Share this page
ya wulla lahira ko?" Kamal ya fadi maganar ya yin da ya mike yana kakkabe rigarsa. Sagir ne ya sunkuya ya kai hannunsa daidai saitin hancin Asadullah. Jin baya numfashi ne ya kalli Kamal tare da cewa. "Mun gama da shi, ka yi sauri mu bar wajen nan kada wani ya biyo ya tarar da mu." "To ya za mu yi da gawar?" Kamal ya tambaya cikin yanayin damuwa kamar zai yi kuka? "Ka yi hauka ne, ta ya ya zamu dauki gawar mu ce me?" Sagir ya bashi amsa yana hararar shi. "To ya za ka yi na san dole guard ɗin sa sun ga fitarku dole za'a tuhume ka." "Shi ya sa na ce maka kuɗaɗen nan za su ishe ni na bar ƙasar nan zuwa wata ƙasar na gina sabuwar rayuwa. Don haka za mu rabu a nan. Yanzu sauran aiki ya rage naka idan ka iya allonka ka wanke." Cikin damuwa Kamal ya ce yanzu wata ƙasar za ka tafi. Sai da ya bude murfin motarsa zai shiga sannan ya ce. "Ba zan iya fada maka in da zan tafi ba, domin hakan na iya zama hatsari a gare ni, na gode da taimakonka. Sai dai ka yi gaggawar barin wajen nan kada bincike ya biyo ta kanka. Hakan zai iya shafar siyasarka." Dawo wa ya yi ya ya ɗauke manya-manyan wuƙaken da suka soke su da shi yana cewa wannan ma hujja ce ba zan barta ba." Yana gama fadar haka ya shige motarsa ya bar wajen a guje. Cikin tashin hankali da Fargaba shi ma ya shiga motarsa ya bar wajen. Bayan mintuna biyar da barinsa wajen dai ga guard ɗin Asadullah sun ƙaraso wajen sakamakon hanyar da suka bi ba su ga alamar su hanyar ba. Burki suka ja da karfi suka fito a guje zuwa in da yake kwance. Baya motsi ga shi kwance cikin jini. Cikin tashin hankali suka ɗauke shi zuwa asibiti baya numfashi. Tsawon sati ɗaya bai farfaɗo ba, sai dai likitoci sun dukafa akansa. Sai dai sun tabbatar yana raye zai iya farfaɗo wa a kowane lokaci. Ga shi abokinsa da aka ce sun fita tare da Asad kafin aka tsince shi ba wanda ya san in da abokin yake ba. Ganin halin da yake ciki ne ya saka Dad da Uncle Adam suka matsa akan a fitar da shi ƙasar waje. Ba tare da ɓata lokaci ba aka shirya komai aka ɗauke shi zuwa ƙasar India. Dad, Mom, da uncle Adam suka tafi tare da shi. Cikin ikon Allah washegarin ranar da aka kai shi ya dawo cikin hayyacinsa. A ranar da ya dawo cikin hayyacinsa. A ranar Uncle Adam ya koma Nigeria. Mom da Dad suke tare da shi. Duk da ba zama wajensa suke yi ba kasancewar ma'aikatan asibitin ne ke kula da shi. Mom da Dad a hotel suke kwana washegari su dawo nan asibiti. Bayan sati biyu aka sallame su ya warware garau. Har lokacin ba wanda ya tambaye shi wanda ya yi masa wannan aika-aikar. Ganin yanayin da yake ciki kamar wanda ke cikin ruɗani. A ranar ne suka dawo ƙasar 9ja cikin farin ciki da annuri. Dad ya dinga kiran wayar Kamal don ya kira shi ya zo ya ɗauke su amma wayar a kashe take. Don haka ya kira Uncle Adam ya sanar da shi, Uncle Adam ba ya gari don haka ya kira ɗan sa Nasir ya sanar da shi. Take ya ɗauki key ɗin mota yana sanar da Mami in da zai je. Ganin haka ya saka Abida ta mike zurun za ta bishi. Maryam ma haka ta je za ta je ta tarbo masoyinta. Dakatar da su ya yi tare da cewa da mutum ɗaya zai tafi, sai ya yanke shawarar zuwa da Abida kasancewar ita ta fara yin magana. Maryam ya ce ta yi hakuri ta tarebe shi a gida. Ba da son ranta ba ta hakura Abida ta bishi cikin rawar jiki. Cike da farin ciki suka fita daga cikin ASADULLAH MANSION ɗin. Bayan sun ɗauko su akan hanyarsu