Share this page
ta miƙa hannu ta ciro glass din photon Tana shafar photon tana murmushi cike da shauki. Tsawon mintuna goma ta dauka a haka, kafin ta kai hannu da niyyar mayar da photon bisa tsautsayi dai ya faɗo ya tarwatse. Hilal dake cikin closet yana shiryawa ya ji wannan karar, da sauri ya fito in da ya yi tozali da ɓarnar da ta yi masa. Ganin ɓacin ran dake kan fuskarsa ya wanda babu sassauci a tattare da shi ne ya saka jikinta ya fara rawa. Nufo ta ya yi wanda ganin haka ya sa ta fara neman hanyar tsira don ta san mai ƙwatarta a wajensa sai dai Allah. Tsalle ta yi ta diro daga kan kujerar a guje ta nufi hanyar fita za ta fice. Cikin zafin nama ya zare takalmin dake ƙafarsa ya jefi ƙafarta ta dama daidai saitin guiwarta, kasancewar ta baya ya jefe ta hakan ya sa ƙafarta ta lanƙwashe ta faɗi a wajen. Ƙara ta saki saboda ta ji zafi kuma ga buhuwar da ta yi. Tsawon mintuna biyar tana kwance a ƙasan kafin ta yunƙura idanunta na zubar da ba hawaye ta juyo ta kalle shi ta ga ya wurga mata harara tare da yi mata alama da hannu na ta zo. Tana ɗingisa ƙafa ta karasa gabansa, tsawon mintuna uku bai yi magana ba kafin ya fara magana cikin fusata. "Kin yi mun ɓarna za ki gudu uban waye zai kwashe tarkacen da kika tarwatsa!?" Waige-waige ta fara yi can hanyar bathroom a cikin wani corridor ta hangi kwandon zuba shara da da abin kwashewa. Ɗauka ta yi ta zo ta tattara Wajen ta share tas. Sai da ta gama ta mayar ta ajiye, kallonsa ta yi ta ga ya zuba mata rikitattun idanunsa ba tare da ya yi magana ba. "Na rasa wani rin hukunci zan maki ma, ke ba abar a daka ba, idan na ce zan dake ki sai kin kusa mutuwa a hannunsa." Ƙofar fita ya nufa kafin ya fice ya juyo ya kalle ta ya ce. "Ki fada tsallen kwaɗo ba tare da kin tsaya ba, idan kuma kika tsaya na lahira sai ya fi ki jin daɗi. Kuma ki sani duk abinda za ki yi a cikin ɗakin nan akan idanuna kike yinsa, don ina kallonki." Yana gama fadar haka ya fice yayin da ta fara tsallen kwaɗo tana kuka. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣4️⃣ Yana gama fadar haka ya fice yayin da ta fara tsallen kwaɗo tana kuka. Ummin Zahrah kuwa tana ganin karfe goma ta yi Zahrah ba t dawo ba ta yi tunanin kila a ɗakin Dada za ta kwana. Don dama wani lokacin tana kwana a wajen kakarta. Sai da asuba take dawowa part ɗin su. Don haka Ummi na leka ɗakin Zahrah ta ga ba ta nan ta san tana wajen Dada don ba ta fita. Yayin da ita kuma Dada ganin Zahrah ta jima ba ta dawo ba ne ya sa ya yi tunanin bayan ta sanar wa Hilal ɗin saƙonta ta koma wajen Umminta ne. Don dama daga kaka har Papa cikin jikokin su sun fi son Hilal da Zahrah. Duk da cewar iyayensu ba sa ko ko ga maciji da juna. _Hilal_ Yana fitowa daga part ɗin sa downstairs ya nufi ɓangaren Kakanninsa. A can ƙasar maƙoshi ya yi sallama, don ko Dada ba ta ji shi ba, ganinsa kawai ta yi ya shigo. Kallonsa ta yi daga sama har ƙasa don ta ga alamar shirin fita