tare da cewa
"Ga tsarabar ki nan gimbiyata."
Kallon kayan ta yi tare da cewa.
"Yaa Ammar don Allah ka bari na dauki ɗaya sun yi yawa, dayan ma na don Ummi ma sai ta yi faɗa. "
Duk yadda ta yi akan su rage kayan ba su saurare ta ba suka fice suna mata sallama.
Ba ta da wani zaɓi ta ɗauki kayan niƙi-niƙi ta nufi part ɗin Dada, don tana tsoron Ummi, saboda Ummi ta hana ta karbar komai daga hannun wani ɗa namiji.
Da sallama ta shiga wajen Dada, tana kokarin shiga bedroom ta ga Zaheah da kaya niƙi-niƙi a hannunta.
"Wadan nan kayan daga ina haka?"
Kamar za ta yi kuka ta fara magana.
"Yaa Ammar ne ya bani, kuma Ummi za ta yi Mani faɗa ya sa na kawo nan, na ce ya rage kayan amma ya ƙi."
Shiru Dada ta yi kafin ta ce.
"Umminki ba ta yi laifi ba gaskiya, domin babu amfanin ki yi ta karɓar abun samari bayan ba aurensa za ki yi ba."
Da sauri ta kalli Dada jin zancen ta, Allah ya sani tana don Ammar har cikin zuciyarta.
"Kada ki damu ki yi addu'ar Allah ya zaba maki mafi alkhairi a gare ki, idan Allah ya sa Ammar mijinki ne sai kin aure shi."
Jinjina kai ta yi tare da cewa.
Ki kai kayan ɗakinki daga wannan ɓangaren ba ɓangaren Umminki ba, zan yi magana da ita in sha Allah."
Daga haka ta kai kayan bedroom ɗin ta dake kusa da bedroom ɗin Dada, sannan ta yi mata Sallamar za ta koma part ɗin Ummi."
"Ba nan za ki kwana ba ne?"
"A'a wajen Ummina zan kwana sai da safe."
Daga nan ta fice Dada na cewa.
"Yarinyar nan ƴar ganin dama ce, sai in da kika dama za ki kwana ko? To Allah ya tashe mu lafiya."
Daga haka ta koma part ɗin Umminta.
*Washegari*
Kamar yadda Ammar ya ce zai zo bayan kwana biyu kasawa ya yi, sai ga shi ya zo a ranar. Ko da ya kira ta a waya lokacin tana part ɗin Dada.
Don cewa ya yi ta fito ba zai shiga ciki ba, don baya son Mummy ko Aunty Laila su sake ɓata masa rai ko su ɓatawa Zahrah rai.
Sanye take da hijabi har ƙasa onion colour ya mata kyau.
A hankali take tafiya wanda tun da ya hango ta ya fito daga cikin motar.sanye yake cikin ɗanyar shadda fara, ɗinkin daidai jikinsa na zamani wanda ya dace da shi. Sai baƙar hula da bakin takalmin dake ƙafarsa, ƙamshin turarensa ke tashi a jikinsa ya rungume hannayensa a ƙirjinsa yana sakar mata sanyayyar murmushinsa.
"Assalamu alaikum"
Zazzaƙar muryarta ta daki don kunnensa. Sai da ya lumshe Idanu ya bude a kanta kafin ya amsa mata.
"Ina wuni Yaa Ammar."
"Lafiya lau. Ya ƙarfin jikin?"
"Alhamdulillah na warware."
"Yau ba zan shiga ciki ba"
Hakan ya saka ta nufi wajen kujerun da aka tanada dan zaman shan iska daga can gefe.
Bin bayanta ya yi suka zauna suna fuskantar juna. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle.
*America/New York City*
Dawowarsa kenan gidan ya ɗauko ruwa a fridge, tsiyaya wa ya yi a kofin glass zai sha. Wayarsa ce ta soma ringing, ya duba ya ga Mummy ce.
