ƴar uwar ta ta idanu.
Harara ta watsa mata tana cewa
"Idan za ki cire idanunku akan my Hilal ki cire, don na wa ne shi. Ai Yaa Ammar ɗin ma fa ya haɗu duk da bai kai Yasa Hilal ba amma shi ma mijin nunawa sa'a ne."
Nan suka fara sa'insa Maryam dai kallinsu take tana murmushi yayin da Nadeeya ta ce
"Iska na wahalar da mai kayan kara, ku dinga faɗa akan Yaa Hilal wanda ko kallon banza ba ku ishe shi ba. Da ni ma na ɗaurawa kaina son sa amma tun da na ga alamar ba zan samu soyayyarsa ba na cirewa kaina dakon wahala."
Maryam suka kalla kasancewar ita ce suka fito ciki ɗaya da Hilal ya sa Nabeela cewa
"Maryam ba ki taba jin ya ce ga wacce yake so ba?"
Taɓe baki Maryam ta yi tare da cewa.
"Wake sanin halin da yake ciki, ko Mummy jiya da ya shigo na ji tana masa fadar cewa yana nuna halin ko in kula da kowa har da ita ba ta sanin halin da yake ciki ta ce dole ya fitar mata a cikin ƴan matan da suke sonsa har da ku ta ambata amma budar bakinsa ya ce shi bai ga maccen da ta masa ba da zai sure ta ba."
Nadeeya ta kece da dariya tana cewa
" ku na jin..."
Ƙasa karasawa ta yi sakamakon ƙamshin turarensa da suka ji, alamar yana kusa da su kenan. Nan kowacce ta yi shiru suka dakar da firan ballantana dariya, kamar ruwa ya ci su haka suka yi tsit.
Jin takunsa kamar yana nufo un da suke ne ya saka kowacd ta juyo ta kalle shi. Ƙananan kaya ne a jikina ya zuba hannayensa a cikin aljihun wandonsa. Fuskar nan tamau ba fara'a kamar kullun.
Kowacce ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi. Don sun san halinsa idan ya samu suna hayaniya ba karamin aikinsa ba ne ya zare belt ɗin wandonsa sai kowacce ta ji jiki.
"Kausar ce ya sake kallonsa hararar da ya wurga mata ne ya saka ta sunkuyar da kai da sauri.
"Gyara mun ɗaki."
Abinda ya ce kenan ya nufi ƙofar fita cikin takunsa na mazantaka.
Gabaɗaya suka amsa da to tare da masa a dawo laflya. Bai tanka masu ba ya fice .
Sai da suka tabbatar ya yi nisa sannan Maryam da Nadeeya suka ƙyalkyace da dariya. Maryam ta ce.
"Yanzu kuka gama ciki baki akan son da kuke masa, amma yana fitowa kuka yi kamar ruwa ya ci ku a haka za'ayi soyayyar?"
Nadeeya ta amshime da cewa.
Ni ma haka na gani da sai wata ta tashi ta karasa wajensa tana tamabayarsa fita za ka yi ko na zo na raka ka ne?"
Kausar ta dafe ƙarji tana cewa
"Wace ni, ai sai ya ci ubana la'ada waje."
Nabeela ta ce.
"Na taɓa gwada wa sau ɗaya na tare shi da niyyar ya rage mani hanya zai fita, ai kafin na yi magana kallon da na ga ya mani sai na daburce na rasa ta cewa."
Dariya suka yi Maryan ta ce.
"Ya Hilal kenan shi ake kira kamar maza tana ga mazuru ko ba faɗa akwai mugun kallo."
Dariya suka yi kafin suka su huɗun suka nufi ɗakinsa don gyara masa.
Zahrah da ta shiga Part ɗin Kakanninta ta tarar da Papa yana tsaye a falo yana cewa Dada ta fito su tafi.
Da sallama a bakinta ta shiga Papa ya amsa yana kiran sunanta tare da tambayarta ya karfin jiki. Ta amsa a Alhamdulillah.
Tana shiga ɗakin Dada ta same ta tana yafa mayafinta.
"Dada fita za ku yi ba ki ce na shirya mu tafi tare ba?"
"To tun da kin zo ai sai ki juya mu tafi ."
Ɗakinta ta shiga ta ɗauko facemask ɗin ta ta saka, a tare suka bar part ɗin.
Papa na gaba Dada da Zahrah na baya.
