Share this page
Hilal yana sanye cikin wando na uniform ɗin su sau sai farar T-shirt mai dogon hannu. Cikin takunsa na isa da ƙasaita da kaga idanunsa ka ga zarra ƙirar jikinsa irin na jarumam mazan nan ƙarfafa saboda yawan motsa jiki da yake yi . Cigaba ta yi da tafiya yayin da yake bayanta. Tunawa ta yi da wata rana ƙanwarsa Maryan ta shiga gabansa tana tafiya kawai sai ya janyo ta tare da hankaɗa ta ta fadi a saman tiyel ta fasa goshi. Tunawa da hakan Fatima Zahrah ta yi ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya ya ji mata haka ballantana ita da ta zamo kamar mujiya a wajensu. Da sauri ta matsa jikin bango don bashi hanya. Ko kallonta bai yi ba ya wuce abinda ya barta da ƙamshin turarensa. Bayan ta fito ne ta hangi ficewarsa gidan shi da sojojinsa. Parking lot ta nufa ta shiga motarta har ta yi mata key kenan sai ga kira ya shigo wayarta . A'isha ce ƙawarta ke kira bayan ta isa gida. "Assalamu alaikum." Daga can ɓangaren A'isha dake zaune a falon mahaifiyarta ce ta ce. "Wa'alaiki salam, ya jikin naki?" "Alhamdulillah." "Kin ci abinci kin sha magana kamar yadda Dr ya faɗa?" "No yanzu dai zan je restaurant na siyo." "Akan me ba kuna da masu girki har mutane uku ba?" Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa. "Kin san ɗan gatan gidan ya dawo, kuma baya son girkin masu aiki aiki, shine suka ce masu aikin su bari su ne za su girka. Na je zan ɗebi abinci shi ne mahaifiyarsa ta hana ni saboda ɗanta aka girka." Cikin fusata A'isha ta ce. "Ji wani maganar banza, yadda fa suka takama da gidan kema dole ki yi, shi ɗangatan na su ai gidan kakansa da ya haifi ubansa ne kema haka gidan kakanki da ya haifi Babanki matsayinku ɗaya akan me za su nuna maki wariya?" "Kada ki damu da Ummina na nan da dole za ta bani abincin da zan ci." 'kin ga ki koma gida kawai bari yanzu zan kawo maki abinci, kin ga ba ki da lafiya Please kada kuyi driving a cikin wanna hali ." Godiya ta yi mata sannan ta fice daga motar ta kashe ta cire key. _Jidderh_ Gabaɗaya ranar ba ta yi barcin kirki ba saboda halin da ta ga Sir Asadullah a ciki. Kamar kullum bayan ta yi sallar asuba ba ta koma barci ba, ayyukan gidan ta yi kamar yadda ta saba yi. Bayan ta kammala ta yi wa Mahifiyarta sallama ta nufi hanyar titi don yau da ƙafa za ta tafi saboda ba ta da kudin abun hawa. Hakan ya sa ta bar gidan da wuri yau. Tana tafiya hankalinta na ga wajen uban gidanta, sai jinjina lamarin take yi a zuciyarta. *SHEKARU BIYU DA SUKA WUCE* Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe motocin sir Asadullah suka shigo harabar kamfaninsa. Kai tsaye motocin suka nufi parking space, motoci ne guda biyar biyu a gabansa biyu a bayansa sai wata hadaddiyar mota dake tsakiya, ita ce wacce Sir Asadullah ke ciki. Security ne tsaye ƙikam a parking space ɗin. Bude masa murfin bayan motar direbansa ya yi ya fito yana gyara zaman rigar suit ɗin da ke jikinsa. Ya wuce ciki yayin da amintaccen bodyguard ɗin sa wato Sulaiman ya take masa baya har zuwa hanyar da za