Share this page
da yake ta kai masa bakinsa. Nan da nan ya gutsiri cake ɗin, ganin haka ya sa ta dinga gutsura tana bashi a baki yana ci. Tana kuka bashi youghurt , sai da ya cinye tas ya kuma shanye robar youghurt ɗin sannan ta kalle shi ganin yadda ya rame. Ƙwallar tausayin sa ne ya zubo mata, ta mike ta bar wajen da sauri don kada wani ya zo ya tarar da ita wajensa. Ta tafi ta ƙudiri niyyar sai ta yi wa Mama magana, duk da cewar Mama ƴar aiki ce a gidan amma ta dade don ta ji labarin cewa Mama ta reni Asadullah yana yaro ita ke kula da shi. Za ta yi shawara ta sanar mata halin da ake ciki. Don tana tsoron tunkarar ƴan gidan da zancen ya kasance ta saka kanta a cikin hatsari. _Hilal_ Zaune yake a bayan motarsa yayin da ke gaba yana driving. Wayarsa ce ta yi ruri ya duba. Ganin Papa ne ya ɗaga tare da yin sallama. "Assalamu alaikum" Daga can ɓangaren Papa ya amsa tare da cewa. "Sojana ya kake?" "Am fine." "Yauwa dama ƙanwarku ce za su yi gasar karatun Al-ƙur'ani a garin Kaduna. Shi ne nake so a ce ka kai ta." A tunaninsa Maryam ce da suka fito ciki ɗaya ko Nadiya ƴar wajen Uncle Adam ko ɗaya daga cikin yaran Aunty Laila, sai dai ya san cewa ba damuwa suka yi da karatun Alqur'ani ba ballantana su je wani gasa. Gara ma Maryam duk da ita ba ta sauke ba ya san daƙyar idan ita ce. "Papa wacce kake nufi? Don na ga dukkansu ba wani nisa suka yi a cikin karatun Alqur'ani ba." "Ka mance Zahra ta sauke har walima ta yi, to ita ce nake nufi ai." Haɗe fuska ya yi tare da cewa. "Kuma ba wanda zai kai ta sai ni?" "Yayanninta ba sa nan kai ba Yayanta ba ne idan aka cire Mahmud da Sadik. " "Papa a gaskiya ni ba zan...." Katse shi ya yi ta hanyar cewa "Ba na bukatar wani uzuri daga wajenka. Ba wanda zan iya sawa ya kai ta bayan kai, don mahaifinta da mahaifiyar ba sa nan, ko na da ina nan zan bi ta ji tafi duka gidan nan na san ba wanda zai kai ta, don haka ka koma gidan yanzu ka same ta ku tafi can Makarantar ka yi magana da Mallamansu. Don ban yarda ta tafi tare da kowa a makarantar ba ƴa mace ce ita sai da saka idanu da kula. Na san ban isa da mahaifiyaeka ba amma idan ba za ka je ba zan kira ubanka na bashi umarnin da dole sai ya bi. Don haka yanzu na gama magana da Mallamansu suna jiranku kai da ita." Yana gama maganar ya kashe kiran wayar, ransa a ɓace, wai shi ne zai dauki yarinyar can ya kai ta wani gari Umarni ya bawa direban ya juya akalar motar zuwa gidan. A parking space ya tsaya, tsawon mintuna biyu da bude basa motar bai fito ba, kafin ya fara fito da ɗayar ƙafarsa waje, sannan ya fito da ɗayan ya fito gabadaya. A falon ta samu ƴan matan gidan duka suna kallon T.V suna fira. "Sannu da zuwa Yaya." "Kausar ta fada tana miƙewa don ta ɗauka saboda messages nata ya dawo da ta sanar da shi ya dawo gidan ta masa girki kuma akwai maganar da za ta masa. Bai amsa gaisuwar ba ya kalli Maryam ya ce. "Je ki kira mani yarinyar can?" Wace yarinya Yaya?" Harara ya banka mata tare da sauke kai " "To Yaya ba kowa a