Wata mota ta ga sun nufa wacce ba ta san motar a gidan ba, ba ta yi magana ba tana jiran su ƙarasa.
Papa ne ya buɗe gidan gaba ya zauna gefen mai zaman banza.
Dada ta bude bayan motar ta shiga, Zahrah ma ta shiga ciki. Ƙamshin da ta ji ne ya haifar mata da faɗuwar gaba, da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi, suka hada idanu ta cikin madubin dake cikin motar. Gabanta ya tsananta faduwa don ba ta san shi da motar ba, kuma Allah bai bata ikon tambaya ba.
"Ita kuma wannan fa ina za ta je ko akwai sa'anta anan ne da za ta bi mu?"
Papa ya ce.
"Ba ta san in da za mu je ba ka san ta saba fita da kakar ta ku shi ne ta biyo ta."
Harara ya watsa mata tare de cewa.
"Get out!"
Ya faɗa a tsawace. Yunƙurawa ta yi za ta fita Dada ta rike ta tana cewa.
"Wallahi ba za ta fita ba akan me ba na son takura ehe."
Zai yi magana Papa ya ce .
"Ka ja mota mu tafi ka san gaba za mu je daga nan."
Kasancewar baya yi wa Papa musu akan komai ya saka ya yi shiru . Zahra kam shirin fita take yi Dada ta ce ki zauna ba inda za ki je."
Ita kanta ba ta so ba don da ta san ba direba zai kai su ba ko da wasa ba za ta biyu Papa ba
Kunkuni take yi kuma ya ganta ganin facemask din da ta sa yana motsawa.
Kwafa kawai ya yi tare da yiwa motar key yana cewa.
"Idan kika shiga hannuna sai kin faɗa mani abin da kike cewa."
Ba abinda ta ce ba na son sharri."
Dada ta faɗa cikin fada.
Tafiyar mintuna talatin suka yi kasancewar a a hankali yake tuki.
Wani tangamemen gate ya tsaya remote ya danna dai gate ɗin ya wangale kansa, ya danna hancin motar a ciki.
"Ma sha Allah."
Shi ne abinda Dada da Papa suke faɗa, Zahra ma haka ta ce a zuciysryarta. Don babban gida ne mai girma wanda ya ƙawatu da abubuwan more rayuwa.
Dada ta ce
"Gida ya kammala saura a ajiye iyali, ba a abinda ya rage maka yanzu tun da ka kammala burina na ga auren wannan tuzurun."
"Haba Dada ni ne tuzuru?"
Kafin su shiga zagayawa suka fara yi har suka iso wani garden, wajen gwanin sha'awa ha waken hutawa nan ga kayan marmari nan daga gefe can kuma ga swimming pool, gafe ga wani gado na kwanciya yana ɗan kaɗawa.
Ciki da suka shiga a babban falon wanda ya gaji da haɗuwa.
Cikin tsautsayi Rigar abayar Zahra ya ɗan harɗe mata ƙafa lokacin da za ta bi su upstair, kifawa ta kusa yi wanda cikin ikon Allah ba ta faɗi ba sai dai ta ture wani glass da fulawa masu kyau ne ciki, wanda hakan ya saka suka tarwatse, ƙarar ya janyo hankalin su suka kalli abinda ya fashe wanda aka ajiye shi a gefen benen.
Kallon Hilal ta yi ta ga ya zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta , yana aika mata da wani kallo. Gabanta ne ya fadi ta fara ja baya za ta shiga cikin fasassun glass ɗin
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️ Kayan Matta Pure and Natural with Zero Side Effect
*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*
*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*
Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.
Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.
Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩
1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more
Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.
*YAR GIDAN TAFIDA*
Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.
*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.
Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯
Page4️⃣4️⃣
Kallon Hilal ta yi ta ga zuba mata rikitattun idanunsa masu firgita ta, yana aika mata wani kallo. Gabanta ya faɗi ta fara ja baya za ta shiga cikin fasassun glass glass ɗin.
Ba abinda take tunawa sai ranar da ta shiga ɗakinsa Dada ta aike ta sai ta ga wani frame an zana butterfly cikin tsautsayi ta taɓa wanda hakan ya saka frame ɗin ya faɗo. Da ya ga ɓarnar da ta yi har ya saka ta punishment wanda tsabar azaba dai da ciwon athma ɗin ta ya tashi ta sume don wahala. Ga shi yanzu ta sake masa wata ɓarnar wacce tafi waccen ta san halinsa dole sai ta yabawa a aya zaƙinta.
