Share this page
dariya har dimple ɗin ta na lotsawa, Inna da isah fuksar kowa da farin ciki anyi nasarar ciro baby boy dake cikin Sa'adatu. Sa'adatu da baby suna barci suna hutawa, babyn ma sha Allah sai barcinsa yake kan gadon baby yana sanye da Kayan sanyi a jikinsa. _Fatima Zahrah_ Kasancewar ba ta samu barci a daren jiya ba ya saka tana isar da salla ta kwanta tana barci. Can cikin barcinta sai ta ji ana kiran sunanta a hankali ta bude idanunta ta sauke su akan na Umminta. Da sauri ta tashi zaune ganin idanun Umminta ya naɗa ya yi ja. "Ummina lafiya ?" Ba ta ba ta amsa ba ta ce. "Ki zo falo ana son ganinki." Daga nan Ummin ta fice, gaban Zahrah ya fadi, don kamar kuka ta ga Umminta na yi . Da sauri ta tashi ko sanye da hijabi da ta yi sallah ta fito babban falon gidan. Gabaɗaya ahalin gidan ne suka hadu, tana fitowa kowa ya zuba mata idanu. Kallon yayyunta ta yi Mahmud da Sadik ta ga ransu a ɓace ga Umminta ido ya yi ja. Kallon kakanninsu ta yi ta ga ita suke kallo, cikin sanyi jiki ta karasa tare da zubewar akan guiwarta. 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z Ba *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *SADAUKARWA* _Wannan shafin sadaukarwa ne ga ƙungiyar Jajirtattu writers association Alla ya ƙara mana ƙwarin guiwa fa haɗin kai_🥰🤝 Page0️⃣8️⃣ Kallon Kakanninsu ta yi ta ga ita suke kallo, cikin sanyin jiki ta ƙarasa tare da zubewar akan guiwarta. Ta kalli Kakannin nata ta ce. "Barka da safiya kun tashi lafiya?" Suka amsa mata ba yabo ba fallasa. Daga nan ta kalli iyayen nata maza ta haɗa jam'i wajen gaishe su ta ce. "Ina kwana?" Mahaifinta ya amsa amma sauran ƴan uwansa ba wanda ya amsa, ta saba da haka don kullum ba su amsa gaisuwarta sai dai idan sun ga idon Papa da Dada. Wanan karon ma Papa ya kalle su ya ce. "Ba ku ji tana gaishe ku ba ne, kullum abu ɗaya ya ƙi wucewa wa, yaushe za su haɗa kai ku so juna sai bayan mutuwsata?" Jin haka ya saka suka amsa mata da lafiya lau daga nan ta juya kallonta ga iyaye mata wanda suka share ta ba su amsa ba har sai da suka ga ɓaci ran Papa sannan suka amsa iya surukan ne suka amsa amma ita kam Aunty Laila ba ta amsa ba. Zahrah ba ta damu ba ta juya wajen Yayyun su maza da suke zaune gefe ɗaya. Bilal, Mansur, Faisal, Mahmud da Sadik. Gaishe su ta yi wanda ba su so amsawa ba idan aka cire Mahmud da Sadik. Hilal kam dama ba ita ba kowa sauran yaran gidan suka gaishe su kallo ba su ishe shi ba ko da kuwa Faisal da Maryam ne wadanda suka fito ciki ɗaya , duka yaran Abba da Umma ne to ba amsa gaisuwar su yake yi ba Sannan ta kalli gefen ƴan matan gidan Maryam, Nadiya, Nabeela da Kausar. kasancewar duk sun girme ta nan ma ta gaishe su Maryam kawai ta amsa tare da. "Lafiya lau sister." Umma kam harara ya ta gallawa ƴarta, don ta tsani halayyar ta. Gyaran Murya Papa ya yi wanda hakan ya saka kowa ya dube shi tare da kallonsa, idan aka cire Hilal wanda shi tun da ya shigo wajen bai yi wa kowa magana ba, tunda ya tsarin ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan daya yana danne-,danne a wayarsa. Duban Aunty Laila Papa ya yi tare da cewa. "Auta faɗa abinda kika faɗa mani gaban kowa." Ba tare da tuninin komai ba ta fara magana. "Dama wancan banzar yarinyar da nake faɗa maku cewa tana bin maza kuka ƙi yarda da zance na yau za ku yarda. Don na dade da sanin wannan yarinyar yawon banza kawai take zuwa da sunan makaranta." "Ki faɗi a abinda kika faɗa mana kai tsaye." "Wannan yarinyar tana zuwa ɗakin Hilal idan ga tara mazajen waje, hakan ya saka na ga ya kamata a taka mata burki na san bayan Hilal za ta iya bin wasu mazan na gidan nan don ga wasu samarin nan a gidan." Fatima Zahrah ta fashe da wani kuka mai cin rai da ƙunar zuci. Jin sharrin da ake mata . Papa ya kalle ta tare da cewa. "Kina da tabbacin cewa maza take bi a waje za ki iya rantsuwa akan haka?" "Papa me ya kawo zancen rantsuwa fa, na rassa waye zan yi wa sharri sai wannan ƴar yarinyar duk cikin yaran gidan nan." "Me zai hana idan ita kaɗai kika tsana." Dada ta yi magana tana kallon ƴarta wacce ta tsani halinta, shi ya saka ba sa shiri sai ta ce sai ba ta son ta. Kallonta mahaifinta ya ji tare da cewa. "Kina da tabbacin akan abinda kika faɗa?" "Ƙwarai kuwa da asuba kafin ayi sallar asuba na ganta tana fitowa daga ɗakin Hilal da alama nan ta kwana, sun fito tare da shi hijabinta a hannu Sautin kukan Fatima Zahrah kawai ke tashi a falon, shi kuwa gogan Hilal har yanzu yana yadda yake sai sarrafa wayar hannunsa yake yi cike da ƙwarewa. Ko a jikinsa bai nuna alamar cewa yana jin me suke faɗa ba, ko a jikinsa. "Za ki iya rantsuwa akan zargin da kike masu cewa sun yi lalata a ɗakin Hilal?" "Ba zan rantse ba amma na san tabbas wani al'amari y faru a tsakaninsu." Kallon Hilal Papa ya yi tare da cewa. 'Hilal ka sanar da mu abinda ya faru." Tsawon minti ɗaya kafin ya bude baki ya ce "Dad ku tambayi yarinyar mana,." Ya yi magana har lokacin idanunsa kan wayarsa, kamar ba shi ne ya yi yi maganar ba. Daga karshe ya ce "Ku faɗa wa ƴar ku shaidar zina wuya ne da shi ta kiyayi hakan matukar ba tana da juriyar da za ta iya jure bulala tamanin ba." Yana gama fadar haka ya tashi ya nufi upstairs ɗin. Binsa da kallo suka yi Aunty Laila ta fara masifa tana cewa "Hilal rashin mutumcin naka har ya kai haka, to ka zo ka ka yi mani bulala tamanin ɗin mara kunya." Dada ce ta janyo Zahrah ta zaunar a gabanta tana goge mata hawaye ta ce "Ki yi shiru Shalelen Dada, ki wanke ka ki ta hanayar fada mana gaskiya abinda ya faru na yarda da ke." Nan ta goge hawayenta sannan ta basu labarin komai da ya faru tun daga kan aiken da Dada ta yi mata har zuwa ɓarnar da ta masa da punishment da ya saka ta duk ta sanar har ya zuwa kasa tafiya wanda hakan ya saka ba ta da zaɓi ta kamata a wajen. Shiru falon ya ɗauka ba abinda ke tashi sai sautin kukan Zahrah. Dada ce ta janyo ta a jinkinta ta rungume ta tana rarrashinta. "Ki yi hakuri shalele na san dama sharri ne kawai aka maki." ",Ke Laila ki kiyaye ni ba za