Ɗaukar wayar ya yi ya kara a kunnensa, ya dauki kofin ruwa ya riƙe.
"Hello Mummy dawowa na kenan, ina son idan n huta na kira ki."
"To ya kake ya aiki?"
"Alhamdulillah Mummy."
"To ma sha Allah."
Ta fada kafin ta ce.
"Wai abokinka nake son ka ba shawara."
"Wane abokin kike nufi Mummy."
"Ammar mana."
Ruwan da ya zuba a kofi ya sha kafin ya ce.
"Okay."
Ya ce yana jiran jin abun da za ta ce
"Wai shegiyar yarinyar Zahrah zai aura, kuma ya samu goyon bayan Kakarku."
"To ni me zan yi akai?"
Ka bashi shawara yarinyar nan fa Yar iska ce bin maza take yi, ta sha zubar da ciki, ja bashi shawara ya rabu da ita ya nemi wata ya aura."
"Mummy saboda wannan dalili ya saka kika kira ni?"
"Eh mana, Hilal na san Ammar ba ka da wani abokin sama da shi zai ji maganarka."
"Mummy ki mai da wajen abun da yake gabanki. Na gaji yanzu zan huta sai mun sake magana."
Bai jira cewarta ba ya katse kiran wayar.
Daga can ɓangaren kuwa Mummy kallon wayar take yi tana mamaki.
Kallon wayar kawa ta yi tare da ajiye wa.
"Dama na sani yaron nan ba zai taba saurara ta ba, duk maganar da zan masa, ya fifita waɗan can tsofaffin akan kowa, su kadai za su yi masa magana ba zai tsallake ba, ba zai yiwu ba dole na yi wa tufkar hanci. Idan ba haka ba ina ji ina gani zai fi karfina."
"Fin ƙarfinki na nawa kuma ?"
Da sauri ya juya ta kalli Aunty Laila dake tsaye a bakin ƙofa.
"Ai Hilal dama tun can baya jin maganarki ko na Mahaifinsa, mutum daya ke masa magana ya ji shi ne Papa sai kuma Dada, su yi iko da ɗa sannan su yi da jika."
Jikin Mummy ne ya yi sanyi, sai jin muryar Aunty Laila ta yi ta sake cewa.
"Na tabbatar da Papa ne ko Dada suka ce ya dakatar da Ammar wallahi da ya dakatar da su. Don su ya dauka uwa da uba, shakuwar dake tsakaninsa da su baya tasaninki da shi ko wani shawara da su yaje yi me kika dauki hakan?"
Shiru Mummy ta yi kafin ta ce.
"Na ɗauka shakuwa ce saboda kin san shi ne jika na farko a gidan nan, kuka tun da aka yaye shi ya fi zama da su Papa ya kan fita da shi ko Dada ma na fita da shi ko abinci ya fi cin na su na ɗauka shakuwa ce. Sai bayan ma da aka haifi shegiyar yarinyar can Zahrah na ga sun raba kaunar da suke masa gida biyu sun ba ta gida ɗaya shi na gida ɗaya. Tun lokacin da na ga Zahrah ta shaƙu da kakanni suna sonta hankali na ya tashi amma da na tuna yadda suka nunawa mahaifin ta kauna da fifiko ya sa na gane hakan ya saka ita ma soyayyar mahaifinta ya shafe ta. Na so janye Hilal daga wajan su don kada shakuwa ta shiga tsakaninsu da yarinyar amma bai saurare ni ba. Sai sai na yi nasarar cusa masa tsanar yarinyar a cikin zuciyarsa. Kuma Alhamdulillah ya tsane ta wanda na lura ba sa zama inuwa ɗaya."
Mumrmushi Aunty Laila ta yi kafin ta ce.
"Da sauran rina a kaba."
Daga nan ta juya ta bar Mummy tana aikin fashin baki akan kalmar Sunyi Laila.