ta dawowa ne Dad ke tambayar Nasir in da Kamal yake don wayarsa ba ta shiga. Ya ce juya dai sun ga juna da safe amma yau bai saka Kamal a idanunsa ba kenan. Mummy ta ce. "Ko yana kamfani ne tun da shi ke kula da kamfanonin ɗan uwansa." Ba mai Wannan amsar don haka suka yi shiru aka koma gida. Kowa ya ga Canji a wajen Asadullah don ko magana ba ya son yi. Wannan murmushi da ya saba yi a cikin ƴan uwansa duk babu ga kowa ya taru har da uncle Adam da iyalansa bangaren Dad ma kowa na nan hatta Hajiya Zulaihat wacce suke kira da Aunty ta zo duk da kasancewar ba ta shiga lamarin mutanen gidan musamman Asadullah. Har da ƴarta Suhailat sun zo. Wanka kawai Asadullah ya yi ya sanya riga JC da wando ya fito zuwa falon. Nan ya same su Dad ya tamabaye shi abinda ya faru da shi su waye suka so kashe shi. Nan ya basu labarin komai tun kiran da Sagir ya masa akan cewa Kamal na cikin mawuyacin hali har soka masa wukan da suka yi. Sai dai ya ce bayan Kamal ya soke shi ta gaba ya ji wani sukan ta baya ko da ya juyo bai iya gane ko waye ba, sai dai yana zargin Sagir ne, dan duk da yana kwance cikin jini yana jiyo maganganun da suke yi har sanda Sagir ya kai hannu sautin hancinsa don ya ji ko yana numfashi. Hakan ya saka ya ɗauke mumfanin na wasu daƙiƙu yadda za su yi zargin cewa Mutuwa ya yi. Har zuwa ɗaukar sa da guard ɗin sa suka yi ya sani akan hanyar zuwa asibiti ne bai sake sanin in da kansa yake ba sai da ya tsinci kansa a kasar India. Gabaɗaya firgici da tashin hankali ne ya ziyarci jama'ar wajen. Salati kawai suke yi yayin da ƴan matan ke kuka. Mum ce ta ɗauki wayarata ta kira jami'an tsaro akan su nemo Kamal duk in da yake a fadin garin nan. Kasancewar Kamla sanannen mutum ne kasancewarsa yana siyasa. Kuka Mom ke yi tana alwadai da halin ɗan nata. Tare da cewa sai ya girbi abun da ya shuka daga shi har abokin na sa. Uncle Adam ne ya tambaye Asad cewa wani abu ya taba shiga tsakaninsa da ɗan uwan nasa ne ko abokinsa. Nan ya sanar da su miliyoyin kuɗaɗen da suke diba daga kamfanin, wanda sanadiyar haka ya masu gargaɗi ba su daina ba ya dakatar da su. Nan aka dinga alwadai da halin na su musamman Kamal da suke uba ɗaya Asadullah a ce ya masa haka. A ranar aka kama Kama yana ƙoƙarin barin ƙasar a filin jirgin sama aka kama shi. Bayan jami'an tsaro sun tura su kotu an taru ana tuhumar Kamal akam laifin da ya aikata amma ya ce sam bai aikata abin da ake zargin sa da shi ba. An tambaye shi in da Sagir yake ya ce bai sani ba. alkali ya bayar da hutun Sa'a ɗaya kafin a cigaba da shari'ar. Nan ya nemi ganin Dad da iyalansa suka hadu a keɓance kasancewar Alkalin ma abokin Dad ne. Bayan sun haɗu Mom, Dad, uncle Adam, Aunty, Asadullah da Kamal. Kallonsu alkalin ya yi tare da yin gyara murya. "Hakika ban ji dadin yadda wannan lamarin ya kasance ba, Kamal ka amsa laifinka ba tare da ka wahalar da shari'a ba, yanayin da kake ciki ya isa ya tabbatar ba ka da gaskiya, an yi magana ka ce a kawo hujja saboda ka san kun binne duk wata hujja da za'a gane ku ko? To fa ka sani ina da hanyoyi da yawa da zan gane abun da kuke binnewa. Me ɗan uwanka ya yi maka haka?" Ya yi maganar yana kallon Asadullah wanda idanunsa suka yi jajir saboda tashin hankali. Kafin ya cigaba da cewa. "Ka masa laifinka zan maka sassauci a wurin Shari'a. Kasancewar wanda kuka yi yunkurin kashewa bai mutu ba yana nan da ransa. Ka ga ba