ki kaso aurenki ki dawo mani gida kina wargaza mani zuri'a ba. Akan me za ki bayar da shaidar da ba ki ta tabbacin faruwarsa, za ki bi ki tayar wa mutane da hankali ki ƙuntata rayuwar baiwar Allah Saliha na rasa me yarinyar nan ta yi maku da kuka bi kuka ɗora mata karan tsana. Kun tsane ta daga ita har sauran ƴan uwan ta da iyayenta. Na ji kokarin ganin na gyara komI amma hakan ya ci tura so kuke bakin ciki ya kashe ni?" Papa ya yi maganar idanunsa sun canza launi saboda ɓacin rai da yake fama da shi na tsawon shekaru. Ganin lokaci na tafiya ne ga yaran gidan akwai masu zuwa aiki da masu zuwa school ne ya saka Papa cewa . "Ya kamata kowa ya tashi ayi breakfast lokaci na tafiya kada su makara." Gabaɗaya kowa ya mike maza da mata zuwa wajen yin breakfast. Babban dinning table ne wanda ke zagaye da kujeru guda ashirin. Ma'aikatan gidan ne tsaye sun kai su huɗu suna jiran a basu umarnin abincin da za su zuba wa kowa." Nan kowa ya fadi abin da ransa yake so a zuba masa. Umma ce kaɗai ta kasa cin komai, don ta lura Sam huɗubar da take yi wa yaranta da alama Hilal baya ɗauka. Maganar zuci take yi tana cewa. 'Anya ba yaron nan ba ne ya ceci rayuwar yarinyar nan, duba da yadda yarinyar nan ke bayar da labarin cewa ciwonta ya tashi da alama har suma ta yi, to idan ba shi ne ya yi mata magani ba babu yadda za'ayi har ta wanke ta iya tashi har ta fita daga ɗakin sa ƙafafunta, shin ina ma ya samu maganin da ya mata amfani da shi! ? Ta sha fada masu ba ta yafe ba duk wanda ya taimaka wa Zahrah akan ciwonta, idan ya tashi sai dai su barta har numfashinta na karshe ya iso gare ta. Amma Hilal baya jin maganar ta shi ne har da yi mata magani ko, wanda nake tunanin zai iya ƙarasa ta lahira ne ya ceci rayuwarta. Dole na tashi tsaye akansa.' Jin Abba ya taba ƙafarta ne ya saka ta lalle shi tare da fara cin a abinci. Hilal ne ya fito sanye da shigar kananan kaya sa sai zuba ƙamashin turarensa mai daɗin ƙamshi yake yi . Zama ya yi tare da kallon mug ɗin da ruwan shayi ke ciki, wanda hakan ya tabbatar wa da mai aikin ruwan shayi zai sha. Zuba masa ta yi ya ɗauka ya fara sha ba tare da ya haɗa da komai ba. Suna bama cin abinci ne Papa ya lalle su ya ce. "In sha Allah ranar Asabar Fatima Zahrah za ta yi walimar saukar alƙu'ani mai girma. Don haka ranar ba aiki ba zan karbi uzuri daga wajan kowa ba dole kowa ya je wannan walimar in sha Allah." Ba wanda ya tanka a wajen ballantana su ce Allah ya sa Albarka ko su yi mata murna. Don bakin ciki ne ya bayyana a kan fuskarta . Kallon sauran ƴan matan Dada ta yi tare da cewa Nabeela da Kausar Allah ya sa ma kun iya karatun sallah, ga ƙanwar bayanku nan ta sauke kuma nan kuma sakarci uwarku ta daure maku gindi." kallon Maryam da Nadeey ta ji tare da cewa . ",Ku kuna zuwa amma kun kasa hada ko da izu goma Allah ya shirye ku." Zahara ta mike tare da cewa. "Bari na je Dada na shirya zan makara fa." "To Shalele a dawo lafiya Allah ya maki albarka." Da amin ta masa ta tashi ta nufi part ɗin