fa alama hukuncin na san ba zai yi wa kowa dad'i ba."
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
Page5️⃣9️⃣
Allah masani sai dai goben mu ji hukuncin da zai ɗauka. Tabbas ban taɓa ganin Papa cikin irin wannan ɓacin rai haka ba, kuna da alama hukuncin na san ba zai yi wa kowa dad'i ba."
Jingina lamarin Ummi ta yi kafin ta ce.
"Tabbas da alamar haka."
_Zahrah_
Horn ta yi a bakin gate yayin da security ya bude mata ƙofar ta shigo da motarta ciki .
Hilal dake tsaye a harabar gidan ya hangi shigowarra. Dama ita yake jira ya hadu da ita.
Kai tsaye ya nufi parking space ɗin, tana gama parking ta turo murfin motar za ta fito. Tana saka ƙafa ɗaya a waje ta ganshi tsaye rike da murfin motar fuskarsa a murtuƙe.
Ɗaga niƙab dake fuskarta ta yi don ya samu damar ganinta yadda ya dace, ita a tunaninta bai gane ta ba ne tun da ko magana ba ta haɗa su, Gaisuwa ma idan ta masa baya amsawa. Hakan ya saka ta yi tunanin bai gane ta ba ne tun da ya zo wajen motarta ya tsaya.
Sai dai tana cire niƙab ɗin fuskarta ta bayyana ya shaƙo wuyan hijabinta ya murɗe. Nan take hijabinta ya shake mata wuya ta fara fafutuka da rayuwarta, Idanunta sun firfito waje, sai da ya ga kamar za ta dauke numfashi sannan ya sake ta ta fadi ƙasa yaraf. Kin yi kuskure na shiga gonata, har kin yi tasirin idanun da za ki ɗauki photo na ki kai wa Papa?"
Ɗago ta ya yi ta mike tsaye tagwayen maruka biyu ya sauke mata a fuska, kafin ya yi jira da ita ta fadi a wajen ta ƙoje sai ga jini ya fara zuba daga hannunta.
Zare belt ya yi daga jikin wandonsa yana cewa .
"Ke ga munafuka ko? Mai kai rahoto wallahi wata rana ko an ce ki shiga harkata ba za ki shiga ciki ba."
Belt ɗin ya rike ya dinga dukanta da shi, ihun azaba da take yi ne ya saka ma'aikatan gidan ƙsrasowa wajen don ganin meke faruwa.
Carko-carko suka yi suna kallon yadda yake dukan Zahrah kamar Allah ne ya aiko shi.
Tausayin ta cika su, don sun san cewa Zahrah ba ta da hatsaniya ko wani abu da zai saka ya dake ta, hasalima tafi sauran yaran gidan nutsuwa, hankali, da sanin ya kamata.
Take jini duk ya ɓata farin hijabin dake jikinta. Ganin da suka yi ba su da zarrar da za su tari gabanshi ne ya saka ɗaya daga cikin direban gidan ya ruga don kiran wani daga cikin gidan.
Zuwa lokacin Zahrah ko motsi ba ta yi jikinta duk ya farfashe da duka ta daina motsi kamar matacciya, sai da ya ga ta daina motsi sannan ya bar ta nan kwance, motarsa ya shiga ya fige ta, da sauri maigadi ya wangale masa gate saboda tsorata da yanayinsa. Ya bar gidan a guje.
A babban falon gidan ya yi sallama sai dai ba kowa a falon, don haka ya karasa part ɗin Dada ya ya yi sallama .
Dada ta amsa tare da bashi izinin shigowa.
"Dada ku kawo ɗauki soja zai kashe Zahrah."
Salati Dada ta saka tana ƙwalawa Papa kira, ba shiri ya fito yana tambayar me ya faru.
"Wai Hilal ne zai lashe Zahrah."
"Suna ina?"
Papa ya tambaye direban.
"Suna parking space don daowarta kenan."
Da sauri suka fita don zuwa parking space, duk da kasancewar su tsofaffi ne amma suna da ƙwarin jiki.
