dad'i ka ga ana cin mutumcin iyayenka ka ƙyale, da ake yi wa Mahaifina ina kallo har da murnushi kake, yanzu da na mayarwa mahaifinka da martani ka ji zafi ko?"
Yaa Mahmud ne ya rike hannun ƙanin na sa Sadik yana cewa
"Ya isa haka Sadik."
Zai yi magana amma ganin kallon da Abbi da Ummi ke masa ya saka ya yi shiru. Don da ido sukan tsawatar da yaransu kuma su hanu.
Daidai lokacin Maryam, Nadiya, Kausar, Nabeela suka fito daga kitchen hannunsu rike da food flask. Kasancewar Hilal ya saka su yin girkin dole tun daga ranar tare da su ake girki kuma suke service ɗin mutanen gidan dokar da Hilal ya saka masu kenan.
Papa da Dada ne suka fito tun daga nesa suka hango Mansur da Sadik suna yi wa junansu kallo mai cike da gargaɗin juna.
Gyaran murya Papa ya yi wanda ya saka kowa shiga taitayinsa. Don ba wanda baya baya shakkar Papa a familynsu gabaɗaya.
Kowa ya nemi wurin zama. Sai dai masu zuba abinci ne kawai a tsaye suna serving ɗin su.
Kowa ya gaida Papa da Dada cikin girmamawa. Ganin ba Zahrah ne ya sa Papa cewa.
"Ina Zahrah?"
Ummi ta ce.
"Na barta ta fito wanka ta ce tana zuwa ga ta shiru har yanzu."
"Idan ta ji yunwa ai za ta fito da kanta, yunwa ba ƙanwar uwa ba ce uwa ce da kanta."
Aunty Laila ta yi maganar tana tura soyayyen ƙwai a baki.
Kafin kowa ya yi magana sai ga Zaharah ta ƙaraso da sallama. Kasancewar ta gaida iayakinta da yayunta shi ya sa da ta yi sallama ta suka amsa gabaɗaya, don su Papa na wajen ne kowa ya amsa mata.
Cikin girmamawa ta durkusa ta gaida Papa da Dada. Suka amsa mata cikin sakin fuska da walwala cike da so da ƙaunar da suke mata. Kuma ba komai ya saka suke son ta ba sai don halayyar ta da ɗabi'unta wanda ya sha banbanci da sauran yaran gidan.
Daddy ta fara gaisar wa, ya amsa mata kamar an yi masa dole. Daga nan ta gaida Abba shi ma haka ya amsa mata.
Daga nan ta gaida su Mom suka yi kamar ba su ji ba, sai da Papa ya yi fada suka ba shi haƙuri wai ba su ji ba ne.
Kallon su Mansur ta yi da niyyar gaishe su duk da ta san ba amsawa za su ba Sadik ya dakatar da ita ta hanyar watsa mata harara, tura baki ta yi ta zauna. Zaman ta ke da wuya sai ga kiran Ammar ya shigo wayarta.
Ɗauka ta yi tare da yin Salma ta ce.
"Assalamu alaikum, Yaa Ammar zan kira ka anijma."
Gabaɗaya kowa ya kalle ta, Nabeela da Kausar na sakin tsuki a tare.
Ruwan shayi kawai ta ɗiba sai bread. Don ba z ta iya cin girkin su ba, don ba dad'i yake yi mata ba. Dada da aka zuba mata farfesu kasa ci ta yi, Papa ne ya ɗan ci dankalin turawa ya ɗan ci, nan ma ya ji bai soyu ba. Haka ya ajiye .
Yaa Mahmud da Yaa Sadik da suka saba da daddaɗan girkin Ummi da na Zahrah. Ba za su iya cin wannan ba.
A baya suna cin na masu aikin, amma tun da yanzu ƴan matan ba sa yarda masu aikin su nuna masu yadda za su yi komai, take za su fara masu masifa.
