don cin abinci ba. Don dama dokar Papa ne tare ake cin abinci a gidan gabaɗaya bayan masu aiki sun kammala yin girki.
Zahrah kasancewar a ɓangaren Dada ta kwana don haka ta shiga kitchen don hada wa kanta breakfast. Don ta ce yau fankasau take son yi.
Don haka tun da asuba bayan ta gama azkar ɗin safiya ta shiga ta gaida Papa da Dada. Kitchen ta nufa ta kwaɓa fulawa ta ɗan zuba gishiri da sugar da Baking powder ta rufe.
Sannan ta fara shirin yin miyar taushe.
_Hilal_
Yana tashi da safe ya nufi ɗakin motsa jikinsa. Kasancewar tare da Ammar suka kwana a ɗakinsa. Ammar kam yana tashi ya yi ya yi wanka bayan ya fito ne ya tsane jikinsa sannan ya shafa man shafawar Hilal ya kuma saka kayan Hilal ɗin. Turarensa ya shafa sannan ya saka takalmi ya ɗauki wayoyinsa ya sauka zuwa downstairs.
Kamar yadda Papa ya wajabta wa kowa na gidan yin breakfast a tare da juna sai dai wanda baya nan ya fita.
Duk da hakan bai saka an samu jituwa a tsakanin Abbi da mutanen gidan ba.
Gabaɗaya jama'ar gidan sun taru a dinning area. Dada da Zahrah ce ba sa Wajen. Papa, Dady, Abba, Abbi, Mummy, Umma Ummi, Aunty Laila. Haka yara mazan gidan ma Hilal ne kawai ba ya wajen amma tun daga kan Mansur, Mahmud, Faisal, Sadik duk suna wajen. Haka ƴan matan gidan ma. Nabeela, Kausar, Nadiya da Maryam duk sun hallara kowa na cin abinda ransa ke so.
Ammar ne ya karaso wajen yana tafiya cikin halittarsa ta nutsuwa da cikar kamala.
"Assalamu alaikum warahmatullah"
Ƙamshin turaren Hilal da suka ji ne sun ɗauka shi ne, amma sai suka ji saɓanin abinda suka yi zato wato sallamar da Ammar ya masu. Sabanin Hilal da idan ba wanda ya kalli fuskarsa ba ba zai san ya yi sallamar ba.
Gabaɗaya ba wanda bai san Ammar ba a cikinsu, don haka Papa da bai san cewa ya iso kasar ba yake cewa.
"A yau mutane Ingila ne a kasar ta mu?"
Murmushi Ammar ya tare da sunkuyawa cikin girmamawa ya gaida Papa, ya amsa masa cikin jin dadi tare da tambayarsa iyayensa. Ya amsa da suna lafiya. Ya sake cewa yaushe ka ƙasar ne?"
"Jiya mun shiga ɓangaren ka ba ka nan."
"Eh to haka ne gaskiya juya sai dare na dawo."
Nan ya gaida su Dady da Abba da Abbi. Suka masa masa. Sannan ya gaida su Mummy Umma da Aunty Laila. Lokacin da ya sauke idanunsa kan Ummi sai ya ga tsananin kamanninta da Zahrah kamar ta yi kaki ta ajiye. Sai ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa masa cikin sakin fuska da walwala duk da ba ta san shi ba. Don ita ba ta cika zama main falon gidan ba ballantana ta san masu shige da ficen da ke zuwa gidan. Ko fitowa cin abinci sai Papa na. nan take fitowa wani lokaci za ta yi girkin ta a kitchen dake part ɗin ta ne.
Nan su Kausar suka shiga gaida shi cikin kauɗi. Ya amsa masu ba yabo ba fallasa. Shi dai bai ga Zahra ba kuma ba halin ya tambaya. Don haka ya kalli Papa ya ce.
"Ina Dada take?"
"Dada tana can ba ta fito ba ita da Zahrah wai can za su yi breakfast."
Jin an ce ita da Zahra ya fara tunanin ganin Zahrah.