Hawaye ke bin fuskarta tana sake ja da baya. Dada da Papa na cewa ta dakata kada ta ji wa kanta ciwo za ta taka kwalba. Amma ina ba ta ma san me suke cewa ba tsoron Hilal ne fal a zuciyarta wanda ta san ba raga mata zai yi ba. Ta masa ɓarnar da ba ta kai wannan ba ya sumar da ita wanda har ta kasa tafiyar da ƙafarta ballantana wannan .
Zame facemask dake fuskarta ta yi za ta bashi hakuri ganin yana matsowa in da take
Ɗaga ƙafar da zata wanda idan ta aje ƙafar za ta ɗora shi ne akan wani tsinin kwalba da ke tsaye a sama, cikin zafin nama ya janyo ta da ƙarfi ta faɗo jikinsa. Bakinta ya mannu da ƙirjinsa. Tsabar firgita ba ta san ta ƙanƙame shi da hannayenta duka biyu ba. Idanunta a rintse suke gabanta na faɗuwa jiran hukuncin da zai ɗauka akanta kawai take jira.
Kalaman da ta ji a ƙunnenta ne suka firgita ta ta zare idanu tare da sakinsa ba shiri .
"Ban yi mamaki ba tunda kin saba bin maza kina haɗa jiki da su, to ni ba ƴan iskan samarinki ba ne da kika saba haɗa jiki da su kuna iskanci, kuma sai kin faɗa mani uban da ya maki ciki kika zubar a kwanakin baya."
Ca baya kawai take yi tana kallonsa hawaye na wanke mata fuska tana girgiza masa kai.
Kasancewa tana jikinsa ya yi maganar kuma a hankali ya yi hakan ya saka Dada da Papa ba su ji mugayen kalaman Hilal ɗin ba .
"Zaharah lafiya kuma?"
Dada ta tamabya ganin yadda take girgiza kai tana kuka. A tunanin su Papa sun ɗauka rumgumar Hilal da ta yi ya saka take ja baya tana tsoronsa kamar yadda yaran gidan sun tabbatar kowa na tsoronsa.
"Ki kwantar da hankali Fatima Zahrah ai tsorata kika yi ba komai ba ne."
Cewar Papa lokacin da ya karasa ya riko hannunta. Cikin kuka ta ce.
"Papa wallahi ni ba ƴar iska ba ce ban taɓa aikata fasiƙanci ba."
"Kada ku damu mun sani ku kwantar da hankalinki."
"Zo mu shiga ciki mu ga ni ko?"
Girgiza kai ta yi alamar ba za ta shiga ciki ba, rarrashinta suke yi ta yi shiru ta ce.
"Zan jira ku a nan."
Ganin ta kafe Papa ya ce .
"Ba za ki shiga ki ga gidan Yayanki ba?"
Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo ganin yadda Kakannin na su suka damu don haka ta ce .
"Zan biyo ku yanzu bari na kwashe fasassun glass ɗin nan."
Tana dube dube-dube idanunta suka sauka akan abun shafa har da kwandon zubawa ta hanga a wani corridor da za ta sada ta da wata hanya wanda ba ta san hanyar ina ba ne.
"Papa mu je?"
Ya faɗa yana masu jagora zuwa sama yayin da Dada ke ta mitar cewa ƙafarta na mata ciwo ya kawo ta in da za zata wahala.
Zara kuka take yi tana share wajen zuciyarta na mata zafin Kalaman da Hilal ya faɗa mata.
Tambyar kanta take yi shin me ta yi wa Ahalinta ne da zafi haka, gabaɗaya kowa na mata kallon ƴar iska watsatstsiya Kakanninta ne kawai ta san cewa ba sa mata wannan kallon sai iyayenta da yayunta.
Da farko Aunty Laila wacce ta kasance ƙanwar Mahaifinta uwa ɗaya uba ɗaya ce ta fara jifarta da kalmar ƴar iska. Sai Mummy mahaifiyar Hilal da ita ma ta bi bayan Aunty Laila suke kiranta da karuwa. Haka ma Umma , Hawaye Masu zafi suka zubo mata.
Sai da ta share wajen tass ta kwashe fasassun glass ɗin da kwalaben ta samu wuri ta rakuɓe ta kasa haurawa saman.