Suna ƙarasowa parking space daidai lokacin motar Mahmud ta karaso. Ganin suna cikin tashin hankali ya saka ya fito daga cikin motar da sauri, ya bude baki da niyyar ya tamabaye su abun da ya faru sai ya yi tozali da Zahrah dake kwance ba ta motsi.
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Shi ne kalmar da ya furta ya karasa wajen da take kwance yana cewa.
"Accident ta yi ne?"
Ba wanda ya iya magana don Dada da Papa ma sun kiɗime da ganin halin da suka gan ta a ciki.
Mahmud ya durkusa ya ɗauke ta yana cewa.
"A kai ta asibiti mana."
"A'a ka kai ta ɗakinta dake ɓangarena zan kira Doctor ya zo da kayan aiki, zai yi mata duk abinda ya dace."
Daga haka ya yi gaba Mahmud ya bi bayansa suka koma cikin gida.
Ɗakinta dake bangaren Dada ya Mahmud ya kai ta. Akan gadonta ya shimfidar da ita. Har lokacin ba ta motsi.
Daidai nan Papa ya kira Doctor a waya, bayani ya yi masa ya ce ya zo da kayan aiki gida.
Nan Doctor ya ce masa ga shi nan zuwa.
Mahmud ya kalli Papa cikin damuwa ya ce.
"Me ya same ta haka ne?"
"Wai Hilal ne ya yi mata duka ."
Zaro idanu Mahmud ya yi yana cewa
"Wane irin duka ne haka kashe ta ya yi niyyar yi ko me?"
Fita daga dakin ya yi da sauri zuciyarsa na masa zafi, ganin ƙanwar ta sa a cikin wannan halin ba karamin tashin hankali ya saka shi ba, duk da cewar ba ƙaramin abu ba ne idan aka ce Hilal ya yi wa mutum irin dukan nan, saboda yana da zafi, amma ya tabbata Zahrah ba za ta aikata masa laifin da zai yi mata irin wannan dukar ba, Gara kowa a gidan nan idan ya dake su amma ban da Zahrah. Ba za ta yi masa laifin da zai mata haka ba.
Yana shiga part ɗin ya dinga ƙwalawa Abbi Kalifa, da kuma Ammi.
"Abbi Ammi."
Ya fada cikin daga murya.
Ba shiri Abbi da Ammi suka fito daga cikin falon, don su san wannan kiran ba na laflya ba ne, musamman jin Muryar da sun san ba komai yake magana a kai ba saɓanin Sadik.
"Lafiya Mahmud.?"
"Zahrah ce Hilal ya yi wa mugun duka ko motsi ta kasa yi."
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Ummi ta fada cikin tashin hankali.
Gabaɗaya suka fita zuwa part ɗin Dada har dakin Zahrah suka shiga . In da suka tarar da Papa da Dada akanta.
Shigowarsu ba jimawa sai ga ga Daddy da Mummy sakamakon kiran da Papa ya yi masu.
Suna shigowa suka zuba idanu akan Zahrah, sai Ga Umma da Abba sai Aunty Laila a ƙarshe.
Kowa ya kasa yin magana suna ta tambayar kansu abinda ya dame ta.
Gyaran murya Papa ya yi tare da kallon Daddy ya ce .
"Kun ga abinda yaron nan Hilal ya aikata wa yarinyar nan ko? Akan abu da ba t d masaniya akai, lallai sai ya biya bashin abinda ya aikata, sai ya gyara abinda ya ɓata."
Kowa ya kasa magana Ummin Zahrah sai zubar da ƙwallar tausayin ƴarta take yi.
Doctor ne ya shigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama.
Gabadaya suka amsa masa ya shigo hannunsa dauke da kakar kayan aikinsa.
Gaisawa ya yi tare da suka gaisa sannan Papa ta ce sun fita su ba Doctor wuri ya yi aikinsa."
Gabaɗaya suka yi daga dakin Ummi ta nufi part ɗin su da sassarfa ƙwalla na ciko mata idanu.
Ganin haka Abbi da Mahmud suka bi bayanta. Tana shiga ciki ta tarar da Sadik wanda dawowarsa kenan ya ga ba kowa a part ɗin.