Abincin dai ga shi nan haka dai kowa ya ɗan tsakura ba su iya cin na kirki ba.
Haka dai a hankali kowa ya watse da wajen masu zuwa office suka tafi.
_Asadullah_
Fitowa ta yi daga bedroom ɗin sa zuwa falon. Daidai lokacin da kukunsa ya ke jera abinci a dinning table. Kasancewar yau Barrister Haris ya nemo masa kuku da zai dinga dafa masu abinci a gidan.
Sualaiman ne ya shigo kasancewar sun yi magana ya ce masa ya ƙaraso. Hakan ya saka ya fito.
Bayan kukun ya gama jera abincin ne ya karaso wajen su yana cewa
"Barka da dare Yallaɓai."
Kai ya jinjina masa ba tare da ya ce komai ba.
"An kammala jera komai a dinning table."
"Okay sannu da aiki."
Ya amsa yana barin wajen.
Asadullah ya kalli Sulaiman ya ce.
"Idan Allah ya kai mu da safe za su tafi tare da Doctor Isma'il. Sai dai mu yi mata addu'ar Allah ya bata lafiya. Na san duk in da iyayenta suke hankalinsu ya tashi sakamakon rashin sanin halin da take ciki ba."
Jinjina kai Sulaiman ya yi sannan ya ce.
"Gaskiya ne, da irin wannan gara ko gawar ɗanka ne ka gani ka san cewa ka rasa shi da rashin sanin halin da yake ciki."
"Ka gwada yin bincike ko Allah zai sa a samu bayanin in da iyayenta suke."
"Okay sir."
Sannan abu na biyu, ina son duk in da family Doctor na mu yake, ka tabbatar ka kawo Mani shi a cikin gidan nan, saboda duk da wani lokacin ba na sanin abin da ke faruwa amma tabbas ba zan mance fuskarsa ba, kamar yadda na baka labarin komai."
"Bayan shi ba za ka iya tuna komai ba?"
"Ba abin da zan iya tunawa, sai dai yakan yi waya a gabana, da alama umarni yake karba, bayan ya yi Mani allura ba na sake sanin komai."
"Kar ka damu zan kamo shi zai yi bayanin wadanda suka saka shi wannan aiki."
"Ka tashi ka je ka ci abinci."
Tashi ya yi ya nufi dinning area.
Asadullah kuwa ya nufi ɗakin da su Jidderh suke. Sai da ya yi knocking Aninsa ta amsa sannan ya shiga .
Jidderh na zaune tana kallon TV kamar Idanunta za su fito, Anisa na zaune a gefenta tana danne-danne a waya.
"Barka da dare."
Anisa ta faɗa tana ajiye wayarta.
Zama ya yi gefen Jidderh yana sakin murmushi.
"Kallo ne haka kamar za ki fitar da Idanun waje?"
Kallonsa ta yi ganin yana mumrmushi ita ma ta masa tana kallonsa.
"Gobe da safe za ku tafi Allah ya baki lafiya."
"Amin."
Cewar Anisa tana murmushi, kallonta ya yi ya ga shi take kallo fuskarta dauke da murmushi.
"Ku fito ku ci abinci."
"To za mu fito."
Ya fita ya bar su. Yana fita Anisa ta dauki waya ta kira Barrister Haris.
Yana ɗagawa suka gaisa .
"Wai Yaya Haris Meye tsakanin Asad da yarinyar nan, ina nufi alƙarsu da ita?"
",Aiki ya kai ki ko binciken dangantakar su da yarinyar?"
"Aiki mana."
"To ki tsaya iya abinda ke gabanki."
Tura baki ta yi kafin ta kashe wayarta.
Tashi ta yi tana sake zaman riga da siket dake jinkinta, wanda kamar za ta yi nishi su yage. Don sun bayyanar da surar jikinta sosai.