Duk yadda Sulaiman ya yi kokarin ganin ya samu yayan Jidderh ya kasa. Don da ya hau titin ma bai ga mai kama da mashin ɗin da ya gan su da shi ba
Wunin ranar haka ya dinga yawo amma bai gan su ba, cikin takaici ya koma mansion ɗin.
Wanka ya yi ya canza kaya ya ɗan yana son komawa wajen uban gidansa ya sanar da shi halin da ake ciki.
Yana fitowa Falo wayarsa dake cikin aljihu ya fara ringing ɗauka ya yi tare da cewa.
"Hello Yallaɓai ban same su ba, amma gani nan zan sanar da kai komai, ka gafarce ni mai gidana na kasa cika maka burinka. Amma in sha Allah sai na samo maka su a duk in da suke, gani nan zuwa .
Yana ajiye wayar suka yi Idanu biyu da Dady da alama tun kafin ya fito yake nan, kuma alamu sun nuna ya ji duk maganar da ya yi a wayar.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: *GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/DK3nAxNaxVV6U3giyRUZQO?mode=r_c
*Albishir! Albishir!! Albishir!!!*
Jama'a na ina maku albishir da cewa na kawo maku kayan kitchen masu kyau da inganci. Za ku darje ku zaɓi kayayyaki masu dangareren kyau. Duk a cikin farashi mai sauƙi da rahusa daidai da aljihunku.
Ƴar uwata idan kina son ki damu kayayyakin da babu kamarsu masu bigewa da inganci to Hajiya ga dama ta samu .muna siyar da kaya kamar haka.👇
Flasks
Cups
Dinnerset
Kitchenware
Pot
Jugs
Food processor
bedsheet lamps
Second hand gas
Duk wani kitchens items na kayan kitchen muna saidawa. Zu ku iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 07018401887
Page5️⃣6️⃣
Yana ajiye wayar suka yi Idanu biyu da Dad da alama tun kafin ya fito yake nan, kuma alamu sun nuna ya ji duk maganar da ya yi a wayar.
Murmushi Sulaiman ya yi kafin ya ce.
"Dad yau..."
Dakatar da shi ya yi ta hanayar daga masa hannu.
"Rainin hankalin ya ishe ni haka Sulaiman, tun yaushe kake ɓoye Mani gaskiyar abun da ke faruwa?"
Shiru Sulaiman ya yi ya kasa cewa komai, in da Dad ya cigaba da cewa.
"Dama na yi tunanin abin da kake boye mani, domin na ga canji a tattatre da kai. A lokacin da Asad ya ɓata ko kuma na ce ya gudu tun da nemansa muka yi muka rasa, a lokacin ka shiga damuwa sosai ba kaɗan ba, kai ka la shiga wannan damuwar wanda duk wanda ya kalle ka ka ya san cewa kana cikin damuwa. Amma dawowar nan da na yi ban ga alamar damuwa a tattare da kai ba. Kuma na san a baya akwai damuwar saboda kana da kusanci da Asad ko zai boye wa wani kai ba zai boye maka ba."
Numfasawa ya yi sannan ya cigaba da magana cikin rauni.
"Ban san me ya ɗauke ni ba, ko kuma ya mayar da ni matsayina na mahaifinsa dole ba shiga cikin damuwa sosai ba kaɗan ba. Shi me na yi masa da ya guje Ni?"
Ya yi maganar kamar zai yi kuka. Sulaiman ya yi saurin cewa .
"Dad bai guje ka ba, yana da dalilinsa na aikata hakan, yanzu ka shirya mu tafi wajensa. Amma da sharadi."
Da mamaki Dad ke kallonsa wai shi za'a gindaya wa sharadi akan zai je ya ga ɗansa.
"Dad ba wani sharadi ba ne, ina son kada ka faɗa wa kowa in da za mu, kafin nan wannan maganar ta zama sirri a tsakanin mu, akwai dalilin hakan ne, idan muka je za ka k ji komai daga bakinsa.
Kai ya jinjina sannan ya ce .
"Muje ko?"
'
"Dad je ka shirya na ga jallabiya ce a jikinka?"