Cikin tashin hankali ya nufi mahaifiyarsa yana rike hannunta ya ce
"Subhanallah! Ummina ya aka yi ko mutuwa ce ka yi ban sani ba."
Kasa magana ta yi sai kuka , Mahmud ya rike hannunta yana cewa
"Dan Allah ku yi hakuri Ummi ba cewa aka yi ba za ta tashi ba, in sha Allah yanzu za ta farfaɗo tun da Doctor ya zo ,"
Sai a lokacin hankalin Sadik y je ga Zahrah yana cewa.
"Ina Zahrah ne ya same ta, ba dai ciwonta ne ya tashi ba ko?".
Haka y jera masu tambayoyi, yana kallonsu cikin tashin hankali. Mahmud ne y yi karfin halin cewa.
"Yaa Hilal ne ya yi wa Zahrah dukan mutuwa ga ta can ɓangaren Dada ko motsi ta kasa yi."
"What's!"
Kai Mahmud ya jinjina masa alamar tabbatar da cewa maganarsa haka take .
Ciki. Fusata Sadik ya fara magana.
"Wannan wani irin cin zali ne, na tabbatar da cewa Zahrah ba za ta shiga sabgarsa ba, na ji shaidar cewa Zahrah ko mu fa muke uwa ɗaya uba ɗaya ba za ta aikata mana abun da za mu dake ta ba, ballantana shi da yaran gidan ne tsoronsa."
Nisawa ya yi kafin ya ce .
"Yanzu wane mataki akan ɗauka akan abinda ya yi wa Zahra.?"
"Kai ma ka san ba wani matakin da za'a dauka akansa tun da ya zaba hukunta yaran gidan sai dai a ce wannan karon ya uku tsauri da yawa."
Da mamaki Sadik ke cewa .
"Ai ko wannan bai dace a yake shi ba, don na ga alamar gabadaya gidan nan shakkar sa ake yi, ba mai iya dakatar da shi . Zan same shi na fada masa gaskiya duk abinda zai faru ya faru."
Yana gama fadar haka ya ce.
"Ina za ka je?"
"Zan je na samu Hilal ne sai na fada masa duk maganar ta zo bakina, tunda anan gidan ba mai iya magana , ka duba yadda ya saka Mahaifiyar mu kuka ba zan ƙyale ahi ba. Sai dai ya kashe ni."
'idan ka fita a nan sai ranka ya ɓaci "
Cewar Ummi tana goge hawayen fuskarta, kafin ta cigaba da cewa
"Na tabbatar da cewa Papa da Dada ba za su bar shi ba har shi ba."
Nan da daina kuka sabida sanin zuciyar zuciyar Sadik , kuma ba su fada masu komai abinda ya saka ya dake Zahrah. Sai da Ummi ta saka wa ta ya Zahrah na warkerwa zata kwshe yaranta su bar gidan ne ta gaji.
_Hilal_
Bayan ya bar gidan kai tsaye sabon gidansa ya nufa, zuciyarsa a cunkushe yake, abinda Zahrah ta yi masa ya kunyata yau, tun da yake a rayuwarsa bai taɓa jin kunya irin na yau ba, sannan Papa yana cewa zai yanke hukunci akan wannan al'amari to wane irin hukunci yake shirin yanke wa akan sa oho.
Ummi duk juriya da kawaici yau sai ta kasa hakura, don haka ta koma part ɗin Dada dan ta dubo halin da Autarta take ciki.
Kamar wacce aka tsikara ta nufi kofar fita, Abbi dake cikin damuwa shi ma ya kalle ta ya ce.
"Ina zuwa kuma yanzu?"
"Am zan je na duba ko ta farka ne."
Jinjina mata kai kawai ya yi, ta nufi hanyar fitowa, a babban falon ta ji muryar su Umma da Aunty Laila sai Mummy suna tattaunawa. Aunty Laila na cewa.
"Duk da ban ji dadin abinda Hilal yake aikata wa ba, amma na ji dadin dukan mutuwar da ya yi wa shegiyar yarinyar nan."