Ba tare da mayafi ko hijabi ba ta tashi tana jan hannun Jidderh wacce ke zaune sanye da doguwar riga kanta ba ɗankwali. Gashinta da Anisa ta gyara mata ya sauka a kafaɗarta da ta tufke mata shi.
Jin kishin yarinyar ta yi don haka ta dauki hula bayan ta nannaɗe mata gashin ta saka mata hula don kar ma ya birge Asadullah idan suka je.
Tare suka fita tana rike da hannunta suka fito daidai lokacin da Sualaiman zai tafi, Asadullah na sake tabbatar masa gobe ya tabbatar ta zo da Family Doctor na su ko ta halin yaya.
"Okay sir, good night."
Ya faɗa ya fice.
Asadullah na zaune a dinning chair yana shan shayi, Anisa ta zaunar da Jidderh kan kujera sannan ta zauna ka. Kujerar dake fuskantar Asad.
Zuba wa Jidderh jollop ɗin cuscus ta yi sannan ta zuba na ta, sai farfesun kazar da ta zuba masu. Nan suka hau ci bayan ta zuba masu ruwa da lemo.
"Yallaɓai na zuba maka ne?"
"No need."
Ya faɗa. Yana kallon Jidderh dake cin abinci.
"Amma na ga ruwan shayi ba abinda zai maka."
"Haka nake buƙata."
Ganin yadda hankalinsa ke kan Jidderh ya saka Anisa ba wa Jidderh kulawa na musamman har tana ba ta abinci a baki. Hakan ba karamin daɗi ya masa ba. Har ya saki jiki suka fara fira da Anisa kuma duk akan Jidderh.
Tana ƙoƙarin bugun cikinsa don gane dangantar dake tsakanin su. Amma bai ba ta damar jin abinda take son ji ba.
Sai dai ta gane cewa ta hanyar Jidderh ne kawai haƙanta za ta cin ma ruwa. Don haka sai nata saki murmushi da ita kadai ta san ma'anarsa.
Kati ya mika mata mai ɗauke da lambar wayarsa.
"Idan kun je can sai ki nemi ni bayan an saka maki kayi na can ƙasar."
Tashi ya yi yana yi masu sai da safe ya haura upstairs. Anisa na masa murmushi har ya ɓacewa ganinta.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
*Albishir! Albishir!! Albishir!!!*
Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku.
Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇
Flasks
Cups
Dinnerset
Kitchenware
Pot
Jugs
Food processor
bedsheet lamps
Second hand gas
Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣0️⃣
Tashi ya yi yana yi masu sai da safe ya haura upstairs. Anisa na masa mumrmushi har ya ɓacewa ganinta.
Yana shiga bedroom ɗin sa ya zube kan gadon. Abubuwa sun yi masa yawa a cikin kansa. Kullum da tunani yake kwana. Ba abinda ya fi tsaya masa a zuciya kamar idan ya tuna zancen da ya ji Doctor na yi a waya lokacin da suke masa allurai.
"Ka ga ka kwantar da hankalinka ba kai kaɗai ke son ganin bayan Asadullah ba. A cikin gidan nan ma maƙiyansa ne zagaye da shi. Kuma sun yi mani tayin makudan kudade idan na kashe shi. So ka bi komai a hankali , yanzu haka allura da magungunan da nake bashi a hankali suke raunana jinsa da ganinsa, za su yi masa illar da zai rayuwar da gwamma mutuwarsa ma akan rayuwarsa, domin rayuwa ce mara amfani ka jira lokaci."
Hawaye ne ya ci ya ciko Idanunsa, domin ya san alluran da magungunar da ake masa amfani da su ba don ƙarfin iko na Ubangiji ba da yanzu ba wannan zanen ake yi ba.
"Su waye suka saka ka, lallai ina bukatar waɗan nan amsoshin daga bakinka Doctor."
*America/New York City*
Motoci guda uku ne suka shigo harabar gidan, kai tsaye wajen da aka tanada don parking motoci suka nufa.
