harabar gidan. Fita suka yi shi da sojojinsa a tare. Mota uku suka fita da ita.
_Mansur_
Bayan ya gana program din da zai gabatar ne kasancewarsa ɗan jarida ne. Yana zaune a office ɗin sa yana hutawa aka yi knocking. Izinin shigowa ya bayar yayin da abokin aikinsa mai suna Auwal ya shigo. Bayan sun gaisa ne ya ce.
"Mansur Adam Tafarki."
Kallonsa ya yi yadda ya kira cikakken sunansa sannan ya ce.
"Me kake so?"
"Fatima Zahrah Salis Tafarki."
Wani banzan kallo ya masa tare da tsuke fuska ya ce.
"Tashi ka fice mun daga nan."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Calm down my friend me ya yi zafi, walalhi ba da wasa nake ba Allah ya jarabe ni da son wannan sister ɗin taka ce."
"Wace ce sister ɗin ta wa?"
"Kamar yadda kowa ya san cewa daga familyn Muhammad Tafarki kuke wato kakanka, kowa ya san sunanka ne Mansur Adam Tafarki, kuma Zahra Salis Tafarki ƴar ƙanin mahaifinka ne ai ƴar uwarka ce ."
"Ba na da alaƙa da ita don haka ka fice ka bani waje, kuma kada ka sake zuwa Mani da makamancin wannan zancen, idan ba haka ba wallahi sai na maka rashin mutunci."
Mamaki ne ya kama shi don haka ya mike tare da cewa.
"Allah ya kyauta ."
Tsuki Mansur ya ja tare da bin bayansa da harara.
"Da ka san yadda na tsani yarinyar nan da ba ka zo Mani da wanann zancen ba. Mtsww."
_Ammar_
Kasancewar yana son barin garin ya saka ya yanke shawarar zuwa part ɗin su Zahrah da kansa.
Knocking ya yi a ƙofar falon, Sadik ne da ya shirya cikin kayansa na lauya yana sauri zai je kotu. Yana shirin shiga yin sallama da Ummi ne ya ji knocking ya nufi kofar ya buɗe. Ammar ya gani a bakin ƙofar duk da ya ɗan yi mamakin ganinsa kasancewar sa abokin Hilal. Kuma Hilal shi kansa ba gaida Abbi da Ummi yake yi ba ballantana wata alaƙa ta shiga tsakanin abokinsa da su.
Murmushi Ammar ya sakar masa tare da mika masa hannu. Gaisawa suka yi sannan ya ce.
"Suna ciki?"
"Eh bisimillah."
Shiga ya yi yayin da Sadik ya mayar da kofar ya rufe. Ammar ya zauna a kujerar yayin da Sadik ya shiga ɗakin Abbi tare da sallama. Ya same shi yana duba wasu file.
Abbi ya masa masa sallamar tare da cewa.
"Barrister ka fito kenan."
"Eh Abbi zan tafi ne sai ga wannan abokin Yaa Hilal ya zo yana falo."
"Wane abokinsa wanda ya zo daga Ingila ?"
"Eh Abbi yana falo yanzu haka."
Shiru Abbi ya yi kafin ya ajiye file ɗin hannunsa ya bi bayan Sadik zuwa falo.
Abbi na fitowa Ammar ya sauka daga kan kujerar da yake zaune ya durƙusa har ƙasa ya gaida Abbi.
Abbi ya amsa masa cikin sakin fuska da walwala tare da tambayarsa gajiyan hanya.
Amsawa ya yi da Alhamdulillah yayin da yake komawa ya zauna.
Ummi ce ta fito daga cikin ɗakinta ita ma kallon Ammar take yi tare da yi masa barka da shigowa.
Ita ma sai da ya durƙusa ya gaida ita kamar yadda ya gaida Abbi. Ita ma Ummin amsa masa ta yi cikin sakin fuska da walwala kamar yadda Abbi ya masa.
Ammar ya fahimci cewa iyayen Zahrah suna da mutunci da karamci. Kasancewar ya san ba zaman dad'i suke yi da iyayen abokin nasa ba, duk da sun san alakar dake tsakanin sa da Hilal sun tarbe shi da kyau .