Umma ta daura da cewa
"Dama ai sakamakon abinda ya kamata ayi mata kenan."
"Ba ku kai ni tsanar yarinyar nan ba wallahi."
Ran Ummi ya ɓaci da jin yadda suke aibata mata yarinya suna zaginta akan abun da ba laifinta ko da sanin ta ne ta aikata ba. Cikin ɓaci rai ta ce.
"Don Allah me yarinyar nan ta tsare maku a duniyar nan ne, Meye laifinta akan abinda ya faru? Ita kanta ba da saniya ne ta aikata wannan abun na daukar photo ba. Ga ɗanku nan da ya kamata ku mayar da hankali wajen bincikar lamuransa da mu'amalarsa da mutane don ku gane me yake aikata wa ba, shi ne Idanun ku ya rufe ba ku ga laifinsa ba sai na Zahrah ko?"
Murmushin takiaci ta yi tare da cewa.
"Ba yadda za ku yi da mu sai dai cikin..."
Abbi ya kira sunanta da ƙarfi wanda hakan ya saka ta kasa karasa maganar da take da niyyar yi. Duk abinda suke yi ko suke cewa akan ta da yaranta ba ta taɓa cewa komai ba sai yau , yau din ma don ranta a nace yake ne, tana ƙoƙarin ganin ta bi ra'ayin Abbi da ya hana ta tanka masu a kan duka abinda za su ce akan ta da yaranta . Don haka ta yi shiru ta nufi part ɗin Dada yayin da shi kuma ya bi bayanta.
Ko da suka shiga ɗakin Zahrah sun tarar tana barci, an yi mata ƙarin ruwa, Dada na zaune a gefenta cikin damuwa .
Kallonsu ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba, ta san suna hakuri da zaman gidan nan, da ba don Papa ba da tuni sun bar gidan nan, don sau tari Abbi na yunkurin tashi daga gidan Papa na hana shi.
"Kada ku damu ta farfaɗo za ta samu lafiya in sha Allah."
*Washegari*
Yau ne ta kama ranar juma'a, kuma rana irin ta yau jama'ar gidan Alhaji Muhammad Tafarki wajibi ne su ci a abinci a tare, ko Dada da Papa da sukan yi na su a part to ranar juma'a gabadaya suke cin abincin a tare.
Kamar kullum yau ma sun hadu a babban teburin cin abincin dake dinning area. Papa, Dada, Daddy, Mummy, Abba, Umma, Abbi Ummi, da kuma Aunty Laila duk sun haɗu. Haka jikokin gidan ma duk sun haɗu sai sai ban da mutane biyu. Wato Hilal da Zahrah wacce ke kwance taba barci sakamakon rashin lafiyar dukan da Hilal ya yi mata. Faisal, Mansur, Mahmud, Sadik sun hallara. Nabeela, Kausar, Nadiya, Maryam duk suna nan.
Masu aikin na tsaye in da suke zubawa kowa abinda ransa ke so. Papa ya kalli Faisal ya ce.
"Je ka kira mani Babban Yayanku."
Faisal ya tashi ya nufi stairs ɗin, ɗakin Hilal ya shiga, kasancewar kofar ɗakin a buɗe yake . Ganin baya falo ya saka ya nufi bedroom ɗin sa. Lokacin ya fito daga wanka yana sanye da bathrobe a jikinsa.
"Assalamu alaikum warahmatullah"
Muryar Faisal ya ji tana sallama.
Ciki-ciki ya amsa masa sallamar iya ƙasan maƙoshinsa wanda shi wanda ya yi Sallamar bai ji ba.
'
"Barka da safiya Babban Yaya."
Bai amsa masa ba ta fara ƙoƙarin shafa man shafawarsa a jikinsa bayan ta tsane ruwan dake jikinsa da kansa.
Har lokacin fuskarsa a murtuƙe take tamau, don ko barcin kirki bai yi ba, karfe dayan dare ya dawo gidan.