Mitacin na tsaya wa suka fara fitowa daga cikin motar yayin da James ya fito ya buɗe wa Hilal ɓangaren da yake.
Fitowa ya yi tare da zubawa motar wata motar da suka ganin Idanu. Bayan ya ɗauke idanunsa daga kallon motar ya sauke su akan sojan da ya bari yana gadin gidan.
Tsoro ne y bayyana a Idanunsa ganin irin kallon da Hilal ke jifansa da shi. Cikin rawar murya ya fara magana.
"Sorry sir wallahi ba laifina ba ne, sai da na ce kar ta shiga oga ya hana amma ta wuce ba ta saurare ni ba."
Shi kaɗai ya nufi ƙofar da zai shiga yayin da James ya bishi da jakarsa.
Yana tura ƙofar ya sauke Idanunsa akan wayarta dake ajiye a saman ɗaya daga cikin kujerun falon.
Alama ya yi wa James da ya ajiye ta fita. Take kuwa ya ajiye ya fice bayan ya ka masa kofar ya rufe.
Bedroom ɗin sa ya nufa ya fara cire hularas. Riga kakinsa yake ƙoƙarin cire wa ta turo ƙofar ta shigo.
Dakata wa ya yi daga cire rigar ya juya ya kalle ta da rikitattun idanunsa fuska ba fara'a. Yayin da ita kuma sai murmushi take sakar masa.
"Barka da dawowa soja na."
Cewarta cikin harshen Hausa. Daga jin Maganar ta za ka fahimci cewa cikakkiyar bahaushiya ce, sai sai dai zama a cikin turawa ya saka yanayinta da shigarta ba za ka taɓa cewa bahaushiya ba ce.
Suraiya kenan ƴa ga ga wani minister Abdulƙadir Muhammad kenan. Ita kadai ce ƴa ɗaya da Allah ya bashi, ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata. Mahaifiyarta ta rasu kuka ba ta jituwa da matar mahaifinta saboda gafara da take nuna wa matar uban. Akan dukiyar da mahaifinta ya tara mata. Tun da ta gama karatu ta komawa gida Nigeria ta tare a nan ƙasar Amurika. Tana sheƙe ayarta da turawa. Sai lokaci zuwa lokaci yake zuwa ta ga mahaifinta da kakanninta su ma sai ta gaji da mita kafin ta je. Sai dai mahaifinta na yawan kawo mata ziyara ƙasar.
Fuska ba annuri Hial ya cire hannun Sumayya wacce suke kira da Sury.
"Me ya kawo ki gidsn nan, sau na wa nake fadar cewa idan ban bukaci mace ba kada ta zo mani a nan."
Madadin ta damu sai ma murmushi ta yi masa.
"Ai ni ta daban ce shi ya sa."
Ta bayansa ta rungume shi tana dariya ta yi maganar."
"Sury don Allah ki barni abubuwa sun yi Mani yawa a kaina, ina bukatar hutu."
"Why not ka huta a jikina na san za ka samu mutawa ka yi duk abinda kake so cikin kwanciyar hankali."
Ta sani sarai baya taɓa yin sex da mace, amma lokuta da dama yakan rage zafi da ita. Ko shi din ma sai idan shi ya nemi hakan. Har ta fara tunanin cewa ko baya da lafiyar mazantaka ne, ganin zai yi wasa da mace har ya kai ƙololuwa amma da zaran ya yi kamar zai yi sex da mace sai ya fasa.
Kasancewar magrib ta gabato ne ya saka ya yi saurin cire ta daga jikinsa. Tana shirin sake shige masa sai ta ja baya, sakamakon kallon da ta ga ya jefa mata.
Cire kayansa ya yi ya saura daga shi sai boxer ya nufi bathroom. Ta bi shi da kallo tana tura baki.
"Na rasa wani irin mutum ne wannan, sai ya yi ta ji da kansa don ya ga ana binsa."