Shiru ne ya biyo baya in da Ummi ta shiga kitchen ta kawo masa cake da ta haɗa sai kuma lemun kwali ta ajiye masa, kasancewar yau girkin mai aiki suka ci su ma .
Haka kwai Ammar ya tsinci kansa da jin kunya irin na surukai. Ya kasa ci ya kasa sha sai sunkuyar da kai ƙasa ya yi .
Abbi ne ma ke ɗan jan sa da fira, wanda ganin haka ya saka shi ma ya fara yin fitar. Sadik ne ya masu sallama ya wuce . In da Ammar ke cewa.
"Allah ya bada sa'a barrister."
Da Amin ya amsa yana murmushi ya fice.
Ɗan jimawa kaɗan Ammar ya yi masu sallama ya fice daga part ɗin. Duk da su ba su san me ya kawo shi ba amma ba su kawo komai a cikin ransu ba.
_Jidderh_
Jin ta a ƙasa ya saka ta saki ƴar ƙara tare da cewa.
"Wayyo Inna ta ."
Kallon tuhuma Aunty ta yi mata tare da cewa.
"Wace ce ke, kuma me ya shigo da ke cikin gidan nan?"
Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalli Aunty tare da cewa.
"Ni ba kowa ba ce face marainiya."
"Me kike ƙullawa a cikin gidan nan?"
"Wallahi ba a abinda nake ƙullawa sai alkhairi."
Tsuke fuska Aunty ta yi tare da cewa.
"Duk yanayin rashin gaskiya ya bayyana a jikinki, ɗazu na fito na hange ki kina saɗa kika ce Mani Mama kike nema bayan kin san ba ta wajen. Bayan na koma ɗakina na hange ki kina biyiwa ta nan kina juye-juye alamar ba ki son wani ya ganki. "
Shiru ta yi don ba za ta iya fada mata abinda ya kawo ta wajan ba, musamman da Asadullah ya ce kar ta faɗa mata. Yanzu ya za ta fitar da kanta take tunani.
Maganar Aunty ce ta katse mata tunini.
"Ina saurarenki me kike yi a nan, wajen da ba kowa a wajen me kika je yi?"
"Kawai dai na ce bari na zagaya ne na ga Asadullah mansion ɗin na da girma ban sani ba sai...."
"Ke raina mani hankali za ki yi ne?"
Jan hannun Jidderh ta yi suka koma in da ta ga Jidderh ta fito, ta ce sai ta nuna mata abinda ta zo yi nan. Jidderh kuka ta saka mata tana cewa ba komai zagayawa kawai take yi.
Ganin wurin ba wani abu na daban ya saka ta kalli Jidderh ta tare da sakin hannunta tana mata gargadi akan ta tsaya iya abinda ya kawo ta gidan.
Jidderh ta wuce ciki tare da shiga ɗakin masu aikin gidan. Kallonta Mama ta yi tare da cewa.
"Jidderh Lafiya kuwa?"
Murmushi ta ƙakalo ta ce.
"Lafiya lau Mama."
Wayarta ta ciro daga cikin aljihun dogon rigarta ta nemi wani lamba ta tura sakon text message.
Ba jimawa kira ya shigo wayar. Ganin mutanen dake cikin ɗakin suna kallonta ya sa ba ta ɗaya ba. Har Larai ta ce.
"Ba kiranki ake yi ba?"
"Uhm"
Katse kiran wayar ta yi sannan ta tura text message.
Kusan sau uku ana turo mata da messages tana mai da reply kafin ta tashi da sauri kamar wacce aka tsikara ta shiga ɗakin Mom."
Sanin Mom ba ta gidan ya saka ta hau bincike a cikin ɗakin na ta. Ganin ba ta samu abun da take nema ba ya saka ta saki tsuki cikin takaici.
Har ta nufi kofar sai ta juya ta kalli wani dorowa wanda sam hankalinta bai kai gare shi ba.