Faisal ya ga ko gaisuwarsa bai amsa ba ya share shi fuska a murtuƙe ya ce.
"Allah ya huci ran maza gu..."
Ɗaga masa hannu ya yi alamar dakatarwa, sannan ya nuna masa kofar fita.
Murmushi Faisal ya yi kafin ya ce
"Zan fita, dama Papa ne ya ce na kira ka."
Yana fada masa haka ya fice.
Shi kuma ya cigaba da ƙoƙarin shafa man shafawarsa da yake yi.
Ko da Faisal ya koma a dinning area ya sanar da Papa cewar yana zuwa .
Jingina kai kawai Papa ya yi yana shan ruwan shayin dake gabansa.
Bayan kamar mintuna goma sannan Hilal ya sauko zuwa downstairs
Ƙamshin turarensa na Armani Georgia hade da Valentino ke tashi a jikinsa, ƙamshi ne ya fara yi masu sallama, wanda ko bai fesa turaren ba ƙamshin na nan a jikinsa.
Ciki-ciki y yi sallama wanda ba wanda ya ji shi, ƙarasowa ya yi kan kujerar dake gabansa ya ja ya zauna suna fuskantar juna da Papa. Sai dai bai kalle Papa ba duk wajen ba wanda ya kalla, bude baki ya yi ya ce
"Morning."
Daga nan bai sake magana ba ya dauki wayarsa ta hau danne-danne.
Ƙannensa suka hau gaishe shi da ina kwana ba wanda ya kalla a cikinsu ballantana a saka ran zai amsa wa ko mutum guda ne.
Wato saboda yana fushi ne ba zai yi wa kowa magana ba, ya masu gaisawar jam'i wai Morning.
Kwafa Papa ya yi don har yanzu shi ma ransa a ɓaci yake da abinda ya faru. Don haka dama ya gama shan shayi kawai ya iya sha
Har Papa zai bar dinning area ɗin ya juyo ya kalle su ya ce.
"Wannan sallar juma'a da za'ayi yau ɗin nan ba na bukatar a ce kowa ya tafi da motarsa yadda kuke yi ku shirya akan lokaci kuma ba wai daga wajan aiki ko kasuwa za ku tafi ba, ku tabbatar kafin lokacin sallar ta yi kun dawo gidan an tafi tare, ba na bukatar wani ya kawo Mani wani uzuri."
Yana gama fadar haka ya juya ya cigaba da tafiya zuwa part ɗin sa.
*Maman Ihsan ce*
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page6️⃣0️⃣
Yana gama fadar haka ya cigaba da tafiya zuwa part ɗin sa.
*LAGOS*
Wata bakar mota ce ta yi bakin daidai ƙofar wani madaidaicin gida. Fitowa mamallakin motar ya yi sanye da rigar mai hula sai bakin Glass da ya sanya wa fuskarsa hular ta rufe kusan rabin fuskarsa.
Kasancewar safiya ne ba yawan jama'a dake kai kawo a unguwar. Wayarsa ƙarama ya fito da shi daga aljihun wandonsa. Wata lamba ya dannawa kira, bayan an daga kiran wayar ne ya ce.
"Ki fito da sauri ina son zan bar garin nan yau ne?"
Yana fadar haka ya katse kiran wayar.
Bayan kamar mintuna uku sai ga wata budurwa ta fiti daga cikin gidan. Sanye da riga da siket na atamfa, sai mayafin da ta yafa a kanta madadin Ɗankwali.
Yamutse fuska take yi Aalamar daga barci ta tashi .
"Assalamu alaikum."
Ta yi masa sallama ya amsa da.
"Wa'alaiki Salam "
"Sagir wai wannan sammakon na tafiyar ne?"
"Eh ina sauri ne."
"Wai me ya saka kullum cikin sauri kake ne, sai ka dinga yin abu. Kamar mara gaskiya wani lokacin."
Kallonta ya yi kafin ya ce.
"Sadiya na yi maki kama da mai laifi ne?"