su. Dada ta kalli Ummi ganin duk jinkinta a sanyaye yake ta ce "A'isha kada fa wannan abun ya dame ki." Murmushi ta aro ta yafa a fuskarta sannan ta fara kokarin yin breakfast. A can ɓangaren su Jidderh kuwa yanzu damuwarsu ta kau, ba abinda ke damunsu yanzu, tunda an yi nasarar ciro yaro a cikin Sa'adatu kuma duk suna cikin ƙoshin lafiya. Tana samun kulawa sosai daga wajan likitoci da kuma dangi. Don iyayenta ma suna zuwa asibitin sai yamma suke komawa gidan. Inna a asibitin take kwana Jidderh ke tashi da asuba ta girka masu abincin breakfast. Don kudin da Asadullah ya ba ta da shi duka siyen kayan abinci, idan ta yi shirin zuwa school sai ta dauki abincin idan ta kai asibiti daga na za ta nufi school. _Asadullah_ Saukowa yake yi daga upstair ɗin Zuwa downstairs. Da sallamarsa ciki wanda ba wanda shi kaɗai ya ji sallamar da ya yi ya ƙaraso dinning area. Gabaɗaya sun dinning table suna yin breakfast. Dady da Mom, sai Hajiya Zulaihat, Kamal Fauziyya da Suhailat. Kasancewar ba wanda ya ji sallamarsa ballantana ya amsa masa. Sanye yake cikin Suit blue black with white inner sai necktie blue white ƙamshin turarensa ne ya tabbatar masu da isowarsa. Kallon Dadynsa ya yi tare da cewa. "Gud morning Dad " "Morning my Son ka tashi lafiya?" "Alhamdulillah." Ya amsa yana mai da dubansa ga Mom ɗinsa wacce ke masa kallon kake ya yawo da hankali ko. "Mom Barka da safiya sai yanzu na ga kiranki." Taɓe baki ta yi tare da cewa . "Ka gama duk abinda za ka yi aure ba fashi sai ka yi shi anan kusa kuwa." Kallon matar mahaifinsa ya yi wacce ko kallonsu ba ta yi ba ya ce. "Hajiya ina kwana?" Hajiya Zulaihat ta kalle shi kamar ba za ta amsa ba sannan ta ce. "Lafiya." Idan ba wa da ya kalli bakinta ba ma ba za su gane Hajiya Zulaihat ta amsa gaisuwar ba. Ƴarta Suhailat ce ta gaishe shi cikin farin ciki ya amsa mata cikin kulawa tare da tamabayar ta ya school. Kamal ne ya mike tare da rike hannun Asadullah ya ce. "Big bros ƙafata ƙafarka." Nasir wanda shigowar sa kenan part ɗin ya rike ɗaya hannun Asadullah shi ma yana cewa. "Big bross ni ma ƙafata ƙafarka." Dariya suka yi in banda Hajiya Zulaihat da ta tsuke fuska. Mansur ya gaida su Dady da Mom da Hajiya Zulaihat wacce ta masa kamar dole. Asadullah ya lalle Mansur ya ce "Uncle ya tashi kuwa?" "Eh na barshi yana breakfast." Sallama suka yi duk da Mom ta so Asadullah ya yi breakfast amma ya ce zai yi a kamfani. Ɓangaren ƙanin mahaifinsa ya nufa wato Uncle Adam mahaifin Mansur ɗin. Nasir ne ya masu jagora zuwa ciki. Da sallama a bakinsu suka shiga. Duk suna zane a dinning table Uncle Adam Mami da kuma Maryam da Abida. Gaida Uncle Adam ya yi sannan ya gaida Mami, ta amsa masa cikin sakin fuska tana tamabayar sa aiki. Ya amsa da Alhamdulillah. Abida da Maryam suka taso zuwa gabansa suna gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska da walwala. Kowacce na na ƙoƙarin jan hankalinsa cikin salo Abida ta ce. "Mu da Yayanmu amma ganinsa na mana wahala sai dai a jaridu da gidan