yake yi. Don haka ta ce. "Kai kuka ina zuwa cikin daren nan, sannan k shigo Mani ko sallama babu kamar gidan kafirai ko, to ai ko kafirai ne ka ƙwankwasa ƙofa, saboda an kai ka cikin nasara asarar duniya ka je can ka koyo mugun hali." Bai ce mata komai ba ya miƙe ya nufi hanyar fita ya fice. Taɓe baki Dada ta yi tare da cewa. "Wannan kam matarka na da aiki wallahi, a ce ma magana sai ka ga dama kake yinsa, idan. Ka ga dama ba ka yi kamar kurma, dubi yadda ya shigo ya zauna mani ko magana babu, ai ko kurma ne ya ɗaga mani hannu zan san ya gaishe ni. To Allah ya kyauta."da _Jidderh_ Tana shiga cikin ɗakin ta dade kai tare da furta kalmar. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Jakar makarantarta ta saki ganin matar Yayanta kwance a cikin jini da alama naƙuda take yi. "Aunty Sa'adatu garin ya kika zauna har hakan ta faru?" Sa'adatu wacce ta gama galabaita na naƙudar da take yi ta saka magana. A guje Jidderh ta fito daga ɗakin ta nufi hanyar fita, kai tsaye ta nufi titi duk da sam ta mance wata gajiya da yunwa da ta kwaso. Sai da ta kai bakin titi sannan ta tsaya daga gudun da take yi. Wani mai keke napep (adaidata sahu) ta tare ta shiga. "Mallama don Allah ka yi sauri mu tafi nan za ka bi matar Yayata ce ba lafiya." Ta karasa maganar tana nuna masa layin da ta fito, don haka ya bi in da ta nuna masa. kai tsaye har kofar gidan suka sauka. A guje ta fita ta shiga gidan ta same ta har lokacin a kwance. Wani zani ta ɗauko ta ɗora mata ta cire mata wannan da ya ɓaci. Dakyar ta iya taimaka mata ta tashi tare da jingina a jikin bango. Hijabinta ta saka mata shi a jiki ta taimaka mata duk da ba wani iya tafiya take yi ba, amma Jidderh ta taimaka ta rike ta har suka fito ƙofar gida. A cikin napep ɗin ta saka ta ita ma ta shiga suka bar ƙofar gidan. General hospital ta nemi ya kai su, don can ne take da yakinin sauƙin kashe kuɗi. Suna shiga harabar asibitin wasu ma'aikata suka hange su shi ne suka ɗauko keken da aka ɗaukar marasa lafiya suka saka ta a ciki. Mai keken na ganin Jidderh za ta wuce ya ce . "Kud'ina da?" Sai a lokacin ne ta tuna cewa ai ba ta ko sisi. "Mallama don Allah ka yi hakuri Wallahi ban da kuɗi." "Fitowa ya yi daga cikin napep ɗin ya lalle ta ya ce. "Amma ke ba karamar ƴar rainin hankali ba ce, ta ya ya za ki kira ni ki ce baki da kuɗi, wanann I zancen banza ne, fitsari na zuba a cikin keken ne ba fetur ba, wallahi ko ki bani kud'ina ko na tafka maki rashin mutumci a a wajen nan." "Ka ga Mallam meye na rashin mutunc, ba na cikin nutsuwata ce, duk na bi na rikice ba ka ga a halin da muka kawo ta ba ne, kai ba ka da tausayi ne idan ƴar uwarka ce ya za ka ji?" Wata ma'ikaciyar asibitin ce ta zo ta ce. "Ke koyi sauri ana jiranki." "Ba in da za ta je sai ta biya ni kuɗina." "Nawa ne kudin naka?" Matar da ta zo kiran Jidderh ta tambaya. "Naira ɗari biyar ne." Ta mika masa kudinsa yayin da Jidderh ke mata godiya. Da sauri