"A'a ba haka nake nufi ba, na ga dai kullum idan ka zo ƙasar nan sai ka yi ta ɗari-dari, ba ka sakin jiki sosai, da zaran ka zo ba ka dadewa kake barin Wajen nan, sai ka yi ta kalle-kalle kamar bai neman wani abu, gabaɗaya ba ka da sukuni ne. Ko ja zo ba ka dadewa."
"Eh saboda yanayin aiki na ne ba na da lokutan kaina, amma fa zaran mun yi aure na dauke ki mun bar ƙasar nan, za ki samu isasshen lokacina yadda kike so."
Kuɗaɗe masu yawa ya miƙa mata sannan ya yi mata sallama ya shiga motarsa ya bar unguwar.
Jinjina kai Safiya ta yi ta dubu yawan kuɗin da ya bata sannan ta ce.
"Sagir kenan."
Komawa ta yi cikin madaidaicin gidan na su, gidan ne mai ɗauke da ɗakuna guda uku. Ɗaya na Mamanta sai ɗaya na mahaifinta sai ɗayan kuma na ta. Watanni biyar kenan da rasuwarsa.
Ɗakin mamanta ta shiga da sallama a bakinta, Mama na barci ta ci Sallamar Sadiya. Ta amsa tana tashi zaune, ganin ta ajiye kudi a gefen filon ne ya saka Maman tashi zaune ta ce.
"Ke Sadiya wai Sagir ne ya baki kudi masu yawa haka ?"
"Eh Mama."
"Wai yaron nan ɗan albarka ne akwai son kyauta."
"Uhm."
Sadiya ta ce tare da tashi ta barwa Mamanta kuɗaɗen.
_Hilal_
Saukowa yake yi daga upstairs ɗin sakamakon kiran wayar da Papa ya dame shi da ita.
Sanye yake cikin ɗanyar shadda fara, ya sanya bakin hula da bakin takalmi. Sai kamshi ke tashi daga jikinsa.
Ya rasa dalilin da ya saka Papa cewa yau sai dai gabaɗaya familyn Tafarki su haɗu zuwa babban Masallacin juma'a na garin. Bayan ba tare suke zuwa ba, wasu ba nan masallacin sune sallah ba. Dan Yaa Mahmud masallacin da ke kusa da bakinsu su yaje zuwa. Haka Faisal Masallacin juma'a dake kusa da kasuwa yake zuwa kasancewar sa dan kasuwa. Amma yai Papa ya tsiro cewa yau da ƴaƴansa da jikokin sa tare za su tafi sallar juma'a.
Ko da ya sauko Downstairs ɗin nan ya tarar da kowa da kowa. Sun hallara da alama saukowarsa ake jira.
Yana saukowa Papa ya yi gaba kowa ya bi bayansa suka nufi parking space.
Papa ya kalli Sadik wanda shi ne karami a cikin jikokin ya ce.
"Ku tafi a motarka dukakkan ku."
Mansur ya bude baki zai yi magana sai ya faɗa sakamakon kallon da ya ga Papa ya jefa masa.
Ba wanda ya iya magana don fuskar kakan na su kamar zai yi aman wuta haka yake.
Sadik ya shiga mazaunin direba yayin da Mahmud ya zauna gefensa. Hilal dake jin kansa wani iri ya bude bayan motar ya shiga don baya da wani zaɓi. Ganin ya shiga ya saka Faisal ya shiga Mansur ma ya shiga.
Papa ya zauna gefen direbasa wato wajen me zaman banza, ya ce wa su Daddy duk su shiga baya.
Daddy ya shiga sai Abba sannan Abbi ya shiga bayan suka zama su uku a baya.
Daga haka motocin suka bar gidan.
_Zahrah_
Koda ta fara da safe jikinta duk ya yi mata tsami sosai.don ko ina ciwo yake yi mata a jikin na ta, ga wani zazzaɓi da take jin ya rufe ta.
Daƙyar ta iya buɗe idanunta da suka yi mata nauyi sosai. Da taimakon Dada ta tashi zaune, har bathroom ta raka ta,sannan ta tabbatar ta haɗa masa ruwan zafi ta yi wanka da shi ta gasa jikinta da ya yi mata tsami sosai.