Takunsa ta ji yana saukowa kafin ta ankare har ta gan shi a gabanta.
"Ba ke kin iya barna kamar ɓera ba, to wannan karon ba ƙyale ki zan yi ba, albarkacin idanun du Papa kika ci ya saka ban maki komai ba, amma ina mai tabbatar maki sai kin biya ɓarnar da kika yi."
Murya na rawa ta ce.
"Nawa ne zan biya?"
"Au har kina da kudin biya ne? Oh na manta ko wace ce ke kin sani kuɗaɗe wajen gasar karatun Alkur'ani ko? Sannan ga na samari da ake baki. To sai dai wannan ba da kudi za ki biya ba."
Da sauri ta kalle shi ta ce.
"Da me zan biya?".
Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba kafin ya ce.
"Ba kuma da jikinki za ki biya ba, domin kamar yadda kika..."
Kuka me sauti ta sake wanda ya saka ya dakata da zancen da yake yi
"Kukan uban me kike yi ƙarya aka yi maki ne, ina a gabana Aunty Laila ta ce ciki kaka zubar na dauke ki na kai ki asibiti Doctor ya sake tabbatarwa ƙwayoyin zubar da ciki kika sha ciki ya zube. Dan an yi magana ki dinga yi wa mutane kuka ƴar iska mai fuska biyu ana ana maki kallon nitsatstsiya mai kamun kai saboda ilimin addini da kike da shi alhakin bakya aiki fa duk Musa a baki ne Fir'auna a zuci."
Sautin kukan ta ne ya ƙaru wanda ya saka har ta ji numfashinta baya fita daidai.
"Uban me na maki kike kuka? Na dake ki ne, yanzu zan maki dukan tsiya a wajen nan kiyi kuka mai dalili."
Ya yi maganar yana ɗora hannunsa akan belt ɗin wandonsa. Ganin haka ya saka ta kalli fuskarsa da sauri. Fuskarsa ɗaure tamau Babu sassauci ko kaɗan.
Hannunsa ya dora a saman lips ɗin sa alamar ta yi shiru.
Haɗiye kukan ta yi sai ajiyar zuciya take saukewa, ga numfashinta ya fara fita sama-sama alamar ciwonta zai iya tashi.
Suna cikin wannan halin ne sai su Papa suka fito suna ta yaba kyawun gidan tare da masa fatan alkahiri da samun mace tagari.
_Jidderh_
Ko da ta fito daga bathroom ɗaure da towel kamar yadda ya nuna mata.
Ya shigo ya ajiye mata wasu kayan. Ya ganta tsaye .
"Akwai matsala."
Ya faɗa yana ƙarasowa wajen.
"To idan mutum ma ya yi ya rasa tunaninsa sai ya rasa komai a ƙwaƙwalwa? Har wanka da shirya kanta ma ba za ta san yadda za ta yi ba.?"
Ya ƙarasa maganar tamkar wanda zai yi kuka.ledar ya duba ya ga har da pant. Ɗaukar daya ya yi ya nuna mata yadda za ta yi sannan ya ɗauki doguwar rigar ya karasa in da take ɗure da towel, sai da Allah ya sa towel ɗin mai girma ne ya sauka mata. Bayan ya zira mata rigar ne ya nuna mata yadda za ta sake pant ya fice yana jinjina lamarin a zuciyarsa cikin damuwa.
Yana fita ya tarar da Dr Isma'il ya karaso. Nan suka gaida ya tamabaye shi jiki ya amsa da Alhamdulillah.
Bayanin lamarin Jidderh ya bashi da yadda take . Shiru Dr Isma'il ya yi kafin ya ce.
"Maganar gaskiya dole sai an kai ta asibiti."
Jinjina kai Asad ya yi tare da cewa.
"Sulaiman sai dai ku tafi tare da ita."
"Okay Sir "
Sulaiman ya faɗa yana miƙewa.
Asad ya koma dakin ta bar su nan tsaye.ba jimawa suka fito tana sanye da Hijabi ya masu jagora suka fita.
Sai da ya ga wucewarsu sannan ya dawo ciki zuciyarsa fal tausayin yarinyar.
_Maryam_
Suna shiga dakin Hilal kamar yadda ya basu umarnin su je su gyara masa part ɗin sa.
Suna shiga falon nasa wani daddaɗen ƙamshi ya ziyarci hancin na su. Nabeela ta ce.