suka karasa ciki inda ya hangi Aunty Sa'adatu zaune a keken da aka ɗauko ta kuma ko numfashi ba ta yi. "Nurse a kai ta kan gado a ajiye a duba ta mana, dubi yadda kuka barta cikin wannan halin." "To ai sai ki ɗauke ta ki kai ta a gadon ki yi mata abinda ya dace." Ɗaya daga cikin nurse ɗin ce ta faɗa. Jidderh ta kalle ta da mamaki za ta yi magana sai ta ji Muryar nurse ɗin da ta bayar da kuɗin napep ɗin su ta ce. "Ki kawo takardar awonta da kayan da ake rubuta masu idan za su zo haihuwa su kawo." Shiru Jidderh ta yi kafin ta ce. "Ba ta zuwa awo ai." Gabaɗaya suka kalle ta tare da kallon Sa'adatu da ba ta san ma me suke cewa ba. Wata ce . "To sai ki kwashe ta ku tafi ku bamu waje, duk wayar da kai da ake yi wa mata akan mahimmancin zuwa awo ga masu ciki a banza ne wajenku. Ya ya ya mace da ciki za ta zauna ba ta zuwa asibiti ana yi mata awo a duba lafiyar Babyn a bata magunguna, sannan kun bar ta ta gama galabaita kun kawo ta idan ta mutu ku ɗora mana laifi ko?" "Duk abinda za ku faɗa ku faɗa amma daga baya na yanzu ba, saboda tana cikin wani hali ku taimaka yi abinda ya dace don Allah." Haka Jidderh ta dinga roƙonsu tana magiya da taimakon wanan nurse da ya biya masu kudin nape suka ta saka baki suka karɓe su. Bayan an shigar da ita ɗakin haihuwar ne aka lissafa wa Jidderh kayayyakin da za su yi amfani da su wajen karbar haihuwar da bayan ta haihuwar. Lissafin dubu goma suka yi mata na abubuwan da za su bukata. A guje Jidderh ta sake fita duk da ba ta san ya za ta yi ba. Yanke shawarar komawa gida ta yi ko Inna ta dawo, haka kuwa aka yi ya tare da nape ta ce sai ya kai ta gidan za ta amsa masa kudin. Har ƙofar gidan ya sauke ta, ta na sauka Inna na dawowa. Don haka a wajen Inna ta karbi ɗari biyu ta nawa mai nape ya tafi. "Lafiya na gan ki a firgice Jidderh?" "Inna Aunty Sa'adatu ce na dawo na tarar da ita cikin jini, ta fita igayyacinta. To asibitin Gwamnati na kai ta suna ta fada kin san ba ta zuwa awo, dakyar suka amshe ta, yanzu kayan da zasu yi mata amfani suka ce sai na siyo wai dubu goma. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, duba goma ina za mu dame shi yanzu, daga ni sai Naira ɗari biyar. Ko shi Yayan naki bana tunanin yana da kuɗin, don ko da zai fita hannu na ya karbi ɗari biyun da zai yi bayan baro da zai dinga ɗaukar kaya." "Umma bari na je kasuwar na same shi ko za'a samu wani abu wajensa, ko wajen abokansa ya nemi aron kudin, Inna ke ki tafi asibitin ni kuma zan ke kasuwar da yake aiki na nemo shi. Tana gama fadar haka ta juya ta tafi don ba su da nisa da kasuwar. Inna ta shiga cikin gidan ta dauki zannuwa tsofaffi da flask na ruwan zafi ta rufe gidan ta wuce asibiti. _Asadullah mansion_ Dad ne ya fito da shirinsa na fita, bayan ya leƙa ya yi sallama da babban ɗansa Asadullah. Har zai nufi wajen motarsa in da direba ke jiransa, juyawa ya yi ya kalli part ɗin ƙaninsa Uncle Adam. Har yamma ta yi ba su ga