hukuncin kisa zan yake maka ba ko?" Sai a lokacin Asadullah ya yi magana ya ce. "Ba zai taɓa fada ba yallaɓai, zaman gidan gyaran hali ne ya dace da shi kafin ya girbi abinda ya shuka. Butulu maci amana." Duk yadda aka kaɗa aka raya bai amsa laifinsa ba, kuma ya ki fadar in da Sagir yake. Tsabar ɓacin rai ya saka Mom ta shi ta wanke shi da mari tare da kai masa duka ta ko ina, sai da Uncle Adam ya ƙwace shi. Bayan awa ɗaya aka koma zaman Shari'a nan ma babu wani cigaba da aka samu. Daga nan Alkali ya bada umarnin akai Kamal gidan yari ajiyarsa za'ayi kafin a kamo Sagir a yanke masu hukunci daidai da abinda suka aikata. Daga nan ne Ka dauki Kamal aka kai shi gidan yari aka ajiye shi. Kallon Asadullah mutumin ya yi ba tare da ya cire facemask din ba ya kalli Asadullah dake cike da mamaki ya ce. "Duk da yana gidan yari amma ya fi ka rayuwar jin dad'i. Kalli yadda kake a kulle a daki kuma daure da sarƙa. Sai an baka abinci ko wane iri ne dole ka ci." Yana gama fadar haka ya fice ya bar Asadullah yana binsa da kallo. Har lokacin yana daure da sarƙa a hannunsa. Yana kai wa bakin ƙofa ya ya juyo yana cewa. "Ka san me ya janyo naka haka?" Murmushi ya yi sannan ya ce. "Yarda da mutane, da ba don lokaci ya kure maka ba da na baka shawarar cewa ka rage yarda da mutane, domin wani lokacin wadanda ka yarda da su sune za su iya cutar da kai." Yana gama fadar haka ya fice ya ja masa kofar ya rufe. _Ummi_ Tana fita daga part ɗin su ta nufo Babban falon gidan ta ga Hilal zaune yana danne-danne a system ɗinsa. Rai a ɓaci ta kalle shi ta tuna yadda Zahrah take kuka da kumburin da fuskarta ta yi sakamakon marukan da ya dinga sabga mata. Domin Ita uwa ce. "Hilal!" Ta kira sunansa rai a ɓace, ɗaga kai ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa ba. "Me Zahra ta yi maka da ka yi mata wannan dukar haka, to tura ta fara kai wa bango. Ba wannan ba ne karo na farko da ka fara dukan ta, ka sha azabtar mun ca yarinya da duka ko punishment har sumewa ta yi a dalilin ukubarka. Sannan duka da haka bai ishe ka ba saboda na kawar da kai ban taɓa nuna ɓacin rai akan abinda ake mata ba wai hakan na nufin ba na ƙaunar ƴata ba ne, kawaici nake yi maku amma tun da ba ku gane wa na gaji ya isa haka nan kada ka sake taɓa lafiyar Zahrah." Tana faɗin haka ya nufi part ɗin Papa bin ta ya yi da idanu, ita ma ba ta saka ran zai amsa mata ba duk da ta san ya ji ta sarai. Sai dai ya san cewa an ƙure ta ne don shi kansa shaida ne akan ƙiyayyar da ke yi wa Ummi da ƴaƴanta musamman Zahrah sun fi tsanar ta amma hakan bai saka Ummi ta nuna ɓacin rai ba sai yau. "Ni dai ba zan taɓa zuba idanu na bar ɗaya daga cikin ahalin gidan nan su yi duk abinda suka ga dama ba. Musamman Zahra dake da masoya ga shi yanzu har ta fara zubar da ciki, sannan a ce na ƙyale ta?" Ya faɗa yana girgiza kai tare da sarrafa na'urar dake gabansa. Wani tsanar Zahrah ne sabo ya dirar masa. "Zan yi maganin ƴar iskar yarinyar nan, ƙura ce ita lulluɓa da fatar akuya." *Maman Ihsan ce*✍️ da 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page3️⃣5️⃣ "Zan yi maganin ƴar iskar yarinyar nan, kura ce lulluɓe da fatar akuya. Da sallama Ummi ta ƙarasa part ɗin Papa. Dada ce a falo tana zuba kwadon zogale cikin bowl. Ta amsa sallamar tare da kallon Ummi ta ce. "Zahrah ne na ga kin zo da kanku?" Ta tambaye ne kasancewar ta san idan Ummi ta shigo da