"Muje haka nan n shirin da zan yi."
Ya yi maganar cikin ɗokin zai ke ya ga gidan jininsa.
A tare suka fito har parking space suka nufa. Kallonsa Sulaiman ya yi kafin ya ce
"Dad ba Direban ka zai kai ka ba fa, ni zan kai ka da kaina kuma na dawo da kai ."
Kafin Dad ya yi maganar har Direban ya karaso Wajen, don ya ga Dad a parking space ya san fita zai yi .
"Barka da warhaka Dad."
"Yauwa Barka, ka yi zamanka a yanzu zan dawo in sha Allah, a motar Sulaiman za mu tafi."
Jinjina kai ya yi sannan ya bar wajen yana masu Allah tsare hanya.
Su kuma suka shiga motar suka bar mansion ɗin.
_Zahrah_
Suna zaune wajen shan iskar nan ita da Ammar. Fira suke yi mai cike da so da kaunar juna. Kuma da zaran ka kalli fuskokin su ka san ba karamin so suke yi wa juna ba. Don suna cikin nishaɗi sosai b kadan ba.
Mummy bayan ta gama waya da Hilal cikin takaicin yadda bai nuna damuwa akan abinda ta fada masa ba ta miƙe, jikin window ta karasa ta yaye labulen window ɗin, dama ta gansu ne shi ya sa ta kira Hilal ta sanar da shi komai.
Sake hango su ta yi har lokacin fuskokinsu cike da farin ciki.
Komawa ta yi ta zauna bakin gadon cike ta takaici.
Sallama Ammar ya yi mata don gobe yake son komawa London. Sai ya yi shiga ya yi wa Dada da Ummi sallama sannan ta raka shi parking space ya tafi. Duk da ya so shiga gaida Mummy sai dai ya san muddin ya shiga sai ya tarar da ɓacin rsi don sai ta yi masa abun da zai bata masa rai kamar yadda ya yi masa a a daren jiya.
Bayan ta ga tashin motarsa ne ya bar gidan gidan sannan ta koma ciki.
Magana ɗaya da ya yi mata ya tsaya mata a rai ta kasa yadda za ta iya sanar wa Ummi ko Abbi zancen.
Wato cewa da ya yi ta sanar da Abbi zancen zai turo magabatansa s nema masa auren ta. Ta nuna masa cewar sai ta kammal karatunta. Ya nuna mata cewar bai yarda ba kuma ba zai iya jira yana can wani ya yi masa sakiyar da ba ruwa ba, sai dai a yi auren ta cigaba da karatunta a can ƙasar London ɗin.
Da wannan tunanin ta koma ciki, sai dai ta saka wa ranta ba za ta sanar da iyayen ta komai ba, don tana son sai ta kammala karatunta na digiri kafin ta yi aure.
*America/New York City*
Sai Safa da marwa yake yi a ɗaukinsa,, gabaɗaya ya kasa gane abun da ke damunsa. Amma haka kawai yake jin zuciyarsa babu nutsuwa a cikinta .
Kalaman Mummynsa ke yawo a cikin kansa. Da maganganunta da ta yi masa da yadda ta nuna ɓacin rai da damuwa kan lamarin.
Yana tsaka da yin tunani sai ga kiran Ammar ya shigo wayarsa.
Ƙarasowa ya yi ta kalli fuskar wayar sai ya ga Ammar ne ke kira. Haka kawai sai ya ji ya tsinci kansa da jin haushin kiran da ya yi masa da kuma jin haushin Ammar ɗin shi kansa.
Sau biyu yana kira bai ɗaga ba, sai a na uku ya ɗaga cikin takaici.
Bai yi magana ba har tsawon sakanni goma, sanin ba zai yi magana ba ne ya saka Ammar yin murnushi ya ce.
"Hello."
"Ina jin ka."
Shi ne abin da Hilal ya ce masa.