juna ba. Don haka ya ciro wayarsa ya danna masa kira. Uncle Adam dake zaune tare da matarsa Hajiya Mami, sai yaransu uku Nasir, Maryam, da Abida. Wayarsa ce ta soma ringing, ganin Yayansa ke kira ya sa ya kau da kai tare da cewa. "To me kuma zai sanar mani?" "Mamy da ke kallon wayar ta ce. "Ai ba laifin kowa ba ne sai laifin wannan munafukar matarsa, idan ba munafurci ba ta san cewa ƴaƴanmu na son Asad sannan za ga je ta kwaso wata bare ta kawo a cikin gidan nan, wallahi ba zai yiwu ba, sai dai hankalin kowa ya tashi a cikin familyn nan." Har sau uku Dad na kiran wayar Uncle Adam bai ɗaga ba, sanin cewa ba lafiya ba don kullum dai ya zo gai da Dad amma yau bai zo ba, ya kira shi ba'a ɗaga ba, hakan ya saka nufi ɓangaren Uncle Adam. Knocking ya yi Nasir ya je ya buɗe ƙofar, ganin Wan mahaifinsa ya sa ya gaida shi cikin girmamawa. "Abbanku na nan?" ",Eh yana ciki." "Ka ce masa ina jiransa." Ciki ya shiga ya sanar da Uncle Adam sakon Dad, don haka Mami ta taɓe baki tana cewa. "Wallahi kada ka yarda da wannan zancen, dama kai ne mai ɗaurawa Asad aure gida bai ƙoshi ba ai ba za'a kai dawa ba. Ta ya ya zamu bari damar da muke hange ya wuce mu, idan Asad bai auri ɗaya daga cikin ƴaƴanka ba wasu banza ne za su ci daga waje. Sai dai mu kare a cin arziki muna zaune a gidan da ya gina muna cin abincin da yake siya muna sha daga gare shi muna sutura daga gare shi a haka za mu kare ba za mu mallaki dukiyarsa ba sai dai wasu banzaye ina da sake wallahi. Ka je ka same shi duk abinda za'ayi ayi don na dan Asad bai da zaɓi." Uncle Adam bayan ya gama sauraren Mami kuma ya hau kan maganarta ya zauna, ya fice don zuwa amsa kiran Dad. _Isah_ Tsaye yake rike da baro ana loda masa buhuhunan suga yana kai wa wani shago. Duk da rabin hankalinsa na gida wajen Sa'adatu don ya san tana naƙuda. Ganin lokacin sallar la'asar ta yi ne ya saka shi bayar da ajiyar baron ya nufi masallaci don yin sallar la'asar. _Jidderh_ A guje ta shigo kasuwar tana mayar da numfashi, don ba ta ma san ta in da za ta fara neman Isah ba, tunda yawo yake yi ba zama wake guda yake yi ba. Waige-waige ta fara yi ta in da za ta gan shi. Ga shi zuwa lokacin yunwa ya ci ƙarfinta, don tun koko da ta sha da safe ba ta sake saka komai a cikinta ba. Yawo kawai take yi a cikin kasuwar ba tare da ta san in da za ta gan shi ba. Gajiya ta yi da yawo ta jingina da jikin wani shago ta kumshe dara-daran idanunta. Halin da Aunty Sa'adatu take ciki kawai take tunawa, tausayin ta ya saka ƙwalla suka fara bin fuskarta. Ga shi Isah bai da waya ya siyar da ita ya siya masu abinci. Ji ta yi an goge mata hawayen dake kan fuskarta, ta bude idanunta da sauri ta sauke su akan Isah. _Fatima Zahrah_ Tana cikin yin tsalle kwaɗon da ya saka ta duk ta gaji, ga sanyin dake ɗakin ya mata yawa, kasancewar ba ta son sanyi. Don shi kuma ɗakinsa kullum cikin sanyi yake don sai ya ƙure gudun A.C ga shi yanayin damuna ake ciki