safe ta gaishe su ko wani abu ne sai dai ta aiko Zahra. Murmushi Ummi ta yi tare da cewa. "Wannan zuwan na wa ne Dada." Ajiye bowl ɗin da ta zuba zogale ta yi tare da cewa. "Tun da kin shigo shiga kitchen ki ɗauko plate ki zuba zogale, wancan mai murɗaɗɗen halin ke saka Ni yi masa zogalen nan, ga uwarsa ga masu aiki ya ce ba zai saka su ba na wa yake so." Gajeren murmushi Ummi ta yi don ta gane cewa Hilal Dada ke nufi tun da ta ce mai murɗaɗɗen halin. "Dada na gode ba zan ci zogale ba, wajen Papa na zo." Tana rufe baki sai ga Papa ya fito daga ɗakinsa. Ya kalli Ummi ya ce. "A'isha ke ce?" Ya yi magana yana gyara zaman medical glass dake saman karan hancinsa. "Eh ni ce." Ta fada kanta a sunkuye yayin da ta zube a saman guiwarta kamar mai rokon gafara. Zama Papa ya yi yana fuskantar ta ya ce. "A'isha lafiya dai ko?" Hawaye da ya taru a idanunta ta goge. "Papa wata alfarma nake nema a wajen ka, duk da na san abu ne mai matukar wahala a gare ka, amma dole na tamabaye ka shi don idan ba haka ba wata rana za'a wayi gari bakin ciki ya kashe ni." "Subhanallah me ya yi zafi haka?" Murmushin takaici ta yi tare da cewa. "Papa ina neman alfarma don Allah ka bar mu mu tashi daga gidan nan, mu nemi wani gidan mu zauna ni da yarana, ko ba komai za ku yi rayuwar farin ciki a cikin gidanmu." Shiru ya yi tare da yin nazarin kalamanta don tabbas ya san irin zaman da take yi a cikin gidan. Yadda ta zama sanayar ware a cikin matan gidan. Duk da ya so a ce ta ƙara hakuri na wani lokacin. "A'isha me kike son cewa ne?" "Sama da shekaru ashirin ina zaune a cikin gidan nan, duk da wariya da ƙiyayyar da ake nuna mani haka na kawar da kai. Sakamakon hakuri da juriya da na ga mijina na yi na zama da ƴan uwansa. Ni ma na ɗora wannan aniyar. Zuwa gaba bayan ba fara haihuwa na fahimci tsanar da ake mana ya shafi yaran da muka haifa. A lokacin hankali na ya tashi amma ganin ba zaman kowa nake yi a cikinsu ba, kuma ina samun kulawa daga wajan mijina da iyayensa ya sa na watsar da lamarin kowa na cigaba da mu'amalantar kowa duk da ko na masu magana ba sa amsawa ƴaƴansu ba sa mu'amala da ƴaƴana ban nuna damuwa ba na mayar da hankali wajen tarbiyyar yarana da cusa masu aƙida mai kyau a cikin zuciyarsu, ban koya masu tsanar danginsu ko ƴaƴan cikin gidan ba. Amma na lura sun fi tsanar Zahrah fiye da tsanar da suke muna da sauran ƴan uwanta. Na rasa me ta yi masu a rayuwa sun cusawa ƴaƴansu tsanar ƴaƴana kamar ba jini ɗaya suke ba. To yanzu har ya kai a yi wa Zahra ƙazafin zubar da ciki sannan ayi mata duka har da kumbura mata jiki, gaskiya hakurina ya fara ƙarewa ba zan iya ba." Shiru Papa ya yi na wani lokacin daga shi har Dada kowa ya kasa magana. Don sun san tsananin hakuri da kawaici irin na Ammi tun fa ta fara kawo ƙorafi tura ce ta kai bango. "Aisha." Papa ya kira sunanta. A hankali ta ɗago kai ta kalle shi cikin sanyin murya ta ce. "Na'am Papa." "Mijinki ya dade yana burin barin gidan nan saboda halin da ƴan uwansa ke nuna masa. Ni ne na hana shi tashi sakamakon ina ganin ni ne Ummul aba'isin wadan nan abubuwa dake faruwa a cikin zuri'ta gabaɗaya. Yanzu dai don Allah ina rokonki wannan karon in sha Allah za ki ga abinda zan yi. Ki ƙara hakuri in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe." Ya faɗa yana jinjina mata kai alamar tabbatar wa. Godiya ta yi masa sannan ta yi masu sallama za ta bar