Ficewa ta yi daga cikin ɗakin ta koma ɗaya daga cikin bedroom dake falon.
Nan ta ajiye jakar Kayanta. Sai mita yake take yi. Akan halin Hilal ɗin. Shi ba ma harka da shi ba, sai kun fara more juna ya kai ka ƙololuwa madadin ya biya maki bukata sai ya bar ki cikin halin matsuwa. Amma ina mai tabbatar maka in dai Ni ce sai ka yi abinda kake gudu. To wai ma Meye a ciki, wanda har ua iya wasa da mace ya sunmbace ta son ransa ya luguiguita ta son ransa amma ya ce yana gudun sex to me ya rage, ai idan za ka sha giya ka sha ta dubu."
Ita ma wanka ta shiga yi don tana son wannan daren ya kasace na musamman ne a wajenta.
Ko da ya fito daga wanka man shafawansa ya shafa, da turare. Sannan ya saka gajeren wando ya saka jallabiya.
Sallar magrib ya yi sannan ya zauna akan sallaya yana lazimi.
Sai da ya ga lokacin sallar Isha'i ya yi sannan sai gabatar.
Falo ya nufa don ya samu shayi ya sha.
Kitchen ya shiga, ba jimawa ya fito da mug ɗin shayi a hannunsa. Kasancewar ya san ba shi kadai ne a cikin gidan ba. Hakan ya saka ya koma bedroom ɗin sa don baya son damuwa.
Zama ya yi kan sofa akwai Centre table dake gabansa system a gabansa yana bincike. A hankali yake shan shayin. Har ya shanye.
_Asadullah_
Tare suka fito zuwa harabar gidan. Shi da Barrister Haris sai Doctor Isma'il da zai jagoranci tafiyar su Jidderh. A baya kuma Anisa ce tare da Jidderh.
Har parking lot Asad y raka su. Barrister Haris ke driving gefen sa mun Doctor Isma'il.
Sai Anisa da Jidderh dake bayan motar. Addu'a ya yi masu da fatan alkhairi kafin suka bar gidan yana ɗaga masu hannu.
Suna barin gidan Asad y kira Sulaiman a waya bayan sun gaisa ne ya ce.
"Ya ake ciki ne?"
"Na bari ne sai na fara kawo maka maci amanar likitan nan kafin na bincike in da iyayen yarinyar suke."
"Okay."
"Yanzu haka na fito zan je gidan Doctor ɗin ne, idan ban same shi ba zan je asibitinsa ne."
"Ina jira."
Daga nan ya katse wayar ya shiga cikin gidan.
_Doctor_
Fitowa ya yi daga cikin gidansa ya shiga motarsa zai tafi asibitinsa.
Yana tsaka da tafiya akan tati sai wayarsa ta yi ruri, ganin mai kiran wayar ya sa ya samu gefen hanya ya tsaya.
Shiru ya yi kafin ya ce.
"Okay."
Fitowa ya yi daga cikin motar ta sa ya tsaya gaban motar har lokacin waya na kunnensa.
Ba zato ba tsammani wata babbar mota ta yo kansa gadan-gadan, kafin ya aknkare ta bi ta kansa.
Daidai lokacin da motar Sulaiman ke ƙarasowa wajen.
Babban motar kuwa barin wajen ta yi jama'a aka yo kan Doctor ana salati.
Duk wanda ya kalle shi ya san cewa rai ya yi halinsa.
Cikin sanyin jiki Sulaiman ya shiga motarsa ya bar Wajen.
Wasu kuwa duk da sun san baya da dai bai hana su ɗaukarsa zuwa asibiti ba.
Tuki Sulaiman yake yi amma gabadaya ba ya hankalinsa na ga abun da ya faru.
"Marasa mutunci kawai."
Har ya karasa gidan Asad yana cikin damuwa.
Kallon fuskarsa kawai Asad ya yi ya gane cewa akwai matsala.
