Share this page
ba, don da ace don ita ne ba zan tafi ba." ",Daga nan ya fice. Kallon juna Dada da Papa suka yi kafin Papa ya girgiza kai tare da cewa "Allah ya shirya ." Daga haka ya tafi zuwa part ɗin iyayensa, suka gaisa bayan haka ƙannensa Faisal da Maryam suka gaishe shi , ganin za su dame shi da surutu ya tashi ya bar falon Part ɗin Abba ya nufa nan ma ya same su duka , ya gaida Abba da Umma yayin ga Mansur da Nadiya suka gaishe shi. Bayan ya bar part ɗin ne ya nufi part ɗin Aunty Laila. Nabeela da Kausar kamar za su cinye shi. Ganin yadda suke kallonsa ne ya saka shi tsuke fuska. "Barka da warhaka Aunty." Cikin jin dadi ta ce. "Barka dai Son ka dawo?" "Eh" Ya amsa a takaice. Nabeela ta fara gaishe shi ya ce "Ina wuni Yaa Hilal?" "Lafiya lau." Ya amsa ya yin da Kausar ke ƙoƙarin gaishe shi ta ce. "Ya Hilal ina wuni ka dawo?" "Eh na dawo." "Alhamdulillah na ji dadi da ka dawo laflya." Bai ce komai ba sai tashi da ya yi ya ce. "Aunty zan tafi." "Ka zauna mu yi fira mana." "Aunty na gaji zan kwanta ne." Daga haka ya wuce, don yana son yin barci dan ya koma part ɗin sa Alexandra za ta dame shi. Don haka ya yi kwanciyar sa a babban falon gida, kasancewar ba kowa a falon." Bayan kamar awa ɗaya da kwanciyarsa sai ya ding jin hayaniyar ƴa matan gidan, sai dariya sha da shewa. A fusace ya tashi tare da daka masu wata irin tsawa wanda ya saka hanyar cikinsu kaɗawa. Nadiya da Maryam har z su gudu suka ji muryarsa yana cewa. "Kada wacce ta gudu, duk kuwa wacce ta gudu sai na yi mata ninkin wanda zan yi wa Sa'id." Sanin waye shi da abin da zai iya aikatawa in dai ya furta ya saka suka dawo. Belt ɗin wandonsa ya zare da ta kan Maryan ya fara, dukanta kawai yake yi, dai d ya tabbatar ta ji laushi kafin ya janyo Nadeey. Ita ma ya fara dukanta sosai kamar Allah ne ya aiko shi. Ganin Haka ya saka Nabeela gudu wa . Tsalle ɗaya ya yi ya isa gabanta. Finciko ta, ganin haka Kausar ta kara tsorata. A guje ta nufi ɗakin Mahaifiyarta. Sunyi Laila da ke kwance ta mike da sauri tana tamabayar Kausar abin da ya firgita. Nuni take yi da ƙofa ganin haka ya saka Aunty Laila rufe ƙofa ta murza key. Sai da ya gama dukan Maryam, Nadeeya, da Nabeela sannan ya lura da Kusar ba ta nan. Kuma duk dukan nan ba wanda ya ji ballantana ya fito cetonsu. Don ya hana su kuka wai baya don hayaniya. Kausar kuwa tana can wajen Aunty Laila tana rarrashinta duk da ba dukan nata ya yi ba. Ƙarin guiwa take bata akan ta daina wanann kukan tun da ta zo wajen ta ai ta tsira bai isa ya ce zai dakar mata 'ya a gabanta ba. "Wai me kuka yi masa?" "Wallahi ba abinda muka masa.' Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Ƙarya ne haka kawai ba yadda zai iya cewa zai dake ku, sai dai da dalili." "Eh to yana barci a Falo mu kuma muna ta fira shi ne ya farka ya zare bellet daga wandonsa ya fara ta kan ƙanwarsa Maryam, daga ita dai Nadeeya yana zuwa kan Nabeela shi ne na gudu." "Kuma ai kun san halinsa baya son hayaniya da kuka kan shi kwance a wajen ai da sai ki tafi. Wani Wajan." "Mun ɗauka ba zai..." Dukan kofar da ake yi ne ya saka Kusar ƙankame Aunty Laila. "Ki fito kafin na ɓalle ƙofar nan na zo na same ki ." Rai a ɓace Aunty Laila ta ce . "Halal ka fita i idona ko mutuwa na kunyar idon mahaifi a ɗakina za ka zo ka ce zaka ɓalla?" "To idan ba haka kike so ba ki miƙo Mani yarinyar nan" "Wace yarinyar? Yarinyar da za'a aura makan ne za ka daka, so kake ta tsotsa da kai ta ce ta fasa?" Tsuki ya yi cikin takaici ya ce. "Kausar wallahi idan ba ki kawo mun kanki ba har kika bari na ɓalle ƙofar nan dukan ki sai ya ninka na su." "Ƙofar za ka ɓalle mun saboda ba ka ..." Kafin ta ƙarasa zancen nata ne ta ji wani ƙara take Kum ƙofar ta faɗi ƙasa, sakamakon duka ɗaya da ya yi wa ƙofar Bature sai ga ga ƙasa. Haka ya nufi Kausar da na ta ƙara tsorata don dama akwai ta da taron duka. Ƙanƙame Aunty Laila ta yi tana cewa . "Mum ki taimake ni." Yana zuwa ya finciko ta tare da hankaɗa ta ƙasa ya hau dukanta da belt ɗin hannunsa. Duk yadda Sunyi Laila ta yi kokarin ƙwatar ta amma ina ta kasa. Don wajen ƙwatar ta har ita ma ta samu rabonta ba shiri ta yi gefe tana duba hannunta da ya daka. Sai da ya tabbatar ya mata lilis sannan ya bar ɗakin yana huci. _Fatima Zahrah_ Bayan ta tashi daga barci ne sai ta ji dadin jinkinta sosai. Tashi ta yi ta nufi bathroom ta yi wanka da wani ruwan ɗumin. Sannan ta ɗauro alwala ta zo ya gabatar da sallah. Bayan ta yi addu'a ta fito ta samu kowa nata a falon. Abbi, Umma, Yaa Mahmud da Yaa Sadik. Yayyun nata ta bawa keys din motar, Mahmud ya ce. "Ta ya ya za ki bamu ai kece aka ba." "Yaya wallahi ba na so ɗaya ta ishe ni" Ba yadda suka iya dole suka karba suna mata godiya. Dubanta ta mayar kan Abbi ta ce. "Abbi sauran kujerar Hajji ka bawa wandanda ka ga sun dace, musamman masu bukata da ka san ba su taba zuwa ba sai ka basu, don ka ga mu kam Alhamdulillah Allah ya hore ana zuwa duk shekara." Sanya mata albarka kawai suke yi tare da yaba kyawun zuviyarta, don duniya ba ta dame ta ba. Washegari tun a school take jin Mararta na mata ciwo, dakyar ta iya fitowa daga lecture ko Amini da A'isha yau ba ta tsaya sun yi sallama ba ta nufi motarta. Gudu take yi wajen yin driving ɗin sauri take ta ganta a gida. Ikon Allah ne kawai ya kawo ta gida lafiya. Tana parking ta fito ko wayarta da jaka ba ta tsaya ɗauka ba ta fice daga motar. Tana shiga falon sai ta zube kan dogon kujerar ta kasa ƙarasa wa . Dama haka take fama a duk lokacin da za ta yi period, shi ya sa Ummi ke hana ta yawan shan zaƙi da take yi. Haka ta dinga murƙususu na azaba ga shi ta kasa, ga shi ta bar wayarta a mota. Tana cikin wannan yanayi sai ga Aunty Laila ta shigo ita da Mummy. Da alama daga unguwa suke. Kasancewar tana zubar da jini sosai ya saka Kayanta ya ɓaci don haka juyawa da ta yi kuma Abaya ruwan madara ta saka wanda jinin ya nuna a rigar sosai. Dama tana shan wahala sosai idan za ta yi baƙon wata. Daidai lokacin nan Hilal ya shigo falon, ganin yadda Zahra take ya saka ya kalli su Mummy da sauri ya