"Yanzu wata rana fa nan ne falona ni da Yaa Hilal har na hango ni ina zuba masa shagwaɓa yana ta lallaɓani muna zaune s wancan kujerar."
Ta yi maganar tana nuna kujerar mai zaman mutum uku dake falon. Gabadaya suka saka mata dariya wanda hakan ya saka Nabeela ƙuluwa da haushi.
"Kin san Allah idan ma kina mafarkin cewa ko kin auri Yaya Hilal za ki masa shagwaɓa ta ɗauka kin yi kuskure. Domin shi bai san rarrashi ba ballantana lallaɓa mutum Abu guda ya sani shi ne hukunci a duk lokacin da kika masa ba daidai ba."
Maryam ta yi maganar tana dariya.
Kausar ta taɓe baki tana cewa.
"Ni zan yi daidai da shi don na iya zama da shi kuma zan koya na jure."
Nadeeya dai zama ta yi tana cewa
"Kanku ake ji ƴan wahala kawai."
Hotonsa dake manne a bango ne Kausar ta kalla.
Sanye take da kakinsa ya yi kyau sosai.
Shafa hoton ta yi tana murmushi.
Madadin su yi aikin da ya saka su sai suka zauna suka ɓige da yin fira.
Kusan mintuna talatin suna a haka suna fira kafin Maryam ta ce.
"Mu tashi fa kada ya zo ya same mu ba mu yi masa aikin da ya saka mu ba."
Nan suka tashi in da suka yanke shawarar mutane biyu su shiga su gyara bedroom su wanke toilet, sai mutane biyu su zauna su gyara falo.
Da wannan shawarar suka yi amfani. Nabeela da Nadiya suka shiga don gyara masa bedroom. Maryam da Kausar suka tsaya gyara masa Falo.
Nan ma suna shiga bedroom ɗin Nabeela ta zube a gadon tana shaƙar daddaɗen ƙamshisa.
Nadiya ta ta shiga don wanke toilet. Tana shiga ta ga toilet ɗin tsaf .
"Ni ban ga abinda za'a wanke a anan ba komai tas yake."
Nabeela ta taso ta gani ta ji kamshi ne ma a ciki. Don haka ta ce.
"Watsa ruwa kawai ki fito."
Haka kuwa aka yi tana watsa ruwa ta fito.
Suka dawo suna dube-dube a wajen madubi.
"Kalli duk waɗan nan maiyuka da turaruka duk na mutum ɗaya ne, sai ka ce mace, duk nan fa mayukan jiki ne da ba gashi, sai turaren jiki da na jiki. Komai na sa disigner ne.
Nadiya ta faɗa tana dudduba su yayin da Nabeela ma ke dubawa tana cewa.
"Bari na fesa turaren masoyi."
"Kada ki fesa kin san dai tutarensa ba gamagarin turere yake amfani da shi ba, sai an gane ki idan kika fita ko shi idan ya shigo zai gane ne kin san halinsa ."
Jin haka ya saka ta ajiye tana cewa su gyara gadon.
Duk da ba yamutsewa ya yi ba zanin gadon ma a gyare yake. Sai suka yaye bargon da zanin gadon suka hau kici-kicin gyarawa.
Amma sai suka kasa shimfida zanin gadon da kyau, sun yi iya iyawarsu don ganin sun gyara gadon sun kasa.
Sai haki suke yi duk sun gaji amma sun kasa shimfida zanin gado.
Cikin ƙosawa Nabeela ta ce.
"Wallahi Nadiya na gaji, ke ma kin san ba iya gyara ɗaki muka yi ba saboda masu aiki ke gyara muna ɗaki ta ya ya za mu iya wannan aikin tun da ba mu taba yi ba."
"Gaskiya ne to yanzu ya za mu yi yanzu?"
"Mu kira su Kasar ko za su iya gyaran."
Fita suka yi nan suka same su a falo suna kuciniya su su ma ba iya aikin suka iya yi ba.
Maryam ta jika towel da ruwa ta zuba omo sai kuma yake yi haka take ta laptawa Tv da duk wani abu dake wajen. Da suka abinda ya shafi glass dake wajen.
Kausar kuwa ita ma ta sai mofin take tana goge tiles ɗin sai kumfa yake yi sosai ta zuba detergent.