Buɗewa ta yi sai ta saki murmushi lokacin da ta yi tozali da keys ɗin da ke cikin dorowar. Da sauri ta kai hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin makullan dake cikin drawar ɗin.
Saka shi ta yi cikin aljihunta sannan ta nufi ƙofar fita.
Daidai lokacin da Mom take dawowa daga unguwa. Tana sanye da mayafin take sai handbag ɗin ta daje riƙe a hannunta.
Gaban Zahrah ne ya fadi sakamakon ganin irin kallon da Mom ke yi mata.
"Me kike yi a ciki?"
"Mom na je na gyara maki ɗakin ne?"
"Ina tun safe kika gyara Mani ɗakin ko?"
"Eh na duba ko akwai abinda zan kara yi ne?"
Wani kallo Mom ta yi mata na rashin yarda kafin ta ce
"Shi kenan je ki."
Ajiyar zuciya ta sauke ta fice da sauri daga ɗakin.
Da kallo Mom ta bita zuviyarta cike da tarin tambayoyi.
Sai da ta ga ta ɓacewa wa ganinta ne ta shige cikin ɗakin tare da tura ƙofarta ta rufe.
Sulaiman take ta raba idanun nemansa amma ba ya nan. Sai dai sauran guard ɗin da wasu security.
Komawa ta yi ta nufi wata hanya. Can sai ta fito dauke da wani galam na fetur da ashana a hannunta.
Wannan karon ba ta bi hanayar da Aunty ta gan ta ba sai ta bi wata hanyar daban ta zagaya.
Sai da ta ɓulle in da take son zuwa sannan ta buɗe galan ɗin fetur ɗin ta watsa a plate ɗin da ke wajen, sannan ta watsawa a na kusa da shi. Duk ta watsa bayan ta zuge glass din window har ciki ta watsa .
Ja baya ta yi daga wajen sannan ta ƙyasta ashana ta jefa ciki.
Take wuta ya tashi bal bal a wajen. A guje ta zagaya in da ba wanda zai hange ta a guje.
_Hilal_
Motocinsa ne suka cinno kai cikin gidan. Bayan direban motar da Hilal ke ciki ya yi parking ne wani soja ya fito da sauri ta bude masa murfin motar.
Ƙafarsa ɗaya ya ziro waje kafin ya fito da ɗayan kafar gabaɗaya. Ƙamewa sojojin suka yi ba ogan na su.
Da sallama iya fatar bakinsa ya shiga babban falon gidan. Sautin dariyar da ya ji ne ya saka ya juya ya kalle su. Ammar ne da Zahrah yana ba ta labari ita kan sai dariya take yi masa.
Kallo ɗaya yi masu ya ɗauke kai tare da nufar upstairs. Ba su san da shigowarsa ba sai yakin takalimnsa da suka ji yana hawa upstair. Ammar ne ya ce.
"Man ka dawo?"
"Eh Ammar ya faɗa ba tare da ya juyo ba."
"Nabeela da Kusar ne suka fito daga part ɗin su. Ganin Zahrah da Ammar ya saka Kausar ɗura wata uwar ashar
Da sauri ta koma tare da ƙwalawa Aunty Laila kira tana cewa.
"Mum! Mum!!!"
Da sauri Aunty Laila ta fito tana cewa.
"Lafiya wannan kiran kamar na mafarauta?"
"Mum zo ki ga wannan mayyar yarinyar yadda ta liƙewa Yaa Ammar ?"
Ita dai Mum ba ga gane abinda take nufi ba ta sai biyu bayanta ne.
Tana zuwa ta ga Ammar wanda ke zaune tare da Zahrah. Kallon sa Aunty Laila ta yi mata ya sa ta sunkuyar da kai ƙasa.
"Ai dole ki sunkuyar da kai mana munafuka, tun da kin saba da bin maza kamar karya, shi ma wannan ɗin da yake kamilalle ne za ki saka shi cikin jerin ƴan iskan mazan da suke bin ki.?"