harin ya yi sanyi. Numfashinta ne yake barazanar ɗauke wa, hakan ya sa ka ta kasa cigaba da tsallen kwaɗo, don duk jin jikin da ta yi ta kasa tsayawa saboda ya ce yana ganinta. Zubewa ta yi a saman tiyel ɗin dake ɗakin. Nan ta dinga fafuka da numfashinta dake barazanar ɗauke wa. Tsawon lokaci tana cikin wannan halin har ta kai ta daina gane komai ta sume a wajen. _Hilal_ Da misalin ƙarfe ɗaya na dare motarsa ta da danno kai a cikin gidan. Wani soja ne ya ke driving ɗinsa, ya bude masa murfin bayan motar ya fito kai tsaye ya nufi cikin gidan. Bayan ya shiga babban falon gidan ne ya lashe wutar falon, cikin duhu ya cigaba da tafiya har ya haura upstair. Kai tsaye ya nufi part ɗin sa. Nan ma ya rage hasken falon sannan ya wuce bedroom ɗinsa. Sam bai lura da Fatima Zahrah dake kwance a can ƙarshen ɗakin ba. Kayan jikinsa ya rage ya shiga bathroom ya yi wanka. Fitowa ya yi sanye da white bathrobe a jikinsa. Shiryawa ya yi cikin riga da wando na barci farare, don shi komai nasa fari ne . Haurawa gadonsa ya yi da niyyar da niyyar yin barci, kashe hasken ɗakin ya yi ya kwanta bayan ya yi addu'ar kwanciya barci. Tunawa ya yi da wani aikin da zai yi a aka. System ɗinsa, tashi ya yi ya kunna hasken ɗakin, idanunsa suka sauka akan Fatima Zahrah dake sume. Dafe goshi ya yi don shi sam ya mance da ita. "Wanan wace irin sakarya ce, tun da ta san tana da lalura why not idan ta ga zai tashi ta je ta nemi maganinta ta sha. Mtssssw." Ƙara sawa ya yi gabanta yana kallonta ya ma rasa abun yi. Fita ya yi daga ɗakin kai tsaye ya nufi part ɗin su Fatima Zahrah, karon farko kenan da ya shiga part ɗin tun bayan da aka ƙara wa gidan girma aka gyara aka bawa Kowa part dinsa. Ko da ya zo kasar bai taba zuwa ba sai yau Kasancewar duhu ne ya sa ya kunna hasken wayarsa. Bayan ya shiga falon wanda ya ke tashin ƙamshi ya tsaya yana nazari ina ne ɗakinta, don ya san can ne zai samu maganin da zai bata. Kuma bai dace ya kawo ta ya ajiye cikin halin da take ciki ba don iyayenta ba su sani ba ballantana su yi mata wani taimakon. "Ina ne ɗakinta? Kada na shiga ɗakin mahaifiyarta ko mahaifinta a samu matsala." Rintse idanunsa ya yi ya bude kai tsaye ya nufi wani ɗakin ya shige. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SADAUKARWA* wannan shafin sadaukarwa ne a gare ki masoyiyata.AMMEY LAYLERH ki yadda kike so da shi Allah ya bar ƙauna. Page0️⃣5️⃣ Rintse idanunsa ya yi ya bude kai tsaye ya nufi wani ɗakin ya shige. Yana shiga ba kowa a ɗakin, ɗakin ya sha gyara tsaf sai ƙamshi kawai ke tashi a ɗakin. Kallo ɗaya ya ji wa ɗakin ya gane ɗakinta ne don ga photon ta manne a ɗakinn. Da kuma takardun da ya gani kan gado wanda alama ya nuna karatunsu take yi. Dube-dube ya fara yi a cikin ɗakin ko zai ga magani babu a fili, don haka sai ya fara bude drawers har ya gani a side drawer ɗint. Ledar ya ɗauko ya bude ya ga inhelar da magungunan ta na sha da kuma allurai. Ganin