ce. "Lafiya kuwa?" Buɗar bakin Aunty Laila ta ce "Ciki ta zubar shi ne ta zo ta kwanta wa mutane a nan." Da mamaki ya kalle ta tare da cewa. "Ciki kuma?" ", Kwarai kuwa ai wannan kana ganinta ne kawai baka san mugun abu da take aikatawa ba." "Waye ya faɗa maku ciki ne?" Mummy ta kalle shi a fusace ta ce "Ina ruwanka ne wai ma da kake tamabayar mutane, wannan jinin ya wuce jinin haila kam." Kallon mahaifiyar ta sa ya yi tare da kallon Aunty Laila daidai lokacin da Zahra ta saki jiki ta mirgino za ta faɗo ƙasa. *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *GABAR CIKIN GIDA* *NA* Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan ce) *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣6️⃣ Kallon mahaifiyar ta sa ya yi tare da kallon Aunty Laila daidai Lokacin da Zahra ta saki jiki da ta faɗin. Cikin zafin nama ya nufi wajan da take kwance da niyyar ta tare ta kafin ta faɗo ƙasa. Tsawar da mahaifiyarsa ta daka masa bai saka ya fasa abinda yake yi ba. Tare ta ya yi ta fado akan hannunsa. Cikin fusata Mummy ta daka masa tsawa ta ce. "Hilal ba da kai nake magana ba ko?" "Ku yi hakuri Mummy kin ga yanayin da take ciki ga shi iyayen nata sun fita zuwa ta'aziyyar abokin Papa, Yayyun ma basa gidan idan wani abu ya faru da Ita ku da kuke gidan za'a tuhuma." A fusace Aunty Laila ta ce. "Uban waye zai tuhume mu ko akwai wanda ya sa ta yin cikin shege be ballantana ta zubar?" "Kuna da Hujja kan hakan?" Ba wacce ya bashi amsa, ɗaukar ta ya yi ya nufi kofar fita, Mummy za ta dakatar da shi Aunty Laila ta mata alama ta bar shi. Ta yi murmushi mai cike da ma'anoni. Yana fita harabar gidan sojojinsa suka taso alama ya masu da su koma, haka ya saka suka koma ya nufi daya daga cikin motocinsa. Direbansa ya bashi key ɗin motar ya karba sannan ya yi wa motar key a guje ya bar gidan. Asibiti ya kai ta in da ya yi parking ya fito ta ɗauke ta zuwa ciki. Aka karbe su cikin gaggawa kasancewar an san su a asibitin. Doctor ne tare da nurses suka rufa akan ta don zuwa lokacin a sume take. Jini ne ya ɓata masa amma bai damu da hakan ba. Yana nan zaune sai ga Dyoctor Ahmad ya fito ya ce masa ya biyo shi a office ɗin sa. Tashi ya yi ya bishi bayan sun gaisa yake cewa. "Amma na yi matukar mamaki da abin da idona ya gane Mani." Kallonsa Hilal ya yi ba tare da ya ce komai ba. Doctor Ahmad ya cigaba da cewa. "Maganin zubewar cikin da ta sha ne ya saka ta a cikin wanann halin." Wani kallo Hilal ya masa wanda har sai da Doctor ɗin ya tsorata. Don shi bai yarda ba. "Ka tabbatar da abun da ka faɗa?" "Ƙwarai kuwa ba abinda zai saka na fadi abin da ba haka ba, yaushe Zahra ta yi aure ne ban sani ba, kuma ban jima da zuwa gidan ba. Kai ne mijinta?" Banza ya yi masa zuciyarsa kawai yake jin yana masa zafi. Kai tsaye ya shiga ɗakin da aka kwantar da ita ya samu tana barci an saka mata ƙarin ruwa. Kallonta yake yake yi cike da ƙarin tsanarta a cikin zuciyarsa. Haka ya nufi motarsa ya nufi gida Tsuki yake ja lokaci zuwa lokaci . "To wai ma meye na wa na