Ammar kallon Aunty Laila ya yi da mamaki , don ya san ita ɗin Gwaggo ce a wajen Zahrah saboda don sanin kowa bayan an yaye Salis Muhammad Tafarki ne aka samu ciki aka haifi Laila Muhammad Tafarki. Mahaifin Zahra take bi. Tana matsayin uwa a gare ta take faɗin haka.
Maganar Aunty Laila ya ke nazari can ya ji ta ce.
"Kai ko Ammar me ya haɗa ka da wannan yarinyar?"
"Son ta nake kuma aurenta zan yi."
Ba iya Nabeela da Kusar ba hatta Aunty Laila ta tsorata gabanta ya fadi . Don ta ƙudira niyyar idan har Allah ya cikaata burinta Hilal ya auri ɗaya daga cikin yaranta sai Ammar ya auri ɗaya. Amma wannan Zharah ta zame mata ƙadagaren bakin tulu.
"Haba Hilal yanzu duk matan da suke gidan nan ka rasa wacce za ka ce kana so sai wannan yarinyar? Wannan yarinyar fa angulu ne da kan zabo, kana ganinta kamar na Allah amma ba haka ba, kana ganinta nan har ciki ta zubar a cikin gidan nan, idan kana ganin ƙarya ne ka tambaye abokinka Hilal ka san dai idan ni ba ka yarda da maganata ba shi za ka yarda da ta sa. Duk da ya shiga cikin firgici amma sai ya daure ya ce.
"Aunty wannan ba damuwa ba ce, zan iya aurenta kuwa a duka yadda take?"
Nabeela da ta ƙulu da maganarsa ta ce.
"Haba Yaa Ammar ai..."
Kallon da ya jefa mata ne ya saka ta fasa ƙarasa maganar ta.
Zahrah kuka take yi mai cike da ƙunar zuci, wace irin rayuwa ne a ce wai dangainta su ne suke mata irin wannan ƙazafi haka ne ta tare masu ne tashi ta yi zata bar wajen ya rike mata hijabi ya ce.
"Daina kuka ki share hawayenki duk yadda kike duk yadda kike ina son ki a haka. Ko da a gidan ƙaruwai kike zaune wannan ba damuwa ba ne wallahi ina ƙaunarki fisabilillah."
Yana sakin hijabinta ta ruga part ɗin Umminta tana kuka.
Bai sake kallon in da Aunty Laila take ba ya juya ya nufi upstairs cikin wani irin yanayi.
Jinjina kai Sunyi Laila ta yi tare da cewa.
"Wallahi ba za ta saɓuba bindiga a ruwa, Zahra ba za ta auru ba ina cikin gidan nan. Ga sauran yayunta nan sai ita ce ƙaramar su. Ga farin jinin tsiya anya kuwa uwarta zaune take a kanta?"
Kwafa ta yi ta koma part ɗin ta ƴaƴanta suka mara mata baya.
_Jidderh_
Numfashi take maida wa bayan ta koma nesa da in da ta cinna wuta.
Hankalin security ne ya fara zuwa ga wutan dake ci a wuri. Da mamaki kowa ke kallon wajen da aka ce gobara ya tashi don a iya saninsu ba kowa a ciki me ya kai wuta wajen.
Uncle Adam ne tare da Mami suka fito daga part ɗin su, sakamakon hayaniyar ma'aikatan gidan da suke yi. Naseer, Maryam, Abida suka mara masu baya.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page4️⃣1️⃣
Uncle Adam ne tare da Mami suka fito daga part ɗin su, sakamakon hayaniyar ma'aikatan gidan da suke yi. Naseer, Maryam da Abida suka mara masu baya.
Mamaki da al'ajabi haɗi da tashin hankalin ne ya bayyana a tare da su.
Can sai ga Aunty da ƴarta Suhailat sun fito Mom da Fauziyya ne a bayan su.