nan iyakar mu kenan sai dai idan Zahra kake nufi." "Eh ita." Da mamaki suka kalle shi Nabeela ta zaro idanu tana cewa. "Lafiya?" Bai tanka mata ba, ba jimawa Maryam ta dawo tare da Zahra Sanye da Hijabi kamar kullum. "Mugun kallo ya mata sannan ya ce. "Idan kin shirya ki same ni a mota." Yana gama fadar haka ya fice ya barsu da ƙamshin turarensa. Fatima Zahrah ta koma ta dauko wayarta a ɗaki, tana fito Kusar ta ce. "Uban meye za ki masa meye tsakaninku?" Ba ta tanka mata ba ta nufi hanyar kofar fita. Ƙasancewar akwai matattakala kin fita wanda sai kin sauka ta nan. Tana fita Kausar ta bi bayanta ta hankaɗa ta da ƙarfi ta tafi luu idsnunta a rintse ta sadakar dole sai ta illata. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣4️⃣ Kasancewar akwai matattakala ƙoagar fita wanda sai kin sauka ta nan. Tana fita Khausar ta bi bayanta ta hankaɗa ta da ƙarfi ta tafi luu idanunta a rintse ta sadakar dole sai ta illata. Bayan ta sadakar tana jiran ta ji yadda Allah zai yi da ita Idanunta a rintse ta ji sauka a jikin mutum, don tabbas hannun mutum ne, tabbatar da cewa ba faduwa ta yi ba ne ya sa ya ƙanƙame shi a jikinta. Jin daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya sa gabanta ya faɗi, saboda tsoronsa da take ji. Tana buɗe Idanunta ta sauke akan idanunsa masu rikita mai kallonsu. Harara ya watsa mata tare da sakinta ta faɗi ƙasa, ƙara ta saki ta ɗan ji zafin faɗuwar sai dai duk da haka ya gode masa ya ceci rayuwarta. Don da daga can saman matattakalar ne ta faɗo tabbas sai sai ta karye. Tashi tsaye ta yi tana tura baki tare da goge ƙwalla a zuciyarta tana cewa. 'Ya san dama zai yarda ni na fadi me yasa ya tare ni, ai da ya barni kawai na fado na ji ciwo, bayan na sakankance da cewa ya taimake ni ashe wani sabon muguntarsa zai mani. Sai sai na shi da sauki tun da daga jikinsa ne ya yarda ni da daga matattakalar na fado ba. ' Ɗaga kai ta yi ta kalli ƙofar ta ga Kausar, Nabeela, Nadeeya da Maryam sai kuma su Mama da Aunty Laila. Mugun kallo suke mata sai Maryam ce kaɗai ke mata kallon tausaya wa. Ko da ta juya ta ga baya wajen har ya karasa parking space, da sauri ta karasa wajen tana ɗan ɗingisa ƙafa. Yana zaune a bayan motarsa direbansa na gaba. Tana tsoron ta zauna kusa da shi sai ta tsaya. Don sanin halin mutanen gidan sai su ce ba zasu shiga mota tare da ita ba, mazansu da matan.Cikin takaici ya fara magana. "Tsayuwar me kike yi a wajen da ba za ki shigo ba." Da sauri ta bude bayan motar ta shiga. Ba abinda kake ji a motar sai sanyi da kuma daddaɗan ƙamshi wanda ya sa sai da ta yi ajiyar zuciya. Direban ya ja motar suka fice daga gidan. Tana mamakin yadda wani lokacin Yaa Hilal ya ɗan banbanta da sauran mutanen gidan. Don shi baya hantararta ko kyararta ballantana ya nuna ƙyamarta kamar yadda sauran suke yi. Shi dai idan sun haɗa idanu ya harare ta ko ya mata mugun kallo, amma ko gaishe shi ta yi baya amsawa, sallama dai yana amsawa kamar yadda ya zama wajibi a Addinin Musulunci. Amma