"Son zo ka zauna mu yi breakfast tare mana. Duk da an kai maku a part ɗin abokinka, amma idan ka biye masa ba yanzu za ka ci abinci ba sai rana ta fito."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Bari na je na gaida Dada."
Yana gama fadar haka ya nufi part ɗin Dada.
Da sallama a bakinsa ya shiga falon, ta amsa tare da yi masa sannu da zuwa. Tana zaune a falo ita kaɗai ta kalle shi tare da washe baki ta ce
"Ammar kai ne?"
"Eh ni ne Dada?"
Ya karasa ya gida ita cikin girmamawa. Ta amsa tare da cewa.
"Ka ga mutanen Turai."
Zama ya yi yana addu'a Allah ya sa Zahra ta fito ya ganta.
Bai gama zancen zuci ba sai ga ta ta fito daga ɗakinta ta nufi kitchen.
Tana tafiya a hankali ta nufi matattakalar stage ɗin tana sanye da wando pallazo purple colour sai shirt wanda shi ma purple ne. Wato up and down ne a jikinta.
Kanta babu ɗankwali sai gashinta da ta yi parking a tsakiyar kanta ya sauka a gadon bayanta sai lilo yake yi. powder kawai ta shafa sai lips glow pink lips ɗin ta sai shinning yake yi.
Flasks din da ta zuba fankasau ta jera a babban faranti da farfesun kayan cikin da ta yi ta jera komai ta sannan ta ɗauki don zuwa wajen Dada su yi breakfast tare.
Sanyayyaen ƙamshin turerenta ke tashi daga jikinta. Tun fitowarta yake kallonta kamar zai cinye ta. Ita ko sam ba ta lura da shi ba, tafiyarta kawai take yi cikin nutsuwa.
Ta ƙaraso ta ajiye darantin a gaban Dada, ta zauna suna fuskantar juna fuskarra ɗauke da Murmushi ta ce
"Na san yawunki ta tsinke kin Kagara ki ci girkina ko?"
Taɓe baki Dada ta yi tare da cewa.
"Ai dole yarinya kin ɗauko hannun Umminki a wajen zaƙin girki."
Mumrmushin jin dadi ta yi, jin Muryar Dada ta yi tana cewa.
"Ga Yayanki nan ba ki gaishe shi ba "
Sai da gabanta ya faɗi sakamakon ƙamshin turaren Hilal da ta ji yo, don ƙamshin girkinta ya hana ta ji ƙamshin sai yanzu.
Tura baki ta yi don ko ta gaishe shi ta san ba amsawa yake yi ba. Don haka ta share kamar ba ta ji ba. Amma sai ta juya da sauri sakamakon jin wani muryar Ammar. Idanunta ta sauke cikin nasa yana sakar mata sanyayyar murmushinsa.
Da hanzarin ta koma dakinta dake nan part ɗin. Ba jimawa ta fito sanye da hijabi iya guiwarta ya tsaya mata.
Cikin sanyin murya ta ce.
"Ina kwana?"
"Lafiya lau ya kike?"
"Alhamdulillah."
Ta furta yayin da take bude flasks ɗin funkasau. Tare ta zuba masu ita da Dada kamar yadda suka saba ci . Ta zuba masu miyar taushe da ya ji naman kan rago.
Kallonta Dada ta yi tare da cewa.
"Ki zubawa Yayanki na shi mana."
"Ba musu ta tashi ta koma kitchen ɗin ta ɗauko plate ta zo ta zuba masa. Ruwan shayin da ta dafa wanda ya ji kayan ƙamshi ta zuba na su shi ma ta zuba masa bayan ta haɗa madara da milo. Sai biredi ta jera masa a gabansa.
A hankali ya furta .
"Na gode Beauty."
"Ko ba ka ra'ayin cin wannan akwai kaloli abinci a can babban falon ka fadi abinda kake so sai a kawo maka?"
"Dada waɗan nan ma sun isa."
Daga haka ta juya wajan Dada suna cigaba da yin kalaci yayin da Ammar ke ta santin girki.