damuwa akan abun da ta aikata?" Wata zuciyar kuma ta ce masa, 'Ai dole ka damu don ko kana so ko ba ka so ita ɗin jininka ce, kuma idan ta zubar da mutuncinta tamkar ta zubar da Mutuncin ahalinku ne.' Yana shiga falon ya samu Mummy da Umma sai Aunty Laila suna zaune a Babban falon gidan a kan kujera. Suna jin karar ƙofar suka juya suna tambayarsa meke damunta. Yanayin ɓacin rai da yake ciki ne ba zai iya magana da kowa ba, don haka bai ce masu komai ba ya haura sama. Ko da ya shiga falon Alexandra ne zaune a falon. Don sai da ya saka key ya bude saboda baya son a san da zamanta ya saka yake rufe part ɗin da key. Tana ganin ya dawo rigarsa da jini ya tashi take tamabayarsa cikin tashin hankali. Ce mata ya yi ba komai mai ciwo ne ya ɗauka zuwa asibiti. Bedroom ya wuce har ya shiga ya dawo ya rufe kofar da key don gudun kada wata ta shigo ta ga Alexandra. Bayan awanni biyu Abbi da Ummi suka shigo falon bakinsu ɗauke da sallama. Daga Umma har Mummy da Aunty Laila ba wacce ta amsa. "Ummi ta ce barkanku da gida Ina wuninku?" Aunty Laila ce ta yi tsuki sauran ko ba su ma kalle ta ba ballantana su amsa. Don dama sun san ba amsawa za su yi ba Amma kullum sai sun yi masu sallama sun gaishe su duk da sanin ba amsa wa suke ba. Har yanzu Handbag ɗin Zahra na tsakiyar falon sai dai sun kira mai aikin ta goge hanci jinin. Ganin Handbag ɗin Zahra Ummi ta dauka ta shiga da shi tana cewa. "Zahra kenan ta ajiye jaka ta shige ciki ko?" "Abbi ne yake cewa. "Ta gaji ne shi ya sa ta ajiye anan." "Haba wani gajiya sai ka ce Jakar nauyi ne da ita?" Haka suke tafiya suna magana har suka karasa part ɗin su. Bedroom ɗin Zahra suka fara zuwa amma ba ta ciki. Ummi ta karasa jikin kofar bathrobe ta ji ba motsi, knocking ta yi shiru. Hakan ya saka tura ƙofar ba ta ciki. Abbi ya ce. "Ina ta shiga kuma mai baro Dada da Papa wajen ta'aziyya ballantana ace tana can." Kiran wayarta Abbi ya yi suka ji wayar a handbag ɗin ta. Mamaki suke ina ta shiga don ba ta fita sai ta nemi izinin iyayen ta. _Hilal_ Koda ya koma asibitn ya samu har ruwan da aka ƙara mata sun ƙare, Tana zaune ita kadai a ɗakin, tagaumi ta yi tana tunani waye ke tare da ita a nan. Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar mata da faɗuwar gaba. A hankali ta da ɗaga kai tana kallon ƙofar. Sakin kofar ya yi ya shiga fuskarsa a murtuƙe, ita kanta ta tsorata da ganin yanayinsa. "Ba za ki daina kallona ba da wannan shegun idnaun naki kamar na mujiya ba?" Da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa. Munafuka kawai Musa a baki Fir'auna a zuci ana maki kallon mutumiyar ƙwarai ashe ba haka ba kura ce ke lulluɓe da fatar akuya." "Ya Hilal me na..." Katse ta ya yi cewa. "Tun yaushe kika fara wannan harkar a ƙarancin shekarunki?" Kallon rashin fahimta ta yi masa ta ce. "Harka?" "Tambayarki nake yi waye abokin fasiƙancin na ki?" Shiru ta yi yayin da ƙwalla ke kwaranya a idnaunta. Ba ta yi aune ba ta gan shi a gabanta sai huci take. Shaƙo wuyanta ya yi ta fara zaro idanu tana kakari. "Na