ta sada shi da office ɗinsa. Secretary ɗin sa ta miƙe ta ce. "Good morning welcome sir, your friend is here to see you ilet him in as per your request anytime your friend are around I should always let them in." "Okay." Ya faɗa yayin da ya shiga office dinsa bayan bodyguard ɗinsa Sulaiman ya bude masa ƙofar office ɗin ya shiga. In da ya samu abokinsa Sagir zaune a office ɗin yana jiransa. Bayan sun shiga ne Sulaiman ya tura ƙofar office ɗin. Sir Asadullah ya wuce wajen hanger ya cire jacket ɗin dake jikinsa ya yi hanging ɗin jacket ya bar shert dake jikinsa. Zama ya yi a mazauninsa ya zauna yana kallon Abokin nasa ya ce "Sagir ya aka yi ne daga ina haka da safe? Okay sorry ba mu gaisa ba ko?" Ya yi maganar yana murmushi , shi ma Sagir ɗin murmushi ya yi tare da cewa. "Ban sani ba." _Fatima Zahrah_ Fitowar ta kenan daga cikin ɗakinta tana sanye da hijabi hannunta rike da waya ta kara a kunne tana cewa. "Okay ga ni nan fitowa ba bari na zo na shigo da ke." Ko da ta ƙaraso falon gidan gaba ɗaya ilahirin jama'ar gidan suna falo, sai dai kowa ya yi shiri kamar ruwa ya ci su. Hajiya Dada ce ta kalli Fatima Zahrah ta ce. "Ina za ki je hak cikin ranar nan?" Mumrmushi ta yi tare da cewa. "Kakus kin manta na faɗa maki cewa tun da muka shiga s.s ce ɗin nan an kawo sabuwar student tana so na?" Kai Dada ta jinjina alamar gamsuwa sannan ta ce. " Eh na tuna har kika ce A'isha sunan ta ko?" "Yauwa to ita ce ta ce na yi mata kwatancen gidanmu ta zo tana waje." Bayan kamar mintinan bakwai suka shigo rike da hannun juna murmushi bakinsu dauke da sallama. A'isha ta durkusa ta gaida jama'ar gidan suka amsa gabaɗaya sakamakon tsofaffin gidan na falon. Har Fatima Zahrah ta ja hannunta suka wuce cikin part ɗin su. Suna zuwa falon A'isha ta kalle ta tare da cewa. "Zahrah duk wadannan nan ahalin gidan nan ne?" "Eh me kika gani?" "Kun yi yawa na gani." Zahrah ta yi murmushi ta ce . Shi Wannan tsohon da kika gani wanda yake sanye da medical glass yana karanta jarida , shi ne Kakanmu wato Alhaji Muhammad Tafarki kenan, amma muna kiransa da Papa. Sai matarsa wacce ke zaune a gefensa wato Hajiya Jummai muna kiranta da Dada. Ƴaƴa guda hudu suka haifa cikinsu har da Abbi na. Babban ɗan su shi ne Alhaji Abubakar Tafarki, muna kiransa da Abba nan gidan yake zaune tare da matarsa Hajiya Maimuna muna kiranta da Umma. Suna da yara uku Yaya Hilal da Yaa Aminu sai Aunty Maryam. Bayan Abba sai ƙanin Abba wato Alhaji Adam Tafarki muna kiransa da Dady, shi ma nan yake zaune tare da matarsa Hajiya Amina muna kiranta da Mummy suna da yara biyu mace da namiji Yaa Mansur sai Aunty Nadiya. Daga Dady sai mahaifina wato Alhaji Salis Tafarki muna kiransa da Abbi sai matarsa Hajiya Zainab muna kiranta da Ummi ina da yayyu maza biyu wato Yaa Mahmud da Yaa Sadik sai ni auta. Daga Abbina sai autarsu wato Hajiya Laila muna kiranta da Aunty aurenta ya mutu nan take zaune da yaranta mata biyu wato Aunty Nabila da Aunty Kausar." "Ma sha Allah shi ya sa na ga kuna da yawa." Ai idan