Bayan Dada ta ƙoshi ta tashi don zuwa ta yi wanka.
Ya saura daga Ammar sai Zahrah. A falon.
"Beauty."
Ɗaga kai ta yi ta kalle shi
"Me ya saka ba ki ɗauki wayata ba?"
Shiru ba ta bashi amsa ba wanda hakan ya saka shi cewa.
Ba na da lokaci gobe zan koma saboda ina da wasu zirga-zirga da zan yi. Don Allah kafin na wuce in son jin ra'ayin ki ina fatan zan samu girbi a cikin birnin zuciyarki ko tauraruwar mata."
Shiru ba ta ce komai ba, ya cigaba da cewa.
"Idan ba ki mani magana ba yanzun nan zan yi maki kuka a wajen nan."
Jin haka ya saka ta ɗaga kai ta kalle shi wai zai yi kuka kamar wani ƙaramin yaro. Ba ta san lokacin da dariya ya suɓuce mata ba har sai da dimple ta suka motsa.
Sanye yake cikin ƙananan kaya riga ja da wando ɓaki Kyakkyawar ƙiransa na mazantaka da ƙuruciya sun bayyana . Turo ƙofar ya yi tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi wanda shi kaɗai ya ji kayansa.
Idanunsa suka sauka akan Ammar da Zahrah da suke yi wa juna dariya. Wanda har sai da fararen haƙoranta suka bayyana, ga dimple ɗin ta ya lotsa sai dariya take masa. Shi ma kallonta yake yi ganin yadda take dariya daga cewa zai yi kuka.
Wani kallo Hilal ke bin su da shi fuskarsa ba sassauci. Zahrah dake facing ƙofar ta ga shigowar Hilal ɗin. Gabanta ne ya fadi sakamakon ganin fuskarsa da ya ba ta tsoro kamar wanda zai yi aman wuta.
*Ku yi hakuri da wannan*🙏🏻
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page3️⃣9️⃣
Wani kallo Hilal ke bin su da shi fuskarsa ba sassauci. Zahrah dake facing ƙofar ta ga shigowar Hilal ɗin . Gabanta ne ya fadi sakamakon ganin fuskarsa da ya ba ta tsoro kamar wanda zai yi aman wuta.
Kasancewar Ammar yana kallonta ne ya sa ya mai da hankali ga in da yake kallo. Bai damu da yanayin fuskar Hilal ɗin ba don ya san dama shi ba mutum mai fara'a ba ne.
Ƙarasowa ya yi ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon.
"Man ka shigo?"
Ya faɗa yana kallon Zahrah. Wacce ta sunkuyar da kanta tana juya zoben azurfan dake yatsarta.
"Eh na fito ya gajiyan hanya?"
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Ai ba gajiya ga mutum da ya saba zirga-zirga."
Zahrah cikin sanyin muryarta ta gaida Hilal duk da ta san ba amsawa zai yi ba. Kuma bai amsar ba.
Dada ce ta dawo falon Idanunta a kan Zahrah da ta ji tana dariya.
"Ke kuma ina ta jin Muryar ki kina dariya keke baki dariya ne.'
Kallon Ammar ta yi ta ga yana kallonta yana murmushi.
"Ko ke da Ammar ne ya saka ki dariya haka, don idan ba shi ba kam ban ga abun da zai saka ki dariya."
"Kai kuma yaushe ka shigo?"
"Bai ba ta amsa ba ya ce.
"Barka da safiya."
"Yauwa barka dai ina fatan kana lafiya ya aiki?"
Ita ma bai amsa mata ba.
Zahrah ta kasa ɗaga kai saboda tasirin da kaifin idanunsa suke yi a jikinta. Tana jin tasirin Kaifin idanunsa a cikinta.
Ɗagowa ta yi ta kalle shi sai ya galla mata harara . Sauke Idanunta ta yi sannan ta ɗauki kofin shayin dake gabanta ta fara sha.
Dada ce ta kalli Ammar ta ce.