T.V ko?" Murmushi ya yi ya ce "Abida aiki suna Mani yawa ba na da lokaci sai dare wani lokacin nake dawowa kuma a gajiya." Maryam ta yi saurin cewa . "Ya ya a bamu lokaci mana a cikin satin nan mu yi fira sosai." "Ba damuwa zan duba na gani ko zuwa Friday da yamma ." Cikin jin dadi suka ce "Promise" Jinjina kai ya yi tare da yi masu sallama suka fice Kamal da Nasir suka yake masa baya. Body guard ɗin sa na tsaye ƙikam suna jiran fitowarsa, yana fitowa hana ɗaya suka karasa in da motocinsa suke. Uncle Adam ya kalli Mami ya ce . "Wai cikin yaran nan wace ce za'a bawa Asadullah??" "Maryam mana ita ce babba " "To ai ni kam Abida na ce masa amma ba matsala sai a canza da ita." Abida ta mike tsaye tana cewa. "Wallahi ban yarda ba akan meye za ku ce haka bayan kun san za'a bashi auren ne saboda kwadayin dukiyarsa, kuma Maryam ba ta da wayon da za ta kwashi dukiyarsa. Don na fi ta gohewa da wayewa da zan san banyar da zan kwaso maku dukiyarsa. Kar ku manta Yaa Asad fa ba karamin attajiri ba ne yaro ne da kuɗi. An ce fa shi kansa bai san iya adadin dukiyar da ya mallaka ba. Kamfanoni gidajen man fetur hannayen jari duk banda sauran kadarorinsa sai na mallake, kuma duk shekara sai na haihu." "Na ji ke mai wayo ko to ba zan hakura ba kuma idan kika nuna Mani bakin ciki da hassada to kin san dai wannan gidan da muke ciki gabaɗaya wanann Mansion ɗin mallakinsa ne, abaunda ake ci da sha da sutura da karatu da motoci da muke hawa duka daga cikin dukiyarsa ne ko? To wallahi kika yi wasa idan na sure shi sai na sa an kore ki daga cikin Asadullah Mansion." A fusace Abida ta yi cikinta suka kacame da dambe. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣9️⃣ A fusace Abida ta yi cikinta suka kacame da dambe. Uncle Adam mamaki ya kama yaran nasa, daga magana har da dambe akan mutumin da bai ma san suna yi ba. Mami ce ta daka masu tasowa wanda ya saka suka saki juna kowace na maida numfashi. "Wani irin hakka ne wannan shi da kuke yi akansa ya san ma kuna yi ba. Kowace ta ɓace mani da gani sai mun yi shawara da mahaifinku akan wacce za'a bashi. Don ko ma wace ce cikinku ai duk ɗaya ne idan ɗaya ta samu arziki ai tamkar ita ce ta samu, saboda kowa ce za ta mori arzikin ƴar uwarta." A'a Mamy tun da ni ce babba dole ne na fara yin aure kafin ita ta yi, kuma ni nafi dacewa da shi ba ita ba, ki daina cewa ai duk ɗaya ne domin duk shan inuwar gemu bai kai ya maƙogoro ba. Dan sai ta fara gina kanta kafin sai abin da ta ba mu sannan ki ce duk ɗaya?" Maryam ce ta cigaba da yin magana ran ta a ɓace. Nan suka fara sa'insa dakyar Uncle Adam ya shawo kan yaran nasa suka watse kowacce ta nufi ɗakinta. _Fatima Zahrah_ Fitowa ta yi sanye da riga da wando hadi da hijabi har ƙasa, hijabin fari ne yayin da riga da wando na uniform ɗin ruwan toka. Sanye da niƙab da ta ɗaura a fuskarta wanda idanunta kawai ake gani. Ko k'afarta ta saka Safa. Sanyayyen ƙamshin turaren ta ke tashi daga jikinta. Ƙarasowa ta yi tana kallonsu ta ce. "Zan tafi