part ɗin. Har ta dawo babban falon gidan Hilal na nan in da ta bar shi. Tana wuce wa ya tashi ya shiga ɓangaren su Papa. Ciki-ciki ya yi sallama wanda shi kaɗai ya ji kayansa, don su ba wanda ya ji sallamarsa ballantana su amsa masa. Kuma shi ma bai sake yin magana ba, ƙarasa wa ya yi gaban Centre table ya dauki bowl ɗin da Dada ya haɗa masa kwaɗon zogale. Bai yi magana ba saboda ya san shi ta haɗawa. Har ya kai bakin ƙaofa ya ji Muryar Dada tana cewa. "Kai kam matarka tana da aiki mutum sai bakin hali. To uwarka ce ta dafa maka zogalen da za ka ɗauka babu sannu da aiki ballantana ka yi Mani godiya ko? To ƙaniyar gobe, don ba za ka saka ni aiki na yi ba." Ya juyo ya kalle ta dai ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba. Kallon Papa ta yi tare da cewa. "Kana ganin wannan yaron jikan naka abun da yake mani ko? Ba za'a taɓa yi masa abu ya nuna ya ji dadi ba, kuma an alhalin abin da yake so ne aka yi masa shi, amma jin kai da mishkilanci irin nasa ba zai nuna ba. Yo ba don shi ba kaf jikokin gidan nan idan aka cire Zahrah ai ba wanda zan yi wa bauta. Don ba zai yiwa na yi wa ubansa shi ma na masa ba, sai dai shi ba zan iya ba." Papa kallonta ya yi yana murmushi don ya san irin son da take yi wa Hilal da Zahrah na daban ne a zuciyarta. Kamar yadda shi ma haka yake jin su a ransa. Gara Zahrah tana yawan shigewa Kakannin nata har kwana ɓangaren su tana yi wasu Kayanta ma suna ɓangaren kamannin na su ne sai in da ta ga dama za ta ci ta sha ko ta kwana. Duk da akasari ta fi kwana a bangaren Umminta. *Bayan sati ɗaya* Zahra ta warke ta warware ta cigaba da sabgarta. Kuma har lokacin ba ta sake saka Hilal a Idanunta ba. Don ko zuwa part ɗin Dada ba ta yi ballantana ta hadu da shi. Ranar Ummi ta gama abincin rana ta aiki Zahra ta kai wa Dada. Duk da kasancewar suna da masu aikin girki a gidan da suke abinci gabaɗaya amma Ummi ta kan yi abin Marmari da ta san tana so kitchen ɗin ta da ke part ɗin ta. Ɗanwake ta yi ta san Dada na so ta zuba don a kai mata. Zahara ta ɗauki abincin ta nufi part ɗin Dada don kai mata. Bayan ta kai mata ne ta samu tana aiki a kitchen tana dafa zogale, ganin Zahra ta zo sai ta saka ta daka mata yajin ƙuli. Bayan ta gama daka mata ta zubawa Zahra na ta ta zuba wani a wani bowl ta zuba yajin ƙuli da yanka su tumatir da albasa. Ya Mika wa Zahrah ta yi tare da cewa. "Kar bi ki kai wa Yayanku wannan a ɓangarensa." Rass gabanta ya faɗi. Ƙasa amsa ta yi ta tsaya tana kallon bowl ɗin. "Karbi mana ki je ki dawo ga naki." Tura baki ta yi tare da cewa. "Da ban shigo ba waye zai kai masa?" "To kin san ina da ciwon ƙafa ba iya hawa bene nake yi ba, kuma sauran yaran ba sa shigowa saboda wai ke nake so ba na son su duk da na san hudubar iyayensu ne saboda sun san kina zama a nan wajena. Dama shi ne idan ya shigo ya dauka amma tun da ga ki ba wanda zan aika don ya hana masu aiki zuwa part ɗin sa ballantana na aika su kai masa." "To ki jira ya zo ya ɗauka, ba zan je ya ci zalina ba tunda shi mugu ne ba imani a zuciyarsa." Mumrmushi Dada ta yi tare da cewa. "Tun da ba mahaukaci ba ne shi ai ba zai dake ki haka kawai ba." "Ni fa ba zan je part ɗin nan ba." "Ku ji mani ja'irar yarinya ko ubanki Salisu na aika bai isa ya faɗa Mani haka ba, ballantana uwarki A'isha." Ganin ida idanunta ya ciko da ƙwalla ta ce. "Ki yi hakuri je ki dawo ƴar albarka kin ji, ba na son