"Wai kai yaushe za ka yi aure ne, kar dai ka biyewa wa wannan abokin na ka da ya kusa zama tuzuru."
Dariya sosai Ammar ya yi tare da cewa.
"Ba zan biye masa ba Dada, ni idan har kun amince mani ma a cikin satin nan zan angwance."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Ni kuma Ammar?"
"Ƙwarari kuwa Kakus, idan za ki bani Wannan jikar taki."
Zahrah dake shan shayi har sai da ta ƙwarewa ta yi, cikin tashin hankali Ammar ya mika mata ruwa shi da Dada sai jera mata sannu suke yi. Shi ko gogan yana hakimce kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana latsa wayansa.
Dada ce take ɗan bubbuga bayanta tana shafawa alamar rarrashi.
Bayan tarin ya lafa ne Dada ta ce
"Ammar wannan ai ba hurumina ba ne, ka nemi soyayyar Zahrah idan ta amince ni ba ni da matsala sai ka nemi Papa. Duk da ba lallai ka samu hadin kansa ba don ban san me yake nufi da Zahrah ba. Lokacin da ta ci gasar karatun Kur'ani ta da ka gabatar na san kila ka sani ko?"
"Na dai ji labarin ƴar gidan nan ce ban ma san ita ba ce."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Allah akbar ashe hafizan alƙur'arni ce, tabbas na san na zaɓawa ƴaƴana uwa ta gari."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa.
"Dada kina nufin Papa ba zai yarda ba ne?"
"Ban san ya zai karbi zancen ka ba, amma a lokacin mutane manyan ƙasar nan sun zo nemam auren Zahrah wasu ƴaƴansu suka zo nema wa auren wasu kuma kansu suka zo nema wa. Kuma manyan mutane masu daraja da ba sa da aibu. Kai har ƴaƴan Gwamnoni da minister har kan manyan Mallamai amma Kakanta ya basu haƙuri don bai ma bari sun ga Zahrah ba. Sai ya ce tana da wanda za ta aura. Sai dai gaskiya ban sani ba ko a cikin samarin ta dake sonta ne. Don da wuya ta fita ba ta yi samu wanda ya nuna yana son ta ba. Hakan ya saka take fita da niƙab ko facemask."
Jinjina kai Ammar ya yi tare da cewa.
"Hakan ya mani."
Dada ta ce.
"Gaskiya sai dai ka nemi soyayyar Zahrah idan ta amince na tabbatar Papa ba zai yi mata dole ba zai bari ta zabi son ranta ne."
Jinjina kai ya yi tare da cewa.
"In sha Allah Dadarmu zan yi yadda kika ce."
Kallon Zahrah ya yi tare da cewa.
",Yau nake son komawa dama kwana ɗaya na zo da niyyar yi. Ban san ina ne part ɗin na ku ba, ki zo ki yi Mani jagora ina son na gaida su..."
Yadda ta zaro idanu ta rike baki ne ya saka bai karasa ba ya yi dariya.
"Ina son gabatar masu da kaina ne kafin na wuce. Na san yanzu kowa ya bar dinning area .
Kallonsa ta yi wato tun bai ji ra'ayinta ba har yana shirin gabatar da kansa ga su Abbi
Shiru ta yi masa ba ta motsa ba, ya cigaba da cewa.
"Please beauty ganin mu tare zai saka su san cewa saboda ke na je gaishe su "
"Tura baki ta yi a hankali ta ce ka je saboda Allah mana."
Hilal ne kawai ya ji me ta ce saboda yana da ƙarfin ji, duk yadda aka yi magana a hankali yana ji ko gulmarsa ba'ayi yana wajen. Duk da idanunsa na kan waya amma duk maganar da suke yi yana jin su. Ammar ya kalli Hilal ya ce.
"Man kai ya kamata ma na kama ƙafa da kai babban Yaya, ka raka ni sai ka gabatar masu da kaina."
Bai tanka ba ganin haka Ammar ya ce.