sauran mutanen gidan ba sa amsawa ko sallmarta ce. Direban ya ɗan juyo ya kalli Hilal ya ce. "Sir ina za ku je?" "Ka tambayi yarinyar nan ina ne makarantar islamiyyarsu." Jin haka ya sa Fatima Zahrah ta sanar da shi wajen. Wayarsa ta kawo haske alamar kira ya shigo. Ɗaga wa ya yi kafin ya yi magana ya ji Muryar Mama na fada tana cewa. "Ina za ka je da wannan banzar yarinyar ?" "Mama Papa ne ya aike ni makarantarsu." Tsuki ta ji tare da cewa. "Akan me za ka yarda?" "Mama cewa ya yi idan ban yi ba ai sai ya kira Abba ya bashi umarni." Tsuki Mama ta ja tare da katse kiran wayar. Kallon Aunty Laila da Mummy ta yi tare da cewa. "Kin ji wai mahaifinki ne ya tura su wani wajen." Aunty Laila ta ce. "Gaskiya ba na son kusancin wannan yarinyar mai ƙirar aljanna kusa da Ajmal, ga Nabeela da Kausar suna mutuwar sonsa." "Kwantar da hankalinki matar Yaya matuƙar ina raye ai ko da wasa n hakan ba zai taba yiwuwa ba kar ki saka Ni ma na shata masa dogon layi akanta " *Prison Gidan yari* Sanye yake da kaya irin nasu na ƴan gidan yarin, sai faman Safa da marwa yake yi a cikin falon. Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan yarin ya shigo tare da sallama. Bai amsa masa sallamar bs sai da ya karaso ya ce. "Yallaɓai wadannan jaridun da n kawo maka iya su ne waɗanda aka fitar yau.da sauri y kalli ma'ikacin ya ce. "Ka tabbatar ba wani jaridar bayan wandada aka kawo mani da za'a iya rubuta abun da nake bukatar ji?" Cikin tabbatarwa ya amsa masa da "Ƙwarai kuwa." Dunkule hannu ya yi ya naushi iska yayin ma'aikacin ya ce. "Yallaɓai zan tafi bakin aiki na." Kuɗi dake kan kujerar ya yissa nuni da hannu, ɗauka ya yi yana yin godiya ya fice. Dunƙule hannu ya yi ya dakin bangon ɗakin yana cewa. "Dole ka mutu Asadullah ba zan taba samun kwanciyar hankali ba sai na ji labarin mutuwarka zan samu nutsuwata. Tura ni gidan yarin da ka yi shi ne kuskure mafi munin da ka tafka a rayuwarka. Tunda likitan ya gagara kashe ka to ni zan ɗauki mataki da kaina. Don a duk lokacin da na ganni a cikin gidan yarin nan na tuna kudanci da dangantakar mu amma ka iya aikata Mani haka sai zuciyata ta yi ya tafarfasa. Me ya da ka kasa yafe mani kana da iko da alfarma na fitar da ni ka kasa. To an zo wajen da na ƙasa jurewa da gatana ka kawo ni nan." Haka ya dinga surutu shi kadai karshe ya fice daga ɓangaren ya nufi wani ɓangaren na gidan yarin. Wasu maza hudu ne suke shan sigari dai busa hayaƙi suke yi. A hankali ya karaso wajen, kallo ɗaya suka masa suka ɗauke kai. Shi ma shiru ya yi bai yi magana ba, don tsabar jin kai irin nasa yafi karfin ya masu sallama ko ya gaishe su. Ɗaya daga cikin su ne ya kalle su ya ce. "Mallam lafiya ka zo ka wani tsaya wa mutune akai?" "Kai ka damu da shi ni dama ban cika shiga sabgar ƴaƴan manyan nan ba." Wani ya faɗa aji bayan ta yi gama busa hayaƙin sigari. Kallon banza ya yi masu tare da cewa. "Waye madurguji?" Da sauri suka kalle shi tare da cewa. "Me yasa kake nemansa mutum ne shi mai hatsari." "Sanin haka