Gabaɗaya kowa ya shiga tashin hankali da ganin wutar yayin da security da ma'aikatan gidan ke ta ƙoƙarin kashe wutar. Amma kamar ana ƙara ilangiza masa fetur. Gabaɗaya hankalin kowa a tashe gidan duk ya hargitse kowa sai ƙoƙarin bada gudummawar sa yake yi. Hatta security dake bakin gate sun bar wajen kowa hankalimsa na kan wutar.
_Jidderh_
A daidai wannan lokaci ne Jidderh ta nufi ɓangaren da Asadullahi yake. Hannunta rike da wani baƙin riga, Key ɗin sa ta ɗauko ɗakin Mom wanda take da tabbacin zai iya buɗe kowane ƙofa na gidan.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin murmushi lokacin da ta ga ƙofar a buɗe.
Daidai lokacin da motar kashe gobara ta shigo gidan. Jin ƙarar sautin motar ta ce.
"Yallaɓai ka hanzarta mu bar gidan nan ba lokaci."
Rigar sanyin ta ɗaura masa a saman kayan dake jikinsa, rigar kai hula ce sai ta janyo hular ya rufe kusan rabin fuskarsa, facemask ta saka masa don ta lura kamar jikinsa ba ƙarfi ko kaɗan. Ga ƙafarsa ma kamar ba za su iya ɗaukar sa ba.
"Yallaɓai mu tafi ka sunkuyar da kai yanzu ba wanda hankalin sa zai zo gare mu, mu yi saurin fita akawai motar dake jiranmu a waje, idan wutar nan ya mutu hankalin wasu zai iya dawo wa ga jama'a har a gane mu.
Jin haka ya tattara dukkan ƴar karfin dake jikinsa, sakamakon jikinsa ba ƙarfi don alluran da suke masa yana kashe masa jiki da kuzari dake jikinsa. Ta yadda ba zai iya yunƙurin cewa zai ƙwaci kansa ko ya gudu ba.
Daƙyar take ɗaya ƙafarsa tana gaba yana bin bayanta.
Hankali kowa na wajen wutar, hatta wadanda gidansu ke kusa da mansion ɗin sun shigo.
Bai ɗaga kai ya kalli kowa ba amma daƙyar yake tafiya. Jikinsa sam ba ƙarfi kamar ba nasa ba. Kasancewar mansion ɗin akwai girma sun yi doguwar tafiya kafin suka iso gate ba kowa a wajen. Sai wani security dake waya hankalinsa ma baya jikinsa yana magana ne akan wutar.
Ajiyar zuciya ta sauke daidai lokacin da suka fita daga gidan. Sai sai kuma wata mummunar faduwar gaba da ya ziyarce ta. Wanda har sai da ta dafe ƙirjinta.
Suna ƙarasawa wajen motar da ta saka ya zo ta bude bayan motar ta ce.
"Yallaɓai shiga."
Yana shiga ita ma ta zauna gefensa sai kanta da ta ji yana ɗan juya mata. Direban ya ja motar suka bar wajen.
Suna fita daga cikin unguwar suka kama hanyar in da Jidderh ta ce ya bi da su.
Wato unguwarsu gidan iyayenta kenan take so ya kai su.
Daidai kan wata kwana wata babbar mota ta zo ta daki motarsu wanda hakan ya saka motar ta gangara ƙasan titi ta daki wani bishiya.
Gaban motar ta ragargaje sai sai cikin ikon Allah ba wanda ya fito daga cikin motar .
Jama'a aka taru aka buɗe masu suka fito. Tabbas da Asadullah bai saka wannan hular da facemask ba da jama'a sun gane shi .
Direban ya shiga tashin hankali sosai ba kaɗan ba. Sai kuka yake yi yana wayyo Allah ya zai yi da mutumin da ya bashi bayan motar ga shi bai da mutunci akan kuɗi ba zai dauki asara ba.
Jidderh dai gata nan ne sai kallonsu take ta kasa magana. Sai dai ta dafe kanta tana yamutse fuska.
Kowa na ta masu Allah kiyaye gaba, ganin kowa ya tsira da ransa. Ganin yadda direban ke sambatu ne ya saka wasu ba tausaya masa akan rashin mutunci na mai motar da zai masa.