"Wannan bahagon mutum ba in da zai je na ga alama tun da bai san ciwon so ba, sai dai ka ji na yi aure na barka a tuzuru don ko zancen ba ka yi."
Ganin bai tanka shi ba ya kalli Zahra ya ce.
"Beauty."
Ita kunya ce ma ya bata tana don tashi ta bar wajen ta kasa.
",Bana da isasshen lokaci Please ko ba za ku shiga ba ki tsaya daga main falo ki nuna mani zan shiga ni kaɗai."
Ganin ko motsi ba ta yi ba Dada ta ce.
"Ba na son gulma ba tun ina ciki nake jiyo Muryarki kina ta masa dariya ba kuma
Fira. Yanzu ki nuna masa waje ne kike wani ñoƙe-noƙe?"
Tashi ya yi ya yi gaba ita ma ta mike za ta bi bayansa. Tana kawowa saitin kujerar da Hilal ke zaune ya sanya ƙafarsa ya harɗe mata ƙafa ta faɗi ƙasa. Ƙara ta saki ya sa yatsarsa ya ɗalle mata baki ta saka kuka."
Dada ta ɗauka faɗuwa ce ta yi sai salati take yi tare da tambayarta garin ya ta fadi haka. Ammar ne ya yi wa Hilal wani kallon mamaki don ya ga sanda ya harɗe ta sannan ya bugar mata baki. Sai dai bai san me ya saka ya yi mata haka ba ko ta masa wani laifi ne. Duk da ko da laifin ta yi masa ya dace ya hukunta ta irin wannan faduwar idan ya zo da tsautsayi za ta iya karyewa.
*Prison/Gidan yaro*
Gabaɗaya ya kasa zaune ya kasa tsaye. Sai zirga-zirga yake yi a ɗakin. Ya rasa me yake masa daɗi. Ya so ya haɗa hannu da ɗan ta'addan dake cikin gidan yari. Sanin hakan ba zai amfane shi da komai ba ne ya saka ya fita harkarsa.
Wayarsa dake kan gadon ya ɗauka, tare da lalubo wata lamba ya danna kira.
Bugu ɗaya aka ɗaga.
"Ka zo."
Shi ne iya abinda ya ce sannan ya katse kiran wayar ya ajiye.
Ba'a fi mintuna biyar ba sai ga wani ma'ikacin gidan yarin ya shigo.
"Tura mani account number ka?"
Take mutumin ya faɗa masa in da ta yi masa transfer na kuɗi.
"Ina son a kawo mani katon ɗin ruwa don ruwan sha na sun ƙare. Ina son sabulu da omo da dai abubuwan da ka siyo Mani last time. Sauran canjin sai ka rike."
Godiya mutumin ya yi masa tare da yi masa addu'a.
_Jidderh_
Bayan ta shirya zuwa wajen aiki ta biya ta wajen Yayanta dan su karasa maganar da suka yi da shi.
Bayan ta yi sallama a kofar ɗakin ya ba ta izinin shiga ne ta shiga.
Yana zaune a bakin gado ta gaishe shi. Ya amsa tare da cewa.
"Har kin fito za ki wuce aikin kenan?"
"Eh Yaya dama ina son ne na ji ya ka ji shawara da na kawo?"
"Ban ƙi ta ki ba Jidderh kamar yadda kika ce za ki Sanarwa amintaccen bodyguard ɗin sa in da aka tsare shi a cikin gidan kina ganin ba zai iya yiwuwa da shi aka haɗa baki ba?"
Shiru ta yi tana nazari kafin ta ce
"Na san zai ya aminta da shi kuma shi ne wanda kai tsaye yake iya shiga duk in da yake a cikin gidan."
"Idan da hadin bakinsa a ciki kika tunkare sa da zancen fa za ki saka kanki a matsala ne?"
"To sai dai idan jami'an tsaro zan fadawa zancen."
"Tab kina ganin jami'an tsaro za su iya shiga cikin irin wannan gidan ne kai tsaye su fara bincike ba tare da sun nemi izinin mai gidan ba ko sun sanar da su shi abinda ke tafe da su?"