ya sa nake nemansa don zai mani amfani." "Ka zagaya bayan dutsen nan za ka same shi da shi da muƙarrabansa." Suna fada masa haka ya juya ya bar su ya nufi bayan dutsen da suka kwatanta masa. Tafiya yake yi yana murmushi tare da girgiza kai. Wasu mutane ne kimanin du biyar a bayan dutsen, ɗaya daga cikinsu wanda alama ya nuna shi ne oga yana shan sigari, zaune yake akan dutsen yayin da sauran mutane huɗu suke zaune a ƙasa. Yana zuwa wajensu ya tsaya akansu yana cewa "Waye madurguji a cikinku?" Kallo ɗaya madurguji ya masa ya zuƙi hayaƙi tare da kallon ɗaya daga cikinsu ya ce. Wanda aka kalla ne ya tashi ya kwashe ƙafar mai tambayar tare da cewa. "Ka rage tsawonka sannan ka san waye a gabanka ko kai waye." Murmushin takaici ya yi tare da kallon jikinsa yadda aka kwashe masa ƙafa har sai da ƙura ya ɓata masa jiki, yana duƙe akan guiwarsa ya ce. "Da kun san waye da matakin da na taka a rayuwa da za ku san cewa na fi ƙarfin wulakancin tantirai irinku." Dariya Madurguji ya kece da shi sannan ya bushi hayaƙin ya hura a fuskarsa sannan ya ce . "Mu tantirai ne kuma na sani amma duk tsiya ba na butulu ba ne, ka koyi halarci a Rayuwarka, ina da tarihinka da butulcin da ka yi wa ɗan uwanka uban gidansa wanda ya zama garkuwa a gare ka lallai kai babban maci amana ne." Tsuke fuska ya yi tare da cewa . "Wannan bai shafe ka ba aiki na kawo maka kuma zan maki biya mai tsoka idan za ka yi." _Jidderh_ Bayan ta kammala aikinta ta nufi ɓangaren ma'aikatan gidan, kai tsaye ta nufi ɗakin Mama. Da sallama ta shiga, Mama ta amsa tare da ba ya izinin shigowa. Shigo wa ta yi t tarar da Mama na ninke kayan z ta wanke. "Jidderh ke ce?" "Eh Mama ni ce." "Na ɗauka kin tafi gida lokacin tashin ki ya yi." *Ban tafi ba Mama dama ina son magana da ke." "To ki zauna mana Jidderh." Ta yi maganar tana nuna mata kujera mai zaman mutane uku. Zama ta yi tare da cewa. "Barka da warhaka Mama." "Barka dai Jidderh ina fatan dai lafiya." "Lafiya lau dama ina son na sani yaushe Dad zai dawo?" Kallon ta Mama ta yi tare da yin ɗan jim sannan ta ce. "Ni ina zan sani ai wannan ba hurumina ba ne." "Haka ne amma dan Allah ina son na tamabaye ki ko ka kin san in da Sir Asadullah ya tafi?" Kallon mamaki ta yi mata tarar da cewa. "Jidderh wannan amsar ban san amsar da zan ba ki ba." "Am dama na gan shi a cikin gidan nan ne?" Da mamaki ta kalle ta tare da cewa. "Ban gane yana gidan nan ba, bayan kowa na gidan nan ya tabbatar da cewa baya nan, a ina kika gan shi ?" "Shiru ta yi tana nazari don da alama masu neman kashe shi suna cikin gidan da alama ma na kusa da shi ne, kada yanzu magana ta fita ga shi baya cikin hayyacinsa kada ta ɗaure kanta. Don haka ta canza zancen da cewa. "Shekara nawa kika dauka Mama kina masu aiki a gidan nan?" "Zan kai shekaru talatin ina aiki a gidan nan, akan idanuna aka haifi Asadullah da sauran yaran." "Mama idan ba damuwa zan so ki bani tarihin wannan gidan." Murmushi Mama ta yi tare da cewa "Ba damuwa yanzu ina da aiki