"Laflya meke faruwa?"
"Sun kashe shi."
Ya faɗa yayin da yake kokarin zama a daya daga cikin kujerun falon, yayin da kuma Asad ya mike zumbur kamar wanda aka tsikara.
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un. Su waye suka kashe shi.?"
Shiru ya yi masa ya rasa wace amsar zai ba shi.
"Ina tambayarka ka yi Mani Shiru."
"Ban san su waye ba, amma na san hakan za ta iya faruwa. Saboda sun san cewa ka kuɓuta kuma tun da su ba ka san su ba sun san dole za ka nemi sanin su waye, ta hanyar Doctor kawai za ka iya gane ko su waye. Saboda shi ne tsanin dai zai kai ka zuwa gare su. Shi ya saka suka sa mota ta taka shi yadda ba ka da wata hanyar da za ka iya gane su."
Dafe kai Asad ya yi cikin damuwa ya ma rasa abun da zai ce.
"Waye zai yi mani wannan aikin Sulaiman?"
"Yallaɓai Allah shi ne masani. Amma gaskiya duk ma waye ya shirya wannan munaƙisar na cikin gida ne."
"To na rasa akan wane dalili ne na kusa da ni zai yi mani haka, Meye ban masu ba. Na dauke masu nauyin komai cin su shan su suturarsu da laflyarsu duk a wuyana yake. Motoci kudade Ga gabadaya mansion ɗin nan ba abinda da ban ɗauke masu ba. Amma suke ƙoƙarin ganin bayana why?"
Ya karasa maganar yana hawaye.
Tausayinsa ne ya cika Sulaiman.
"Ba abinda ka yi masu, jarabawa ne Allah ya baka ikon cinyawa."
"Amin ya Allah."
Ya furta cikin sanyin murya.
_Zahrah_
Tana zaune babban falon gidan tana karatu saboda za su fara text. Kasancewar tana da son karatu ya sa ba ta wasa da ta samu zama za ta fara karatu.
Kausar ita da Nabeela ce suka zo suka same ta. Harara suka watsa mata sannan Nabeela ta ce.
"Ke lambar Yaa Ammar za ki ba mu."
Karatun ta take yi ta cigaba da yi ba tare da ta ɗaga kai ta kalle su ba. Musamman da ta san cewa ko magana ba ya haɗa ta da su. Don haka ba ta kai hankali wajensu ba ballantana ta san cewa da ita suke yi."
" Ke!, magana fa muke yi da ke amma kin mana banza waye sa'anki a nan?"
Sai a lokacin da ɗaga kai ta kalle su, jin yadda suka daga mata tsawa wai kuma suna kiranta da ke, su sun fi karfin su kira sunanta.
Ci gaba da karatu ta yi ba tare da ta bi ta kansu ba.
Kausar ce ta ƙwace takardar a hannun Zahrah. Zahara ta mike tsaye tana cewa.
"Wai me ya saka kuke neman tashin hankali ne a tare da ni?"
"Dan wulakanci kuna jin ina maki magana kuka share ni?"
"Na ji kuna cewa ke, ni kuma ba suna na ke ba."
"Lallai yarinyar nan ba ta da mutunci."
Cewar Nabeela tana kallon Kausar. Ita ma Kausar ɗin kallonta ta yi kafin ta sake magana cikin isa da gadara."
"Lambar wayar Yaa Ammar za ki bani."
"Ba na da shi ."
Ta fada tana ci gaba da karatun da take yi. Da mamaki suke kallonta jin kalamanta.
"Za ki bayar ko sai kin sh wahala kafin ki bayar?"
Ba ta ce masu komai ba ta cigaba da karatun ta.
Barin wajen suka yi, karatun da take yi ta cigaba da yi.
"Ba jinawa sai ga su sun fi dawo kowacce ta kaskon turaren wuta an zuba gawayin kanti suna zuwa suka buɗe wata kwalba suka zuba turaren a cikin garwashin da yawa su duka biyu suna kora hayaƙin da hannu daidai saitin fuskarta.