Suna cikin wannan halin suka zo suka same su, nan suka ce sun gama na su suka ɗunguma bedroom ɗin .
Nan ma suka hadu su hudu suna kokarin gyara wajen amma sun kasa.
Haka suka lulluɓa zanin gadon suka ɗora bargo akai.
Irin mopping stick 🏒 suka ɗauko nan ma suka jiƙa masa ɗakin suka fice.
Maryam ce ta ce
"Kun san ba iya aiki muka yi ba tunda masu aiki ke gyara mana ɗaki ba za mu kira su nan su shigo su gyara masa ba?"
"Ke ma kin san baya yarda mai aiki ta shigo masa part ɗin sa. Ko girkinsu kina ganin bai cika ci ba sai dai ya sha tea. Ko kuma ya tafi part ɗin Dada saboda ba ƴar aiki ke mata girki ba."
"Wai ba Yaa Faisal ke gyara masa ɗaki ba, me ya saka yau bai yi masa ba?"
"Yau da wuri ya fita kasuwa ."
Maryam ta faɗa suka janyo masa kofar suka sauko Downstairs. Ba kowa don haka Kausar da Maryam suka nufi part ɗin su. Yayin da kuma Maryam da Nadiya kowace ta nufi part ɗin mahaifiyarta.
_Sulaiman_
Yana nan zaune a asibitin yayin da Likitoci ke kan Jidderh don gano matsalar dake damunta.
Yana nan zaune sai ga wayar Mom ya shigo cikin wayarsa. Ɗauka ya yi bayan sun gaisa daga can ɓangaren Mom ta ce.
"Sulaiman ina ka shiga ne daga maganar CCTV Camera aka neme ka aka rasa?"
"Mom na ɗan fit ne yanzu zan dawo."
Kashe wayar ya yi yana fita da sauri don sanar da uban gidansa.
Motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar wajen .
A falo ya samu Asad wanda ganin shigowarsa ya ce.
"Ya aka yi ne ina take?"
"Ban sanar da kai ba ne wallahi Mom ta kira ni akan bincike da za mu yi na gobarar da ya tashi to zan bincik..."
"Kada ka yi wannan bincike ka ɓatar da komai da y faru."
Kallonsa Sulaiman yake cikin mamakinsa. Jinjina masa kai Asad ya yi alamar tabbatar wa.
Jinjina kai ya yi cikin girmamawa ya fice daha gidan.
_Zahrah_
Tana nan tsaye a wajen da take sai haɗiyar kuka take yi , yayin da Hilal ke aika mata wani kallo. Har lokacin numfashinta baya fita daidai.
Fita suka yi gabaɗaya don Zahra ta ce ba za ta shiga ba.
A motar ne Dada ke cewa Zahrah za su biya gidan abokin Papa ɗansu ya rasu. Ko za ki je mu mu tafi tare?"
Girgiza kai ta yi alamar a'a don tana don tana ji. Yadda numfashinta ke fita ba ta don Dada ta sani.
Sai da Hilal ya fara ajiye Papa da Dada gidan rasuwa Sannan suka fita.
Zabarah na bayan motar y dskata bai tayar da motar ba ya yi shiru.
"Waye Direban ki da za ki zauna Mani a bayan mota?"
Fitowa ta yi ta zo ta shiga gaban motar wajen me zaman banza. Gajeren tsuki ya ja sannan ya ja motar suka bar wajen.
Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana sai sanyin AC da ƙamshin dake tashi a motar.
Bayan sun isa gidan ne ta fito da sauri don neman magani.
Tana zauna kofar falo ta tura kofar tare da sallama. Mummy ce da Umma sai Aunty Laila.
Ba su amsa ba kuma ba ta saka ran za su amsa ba . Sai da ta zo daidai in da suke har ta gifta Aunty Laila ta daka mata tsawa.
"Ke!"
Tsayawa ta yi ta juyo tafe da zuwa in da suke.
Wani kallo Ne Mummy ta yi mata tana cewa.
"Ya na ji ƙamshin turaren Hilal a jikinki?"
Gabanta ya fadi tuna lokacin da ta tuna tsorata da ta yi ta rungume shi .
"Ba komai."
Ta fada da daƙyar.
"Iskancin da kike yi da maza a waje yau ya zo kan Ɗana?"
Umma ce ta ce.
"Wannan mkirar yarinyar ba za ta fada ba, ya aka yi turaren rigarsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 39