islamiyya sai na dawo." Ba wanda ya amsa sai Dada da Papa sai kuma yayyun Zahrah. Jin ba wanda ya amsa ne ya saka Papa ya kalle tare da cewa. "Ba ku ji ana sallamar ku ba ne?" Ya yi maganar ransa a ɓacewanda hakan ya saka dole suka amsa mata da a dawo lafiya. Girgiza kansa ya yi cikin damuwa ya bar wajen. Dada ta kalle ta tare da cewa. "Me ya saka baki son shafa kwalli, sai ki bar fuska haka nan ba kwalliya sannan saka kuwalli ma ya zama Maki wahala.? Ga idanun ki masu matukar kyau da jan hakali sai ki bar su a koɗe ba kwalli." Kallon ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ta jyi tare da cewa. "Ke Tani je ki ɗakina ki ɗauko Mani kwalli a gaban dressing mirror." Cikin girmamawa matar da aka kira da Tani ta amsa wa Dada tare da nufar ɓangaren Dada. Minti ɗaya ta dawo ɗauke da Kwalli ta zo ta kawo wa Dada . Durkusa wa Zahrah ta yi a gaban Dada, nan Dada ta zizara mata kwalli a idanunta. Sai yaba kyawun idanun take yi kafin Zahrah mike ta nufi hanyar fita don zuwa makaranta. Tana zuwa parking lot sai ɗaya daga cikin direbobin ya taso, don dama akasari shi ne yake kai ta makarantar. Har zai buɗe mata bayan motar sai ga Yaa Mansur ya fito. Wani mugun kallo ya yi wa Zahrah kafin ya kalli direban da ya bude mata bayan motar ya ce. "Kai Falalu zo ka ka kai ni wajen aiki na makara." Kallonsa Zahrah ta yi don ta san da gangan yake yi, duka mazan gidan nan suna da motoci su suke driving da kansu. Yana ji tana faɗa ta yi letti amma yana cewa a kai shi. Waige-waige ta fara yi don dama direbobin gidan su biyu ne ɗayan ya tafi garinsu ganin gida. Cikin damuwa ta kalli Ya Munsur ta ce. "Ya dan Allah ka yi hakuri tun da ga motarka nan sai ka hau, ka taimaka ka bar shi ya kai ni na makara." Wani banzan kallo ya mata kamar ba zai yi magana ba sannan ya ce. "Kin fi ni sanin da motar ne, ko ubanki Salisu ne ya siya mani motar.?" Daidai lokacin da Hilal ya fito daga ciki ya nufi motarsa, kallo ɗaya ya yi masu ya kau da kai ya shige motarsa tare da yi mata key. Maigadi ya bude buɗe massa gate ya shige ya fice. "Yaa Mansur don na roke ka akan uzurin da nake da shi kake zagin Abbi, amma kai ma ai ɗa ne a wajen sa kamar..." "Dalla rufe mani baki kafin yanzu na sauya maki kamanni, Salisu Uban Mahmud da Sadik sai ke amma ban da Ni." Da sauri ta kalle shi tana mamaki ko ba komai ai mahaifinta ƙanin mahaifinsa ne bai isa ya canza shi a matsayin kawunsa ba amma yake kiransa sunansa gatsai ba. Juyawa ta yi ta nufi bakin gate don zuwa neman abin hawa. Shi kansa Falalu direba bai so haka ba, saboda mazan gidan kowa motarsa yake hawa. Neman ya ƙuntata rayuwar ta yake so. Wani tunanin Zahrah ta yi ta dawo don ta roki ɗaya daga cikin Yayyunta su kai ta, don kafin ta karasa ta nemi abun hawa za ta ƙara makara. Da sallama ta koma cikin falon, zuwa lokacin duk sun watse Yaa Sadik ne yana kokarin komawa ciki ya ji sallamarta. Amsawa ya yi tare da cewa "Shalelen Dada lafiya ko mantuwa kika yi ?" "A'a Yaa Sadik ban yi mantuwa ba, dan