Shiru ta yi cikin ɓacin rai ta ce.
"To ya kake so na yi wallahi ba zan iya barinsa cikin wannan halin ba."
"Kuma duk hanyar da kike ɗaukowa ba mai ɓullewa ba ce."
Ganin duk sanda ta kawo shawara kowace iri ce baya bata goyon baya ya saka ta tashi tana tuninin hanyar da za ta bi."
Rai a jagule ta nufi ƙofar fita ko sallama ba ta yi wa mutanen gidan ba.
Keke napep ta tare ta shiga mutane biyu ne a ciki ita ce ta ukun su.
Sai da aka sauke su ya kai ta har ƙofar gate ɗin *Asadullah mansion* ɗin tana sauka ta biya mai napep kuɗinsa ta nufi gate ɗin. Security na ganinta suka bude mata gate ta shiga.
Kai tsaye main house din ta nufa. Mummy ta tarar a Falo, ta gaishe ta ta amsa mata ba yabo ba fallasa.
Shiga ciki ta yi don gudanar da aikinta. Don sauran ma'aikatan gidan nan suke kwana ita kadai ce take zuwa daga waje. Da Mom ta nuna in dai zata dinga fita za'a sallame ta, Asadullah ne ya tsaya akan cewa a barta sannan Mom ta bar ta.
Jidderh ta juya ta kallo Mom kamar ta sanar da ita cewa ga in da Asadullahi yake sai ta fasa sakamakon ta tuna Mama mai aiki ta taɓa sanar da ita cewar Mahaifiyar Asadullah ta rasu. Hakan ya durƙusar da yinƙirinta. Don a wannan gabar ba ta son ta aikata abinda zai iya janyo wa Asadullah ya shiga wani hali.
Sai dai yadda gidan nan ke da matakan tsaro ta ya ya za ta iya fitar da shi ba tare de kowa ya ganta ba. Ga shi baya cikin hayyacinsa ballantana ta ji ta bakinsa ya bata mafita.
Abun da Jidderh ba ta sani ba shi ne an daina yi wa Asadullah alluran gusar da hankali da magunguna da za su yi masa illah. Saboda yanzu an zo gabar da suke so.
A hanzarce ta gama ayyukan da take yi sannan ta fara tunanin hanyar bi wajen da za ta je ɓangaren da aka ajiye Asadullah.
Har za ta bi ta ƙofar kitchen ta fice sai ta ji Muryar Hajiya Zulaihat wacce suke kira Aunty ta ce.
"Ke ina za ki je kike wani sanɗa?"
A firgice ta juyo don ta tsorata jikinta har rawa yake yi .
"Kallo ɗaya ta yi mata ta fahimci ba ta da gaskiya. Don haka ta sake tamabayarta a karo na biyu.
"Amm uhm amm zan je wajen Mama ne na taya ta aiki?"
"Wace Mama? Mama da ta gama aikinta ta fita kitchen."
Dawowa ta yi tana sunkuyar da kai ta nufi ɗakin masu aikin gidan.
Da kallo Aunty ta bita kafin ta ce .
"Zan gano ki ne yarinya."
Bayan kamar mintuna talatin ne ta sake fitowa cikin ikon Allah har ta bar sashen na wamdabya ganta.
Ta baya ta zagaya har ta isa bangaren da aka ajiye Asadullah.
Sai dai ƙofar a datse. Glass din window ta zuge sai suka hada idanu. Gabanta ta ji ya fadi rass.
Ganin kallon da yake yi mata. Don duk ganin da take masa cikin wani yanayi yake amma yau ga shi zaune yana kallonta sai dai an daure masa hannaye da ƙafa suka an rufe masa baki da salatef.
Ƙwalla ne suka cika Idanunta har suka gangaro. Ga mamakinta sai ta ga yana girgiza mata kai alamar ta daina kuka.
"Yallaɓai kana ji na kana gani na?"
Kai ya jinjina mata alamar eh. Farin ciki ya saka ta saki murmushi tana goge hawayen dake Idanunta.