ce waye ya yi maki cik?" _Jidderh_ Ko da ta koma gida yau sam ta ƙi cin abinci kuma ta ƙi magana da kowa. Da Inna ta tamabaye ta sai ta ce mata ba komai. Tana cikin wannan yanayin ne sai ga Yaya isah ya dawo gidan. Kallo ɗaya ta mata ya gane tana cikin damuwa. Ƙarasa wa ya yi wajen yana cewa. "Subhanallah Autar Inna lafiya?" Kuka ne ya kufce mata ta ce. "Yaya tausayinsa nake ji." "Waye kike jin tausayinsa?" "Yaya wa ka sani bayan Asadullah da kullum nake maka zancensa." "Allah ya kawo masa ɗauki?" "Yaya ka taimake ni mu fitar da shi daga wannan halin da yake ciki." Kallon baki da hankali ya yi mata kafin ya ce. "Kin san me kike fada kuwa?" "Na sani Yaya." "Babban mutum ne fa ta Yaya kike tinanin fitar da shi, kada ki je ki saka rayuwarki a hatsari da." Mumrmushin takaici ta yi tare da cewa. "Matarka da ɗan ka suna raye a yau ne saboda Sir Asadullah, ko ka mance a halin da muka kai ta asibiti za'ayi mata aiki ba ka da kuɗi, na yi yawo ban samu ba, ka yi buga-buga ba ka samu ba na bika kasuwa ba ja da shi, ka nemi taimakon ubannin gidanka ba su taimake ka ba, sai da ja je kamfanin Asadullah ya taimaka mana da kuɗi wanda lokacin matarka tana gaɓar rayuwa da mutuwa . Don Allah ka taimaka masa ko don taimakawa da ya yi wa iayakinka duk d bai san waye ba " Ajiyar zuciya Isah ya sauke tare da cewa. "Kin saka jikina yin sanyi. Bari na shiga na fito sai mu san yadda zaj ɓullo wa lamarin." Murmushi ta yi tare da jinjina masa kai. *Waye Sir Asadullah?* Asadullah Ahmad Abubakar shine cikakken sunansa. Asalinsu mutanen jihar Yola ne a garin Adamawa, Asalinsu Fulani ne, makiyaya. Ahmad wato Mahaifin Asadullahi Ya taso shi kaɗai ne a wajen mahaifinsa Abubakar. Abubakar yana da ƙani mai suna Sale Ko da ya taso bai san Mahaifiyarsa ba. Don ta rasu yana da shekaru biyar a duniya. Sale lokacin da matar Yayarsa ta rasu bai yi aure ba saurayi ne shi. Mahaifinsa ke kula da shi su biyu ne suke rayuwa a cikin wannan gidan. Sai dai ƙanin mahaifinsa wato Sale shi yake masa komai na larura da ya shafi kuɗi. Saboda yana da rufin asiri da ƙoƙarin neman na kai. Ganin Yayan nasa ya daina fita ko ina saboda ɗawainiyar yaro ne ya saka yake masu komai na ci da sha har da sutura. Kullun idan Zai dawo sai ya siya masa ƙosai da biredi. Ana cikin wannan lokacin ne Saleh y yi aure, in da ya auro matarsa ƙyakyatawar Bafulatana mai suna Joɗa nan gidansa dake jikin gidan Yayansa ya ajiye ta . Shawara ya yanke tun da shi ya yi aure ga Yayansa tin mutuwar matarsa ya kasa ƙara aure. A wata ranar Juma'a ne y shiga gidan Yayansa bakinsa ɗauke da sallama. Hannunsa ɗauke da bakin leda. "Assalamu alaikum" Mallam Abubakar ya amsa yana sakin murmushi ya ce. "Saleh har ka dawo?" "Eh na dawo." Ya karaso ciki yana mikawa Ahmad ledar biredi da tsire da ya siyo masa . Karba ya yi cike da murna yana nuna wa mahaifinsa. Bayan sun gaisa ne Abubakar ke tamabaye shi kasuwa. Ya amsa masa da Alhamdulillah. Shiru ne ya biyo baya kafin Sale ya yi magana ya ce. "Yaya na ce me zai hana ka kawo Ahmad Gidana ya zauna, tun da ka gajara ƙara aure." Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Ban hana ka ɗaukar Ahmad ba sobida kai ma uba ne a wajensa kamar yadda nake uba. Abu ɗaya ya yi mu da ni da kai uwa ɗaya uba ɗaya, to akan ne zan maka iko da shi. Cikin farin ciki duk suka yi sallama tare da cewa Gobe zai ya ɗauke shi. Washegari kuwa bayan ya sanar wa da Matarsa Joɗa ta yi farin ciki, don tana son Ahmad sosai. Da safe kafin ya fita ya shiga gidan Yayansa ya dauko Ahmad da Kayansa. Kafin ya yi tafiyarsa don yana zuwa Lagos kai shanu ne. Joɗa tana matukar don Ahmad sosai ba wanda zai ce ba ita ta haife shi ba. Duk da ba kowa yake kai yara ba Koda Joɗa ta sanar wa mijinta shawarar kai Ahmad makarantar boko. Bai yanke hukunci ba sai da ya sanarwa Mahaifin Ahmad, ya nuna duk masa duk hukuncin da ya yanke ka akan Ahmad daidai ne domin ɗan sa ne shi ma . *Maman Ihsan ce*✍️ 09065327995 [11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ Page2️⃣7️⃣ Ko da Koda ta sanar wa mijinta shawarar kai kai Ahmad makarantar boko, bai yanke hukunci ba sai da ya sanarwa Mahaifin Ahmad, ya nuna masa duk hukuncin da ya yanke akan Ahmad daidai ne, domin ɗansa ne shi ma. Haka aka kammala masa komai ya fara karatu. Komai Sale ne ke yi masa. Don dama ya fi mahaifin Ahmad rufin asiri. A daidai wannan lokacin Joɗa ta fara laulayin ciki. Kuma cikin na wahalar da ita. Abubuwa suka yi wa Sale yawa, ya ɗan dakatar da wasu tafiye-tafiye da zai yi. Abubakar ne ya tashi da zazzaɓi mai zafi sosai hankalin Sale ya tashi sosai. Ya ɗauke shi zuwa asibiti. Shi ya dinga jinyarsa. Ahmad ya dinga kuka don ya yi wayau ya san abun da ke faruwa. Kwanansu biyu a asibiti Allah ya yi masa cikawa. Sale ya sha kuka Sosa don har sai da ya suma, Kasancewa Abubakar kadai ne ɗan uwansa Wanda ya rage masa. Ahmad ma ya sha kuka sosai da sosai don ya san mutuwa ya san mahaifinsa ya tafi kenan, ba uwa ba uba. Joɗa kuwa Ita ma sai da ta yi rashin lafiya don dama ga laulayin ciki da take yi. Bayan kwana arba'in suna zaune a tsakar gidan kan tabarma, Sale na shan fura da Joɗa ta dama masa. Ahmad ya yi sallama ya dawo daga makaranta. Gaishe su ya yi Joɗa ta masa alama da yazo gare ta. A hankali ya taka bayan ya cire Sandals din makarantarsa, kwantar da shi ta yi saman cinyar ta tana shafa kansa. Ganin kamar yana cikin damuwa ta ce. "Me yake damunka?" "Yanzu ni ma na zama Maraya ban da mama da Ba..." Hannu ta sa ta toshe masa baki ta ce. "Ka da ka sake kiran kanka maraya, domin kai ba Maraya ba ne tun da kana da mu ni ce mahaifiyarka ga kuma mahaifinka." Ta ƙarasa maganar tana nuna Sale dake kallonsu yana murmushi. Sannan ta ɗora da cewa. "Nan da watanni kadan zan haifa maka ƙani ko ƙanwa." Murmushi ya yi har sai da ƙananan haƙoransa suka bayyana. *Bayan watanni Bakwai* Wata ranar Litinin Joɗa ta tashi da naƙuda, wata maƙociyarsu ce Saleh ya kira. Dattijuwa ce da taimakon Allah da taimakon ta Joɗa ta haihu. Ta haifi ƴa mace fara kyakkyawar gaske, son kowa ƙin wanda ya rasa. Ranar suna aka saka wa yarinya suna Na'ima, murna da farin ciki a wajan su ba'a magana. Ahmad ya na matukar kaunar ƙanwar ta sa sosai. Ko kukanta ya ji ya yi yawa shi ma zai yi kamar zai yi kuka. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yaye Na'ima. Shakuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Ahmad da Na'ima. Kullum yana ɗauke da ita inda sun rabu sai dai idan makaranta ce zai tafi, nan ma har kuka take yi za ta je. Idan ya tafi ya barta daƙyar take yin shiru sai Joɗa da Sale sun sha aikin rarrashi. Lokacin da ta cika shekaru uku aka saka ta makaranta ita ma, lokacin Ahmad na ajin karshe a primary school. Tare suke zuwa kamu na su gwanin sha'awa ba wanda zai ce ba su ne suka haifi Ahmad ba. Ɗan ƙaramin gidan da Mahaifin Ahmad ya rasu a ciki shi ne kawai mallakinsa, don dama shi ba mai shi ba ne, hakan ya saka Sale yake taimaka masa, har yakarbi Ahmad ya saka shi a makaranta. Zuwa lokacin kuwa dukiyar Sale sai bunƙasa take yi. Don shanu ne da shi sosai, ga filayen da ya siya ya ajiye a matsayin ƙadarori. Don ya tashi a gidan da yake ya siye babban gida ya koma, ga ɓangaren kiwo ta bayan gidan, sai dai akwai ƙofa daga cikin gidan da za ta sada ka da filin da ake kiwon. *Bayan shekaru goma sha biyar* Wata ƙyakyatawar yarinya ce tsaye a bakin titin a gaban wani makaranta, kallo ɗaya za ka yi wa makarnata ka san cewa makaranta ce ta ƴaƴan masu hannu da shuni. Sanye take da uniform ɗin makarantar riga da wando sai ƙaramin hijabi iya wuyanta. Wata lokaci-lokaci take kallon agogon hannunta yana ware Idanunta tare da tura baki gaba. Wata baƙar mota ce ta tsaya a gabanta tura baki ta yi tana kau da kai . Murmushi ya yi tare da cewa. "Tuba nake." Shiga ta yi tare da buga marfin motar da ƙarfi. "Ai sai ki ɓalla Mani marfin motar." "Wallahi Yaya Ahmad ka ɓata Mani lokaci ga shi na gaji." "Sorry ƙanwata ka da ki damu tun da yazu kin kammala zana waec da neco ai sintirin nan ya ƙare ko?" Banza ya masa kamar ba ta ji me yake cewa ba, don haka ya ce "Amaryar duk gajiyar ne?" "Wallahi na gaji ni kam Yaya kana damuna." "Kin ga ni kam ina cikin farin ciki, don daga yau ki fada ƙirga kwanakin aurenmu." Jin ta yi shiru ne ya saka shi cewa. "Na'ima." "Yaya." Ita ma ta kira shi. A hankali ta bude Idanunta ta sauke akansa . "Ina son fa na ci gaba da karatuna kafin na yi aure sai na shiga University." Dariya ya yi tare da cewa. "Ai kin san cewa ba za'a bari ba ko?" "To bayan mun yi aure za ka bar ni ko?" "Ban sani ba amma sai yadda ta kasance." A wani katafaren gida motarsa ta tsaya, horn suka danna aka buɗe masu gate. Shiga suka yi ya yi parking din motar, kusan a tare suka fito daga cikin motar. Hajiya Joɗa na zaune a kan kujera mai zaman mutum uku. Na'ima na shiga ta yi kira da jakarta ta karasa ta kwanta jikin Joɗa. "Wash na gaji." Ahmad ya gaida Joɗa ya shiga ɗakinsa. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka tsaida ranar auren Ahmad da Na'ima. Don saura sati biyu

Chapter 14 of 39