Allah ka taso ka kai ni na makara." "Ina Falalu yake?" "Yana nan." "To me yasa ba ki je ya kai ki ba?" "Na je har ya bude mani motar zan shiga shi ne Yaa Mansur ya ce wai ya kai shi wajan aiki." "What, aiki fa kika ce, ina motarsa take ?" Ba ta bashi amsa ba hakan ya saka ya kalle ta tare da cewa. "Mu je." Fita ta yi daga falon ya mara mata baya, suka nufi parking space, daidai lokacin da direban ke ƙoƙarin barin wajen. Da sauri Sadik ya tari gabansa tare da yi wa Falalu alamar tsaya. Bayan Falalu ya tsayar da motar ne sai ya fito tare da cewa Sadik. "Barka da safiya yallaɓai." "Yauwa barka, ya aka yi Zahrah da ta riga fitowa daga gidan amma ba ka ɗauke ta ba, bayan ka san kowace safiya kake kai ta makaranta." "Eh ina shirin kai ta ne har na bude mata marfin motar sai ga Mansur ya fito ya ce sai na fara kai shi wajen aiki." Sadik ya karasa tare da bude murfin motar na baya in da Mansur yake zaune ya ce. "Shiga ki zauna." Wani kallo Mansur ya yi wa Sadik Sannan ya ce. "Ba ka isa ba wallahi." Ganin haka ya saka Zahrah cewa. "Yaa Sadik ka bari kawai na je na nemi abun hawa idan ba za ka kai ni ba." Ta yi maganar kamar wacce za ta yi kuka. Ba in da za ki je don neman abin hawa, kamar yadda kika ya saba kai ki zai dauke ki ya kai ki idan ya fara ajiye ki sai ya kai mo ma waye in da zai je." Mansur ya fito ransa a ɓace yana yi wa Sadik wani kallo kafin ya ce. "Ba ka isa ba wallahi me kake takama da shi ne da har za ka nemi rai na Mani wayo ko Mahmud zai yi Mani wannan iskancin ne ballantana kai?" " Yaa Mahmud ka ce idan shi zai iya ɗaukar wulakancin da kuke yi ni ba zan iya ba. Akan me za'a kai yarinya makaranta za ka hana sai ka ce kai ne ka siya motar ko kake zuba man da ake amfani da ita, Papa ne ya siya ya ke zuba mai kuma ya ɗauki direban da zai dinga kai yara makaranta wanda saboda su ne aka siya motar. Don kai yara ba saboda mu dinga zuwa aiki da ita ba. Ba ka da hujjar hana ta a kai ta makaranta sai dai ka fito ka shiga taka motar ka je aiki?" "Saboda ubanka Salisu ya siye motar?" "Ba shi ya siya ba kamar yadda kai ma ba ubanka Adamu ya siya ba?" Cikin ɓacin rai Mansur ya ce. "Mahaifin nawa kake kira gatsai haka?" "Oh ashe ba dad'i kake kiran nawa maihaifin kai tsaye, ai uba bai fi uba ba." A zafafe Mansur ya fito daga cikin motar tare da cakumar Sadik shi ma Sadik kamar jiransa yake ya kai masa naushi a baki nan da nan bakinsa ya fashe.Mansur ma ya kai masa naushi ya fasa masa baki. Suka fara dukan juna suna dambe sosai. Cikin tashin hankali Fatima Zahrah ta nufi cikin gidan aguje tana kuka. _Asadullah_ Yana cikin kamfaninsa mai suna ASADULLAH VENTURES. Yana tsaye a ofishin sa yana kai da kawo wa. Staff dake aiki a kamfanin suka ji ƙarar ringing bell. Ƙarar karaarrwar ne ya saka kowa ne ma'ikaci tunanin ko kiran me yau ake masu. Don da sun ji karar ƙararrawa sun san abu mai mahimmanci ne ya saka ake neman su. Sai suka ji magana daga cikin kowace na'ura dake cikin ko'ina na kamfanin

Chapter 5 of 39