cewa har ya kai matakin da ta suma ba zai fi dacewa ya yi mata al ki Alluran, don haka ta ya ɗauko alluran da sirinjin ya saka a cikin Aljihu rigar barcin dake jikinta. Mayar da sauran magungunan ya yi ya fito yana zuwa falo sai ya ga an kunnah hasken falon. Ido huɗu suka yi da mahaifiyarta wanda ta ji motsin rufe ƙofar lokacin da ya shiga ɗakin, ta yi tunanin Fatima Zahrah ce sai dai sanin ba ta dawowa cikin dare idan ta kwana ɓangaren Dada ya sa ta fito ta ji lafiya me ya dawo da it a tsakiyar dare. Kallo ɗaya Hilal ya yi wa Ummin Zahrah ya ɗauke kai ya nufi hanyar fita, jin muryarta ya yi tana cewa. "Me kake yi a nan a cikin daren nan?" Bai ba ta amsa ba ya yi ficewarsa. Abbi ne ya biyo bayan Ummi ya ce. "Lafiya?" "Ba lafiya?" "Subhanallah me ya faru?" "Wannan yaron Hilal ne ya shigo part ɗin nan." Kallon mamaki ya mata tare da cewa. "Hilal kuma, to me ya zo yi?" "Tambayar da nake masa kenan amma kai ma ka san ba zai taɓa bani amsa ba." Shiru Abbi ya yi kafin ya ce. "Ba damuwa je ki kwanta kawai." "Ba damuwa fa ka ce, akan me zan iya kwanciya ka san mutanen gidan nan ba ƙaunarmu suke yi ba, ba su ƙi wuta ta cinye mu ba su huta. Musamman mahifiyar Hilal ta tsani ganin mu a rayuwarta ita da Laila, ba sa ƙaunarmu ba sa ƙaunar ƴaƴanmu musamman Zahrah sun tsane ta sannan na ga ɗan su mafi soyuwa a gare su ya shigo part ɗin nan wanda na san ba alkhairi ya kawo shi ba ɗakin ƴata budurwa a cikin wannan daren ka ce ba damuwa?" Hannunta ya rike suka shiga cikin ɗakin Hilal na koma wa ɗakinsa har lokacin tana sume, allura ya ciro da sirinji ya ɗebi ruwan alluran ya yi mata a jijiyar hannunta. Ba jimawa ta ja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya. Tashi ya yi ya jefa alluran a kwandon shara. Ta kasa tashi kasala ce kawai take ɗawainiya da ita, ga ƙafafunta sun gaza ɗaukar ta sakamakon tsamin da ƙafar suka yi mata na tsallen kwaɗo da ta yi. Yunƙurawa ta yi da niyyar tashi tsaye ta kasa, komawa ta yi ta zauna idanunta na ciko wa da ƙwalla. "Ke dalla tashi ki fitar mani a ɗaki!" Ya faɗa yana galla mata harara. Sake yunkurin tashi ta yi a karo na biyu amma ta kasa. Kukan shagwaɓa ta saka masa tare da cewa. "Wallahi ba zan iya tashi ba ƙafa ta ciwo take yi." "Idan ba ki tashi kin fice ba sai na sake saka ki punishment ɗin." Kallonsa ta yi cike da tsanarsa wanda ta ji ya yi ɗarsu a cikin zuciyarta. "Dama ba ƙauna ta kuke yi ba, idan son damunku ne na mutu ku huta da gani na a duniyar nan." Ƙasa-ƙasa ta yi maganar yadda ba zai ji ta ba. Ganin bakinta na motsi ya sa shi cewa. "Me kike cewa?" Shiru ta yi don ba za ta iya maimaita abinda ta fada ba. "I Sa'id out!" Ya faɗa cikin tsawa. Kallonsa ta yi cike da jin tsoronsa ta mike da ƙyar tana kuka mai sauti. Sautin kukan ne ya ji ya dame shi, don haka ya furta kalmar " shhhp." Haɗiye kukan ta yi tana miƙewa ta zube kada don ƙafarta ba ta iya tafiya. Tana zube wa ƙasan wajen saman tile