kin kira Babban gida ne, don Papa ya ce ba wanda zai tashi ya koma wani gida cikin ƴaƴansu, kowa ya zauna a family house, sai dai Aunty dake mace ce ta yi aure a wani gidan, Kafin auren ya mutu ta dawo ya yaranta." "To me ya saka Papa ya hana sosai tashi sai dai su zauna family house?" "Ba jituwa ne a tsakanin alhakin namu, tamkar maƙiyan juna haka muke." "Ta yi maganar cikin takaici." Ganin ranta ya ɓaci ya sa A'isha kawar da zancen, don da alama abun na ƙona mata zuciya. Fatima Zahrah ta tashi ta je ta kawo wa A'isha ruwa da lemu. Daga nan suka fara firan school ka asancewar suna shekaran ƙarshe a a secondry school, suna shirin zana waec da neco. _Asadullah_ Kwance yake yana saman tangamemen gadonsa yana barci, da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana. Kiran wayarsa ce ta farkar da shi daga barcin da yake yi. My Mom shi ne sunan da ya bayyana a kan fuskar wayarsa. Cikin Muryar wanda ke barci ya ce "Mom." "Wai har yanzu barci kake yi ne, bayan na fada maka yau za'a kawo maka matar da za ka aura ko ka mance?" "Mom don Allah ki daina wahalar da kanka wajen nema mani matar aure, shi aure lokaci ne da shi idan lokacin ya zo zan yi." "Ba na son gardama, ga ta nan tana jiranka ka shirya ka fito." Ba ta jira cewarsa ba ta katse kiran wayar . "Oh Mom ke baki gajiya kin kawo mani ƴan mata sama da sau biyar na ce ba su yi mani ba, amma ba ki gaji da aikin nemo matan ba. Wannan ma haka za ta koma don ba wata ƴa mace a gabana." Tashi ya yi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa 🚿 shower kusan mintuna talatin yana wanka, fitowa ya yi sanye da white bathrobe a jikinsa sai ƙamshin turaren wanka da sabulunsa yake yi. Hand dryer ya sa busar da gashin kansa. Man shafawarsa mai tsada ya shafa a jikinsa. Ya shirya cikin ƙananan kaya riga J.C na kamfanin ƙwallon ƙafan Manchester united. Sai baƙin wando 3quater da ya sanya. Ya fesa turarensa mai daɗin ƙamshi da tsada. Tsadadden agogonsa na kamfanin GUCCI ya ɗaura a tsinysiyar hannunsa. Sai takalmi shi ma na kamfanin GUCCI ya saka a ƙafarsa. Wayoyi guda biyu ya ɗauka ya fice daga ɗakin. Downstairs ya nufa inda ƙamshin turarensa ya riga shi isa gare su. Suna zaune a main falon gidan. Alhaji Ahmad da matansa biyu Hajiya Hajiya Zubaida da Hajiya Zulaihat suna zaune samun kujera. Yayin da Kamal da Fauziyya da Suhaila na ke zaune a ƙasan carpert. Can gefe kuwa budurwar da aka kawo masa ya gani ko ta yi masa ne. Tunda budurwar ta ji ƙamshin turarensa ta juya zuwa in da ƙamshim ke fitowa . Idani ta zubawa Asadullah tana ganin tsantsar kyau da Allah ya masa. Kallo ɗaya za ki masa kin san ya haɗa jinsi da Fulani. Dogo fari ne yana da kayan siffa da nagarta kyakkyawa ne yana da zagayayyen fuska mai ɗauke da manyan idanu ƙwayar cikin idanun ba baki ba ne Ash color ne ruwan toka kamar dai idanun mage.hancinsa dogo wanda ya dace da fuksar sai ƙaramin bakinsa wanda ya yi kasance pink color. 