Dafa kafadarsa ya yi tare da cewa.
"Zan biya ka kudin motar."
Wani kallo ya masa tare da cewa
"Kasan nawa kudin motar, kana da kuɗin siyen motar ne ka saka aka nemi ni? Ga direban da ya buge mu ya gudu."
"Wallahi zan biya ka na ce ka kwantar da hankalinka."
"Waye kai?"
"Sanin waye ba shi ne ya fi mahimmanci a gare ka ba, yanzu ka bani takarda da biro zan aike ka wata kotu ne , idan ka je ka kai masa sakon zai zo tare da kai."
Kwatancen ya yi masa sannan ya nemi ya bashi takarda da biro, ya nemo ya bashi ya yi wani rubutu ya ninke ya mika masa.
"Idan ka je ba za'a bari ka shiga ciki ba, ka ba wa security wannan takardar ka ce a kawo Barrister Haris Umar wannan takarda. Sai ka jira ya fito.
Karba ya yi da sauri ya nemi abun hawa ya hau suka bar wajen. Asadullah ya kalli Jidderh ya ce .
" ki zauna a inuwa."
Daƙyar yake magana saboda ba kwari ƙafarsa ma sun gaza ɗaukarsa jingina ya yi da motar.
Ba ta ce komai ba sai kallonsa. Sau uku yana mata magana ita dai sai ido ba baki. Mamaki ne ya kama shi ganin yadda ta koma don haka.
_Zahrah_
Da kuka ta nufi part ɗin su Ummi da fitowarta kenan daga kitchen ta bi ta tana kiran sunanta.
"Zahrah me ya same ki?"
Zubewa a gadon ta yi tana kuka mau cin rai, take Kuma sai numfashinta ya fara fita daƙyar.
Hankalin Ummi ya tashi sosai da sosai don da alama ciwonta ne ya tashi.
Cikin tashin hankali ta fara laluben in da za ta ɗauko mata Inhelar ɗin ta.
Sai ta neme shi ta rasa handbag da ta fita last das shi ta nema ta rasa. Ga shi a cikin wannan yanayin da take ciki ba za ta iya shan magani ba, ɓangaren Dada Ummi ta shiga tare da sallama.
Papa da Dada ne a falon ganin yanayin Ummin ya saka suka mike suna tambayarta meke faruwa. Da
"Dada ko handbag ɗin Zahrah na nan ne?"
"Eh to bari na duba ɗakinta ko yana nan?"
Shiga Dada ta yi wanda Ummi ke ganin tafiyar Dadar ya mata nawa, sakamakon ciwon ƙafarta ba ta iya tafiya da sauri.
Papa ne ya kalli Ummi ya ce.
"Ba dai ciwon nata ne ya tashi ba ko?"
"Eh Papa shi ne ya tashi."
Tare suka hada baki da Dada wajen cewa.
"Subhanallah"
Ummi na karbar jakkar ta buɗe ta cire Inhelar daga cikin kakar ta ajiye harkar a kan kujera mai zaman mutum uku.
Gabaɗaya suka fito Ummi na gaba Papa da Dada suna baya.
Suna kawowa tsakiyar babban falon gidan suka ga Hilal da Ammar suna saukowa daga downstairs.
Ganin halin da suke ciki ne ya saka cikin tashin Ammar ke tambayar su abinda ke faruwa. Hilal kam tun da ya gan su ya san kwanan zancen, don ba shakka ya san ciwonta ne ya tashi.
Papa ne ya ce .
"Zahrah ce ba lafiya."
"Subhanallah"
Ya bi bayansu yayin da Hilal ya taɓe baki ya nufi part ɗin su Dada, dama can za su je shi da Ammar ɗin.
Suna shiga suka same ta cikin wannan halin, hankalin Ammar ya yi mugun tashi musamman da bai san Zahra na da ciwon athma ba.
Inhelar Ummi ta rike bayan ta zauna bakin gadon ta janyo kan Zahra ta ɗaura a saman cinyarta ta kafa nata shi.