sai ta ga duhu ya mamaye ɗakin. "Wayyo Ummina ki zo ki taimaka Mani." Sai jin muryarsa ta yi yana cewa . "Idan na sake jin muryar sai na sauya maki kamanni, ƙarfe biyun dare za ki dame ni da hayaniya, to ki shiga hankalinki. Duk lokacin da ƙafarki ta sake ki to ki fita ki bar mani ɗaki." Shiru ta yi kamar ruwa ci ta sai hawaye da ke bin fuskarta. Daga nan ya juya ya kwanta tare da addu'ar kwanciya barci, ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi . _Jidderh_ Murmushi ta sake lokacin da idanunta suka sauka akan Isah. Yaya Aunty Sa'adatu ce ba lafiya tana naƙuda na kai ta asibiti ana bukatar kuɗi kimanin dubu goma." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un." "Yaya meye abun yi tana cikin mawuyacin hali ." Aljihunsa ya lalubo kudin da ya samu na yau. Naira dubu biyu da ɗari biyar ce. "Kin ga abinda nake da shi." "Yaya ko aro ne ka nema." "Mu je wajen abokin aikina." Suna zuwa ya ya yi wa abokin aikin bayanin halin da matar ke ciki, dubu takwas ya bashi , godiya suka masu suka tafi. Daga nan suka nufi asibitin a cikin keke nape, bayan sun sauka suka nufi in da ɓangaren masu haihuwa . Nan suka tarar da malaman asibiti na ta yi wa Inna faɗa, sakan Sa'adatu ta dade tana naƙuda ba'a kawo ta ba, a halin da ake ciki ma yanzu ba za ta iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata tiyata. Kudin da aka fada ne ya saka hankalin su tashi, ba Inna hatta Isah da Jidderh da ksarasowarsu kenan sai da hankalinsu ya tashi, sakamakon jin wai ana neman Naira dubu ɗari daga hannunsu. Ɗaya daga cikin nurse ɗin ce ya ta kalli Isah ta ce masa. "Ka je Doctor ya yana son ganinka." "Ina Ofishin Doctor?" Da hannun ta yi masa nuni, cikin sanyin jiki ya karasa kofar tare da yin knocking, izinin shigowa Doctor ya bashi ya shiga . Hai da Doctor ɗin ya yi ya amsa masa tare da tambayar sa "Kai ne aka kawo matarka za ta haihu ko?' "Eh nine." "Garin ya ka yi sakaci har haka nan, dai da ta galabaita ƙarfin ta ya kare har ta fara fita hayyacinta ne za ku kawo ta, ga shi yaron bai zauna da kyau ba a cikin mahaifa ba ku sani ba saboda sakaci irin na ku. To yanzu dai dole sai an yi mata aiki ana bukatar kudi kimanin Naira dubu ɗari, na sanar da nurses su fada maka. "Doctor to yanzu dan Allah ba hanya?" "Babu in dai kana son ceton rayuwar matarka." "Doctor ba na da kuɗin za'a iya fara mata aikin kafin na dawo zan je neman kudin ne." "Ba zai yiwu na taɓa ta ba, dole sai ka nemo kudin nan." Da sauri ya tashi har ya nufi hanyar fita, wajen su Inna da Jidderh ya nufa. Bayanin komai ya masu in da hankalinsu ya tashi . "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Isah ina za ka samo wadannan makudan kuɗaɗen?" "Wallahi Inna ban sani ba ba na da shi ban da hanyar samun da, yanzu haka dubu goma ne a hannuna, da Jidderh ta sanar da ni halin da ake ciki ne na nemi barin dubu takwas." "Kuma ga shi mu ba wata ƙaddara muke da ita

Chapter 3 of 39