'Wow' Ta furta tana kallonsa wanda shi ko kollonta bai yi ba idanunsa na kan Mom da take masa kallon sai yanzu ka ga damar fitowa. Murmushi ya sakarwa Mom tare da mata alamar ta yi haƙuri. Bayan ya ƙaraso ne ya ya kalli Mahaifinsa tare da cewa. "Barka da safiya Dad." "Barka dai Son ka fito, ya aiki?' "Alhamdulillah." Kallon Mom ya yi tare da cewa. "Barka da safiya my Mom." "Barka my son ya kake?" "Alhamdulillah." Kallon Hajiya Zulaihat ya ce. "Barka da safiya Aunty." "Barkanka." Ta fada a takaice. Taɓe baki Mom ta yi tare da kau da mai daga kallon kishiyar ta ta. "Barka da safiya Babban Yaya.?" Cewar Kamal yana murmushi, shima mumrmushin ya mayar masa da martanin tare da cewa ƙanina ya kake?" Fauziyya ta ce. "Morning big bros." "Morning my dear ya kike?" "Am fine." Suhaila dake maƙale jikin Hajiya Zulaihat ta kalle shi ta ce. "Ina kwana Yaya." "Ƙanwata ya kike?" "Lafiya lau." "Ma sha Allah." Mom ta yi gyaran murya ya kalle ta sai ta yi masa nuni da budurwar da aka kawo masa. Bai kalle ta ba ya ce. "Ita ma wannan kamar sauran dai a sallame ta kawai, idan na tashi zan nema da kaina ." Ɓata fuska Mom ta yi tana kallonsa. Kamal ya ce . "Babban Yaya wannan fa tafi sauran wadanda aka kawo maka a baya. Ba ka kalle ta ba ne ta hadu." Suhailat dake jikin Hajiya Zulaihat ta ce "Yaya kam wannan kyakkya..." Hajiya Zulaihat ta kai mata duka a baki, cikin ɓacin rai ta ce "Ina ruwanki ban fada maki ki daina shiga sabgar mutanen nan ba, Ina ruwanki?" Dad ne ya kalle ta yace. "Haba mana Zulaihat me ya sa kike haka, ko da ba kece kika haifi Asadullah ai ɗan ki ne, tunda ɗana ne, kamar yadda Suhaila take ƴata, ki daina raba Mani kan yara ba na so." Ba ta ce komai ba ta ja hannun Suhailat suka wuce cikin. Asadullah ya ce. "Na rasa me na yi wa Aunty." "Kada ka damu wani shawara ka yanke akan yarinyar nan, tana da tarbiyya ƴar ƙawata ce." Shiru ya yi yana kallon budurwar da ta sunkuyar da kai kafin ta ɗago ta kalle shi suka haɗa idanu. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page0️⃣3️⃣ Shiru ya yi yana kallon budurwar da ta sunkuyar da kai kafin ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta yayin da ita kuma sai kallonsa take yi. Yamutse fuska ya yi tare da kallon Mom ya ce. "Mom ba ta da wani banbanci da sauran matan da kika kawo mun fa, kuma duk na ce ba su yi ba kika hakura wannan karon ma ina so ki hakura Mom zan nemo mace da nake gani ta dace da rayuwata." "Son wannan karon fa ba zan saurara maka ba, don haka ko me za ka ce sai ka auri Fadeela." Kallon Dad ya yi zai yi magana Dad ya ce. "Ba ruwana tsakanin ku da Mom ɗin ka ce, duk abinda ta fada ya zauna, idan aka biye maka a tuzuru za ka yi ta zama. Shekarunka talatin amma a ce ba ka da budurwa, sai ka ce wacce aljani ta aura?" Bai ce komai ba ya nufi upstair a abin sa, don ya lura yau kam Mom ta gama da shi ba za ta saurare shi ba . Ita kam Fadeela duk da ta lura ko kallon arziki bai yi mata ba, kuma da alama baya son ta amma hakan bai son ta amma hakan bai sa ta ji za ta iya haƙura da shi ba. Mom ta kalle ta tare da cewa. "Kada fa wannan ya dame