idan ki ka sake zuwa zan baki tarihin wannan bahagon gidan." Kallon mamaki ta yi mata tare da cewa. "Bahagon gidan kuma Mama." Murmushi irin ta su manya sannan ta ce. "Ba za ki gane ba, wannan gidan ya wuce sanin tunaninki , Allah ya kyauta." Ta so jin wani magana daga bakin Mama amma ba yadda ta iya haka ta yi wa Mama sallama ta bar gidan zuciysrta cike da saƙe-sake. *Kuyi hakuri da wannan* Maman Ihsan ce✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page1️⃣5️⃣ Ta so jin wani magana daga bakin Mama amma ba yadda ta iya, haka ta yi wa Mama sallama ta bar gidan zuciysrta cike da saƙe-sake. Ko da ta koma gidan sallama ta yi ta shiga, Inna na zaune bisa tabarma a tsakar gidan tana yi wa yaron Sa'adatu. Sa'adatu na tuƙa tuwo a saman murhun gawayi. Amsa mata sallamar suka yi tare da mata sannu da zuwa. Amsawa ta yi sama-sama ta ta shiga ɗakinta. Halin da ta bar Asadullah kawai ke damunta. Tana tuna tarin alkhairi da ya yi mata a rayuwa. A hankali ta fara tuna ranar da ta je kamfanin a karo na biyu da neman aiki. Wata ranar talata da misalin karfe goma na safe, mai keke napep ya sauke Jidderh a bakin kamfanin Asadullah. Bayan ta biya mai napep kuɗinsa ne ta karasa bakin kofar kamfanin. Cikin ikon Allah sai ta samu wancan security ne a bakin gate. Kallo ɗaya ta yi masa ta gane cewa shi ne mutumin da ranar da ta zo neman taimako za'ayi wa Sa'adatu tiyata ya hana ta shiga. Wanda wurin dagewarta na son shiga ne ta faɗi har kokon da A ta kai asibiti ya zube. Yana ganinta shi ma ya gane ta, da sallama a bakinta ta karasa wajensa. Ya amsa mata tare da sauraren me za ta ce. "Don Allah ina son ka taimake ni na hadu da Sir Asadullah ne." "Ke baiwar Allah ganin Sir Asadullah ba abu ba ne mai sauƙi, bar ganin wancan ranar kin gan shi cikin sauki sa'a kika ci yana isowa kika zo shi ya sa kika gan shi kafin ya karasa ciki, amma da zaran ya shiga ganinsa zai maki wuya. Ko nan bakin gate mutum baya shiga ba tare da an bada izinin shigarsa ba." Marairaice fuska ta yi tare da cewa. "Ka taimaka ka barni na shiga." Ko na barki kin shiga daga gate to idan kin shiga ciki ba barin ki za'ayi ki shiga ba. Don ma'aikatan ma hana ki za su yi ki shiga dole sai sun sanar da shi har sai ya bada izinin shigarki ciki." "To ai shi ne ya ce duk lokacin da nake bukatar ganin shi na zo kai tsaye." Ta faɗa tana addu'a Allah ya sa kada ya gane karya take masa. "Ina shaidar yake dole zai baki katinsa mai ɗauke da saka hannunsa ." "Eh ya bani ɓacewa katin ya yi, kuma yau in sha Allah sai na shiga nan, ka je ka tamabaye shi mana." Kallon ta kawai ya yi sannan ya bude mata gate yana cewa "Ai su ba za su bari ki shiga ba kya dawo." Tana shiga wajen ta saki baki tana kallon yadda aka narka dukiya wajen ƙera Kamfanin. A zuciyarta ta ce. 