Murmushi ya sake yi duk da ya san mishkilanci irin na Hilal amma yau sai ya ji yanayin da ya yi magana kamar akwai damuwa .
Don haka ya ce
"Abokina kana lafiya kuwa? Oh sorry yanzu kai Yayana ne tun da ina shirin yin auren ƙanwarka nan da watanni kaɗan."
"Abinda ka kira ni ka faɗa Mani kenan?"
"Eh. Ina neman..."
Kafin ya karasa abin da zai fada sai ya ji Hilal ya katse kiran wayar.
Gabaɗayasu ya kashe wayar don ya san in dai Ammar ne sai ya sake kiransa.
Takaicinsa ne ya karu a cikin zuciyarsa .
"Dole na tafi Nigeria a cikin satin nan,"
Ɗayar wayarsa ya ɗauka ya kunna Data. What'sup ya shiga in da ya ci karo da sakonnin mutane da yawa, kusan duka yan gidansu Tafarki Family ya ga sakonni su idan aka cire Abbi da iyalansa.
Har da sakon Ammar ya ga ya shigo a lokacin, bai bude ba ya cigaban da duba wasu sakonnin. Na Mummy ya shiga ya duba.
Voice message ne ta yi masa, budewa ya yi yana sauraro.
"Wato ni yanzu ban da mahimmancn da zan saka ka yin abu ka yi idan dai ba waɗan can tsofaffin ba ne ko? Na kira ka akan ka bawa Abokinka shawara ya janye kudirin sa na auren yarinyar nan ka yi biris da ni ko? Ai za ka iya juya masa tunani musamman da ka san yarinyar nan yar iska ce ita, ta gana yawon banza da iskancin ta ga gama zazzage 'ya'yanta a kwararo za ka bari ya aura, ina amintar ta ku yake ai ba amana. Ka dakatar da shi idan bai dakatu ba zan sanar da mahaifiyarsa ne."
Shiru ta yi kafin ta yi mata reply ta hanyar typing.
"Zan zo a cikin satin nan in sha Allah."
Daga nan ya ajiye wayar, system ɗin sa ya janyo ya cigaba da wani binciken da yake yi.
_Asadullah_
"Bude kofar falon ya yi ya sauke idanunsa akan Dad ɗin sa, sannan ya kalli Sulaiman.
"Dad dama..."
Dakatar da shi ya yi ta hanyar cewa
"Ba abun da za ka faɗa Mani, dama burina na san halin da kake ciki, kuma na sani yanzu tun da na ganka, Alhamdulillah."
Yana gama fadar haka ya juya ya kalli Sulaiman ya ce.
"Za ka iya maryar da ni gida yau ko na kira direba na ya zo ya ɗauke ni?"
Kafin Sulaiman Ya yi magana Asadullah ya ce
"Dad don Allah ka tsaya ka saurare ni, ba yadda kake tuninin na guje ka ba ne.".
"Ba abinda zan saurara daga gare ka, Asadullah ka bani mamakin ina matsayin mahaifi a gare amma wasu ne su san halin da kake ciki da ni?"
Cikin takaici ya nufi gate ɗin zai fice.
Asadullah ya bi bayansa a buɗe ya durkusa a gabansa ya rike ƙafarsa.
"Don Allah Dad ka saurare ni, wallahi ba yadda kake tunani ba ne."
Ganin Idanun Asadullah ya cika da ƙwalla ya saka Dad ya saurare shi
"Ina jin ka "
"Mu shiga ciki Dad."
Tare suka shiga ciki Sulaiman dai bai bi su ba, mai yiwuwa za su yi wani sirri tsakanin uba da ɗa.
Bayan sun zauna suna fuskantar juna ne Dad ya kalli Asadullah ya ce
"Ina jin ka."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.