ki, ki kwantar da hankulinki ki faɗa wa Mamanki ina na nan zuwa za mu tsara komai." Cike da farin ciki ta yi godiya ta fice daga gidan. "Oh Allah zamani ne ya kawo mu da mata ke tallan kansu a wajen namiji haka, ni kam Mom Wallahi ba'ayi namijin da zan je tallan kaina har gidansu ba. Ko da ya fi Yaa Asad kyawu da kuɗi kuwa." Cewar Fauziyya tana tashi wajen. Kamal ya bi ta da kallo tare da cewa. "To ke meye naki a ciki, da ba don yayanki ba ne zan iya cewa kishi kike yi yi. " "Yaa Kamal kenan." Ta fada tana barin wajen. _Fatima Zahrah_ Gajiya ta yi da zaman ɗakin nata, don haka sai ta yanke shawarar zuwa part ɗin Kakanninta. Don idan kewar ta ishe ta an nan take zuwa ta ɗebe kewa. Ko da ta ido main falo Aunty Laila ce da ƴaƴanta, Kausar da Nabeela. Tun kafin da ta ƙara so ta ji Muryar Nabeela na cewa. "Wallahi ba zan yarda ba sai dai ita ta hakura ta bar mani Yaa Hilal ɗin don ba zan iya haƙura da sonsa ba." Kausar ma ta ce. "Kamar yadda ni ma ba zan iya haƙura da sonsa ba, ai na girme...." Sallamar Zahrah ya sa ta yi shiru kuma ba wacce ta amsa sallamar daga uwar har ƴaƴanta. Sai na tsuki da suka ja. Dama ba ta saka ran cewa za su amsa ba. Don idan da sabo sun saba. Kai tsaye ta nufi part ɗin Kakanninta. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga falon. Dada ce ta amsa yayin da take ajiye wani bowl a saman Centre table. Amsa mata sallamar ta yi tare da cewa. "Duk wayewar garin yau sai yanzu kika shigo." "Ba haka ba ne Dada kin san next month zan yi walima ina karatu ne." "Haka fa ƴar albarka duk kin fi sauran yaran ke da yayunki, amma sauran ba abunda iyayensu suka koya masu sai gaba da baƙar zuciya." Mumrmushin kawai Zahrah ta yi ba tare da ta ce komai ba. Sai ta kawar da zancen ta hanyar cewa. "Dada me kika dafa ne?" "Yayanki da ya dawo ne yake son kwaɗon zogale shi ne na masa." Kallon rashin fahimta ta yi mata tare da cewa. "Wani Yayana kuma?" "Wanann mara imanin mana, ai na gayawa kowa na gidan ya shiga hankalinsa kafin ya illata su, ke na san baki da tsokana ballantana ki shiga gonarsa ya illata ki a banza, ga shi ke ba isashshiyar lafiya ba. Ya zo ya dukanki ya illata ki a banza wai shi soja ." Zama Fatima Zahrah ke ƙoƙarin yi Dada ta ce. "Na ji har yanzu bai zo ba, ki je ki kira mani shi ko ki tambaye shi a kawo masa nan ne a ɗakinsa? Da sauri ta kalli Dada tana cewa. "Ni kuma?" "Ko kema baƙin halin kika fara koya ne da kuma gaba? Kafa ku biye masu kin ji shi wanda na ce ki kira a matsayin Yayanki ne kamar yadda na haifi ubansa haka na haifi ubanki, kuma Hilal bai ɗauko baƙar zuciyar uwarsa ba, yana da kirki gara yanzu da ya zama soja ya fara canza halaye, na rashin imani da tausayi irin ta su ta sojoji Ko kema an koya maki gabar ne?" Da sauri ta girgiza kai tare da cewa. 