'Wannan wani irin gini ne, gaskiya duk wanda ya tsara wannan ginin kamfanin ya iya tsara gini, sai ka ce a ƙasar Turai. Gaskiya duk yadda aka yi turawa suka tsara wajen nan.' Gabaɗaya jikin bango ginin mirror ne ajikinsa, sannan ga wani wuta ne golding ke fitowa daga jikin mirror ɗin. Da wutar solar yake amfani da shi wanda kudinsa zai iya kai billions naira. Tana kai wa bakin ƙofar ta ji an ce. "Hey!" Tana jin haka ta tsaya tana kallonsa, kallon sama da ƙasa ya mata sannan ta ɗaure fuska ya ce. "Daga ina kike ko an faɗa maki ana bari mabarata ne su shigo nan wajen?" "Ni ba mabaraciya ba ce, na zo wajen sir Asadullah ne." Kallon dyama da ƙasa ya yi mata tare da daka mata tsawa . Lokaci guda ya tuna ita ce wacce ta zo ranar da kuma gargadin da aka yi wa security. Don haka ya ce "Me kika zo yi?" "Shi ya ce na zo duk sanda na so." "Ina katin da ya baki?" "Yallaɓai na nema ban gani ba " Haka nan sai ya tsinci kansa da ba ta izinin wucewa. Da kansa ya ce ta biyo shi a baya. Suna nufar wani ƙafa sai ta ga glass din ƙofar ya zuge da kansa. Suka shiga ckki, taɓa kallo ya yadda komai yake cikin tsari da sha'awa. Ganin idan ta tsaya kallo mutumin zai iya wuce wa ya sa ta ɗauke idanunta daga kalle-kallen da take yi . Nuna mata wata ƙofa ya yi tare da cewa. " ki shiga za ki ga wata mata ita ce za ta maki izinin shiga wajensa." Daga nan ya juya yayin da Jidderh ta kutsa kai cikin office ɗin. Wata matashiyar budurwa ce sanye da Suit baƙi tana danne-danne a laptop. Kallo budurwar ta yi mata tare da cewa. "Ke mahaukaciyar ina ce za ki shigo wa mutane ba tare da an baki izinin shigowa ba?" Wayar dake gabanta ce ta yi ƙara. Tana dubawa ta ga yallaɓai ne da kansa, tana ɗagawa ta ji muryatsa ya ce . "Let her in." "Okay sir,." Ta fada sannan ya katse kiran wayar. Tun zuwan ta yake kallonta da yadda suka ji da security na ƙafa har yadda aka yi ta a shigo duk akan idanunsa ne, sai dai yana mamakin karfin hali ir Irin na yarinyar . Bayan an nuna mata ƙofar da za ta shiga ne ta mike da sauri ta nufi ƙofar . Tura ƙofar ta yi tare da yin sallama. Can kasan maƙoshi ya amsa sallamar don shi kadai ya ji kayansa. Tana shigowa ta saki ajiyar zuciya sakamakon wani sanyin AC da da da ƙamdhin da ya yi mata Barka da zuwa. Tsaya wa ta ji tana kallonsa shi ma ya zuba mata blue eyes ɗin sa yana jiran me za ta ce. "Dama na zo ne don na sake yi msla godiya da irin alkahiri da ka yi Mani a rayuwa ta. Ka ce rayuwar matar Yayana ." Ba tare da ya kalle ta ba ya na ta danne-danne s laptop. "Don Allah zab samu aiki?" Dakatar sda abinda yake yi ya yi tare da zuba mata idanu ya ce. "Wane irin aiki, ne ya matakin karatunki?" "Ban yi karatu ba aikin goge-goe nake bukatar yi." "A yanzu muna da isassun ma'aikata, a shekarun ki ya kamata ace kina makaranta ne." "Eh ina zuwa ina son na hada biyu ne." "Yanzu ba buƙatar mai'iakata, anan." "Yauwa to can gidan fa ba buƙatar mai aiki ne?" Wayarsa ya ɗauka ya kira lambar Mom, bayan ta ɗaga ne yake tambaya ko suna bukatar ƙarin mai aiki, Mom ta ce eh don ɗaya daga cikin masu aikin ta tafi gida wai aure za'a mata. Ya ce zai turo ta . Bayan sun gama wayar ne ya bata adireshin ya ce duk mau abun hawannfs ta tare ta