"Dad na san kana zaton cewa ni na bar gida da ƙafuduna ko? To ba haka abin yake ba, a zahirin gaskiya ma sace ni aka yi bayan an gusar Mani da hankali. Dad a cikin ɗakin barcina aka shigo, kafin na juya na ga waye hakan bai samu ba, sai farkawa na yi na ganin a wani ɗaki an daure Mani hannu da baki. Da idan ba wanda yake na gida makusanci na ba wanda yake da zarra da zai iya shigo Mani har cikin ɗakin barcina . Hakan ya saka na kasa yarda da kowa. Wallahi na kwashe tsawon lokaci a cikin wannan halin. Ba wanda zan iya cewa shi ne ya yi Mani wannan aikin. Family Doctor ɗin mu shi ne yake zuwa ya yi mani allurai wandanda sauke gusar Mani da hankali
Ba na iya gane komai sai dai a duk lokacin da nake cikin wannan halin sai na ji wasu muryoyi bayan na Doctor suna bani wani takarda akan na saka masu hannu. Ta yadda kamfanin zai zama mallakinsu. Sai sai dai duk da ba na cikin hayyacina Allah bai bani ikon cika masu burinsu ba.
Tsawon watanni na ɗauka a haka kafin wata rana Allah ya kawo Jidderh. Ban san ya aka yi ta san ina wajen ba, sai dai kullum sai ta kawo Mani abinci a ɓoye."
Nan ya cigaba da ba wa Dad labarin komai har zuwa ranar da ta kuɓutar da shi da da accident da suka samu har zuwa yau.
Kuka Dad ke yi kuma ya tabbatar da Ɗan sa yana cikin makiya ne sai dai ba wanda ya san ko su waye.
"Amma ya jikin ita Jidderh?"
"Dad abun ya na bani tsoro an yi yawon asibitoci da ita nan da ƙasashen waje amma duk sakamakon ɗaya ne, wai ba wata matsala a cikin kanta."
"Innalillahi wa'inna'ilahi raji'un."
Dad ya ambata cike da damuwa, bayan ya numfasa ya ce.
"Lokacin da take cikin hayyacinta ba ta taɓa sanar da kai unguwar su ko wani na ta ba.?"
"A'a Dad tun bayan da ta je office kamfani na taimaka mata da kuɗaɗe kan matar yayanta ba ta da lafiya. Daga baya ta zo neman aiki na dauke ta. Bayan haka idan ba mun hadu a mansion ta zo aiki sai mu gaisa. Sai daga baya da ta fahimci halin da nake ciki ta taimaka ta fitar da ni."
Ya karasa magana hawaye na bin fuskarsa.
Dukkansu sun yi shiru ba wanda ya sake yin magana.
"Yanzu ya ake ciki?"
Dad ya katse shirun da suka yi ta hanyar yin maganar.
"Yanzu mun yi magana da inspector Bashir Ibrahim akan an gano in da Sagir yake , kuma za su yi iyakar kokarin su wajen kama shi, wai yana garin Lagos ne, an gano cewar wata yarinyar yake son ya aura a can."
"Okay yanzu yaushe za'a dawo da Jidderh?"
.ina tunanin za su dawo zuwa wani satin."
Shiru ya yi kafin ya ce.
"Dad ina neman alfarma a wajenka?"
"Wace irin alfarma kake nema?"
"Ba na son kowa ya san cewa na bayyana ko an gano in da nake, har sai bayan an gano waɗanda suka aikata Mani wannan aiki."
"In sha Allah ba wanda zai ji har da Mom ɗin ka kuwa."
Daga nan ya yi masa sallama don yana da meeting da zai je.
*Bayan sati ɗaya.*
*America/New York City*
Kayansa ya gama jerawa a cikin trolley bag ɗinsa ƙarama kasancewar ba kaya da yawa ya ɗiba ba, kayansa na can ma sun ishe shi. Fitowa ya yi. Don ba zai je tare da kowa ba ko James ba zai je da shi ba.
Sallama ya masu tare da ihisani, inda Wasu daga ciki suka raka shi zuwa airport.
A can ya hadu da Sury a airport ita ma za ta tafi Nigeria.