kina ɓata rai je ki dawo in ba ki labari mai daɗi tatsoniya zan maki." Sanin Zahrah na son tatsuniya idan tana ba ta ta yi ta dariya ya saka ta ce haka. Nan da nan ta amsa har tana murmushi. _Hilal_ Yana komawa part ɗin sa ya tarar Alexandra ta kammala haɗa kayanta a trolley bag ɗin ta. Don yau za ta koma ƙasar US. Duk da burinta bai cika akan Hilal ba, don har yanzu sai dai ya yi romancing ɗin ta bai taɓa gigin yin sex da ita ba. Duk iya hanyoyin da za ta bi don ta ja hankalinsa ya kai in da take so ya kai ta kasa. Da sun yi zurfi wajen wasannin su da juna ya fahimci yana neman wuce iyaka take zai raba ta da jikinsa ya je ya sakarwa kansa ruwa. Wata rana ma sai ya sha magani. Ita mamakinsa take yi yadda zai ce ba zai yi sex da ita ba amma zai yi wasa da ita son ransa ya kuma sarrafa ta yadda ransa yake so. Kamar dai yadda ta ji labarinsa a wajen wasu ƴan matan da suke cewa shi ne kaɗai namijin da suka ga zai yi wasa da mace son ransa duk yadda ta so ya yi sex da ita ba ya yi sabanin sauran mazajen da idan sun fara ba su dakatawa sai sun kai ga biyan buƙatarsu ta hanyar sex da su. A lokacin ta ƙalubalance su akan cewa su ne ba su iya janyo hankalinsa ba. Ta ce ita za ta gwada basirar ta sai dai ita ma kamar su ta kasa. Yana shigowa ya ajiye wayoyinsa saman wani table dake cikin bedroom ɗin sa. Ƙarasawa ta yi gabansa ta ɗora hannunta a daddaɗen ƙirjinsa. Cikin harshen ƙasar Spain ta fara magana. "Ni zan tafi na yi kokarin zama a wannan ƙasar ta ku, saboda soyayyar da nake maka na mallaka maka komai na wa dukkanin jikina da kuka zuciyata. Amma kai ka kasa yi Mani haka. Sanin abinda take nufi ne ya saka shi share ta a hankali ta matso da fuskanta saitin na sa ta tallabo fuskarsa ta fara kissing lips ɗin sa. Take shi ma ya mayar mata da martanin abin da take masa zazzafar kiss yake yi mata wanda ta fara zaucewa. Ganin yadda ƙafarta ke rawa ya sa ya dauke ta ya dora akan doguwar kujera dake kusa da su. Cikin kiɗima ta zame yololuwar rigar dake jikinta tana kara shige masa. Boturan gaban rigarsa ta fara ballewa bai hana ta ba, bayan ta balle rigar ne ta yi ƙasa da hannu wajen wandonsa. Rike mata hannu ya yi tare da zare bakinsa daga nata ya ce. "Na sha fada maki ba na bukatar haka daga wajan ko wata ƴa mace ko?" "Ni ina ne ba ka sani ba ko ba ka ƙalla a jikina ba? Sai sai ne za ka ce ba wacce za ta kalle ka?" "Tun farkon haduwa ta da ke na fada maki haka don haka ki tsaya iya matsayin duk ranar da kika sake ƙoƙarin aikata Mani abinda irin haka to hannun da kira kokarin kai wa wajen zan karya. Kuma zan rabu da ke har abada." Cikin kuka ta fara roƙonsa da magiya. "Don Allah ka taimake ni ko sau daya ne ka yi sex da burina kenan." "Ban taɓa sex da kowane mace ba kuma ba zan fara akanki." Kasancewar ba komai a cikinta ya sa ta kalli jikinta tun daga kirji har zuwa ƙasanta, ita da take ja wa maza rai saboda jikinta amma shi yana mata wulakanci ta bar ƙasar ta da kowa ta zo wajensa amma ya kasa yi mata abinda take so. Ganin ta bude baki za ta yi magana ya sake hada bakinsu tare da aika mata zazzafar sumbatar da ke mantar da ita kanta. Yana yawo da hannayensa a jikinta yana shafa duk in da hannunsa ya taɓa. Har lokacin bakinsu na cikin na juna. Zahra ta shigo part ɗin don kawo masa zogalen da Dada ta aiko ta kawo masa. Sallama ta yi ba kowa a falo, ajiye wa ta yi a saman

Chapter 18 of 39