Tana wanka tana kuka tana tuna irin dukan da Hilal ya yi mata wanda ita har yanzu ba ta san laifin da ta yi masa ba da ya yi mata irin wannan dukar har ta fita hayyacinta.
Bayan ta gana wanka ta ɗauro alwala, haka ta tako a hankali tana jin ƙirjinta na bugawa da karfi. Fargaba ne ya shige ta wanda ba ta san dalilin da ya saka take jin faɗuwar gaba ba.
Doguwar riga ta janyo daga cikin Kayanta ta zira a jikinta bayan ta fesa turaren jiki a sassan jikinta, duk da ba ta da lafiya amma ba ta iya zama ba ƙamshi a jikinta.
Hijabi ta saka sannan ta shimfida sallaya, salloli da ake binta ta rama. Sannan ta yi sallar asuba.
Tana kishingide taba azkar Dada ta shigo da kofin shayi da soyayyen ƙwai dai bread ta jera su a faranti.
Duk yadda ta so Zahrah ta ci ƙwai da bread ƙi ta yi sai dai ta ɗan sha ruwan tea shi ma kadan ta sha.
Sai magungunan da Doctor ya bayar Dada ta ba ta , bayan t karba ta sha ne ta sake kwanciya. Yayin da gabanta ta tsananta faduwa, sai ta dinga karanta innalillahi wa'inna'ilahi raji'un a zuciyarta.
Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita .
Bayan sun yi parking a in da aka tanada don ajiye motoci dukkansu suka fito daga cikin motocin. Sai dai abu ɗaya da ya ɗaure wa su Daddy kai su ne. Ganin surukansu sun ƙaraso wajen wanda ba su taba ganin su a wannan masallacin ba.
Wato kakan Hilal mahaifin Mummy kenan, da kuma Kakan su Mansura mahaifin Umma da kuma Modibbo mahaifin Ummi da kuma wasu daga cikin dangin mahaifiyarsu. Sai kuma mahaifin su Kausar da Nabeela.
Bayan an gaggaisa suka shiga cikin masallaci don ba damar su yi wata tamabya, suka bar Papa yana gaisawa da su Modibbo suka shiga cikin masallaci.
Bayan an idar da sallar juma'a an yi addu'a aka sanar da ɗaurin aure da za'ayi a masallacin.
Daga bayan motar ɗin motar Papa aka dinga fito wa da goro dabino da ai drinks da ruwa daga motar Sadik wanda ba wanda ya san da su .
Kamar daga sama aka ji sanar da ɗaurin auren. *Hilal Abubakar Tafarki tare da Fatima Zahrah Salis Tafarki.* Hilal ya ɗago kai a firgice yana kallon wajen da su Papa suke, suna farin ciki har da kakansa mahaifin Mummy da wasu dangin mahaifiyarsa. Wani abu ya ji ya tokare masa ƙirji mai nauyi ya sunkuyar da kai yana kallon darduman dake shimfide a masallacin. Sai kuma aka ji sanarwar ɗaurin auren *Mahmud Adam Tafarki tare da Nabeela Nasir Isah* daga nan kuma *Mansur Adam Tafarki tare da Maryam Abubakar Tafarki* sai kuka *Sadik Salis Tafarki tare da Nadeeya Adam Tafarki*
*Sai kuma Faisal Abubakar Tafarki tare da Kausar Nasir Isah* dukkansu akan sadaki Naira dubi ɗari biyu.
Gabaɗaya angwayen da suka ji wannan sanarwar ɗaurin auren na su tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskarsu. Duk wanda ya kalle su zai shaida hakan, ya san hankulansu a tashe yake .
Hilal ne kawai idan ka kalla ba za ka iya gano rashin hankali a tattare da shi ba, domin yana da wuya ka gane halin da yake ciki ko ka iya karantar abun da ke ransa, da yake yana da jarumtar da zai iya shanye ko wane irin tashin hankali ba tare da kowa ya san halin da yake ciki ba, don haka, ko da Papa ya kallo in da jikokin na sa suke duk
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 39