'A'a" "To kira shi." Cikin sanyi. Jiki ta tashi ta nufi ɗakinsa duk da cewar lokacin ƙarfe tara na dare ne. Ba kowa a main falo dama idan dare ya yi ba su cika zama ba kowa na part ɗin sa. Upstair ta haura don a can part ɗin sa yake, duk da cewar tunda ya gama karatu ya dawo ƙasar ba ta taɓa zuwa ɗakinsa ba. _Hilal_ Fitowarsa daga wanka kenan ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa. Sai wani da yake goge ruwan dake kansa. Gashin ƙirjinsa ya kwanta luf a fafdaɗen ƙirjinsa. Kallo ɗaya za ka masa ka san cewa ƙakkarfa ne don surar jikinsa a murɗe take ga ƙwanjin dake hannunsa wanda kallo ɗaya za ka masa kasan cewa yana yawan motsa jiki da exercise. Ba fari ba ne kuma ba za ka kira shi da baƙi ba za ka iya kiransa da wankan tawaɗa. Dogo ne sosai yana da ƙira da cikar halitta irin na lafiyayen ɗa namiji ga kyau ga cikar zati Allah ya bashi. Sannan yana da ƙira irin na ƙakkarfan namiji jarumi na azo a gani Bayan ya gama tsanar ruwan jinkinsa ne ya ajiye ƙaramin towel ɗin. Sallama Fatima Zahrah ta yi a falon ta ji shiru don sai ta yi tunanin baya nan, har za ta juya sai ta yanke shawarar duba shi a bedroom ɗin sa. Sallama ta yi kai tsaye ta tura ƙofar falon. Ƙamshi ne ya ziyarce ta ta tsaya tana ƙarewwa falon kallo. Ya burge ta komai fari ne a cikin dakin kama daga fentin da labulaye da kujeru komai fari ne, hatta Centre carpet da Centre table komai fari ne sai ɗaukar ido suke yi kamar ba'a taɓa amfani da su ba. Hatta tiyel ɗin ma fari ne. Ƙofar bedroom ɗin da ya kasance shi ma fari ne ta yi knocking. Yana tsaye gaban dressing mirror 🪞 ya juya ya kalli ƙofar ba tare da ya yi magana ba. Sai da aka sake knocking sau uku kafin ya ce. "Come in." Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin, kallo ɗaya ya yi mata ta cikin dressing mirror ya ɗauke kansa. Haka bedroom ɗin ma ya tafi da ita don shi ma komai nasa farin ne. Idanunta ne ya sauka akan wani butterfly 🦋 da aka yi ƙaton elergment aka zana butterfly din shima fari dai ɗaukar idanu yake yi, don har shinning yake yi. Ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba har sai dai dimpul ɗinta suka lots. Jin shiru ta shigo ɗakin ba ta ce komai ba ne ya saka ya kalle ta ta cikin mirror ya ga murmushi ma take yi. Gyaran murya ya yi wanda ya sa ta dawo nutsuwarta. Kallo ɗaya ta yi masa ta ganshi ɗaure da towel iya ƙugu. Kau da kanta daga kallonsa ta yi tare da cewa. "Ina wuni?" Banzan ya yi da ita kamar bai ji me yake cewa ba. Sanin cewa ya ji ta kuma ba ta saka ran zai amsa mata ba, don bai taba amsa mata gaisuwa ba ko ta gaishe shi. Idan ya amsa sallamarta shi ne nan. "Dama Dada ce ta aiko ni wai a kawo maka zogalen anan ne ko za ka zo can ka ci?" Nan ma banza ya yi mata kamar ba da shi take yi ba. Don har sake maimaitawa ta yi nan ma ya share ta kamar bai ji ta ba. Closet din kayansa ya shiga ya bar ta nan tsaye. Tana ganin haka ta juya ta fita tana magana ƙasa-ƙasa. "Mutum sai jin kai da nuna isa. Idan ba don Dada ba mai zai shigo da ni ɗakinka ballantana ka nuna ni banza ce a wajenka, idan ba don naka-naka ne ba da ko kallonka zan yi." Haka ta dinga gunguni ita kaɗai har ya karasa ɓangaren Dada. Dada na kallonta ta ce. "Me ya ce a kai masa ne, ko zai zo nan ya ci?" Tura baki ta yi tare