"Yallaɓai ta ya zan iya fitar da kai ko na je na sanar da Mom kana nan?"
Kai ya girgiza mata alamar
"Aunty fa na sanar da ita?"
Nan ma kai ya girgiza mata alamar a'a.
"Na sanar wa Dad?"
Nan ma kai ya girgiza.
"Na sanar da amintaccen bodyguard ɗin ka?"
Sai a lokacin ya ɗaga mata kai alamar eh. A guje ta bar wajen tana murmushin jin dad'i.
Tana tsaka da gudu ta ji an finciko mata hijabi ta baya wanda har ya shaƙe mata wuya. Kafin ta ankare sai ta ji ta faɗi ƙasa tim.
Rai a ɓace Ammar ya kalli Hilal da ya tabbatar shi ya harɗe ƙafar Zahrah ta faɗi. Haba Man don Allah me ..."
Ɗaga masa hannu ya yi alamar dakatarwa. Dada da a tunaninta Zahra Faɗuwa ta yi ne ta kama ta daƙyar, ta iya tashi ga ƙafarsa zafi ga kabbnta da ya ɗilla da yatsarsa sai zugi suke mata.
Hawaye ne kawai take tsiyayarwa, don ita kanta ba ta san me ya yarda ita ba ta ɗauka ko da plate dake gabanta ta yi tuntuɓe. Sai dai lokacin da ta ji zafi a bakinta ta ga abinda Hilal ya mata sai ta danganta hakan da ihun da ta yi ne kasancewar baya son hayaniya.
Kuma ya saba cin uban duk yaran gidan idan sun yi hayaniya a in da yake. Hakan ya saka in dai yana wuri kowa ke kama kansa ya shiga tausayinsa. Don haka Zahra ta ta ga ya dakar mata baki ta ɗauka karar ihun ne baya so ba ta san shi ya harɗe ta da ƙafarsa ya yarda ita ba, don Idanunta na kan Ammar.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page4️⃣0️⃣
Kuma ya saba cin uban duk yaran gidan idan sun yi hayaniya a in da yake. Hakan ya saka in dai yana wuri kowa ke kama kansa ya shiga taitayinsa. Don haka Zahrah da ta ga ya dakar mata baki ta ɗauka karar ihun ne baya so ba t san shi ya harɗe ta d ƙafarsa ya yarda ita ba, don Idanunta na kan Ammar.
Hawaye ne ke bin fuskarta yana gangarawa wajen ƙunnenta.
Taisayin ta ya saka Ammar ƙarasowa wajen ya kai hannu zai taimaka mata ya ji Muryar Hilal na cewa.
"Kada ka taɓa ta tun da ba Muharramarka ba ce."
Jin haka ya saka Ammar janye hannunsa rai a ɓace. Dada ce ta taimaka mata ta miƙe tana ɗingisa ƙafar suka shiga ciki. Dada sai jera mata sannu take ta yi.
Ammar ya kalle shi fuska babu walwala ya ce.
"Man me hakan ke nufi, idan ta karye ko ta yi targaɗe ko gocewar ƙashi fa? Ko da ta yi maka laifi ya kamata ka hukunta ta ne ta hanyar faɗa, ko duka ma yanzu ba kowane laifi ta yi za'a ce ayi mata duka ba, don ba yarinya ba ce ƙarama ta san me take yi."
Ko kallonsa bai yi ba idanunsa akan wayarsa kamar bai yi komai ba.
"Ga shi ina son na gabatar da kaina a wajan iyayenta kafin na koma London ga shi ka ɓata mani komai."
Ganin bai yi magana ba ne ya saka shi sake cewa.
"Yauwa sai ka raka ni mu je tare kai za ka yi mani jagora babban Yaya."
Wani kallon ba ka da hankali ya yi masa sannan ya tashi ya bar part ɗin.
Har ya kai bakin kofa ya ce.
"Zan fita yin wani aiki me yiwuwa na kai yamma kafin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 39