A tare suka hau jirgi, ta ji daɗin hakan har cikin ranta, Kuma ta kudirri niyyar sai ta bi Hilal har Gidansu .
Haka kuwa aka yi, sai da ya kira Faisal a waya akan cewa ya zo ya dauke shi. Faisal ya yi mamaki don bai sanar da kowa yau zai dawo ba, har da Papa kuwa .
Yaga Sury tsaye a gefensa tana kallonsa, bai kula ta ba, sai da Fisal ya zo ta ga ya nufi motar ta bi bayansa.
Faisal ya rungume shi cike da farin ciki yana masa Barka da zuwa. Bai yabo ba fallasa ya amsa masa. Yana shiga motar ya ga Sury ta shiga baya, su suna gaba, da mamaki suke kallonta.
"Yaya wace ce ita?
Bai bashi amsa ba ya kalli Sury ya ce
"Nan ba US ba ne, kada ki yi kokarin kawo Mani shashanci a nan, ki fita kafin ranki ya ɓaci."
Sanin idan ba ta kwantar da kai ba ne za ta samu matsala da Hilal ya saka ta kwantar da murya.
"Don Allah ka taiamaka mani ba na da kowa a anan, kuma Dad ɗina ya ce sai gobe Direba zai zo ya ɗauke ni, ban sanar da zan dawo ba kuma ka san akwai nisa."
"Za ki samu Fly ai."
"Na fi son na tafi da motar ga yamma na yi."
Zai yi magana Faisal ya ce .
"Ka bar ta don Allah Yaya Gobe da safe sai ta tafi duk da ban san wani gari take ba."
Godiya ta masa ya ja motar suka bar airport.
"Ba na son kowa ya san ta zo har zuwa gobe da za ta tafi."
Ba ta so hakan ba ta so kowa na gidan ya ganta saboda wani dalilin na ta.
"Gakskiya ba zai yiwa ba ko da ka ce ta kofar baya na part ɗin ka za ka bi da ita ka san dai Mommy ta shigo dole za ta ganta.
"Eh na sani, ka bi ta baya mu sauke ta a garden ta jira sai na fito zan shiga da ita a part ɗi na, bayan Mummy ta fita, na san tai dole ta zo part ɗina."
"Amma Yaya me ya saka za ka sauke ta a part ɗin ka bayan ga..."
Kallon da ya masa ne ya saka ya yi shiru suka cigaba da tafi har suka karasa.
Kamar yadda ya bukata haka Faisal ya yi, ta baya ya ajiye motar, sannan Sury ta shiga garden ta zauna zaman jiran Hilal ba don ranta ya so ba.
Daga haka suka shiga cikin gidan. Faisal na ihun kiran mutanen gidan daya bayan ɗaya.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:57 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan ce)
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
Page5️⃣7️⃣
Daga haka suka shiga cikni gidan Faisal na ihun kiran mutanen gidan ɗaya bayan ɗaya.
Sai da Hilal ya dakatar da shi ne sannan ya yi shiru, don ya san Faisal zai iya tara masa mutanen gidan. Ga ji kuwa baya son hayaniya.
Ba wanda ya ji dawowarsa kasancewa kowa na part ɗin sa. Kuma Hilal ya hana Faisal ya masa gayyatar da ta yi niyya, shi ya sa bai sanar da kowa zuwansa ba ballantana su dame shi da hayaniya .
Part ɗin sa ya nufa, sai ya tuna Faisal zai iya faɗa sanar wa Mummy zuwansa. Don haka ya dawo ya nufi part ɗin Mummy gudun kada ta zo da tarar da Sury a part ɗin sa anjima.
"Assalamu alaikum warahmatullah"
Ya yi sallamar ciki-ciki kamar yadda ya saba. Bakinsa kawai idan ka kalla ne za ka san ya yi sallama amma ba wai don ka ji sautin sallamar Sa ba shi kaɗai ya ji kayansa.
Haɗa idanu suka yi da mahaifiyarsa, wacce kallo ɗaya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 39