Jin haka ya saka ta ɗago da sauri zata mike ta bar wajen.
Ganin haka Kausar mayar da ita ta karfi ta zauna.
Kafin ka ce me har numfashinta ya fara barazanar ɗauke wa.
Hakan bai saka sun dau7kata ba sai ma ƙara turaren wutan suke a cikin wuta. Wanda ƙamshin sa ma ba dad'i sai uban hayaƙi
Take ta fita daga hayyacinta tana ko omarkn barin wajen ta kasa take da ke ta sume a wajen.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
*Albishir! Albishir!! Albishir!!!*
Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku.
Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇
Flasks
Cups
Dinnerset
Kitchenware
Pot
Jugs
Food processor
bedsheet lamps
Second hand gas
Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣1️⃣
Take ta fita daga hayyacinta tana kokarin barin wajen ta kasa, take ta sume.
Barin wajen suka yi ba tare da tausaya wa ba suka bar ta a wajen.
*America/New York City*
Har dare ya fara tsalawa bai kwanta ba, yana nan yana wani binciken a cikin computer.
Sury ce ta shigo ɗakin sanye da rigar barci wanda babu maraba da tana tsirara. Yana jin ta bai tanka mata ba ya cigaba da aikinsa. Har mamakin karfin halin yarinyar yake yi.
Ta zo ta tare masa gida ba tare da izinisa ba, sannan tana ƙoƙarin ta saka shi abun da bai yi niyya ba, kuma bai bukata ba. Ya ƙudura a zuciyarsa yau zai nuna mata iyakarta. Shi ba'a masa haka, idan bai bakaci mace ba ba ta zuwa in da yake.
Tana rangad'a da yanga ta karaso wajen da yake zaune.
Zama ta yi a gefensa tana manna jikinta da na shi.
"Har yanzu ba ka yi barci?"
Bai tanka mata ba daidai lokacin da ya kammala abun da yake yi ya rufe computer.
"Jarumina, na yi kewarka wallahi ina son ka don Allah ka yarda mu yi aure mana."
"Ni kuka ba na son ki ko kaɗan."
Rintse Idanunta ta yi cike da jin ba dadin jin kalamansa masu tarwatsa zuciya ta ce.
"Me ya saka?"
Ta yi maganar tana shafa gefen fuskarsa tare da matso da fudkarta dab da ta shi za ta sumbace shi ya daka mata tsawa.
Wan da sai da ta firgita da jin tsawar sannan ya nuna mata hanyar fita.
Da mamaki take jallonsa me yake nufi da ita ne yau. Ko dai ta fara gundurarsa ne.
Tana tsaka da tunani sai ta ji ya finciki hannunta.
"Meke faruwa ina za ka kai ni?"
Bai saurare ta ba ya cilla ta zuwa falo, sannan ya ɗaga mata hannu yana nuna ta da yatsa alamar gargaɗi ya ce.
"Kar na sake ganinki a inda nake sai dai idan ni ne na neme ki, kuma ki tabbatar kafin karfe takwas na safiya kin bar gidan nan."
Daga nan ya tura kofarsa ya shiga ya bar ta nan durƙushe tana kuka.
Sai da ta yi kuka mai isar ta sannan ta tashi ta shiga bedroom ɗin da kayanta suke. Tana shiga ta fada a kan gadon ta kufa ciki tana hawaye. Sai dai duk wulakancin da ya mata ba ta jin za ta fita daga harkarsa.
A haka barci ya ɗauke ta ba tare da ta sani ba.
Ba ita ta farka ba, sai karfe bakwai na safiya, tunawa da gargaɗin da ya yi mata ya sa ba ta tsaya wani ɓata lokaci ba ya tattara na ta ya nata ta bar gidan, don yadda ta ga fuskar nan ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 39