bashi zai kai ta. Sannan ya bata wa i Katin ya ce ta bawa security dake kula da ƙofa idan suka gani za su bari ta shiga ciki. Godiya ta yi masa ya bata kudi masu yawa ta wuce zuciyarta fara tas. Ta samu aikin da za ta tallafawa iyayenta . Bayan ta je ne ta ba wa security katin sannan suka bari ta shiga bayan sun duba. Ta shiga ciki ta samu su Mom da Dady , sallama ta U in suka amsa ta gabatar da kants. Daga nan Mom ta kira Mama ta ce ya nuna mata aikin da alawiyya ke yi sai ta cigaba da yi. Bayan ta gama tunanin da take yi ne ya goge ƙwalla. Tana zancen zuci. 'To dai me yasa aka daure shi aka kulle ji kamar dabba, anya iyayensa na tare da shi kuwa? Ba uwar da za ta juri hakan akwai sake. Ta yaya za'a ɗaure mutum mai daraja kamar Asad ko haukacewa ya yi bai cacanci haka ba. Daga karshe ta yanke shawarar nemo hanyar da za ta taimaka masa. Daga karshe ta fita ta samu Inna da Aunty Sa'adatu. _Hilal_ Suna isa makarantar direbansa ya yi parking motarsa. Ya fito ya budewa Halal bayan motar ya fito. Zahrah ma ta fito ta ɗaya bangaren. Kusan rabin jama'ar dake harabar makarantar zuba masu idanu suka yi. Don motar ta burge mutane sai ɗaukar idanu take yi. Ga mamallakin motar ya haɗu duk wanda ya kalli Hial sau ɗaya sai ya ƙara kallonsa. Ballantana yau Fatima Zahrah ta zo babu niƙab a fuskarta, don duk zuwa islamiyarsu da take yi sai ya sanya niƙab. Idan ko ta fito haka nan to sai ta tsargu da irin kallon da ake yi mata, ba maza ba hatta mata ma shagala suke yi da kallonta. Dan tamkar ita ta halicci kanta haka take. Don duk yadda kuke ji ana faɗin tsantsar kyau da ta wuce haka nan, idanunta ma ɗaukar hankalin mutane suke yi ga ƙaramin pink lips ɗin ta dai shinning suke yi. Sai dai ba ta da ƙiba siririya ce sosai kamar za'a hure ta ta faɗi ƙasa. Wani Mallami ne wanda yake son Zahrah don shi ya san fuskarta wata rana da ciwonta ya tashi a abinsa. Da fara'arsa Mallam Usman ya karaso wajensu. Sai dai yana kallon idanun Hilal ya ji kwarjininsa ya masa yawa. Sai da ya daure ya yi masa sallama tare da mika masa hannu suka yi musabaha. Bayan sun gaisa ya zubawa Zahrah idanu ba ko ƙyaftawa, sai da Hilal ya ji gaba sannan Zahra ta take masa baya. Mallam Usman ya yi gaba tare da yi wa Hilal jagora zuwa office ɗin shugaban makarantar. Da sallama suka shiga bayan sun gaisa da Hilal ne Zahrah ta gaishe shi. Bai san Fuskarta ba, amma ganin kyawon idanunta ya sa ya gane ta, murmushi ya yi tare da cewa. "Fatima Zahrah Salis Tafarki ko?" Kai ta gyada masa tare da sunkuyar da kai ƙasa. Ya sake cewa. "Yau ba niƙab ne?" Murmushi ta yi wanda har sai da dimple ɗin ta suka lotsa. Hilal ne ya lalle shi tare da cewa. "Na ji an ce gobe ne za'ayi tafiyar ko?" "Eh haka ne." "To ya tsarin naku yake?" "Eh iyayen yaran sun ba da yaran da za'ayi da su akwai motar makaranta da za'a tafi da su, akwai masauki da abinci kyauta da za'a basu. Sai dai akwai wasu iyayen yaran da ba yarda su bayar da yaransu, kamar ku kenan to ba za mu

Chapter 8 of 39