cewa "Bai ce mani komai ba kuma ya ji ni." Shiru Dada ta yi kafin ta ce. "Kada wannan ya dame ki, kin san yana da mishkilanci haka yake ba kowane lokaci yake magana ba yin ta yake ba sai ya zama dole." "Ina nawa zogalen na ci? "Ga naki a kitchen ki je ki ɗauk." Ta dauko nata zogalen da ya ji yajin ƙuli da yanke-yanke ta yi bisimillah ta fara ci. Har ta gama Hilal bai zo ba, hakan ya saka Dada ta ce ta ɗauka ta kaiasa kafin ta wuce part ɗin su. "Da ko na je wulakanta ni zai yi, zan ke na kwanta gobe ina da jarabawa." "To idan ba ke ba waye a nan da zan aika, dare ya yi ni ba lafiyar ƙafa ba ballantana na haye upstair." Haka ba don ranta ya so ba ta ɗauki bowl ɗin ta nufi kofar fita, ta ji Dada na cewa . "Nan za ki dawo mu kwana ko ɓangarenku za ki koma ? " Ba ta ce komai ba ta fita don ranta ya ɓaci da komawa part ɗin sa. _Jidderh_ Tafe take sanye Da Kayan makarantan secondry school, makarantar Gwamnati ce take zuwa mai suna Government Day secondry school. Tafiya take yi ga rana ana ƙwalawa tun karfe biyu aka tashi amma kasancewar unguwarsu da nisa da makarantar yake daukarta karfe uku da rabi kafin ta isa gida. Sanye take ta riga fari wanda ya sauko har guiwarta sai farin hijabi da dogon wando wanda ya kasance blue. Sanye take da farin socks socks da takalmin sandal baƙi na roba, duk ya yi ƙura sakamakon tafiyar ƙasa da ta sha. Madaidaicin gidansu ta shiga gida ne mai ɗauke da ɗakuna huɗu Isah yayanta yana zaune a ɗaki biyu ciki da falo, sai ɗakuna biyu wanda Innarsu Jidderh ke amfani da shi Jidderh kuma tana amfani da ɗaki ɗaya. Sai ƙaramin kitchen a tsakar gida da kuma banɗaki shi ma a tsakar gidan. Da sallama Jidderh ta dawo sai dai ba ta ji an amsa ba, amma hakan bai bata mamaki ba saboda ta san Innarsu ba ta nan, sai matar Yayanta Isah wacce kwana biyu take naƙuda a tsaitsaye. Tana shiga tsakar gidan ta nufi randar ƙasa da suke zuba ruwa. Ta bude ta ɗebi ruwa ta sha saboda ƙishirwa ga rana da ta kwaso. Bayan ta sha ruwan ne ta je za ta shiga ɗakinta don ɗakin Inna a rufe Sa'adatu matar Isah kullum cikin barcin rana take, hakan ya sa kai tsaye za ta shiga ɗalibta sai ta ga jini a ƙofar ɗakin Sa'adatu. Ta bi jinin da kallo har jikin labulen, cikin tashin hankali ta nufi ɗakin ta fad'a ciki. _Fatima Zahrah_ Knocking ta yi a bakin kofar falon Hilal, jin shiru sai ta tuna cewa ta barshi a bedroom ne da ta shigo isar masa da saƙon Dada. Don haka ta nufi bedroom ɗin nasa sanin cewa ko ta yi magana ba zai amsa ba ya sa ta yanke shawarar shiga ta ajiye masa. Tura ƙofaf ta yi tare da sallama. Ba ta ga kowa a ɗakin ba, da alama ya fita. Don haka ne ma ya ajiye masa bowl ɗin zogalen a table da ta gani a gaban kujera. Har za ta fita sai ta tuna fa butterfly da ta gani a ɗakin da sauri ta juya ta nufi wajen, sai dai tsayinta bai kai ta taɓa shi ba, kuka tana son ta shafa photon. Don haka ta juya in da ta ga wani kujera da yake zama. Janyo kujerar ta yi ta ajiye a wajen, sai ta hau kujerar ta taka ta. Hakan ya saka

Chapter 2 of 39