Ba jimawa ta ja numfashi, sai a lokacin Ammar ya gane cewa tana da larurar asma.
Sai dai duk da haka numfashin nata baya fita daidai yadda ya kamata.
Kuma sai hawaye take yi daga ganinta kasan akwai bakin ciki a tattare da da ita. Da
Hilal kuwa yana shiga part ɗin Dada ya zauna a kujera mai zaman mutum uku.
Ganin Handbag ɗin ne ya san dai ba na Dada ba ne don wannan na ƴan mata ne.
Miƙa hannu ya yi ya janyo jakkar don zuciyarsa ta bashi na wace ce.
Wayoyinta ya fara cin karo da su, ɗaukar wayar ya yi cikin sa'a kuwa ba password a jiki. Tarin missed call ya gani dubawa ya yi ya ga mutane da yawa amma akasari kiran mutane uku ne ya fi yawa Amininta da Aminiyarta sai kuma Mustapha wanda yake Mustapha Umar da ya nace mata a school.
Sai ya shiga wajen messages nan ya ga tarin sakonnin da ake tura mata masoyanta, sai dai ba ta masu reply. Har mamakin yawan masoyanta yake yi. Don kowa da ƙokon baransa yake akan ta masa soyayyarsa.
Social media ya shiga nan ma ya ga bata cika ta'ammali da social media ba.
Gallery din ta ya shiga, in da duk photo na school ko wanda ta ɗauka a waje to tana sanye da facemask da glass ne, idan kuma ta sanya Hijabi to za ka ganta da niƙab. Amma photon da a gidan aka dauke shi to shi ne za'a ga fuskarta. Sai kuma idan sun yi selfie 🤳 ita da Amininta da Aminiyarta ne takan sauke miƙa facemask ko ta ɗaga ñikab.
A can bangaren Zahrah kuwa sai da numfashinta ya daidaita ne sannan Dada ta fito ita da Papa. Ammar ma ya mara masu baya bayan ya gama jera wa Zahrah sannu. Ummi ta yi masa godiya tana yaba kirkin yaron a zuciyarta.
Ko da suka koma Part ɗin Dada Ammar ya zauna gefen Hilal ganin ya shiga what'sup ɗin ta ne ya saka Ammar cewa.
"Me kake dabawa a wayar Zahrah?"
Tsuki ya ja sannan ya ce.
"Ƴa mace sai da saka idanu ana binciken wayarsu don sanin abinda suke aikatawa da waya."
Jinjina kai Ammar ya yi tare da cewa.
",Haka ne, domin waya da kake illarta ta fi amfaninta yawa. Ya lalata tarbiyyar yara da yawa duk da dai ko da wasa ba zan kawo Zahrah za ta iya aikata wani abu na rashin daidai ba. Don na san na zaɓawa ƴaƴana uwa ta gari wacce zan yi alfahari da ita duniya da lahira."
Taɓe baki Hilal ya yi don tare da ajiye wayar. Kallon Dada ya yi tare da cewa.
"Yunwa nake ji."
"Sai ka je ai na san ba'a rasa abinci a gidan nan ba."
"Bana son cin abincin masu aiki kin sani."
"Uhm to sai ka je ka saka Maryam ko Nadiya su dafa maka."
Tsuke fuska ya yi tare da cewa.
"Ba abinda yaran nan suka iya, ranar da na saka su dafa mani indomie kasa ci na yi."
"To ka sanya Kausar ko Nabeela wata ta dafa maka."
"Wallahi gara kowa da waɗan nan yaran ba abinda suka iya."
"Hmmm Laila dai tana cutar yaranta ne, idan na yi magana ta ce wai na tsani yaranta kamar yadda na tsane ta ba na son su."
Ammar ya ji dariya ya ce .
"Ina fatan dai Zahra ta iya ko?"
"Sosai kuwa ai Zahrah ƙarshe ce, idan tana girki sai kamshi ya cika ka ga dad'i a baki hannun uwarta ta ɗauka akwai dadin girki. Ya ka ji wannan sinasir da ka ci?"
"Ita ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 39